Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta bani Breakfast kenan ko kike nufi? Jiki na rawa Husna ta mike tana Ina Ina bar..Bari..nayi maka kayi hakuri Dan Allah karka Dukeni wlh Marin dazu sai da Naga Wutar lahira, Harararta yayi ya fice, da sauri itama sai kitchen.

Palo ya dawo Yana jiranta,yaga Fuskarta yanda tayi jajir ta kumbura Amma ko tausayinta Bai ji ba,yace Good Gobe ma ki Kara fada min magana,Chips and Egg kawai ta hada Masa sai tea ta kawo Masa,yace ae yanzu na gane so kike cuta ta kamani kusan kullum sai kin min abinci da kwai idan asarar kudi kikewa mutane a school a Cireki gaba Daya.
Da kallo Husna ta bishi kawai tace kayi Hakuri Bari nayi wani,ba Imani yace Better, Yana gani ta kwashe abincin ta bawa masu aiki ta Fara shirya sabo sai data hada Kala uku na zamani Wanda ba kwai,ta kawo gabansa tana murna da fara'a tasan Dole ya yaba,ya bude tare da tabe Baki yasa kafa ya ture tire din bana cin wannan duk nama a ciki hada min tea kawai ya isheni,Husna taji Haushi Tasha wahala tayi Masa Bai ci ba,ai da yaci da taji Dadi masoyinta yaci wannan girki data tsara Masa.

Gabansa ta Tsuguna tana kallonsa,shi kuwa ya harde kafa Yana Danna wayarsa ko kallonta bayayi, a hankali Kamar me rada tace pls Forgive me, I don't mean to Hurt u, I take back my words, I'm so sorry If i Upset u, yayi mamaki da Jin yanzu tana iya hada kalmomi In English da wuri Haka ba tare da an dauki dogon lokaci ba,sannan gashi ta damu da cikinsa Dole sai yaci abinci,Kuma tasan dazu tayi Masa laifi duk da ya daketa Bata ji haushi ba tana bashi Hakuri,a Matan yanzu na zamani ba kowacce ce zata iya ba gaskiya,musamman zamanin Nan da kowa idan akayi Masa abun zafi sai yace bazai hakura ba bazai kyale ba sai ya dauki mataki ya Rama Dole,irin wannan shi ke jawo aikin Dana sani Saurin fushi da kin yafiya.

Harararta Farhan yayi duk da Haka Yana kallonta ta Kara marairacewa Kamar zatayi kuka Kwalla ta cika Mata Ido,suna hada Ido tace pls kaji..kansa ya dauke gefe sannan yace Serve me da kyar Yana Bata Rai,Allah sarki farin ciki ya cika Husna tana Murna tace tanx, tana zuba Masa Yana mamakin yanda take uwar murna, suna cikin Haka sai ga Salma ta shigo cikin wani Danyen lace Green tayi kyau, Amma Husna tafi ta kyau a shigarta,Ko kallonta Husna Bata yi ba har ta Gama zubawa Farhan abincin ta mike tayi kitchen,Salma taja uban tsaki tare da furta Ya Farhan wlh na tsani matar Nan taka Yar wulakanci ce,baka gani tana kallo na ko kallo ban ishe ta ba bare ta gaishe ni, Farhan ya kalli Salma kawai ya tsani rashin tarbiyarta Bata San darajar mutum ba Sam,yace Ke da kike me kirkin ba sai ki gaisheta ba ai Aunty dinki ce yanzu tunda matata ce,last warning karki Kara zaginta wlh Kika Kara zaginta ko da Wasa naji sai kin bar gidan Nan Kuma kin San zan iya? Allah sarki Husna tana kitchen ta boye kanta sabo da Bata son ganin Salma kusa da mijinta tasan Kuma yanzu Zama zatayi tana gugan jikinsa,Hawaye ne ya cika Mata Ido,zuciyarta tana harbawa da karfi,kasa jurewa tayi ta fito, Bata san Farhan ya tare Mata fada ba tana kitchen.

Tana Fitowa Suka hada Ido da Farhan,da Sauri ta janye idonta a cikin nasa,ta kalli Salma wacce ta zauna Rabin jikinta Ana Farhan tana ta damunsa da labaran Shirme gani take hakan shi zai sa ya so ta,Spoon din Daya ke cin abinci dashi ta dauka itama ta ebi Abinci zata ci tana Bari muci jagwalgwalo kafinta ta Kai bakinta Husna ta fisge spoon din ta jefar dashi da abincin data ebo ya fancakale a kasa.

Wani spoon din ta dauka a tire din ta canjawa Farhan tana Hararar Salma,Salma ta mike cike da bacin Rai zata damki Husna,Farhan ya daka Mata wlh Kika taba ta sai kin gane kurenki a gidan Nan,tasan Halin Farhan zai iya sa securities su zaneta tas kawai sai ta bar part din cike da takaici tace wlh ya jawo Mata masifa sai na tozarta Husna,sai na Mata illa.
Husna yau Farhan ya Gama Mata komai taji Dadi sai ta tafi Bedroom dinta cike da murna ta fada saman bed tana ta tsalle tana wooo Ni...wooo Ni...

Bayan wani lokaci kadan Haka kawai Baffa yaje ya Rubuta retire da kansa takardar barin aiki,shi yarsa tayi kudi Allah ya hore Masa yanzu ya kusa Zama me kudi saura kadan, abokansa sukayi ta bashi shawara yace shi yafi karfin aikin Gomnati yanzu bare wani principal Allah ya kiyaye Masa.
Bayan kwana Uku tsakani Baffa ya matsawa Husna shi da Mama Lallai ta Fara turo musu wani abu ta account ko ba yawa,
Husna ta fito Palo zata Yi kallo ta iske Farhan kwance yana aikin nasa wato karanta jarida, plate din gabansa Daya Ci snacks ta kwashe ta Kai kitchen masu aiki suka wanke tare da gyara ko Ina,tana Palon tana kallon wani series jefi jefi tana satar kallonsa, wayarta ce tayi Kara,tana dubawa gabanta ya Fadi Ras,Sunan Baffa ta gani,Taki dagawa,ta Kara ringin Karo na biyu har ta katse Bata dauka ba,Ana ukun Farhan yace kina disturbing dina, idan ta tashi zai ce Bata da gaskiya ko ya zargeta shi yasa Kawai sai ta daga tace Ina kwana Baffa? Baffa ba gaisuwa ba komai yace ba gaisuwa ce ta kawo ni ba.

Mene ne a kasa yan zu? Me Kika Tara ya kamata naji Alert me zafi, Husna tace yanzu Baffa baza ka hakura ba? Ke bafa na Wasa dake kin sani wlh matukar Baki turo komai ba zuwa Nan da kwana biyu to sai na raba auren Nan Dole, kayi Hakuri Baffa,Bazan Hakura ba Ni Zaki mayar Dan iska, Husna jin za a rabata da Wanda tafi kauna a duniya Farhan tace ba komai Baffa zaka gani Inshaallah, ya dai fiye Miki kit ya kashe wayarsa,ajiyar zuciya ta sauke Wanda sai da Farhan ya kalleta,Tagumi tayi kawai ta dafe goshinta tana tunanin Ina zata samo kudi ta turawa Baffa,Sadakinta ma Dashi aka Yi Mata wasu abuwan kafin ta tare ragowar ta barwa Yafendo da Abba Su,yanzu ya zata Yi kenan.

Farhan Yana satar kallonta ta zuba Tagumi yarinya karama tana faman tunani haka,Husna Bata Iya tura komai ba Kuma Bata fadawa kowa ba har kwana ukun da Baffa ya ibar Mata ta cika,tun daga wannan ranar Bai sake kiranta ba har sauran Yan uwanta ta kyalesu itama sai jefi jefi take kiransu idan Basu ga dama ba ma baza su daga ba.

Yafendo Husna ta Kira a waya tare da sanar Mata abinda ke Faruwa,Yafendo tana mamakin Shu'aib mutumin kirki shi da Matarsa Amma akan Abun duniya sun lalace da son Duniya, Husna tana Hawaye tace kina ji na Yafendo yanzu ya zanyi dasu? Numfashi Yafendo taja tare da furta ki kyalesu zanje har gida nayi Masa fada,Da Sauri Husna tace Dan Allah Yafendo ki rufa min asiri karki ce na fada Miki ki kyalesu idan Kika fada Baffa zai Kara Jin Haushi na,Haka ne Husna Sai mu dage da Addua ai Basu karfin Allah ba,idan ba sakarai ba yarka ta cikinka akan kudi kace zaka Raba auren cewar Yafendo,Hawayen dake fuskar Husna ta goge tare da cewa Sai munyi waya Yafendo ta kashe wayar tare da kwanciya a saman Bed ta Lula tunanin Ina zata samowa Baffa kudi,Dabara ce ta fado Mata kawai ta siyo asusu ta daina kashe kudin break dinta a schl tunda Dubu Daya Kullum Umma ke Bata,sannan duk sati Umma na Bata kudin saloon dana wasu Abubuwan kawai sai ta dinga Tarawa har ta hada masu Dan yawa ta tura musu.

Sunday yau Salma sukayi waya da Asiya kan zata koma Kano akwai sabon plan ya samu na yin maganin Husna Tunda Yanzu Bata ji komai ba,Rana tsaka Salma ta shirya tsaf tace Baba ne yayi Mata waya Lallai ta koma, Umma ta Bata kudade ta wuce Kano.
Koda Baba yaga Salma ta dawo gida, kyaleta kawai yayi tare da zura Mata Ido a ransa Yana tunanin hukucin da zai Mata.

Friday Misalin 5pm Farhan ya dau shegen wanka cikin wata Shadda Saka Fara,dinkin zamani Hannun links gashinsa ba Hula yasha gyara Yana kamshi da walwali Kamar sabon Ango, Husna tana sama Bedroom dinta tana jikin window tana gyara Labile n window dinta ta hanko Farhan Yana taku dai dai cike da takama Kamar wani sarki, ya Kara waya a kunnensa da Alama waya yakeyi ya nufi parking space nasu Securities da masu aiki duk sun mike Sai gaisuwa suke kwasa Yana raba musu kudi dama ya saba raba musu kudi duk ranar Friday.
Cike da kauna Husna ke kallonsa tana zuba Murmushi,a fili tace Bari nayi tsokana,da sauri ta bude kofar Corido dinta ta saman, da karfi tace Ya Farhan,da Sauri ya juyo tare da kallon Inda yaji Kiran,Ido Biyu sukayi da Husna ta daga Masa hannu tare da cewa a siyo min Ice cream,ta bashi dariya kamar Yar yarinya Haka take tsale tana daga Masa Hannu,sai yaga tayi Masa kyau Amma ya shareta Kamar Bai ji ba ya shiga mota Driver ya ja shi, yau a mota Daya ya fita.

Bayan Sallar Isha Husna ta cakare cikin Shadda peach color tayi dauri Kamar wata Amarya Haka ta hakimce a Palo tana kallon Film ga Littafin English a hannunta,Door Bell taji ta mike tare da lekawa ta Yar kafa taga Farhan tsaye,sai data gyara rigarta tare da daurinta sannan tana murmushi ta bude kofar, sai da yayi Salati a ransa tsabar kyau da Husna tayi Amma a fili sai ya tabe Baki ya wuce ciki abinsa hannunsa dauke da Ledar ShopRite, kofar ta rufe ta bishi da sauri tare da cewa Sannu da dawowa, Harararta yayi sannan ya Mika Mata ledar gashi Nan nasan wannan kike bi.

Karba tayi ta bude da sauri taga Ice cream roba biyar manya tare da wani gashin Kaji,Farin ciki ya kamata yau Farhan da Hannunsa ya siyo Mata Abu,ta bashi sautu Kuma ya siyo Mata gaskiya Yana da mutunci, tana murmushi ta kalleshi Ido cikin Ido tace Amma kuwa Allah ya maka Albarka Dan Nan,ka Gama min komai,sai da yayi Dana sanin siyo Mata tunda tace Masa Dan Nan, Kamar danta tsaki yaja tare da Haurawa sama,Husna Kuwa guda Daya ta dauka tare da Kazar ta Kai sauran Fridge,ta zauna a Palo ta baje kafin ta Fara ci sai ga Farhan ya fito Palon ya zauna tare da kamo Chanel din BBC news, Yana kallon Husna ta gefen Ido kamar an biya Mata makka sai Murna takeyi ita kadai.

Kazar ta Kama tace Bismillahi da Kirjinki Zan Fara ta ballo kirjin tare da cewa Mun godewa Allah daya yarje Mana muci kaza tayi Bismillah tasa a Baki ta wani daga Kai sama tare da lumshe Ido kamar me Suma,ta ebo Ice cream ta Sa a bakinta, Haka kawai ta saki Kuka Farhan a ransa yace to me akayi Mata Kuma,kafin ya Gama tunanin me yasata kuka yaji cikin rawar murya tace Dan Allah Muci gaba da sauke Hakkin aurenmu kaji, da kallo Farhan ya bita Yana bukatar Karin bayani Dan Bai gane Nufinta ba,sai ko yaji tace Allah sarki da tuni Baffa ya aura min Tijjani Ina can Ina sharbar miyar kuka koriya Shar, Dariya ta bashi ya Shiga yinta ba shiri tare da cewa waye Kuma Tijjani?

Husna tace wani Dan abokin Baffa ne in fada maka Allah kansa Kamar Murhu,Ina ma an aura Masa ke cewar Farhan,da Sauri Husna tace ta Allah ba taka ba ina Zan Kai kansa yazo Yana mirgina min shi a Kan gado, Dariya Farhan ya dinga Yi ,Husna ba Wasa tace Allah ka daina dariya da gaske nake kansa kadai zai kai killo 65,kaga Marin daka Yi min rannan to Ina tabbatar maka da Tijjani ne sai an kaini asibiti ko gawata.

Tijjanin Yana zuwa zance ne time din kina gida? Farhan ya tambaya Yana Dariya,Husna tace yo Ni Ina na San zance yazo wajena lokacin bani da hankali kafin ka aure Ni, idan yazo gidanmu yayi ta min Signa Nayi tunanin ma Harara ta yake Ashe Wai kallon so ne,Farhan yace Allah sarki Tijjani na tausaya Masa,tun Yana amasawa Husna Hirarta kadan Kamar Wasa Hira tayi nisa tana ta bashi dariya sun Dade yau suna Hira.

Sai da ta koshi da naman sannan tace na manta Kai baka ci ba? sai da Kika Gama jagwal gwalawa Zaki bani na koshi.

Misalin Karfe Daya na dare Husna tana bacci kawai sai Hayaniyar mutane taji a kanta da Salati ta mike a firgice tana salati,jikinta ya dauki rawa Kamar mazari ganin wasu yan daba sun Kai su Goma a kanta Babu makaman da babu a hannunsu,Tsawa Suka daka Mata tashi muje ko mu yankaki
yanzu,ba tare da tace komai ta mike tare da daura katon Hijab da Zanin atamfa a saman bingilar rigar baccinta, muje Suka sake daka Mata tsawa, ta saki kuka tana Basu hakuri, suna Fitowa Taga Farhan sun Shaka Masa Powder ta bacci ya Koma Kamar matacce,Kuka ta saki tunaninta sun kasheshi,ganin zata Tona musu asiri itama Suka Shaka Mata a hanci ta zube kusa da Farhan,Gaba Daya Suka daukesu tare da Sasu a mota suka ja motocinsu tare da barin gidan a tamanin.

Tun daga Kan Yan aiki,zuwa securities da Umma gaba Daya sai da Suka Fara yin sihiri da surkulle na abin Bacci ta hanyar dabaru irin na Yan ta'adda sannan kowa ya Fara bacci Kamar na mutuwa sannan Suka nufi part din Farhan,kowa a gidan bacci yakeyi ta hanyar asirinsu da sukayi a gidan.

Bayan kwana daya Farhan ya Fara farkawa daga dogon baccin Powder, ya ganshi cikin wani daki Kamar akurki me tsananin duhu,Husna tana gefenshi tana bacci Bata farka ba,Abinda ya faru jiya ne ya dawo Masa kwakwalwarsa,Yana cikin halin tunani da mamaki waye yayi kidnapping dinsu Husna ta farka da kuka tana Kiran Ya Farhan wayyo sun kashe min Mijina Allah ka ceceni, ke Yi Mana Shuru ba gani kusa dake ba,Da Sauri Husna ta fada jikinsa cikin duhu ta rungumeshi tana kukan farin ciki Basu kashe Mata Abin kaunarta ba, Waye ya sato mu Ya Farhan?, Sosai ta Kara shigewa jikinsa tsoro nakeji Babu haske,Bai hanata ba Kuma Bai ce komai ba.


Rashin Sa'a Naira dari biyu ne(200) ga masu bukatar siye.


Masu son siye ta Bank ga accnt number 2177560408 Yahaya Garba Muhammad, Zenith bank.

Masu son tura number Kati MTN ta WhatsApp ko Sms ga number
08033933642

Masu son siye ta hanyar yin transfer kati ko Vtu ga number 09032409668.


dd



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment