Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[2/29, 10:42 PM] Sis Asma: BISMILLAH
COPY BY ZAINAB BUTALAWA



🌄🌄RASHIN SA'A🌄🌄








1








Official






By
AsmaBaffa









Muna Godiya da Allah ya kawo mu sabon Novel Allah yasa mu Gama lafiya.

Ina gaida Fans Dina musamman masu Sharhi Allah ya biya.





Da ku Zan Fara mutanena ga page naku

MAMAN SAMHA
NABEET ABSA
MAMU GALADIMA
AMINA ABDULLAHI
MARCYCOOL and
FLOWER.



Gaisuwa me tarin yawa zuwa ga JIDDER ZARIA, ASYCOOL,AUNTY SUMEE,KHADIJA A HAMZA,HADIZA MUKHTAR,JANNAT,HAFSAT, HAFSY, KHADIJA DANDUME and FULATA LUV.









Katsina state cikin wani kauye sosai na Fulanin asali Rugar jabbama, wata Yar budurwa ce baza ta wuce 15yrs ba zaune take Bakin makarantar bokon wacce take guda Daya tal a kauyen itama ba wata ta kirki bace, kuka take rusawa iya karfinta abokan karatunta Yan Mata da maza sun taru akanta Ana ta Yi Mata dariya da ihu, Mikewa tayi jiki ba kwari ta dauki Yar Jakarta ta dauki hanyar gidansu tana bi ta lungunan kauyen har ta Karasa gidansu Wanda duk garin shi kadai ne na bulon siminti me kyau dashi dagwas dagwas,ciki yasha tiles Kamar ba a kauye ba,Dakuna Hudu ne da Palo sai Toilet biyu da kitchen,toilet Daya a cikin wani room yake daban Daya Kuma a tsakar gidan, Rijiya karama a tsakar gidan me dauke da Bishiyar Umbrella katuwa, gidan a tsaftace komai Neat ba tarkace.

Yar Budurwar kyakyawar gaske ta shiga da sallama tana murza idonta Dara Dara Wanda Suka koma jajir dasu,Wata Dattijuwa sosai me Kamala ta amsa Sallamar tana Aikin Wanke Kubewar Miya danya tace Husna Lafiya? Ke anyi Hutun makaranta Ana murna ke kina kuka kullum duk yanda akayi abinda kika Saba shi Kika sake samu a result dinki,duk yanda akayi term din Nan ma bakiyi kokari ba kin dauki dakon aji,ke kullum kece a karshe.

Wacce aka Kira da Husna ta Kara fashewa da Kuka cike da shagwaba tace yo Yafendo Ni ya ake so nayi sabo da Allah iya kokarina kenan kina gani kusan kwana nakeyi karatu Amma bana cin jarabawar Ni ban San me yasa ba,mu gani result din ta nawa kikayi? Yafendo ta tambaya,Husna tana turo Baki tace cikin Mu 95 nayi ta 94, tabe Baki Yafendo tayi tace aikin kenan mutum Daya Kika kayar Lallai Husna Allah ya kawo Baffanki ai zaizo daukanki birni na gaji da rufa Miki asiri sai na fada Masa,gwara ya tafi dake gabansa kawai.
Magiya Husna ta shiga yiwa Yafendo Kan karta fadawa Baffanta Amma Yafendo tace ta gaji wlh.

Suna Haka Suka ji sallama wata tsohuwa ta Fado da sauri tana Yafendon Husna maza kizo Tasalla tayi Bari, a rude Yafendo ta figi gyale tace Husna maza ki shirya kici Abinci ki tafi makarantar Allo Ni Bari naje Makwafta gidan Tasalla.
Husna Bata gane Mene Bari ba tunaninta Tasalla barin Kwanukan jere tayi ko kayan Abinci ta zubar ko wani garin tuwo ta zubar,tunda taji Ana gayyatar mutane tasan Barin Babba ne, sai ko tace wlh Nima baza a barni a Baya ba sai na gani watakil samirun jerenta ta barar suka rikito, sai da taci abinci tayi wanka ta shirya zuwa makarantar Allo sannan ta wuce gidan Tasalla lokacin tuni su Yafendo sun Gama komai sun fito daga gidan ma Tasalla fes da ita Ana zuwa dubata.

Husna da gudu ta fada Dakin tana zare Ido ta gani me Tasalla ta Barar sai taga ba komai sai sannu akeyi Mata tsaki taja tayi ficewarta ta tafi makaranta.
Ko da ta Isa makarantar Allonsu da kyar ta Kai Haddarta har sai da malamin ya zabga Mata bulala sannan ta tayi karatun da kyar sannan ya Kara Mata ta Iya.

Ko da ta dawo Gida Magrib har tayi Sallah tayi sannan ta dawo kusa da Yafendo ta zauna gefenta tare da daura kanta saman cinyar Yafendo tana Lumshe Ido zata Yi bacci, Sallama Me gidan yayi da Alama ya dawo daga kasuwa ne,Husna ta mike da sauri tana Sannu da zuwa Affa,da Fara'a ya amsa yace Sannu Husna, yawwa Affa ya kasuwa ta Furta tana amsar ledar Hannunsa shi Kuma ya shige Dakinsa tare da Yafendo Matarsa.

Wayar Yafendo ce tayi Kara ta daga da Fara'a gaisawa sukayi ta waya tace to Allah ya kaimu goben Zan hada Mata kayanta,Gama wayarta keda wuya Affa yace Baffan su Husna ko? Ae shine yace zai zo gobe ya tafi da Husna Birni tayi Hutu a can,to Alhmdllh ai yakamata wannan Hutun ya dauketa da wuri sabo da su shaku da Yan uwanta.
Husna kuwa tunda taji Baffanta zaizo farin cikinta ya rushe ita tana son Birni Amma abinda ake Mata yasa Bata son Birni sannan zaiji term din Nan ma batayi kokari a schl ba Kuma yace sai ya zaneta Haka Mamansu ma zata zazzageta a birni bayan Haka ma Yan uwanta ciki Daya suyi ta rainata suna ce Mata Yar kauye komai Bata iya ba sai sune suka iya, tsaki ta ja kawai tayi kwanciyarta tana takaici.


Wani azababben matashin Handsome ne, yaro ne matashi bazai wuce 29yrs ba Cikin shiga ta Alfarma Kamar yau Daurin aurensa sanye yake cikin farar shadda dinkin zamani Kamshinsa ya cika ko Ina, Yana sakkowa Daga steps Yana danna faskekiyar wayarsa Guards ne suke take Masa baya janye da Trolley dinsa da Alama tafiya zaiyi, daga part dinsa ya fito kafin yaje Daya part din sai da ya shiga mota Driver ya kaishi ya fito cike da Izza tare da shiga part din abinka da gidan masu hannu da shuni sallama kawai yayi ya shiga cikin hadadden Palon na masu hannu da shuni,saman Wata arniyar Kujera dattijuwa ce Kyakyawar gaske ba wata Babba bace can Fara kwal da ita kamar ka taba jini ya fito yanda Handsome yake da kyau Haka take har ma ya fita komai da komai, jikinta ya kwanta tare da narkewa a jikinta sannan da kyar yace Ina kwana Ummana? Amsawa tayi ka tashi lafiya Son,lfy ya Bata amsa kawai Bai sake magana ba Haka take ta Masa Hira Amma Sam ko kala Bai ce ba Kuma baiyi dariya ba ko kadan.

Halinsa Yana damun Umman tasa Sam Bata son Halin danta Haka ba magana baya harka da kowa kullum cikin kunci da masifa,da can ba Haka danta yake ba,kallonsa tayi tace Farhan? Kansa ya Dago daga jikinta kawai ya zuba Mata idanunsa farare tas kyawawan gaske abinka da farar fata komai kyau yake Masa, Farhan Bana son Halin naka da kakeyi yanzu ace Dan kawai Haneefa ta rasu sai ka damu kanka,dukkan Dan Adam lokaci yake jira ai,muma ba Zama zamuyi ba, ka Fara girma fa Farhan 29yrs ba Wasa ba,Haneefa Kuma nasan Dole nasan kaji mutuwarta sabo da Kun shaku har an kusa aurenku Allah ya karbi Abarsa ya kamata ka hakura ka koma normal.

Kallon Umman kawai yakeyi kawai yace Zan daina Ummana ki tayi min Addua ya kike so nayi? Addua Ina maka Amma ya kamata ka daina wannan Shuru Shuru da kunci,Hooo Umma nifa ba Haneefa bace tasa nake damuwa kawai Haka na koma Nature nane Haka nake,Mikewa yayi yace Zan wuce Qatar Umma,Hmm kaji Halinka ko yanzu ban San zakayi tafiya ba sai da ka Gama shirinka zaka ce wani zaka Yi tafiya,Anyway Allah ya kiyaye Hanya Amma Karka wuce 1mnth kaji na fada maka, matukar ka wuce Haka wajen Tsohon Ubanka wlh sai ranka ya baci, 2wks ma zanyi Ni na dawo Umma karki Yi fushi pls,Better cewar Umma, fita yayi Suka wuce da escort nasa zuwa Airport jere cikin motoci guda shida na Alfarma ka rantse gomna ne.

Husna fito mana naji Karar Mota ga Baffanku can Allah ya kawo Dan Uwana lafiya cewar Yafendo,Affa mijinta yace Alhmdllh shi yasa naki fita Ina Jiransa Ai daga Jin motar ta Alhaji Shu'aib ce, tabe Baki Husna tayi tare da cewa ko kadan bana murna wannan Jarabar Birni bana kaunarta birni ko jaraba gari kowa Iyayi da karya ba abinda Suka iya sai karya,Rankwashi Yafendo ta zuba Mata ba shiri ta fice da gudu kofar gida tana turo Kyakyawan Dan karamin lips dinta.

Kofar gidan ta leka kadan ta Iske motar Baffa Yar karama ta masu rufin Asiri,gaban Motar kanin Husna Ne Aliyu Dan Shekara 10, sai kanwarta Nusaiba a bayan mota Yar 13yrs,Da kyar Husna ta karaso jikin motar tana fushi tace Ina kwana Baffa, sannu da zuwa, ya Hanya? Kallonta yayi kawai yanda take fushi kawai Murmushi yayi tare da amsawa Yana tambayarta ya makaranta tace lafiya Lau, Nusaiba da Aliyu kuwa sai iyayi sukeyi su a Dole Yan birni wayayyu,Husna tana kallonsu ko kulasu Bata yi ba sabo da suna Yi Mata tsiya Yar kauye,komai tayi suce Bata iya ba sune wayayyu,Baffa yasan halin Abarsa cikin gidan Suka shiga gaba Daya suna Anty Husna Ina kwana?,Harara Husna ta ballawa kannen nata tare da cewa Yana kwano,Haba Mamana dake Husna Sunan Babar su Baffa aka sa Mata Asmau shine suke ce Mata Husna,Sunan kakarsu ta ci, kina Babba kina Haka cewar Baffa.

A Palo Yafendo ta saukesu wanda malale yake da carpet,fura da kaji soyayyu ta kawo musu sai shinkafa da Miya tare salat,Ruwa pure water Affa ya kawo musu Suka ci suka Sha Ana Hira, bayan sunyi Sallar Azahar Yafendo ta kwashe labarin irin rashin kokari na Husna ta fada Masa kaf,ransa ya baci sosai,Affa kuwa baiji Dadin abinda Yafendo tayi ba ta tonawa yarta asiri.

Baffa kuwa Kamar zai Mari Husna Haka yake masifa,Husna ta Fara kuka tace to Baffa Ni fa bani da Sa'a a rayuwata komai nake so bana samu Kuma ai karatu Ina yinsa ya akeso nayi,ko Nasara Dole ya kyaleni wajen karatu,sai ki fada min rashin sa'ar Taki a rayuwa Dan ubanki cewar Baffa.
Husna ta matsa can gefe tana mannewa a bango sannan tace na farkon rashin sa'a ta a duniya da kuka kawoni kauye na girma na rayu a kawai bayan da Kai da Mama da kanne na tare da yayyena duk Kuna birni kun Saba da rayuwa Ni Kuma fa? Sannan kuka rabani da Zama daku iyayena ban girma daku ba,gaku a birni Kuna ta cin kayan Dadi,kuyi kwalliya me kyau irin ta Yan film,kuyi yawo a mota,Ni kuwa an barni a daji,gaku sai turanci kukeyi Wanda Ni ko zo in kashe ka da turanci bana ji Taya zanyi kokari, ai wlh Nan gaba ma jarabawar tunda idan nayi karatun bana ci to da ka Zan dinga dukanta kawai,ko littafina bazan Bude ba.

Harara Baffa ya watsa Mata,Yafendo tace Kya ci Uwarki wlh sai an maida ke birni Baki daya zanga Sa'ar Taki ta birni ya take,Affa yace kuyi hakuri kuruciya ce,Hmm saura wata shida ayi canjen aji zata zo Shiga jss3 lokacin zanzo na tafi da ita taci gaba acan cewar Baffa,Yafendo tace Alhmdllh gwara a kaita can dama tana ta ce min kauye Babu sa'a a kaita birni muga sa'ar Tata,Ita dai Husna Bata ce komai ba Yafendo tace tashi ki dauko jakarki ki tafi Hutu ko na Huta da halinki Husna,yanzu da Yar kishiya ce sai Iyayenki suce zaluntarki nakeyi.

Husna cikin fushi ta Suri Jakarta tayi waje tana kunkuni ita an kawo ta riko kauye ga birni can Ana Jin dadin rayuwa Yan uwanta sai rainata sukeyi gwara itama taje birnin ta waye gaba Daya a daina wulakantata.
A ranta taji har ta Matsu wata shida tayi su koma birni gaba daya, Baffa ne yace ai yanzu Yafendo baza ta bimu ba na fasa tafiya da ita Hutu idan nazo daukanta Baki daya Nan da wata shida sai mu tafi gaba Daya,Husna tana gani Baffa ya korota gida yaja motarsa ya tafi birni tare dasu Nusaiba,Tafi Nono fari cewar Husna gwara Azo a tafi Dani Baki daya,Ana can birni Ana Jin dadi kauye fa nice gona, nice kiwon awaki, nice ebo ruwa,girki,Abinci kullum a damu mutum daga fura da Nono,Dambu,danwake, faten yakuwa,Dashishi,biski,Tuwo etc,Babu suturar kirki,a birni kuwa su ba Haka akeyi ba,Maganganun Husna Ba Yafendo ba har Affa yaji haushinsu Babu abinda basa yiwa Husna na Jin Dadi iya karfin iyawar su Amma Bata gani Sam,ko dansu na cikinsu baza su Yi Musu haka ba,Allah Bai Basu Haihuwa ba ya zasu yi?sai hakuri.

Affa ya kalli Husna yace Shike Nan Husna komai ya wuce ai kin kusa komawa birni,Da Sauri Husna tace Inshaallah, tana cuno lips nata sabo da Husna kyakyawace ta gaban kwatance, kyaune da ita na bugawa a Jarida, Fara ce Amma ba fari me Kal Kal ba wani irin farin skin ne da ita me kyan gaske Kamar ruwa biyu Haka take shi yasa komai tayi kyau yake Mata, Affa da kyar ya lallashi Yafendo akan ta daina damuwa kuruciya ke damun Husna,yanzu sai ace mune muke gallaza Mata azaba ka duba a gaban Dan Uwana Kanina take fadar irin wannan magana,Shekara goma Sha shida ai ya wuce ace Husna Yarinya ce,Wlh kuruciya ce Yafendo kina zamanki zata dawo ta neme mu,shike Nan ba komai ai Bari ba shegiya bace da Ubanta cewar Yafendo.

Babban birnin Qatar Farhan cikin swimming pool ya fito sanye da Boxers Dan guntu a jikinsa Amma Allah yayi Halitta a wajen Nan, shi ba dogo ne ba can ba,normal,Haka jikinsa ba me kiba ba, ba kuma ramme ba,ga Kyan fuska diri da cikar zati,Farhan abin kallo ne ga kowa jajir dashi fari tas ne ga iya wanka,ko wacce shiga yayi kyau yake masa, idonsa kadai ya Isa ya rikita mutum bare hancinsa da Bakinsa wow sai ma Gashinsa da yanda yake gyarashi Uhm Dole a hadiyi yawu, ga kudi da Naira ya gajesu gaba da baya Dan masu arziki ne gashi iyayensa na matukar kaunarsa lallabashi sukeyi sai abinda yake so Amma Yana da tarbiya da ilmin addini Dana zamani sai dai akwai girman Kai ga raina mutane,sannan duk Maganar Daya ga dama direct zai fada maka iyayensa kawai ne Suka Isa dashi,baya shaye shaye sannan Yana Hulda da Mata sosai Amma baya Zina idan kin Masa iya romancing kawai zaiyi sama sama da mace ya kyaleta hakan ma sai ta Kama Dole idan Yana cikin yanayi na bukatar mace sai ya rage zafi,a Matan ma masu aji yake kulawa da kin nuna kina son sex zai daina kulaki,ga Bari da Naira hannunsa a bude yake Kuma Yana taimakon Marasa gata sosai,Sallah Bata wuceshi,Abinci kuwa ba komai yake ci ba sannan ko Yar aiki ce tayi matukar Yana son abincin zai ci ba ruwansa.

Farhan Dan masu Arziki ne Basu gaji tsiya ba,me kudi shine Wanda Yana da kudi Amma Basu da mutunci ba taimakon na kasa,Basu San darajar kowa ba sune masu kudi,masu Arziki sune ga kudi ga tarbiya da hankali tare da sanin ya kamata,Iya kyan mace Farhan ko kallo Baki isheshi ba,iya kudinki da ajinki kinyi kadan ya kalleki ya Kura Miki Ido Baki da wannan matsayin,abokai ma Yana dasu da yawa Amma ba ruwansa da wani shigewa mutum bashi da wani close frnd mutum Uku ne ma Suka Dan Fi shiri dasu,Ayman,Mohd sai Ammar Suma sabo da tare Suka taso tun suna Yara sannan tare sukayi schl, Bai fiye Zama a Nigeria ba kullum a hanyar yawon kasashe yake sabo da kwata kwata baiyi rayuwa a Nja ba bayan ya Gama secondary schl a England yayi rayuwa har University a can yayi yanzu Masters yakeyi shima Online yakeyi,Qatar kuwa garin Babansa ne,ya iya business sosai da sauran Neman Kudi iri iri Amma bayayi sabo da gata yasa ya sangarce,Babansa ya Riga ya Tara Masa arziki Haka Ummansa itama ta Tara Masa Kuma suna ta juya kudin sai abinda yake so,Babansa duk ya Mallaka Masa dukiyar Amma Yana ci gaba da juya Masa ita Haka Ummansa ma, Office dinsa katafaren Building na Qatar da na Nigeria dake Abuja amma baya zuwa ko daya sai ma'aikatan dake karkashinsa ke kula da komai Umma tana tafiyar da komai nasa Haka na bangaren Babansa ma Haka Babansa ne ke komai da yaransa duk sabo da shi kadai suka Haifa a duniya.

Idan kana neman kyau to a tattaro wajen Husna da Farhan asha kallo, doguwa ce ba can ba,gata Yar caras da ita ba kiba ba Rama Kuma,ga hips gashin girarta Dana Ido Baki sidik masu yawa,gashin kanta me uban tsayi sosai da sosai na Fulanin asali Amma ba Baki bane jaja Jaja Baki Baki Haka yake Husna ta Kai karshe.
Rashin godiyar Allah ne da ita,komai Ita ba ayi Mata dai dai, ta samu tarbiya wajen yawan Ibada sai korafi gata Bata da korari a schl sai Taki yin karatu tace Kuma Wai Bata da Sa'a ne,makarantar Allon ma sai ta Dade Bata Kai Hadda ba,Bata da masifa ko wani Hali na banza sai zallar rashin Godiyar Allah da dakikanta a komai na duniya ita baza ta iya ba sai tace ta kasa Bata da Sa'a, sai Jarabar son kudi da tattali,Abinci ko ya rube sai tace baza a zubar ba,gata da Tsafta tana kula da kanta, sai tsirfa da Iyayin jaraba har yayi yawa wajen Husna.


Waye Farhan?

Farhan Al-Mustapha shine cikakken sunansa, Al-Mustapha Dan Asalin Kasar Qatar ne,balarabe ne usul Su Uku iyayensu Suka Haifa, Sahr itace ta farko wajen iyayensu Wanda sun Dade da Rasuwa,Sahr ma shekararta uku da Rasuwa ta bar yaranta biyu manya suna Qatar da aurensu Daya mace daya Namiji,sai Almustapha Wanda dansa Daya Farhan, yayi aure aure da dama Amma Farhan kadai ya Haifa duk sauran Matan har suka rabu Basu Haihu dashi ba.
Sai Kaninsa Shureim shima da Matarsa balarabiya da yaransu uku maza biyu mace daya suna zaune a Dubai can yake Business.

Harkar Business itace ta hada Almustapha da Umman Farhan Hajiya Sadiya har sukayi aurensu Bayan Shekara biyu ta Haifa Masa Farhan Bayan Farhan ya Gama Secondary Haka kawai yace shi ya gaji da auren ya saki Haj Sadiya sannan ya dauke dansa ya kaishi England karatu sannan ya auri balarabiya Eesha Yar uwarsa suke zaune a Qatar dinsu kasancewar shi yafi ganewa Yar uwarsa Balarabiya suna zaune lafiya da Eesha da sauran Yan uwansa suna son Farhan Babu wata matsala suna lafiya shima Farhan Yana kaunar Dangin Babansa Abbi da Kuma matar Babansa Eesha.
Almustapha mutumin kirki ne Dattijon arziki Amma Yana da akidar jinsinsa na larabawa da son kai.

Umman Farhan Haj Sadiya Yar Fulani ne usul Asalin Fulanin mambila Taraba state border da Cameroon,iyayenta duk sun rasu basa Raye dama su biyu suka Haifa yayanta Namiji shima ya rasu Shekara biyar kenan,ya mutu yabar Yan Mata biyu Haneefa21yrs da Salma 19yrs, ganin dangi duk sun Kare saura Yara Umma ta dakkosu gabanta Garin Abuja city ta rikesu tare da Sasu a schl yanzu Suna level 2 a university inda suke rayuwa a Abuja.
Sun goge sun waye suna cikin daula Kamar Umma ce ta haifesu sai abinda suke so sunfi Farhan ma Dan masu arziki iya shege da jiji da kai gasu Suma ba laifi da kyansu dai dai su,yanzu ko kauye basa zuwa ziyara sun waye,kunya ma suke uwarsu Mahaifiya tazo ace ita ce uwarsu idan tazo ganinsu basa ko nunawa itace uwarsu Mahaifiya,Umma tayi fadan har ta gaji.gasu Kuma gaba dayansu son Farhan sukeyi kowacce so takeyi ya aureta amma Farhan Sai Allah yasa Masa son Haneefa,sun shaku sosai har an Sa ranar bikonsu Typoid ta Kama hanjinta aka Yi Mata aiki sai aka samu akasi a aikin Allah ya Mata Rasuwa.

Tun daga wannan Farhan ya sake canjawa ya koma kawai ba mutunci.
Tun Haneefa na Raye idan Umma ta shirya zata je kauye ziyarar dangi sai suce su baza suje ba,ko suyi karya Suki zuwa har ta gaji da halayensu.


Wace Husna?

Husna Shu'aib Bello shine cikakken sunanta











AsmaBaffa
[2/29, 10:43 PM] Sis Asma: 🌄🌄RASHIN SA'A🌄🌄









2








Official









By
AsmaBaffa









Page naku ne

ASMABAFFA FANS CLUB
ASMABAFFA FANS
TUBABBIYA FANS AND
TASKAR ASMABAFFA.








Shu'aib Bello Asalin Fulanin Gombe ne kiwon Dabbobinsu ne ya kawo iyayensu Katsina state rugar Jabbama,iyayensu sun Haifi Yara da dama Amma duk Rasuwa sukeyi Shu'aib da Yafendo Hajiya Binta sune kadai suka rayu a duniya bayan sun taso cikin rufin Asiri,Babansu yasa su a makarantar boko,Yafendo iyakatar primary schl aka Yi Mata aure Da Affa Dan uwanta,Shi kuwa Shu'aib sai Bayan ya Auri Hajiya Hannatu sannan ya Fara sai da gwanjo a Kano state,da ya Fara samun kudi sai kawai ya zauna Ssce ya shiga college inda ya karanci Agriculture NCE, ya samu aikin Gomnati inda yake koyarwa a Secondary schl har Ya Zama principal a yanzu,a Kano yake rayuwa da iyalinsa,daga

Please Login or Register in order to submit comment