Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi sai Yafendo Itace Yayarsa su biyu suka rage sai danginsu dake can Gombe state na Uwa Dana Uba,Yafendo itace ke rike da Husna.

Hajiya Hannatu Yar Uwar Su Yafendo ce Auren hadin zumunci akayi Mata da Shu'aib, mutanen kirki ne kwarai ga hankali da nutsuwa Amma akwai Saurin fushi, bayan sunyi aure da Shekara biyu Hannatu ta Haifi yarta ta farko Amina wacce yanzu Haka tana Auren wani matashin lecturer Ahmad a Kano Gadon Kaya yaranta biyu Mufeeda da Shahid, sai Yaya Kabeer Dan 29yrs sai Husna 16yrs,Nusaiba 13yrs sai autansu Aliyu 10yrs.
Amina Nurse ce yanzu schl of Nursing tayi tana aiki a asibitin murtala,Kabeer ya Gama Degree Yana aiki a ministry of Education,Husna tana Jss2 zasu shiga jss 3,Nusaiba tana Jss3 ita tuni kasancewar yanzu a birni tsallaken karatu akewa Yara Ana gaggawa,Aliyu Yana primary 5.

Yafendo itama Dan Uwanta Isah Affa take aure Suma hadin zumunci ne, sai dai Basu taba Haihuwa ba,Affa har aure aure yayi Amma Allah Bai bashi Haihuwa ba matan duk sun gujeshi Yafendo kadai ke sonsa Dan Allah ta hakura ta zauna Haka da abinta,ganin Haka Kaninta Shu'aib Matarsa tana Haifar Husna bayan an yayeta ya bawa Yafendo ita halak malak, Hakan ya jawo tsana tsaka nin Hannatu da Yafendo.

Na farko lokacin da aka Haifi Husna Hannatu tace Sunan yayarta za a sa Fateema, Yafendo tace Asmu za'a Sunan uwarsu, Baffa yasa Asmau Ana ce Mata Husna, daga Yaye Husna Kuma aka kaita kauye,Hannatu tayi bakin ciki an rabata da yarta,bayan Nan sai taga Husna tafi Kaunar Yafendo da ita shi yasa ta tsani Yafendo sosai sannan take nunawa Husna tsana,tunda Bata sonta to itama Bata damu da ita ba, Dukkansu suna zaune lafiya cike da so da Kaunar juna,Hannatu kadai ke nunawa Yafendo Tsana amma mutuniyar kirki ce duk abinda mijinta ya zartar yayi sabo da biyayyarta.

Husna da Yafendo tare da Affa suna kaunar juna matuka sabo da Shakuwa,yanda Husna take son Yafendo Bata son Baffansu da Ummansu Haka,Sam Bata damu da Yan uwanta ba sabo da Basu taso tare ba,Suma Haka Basu wani Saba da ita ba Sabo da ko tazo Hutu Bata da mutunci Basu Isa su sata ko su hanata ba,sai abinda taga dama,gashi ba a iya Mata komai baiyi ba sai nata shine dai dai,Mamansu tayi fada har ta gaji, tayi Nasiha Amma Ina,shima Baffa Haka har Addua sukeyi Allah kawo Wanda zai gyara Husna ta dawo normal,yarinya karama sai taurin kai ga tsatstsauran ra'ayi idan ta kafe a Abu Sai an Nemo Yafendo ko Affa sune kadai suke taka Mata birki,shi yasa basa shiri da Yan uwanta musamman Yaya Kabeer Bai son girman kanta yayi yawa ita gata dakikiya sannan Yar kauye Amma tafi Yan birni iya shege ko Dan tana da kyau da yawa ne shi yasa oho, ko kadan Kuma Bata da kawa sabo da baza su taba shiri ba,duk Wanda ya dauki Husna sai ya ajiyeta,Amma ta wanni fannin Kuma tana da halaye masu kyau sosai,Bata munafunci,gulma,Hassada,Tsafta da son kwalliya.
Wannan kenan.

Ci gaban labari.

Farhan Ne kwance cikin Palon Abbinsa Yana Hutawa,wayarsa tayi Kara ko kallon wayar baiyi ba sai da kyar ya dauka Yana Bata fuska gami da yatsina,ganin Ummana akan Screen ya mike Zaune ba shiri,cike da ladabi ya dauka kamar Yana gabanta Haka yake girmamata Yana gaida ta,ta amsa sannan tace 2wks yayi ka dawo gida kafin Raina ya baci,Afwan Ummana gobe Zan dawo Inshaallah, fuska ta saki sai suka Fara Hira irin ta Uwa da danta, Shagwaba yake Mata kamar mace Yar Auta.

Washe garin da wuri ya bi jirgi,4pm ya sauka a Nigeria,Nan take a Airport din yayi Sallah lokacin Umma ta iso da Driver tare da guards dinsu,Farhan da murna ya rungume Umman tasa kallonsa ta tsaya Yi sabo da danta nata Yana da kyau ba karya ita kanta tana jinjina kyawu irin na danta,Addua take Masa Allah ya bashi mace ta gari Kyakyawa shima, Ummana kallon fa? Ina Addua ne Farhan Allah ya baka mace ta Gari Kyakyawa wacce zata gyara min Kai ka Fara aiki kana zuwa Office,ka duba sabo da Allah Namiji Har Namiji gaka da son Neman na kanka ga dama Allah ya baka Farhan Amma kaki amfani da ita, wasu fa ka duba gasu Nan cikin talauci Amma Kai Allah ya baka kaki ka gode Masa,Murmushi yayi tare da cewa Ummana Zan Fara zuwa Inshaallah,ke kin damu Abbina kuwa ba ruwansa,To wannan uban naka wani mutumin kirki ne,Dariya ya saki ba shiri yace haba Umma akan ya Sakeki sai kina zaginsa kullum,shi Balarabiya yake so Mene laifinsa? Kai Ni muje ka daina min Zancen tsohon banzan Nan naka,duk sabo dakai naki yin aure Dan Kar na auri Wanda baya kaunar Dana,ai Ni Alhmdllh tunda yace ya bar min Kai ya tafi to Gashi Ai Balarabiyar Bata Haifa Masa ko Daya ba shima Dole sai nawan, muje Ni gida kaci Abinci ka huta,

wata budurwa ce Hadaddiya ta dau wanka Kyakyawa chocolate ce,cikin Arabian Gown light blue Tasha kyau, Ta gefen Ido Farhan ya kalleta kadan ya tabe Baki,Umma ta kalli Farhan tayi dariya tace ko tayi ne a tare maka ita? Fuska ya Bata me zanyi da ita Umma pls ki Bari wannan mummunar, Murmushi kawai tayi tace muje Farhan, bayan Ummansa yabi Yana dariya kasa kasa can suka Shiga motocinsu da uwar jiniya Kamar Gomna har gida.

Koda Suka Isa gida Abinci kawai yaci tare da wanka sannan ya gabatar da Sallar Magrib a masallaci ya dawo bayan yayi Sallar Isha ya kwanta saman Bed sai bacci.
Washe gari cikin shiri ya fito sanye cikin 3quater da T-shirt farare Kal ba karamin kyau yayi ba Yana zuba Kamshi,Umma ce ta kalleshi gaskiya yayi kyau Amma tana so ace ya Saba da manyan Kaya na hausawa Yana Masa kyau sosai duk da cewar duk shigar da yayi suna Masa kyau sosai Allah ya bashi jikin daukan wanka.

Farhan koma ka saka manyan Kaya na gaji da halinka sai dinki kake yi ko yaushe Amma baka sawa sai ka gaji dasu ka bayar dasu kullum cikin Kanan Kaya Kamar ubanka Bature ne, Dole ya koma ya sake shiri cikin Shadda Yar gaske Fara Tasha dinkin zamani sannan Umma taji Dadi ya zauna Suka ci abincinsu sannan ya figi motarsa ya bar gidan.

Husna yau sun kusa Fara exam daga ita za a canja musu aji Wanda lokacin Baffansu zai zo ya dauketa zuwa birnin Kano taci gaba da karatu a can tunda Yana da rufin Asiri ci da Sha sutura Bata gagara ba,motar Baffa Daya ta me karamin karfi sai ta Ya Kabeer karama wacce gaba Daya gidan da ita suke amfani,sai Haj Hannatu itama tana da Tata Yar kwakura.
Daga Makaranta Husna ta dawo da sauri ta wuce bedroom dinta bayan ta kwada sallama,Yafendo tana kallonta ta cire Uniform ta fito sannan tace me kika dafa? Yafendo tace dafadukan shinkafa,fuska ta Bata yanzu Yafendo Dafadukan da Kika Saba ita kikayi kin San fa bana sonta.

To ai ke ba a iya Miki Mijina yace ita yake so sai na bi son ranki idan baza kici ba ga Indomie Nan babanki ai sun kawo ki dafa kici,aini kin San ba ruwana da wata Indomie yaushe zata daukeni,tumbina yafi karfinta Ni dai ki dafa min wani abin ko kuma Allah na kwana da yunwa yau, Yafendo ta kalleta tace karki ci kinji ki kwana da yunwar cikina ko naki? Gefe Husna ta koma tace Allah yasa ma an kusa daukana daga wannan kauyen,na kusa barin Nan gidan naje can na huta Nan sai gallaza min azaba akeyi Haka kawai,baza ku Kara ganina ba idan na tafi,zanje can naji Dadina a birni nayi abinda na keso,kullum abinci Babu Dadi,Yafendo tana jinta ta dakko katuwar sanda ta nufi inda Husna take,da gudu Husna tayi waje tare da barkewa da kuka ta cika unguwar da ihun kuka,mutane suna ji sukace Husnan Yafendo ce sabo da Ana Jin kukanta an San itace kullum sai ta damu mutanen gari.

Affa ne ya dawo ya Iske Husna tana kukanta a kofar gida ta rabe jikin bango tana matse kwalla abinta tana ganinsa ta Kara Volume ta saki Jiniya, da sauri Affa ya rike hannunta Yana lallashi don idan da sabo ya Saba yasan Yafendo ce Dan Haka Bai ko tambaya ba yasan dafaduka ce Bata ci, kudi ya zaro Naira dari ya damka Mata yace maza jeki bakin kasuwa ki siyo abinda kike so kici, Doya da kwai nake so Kuma Naira Dari kacal tayi kadan Affa baza ta isheni ba,kasan katon tumbi gareni, dariya Affa yayi sannan ya Kara Mata kudin ya Zama dari biyu Da Gudu ta tafi tana dariya ba Kuka sai da tayi nisa tace na gode Affa Zan dinga zuwa Hutu sabo da Kai idan na tafi Birni.

Girgiza Kai Affa yayi kawai Yana dariya shi Kam Yana kaunar Husna yarinya ce me shiga Rai,ganin Husna Ta shigo gida da ledar Doya da kwai me yawa,Yafendo tasan Affa ne ya Bata kudin,Yafendo ta dinga fada kamar me,Husna ba ruwanta ko a jikinta ta zauna jikin bishiya taci ta koshi sai da ta cinyeta tas duk uban yawanta, Randa ta bude ta Sha ruwanta sannan ta wanke hannunta tayi Alwala da Sallah.

Har wanki da guga Yafendo kewa Husna, Haka kitso da komai ita ke Mata Bata komai sai makaranta sai taci abinda take so ta kwanta ta kwashi bacci,zasuyi jarabawa amma Taki yin karatu ko kadan.

Yau Monday yaune Husna ta fito uniform yasha wanki da guga zasu Fara jarabawar karshe,Yafendo ta kalleta tana murmushi tace Yan Mata Haka ake jarabawar ba karatu? Husna ta Ware murya Kamar tana fadawa makwafta Maganar tace Haba Yafendo karatun banza ai Da ka zamu daketa Dan ubanta jarabawar, abin Nan sa'a ce fa ba wani karatu dake sawa a aci kawai Suma masu cin ai Haka Allah yayi musu kwakwalwarsu komai sun iya,ni ba gashi da bani da Sa'a ba a kauye aka ajiyeni na taso Ina Shan ruwan Rafi,tuwo, Abinci me Dadi a baka shinkafa ko fura,Allah su Mama sun Gama Dani,miyar kuka ta Gama kashe min kwakwalwa,Yafendo da badan Allah yayi Ni me kyau ba ai da tuni bazan ganu ba,idan nayi karatun ma ba ci zanyi ba Gwara na tafketa da ka.

Yafendo Murmushi tayi tace kuruciya kenan Amma me kikeyi a gidan Nan? Me aka rageki dashi? Ruwan zafi ma Baki iya dafawa ba,nayi nayi ki koyi girki kinki komai Baki Iya ba Husna Haka za ayi Miki aure ko Haka Kika ga anayi? Duk garin nan kinfi kowa gata da Hutu,Dariya Husna tayi Hhhhh da karfi tace yo Allah na tuba Ina Hutu anan? Me nakeyi na Jin Dadi? Nifa Yafendo na gane nufinki so kike na yabe ku nace Kuna min abinda nake so,to ai ban ji dadin ba da zance kunyi kokari,yanzu sabo da Allah ki duba kanne na da yayyena Haka suke? Yan gayu ne su,nifa? Na tabbata da za a gwada jinina to cututtuka ne birjik duk sun shigeni, Talauci yasa Allah ya rufa min asiri baza su tashi ba Amma da zarar nayi kudi zasu tashi su Karar da arzikin nawa kawai kun jawo min.

Sanda Yafendo ta dakko ganin Haka yasa Husna ta fice da gudu ta tafi schl,Yafendo kuwa dariya ma Husna ke Bata Dan Bata San ta duniya ba shi yasa take fadan Haka Amma suna Nan idan taje birni sai ta dawo garesu sabo da Hannatu Uwarsu tana da zafi Kan Yara Bata son Shirme yanzu kaci ubanka,Baffan ma Haka yake don zai iya korar Husna daga gidansa,ba wahala yace da yaro ya bar Masa gida.

Ko da Husna ta Isa schl sai ta ji kowa Yana fadar irin karatun da sukayi,Baki ta tabe kawai ta koma gefe tana ta wasanninta littafi ta dakko text book me dauke da Hotunan Cartoon Bata iya karantawa ba sai dai ta dakko tana kallo kallo tana jin Kamar ta shige cikin zanen itama,wata Kawarta ta nunawa Halima kalli matar Nan tana tafasa ruwa a tukunya kalli Dan dakinta me kyau wayyo Ina ma Zan shiga ciki,kalli gona Ana Noma me kyau,Wannan dakin Kamar dakin Yafendo Ina ma a ciki aka halicceni dafa sai dai ku dinga kallona Nima ko? Halima tayi dariya tace Nima Haka nake ji,Halima tana da kokari sosai sabo da Haka ko da aka zo exam kusa da ita Husna ta zauna suna rubuta amsa Husna tana copying.

Husna kullum idan aka zo Exam a ta Halima take satar amsa sai gashi da suka Gama Exam har tafi Halima cinyewa,Halima tazo ta shida Husna ta Hudu tazo,kowa yayi mamaki har malaman sabo da an San Husna ko kadan Bata da kokari.
Shine Karo na farko Husna ta Dole ta zauna cikin masu kokari ta sace musu amsa kaf,da murna tazo gida ta fadawa Yafendo tana kuri ai na fada Miki Yafendo nima akwai kwakwalwa,shi yasa nace Miki nafi karfin karatu gashi Dana daketa da ka na cinye,Dan ubansu malaman ai sunga Ishara sai dana tace musu kwakwalwa,ai Ni shegiya ce Yafendo Dan Baku sani bane kowa Yana Raina min hankali,ko Gobe Baffa yazo yaga result me kyau Ni za a fadawa kokari.

Yafendo Bata San sirrin ba ta dinga murna ita da Affa,murna sukeyi suna yabon Husna ita Kuma sai kuri takeyi, Yafendo tace ai har dinki Zan Miki idan zakije birni,Affa yace ni Kuma kudin kashewa zan Bata ai Kinyi Abun kirki Husna sai a Kara dagewa.
A garin kuwa Husna ta dinga yanga tana shiga ko Ina tana yanga ita tayi kokari bayan tasan ita kanta copy copy tayi, wasu da yawa tunaninsu Sabo da baiwar kyau da Allah yayiwa Husna yasa take Iyayi bata kula kowa a kauyen.

Tun a waya Baffa da Maman su Husna Suka samu labarin wajen Yafendo cewar Husna fa ta cinye jarabawa tayi zuciya tayi kokari,Baffa da Mama Hannatu suka dinga Murna da kwarin gwiwa Baffa ya turo Ya Kabeer yazo ya dauki Husna zuwa birni.
Bata son Birni sabo da Raina Mata hankali da danginta keyi wannan dalilin yasa Husna take so ta koma can itama ta waye, Sannan duk kokarin su Yafendo da keyi a kanta Bata gani sabo da hadama irin ta Husna.

Yafendo ta kalli Husna yanda take zumudi tace aikin banza Zaki dawo ki sameni marar godiyar uban giji duk samarin Nan naki ai gwara da Zama Kika yi ko Mudi sai ki aura sabo da shi kadai ne na kirki,Sabo da bakin jininki samarinki daga tsofaffi sai nakasassu Mudi shine kadai malamin makarantar Islamiyya,budurwa har Shekara Sha shida Babu masoyan kwarai.
An sosawa Husna abinda ke damunta Nan take ranta ya baci to ai Dan Ina kauye ne ki Bari ki gani na koma birni yanda maza zasuyi rubibina suna Haka suka tsinci Sallamar Yaya Kabeer.

Kyakyawa ne wankan tarwada Dan gayu dashi,Ina yini kawai Husna ta ce Masa sannan ta kirawo Affa Dake dakinsa tana yiwa Yafendo mita duk an bi an lalatani a kauye,gaba Daya rayuwa ta kauye tasa bani da Sa'a komai me kyau bazai zo wajena ba,Haka abinci daga dambu sai tuwo,su danwake anci me Dadi a dafa shinkafa dafaduka,birni kuwa nama,Kifi,miyarsu tasha Mai,ai wlh gwara na koma,dinki ma ba me kyau ba da akewa mutum,a birni kuwa sai an Dame an tsuke duk da bana son mutanen birni gwara na koma Nima.

Affa yace sai kizo Mana hutu ko Husna?,ae wlh Affa Ashe ka gane idan ba Dadi zan gudo kauye Yafendota sai dai kiyi hakuri idan da dadi baza ki ganni ba sai dai ku dawo birni kuma.
Dariya Yafendo tayi tace yarinya Zaki fada Mamanki zafi gareta Bata daukan Iskancin yara Haka Baffan ma,Kabeer Yana jinsu Yana dariya,har Husna ta shirya taje tasa akwatinta a motar sannan Yafendo da Affa suka rakasu har mota,Allah sarki sabo sai ga Yafendo da Husna suna kukan rabuwa,Affa da kb suna Basu Baki karshe Husna tace Zan dinga kiranki Yafendo ta,Affa kaima Haka,Idan kinji ba Dadi ki gudo gida kinji cewar Yafendo,Husna tace da wuri ma zan tsero suka rabu suna dagawa Juna hannu.

Tunda Suka dauki Hanya Husna ke sharbar kuka,Kb ya kure Vol din motarsa Yana Jin waka har tayi bacci, Bata farka ba sai da Suka shigo garin Kano Husna taga city jama'a Ana hada hada ko ina, Kamar abin kirki tace Ya Kb sauke min glass din window kasa zan tofar da yawu,Bai kawo komai ba ya sauke mata, sai da ya shiga Goslow basa tafiya aiko sai ta zuro kanta waje tare da hannunta kamar Yan jagaliyar Siyasa masu campaign ta Ware murya iya karfinta tace Salamualaykum Jama'ar birniiiiiii...., nice Husnan Yafendo gani na dawo Birni Nima....gaba Daya ba hutu nazo ba na dawo nan nimaaaaaa.....kamshin Birni dadine dashi kunyi mana wayo Muna Kauye...Yan Kano gani nice Husnan Yafendo na dawo birniiiii....yeeeeeeeh..saukar dukan Kb taji a bayanta Tasss bayan hankalin mutane da dama ya koma Kan Husna ana kallonta wasu Wanda suke kusa suna ta dariya harda masu Saida pure water da sauransu.

Komawa tayi ta zauna tana washe Baki tace ai ko Marina kayi ya kb bazan jii zafi ba Tunda na dawo Birni Allah sarki Ni an cuceni aka kaini Kauye to Alhmdllh Dan bakin ciki sai dai ya mutu na dawo Birni, kb Yana jinta tana ta surutunta dariya ma take bashi,suna Goslow again sai ga motocin Farhan sun Danno Yana ta sauri zai koma Abujansu dama bikin wani frnd dinsa ne ya kawoshi Kano.
Motocin sun Kai guda takwas suna jiniya Kamar Gomna ne, motocin manyan masu kyau da tsada musamman wacce Farhan yake ciki abar kallo ce,masu mota sai Hanya ake bashi,har suka shigo saitin Motar su Husna.

Husna ba godiyar Allah sai tace wayyo kalli motoci masu kyau, Anan ake motoci wlh ba irin namu ba kwakwurar banza,mota kamar ramin gafiya kai ya Kb har wani dadin shiga wannan motar kakeyi kalli ta waccan mutumin haduwar duniya.

Kb yasan Halin Husna ko kulata baiyi ba sai ta dauki Robar ruwan data shanye faro ta Kara fito da Rabin jikinta waje ta window motar, motar da Farhan yake ciki wacce tafi ta kowa kyau ta jefa Robar a glass dinsa,Tasss yaji Kara Allah yasa baiyi komai ba,ba shiri suuuuu ya sauke Glass Yana kame a bayan mota Yana latsa waya yace driver waye Haka? Driver yace wlh wata yarinya ce Oga da gani Bata da tarbiyya.

Kadan Farhan ya leko da kansa waje shima ya hango Husna rabinta a waje,kyawunsa data gani yasa ta sandare Amma duk da Haka sai ta share, da karfi tayi dariya tace Malam motarka tafi Tamu kyau,ya akayi Haka ta faru bawan Allah? Kalli akwalar Tamu Amma a Haka Yayana har iyayi yakeyi a cikinta,Wai Kai me kudi ne? Harara Farhan ya watsa Mata Ganin yarinya ce ya koma abinsa,bayan ya daga glass dinsa ta Kara daukan Robar lemo ta jefa Masa a glass a fusace ya sauke Glass din kasa Amma Bai ko leko ba,Yana jinta ta mota tana Kai me Sa'ar Rayuwaaa....Malam...Ni bani da Sa'a,sunana Husna na dawo Birni da Zama Nima,Ina can kauye Ana ta cutata, Aikuwa na Zama dakikiya infada maka sai gashi ba shiri Baffa ya dawo Dani birni yau din Nan aka dauko Ni.

Me Sa'a kasan me?Yafendo Bata dafa Mana Abinci me Dadi sai tuwo ko dafaduka, jarabawa na zana yafi sau ashirin bana ci,Aiko na daina karatu na daki shegiya da ka sai gashi na cinye, Mamana da Baffa suna Birni suk... ....Mari Kb ya watsa Mata ba shiri ta zauna ta nutsu tare da fashewa da Kuka.
Shiko Farhan Yana jinta Yana ta dariya Dan shi rabon ma da yayi Murmushi ya Dade sai yau Daya hadu da me tabin kwakwalwa cewar Farhan a ransa.
Goslow na karewa kowa ya Kama gabansa.






Free page masu son ci gaba dari biyu (200)fans







AsmaBaffa
[2/29, 10:43 PM] Sis Asma: πŸŒ…πŸŒ…RASHIN SA'AπŸŒ…πŸŒ…










3









Official






By
AsmaBaffa









FAHEEMAH,DIYAR KATIBI AND KHADIJA A HAMZA
Page naku ne.

Ina gaisuwa fans,pls a dinga Sharhi Dan na Samu Jin Dadin typing.









Dan madaidaicin gida Suka shiga dake rijiyar zaki a garin kano, Gidane da gate dinsa me Dan kyau dai dai na rufin Asiri baza ace talaka ba baza Kuma ace gidan me kudi ba,motar Mama Hannatu da Baffa suna gidan kalar rufin Asiri Suma,Kb ne ya fita tare da bude gate din da kansa kasancewar Babu me gadi,Bayan yayi parking Husna da hawaye a idonta ta fito tare da zarar akwatinta dai dai lokacin Nusaiba da Auta Aliyu ne Suka fito da gudu tare da Rungume kb Husna tana kallonsu ko kulata basuyi ba,Nusaiba ce ta gaisheta da kyar Aliyu ma Haka,Husna kuwa ko kallonsu Bata yi ba ganin suna kallonta suna dariya yanda take sanye da atamfarta Riga da Zani dinkin kamar na tsofaffin Mata tukuf,kafarta slifas ne tun irin na da,Haka ta daura dankwali ta wani zamge kanta dam dam,ga wani jambaki ja data dambara tare da yin gira shafceciya Kamar Yar tallan kauye Haka ta fito,Husna tana ganin ta kure adaka ta Gama kece raini babu kamarta Amma suna Mata dariya a matsayinta na jininsu.

Palon suka shiga komai dai dai na rufin Asiri Amma Husna sai kalle kalle takeyi kamar Bata taba zuwa ba,Mama Bata Dade da dawowa daga wajen aiki ba,kallon Husna kawai takeyi yanda ta kama jelar Dankwalinta tana ci ga kalle kalle tana faman Yi Bata ji bata gani,Tsawa taji Mama ta buga Mata,tayi matukar razana sabo da Bata Saba ba Yafendo bata Yi Mata Haka,Ba Shiri ta durkusa kasa gaban Mama tana Ina yini,ta wani rakube a gefe,Mama tace mu a Nan ba a Mana hauka ki kiyaye ba kowanne Nonsense nake dauka ba, Husna tayi lakwas sannan Mama tace tashi kije dakinki gashi can kafin nazo da kaina Zan Miki wanka wannan gashin naki ban yarda dashi ba tun kafin kisa mu dauki kwarkwarta,Husna mamaki Yana cikata Akan me Wai Mama ta tsaneta,Kamar ba itace ta haifeta ba Dalilin hakan Yan uwanta duk suke Mata wulakanci,sai yanzu taji inama Bata zo ba Amma ba yanda ta iya,Sai ta Shiga dakin da akace nata ne ita kadai,gado ne Karami da sip sai mudubi sai Kuma toilet a ciki komai yasha tiles da Tsafta Yana kamshi, dama ta taba zuwa Hutu sau biyu tasan komai,Alwala tayi tare da gabatar da Sallah tana jira Mama tazo ta Bata Umarnin wanka.

Abinci me aiki ta kawo Mata Sakwara da miyar kwai,Aiko taci ta koshi tare da Hamdala Amma sai yace miyar ma ba wani Dadi karni, sannan ta kwanta sai bacci ya kwasheta,Bayan ta tashi a baccin Mama tazo ta wanke Mata gashi da kanta sannan tayi wanka da kanta ta fito kenan ta Iske Mama ta kwashe kayanta da ta zabo masu kyau sababbi na zuwa birni an zuba su a Dustbin harda sabuwar atamfarta da Yafendo ta dinka Mata ta Dalilin cin jarabawa, da sauri Husna ta yo waje daga ita sai towel ta zazzage sharar gaba Daya a kasa sannan ta dauki ledar kayanta Allah yasa a Leda aka saka kayan sannan

Please Login or Register in order to submit comment