Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk rubutu take kallo tana karantawa Kallo daya Farhan yayi Mata dariya taso kwace masa Amma sai yasa kafa yayi fatali da Littafin turancin data ke karantawa,kanta ta Dago da sauri, Ido Suka hada,ya bata fuska tare da cewa daina kallo na mayya, Babbar banza kamarki Baki iya karatu da rubutu ba,Harara Husna ta aika Masa,yace Ni kike Harara? Da Sauri ta girgiza Kai Wai ae sannan tace dakai nake din ta mike zata gudu,ya cafkota Ihu ta Fara Yi tana bada Kai nake ba Allah, turanci Husna ta shiryowa Farhan I'm Without u wallahi, Wai bada Kai nake ba take nufi, Farhan ya saketa ya dinga sheka dariya a palon Nan kamar cikinsa zaiyi ciwo,Husna tuni zuciyarta ta narke jikinta ya wani dauki rawa,tsananin Son Farhan ya shiga Ratsa zuciyarta,kullum yanda take ji a ranta game da Farhan ta gane zallar kauna take Masa,Amma idan ta tuna yanda Baffa ya bada aurenta ba daraja ba komai Kuma badan Allah ba sai sabo da kudi,sannan ta tuna Farhan yafi karfinta bazai taba sonta ba, ga Baffa tasan matukar Bata samo Masa kudin dayake so ba to auren Nan sai ya rabashi,Jikinta ne yayi sanyi kawai sai ta fashe da matsanancin kuka me ban tausayi,Farhan Yana cikin dariya ya tsaya cik Jin irin kukan data keyi Wanda daga gani har zuciyarta yake fitowa,sai yayi tunanin dariyar dayayi Mata ne,sai ta Dan bashi tausayi Kuma,ya dauko Mata littafin da yayi fatali dashi Yana kallonta da idanunsa masu rikitata yace gashi na daina dariyar Yi karatunki kinji Yar yarinya.

Karba tayi tana goge Hawayenta tare da sakin Ajiyar zuciya,Taci gaba da karatunta Yana kwance a kujera Yana jinta zata ce Queen ta kasa sai tace Que..Qu..Quuuu sai taji Haushi tayi jifa da Littafin tace an daina karatun ma baza ayi ba,tsinannan English,ta jawo Littafin koyon girkinta data ke rubutawa ta Fara karatu da karfi Kamar Haka,Miyar Zogale itace Moringa Soup, Farhan ya Kara kyakyacewa da dariya,Harara ta aika Masa taci gaba da abinta, idan aka samu gyada wato Groundnut Dole miyar Zogale sai da gyada,idan Babu gyada to baza ta Zama miyar Zogale ba,Tunda Farhan yaji yace muga Littafin Nan ke, Husna ta boye a bayanta tana kallonsa tare da turo Dan lips dinta tace Ina ruwanka,Ni kewa rashin kunya Farhan ya nuna kansa da yatsa,Da Sauri ta Fara tafiya da Rarrafe Kamar yaron goye tace gashi,Ya karba ya duba tana da Handwriting me kyau sosai Amma Husna komai sai data rubuta duk Maganar da Malama tayi sai ta rubuta,yaga tasa idan za ayi girki a dinga Daura dankwali kar a shiga kitchen da gashi Bude sabo da Kar ya fada cikin Miya.

Ke har Maganar malamar ma Sai kinyi copying? To ba cewa tayi kome tace mu dinga copying ba shi yasa nake Haka,Littafin ta kwace sai data Gama Yana jinta,sai ta tuna English teacher yace su rubutawa Masoyinsu letter a Kai Masa ya gani.
Zama Husna tayi ta Fara tsara wasikarta.
Bayan ta rubuta Address ta Fara kirkiro turancinta da Wanda yake dai dai da Kuma Wanda ba dai dai ba.
Husna ta dage fa sosai yanzu kokari takeyi ko a class an San tana da kokarinta dai dai gwargwado,ta tsaya tana bada Himma musamman akan English Kuma ba laifi kullum ci gaba ake samu,kullum tana aikinta Daya kamata na gida, Girki kuwa tunda ta iya kullum da irin kalar da zata tsara na gargajiya Dana zamani,Bata taba girka abinda tasan Farhan Baya ci,Umma take tambaya,Kullum idan Umma ta dawo daga Office sai Husna taje Sunyi Hira ta koya Mata Assignment da sauran Abubuwa,bangaren gyaran jiki kuwa duk tana koya iri iri masu inganci Haka Daurin dankwali da kwalliya ta iya kala kala,kula da Miji duk kanta ya waye sai dai Mijin Bai Bata damar da zata kula dashi ba sai gyara Masa room,wanke Masa Inners,girki sai abinda ba a rasa ba duk tana yi Wanda Bai taba nuna Jin Dadi ko Yaba Mata ba.
Gata da rikon Addini sosai,wannan Kam tana birge Farhan.
Wannan rashin godiyar Allah na Husna duk ta rage ta daina sai kadan sabo da Ilmin Addini yanzu tana dashi Alhmdllh.

Yau Saturday Umma da Husna suna zaune a palon Umma suna kallo Sai katsam sai suka ga Salma da Asiya a palon sun kwada sallama,Husna ta amsa cike da mamakin ganin Salma da Asiya,Nan take Brain dinta ta tuna Mata Salma Umma ke riketa shike Nan ta dawo gida,wani kishi ya taso ya tokare Mata zuciya,yanda zuciyarta ta kamu da son Farhan ya zata Yi idan taga Farhan tare da Salma ya zata Yi ga Salma wayayya me ilmi,. Itama Salma Kishi ne ya kamata ji take kamar ta yanka Husna ta huta,Asiya ma tana Taya Salma Kawarta Kishi.

Wani kallon banza Suka yiwa Husna Wanda yasa Husna ta Raina kanta jikinta yayi sanyi,Umma ta fadada fara'arta tace Salma kece Baban naki ya yarda kizo wajena kenan?Salma ta washe Baki tare da cewa ae shine yace muzo ko wata daya ne nayi a wajenki na koma,yasan Bai kyauta Miki ba kiyi Hakuri Dan Allah Umma,,Murmushi Umma tayi tace ba komai ai komai ya wuce Farhan Allah ya bashi wata ma Babu matsala,Wani bakin ciki ya tasowa Salma Jin furucin Umma wato baza ma tace ya aureta a ta biyu ba,Babu komai zata sawa Farhan sonta ta karfi Dole ya aureta.
Asiya harda ke aka zo Mana Ina su Inna? Asiya tace kowa lafiya Umma suna gaisheki ma sunce, to Alhmdllh ke Salma ku shigar da kayanku bedroom dinki kuyi wanka kuci Abinci, Husna ga Salma,wannan Itace wacce Farhan da zai aura Allah baiyi ba cewar Umma,Husna ta kalli Salma da Asiya tayi banza dasu,Umma tayi Murmushi tasan Husna kishin Farhan takeyi,Umma Farin ciki ya kamata Husna ta Fara son Farhan,Umma tana sani ta tsokani Husna tace Husna ku gaisa Mana dasu Salma kina jina kinyi Shuru,wayancewa Husna tayi tace Umma yau me Zaki ci na dafa Miki? Gidanku Husna Ina Miki wata maganar daban kina kawo min wata,da Sauri Husna ta rungume Umma tana dariya tace Baki sannunku da hanya, daga Haka tayi Shuru,Salma taja tsaki tace ke nafi karfin bakuwa a gidan Nan kece bakuwa yarinya,Ni a gidan Nan aka yayeni yar kauye kawai Suka wuce bedroom fuuuu.

Umma tace kyalesu Husna karki Kara kulasu daga yau ko gaisuwa ki sharesu kinji,Husna tace Umma kinji me tace min Fa Allah badan dake ba sai na musu rashin mutunci,Kyalesu Husna kinji ayi hakuri,Ai na kyalesu Amma idan Suka je part Dina to fa sai dai ku Kira Ambulance da wuri ta kwashi jinyatattu Dan saina motsa karfina a kansu,Dariya Umma tayi tace to Husna baza ma su zo ba na sani, tashi ki tafi ya kamata ace kin Fara girkin dare,Mikewa tayi tare da yiwa Umma sallama ta tafi part dinsu.

Da dare ta Gama tsara girkinta ta gyara ko Ina Yana kamshi tayi wanka ta shirya cikin wando 3qtr red da wata Riga tsaleliyar gaske me siririn hannu pupple,gashinta ta gyara tayi kwalliya tare da fesa turaruka,ba Kara min kyau Husna tayi ba kamar a saceta,gashin Nan tayi Masa style me kyau matuka,sai data Gama komai sannan ta fito Palon kasa,lokacin Farhan ya dawo daga Sallar Isha sanye yake cikin wata Shadda Fara yayi kyau ya gaji,Husna tana Shirya Dining,shi kanshi yau ta birgeshi kayan Sunyi Mata kyau,kwalliyar tayi Bata hauka ba simple,Bata taba Yi Masa kyau irin yau ba,kasa dauke idonsa yayi akanta sabo da ko waye yaga Husna to bazai iya Mata kallo daya ba ko mace ce bare Namiji,su kansu kayan da gani masu tsadar gaske ne ba Yan jigari jigari bane Kamar mawakiyar turawa.

Tana ta Kai kawo tsakanin Dining da kitchen,Yana Palo Yana kallon American Film,a hankali Kuma Yana satar kallon Husna a ransa Yana cewa kayan ne Suka Yi Masa kyau ba Husna ba, sabo da Haka kayan jikinta yake kallo ba ita ba,sai data Gama Bata San Yana Yi ba,Bude Kofa Suka ji anyi ba ko sallama,Husna tana juyowa taga Salma da Asiya sunci kwalliya,bakin ciki ya cika zuciyar Husna,kishi ya mamaye Mata Ruhinta,Salma ma kishi take Yi musamman irin shigar da Husna tayi da irin kayan dake jikinta,ga Kuma Farhan suna gani Yana ta kallon Husna.

Da kyar Asiya tayi Sallma a hankali,Husna ta amsa tare da danne kishinta tace sannunku da zuwa ku shugo ciki,Baki Salma ta tabe tare da cewa ko Baki ce ba ai Dole mu shiga,ai Nan gidanmu ne ke kuwa auroki akayi Yar sadaka,Sadaka ubanki ya bada ke yaga dukiya,munafuka dazu Baki gaishe mu ba yanzu Kinga idon Farhan Zaki kula mu Wai ke makira ko? Farhan Yana jinsu irin cin mutuncin da sukewa Husna sai yaji baiji Dadi ba,Husna sai ta bashi Tausayi, Amma yasan Husna da tsiwa ba Lallai ta kyalesu ba,sai da Suka Gama ci Mata mutunci sannan tayi Murmushi tare da cewa me nasara baya fada,baya Fushi,bazan Rama ba Tunda na rigada na Samu nayi Miki zarra, nafi karfinku Mrs Farhan nake yanzu bani da lokacinku,ku daina wani kame kame naga Alama girkin Amaryar Farhan kuka Zo ci to Gashi na shirya kuzo ku cika tumbinku.

Haushin Maganar Husna sukaji sosai kawai tsaki Salma tayi tare jan Hannun Asiya Suka nufi inda Farhan yake,Farhan ya tsani ganin Salma,ko kadan baya son yaga ko pic dinta, Kusa dashi ta zauna kafadarsu tana gugan juna,Asiya Kuma ta zauna a kujerarta daban, Husna tana ganin Haka bakin ciki yasa ta kasa daurewa ta karaso gaban Salma sannan ta juya tare da Zama a tsakiyarsu Rabin cinyarta akan ta Farhan dayar Kuma akan ta Salma,ta muskuta da karfi ta ture Salma gefe can,Salma ta saki Kara wayyo zata karyani shegiyar yarinya,Farhan Yana kallon Haka yace ke dawo Nan side din Husna kamar zata Yi kuka ta koma Daya side din gefensa ta zauna,Salma ta samu dama ta matsa jikinsa sosai,Sun saka Farhan a tsakiya,Husna ta zuro hannu ta gaban Farhan ta ture Salma,Salma Kamar mayya ta gyara Zama,Husna ta Kara tsallake Farhan da Hannayenta ta Mari Salma ji kake Tasss,Salma ta rike Hannayen Husna Suka Fara kokawa a Haka Farhan Yana tsakiya suna tayi,ganin abin Bai gamsar da Husna ba,tayi sufa ta kwantar da cikinta tare da Kirjinta a saman cinyar Farhan kafafunta suna saman hannun kujera ta mike sosai tayi balance Suka ci gaba da fadansu a Haka ita da Salma, Farhan wani azabar Shock yake ji,jikinsa ya fara rawa,Sandar Girma ta tashi tace bata San zance ba,wani Abu ke Masa yawo a jininsa,sabo da Husna ta kwanta Masa a saitin sanda sai mutsu mutsu takeyi suna kokawa da Salma.
Azaba yaji tayi yawa a jikinsa ya daka musu tsawa da karfi yace Salma tashi ku bace min a part,Salma ta mike a tsorace,Asiya tuni ta Kai kofa, Suka fice a tsorace sabo da tsawar da Farhan yayi musu ta razanasu,Husna Kuwa sandarewa tayi a jikinsa,wata tsawar ya Kara Mata tasar min a jikina, maimakon ta tashi sai fashe da kuka tana cewa kana gani anzo anyi min dukan tsiya har gida,a gidan Ubanwa Suka dakeki Yar Kokawar da kukayi da Hannaye ita ce duka? Sai na fadawa Umma cewar Husna,Kika sa Umma tayi min fada Allah sai kin gane kurenki a gidan Nan daga min jikina,Mikewa tayi tsaye tana goge Hawaye tace Allah sai nayi rashin mutunci a gidan Nan,bani da kunya Ni, sai na nuna musu Ni Jaruma ce,Murmushi yayi a ransa.

Dining ya nufa ya barta a Nan, Yana Bude wani plate yaga wani kalar snacks da tayi Kamar Ball,a tsawace yace zo nan,a tsorace ta karaso inda yake yace Dan ubanki yau ma snacks kikayi me shape din kaina kenan?,Dariya ta kwacewa Husna ta danne da kyar tace wallahi a'a me irin Na Yaya Kb nayi,ai kanka kai irin na Igbo ne me shape din giginya,Kai Duk kyansa tace kansa irin na Yan Igbo ne,Lallai zaiyi maganinta,a fusace ya Shakota Allah yasa ta kwace da kyar da gudu ta fada kitchen tare da Sa key, yabi bayanta Yana uban Huci, Yayi yayi kofar ta bude Taki a jikin kofar yace Zaki fito ne sai na karyaki.

Ta ciki ta sheke da dariya tace Me Kan giginya Dangin su Emeka da Chinaza,wata roba ta dauka ta Fara kida tana me hancin biro kwara kwam kwam me kan Giginya Kanin Emaka,Farhan idan Kaine Farhan me ji da kansa to ka shigo kitchen din nan ka kamani,sai na babbalaka,duk abinda takeyi Yana jinta yace zamu hadu ne duk Ranar da Kika fito Zaki gane kurenki, Yana jinta tana ta sheka dariya harda cewa Wai har wani yanga kake yi sai ka Zama Mijin tace Ina Nan da Kai sai na dinga juyaka,da sauri Farhan yace God forbid nafi karfinki yarinya,Ni in soki Allah ya kiyaye, kirji ba komai Kamar Tire, Tana daga ciki tace wa zai gane abu a Riga? yaro Yana cikin riga tumbul tumbul Kuma sai ka roka watarana kana durkusa mini,Dariyace ta Kwacewa Farhan ya kyakyata sannan yace Allah ya kiyaye min me zanyi da kazamin abinki kwaila.a Nan ya juya yayi tafiyarsa dining ya shiga cin abincinsa.


Second to the last Free page.

Rashin Sa'a dari biyu ne(200).


Ga masu son siye ta bank ga bank accnt 2177560408 Yahaya Garba Muhammad, Zenith bank.


Masu bukatar tura number katin Waya Mtn ta WhatsApp ko Sms ga Number ta 0803 393 3642

Maso son siye ta hanyar Vtu Transfer ga number da za ayi transfer 09032409668.







AsmaBaffa.
[2/29, 10:46 PM] Sis Asma: πŸŒ…πŸŒ…RASHIN SA'AπŸŒ…πŸŒ…







36-40






Official






By
AsmaBaffa








Ummyn Zahra and Ummul page naku ne Ina godiya da Sharhi.






Husna tana kitchen sai data tabbatar ya tafi Bedroom sannan ta fito ta Haura sama Bedroom nata tare da yin Shirin bacci ta kwanta,kasa bacci tayi sai juye juye takeyi tana tunanin Farhan sonsa Yana Kara ratsata,Murmushi takeyi tana tunano shi gasu tare suna soyayya,kwanciyarta ta gyara tare da Rungume pillow tana hango kansu tare da Farhan ya rungumeta a jikinsa,Kara mirginawa tayi tana juye juye saman bed dinta, ta Kara hango ta a jikinsa suna Hira Yana zuba Mata kalaman soyayya masu dadi, tana Haka Bata San sanda bacci ya kwashe taba.

Farhan kuwa bayan yayi Shirin bacci nafila ya gabatar sannan ya kwanta Yana Danna waya,sai da ya gaji sannan ya kashe ya kwanta,shima kasa baccin yayi sai da yaji Yana Dan tunanin Husna da Halayenta masu kyau,da sauri ya kautar da tunaninta yayi Addua bacci yayi gaba dashi.
Washe Gari Sunday da wuri Husna ta Gama komai data Saba Yi na aikin gida,girki ta shirya a Dining sannan tayi wanka ta wuce Part din Umma, Aunty Ngozi tuni tazo tana jiran Husna zasu Yi lesson,a gurguje Husna ta haura saman Umma,Umma tana shafa mai da Alama daga wanka ta fito, Sallma tayi Mata ta amsa da fara'a Husna Har kin fito kenan? Ae Umma Ina kwana,lafiya Lau Husna kun tashi lafy? Lfy Alhmdllh,Bari naje wajen Ngozi tazo lesson,ok to a dawo lafiya, Inshaallah Umma cewar Husna.

Tana Fitowa zata tafi Suka ci Karo da Salma Tasha gayu, Husna Bata kulata ba ta wuce,Salma taja Mata tsaki ta wuce. suna Gama lesson ta wuce Part dinta Direct dai dai lokacin Farhan ya dau wanka cikin wani arnen Yard milk color da alama fita zaiyi ya nufi motarsa Driver yaja Suka bar gidan, dama Husna Haka take so sabo da tayi laifi Kar ya kamata.

Sati biyu kenan da zuwan Salma Abuja Amma Babu nasara, ganin Sam Bata samu fuska ba wajen Farhan da Umma ba,hankalinta ya tashi tace sai ta sake sabon shiri.
Baban Salma kuwa tunda ya dawo yaji Salma ta fita yasan rashin Tarbiyyar Salma ya Kai inda yakai,Yace ba komai zanyi maganinta daga ita har Umman,idan ta dawo a kyaleta Ni San me zanyi.
Asiya kuwa tana yin sati biyu ta koma Kano gida,Salma ta Bari ta Hana Husna sakewa da babaken maganganu da kallon banza.

Husna kullum son Farhan Karuwa yake a zuciyarta Bata da aiki sai tunaninsa,yayin da take ta kokari a makaranta,turanci kuwa yanzu tayi nisa sosai Bata Shirme,ta Kara wayewa ta wani irin gogewa ta daban ga uban wanka tana dauka ta Zama wata muguwar Yar gayu idan baka San Husna Sosai ba baza kace ita ce ba,kyawunta da hasken fatarta ya Kara Fitowa,Yau da Asuba Kamar yanda ta Saba zuwa tashin Farhan yanzu tayi hankali ta daina sa Masa Karar waya a kunne,Bedroom din ta shiga a hankali, ta Dade a kansa tana kallonsa Yana bacci a nutse,a ranta tace Yana bacci ma kyau yakeyi,Saitin kansa ta durkusa a kasa jikin bed din,Fuskarsa take kallo cike da shauki.

hannu tasa saman Sumar kansa tare da shafa gashin kadan ai da sauri ta janye Hannun Kamar ta taba wayar Wutar lantarki tare da cewa wayyo Santsi, Hannu ta Kara kaiwa tare da dosana yatsanta Akan hancinsa Nan ma ta janye da sauri tare da furta laushi a hankali yanda bazai farka ba,Bata gushe ba tana kallonsa a nutse tana Kara Jin sonsa na ratsata, zaman cin tuwo tayi a kasa jikin bed,tana ta kallon fuskarsa Yana bacci a nutse,Bata sani ba bacci ya kwashe ta, kanta ta daura jikin gefen bed din kusa da fuskarsa ta Fara bacci itama,daga zuwa tashin Asuba,dukkansu Basu samu Sallah ba suna ta bacci,uban sangartattun dama sai an tasheshi yakeyi,ita kuwa Kallon so yasa Bacci ya kwasheta, Suna ta uban bacci har Rana ta fito kwal.

9am Farhan ya Fara farkawa a hankali ya bude idonsa Yana Adduar tashi a bacci,yayi mamaki Rana har ta fito Husna Bata zo ta tashe shi ba,wannan ai wulakanci ne ta jawo ya rasa Sallah,a ransa yake ta masifa,Mikewa yayi ya sauka kasa daga bed din,me zai gani Husna tana ta baccinta ta kafa kanta jikin Bed, Mamaki ya Kamashi me ya kawota dakinsa harda bacci,yaushe ta shigo.

Ganin Babu me bashi amsa yasa kafa ya Dan bugeta,Bata tashi ba taci gaba da baccinta harda gyara kwanciyarta,Body lotion ya dauka a Mirror ya buga jikin gadon da karfi,Bata ko motsa ba, jikin bed din ya buga da kafa da karfi,ba shiri ta bude Idonta,kallon inda take tayi Nan take ta tuna abinda ya kawota,Rana ta gani mamaki ya kamata,zumbur ta mike tsaye itama, Wa yace Miki ki shigo min daki? Har da kwanciya a jikin bed Dina? Wa ya Baki wannan damar? Farhan ya tsareta da Ido Yana tambayarta,Bata ce komai ba ta Gama tsorata dashi, tana Wasa da yatsunta tare da turo Dan karamin bakinta a hankali tace kayi Hakuri nazo tashinka da Asuba ne baka tashi ba,cikin Bacci sai ka dinga magagi Babba da Kai ya Farhan harda munshari kana magagin bacci Kuma kace Min Husna Zauna a kusa Dani karki tafi tsoro nake ji,Farhan a firgice yace Ni din nayi Munshari a gidan uban wa? Kuma na rasa wacce zance ta zauna sai ke? Tsoron wa zanji? Husna Kamar gaske ba alamar Wasa tace to Haka kace min zanyi karya ne ko na taba fada maka Haka tunda nazo gidan Nan?,cikin Bacci kana magagi kace Husna...ki zauna karki tafi tsoro nake ji, nace Da girman ka? Kace ae ai Ni ba jarumi bane,zaman banza nakeyi ko wajen aiki bana zuwa iyayena na Bari da wahala suke ta Tara min kudi,nace Bai Dace ba Farhan,kace Dalla rufe min Baki Ni bazan tausayawa iyayena ba,nace sun girma fa ya kamata ace yanzu Kaine me kula dasu ba su zasu dinga kula da Kai ba Amma sai kace rufe min Baki Ni Dan zaman banza ne,mace ma ta fini kokari, sai na Fara baka hakuri nace kayi hakuri yanzu idan ka auri wacce kake so ta haifo maka Yara da me zaka ci dasu? Baka Saba da Neman na kanka ba,kawai sai dai a Tara maka ka eba,rayuwa zata yuwu Haka,Namiji kamarka ace baka zuwa ko Ina ba ruwanka da kowa sai dai kaci me kyau ka kwanta ka sheka wanka,Ai ko Wanda yafi kowa kudi a duniya ba a kwance yake ba,Kuma rayuwa baka san ya zata Kare ba,idan kasan farkonta baka San karshenta ba ya kamata kayiwa kanka fada ka hutar da iyayenka shine zaka samu Lada,Aljannarka tana kasansu kayi kokari ka faranta musu ka samu ladansu tun suna raye kafin lokaci ya kure maka, cikin baccin ka juya min baya kace Mahaukaci ya fada Rijiya yace Ni wankana nakeyi, nace ka tashi kayi Sallah kace to zauna ki jirani Ni kuwa nayi zamana,Ina Zama shedan yayi amfani da damarsa bacci ya kwashe Ni kaima Haka shine ka ganni a Haka.

Tsam Farhan ya tsaya Kamar gunki Wai shi Kamar Husna zata yiwa wayo Wai Nan Wa'azi tayi Masa da wayon tsiya, Aiko zaiyi maganinta, ba zato ya cafkota cikin zafin nama,duk hasken idonsa ya koma ja,a Harzuke ya shaketa Bata iya ko motsi,Kamar zata mutu ya dinga fesa Mata Mari ta ko ina, Husna ta barke da kuka tana magiya Dan Allah kayi hakuri wlh na tuba bazan Kara ba,karya nakeyi kayi hakuri,Jifa yayi da ita a kasa ta bige goshinta ya kumbura,da sauri ya jawo Belt kafin ya karaso ta fice Daga dakin a guje tare da afkawa room dinta tasa key, jefar da Belt din yayi a fili yace zamu hadu,naga kin rainani da yawa,Baki San waye Farhan ba.

Husna Tana kuka tana Alwala Haka tayi Sallah da azkhar ta fada saman Bed taci gaba da kukanta sai wurin 11am ta daina kuka tare da bawa zuciyarta Hakuri,Wanka tayi ta gasa jikinta ta shirya cikin Readymade Gown Dark blue and white,me zanen layi layi, an tsaga rigar gefe da gefe har Rabin cinya, Dark blue siririn gyale ta daura a kanta yayi kyau kalar Daurin da tayi na zamani duk da Fuskarta tayi jajir ta kumbura Bai hanata yin kyau ba,Tea me kauri ta hadawa kanta Tasha da Bread ta dawo bedroom tare da kwanciyarta tana tunanin Farhan Yana zuba Murmushi,Sonsa take Kara ji sabo Yana shigarta,dukan da yayi Mata Bata ganinsa a laifinsa ai laifinta ne Wai tunda itace tayi Masa Nasiha,da Bata yi ba da Bai dake ta ba.

So Hana ganin laifi, Farhan kuwa tunda Husna ta Shirya Masa kalamai akan iyayensa gaba Daya ya kasa sukuni,Hankalinsa ya tashi,idan Banda tunanin maganganun Husna ba abinda yakeyi musamman ka samu ladan iyayenka tun suna raye kafin lokaci ya kure maka, yanzu kulawarka suke bukata ba sune zasu kula da Kai ba har yanzu,ka girma Namiji Babba Sai zaman banza,kaci kasha kayi wanka Sai bacci, idan ka Haifi Yara aikin me ubansu yakeyi? Idan kasan farkonka baka san karshenka,baka iya Neman na kanka ba sai dai a Tara maka ka kashe, Iyaye sun manyanta har yanzu rainonka sukeyi, har yayi wanka ya shirya cikin kana Nan Kaya,Creazy Jean Black and White t-shirts masu tsadar gaske Sunyi Masa azabar kyau kamshi kawai yakeyi ta ko Ina, Tunanin maganganun Husna kawai yakeyi hankalinsa Yana Kara tashi, Yana gamawa ya fito Dining wayam ba girki,gashi ya Saba da cin kalolin girke girken Husna masu dadi, wani Haushinta ya Kara ji to Nufinta da aurensa ya koma wajen Umma yace ta bashi Abinci Dan ta rainashi.

Sama ya sake Haurawa ya nufi bedroom dinta,Yana ta faman knocking Bata sani ba har ya tura kofar kawai ya shiga ciki,abin mamaki rigar da tasa Cinyoyinta a waje lukuta lukuta farare ta baje Pillow Yana saman Kirjinta ita kadai tana ta Murmushi tana juye juye saman Bed,Tayi kyau iya kyau shi yasan tayi kyau,a ransa yace Ashe Haka Yar yarinyar Nan take da cinyoyi da uban Hips, Murmushin sai ya Kara Mata kyau,da sauri ya kaucewa tunanin ya buga Mata uwar tsawa, keee..Mene nufinki? Uwata

Please Login or Register in order to submit comment