Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ni da ku Kuma wallahi daga yau kullum sai nazo gidan Nan Zaku ga Rashin mutunci, ta Gama Neman fadanta tayi waje sabo da Haushin an koreta hhh.

Abba yana waje yaga Nabeela da kaji biyu Yace ki dawo da Daya ba Taki bace,Nabeela da tayi nisa da karfi tace a gewaya min Yasin cikina ya kulle na Mutu,gidan Alex ta koma tare da mikawa me gadi tace Dan Asabe karbi ka yanka min su a gyara minsu karshe Kuma ka gididdiba min su Yau farfesu zamu ci na fresh Chicken kiwo na ne,Dan Asabe anga Dadi ya washe Hakoransa manya yace an Gama Hajiya minti talatin yayi yawa Zaki ga yanda kike so.
Safiyya kuwa tunda Nabeela ta fita ta barke da kukan munafunci tun yamma take kuka har dare Hashimu Yana ta Bata hakuri da Hajiya Binta Amma Taki yin shuru sai kuka har dare yayi Taki dainawa ta hanasu Bacci cikin dare 2am ta fito tsakar gida ta dinga kwarara Ihun kuka tana burbuwa tana wayyo kazata,Mutane makwafta aka cika gidan cikin dare Ana tambaya lafiya,Abba kunya ta kamashi a Kan kaza Safiyya take wannan kuka,Hannunta Abba ya rike Yana Lallashinta yace kiyi hakuri gobe ko Rancen kudi Zan samo na biya ki kudin kazar ki ai baza ta wuce dubu biyu ba,Safiyya da tayi zaman Yan bori a tsakar gida tana shesheka tace wlh dubu uku zaka bani kazata katuwa ce sai dai a siye ta dubu uku harfa Gero nake zuba Mata tana ci..Abba Mijin tace da sauri yace ai kuwa Billahillazi Dole tayi maiko indai tana cin Gero ai ban sani ba,Abba ya sake cewa ta turawa zan Miki Safiyya Finish yayi Dariya shi daya ya sake furta aeee nace Finish safiyyata dubu uku an Gama ko Rance Zan samo maza tashi Yar Albarka,Mutane dai ganin Abinda ke faruwa dama sun San halin da ake ciki tafiya sukayi suna zagin Safiyya,Abba Kam bedroom ya jata Suka shige,Ranar kwanan Hajiya Binta ne Amma sai yace Hajiya Binta sai dai kiyi Hakuri Dole Zan zauna na lallashi Safiyya Zan Kwantar mata da hankali,Miko min madarar Nan ta L and Z Dana siyo Miki na fasa Baki Miko min Safiyya ta shanye ta,Hajiya Binta Allah sarki cike da murna tace Allah yasa ban ko Bude ta ba Alhmdllh kaga sai Ka Bata Tasha,Dan Allah Hashim ka lallasheta sosai Karka Bari Hawayenta ya zuba idan da Hali ma ka Bata a Baki da kanka kaji,Abba yace ai dama a Baki Zan Bata da kaina,Haka kuwa akayi Abba ya jawo Safiyya jikinsa Yana Bata madara kamar wata jaririya a ranta sai dariya takeyi,ganin Haka tace Ina da Feeder Hashim na siyo Zan kaita gidan barka Yar yayata ta Haihu wannan ai gwara ka zuba min madarar a ciki ka dinga bani zai Fi min dadin Sha Kamar jaririya,Abba yayi Dariya yace ai jaririya kike a wajena maza dakko ta,Safiyya jibgegiyar tsohuwar ba kunya ta dakko feeder ta Yara wato bulunboti ta Mika masa ya zaro ta a cikin kwalinta sabuwa dal harda wanke ta sannan ya zuba madarar a ciki ya sawa Safiyya a Baki ta shiga jaa...zuuuuuuu....sai ta Kare a zuba wata ko kunya Bata ji tsohuwar banza,Abba Yana ta wahala tace wannan tace wancan kwana sukayi ba bacci Safiyya Nkeci tana ta iya shege,ruwa ma Sai an zuba Feeder ake Bata ta Sha,ita Kuma Hajiya Binta motsi idan taji sai ta fito ta Zo jikin window tace Hashimu ice ko Safiyya lafiya take? Cikin Sauri zai ce Kalau....kalau ma kuwa cewar Hashimu Kamar me karbar Haihuwa.

Nabeela kuwa bayan Me gadi ya Gama yanda tace kawo Mata yayi Har kitchen tana godiya ta karba ta wanke kaji tas cikin tukunya tayi hadinta ta zuba uban farfesu me shegen Dadi,Alex kamshi ya cika Masa ciki a gurguje ya Gama shirinsa bayan ya fito daga wanka Yana kamshi sanye cikin wani yadi fari me tsada sharara da shi ba karamin kyau yayi ba,Nazia tana ta yin Assignment dinta a Palo,Kitchen ya nufa Direct Lokacin Nabeela tana juya kaji,Alex lekawa yayi Cikin tukunyar yasa Hannu biyu ya wani Sharon tiririn kamshin zuwa fuskarsa ya wani Shaka tare da furta uhmmmmmm ayi sauri a Gama da fita zanyi Amma na fasa,Nabeela tace kazar Allah ya Isa ce fa,Alex ya zaro Ido yace to komai dama ai Allah ya Isa komai,uban waye yace Allah Bai Isa ba? Nabeela tace ai Allah ya isa akan komai Kam, yawwa to a zuba Mana muci ai isar ta Allah ce ta sa har ya halicce mu ya Halicci kaza da kwanta,dariya Nabeela ta dinga Yi Alex kwadayin bala'i ne da shi,Plate ya dakko Tun Bai Karasa ba aka zuba Masa yana tsaye a kitchen din Yana ci sai tsotse yatsa yakeyi,
Ya girgiza Kai tare da Furta Ko Yahudu ai Dole yace Allah shine ishashe yace ta waye ne kazar? Ta Safiyya ce matar Abba Daya Kuma tawa,Alex yace wannan masifaffiyar? Ae Mana cewar Nabeela,Alex ya tabe Baki yace to shine zata Ce Allah ya Isa? Ai shi yasa ma ya halicce ta sannan yayi Dan kuda da sauro,Nabeela ta zabo cinya a cikin tukunya tana tiriri ta yaga tana ci tace Allah yasa ta siyo wata cikin satin Nan Zan Sato shegiya,Alex Yana ci yace Dama Ni nafi son wacce ake yankawa a Nan take ba irin ta fridge me kankaraba irin wannan tafi Zaki,Nabeela ta kalleshi da kazarta cikin Baki tace Eiiii wallahi Bargonta ma zaka ji Lallai Bata Dade da mutuwa ba,Amma ta fridge Bargonta ya gaji ya ya suma,Nazia Jin su Nabeela Shuru a kitchen Sai kamshi take ji itama ta shiga kitchen din,Alex ne ya Bude tukunya ya zuba Mata da kansa ta karba tare da komawa Palo tana ci,Sai da ta koshi ta maida plate kitchen tace Gaskiya Aunty Nabeela kina so na yau na sake gano hakan,Alex ya dinga dariya yace wato kema Kinji kaza me Dadi Dole kice sai yau Kika San tana sonki.

Nabeela tana Shan Romo tace Ina so na Zama Yar gayu ya za ayi ne Alex dinmu? Oh kin Gama cutar Safiyya Zaki dawo kaina Kuma? Da gaske nakeyi na gaji da rainin mutane so nake na girgiza makiya na da gayu na,wato dai kudi kike so dai a kashe Miki cewar Alex,Kwarai kuwa Amma fa ko na Zama Yar gayu bazan fasa Neman kudi ba Kuma bazan fasa cin uban duk Wanda ya takani ba,To Zaki Zama Yar gayu verysoon tafiya ma Sai an koya Miki irin ta Yan gayu, to Kai ba mutum ba ya akayi ka sani? Gashi Nan Ina kallon film Ina fita Naga Yan Mata,Nabeela ya Kalla yace Zan fada Miki wani Sirri na,Nabeela ta nutsu tace Ina jinka Alex, yace da ace Ni mutum ne da kullum da mace Zan dinga kwana da yanzu ma nayiwa wata me tsautsayin ciki cewar Alex,Nabeela Baki ta rufe da sauri tace Kai wannan Fitsara ce fa ka daina fada Allah ya kiyaye Zina fa zaka Yi kenan? Murmushi Alex yayi yace Allah to ai yasan manufar jaki shi yasa Bai bashi Kaho ba,shi yasa na Zama Ni ba mutum bane,Amma Ina fada Miki da Ni mutum ne to katon Dan Iska ne ba abinda bazan Yi ba,Nasha giya ta,ga Mata,yanda ake Shan sigari ya gwada yace nayi Kuma shiiii...shiiii na zuki Hayaki,Kai Kai Kai naso ace mutum ne Ni Dole nayi bantal uba a kasar Nan yanda nake da kudi,Nabeela ta kwashe da dariya Jin abinda Alex yake cewa ta Rasa Ina ya iya Hausa Haka Wai Dole yayi bental uba.

Nabeela tace to ka godewa Allah da Bai Sa ka Zama mutum ba,idan Kuma Zaki koya min to,Kai Alex ka daina Sha'awar Iskanci Kwarto kake so ka zama? Harara ya watsa Mata yace see you wanne kwarto kuma duk ba ta Haka aka Haifo ku ba Zaki ce Babu kyau,to ai Aure akeyi Alex idan Lallai kana so Aure zaka nema,Lips dinsa jajaye ya turo gaba yace wa Zan Aura Ni ba mutum ba wacce soyayya zanyi? Amma kake son Iskanci Kuma ai sai kayi aure,Idan na gwada yin auren Zan iya dawowa mutum? Nabeela tace sosai ma,to wa Zan Aura bani da Kowa Banda dangi Kuma ai sai dai ki samo min matar,Nabeela tace to Zan Fara dubawa cikin kawaye na Inshaallah Zan samo maka dai dai da Kai wacce ko baka da dangi zamu nemi Dattijai na kirki su Zama waliyanka a daura maka sai kayi abinda kake so amma sai ka musulunta in dai musulma kake so.
Zanyi kokari kafin ki samo min matar Auren na musulunta,Nabeela ta dinga Murna.












AsmaBaffa.
[5/10, 3:23 PM] Sis Asma: 🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠



FREE PAGE






Masu Bukatar shiga group Din GIDAN GWAURO Naira dari biyu 200 ne.

ACCOUNT NUMBER
0175487861
Asmau Garba Muhammad
GTBank

Masu tura Vtu,Transfer,ko katin MTN ta WhatsApp ko sms ga number ta
08033933642

Yan Niger KU nemi wannan number
+227 90 79 59 39









26-30









Official






By
AsmaBaffa.







Page naku ne

Page naki ne ke Daya sharhinki Yana birge Ni

UMMIN SADDEEQ












Kwana Biyu tsakani kullum sai Alex ya tuntubi Nabeela akan matar Aure, Nabeela tace ka Fara musulunta a ranar daka musulunta ranar Zan Nemo maka matar Auren,Alex Yace Ni yanzu ma a shirye nake ya zanyi na musulunta? Nan take Nabeela ta fada Masa kalmar shahada ya Furta shima sannan ta fada Masa dokokin musulunci,wanne suna kake so? Asad, to daga yau ka koma Asad ka tashi daga Alex,sannan tace ya kamata ka dakko malamin da zai na koya maka karatun Addini,Haka kuwa akayi Alex ya dakko babban malamin sunna.
Ranar farko da Malam yazo Alex Yana zaune shima Malam Haka,Idan Malam ya jawo aya kawai sai yaji Alex ya iya ya karasa Masa,Hadisi Suka koma Nan ma idan malam ya fada kafin Malam ya fassara Alex ya Kai karshe ba shiri Malam Yace to Kai ba Christian bane kawai katon Dan Iska ne Kai ba rashin ilmi ba sabo da Haka bazan batawa kaina lokaci ba malam yayi tafiyarsa ya bar Alex Yana kallo har ya gaji da Zama.

Nabeela ya nema suka tsaya a palon kasa face to face Yace to ai yanzu na musulunta sai ki Nemo matar,Murmushi ta saki tare da furta an Gama,Zan Fara tunani wacce zata Dace dakai me Rangwamen gata za a Nemo maka wacce baza suyi wani bincike a kanka ba zasu baka matar Aure,Ranar da yamma Nabeela tana kwance saman Bed dinta ta tuno da Maryam Kawarta tare da ita sukayi primary da secondary Maryam Bata da Iyaye a hannun Yayanta ta taso matar Yayanta ce ta Rike ta,Bayan Haka talakawa ne na gaske Maryam me hankali ce tasan me takeyi da Alama zasu Dace da Alex,Mikewa Nabeela tayi tare da tube kayan jikinta ta daura guntun Towel tare da shigewa toilet tana Wanke Bra da kayan baccinta kala uku,dai dai lokacin Alex Yana ta danne danne a waya Yana duba Wedding party kala kala Yana zabar kalar Wanda zaiyi idan Aurensa yazo,Wani Wedding party ya kalla na Yan Kudu yayi Masa kyau a hankali yace yawwa irin wannan zamu Yi Bari na nunawa waccen yarinyar mu gani ko zata ce yayi.

Bedroom din su Nabeela ya shiga Sai yaga Toilet a bude ganin a bude take kawai ya kutsa kansa ciki,Cinyoyin Nabeela ya Hango lukuta lukuta gasu luwai luwai farare tas,Yaso ya dauke kansa da kallonta Amma ya kasa a ransa kawai Yana Furta ba Mutum bane Ba ruwana Amma ya kasa dauke idanuwansa,Nabeela tsorata tayi ganin mutum a gabanta yana kallonta,Da sauri ta mike tana tambaya Alex au Asad lafiya zaka shugo idan da wanka nakeyi fa? Shuru Alex yayi Baya ko Kyafta Ido,Nabeela da karfi tace Asadddd.....firgit ya dawo hankalinsa ya wayance Yana Sosa Kai yace Na fada tunanin duniya ne akan Aure na,Yana magana Yana kallon Cinyoyin Nabeela da kirjinta,kar....Karrr.....ki...Yi tunanin kallonki nakeyi Ni ba mutum bane ba ruwana da kallon mutane ,Nabeela tace to gashi Nan kana kallo na maganarka ma Sai Ina.ina...kakeyi alamar baka da gaskiya,Alex yace Noooo Yana kallon Nabeela yace Mamaki nakeyi ganin kafafunki iri Daya Dana Muazzam masu suffar kafafun doki na baya,Nabeela tsakani da Allah ta yarda sai ta saki Murmushi tace to shike Nan Bari na saka Kayana,Karki saka fa Ni ba abinda ya dameni kamar dodanniya Haka nake ganinki,Wai ke Fara ce ko baka? Nabeela tace Fara ce Mana,ke doguwa ce? Yes Mana,To Ni naga kalarki Kamar ruwan toka Yana magana Yana ta Shan kallo kallo,Nabeela tace Amma wannan ciwo ya maka Illa,Ni shi yasa Kika ga na Raina ki da yawa Kamar wada Haka nake ganinki Baki da tsayi,Kinga Ni bansan ya kike ba sai na dawo mutum Nan gaba,Nabeela kamar dai zata yarda sai ta fasa ganin kallon yayi yawa,Ta jawo Hijab cikin kayan wankinta, Alex ya saki Kara Kamar Wanda aka tsira Masa Allura ba shiri yace kina sakawa zanga kin Koma Kamar mage,Tana rike da hijab galala tace to ka tafi Mana Dole ne sai munyi Maganar yanzu yau Naga Ikon Allah kaji mutum,Kirjinta ya kalla Kafin yayi magana ya Mika Mata laptop Dan Kar ta Sa Hijab zai dauke Mata Hankali da cewa kinga irin bikin da zanyi kalla kiga video..lekawa tayi tana kalla Bikin ya birgeta ya tafi da Imaninta tana ta kallo Alex Yana ta faman kallonta har dabara ta Fado Masa ya tsuguna a kasa zai leka Nabeela,Waje Nabeela tayi da gudu ta zurma Hijab tare da Mika Masa System tace ungo yayi kyau matuka yanzu zanje wajen Amaryar taka,Ya sunanta? Ya tambaya,Maryam Sunanta yace masha'allah yayi waje da uwar gadararsa,sai da Nabeela ta Gama Abinda zatayi sannan taci kwalliyarta ta fita Da niyyar zuwa gidan Su Maryam,Motar Alex ta tuka zuwa gidan su Maryam,a tsakar gida ta Iske Maryam tana soya Awarar Siyarwa tayi mamakin ganin Nabeela sabo da ita Nabeela indai ba harkar samun kudi bace to fa baza tazo inda kake ba,matar yayarta ce ta karbi suyar, Maryam ta shigar da Nabeela dakinta tana murna tace Nabeela yau a Gari barka da zuwa,Gaisawa sukayi Ta kawowa Nabeela ruwa da Awara,Nabeela tace to kin San Ni ba boye boye Awarar Nan a zuba min ta dari biyu a Leda da ita Zan tafi gida sabo da Albishir din Dana Zo Miki dashi sai kin biya Ni kudi Amma tunda kece Maryam Na yafe ki bani Awara ta dari biyu kacal,Dariya Maryam tayi tace Allah ya shiryeki Nabeela har yanzu dai Baki canja ba,Nabeela tace ke kin San da me nazo kuwa? Ai da ace wata ce sai ta bani dubu biyar Zan sanar Mata,Maryam tace to Ina jinki.

Gyara Zama Nabeela tayi tare da furta abinda ke tafe Dani kin San Wani Alex? Gidan Gwauro Wanda ke kasan layinmu? Maryam ta Lula tunani na Dan lokaci sannan tace yes na tuno wannan Balaraben ko da aka ce ba musulmi bane Kuma Yana da wani ciwo na gogewar memory na kwakwalwarsa ko? Nabeela tace yawwa Yar Gari,to Dan Allah wace zata ga Alex tace Bata sonsa? Maryam tace Babu wlh Ni farkon ganinsa da nayi wallahi jikina rawa ya Fara ya Hadu karshe ga kudi ga sura,Nabeela tace to Albishirinki? Goro fari Maryam ta Furta,Ya musulunta sunansa Asad yanzu Nabeela ta furta tare da Karawa da karya tace Kuma ya warke daga cutar dake damunsa lafiya Lau yake,Maryam tana murmushi tace Masha'allah ai ance a gidan kike zaune ke da kanwarki Babanku ya kore ki? Kwarai Haka ne Maryam a Hannu na ya musulunta nice sheda,Yanzu Aure yake son Yi shine yace na samo Masa matar Aure ta Gari wacce zasu zauna lafiya,Ni Kuma na hanga Naga bani da wata kawa me hankali sama Dake Maryam,Ina kawayenki su Rasheeda fa?cewar Maryam,Nabeela tace duk Yan iska ne Basu da mutunci ke kadai na yarda da tarbiyyar ki.

Maryam tace Kai Nabeela wallahi watarana kina bani mamaki Baki da wayo sai kiyi Abu Kamar yarinya Yar Shekara Uku,Ke banza ce Nabeela to ke gaki me yasa Zaki Nemo wata,ai idan nice ke cewa zanyi ya aureni,dama Zama kikeyi a gidansa ke ba muharramarsa ba sannan ga halin da kike ciki ta Bangaren Babanku to me zai Hana kawai ya aure ki Kinga shike Nan kin Zama muharammarsa gidan ya Zama naki ba me zaginku ko zarginki,Nabeela taji Shawara sai ta manta ta tonawa kanta asiri tace Maryam Baya iya tuna rayuwarsa ta baya,Bai San shi waye ba,Abu kadan ya iya tunawa na baya,sannan wlh wata cuta da yakeyi idan ransa ya baci ko yaci Abinci irin namu na mutane to sai ya koma Kamar Zaki Yana gurnani Kuma idan ya Kama mutum a Haka sai ya yagalgala shi,Sannan idan na Aure shi ya tuna rayuwarsa yaji baya so na fa? Ko ma Yana da Aure wa ya sani.

Maryam a ranta tace muguwa Nabeela Amma shine sabo da son Kai Ni zata kaini masifa to ba da Ni ba,a fili tace Dalla Mene a ciki da Zaman Haka ai gwara ki Aure shi ga kudi kin huta da wahalar rayuwa Kuma zaku shirya da Babanki tunda kinyi aure abinki,Ki rike kanwarki Nazia a wajenki,idan ya tuna rayuwarsa ta baya sai me ko ya sake ki ai dai kinyi auren Kuma wani Zaki samu ki aura,ai yanzu mutuwar aure ba komai bane ya Zama ruwan dare,wlh ki lallaba ki Aure shi Kika sani ma ko ya warke Raina Miki hankali yake Yi,Haka Maryam ta Gama tsara Nabeela,ita Nabeela da tazo Neman Aure sai ita aka nema.

Kuma fa Maryam shawararki tayi,Maryam tana dariyar muguntar da ta Hadawa Nabeela a ranta tace ita ta yarda Lallai Nabeela akwai kuruciya shegiya wato kinzo ki manna min Mahaukaci Kai kasar Nan ba a Taimako Dan Allah ga son Kai,kije kici ubanki a Nan gaba Hannun Alex.
Nabeela Allah sarki tace Kai Maryam na gode da shawararki Zan gwada Amma kina ganin idan nace ya Aure Ni da kansa Nan gaba bazai min Gori ba? Gorin me? Ai maza sun waye yanzu in kina son mutum fada Masa akeyi Direct cewar maryam,To Zan fada Masa na gode,Nabeela zata tafi Maryam ta zuba Mata Awara ta dari biyu da yaji tare da raka ta har mota.
Maryam tana dawowa daga rakiyar Nabeela ta kwashe labari ta fadawa matar Yayanta,Matar Yaya tace Kai Maryam kinyi Shirme ga me kudi Kyakyawa Kika sani ko Rahmar Aure tasa ya warke muji dadin duniya,ko ya tuna baya ai zai iya tunawa ke Matarsa ce Kinga mu Talauci ya Kare Mana Amma kinyi Shirme cuta ai Allah ke jarabtar mutum da ita Yana iya Kuma yaye Masa ko yaushe ai rayuwar Nan ta yanzu baka da dabara baka yiwa Allah wayo Maryam kinyi kuruciya kin cuci kanki yanzu Haka Arziki ne yazo Miki har gida Kika guje shi Baki da rabo inaga a Haka Zaki Kare rayuwarki a Talauci.

Maryam ta zuba Tagumi tare da furta wlh Aunty banyi wannan tunanin ba,kuma Kinga motocinsa sunfi bakwai masu tsada Babu na kasa da milliyan Bakwai Kuma Nabeela duk inda zata wacce ta ga dama take dauka,Aunty tace naganta tayi kiba ta Kara haske ke Kam Maryam kin cuci kanki kin cucemu Nabeela kuwa da Alama zata tsinci Dami a kala.

Nabeela kuwa a kofar gidansu tayi parking a kofar gida ta Iske Abbanta ko kallonta baiyi ba har ta gaisar dashi ta mike Bai kula ta ba,Dubu biyar ta mika Masa tare da cewa Abba gashi,Amsar kudin yayi Bai ko ce Mata komai ba ta juya taja mota tayi gidan Asad,Gab da Magrib ta shigo gidan Tana yin parking ta hango Zakariyya ya cake machine dinsa a compound Kamar gidan Ubansa,Ganin Nabeela sai Zakariyya yayi sauri ya dakko garin magani na tsafi ya Shafa a fuskarsa,sannan ya dakko wani turare na tsafinsa ya goga a jikinsa ba tare da Nabeela ta gani ba.
Yana ganin ta fito dauke da awararta a bakar Leda sai ko Zakariyya yayi sauri ya tari gaban Nabeela,Ita kuwa Nabeela lokacin ta manta wayarta a cikin mota sai ta juya da sauri zata dakko,Kafin ta dakko tazo wajensa Zeena da wata Kawarta Yan shaye shaye sun shugo gidan ta gaban Zakariyya Suka Zo Zasu wuce.

Zakariyya ya Fara boye fuska baya son kowa ya ganshi ko ya hada Ido da shi sai Nabeela Haka ka'idar maganin yake idan wani ya ganka kuka hada Ido to ya karye,Zeena sarkin munafunci taga Dan saurayi so Gentle sai ta tsaya a gabansa daf shi tare da zuba Masa Ido,Jin Shuru sai Zakariyya ya tabbatar su Zeena sun wuce Nan take ya dago kansa Karaf Suka hada Ido da Zeena wacce ke Kare Masa kallo Kamar zata cinye shi,Bakin ciki ne ya Kama Zakariyya nan take ya dinga durawa Zeena Ashar,Tsoro ma ya bawa Zeena ko Mahaukaci ne sai tabi Kawarta da sauri zuwa palo.

Lokacin Nabeela ta tsaya a gaban Zakariyya Wanda a ransa yace duk da nasan ya karye maganin Bari na gwada sa'a ta ko zaiyi aiki a Haka,kurawa Nabeela Ido yayi tare da kafe ta da idanuwansa jajaye,Nabeela ta kalle shi Ido cikin Ido sannan ta shaki kamshinsa marar Dadi,Wani tsanar Zakariyya taji Wanda yasa Nan take ta buga Masa tsaki tare da Furta karka ma Fara Bana kaunarka duk wani jinin su Safiyya wallahi bazan taba sonsa a duniya ba,Ka fita ka bar Mana gida ko wallahi na sa a maka rashin mutunci,Alex Yana samansa a Coridor Yana latsa waya Amma hankalinsa na Kan Nabeela Dake tsaye da wani suna Hira,Bai San dalili ba wani kishi ya Kama shi yaji kamar ya kashe Zakariyya Dan me Zakariyya zai kula Nabeela,Babu Bincike Alex ya dauki waya ya Kirawo su Muazzam Yan wiwi yace Kuna Ina please? Aliyu yace gamu ma zamu Zo gidan naka su Zeena sunzo muma yanzu zaka ganmu mu Biyar maza,Alex yace yawwa kuzo kuyiwa wani dukan tsiya yazo har gidana Yana zagina,Aliyu yace what?...uban wa ya Isa ya taba ka Muna garin Nan karyarsa ta Kare wallahi dan Uwarsa,Ya taba Oga guda Wanda ke bamu kudi Muna harkar ae yane,Nabeela tsaki taja wa Zakariyya ta dauke Kai.
Suna Haka sai ga Su Aliyu Yan daba sun shugo da Manyan sanduna,Aliyu yace kauce ko mu Hada Dake Nabeela,Zakariyya Bai San hawa ba bare sauka sai duka kawai yaji ruwan sanduna ta ko Ina,Nabeela ta hau murna tana ku kara Masa shege tana tafi,Sai da Suka farfasawa Zakariyya jiki sannan Suka dauke shi tare da machine dinsa Suka Ajiye shi a gefen titi,Yana ta ihu da Neman Taimako,Da kyar ya samu ya zaro wayarsa ya Kira abokinsa ya dauke shi sai asibiti.

Nabeela ta dinga Murna ranar Bata yiwa Yan shaye shaye Fitsara ba sai ma Awarar ta data samo ta baje musu a Palo Suka cinye tare,sai lokacin Asad ya sakko kasa sanye da 3qutr da Riga Armless yayi kyau matuka kamshinsa ya cika ko Ina,Hannun Nabeela ya fisga ransa a bace ya jata zuwa kitchen,Yana Huci yace Samari Zaki Tara min a gida? Shuru tayi tana Wasa da yatsunta ya Bata tsoro,a Ina Kika San wannan jakin? Shuru tayi a tsorace idonta ya kawo kwalla ta Fara ja da baya tana yarfe Hannaye.

Takawa yakeyi Yana binta tsawa ya buga Mata Wanda har su Zeena sunji, answer me who is he? Are you mad? Girgiza Kai Nabeela tayi,tace na tuba ban sanshi ba,Mari kawai ya kwada Mata a Ina Kika samo shi? Nabeela ta dafe kumatu tare da fashewa da kuka ta durkushe a wajen tana wallahi...tallahi Ni ba saurayina bane Dan Uwan Safiyya ne matar Abba yazo mu gaisa,Wanin Marin yayi niyyar sharara mata da sauri tana kuka tace wallahi Zan Fadi gaskiya cewa yayi Yana so na,Asad idonsa yayi jajir Kamar wata yarsa yace Nace ki Fara zance? Nace ma a nemi Aurenki? Baki Nabeela ta Bude

Please Login or Register in order to submit comment