Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne a kofar gida an kafa rumfuna Maza Angwaye suna Zaune Haka Mata da Yan Mata Wai Kamu akeyi sai da akayi Wasa Kala Hudu su Nabeela ne cikon Na biyar sabo da kudi,gashi party sai da akayi kala Uku Hadaddu,Su Ladi an tsege Dauri da speakers ga kayan kida da sauran tsofaffin Mata,Nabeela itace me tsince kudi,Alex ya Sa aka Saita mota dai dai inda zai iya kallar duk abinda akeyi,Shi da Nazia Fitowa sukayi Suka tsaya a jikin mota tana rike a hannunsa,Yan Mata suna ta parking motoci birjik iya kallonka motoci ne a wajen wasu sun kawo kansu wasu an kawo su,biki Yana Dadi sosai Alex Yana ta kallon Yan Mata Yana Jin dama shi mutum ne,musamman idan yaga Hips da kirji sai yaji Hankalinsa ya tashi har wani lumshe Ido yake Yi, Tunda ya tsaya ake kallonsa ya Haske kofar gidan bikin sabo da wasu Sunyi zaton ma balarabe ne sai kallonsa Yan Mata sukeyi Ana hadiyar yawu,Sai wucewa sukeyi ta gabansa suna Taku ko Allah zai sa wata tayi da Dace ya kyasa.

Wata Kyakyawa ce Yar budurwa ga Hips ta Dame jikinta ansha Karin gashi taci make up tayi kyau ba karya kana ganinta kaga yar wani me kudin,Gaban Alex ta tsaya tare da Mika Masa waya tace Dan Allah Malam daukeni pics pls,Alex ya kalle ta Up and Down kallonsa na Raini Wanda sai da ta Raina kanta Alex Kam yaga akwai Hips ba karya ya jinjina Kai yace kinyi rashin Sa'a Ni ba mutum bane ko mutum ne bazan taba daukan wata pics ba sai wacce nake so Abin mamaki Bai karewa in Banda halinku na mutum kece fa gaki nan kin San kanki Amma to ki dauki Hoto kiyi me da shi,Budurwar tayi murmushinta Me kyau lokacin Nabeela tana fili ta hango Alex da wata Yana ta magana tana murmushi,Speaker ta karba da karfi tayi magana sai ji akayi ance Yan Mata masu ganin mazan wasu su kyasa ayi Hattara ku dawo rawarku ta rawa da liki ya fiye muku mutunci baza ku samu Nasara ba Gomnati ta Hana Auren Mata biyu sabo da yawan Haihuwa kasa ta cika dam Babu wajen Karo Yara ko wacce tasan ya zata tayi da Mahaifarta,Dariya ce kawai ke tashi wajen Angwaye da Amare anyi zaton Nabeela Kawai Dan ayi dariya ta fada,Budurwar Dake gaban Alex ta fashe da dariya itama tare da juyowa tana kallon Nabeela Dake Maganar,Nabeela ma ta kalleta ta sake cewa ke daga ganin Dan Bature sai ki manne to ba mutum bane ki samawa kanki lafiya baza ki birge shi ba ke da maza Baku da banbanci a wajensa,gaba Daya Budurwar kunya ta kamata Nabeela ta Tona Mata asiri anyi Harrrrr kanta Ana kallonta sum sum ta silale ta shige gidan su Amarya.

Ladi tace a Fara Kida kafin Amarya ta fito Nabeela ki danyi rawa kafin su Zo,Nabeela kunya take ji Alex Yana kallonta zata Yi rawa,a ranta tace Mutumin da yace shi ba mutum bane munafuki rawa ta zanyi bazai Zai wani zo ya Hana Ni sakewa, Kamar Wasa Alex ya Bude motarsa ya dakko Sababbin kudi Yan Dubu dubu yau zai nunawa Nabeela yasan me mutane sukeyi,Kawayen Amarya sai kallon Nabeela sukeyi a Banza irin talakawa wa zai saurereta har Tausayinta sukeji Talauci yasa tana karama ba Ilimi sai kidan Kwarya take bin Mata,Nabeela kasa rawar tayi Ladi tasan Nabeela Bata rawa sai taga dama take yin kadan,Yanzu ma Kamar baza tayi ba sai ta Dan Murguda Kowa ya gani yasan ta kware duk da Bada yawa tayi ba,Alex ba Wanda ya sanshi anyi zaton ma Cikin abokan Ango yake kowa kallonsa yake Yi sabo da kalarsa daban data kowa ya gaji da Haduwa,Yan Mata sai zare idanu sukeyi sun ganshi rike da Hannun Nazia ya nufo filin,Yan Dubu dubunsa ya Fara likawa Nabeela wacce ke tsaye kikam kunya tasa ta kasa komai,mutane sunga ruwan Naira kowa yaga Alex yaga me kudi,A hankali yace ke muje gida wannan ba sana'a bace ta kirki ga Mata Nan masu Aji suna kallonki a banza,Nabeela tace Ina ruwanka kudi na Zan samu,Alex yace wlh sai kin tafi gida,sai kazo ka Jani na tafi Nabeela ta furta da Rashin kunya,Ganin zata Bata Masa lokaci ya Karasa Inda Ladi take ya Mika Mata kudade masu yawa yace karki sake Kiran wannan yarinyar wannan sana'ar taku tafi karfinta,Ladi taga kudi tace Angama yaro,Hannun Nabeela yaja ta tirje zata Yi kuka,Mutane suna kallo suna mamaki,ganin Taki yarda Alex yace Ku taimaka min jama'a kanwa tace Tabin kwakwalwa ne ya same ta sati guda kenan da bacewarta Muna ta nemanta,Ai kuwa mutane Suka taho yuuu za'a Kama Nabeela wasu dattijan Mata suna Allah sarki Allah ya Baki lafiya Suka damki Nabeela tare da jefata a bayan motar Alex yasa lock Alex da Nazis suna gaba yaja mota Suka bar wajen.

Nabeela Kam Alex ya sata dariya da ya kala Mata wannan sharri tace wlh sai na Rama zaka sani,Nazia ya kalla yace Ina Za muje Babynmu? Ice cream zamu Sha ya dauke Hanya suka wuce wurin Shan Ice cream da kayan tande tande Yana kallonsu Abinda suke son ci da Sha Suka zaba shi Kam Bai dauki komai ba Suka Gama ya biya kudi Suka wuce gidansa,suna yin Sallar Isha ya Maida su gida ya koma gidansa.
Abba Yana kofar gida yaga an sauke su Nabeela a fusace Abba ya bisu cikin gidan,Nazia ya tallafewa keya da karfi yace Dan Ubanki bana Hanaki Binta yawon Gantali ba? Kuka ta saki cike da tsoro ta koma jikin Nabeela tare da boyewa,Nabeela tace Haba Abba Wannan Bai Dace Ba Kamar ba yarka ba wlh ka yarda Dani ba abinda nakeyi na Iskanci karya kike Yi duk sana'arki Babu ta Kirki ance kiyi karatu kinki shine Zaki samu aikin Gomnati me tsoka,Nabeela tace Wa zai dauki Nauyi? Kasan dai karatu yanzu sai me kudi,Da me zanji ciyar da gida? Makarantar Nazia da suturarta? Ina zan samu kudin Daukan Nauyin makaranta ta? Kasan ba Aiki ne Dani ba,kawai buga buga nakeyi Ina zubar da mutunci na Ina kawo wa gida Ana ci,wlh Abinda nake ko a maza ba kowa zai iya ba,da karfi Na da lafiyata nake nemowa duk dan mu rufawa kanmu Asiri na rufa maka Naka Asirin Abba ya kuke so nayi da Raina? Karatun Boko ko anyi shi yanzu Aikin Gomnati sai me rabo,kana gani Yanzu ko dako ko tura Kura matukar Gomnati ce zata daukeka to baza ka samu ba comon Dako ko tura Kura Gomnati Bata iya dauka,idan ma Tana dauka manyan ne ke siyarwa Offer ma yanzu sai me kudi shike siya.

Nazia ba abinda tayi maka Abba Ka daina dukanta ko Mene kayi min ba Nazia ba,me ta sani yarinya karama ta taso cikin wahala Amma ba a tausayinta,Mahaifina ne Kai Amma Abba ka tausaya Mana me yasa ka canja Mana? Me mukayi maka? Nabeela ta furta tare da fashewa da kuka tana cewa shi yasa wallahi ko zaman gidan Nan bana so yanzu,Tsaki Abba yaja ko a jikinsa sai ma cewa yayi kiyi dai a Hankali karki kwaso cutar HIV wa sani ma ko kina da ita ya shige dakin Safiyya,
Nabeela kuwa Share Hawayenta tayi ta shiga Lallashin Nazia suna Haka yaro ya shigo dauke da Sallama yace Nabeela Wai tazo Ini Zakariyya,Nabeela tana mamaki waye Zakariyya ita Bata taba sanin wani Zakariyya ba,Haka ta yafa mayafinta ta fita ranta a bace,Tana fita ta Hango Zakariyya Saurayi matashi Dan gayu Dan kwalisa Baki wuluk Amma Kyakyawa dashi wayayye so Gentle Yana kamshi,Nabeela ta Masa Sallama tare da gaisar da shi,Cike da nutsuwa Yace Nabeela Abinda ya kawo Ni Wajenki ba komai bane face so,Nasan Baki sanni ba Amma Ni Abokin Huzaifa ne Tunda na ganki kinzo Neman Huzaifa muna tare sonki ya shiga zuciya ta,Na Samu Huzaifa da Zancen yace nazo da kaina,Sai da Nabeela ta Gama Jin komai tace Malam Zakariyya kayi hakuri HIV AIDS ce Dani,Zakariyya ya rike Baki yace a Haba Wasa kike, Nabeela tace taimakonka zanyi karka sheka lahira da wuri,Zakariyya tsoro ya shige shi Nan yayi Mata Sallama ya tafi Yana godewa Allah yace Allah ya taimakeni Dana Aure ta sai dai nace Allah ya ji kaina.

Washe Gari da Sassafe Safiyya ta zuga Abba ya fito ya dinga bala'i yace Nabeela jiya Safiyya kaninta Zakariyya yazo zance da gaske zai Aure ki Kika Kore shi kince HIV ce dake yanzu;,;, kanin Safiyya din guda? Nabeela ranta ya baci tace Dama Kanin Safiyya ne dama munafuki yace Abokin Huzaifa ne? Allah ya Isa Bata bakina da nayi da kulashi da nayi bazan yafewa Safiyya ba,Kuma Allah ya tsinewa Dangin Safiyya gaba Daya ba uwata bace Nabeela ta furta da karfi,Safiyya ta fito ta fashe da kukan munafunci tana cewa Baka so na Hashimu wallahi baka so na Yarka ta zage Ni da Iyayena ka barta a gidanka,Abba ya rude yace ke Nabeela dauki Nazia ku bar min gida kije gidan uban da Zaki ko ki kawo miji na Aurar dake idan Kuma baza ki kawo Mijin ba to ki tafi na kore ki sanda Kika samo miji ki dawo Na Daura Miki Aure,Nabeela tace Ba inda zanje Me yasa aka haifeni,Abba wuka ya dauka ba tunani ya jefi Nabeela da ita ta sauka a gefen kafarta tsinin ya Huda Mata kafa jini na zuba.

Nazia ta kwala ihu tana cewa Aunty mu bar gidan Nan Dan Allah,Nabeela kayan Nazia da nata ta kwaso tas Suka Yi waje gaba Daya,Safiyya da Hajiya Binta harda Rawa suna shewa da Dariya,Abba Kuma Haka kawai yake Jin kunci da bacin Rai baiyi murna da Tafiyar su Nabeela ba Sam Kuma Bai son su zauna.
Nabeela direct Gidan Alex Suka wuce Alex ta sama ya hango su sun shugo farin ciki ya Kama Alex dama Zama shi kadai ya Dame shi,Nabeela ya hango tana kuka tana Kokarin share Hawayenta,Nazia ma Haka kukan takeyi, Bai tunanin komai ba yasan Abbansu ne kawai ya kore su tunda yasan komai shi murna ma yaji ya samu Yan Uwa zai koma Kamar mutum.
Allah yasa su zauna tare gaba Daya,Palo ya sakko tun kafin su karaso.








AsmaBaffa.
[5/10, 3:23 PM] Sis Asma: 🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠



FREE PAGE








GA MASU BUKATAR NOVELS DINA NA KUDI KO WANNE DARI UKU 300 COMPLT

RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDU'AR KAWA


MASU BUKATAR SHIGA GROUP DIN GIDAN GWAURO NAIRA DARI BIYU 200 NE


ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK


MASU YIN VTU TRANSFER KO TURA KATIN MTN TA WHATSAPP GA NUMBER NA
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39





21-25





Official






By
AsmaBaffa









Page naku ne

RABIYA BASIRU
HUMAIRAH MK
MOM FATIMA










A gabansa Nabeela ta tsaya kanta a kasa tana ta sharbar kuka sosai Harda shesheka,Tausayinta ya Kama Alex Bai San sanda ya Rungume Nabeela a Kirinsa ba,tayi luf tana shesheka Sun dauki lokaci dogo a Haka tana kwance a jikinsa kafin daga Bisani ta daina kukan ta Fara Murmushi tana danne Zuciyarta tare da Goge Hawayenta,Nazia dama tuni ta daina kuka,Abba ne ya kore ku? Alex ya tambaya,Idanunta Dara Dara ta dago tare da zuba su cikin na Alex a hankali tace ae,Fine ga gida sai mu zauna tare Baku da matsala cewar Alex,Kayansu Suka Ajiye a bedroom dinsu da Suka zaba can upstairs kusa Dana Alex sannan suka dawo main Palo tare da Zama ya kawo musu Chanel din American film suna kallo ba Wanda ke magana sai Idan Anyi abin dariya suyi.

Safiyya burinta ya cika Nan take ta shige Dakinta tare da Kiran wayar Kanwarta Murja,ko gaisuwa Babu ta Bata labarin komai,Murja ta rangada shewa tare da Furta Haka nake sonki Aunty na, shegiya matsiyaciyar yarinya gwara ta daina ciyar da ku tana rainaku,Da Yar Kishiya ta ciyar Dani gwara na kwana da yunwa cewar Murja,Safiyya tace Nima Haka musamman Irin Nabeela gwara muci talaucinmu abinda ya samo a gyaran takalminsa ya ishe mu,Gwara nayi sati Ina Shan garri da sugar,Amma fa in fada Miki da kyar ya koreta Murja Ina tsoro Kar ta dawo shegiyar yarinya ce,Murja taja tsaki tare da furta ki jira Ni gobe Zan kawo Miki kayan aiki ai ba a tsayawa dama idan kayi kayi sai ka Dan huta sannan ka sake danno wani Asirin kin San ko Addua ce ka daina Yi to fa Allah bazai kalle ba sabo da ba a tsayawa ki Nemo Min dubu biyar zanje kawai idan na kawo maganin sai na karba na kaiwa malamin,Safiyya tace ai ba yawa ma kudin,Ae Mana a kauye akan dari biyar sai malami yayi kisan Kai ma ba ruwansa bare na mallakar miji ba irin Malaman birni bane Wanda kudi kawai Suka sani sannan baza suyi maka aiki ba yanda ya kamata bacci zasu Sha suce Zaki ga aiki sai su cinye Miki kudi a banza Amma na kauye kuwa ba yaudara Aunty na,Ni wallahi Murja Dan kin matsa ne Amma Banga abin da zanyiwa Asiri ba a jikin Hashimu shi ba kudi ba sai gyaran takalma uban me yake da shi matsiyacin banza Yana tafiya kamar iska zata bushe shi sai shegen kai kamar Faranti Ni duk na tsaneshi sabo da talaucinsa shege Dan Iska, guntu, asararre,Murja ta dinga yiwa Auntynta dariya tana cewa Mata gaskiya muji tsoron Allah daga an Mana kishiya sai mu dinga zagin mazazenmu Muna Gulmarsa Mata masu zagin mazajensu ku tuba dariya Safiyya tayi tace ai kishiya ba Dadi shi ya jawa kansa da ace baiyi Aure ba wlh bazan Masa asiri ba Dan Banga me zanwa asiri ba a Hashimu Wanda kansa ma bazai iya rikewa ba,Ita Kuma lusarar tasa Hajiya Binta ko ladan aure Bata samu baya Ko saduwa da ita Amma in fada Miki Jakar tayi Shuru abinta tana zaune Bata ko Zancen,Aikin Malam kenan cewar Murja,sun Dade suna waya.

Washe Gari da yamma Murja tazo ta bawa Safiyya maganin tace wannan a Abincin Zaki saka Masa yaci idan yaci shike Nan Su Nabeela ko a Hanya ya gansu bazai ma kalle su ba Kamar Dodo Haka zasu koma Masa sannan Zaki sake mallake shi,Ga wannan turare ne zakiyi idan Kika Yi Hajiya Binta ta Shaka to ta Zama baiwarki gaba Daya, shewa Safiyya ta saki Suka tafa sannan ta mikawa Murja dubu biyar,Murja ta gyara Zama tace sai Maganar Zakariyya Yace shifa Yana son Nabeela da gaske idan kinji inda Suka koma ki fada min sabo da ya bita can Yana zuwa wajenta shima Zan bashi maganin da Nabeela zata fada sonsa Kinga shike Nan Allah yasa dai Bata San Cousin dinmu bane ko? Ta sani da babanmu da babarsa Uwa daya uba Daya suke,Kuma Nabeela baza su Wuce gidan Gwauro ba ki Tura Zakariyya can Zance,Murja tace ai Dole nayi Masa hanya ya same ta tunda Yana sonta Kuma kin San Zakariyya da Neman Mata tunda yaga Nabeela nasan Burinsa ya lasa zumarta Amma Yace Wai da gaske sonta yake Yi aurenta zaiyi koma dai mene Ni Zan Masa hanya ko ma Mene yayi da ita sabo da Ina morar Zakariyya Duk wata idan ya dauki Albashi dubu uku,dubu biyar dubu Daya duk Yana bani rannan ma katifar da yarana zasu kwanta shi ya siyo min sabuwa dal wajen dubu talatin.
To yaje gidan Gwauro nasan tana can kice ya nutsu ya nuna Mata Halinsa na kirki kin San mayyar kudi ce ya nuna Mata kudi akwai harka,sannan kin San tasan ya shafe mu ayi Mata yanda zata kulashi ta soshi,ai na Gama Hada Zakariyya da Magungunan wajen Malam,shima Kuma Yana Yi da kansa kin San ko Neman matansa Yace da asiri yakeyi sai kiga mace ta kasa hanashi abinda yake so,Safiyya tace to yaje ya Gama da da shegiyar Nan ai Nabeela ko Fyade aka Yi Mata murna zanyi,ke nifa idan akace Asiri ya karye Abba zai dawo da ita Nan gidan to wallahi asiri Zan mata ta fada karuwanci.
Haka Suka Dade suna hada muguntarsu.

Washe Gari Da Yamma likis Nazia tana Islamiyya Nabeela ta fito zata Dan zaga layin Su Alex sanye take cikin Atamfa Riga da skert tayi kyau ta yafa mayafinta kalar kayan,Tana tafiya ta ci Karo da Kawarta wacce itama tare sukayi Secondary Habeeba,Habeeba Yar karya ce ta gaske da gayu Bayan gidansu Basu da sisi,Laaa Nabeela kece? Habeeba dama kina Nan? Habeeba Tasha wata Arniyar shadda me tsada tayi kyau,Nabeela tace Habeeba kina goge duniya irin wannan wanka Haka Kamar baza a mutu ba,Habeeba ta karewa Nabeela kallo tace Nabeela wato ke baza ki canja ba? Har Abada baza ki waye ba? Baki da maraba da Yar kauye kullum Haka aka sanki Dan Allah kiyiwa kanki fada kalli kayan jikinki dinkin tsohon yayi duk sunji jiki, duk baiwar Kyawun Nan naki da Allah Baki bakya kula da kanki,yanzu an waye Ko gidanku ba kudi ga samari nan masu kudi masu motoci,kin fini gata Nabeela Ni Marainiya ce Amma kalle Ni samari na rike suke min komai wlh da Zaki gwada Da kin Faso Gari ba sai kin Yi Sex da su ba Dan Romance ma kadai kudi Zaki na Samu kina damfarar shegu,Amma kalle ki wa zai soki a Haka? Tafiya kamar ta maza,ba yanga ba Jan aji ai wlh baza ki samu miji na Gari a Haka ba,maza yanzu sai me daukan wanka,Babu Wanda zai ko kalle ki ya kamata ki canja please Shawara na Baki.

Nabeela tunda Habeeba ta Fara kallonta kawai takeyi har ta gama sannan Nabeela tace Baki ji sunanki ba Habeeba Ni Kuma Nabeela tsarin rayuwarki da kaddarar ki daban tawa daban,kin san meke damuna? Kin San matsala ta? To abinda yake cutar mu a duniya kenan mu Amsa jarabawar da ba taka ba Kinga Dole ka fadi,Kamar ya? Habeeba ta tambaya,Nabeela tace Hmm kamar Questions paper ne aka Baki naki kalar tambayar daban nawa ma daban sai na copying amsarki na amsa jarabawa ta Kinga Dole na Fadi ko? Habeeba tace ae, to Kamar Haka ne a duniya Kuma yanzu kece kike copying na wasu karshe kici Kan jaki wallahi ki gyara rayuwarki wannan abinda Mata keyi na damfarar samari suna samun kudi shike binsu gidan Aure suna samun mazajen bana Gari ba suna cin ubansu to hakkin samari ne ya Kama su,Baki sonsa Baki sonsa kawai,Iskanci yazo dashi baza kiyi ba shike Nan,Idan Kika biyewa mazan yanzu Matse Miki jiki zasuyi a banza kin Zama Shaddar kasuwa,Wannan ya jagulaki ya Bawa wannan kina ganin ba komai to wlh irin wannan zunubin da ake rainawa shike taruwa da yawa ya Kai mutum Jahannama.

Allahu Akbar Habeeba ta furta da gatsali tana yiwa Nabeela kallon banza,Banza sai ki zauna ai baza ki waye ba,Nabeela ta gyara tsaiwa tare da Bata Rai ta Hura hanci tana ciccjiyewa tace ke Habeeba yane? Wallahi sai na tuburbudaki a kasa yanzu nan na kunyata ki a Nan kin San Banda mutunci Ba kunyar uban kowa nakeyi ba Ke kin sanni bana daukar hauka Ni Zaki rainawa Hankali har yaushe Kika waye? Wankan Nan Nima fa niyar daukarsa ce banyi ba Amma a Haka muje wajen maza mu tsaya da Ni da ke aga Wanda za a dauka,ke da kike shafa Mai ma kowa ya ganki yaga Blitching har Ni Zaki Zo ki rainani uban me Kika Tara? Kina marainiyarki wuce ki tafi wajen Goggonki shegiya goyon Kaka,idan kinje gida ki fadawa kakarki dake rike ki Bata iya ruko ba.
Habeeba tace ke Kinga karki zageni daga na fada Miki gaskiya,Uban Gaskiyar Taki Na zageki me Zaki Yi Dan Babanki kije Ki ta rabawa Mazan jikinki Ina ruwana,Kin San dai ko a baya dukan tsiya nake Miki to yanzu ma ba ruwana zaneki zanyi,Cike da takaici Habeeba ta furta dama Iklima sani ce tace idan mun ganki a fada Miki gaskiya ki waye,To ki fadawa Iklimar na zagi kan Uwarta,Ubanta ya masgi Kan Uwarta tazo da kanta idan ta isa,Ba shiri Habeeba tayi Tafiyarta ta bar Nabeela Wacce itama ta Kara gaba abinta, Napep ta Shiga zuwa kofar gidansu Inda Abbanta yake Zama taci sa'a kuwa Yana kofar gida a Zaune Nabeela ta karasa Inda yake Abba ya na ganinta ya mike zumbur Yana Salati Kamar yaga Aljana.

Baba Ina Yini? Yana gidan biki ko na saki ki gaishe ni? Gaisuwar ki nake Nema? Bari kiji Bana son ki gaishe Ni Indai gaisuwarki ce bana so Kuma bana bukatar girmamawarki idan kina so na kula ki to ki fito da miji na daura Miki Aure buri na kenan,Murmushi Nabeela ta saki tare da cewa ai kuwa Abba zaka gaji da kin amsa gaisuwa ta sabo da Ni bazan yiwa kaina Dole ba bana son Abu bazan ce Ina so ba Haka kawai nayi auren bakin ciki bazan Yi ba yawwa Haka kawai ba kune zaku zauna da Mijin ba nice dama ba zuwa nayi muyi wani zance a,Kazar Dana siyo rannan na sata a cage ita nazo dauka sabo da Hakki nace Ni Kuma Kun San bana Wasa da dukiya ta ko jariri ya taba min dukiya Tatsile shi zanyi zanje na dauki abata, kuma ka tsawatarwa matanka a yau idan wata ta min Maganar banza to wallahi kifarta zanyi Ni mutunci yayi min karanci ba wani wadataccen mutunci ne Dani ba,Cikin karaji Abba Yace Matan naw....kafin ya rufe Baki Nabeela tace kwarai kuwa ai ba iyayena bane,Takari can ka ganta ba wata makka da taje cutarka tayi filin yakin Badar da Tabuka a can aka zube su ta Gama badalarta ta dawo aka caka maka, miyar Dage dage Bata iya ba Ina ga ta Habbatussaudat,Abba Yace a Haka na gani Ina so Kuma tafi min ke,Tafiya Nabeela tayi zuwa cikin gidan,Tana shiga da Plate ta ci Karo a kusa da zaure kafa ta sa tare da yin Ball da shi ta shiga bako sallama,Hajiya Binta da Safiyya suna tsakar gida Daya tana wanki Daya Kuma na wanke wank.

Safiyya Gabanta ya Fadi tace keeee...dama Baki hakura da gidan Nan ba? Kuma gidan musulmi ki shugo bako sallama? Nabeela tace au dama da misulmi a gidan nan? Abba ne kadai musulmi kuma yana kofar gida aike Safiyya Babbar Arniya ce ke Baki sani ba? Ai kin Dade da fita daga musulunci kinyi ridda,Tunda kike shirka kina zuwa gidan bokaye ai kin Zama kafira,ke Kuma Hajiya Binta dama zunubin da Kika kwaso a dajin Makkah ma kadai ya ishe ki,Marasa amfani ku dai Allah wadaran Halinku,Safiyya ta kalla Nabeela ta nuna da yatsa tace ke daga yau sunanki Nkeci sabo da dama Kara nake Miki Ina ce Miki Umma Safiyya Amma yanzu ba sunanki Safiyya ba Nkeci,Baki Suka Bude Nabeela tace kun dade Baku Bude Baki ba kuma zakaranki na rannan Daya Bata wallahi nice na dauke shi lokacin Alex Yana dakina da shi Muka kwana a cikin daki shi na dafawa Zakaran Nan yaci Muka Sha ruwa Me Kika Isa kiyi akwai wacce ta Isa tayi magana yanzu sai na fasa Muku Kai,Nabeela haushin an koreta daga gidan ta koma Kamar mahaukaciya ta dinga masifa Kuma tana tonawa kanta asiri irin abinda tayi na tsiya Dan suji Haushi.

Tsoro sukaji Basu iya cewa komai ba suna kallo ta Bude cage din kaji ta damko katuwar kazarta ta turawa guda Daya tal jibgegiya da ita dama kiwatawa takeyi sabo da ta dinga musu kwai Daya kullum sabo da ta soyawa Nazia tana ci da safe,Saura kazar Safiyya a ciki itama ta turawa ce Nan ma Nabeela ta damko ta tace da wannan Zan hada idan kin Isa kiyi magana wlh Naja Muku asarar dubu goma akan kazar dubu biyu,sai dai kiyi Allah ya Isa Safiyya Nkeci ko Kuma ki sa a gewaya min Alqurani yanzu a gidan Nan,Shuru sukayi a tsorace suna kallo,Nabeela tace yau dai dai nake daku ba mutunci yanzu

Please Login or Register in order to submit comment