Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaza a bakinta,Alex duk abinda takeyi Yana jinta Bai kulata ba Yana ta Hawayensa har Nabeela ta Gama Cin Abincinta Tasha fruits ta wanke bakinta da Hannunta ta koma Daya gadon da ba kowa ta kwanta tare da zubawa Alex Ido yana ta kuka,Kukan ma Kyau yake wa Alex Nabeela tana ta kallonsa a fili ta dafe Zuciyarta tace ke zuciya daina kyasawa kudi kike so ba ganin kyau ba.

Wasa Wasa Har Alex ya Kai wurin 11pm Yana kuka lokacin ya Fara bawa Nabeela tausayi ta mike zaune tace Haba Alex Kai kuwa ko Nonon Shekara Goma ka Sha Mum dinka Bata yayeka ba ai ka hakura da wannan kuka,Haba ace kafi mace kuka,Nan ma Alex ba magana Nabeela tace to ko cikinka kwantacce ne sai da kayi Shekara Biyar a ciki ba a haifo ka ba shi yasa shakuwar tayi yawa?
Sai da ya shafe kusan 2hrs Yana kuka sannan ya hakura ya daina ya mike a hankali ya shige Toilet abinka da asibitin masu kudi ka rantse Hotel ne,Fitowa yayi ya kalli Nabeela da jajayen idonsa yace Brush fa? Da towel? Da sauri Nabeela ta duba cikin kayan data kawo ta Mika Masa harda Sabulu,ya Dade a toilet kafin ya fito Daure da towel a kugu,Nabeela taga sura me kyau iya Sura ba shiri tayi waje da Sauri.

Lotion dinsa data kawo ya Shafa sama sama yasa Wata Jallabiyya Fara me kyau da tsada,Yana dubawa yaga Ashe har Short trouser ta dauko Masa ya saka tare da linke Wanda ya cire ya adana a wata Leda ya koma saman Bed zai zauna kenan Nabeela ta shigo Suka hada Ido ya kalleta yau harda hijab dinta Kato me Hannu tayi kyau Kuma,Da sauri ta Jawo take Away ta Bude Masa Gasashen nama ruwa ruwa da Salat da tumatur Kamar yanda taga Yana ci,tace shegiya yunwa tumbi baya jira ungo watsa Masa harka,Ganin Abinda zai iya cine sai ya mike ya karba da sauri sabo da yunwa yake ji,Doctor ne ya shigo da murna ganin Alex yaji sauki har zaici Abinci,da sauri yace Na fada Miki Nabeela ya samu buguwa a Hannunsa kar ya dinga yawan motsa shi kina gani sai da aka gyara Masa Hannun,Nabeela tace har wanka yayi,Alex yace da Daya hannun nayi Amfani ai,to dai ka kiyaye na fada muku ya fita abinsa.

Abincin Alex ya mikawa Nabeela ta karba tare da gyara Zama zata bashi a Baki yace Ni karki bani da Kazamin Hannunki,Iyyeeee Ana tausayinka baka Tausayin kanka to Ni bazan iya yanka kaza da spoon ba,Ala dole ya dinga karba tana bashi Yana ta turo lips dinsa,Nabeela Bata kula Shi ba kanta Yana kasa kunya take ji ma,kadan ya rage sai da yaci ya koshi sannan yasha Fruits da ruwa,Da kansa ya goge Bakinsa da tissue tare da kwanciya Abinsa.
Itama komawa tayi ta kwanta bacci ya kwashe ta shima Haka,Sai 2am ihun wani marar lafiya ya farkar da su,Nabeela ta mike ta zauna Alex ma haka,tambaya ya jefo Mata Wai ke gidanku ba a kula da ke? Naga wasu matam Cikin mutane kowacce Ana kula da ita ke ya akayi ake kyaleki? Nabeela tace yanzu Kai ba mutum bane idan na fada maka tarihina ba ganewa zaka Yi ba,Fada min Haka Ina ji,Dole Nabeela ta gyara Zama ta kwashe tarihinsu kaf ta fada Masa,Yaji Tausayinta sosai yace Amma me yasa bakya zuwa wurin Dangin Babarku? a kauye suke bazan iya Zama ba sai dai watarana Ina zuwa gaishe su,Kuma Abba ma bazai Bari na koma can ba,Kuma Mamanmu danginsu Basu fiye yawa ba,Alex yace to ba sai kiyi Aure ba Ki huta kawai,Nabeela tace bana son kowa ban taba soyayya ba ban San so ba,Alex yace Lallai Ashe Baki taba Kiss ba ko? Nabeela ta rufe Ido sabo da kunya tace ai sai anyi Aure ko?

Ina Zan San wannan Iskancin naku na mutane,Nabeela tace Ina so wlh Allah bani miji me tsafta da kamshi Amma idan na Samu gara Allah bazan yarda ba idan ya takura min da kiss sai na rushe Masa hakoran gaba,Alex Bai San ma yayi Dariya ba,Nabeela tace Wai duk a Ina kasan wannan Abubuwa ne? Hmm wurin su Muazzam da Kuma kallon Film,Idan Anyi Aure sai a bawa Namiji matar ko? Nabeela tace ae tayi ta Haihuwa Ana karuwa a duniya,Alex ya tabe Baki yace to kiyi sauri ki Nemo miji kema Kinga Zaki huta da wannan wahalar duniya Nabeela tace ai Ina ga Ni Bazan samu Wanda nake so ba a duniya sai kwayayen Haihuwa ta sun mutu murus duk wata Ina ta saka kwai a banza suna ta mutuwa bani da mashinshini bare nayi Aure ba Wanda yake so na sai tarin Aboka,Suma Yan iska Su Huzaifa duk abotar da muke Babu Wanda yayi min Kara yace Ina sonki Nabeela ko da Wasa zasu ci ubansu Allah yajin aikin kulasu Zan tafi.

Alex cike da Tausayawa yace Allah sarki kinyi kwantai sannu kinji Allah kawo me siya,Dariya Nabeela ta dinga Yi Bata taba Jin Alex yayi magana Haka me tsayi ba Lallai yasan Abubuwa yanzu.
Sun Dade Suna Hira kafin su koma Bacci,da Asuba Yana gani Nabeela tayi Alwala tare da Sallah tayi Azkhar ta koma Bacci,sai 7am ta fita da sauri a motarsa,Gida taje ta Kai Nazia school tayi wanka ta canja Kaya cikin doguwar Rigar Lace ta yafa mayafi harda kwalliya tayi kyau matuka kamar ba ita ba,Ta figi mota kamar ta Ubanta ta siyowa Alex kalar abincinsa da nata kalar ta dawo ta Iske shi yayi wanka ya shirya fes da shi Yana latsa wayarsa,Tana shugowa Alex ya kalleta ta Masa kyau matuka kasa daina kallonta yayi har sai da taji kunya,Abincin ta Mika Masa yau da kansa yaci abinsa ya koshi Yana ta faman satar kallon Nabeela,tana ankare da shi sai wani Kara gyara Zama takeyi tana wani yanga wacce Bata San ta iya ba sai yau,Alex har ya Gama ya kwanta Amma kallon Nabeela yakeyi kawai ba kyafta Ido.

American Film suke kallo a tv plasma Dake dakin Suna Sharhi sama sama,Idan Alex ya tuna Mum dinsa sai ya Fara Hawaye sama sama,a Haka suka kwashe kwana biyu a Hospital ba laifi Alex ya rage damuwa sosai aka sallamesu da yamma,Ita tayi Driving Yana gaba zuwa gidansa,a ranar ta zage ta gyara gidan ko Ina,kayan wanki ta tattara ta Kira me wankinsa ya karba,Yanda taga Yana girki Haka tayi Masa da dare harda ita irin nasa taci ranar,Haka Har Dare yayi suna Palo suna kallo tare suna Yar Hira sama sama sabo da Alex Bai son surutu shi,Sai yaji Bai son yin Nesa da Nabeela,tunawa Yayi shi fa ba mutum bane kawai ya mike tare da Haurawa samansa,Washe Gari Nabeela ce ta Yi komai kamar yanda ta Saba Har Abinci sai da tayi Masa na dare sannan ta Shirya nata ya nata da yamma likis bayan su Zeena sunzo sun yiwa Alex gaisuwa sun tafi itama ta yiwa Alex sallama zata tafi,Sai yaji duniyar ta Masa zafi Kamar Kar ya bari Nabeela ta tafi ta barshi shi Daya,tana ebe Masa kewa,Sallama Suka Yi ta Mika Masa dubu Ashirin tace gashi ragowar canjinka cikin dubu dari Dana dauka,Murmushi yayi Yace jeki na Baki kyauta, Salary dinki kuma anjima Zaki ga Alert,Godiya Nabeela tayi tace Allah yasa Mum tana Aljana Ameen ya furta tayi waje shi Kuma ya koma sama,Jikin window ya tsaya a corridor dinsa na sama Yana Kurbar lemo Yana kallon Nabeela suna ta magana da me Gadinsa sannan yaga ta fita a gidan gaba Daya. Abin duniya yayiwa
Alex yawa kansa ya dau chaji,duniyar tayi Masa zafi,yaga ma Kamar Bai da Amfani a duniya.

Abba Yana gani Nabeela ta dawo ko kallonta baiyi ba Haka matansa ma daga ita sai Nazia suke maganarsu a cikin dakinsu,Nazia tace Aunty kudin makaranta kin San Baki Gama cika min kudin term ba saura dubu goma sunce zasu kore Ni ranar monday, Sai Textbook guda biyu dubu Daya,Nan take Nabeela ta Irga dubu Goma Sha Daya ta ajiye na makarantar Nazia,Ta dauki dubu hudu ta boye dubu biyar Kuma taje har Dakin Abbanta ta Kai Masa ba kunya ya karba Kuma Yana gasa Mata Harara.
Tana Jin Hajiya Binta tana cewa muna cin Dirty a cikinmu Ana ci da mu da Haram kudin Karuwanci,Nabeela tace Me Dirtyn dankwali ta kabari itace karuwa,Hajiya Binta ta fashe da kuka,Safiyya ta fito tana Salati Uwarki Kika zaga Nabeela? Ai Hajiya Binta Uwarki ce ko kinki ko kinso Nabeela tace Uwar banza ba,Abba ya fito da sauri zai doki Nabeela Yana kumfar Baki Bai kula ba ya bige kum a goshi da Jikin Karfen window ga tabarya da Suka Ajiye a kasa ya tadile Masa kafa Nan ya Fadi a kasa sharaf da Sauri ya mike zumbur Yana neman Nabeela wacce tuni ta shige dakinsu tasa key.

Washe Gari Alex duniya tayi Masa zafi Gashi ba Nabeela bare ta ebe masa kewa aikin nata ba kullum take zuwa ba,mugun son ganinta yakeyi ko ba komai tana rage Masa damuwa,Har dare ya Fara Nabeela Shuru,a ransa yace ko tazo ta duba Ni yau,Har Karfe Tara na dare ya kasa Hakura da ganin Nabeela Kawai sai ya fesa wanka cikin rantsatsiyar shadda milk color Yana zuba Kamshi ya fito daga gidansa Yana Dan zaga Gari a kafa,kawai sai zuciyarsa ta canja ya tare Napep Bai dakko motarsa ba,Har kofar gidan su Nabeela gashi kusan Goman dare,yaga maza suna shiga wajen Nabeela direct Bai kawo komai ba ya fada gidan su Nabeela,Fitowar Nabeela daga kitchen kenan ta Kai Kwanika Taga Alex a tsakiyar gidan su,Gabanta yayi mummunan faduwa,dama Ana Mata sharri Ina ga an kamata da Namiji a cikin gida kusan Goman dare,sanye take da Yar Guntuwar rigar bacci Allah yasa Bata cire Hijab dinta ba bayan tayi Sallah, Ai da gudu ta karaso gaban Alex cikin rada rada tace me ya kawoka gidan mu? Dare yayi na shiga Uku Alex ka fita Mana zanzo gobe,Alex Maganarsa shima ya canja yace cikin rada Baki Zo duba Ni yau ba,ko Abinci ban ci ba kin San Banda lafiya,Da sauri tace to jeka zanzo gobe please Alex,Abba ne ya Bude kofa zai fito Yana cewa waye,Da sauri Nabeela ta cakumi Alex suka fada dakinsu ita da Nazia ta kulle kofar da key ta window ta leko tace Abba mune da Nazia muke karatu,Abba Bai sani ba yace to Dan Ubanku kuyi Shuru Kun hanamu bacci da mis mis mis da murya Kamar Kuna gulma karatu cikin dare ko kune Alhuda Huda ai kwa hakura Yan Iskan Yara ku biyu Kun Addabi mutanen gida idan na Kuma ji sai kunci Ubanku.

Nazia tayi bacci tuni Bata San me akeyi ba,Alex Kamar dakin Uwarsa ya tsallaka saman katifa kusa da Nazia ya kwanta ya wani mike,Nabeela tana zare idanu a daki,window ta kulle Kar Abba tsautsayi yasa ya leko ta Nan,tana jira suyi bacci ta Kori Alex sai taji Abba ya fita ya kulle gida ko Ina yasa sakata,Nabeela tace na Shiga uku yau Namiji a dakinmu shike Nan za a ce na kawo kwarto wayyo ta Furta tana zaga dakin Kamar me Jin zawo.

Alex Yana kallonta yace yunwa nake ji Ni ki dafa min Abu,Yunwa sabo da Allah Alex Ina zanga irin abincinka? Alex yace ga Gascooker karama a Nan dakin naku ki San yanda zakiyi Dani,ko na kwalawa Abba Kira,Nabeela ta sake rudewa can ta tuna Abba ya siyi kaza guda ta Abincin Maulidi Wai Safiyya Matarsa zata Yi girkin Maulidi a makarantarsu ta Matan Aure gobe da safe,shine Abba ya siyo Mata katon zakara ta silalashi gobe zata Yi girki da shi.

A hankali Nabeela ta Bude kofa ta fita zuwa kitchen dinsu,a kitchen ta hango silalallen zakara yasha Maggi da Albasa an kife shi da kwando a plate ai da Sauri Nabeela ta dauke zakara ta saka a wani kwanon daban ta dakko Maggi da Attaruhu da curry, harda gishiri ta dawo dakinsu ta sake garkame dakinsu,Gas ta kunna Alex Yana kallonta tayiwa zakara Hadi yace Banda yaji bana so,Bata sa attaruhu ba ta Masa farfesu a Yar tukunyarsu ta daki, Dake dama Nabeela komai tana ajiye musu a daki sabo da tsaro,sai suna girkinsu ba tare da kowa ya sani ba.

Tana gamawa ta zuba a plate ta kawo Masa,ga ruwansu pure water Leda guda a jingine ta ebo biyu ta ajiye Masa,Alex Yana ta Jin Dadi ya Fara cin kazarsa hankali wance,ita kuwa Bata iya magana sabo da tsoro,Nazia ta farka ta ga Alex kusa da ita har zatayi Ihu Nabeela ta daka Mata tsawa tace yanzu ya Shigo Abba ne zai Masa fada shine na boye shi,Nazia tayi mukus ta mike zaune Alex ya Mika Mata Hakarkarin kaza Wai taci,ta karbe ta Fara ci Kamar beraye, Nabeela tace Ni fa? Ba rabonki daga Ni sai Matata,Nabeela tace ba komai duniya ce,sai da Suka ci Suka barta Nabeela ta jawo Bread Kato ta saka ragowar a gaba da romon taci da Bread ta koshi Alex Yana ta faman kallonta tana bashi dariya.
Sai da ta Gama sannan kowa yasa Hannunsa a tukunyar da aka dafa suka sa Omo a Hannu aka Fara zubawa Alex ya wanke Hannunsa tas da pure water sannan ya Sha,Itama Nazia ta wanke ta shanye ragowar, Sannan Nabeela karshe ta rufe tukunya tare da kasusuwa da plate din da suka zuba duk ta zuba cikin tukunya ta rufe ta daura saman Gas ka rantse ba ayi girki ba,ta gyara wajen da suka Bata.

Alex dama ba son tafiya yakeyi ba sai ya gyara kwanciya a gefen Katifa,Nazia ma tana gefe,Nabeela Kuma sai Shimfida tayi can nesa da su a kasa,Bacci ya kwashe su ba shiri.

Da Asuba Nabeela da Nazia tare Suka fita Nabeela ta juye ruwan tukunya da kasusuwa ta kwara ruwa komai yabi Rariya ya Tafi ya wuce,ta wanke tukunya da abinda Suka bata Daren jiya sannan Suka Yi Alwala suna shiga daki tare da saka key dama window Yana kulle,Sannan Suka gabatar da Sallah Alex Yana ta baccinsa cikin blanket,Allah yasa Ko su Abba Basu fito ba,Nazia ba school yau saturday sai Suka koma baccinsu.

Ihun Safiyya ne ya tashe su da Sassafe ta duba kitchen Ba zakara sai plate da kwando,Su Abba Suka fito da Hajiya Binta,Safiyya tace Nabeela ce shegiya bazai wuce ita ce ba muguwa wallahi a taso ta,Abba ya tunzura yace ko Ni Ina kwadayin Zakaran Nan Amma na Hakura sabo da ke idan itace sai na karya ta yau,Hajiya Binta ta Shiga dukan kofar Nabeela har window a kulle,Su Nabeela anyi tsuru tsuru Ana Salati Kar a ga Alex a dakinsu,Shahada tayi ta Dan Bude zata leko Safiyya da Hajiya Binta Suka danno kofar gaba Daya Suka ce Bude mu Shiga muga dakinki wallahi Kashi idan muka gani kin Shiga uku,Nabeela taga za a kamata da Alex a daki ta dage iya karfinta ta Danna kofa,Suma suna dannowa iya karfinsu zasu Bude,Nazia ta taho da gudu tana Taya Auntynta itama ta Danna kofa,Amma su Hajiya Binta sunfi su Karfi,Tausayi suka bawa Alex ya taso da sauri ta baya yanda baza a hango shi ba ya Danna sai gashi ya rufe kofa ruf yasa key,Su Hajiya Binta tunaninsu Nabeela ce ta fisu karfi suka ce kaga shegiya me karfin doki wannan mijinta jibgarsa zata dinga Yi Amma Zaki fito ne,Nabeela dai komawa Suka Yi suna haki Kamar Wanda Suka Sha gudu harda hada zufa suna ta Dariya har Alex kasa kasa.









AsmaBaffa.
[5/10, 3:23 PM] Sis Asma: 🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠



FREE PAGE





MASU BUKATAR NOVELS DINA NA KUDI KOWANNE COMPLT DARI UKU 300 NE

RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDU'AR KAWA


GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DIN GIDAN GWAURO NAIRA DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER NA
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA VTU TRANSFER KO TURA KATIN MTN TA WHATSAPP GA NUMBER NA
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39






16-20





Official






By
AsmaBaffa







Page naku ne

MUMMY
UMMI
AYSHA ADAM












Suna Haka a tsaye Abba yace Zaki fito ne daga ke har Nazia zaku ci ubanku sai Kun bar min gida Barayin banza Barayin wofi abin naku har ya Kai ku sace Dan zakara guda,Safiyya ta fashe da kukan munafunci Abba jiki na rawa ya zaro Dubu biyu yace Ungo maza a siyo katon zakara Daya Fi na jiya girma,na jiya Dubu Daya da dari biyar na siyo shi yau ki siyi Dan dubu biyu,Share Hawayenki,Hajiya Binta Kamar ita aka bawa sai Murna takeyi sabo da an shanye ta.
Alex Kuwa cewa yayi sai ki San yanda zakiyi Dani Brush zanyi, Nabeela tace Dan Allah ka rufa min Asiri yanzu zasu tafi Wajen Maulidi sai ka tafi gidanka.

Suna Zaune a daki kowa yayi Shuru Banda Nabeela wacce ke Gyara kayan sawarsu tana gyara Akwatinsu ita da Nazia,Alex Yana kallonta Karaf ya hango Braziyya har kala Hudu yan cukul cukul da su Basu da girma,Hannu yasa ya fisgo Daya wata black ya Shiga Kare musu kallo yace Yar wannan kike sawa? caraf Nazia ta karbe zancen tace Uncle tayi Mata kadan Bata saka su yanzu,Alex yace Okay Dama ke naki Kamar ramin tandar waina suke? Amma na rainaki dole ki kasa samun masoyi tab Allah kiyaye wa zai Aure ki ai sai low class,Nabeela da akwai Yar kunyarta Amma tunda taji Alex ya kushe ta taji Haushi tace to Ina ruwanka Kai in ba shishigi ba kace ba mutum bane Amma sai ka Fara damun mutum ko kaine Zan Aura Wanda ya Aura Allah ma yasa yaji ya Shafa Kamar Kan mota Kai Ina ruwanka tunda ba Mutum bane.

Alex ya kalleta sama da kasa irin kallon Raini yace Ni Bude min kofa na fita,Nazia tace Allah Idan Abba ya ganka kawai ka mutu ya fiye maka gwara ma ka zauna su fita,Dole ya zauna Yana jira Nabeela tana ta gyare gyarenta,Har Safiyya ta Gama girkinta tace Hajiya Binta kece karama sa Hijab ki dauki Abinci muje kamar Yarta Hajiya Binta tace banyi wanka ba,Tsawa Safiyya ta buga Mata wa Zaki wa wanka abinda Hashimu ma Sam Bai taba saduwa dake ba Dalla dauki mu tafi,Hajiya Binta tasa Hijab Haka ta dauka Suka tafi Safiyya Tasha gayunta ita kuwa Binta kamar Yar aiki.

Suna tafiya Nabeel tace Nazia Dauki Jakar kayan Nan mubi Alex idan Abba ya Huce sai mu dawo Amma yau akwai Drama matukar muna gidan Nan,dakinta ta Bude suka fito Har Alex shaddarsa duk ta Yamutse,Nazia tace Abba Yana kofar gida Aunty,Nabeela tace karki damu zanji da shi,Abba Yana siyar da kayan Miya a kofar gida sai yaga Nabeela da Nazia sun fito da kaya a bayansu Alex ne yake tafiya cikin Izza da takama,zumbur Abba ya mike ya saki salati yace me Zan gani Nabeela? Nabeela tace Mene Abba? Alex katon gardi a gidana da Alama a ciki ya kwana,Nabeela ta Fara dube dube tana tambaya Abba Ina Alex din? Abba ba kowa daga Ni sai Nazia,Abba ya jawo rigar Alex yace wannan ubanki ne? Ni gaskiya Abba Banga kowa ba Gamo kayi Aljani ne yazo maka a suffar Alex Amma Ni ban ga kowa ba,Alex baiyi magana Ba sai kallon Abba da yayi ya wani saki Arnen Murmushi Abba yayi sototo yace wannan mutum ne wlh ga zahiri na gani ki Raina min Hankali Amma, Nabeela tace Abba muje gidan Malam babu lafiya kayi gamo,Huzaifa Abokin Nabeela Abba ya hango ya kwala Masa Kira,Huzaifa ya karaso da sauri Abba yace Tayani gani Huzaifa kana ganin Alex yaron Nan da yace shi ba mutum bane? Nabeela tace min ba kowa zata Raina min Hankali,Huzaifa fuskar Alex ya leka ya kalle shi sosai Amma Abokin Nabeela ne yasan halinta sai yace Gaskiya Abba Banga kowa ba Nima daga Nabeela sai Nazia tabbas gamo kayi ko idonka ne yake maka gizo,Abba sai ya tsorata yayi Shuru ya zauna a firgice,Nabeela Suka tafi Abinsu Abba Yana kallo har Akex Suka Shiga Napep amma ance ba mutum bane Kuma Haka ya yarda ba yanda ya iya.

Gidan Alex Suka shiga a Nan sukayi wanka da komai Nabeela ta shirya Nazia cikin kana Nan Kaya Jean Skert Black da Yar T-shirt pink color,Gashinta ta gyara Mata sai ta dawo kamar yaran masu kudi,Ba karya Nabeela tana kashewa Nazia kudi,Ita kuwa Nabeela kwancen wani material ta saka Fitted gown kayan sun Dan kode Amma tayi kyau
Dinkin dai dai ita kamar a jikinta aka dinka,siririn mayafi ta yafa kalar material wato dark Green, Nabeela a gurguje ta gyara gidan Alex Yana ta baccinsa har ta Gama bed dinsa ne kawai Bata gyara ba,Kitchen ta shiga ta Soya musu Dankalin turawa tare da kwai sai Hadin kauri da ta Yi musu,Duk da Alex ba komai yake ci ba duk abincin mutane ya siya ya jibge a store kowa abinda yake so yake dafawa suna Palo suna ta kallo sunci sun koshi Har Rana tayi sukayi Sallar Azahar Nabeela ta musu girki Suka koshi har lokacin Alex Shuru,Mikewa Nabeela tayi ta Masa irin girkinsa ta Rufe komai a kitchen,Suna Zaune wayar Nabeela tayi Kara tana dubawa taga Ladi me kidan Kwarya,Dagawa tayi Ladi tace kina Ina ki taho yau akwai harka Muna Gidan Dan Majalisar Tarayya za muyi musu kida Yana Aurar da Yarsa yau Ranar mu ce zamu Sha ruwan kudi,Nabeela tace gani Nan Turo min Address din,Kamshi ne na musamman ya daki Hancin su Nabeela da sauri ta kalli inda Kamshin ke Fitowa ba kowa bane face Alex yasha kana Nan Kaya yau ba karamin kyau yayi ba gaskiya Alex ba karya na daban ne,Nazia ya kalla tayi kyau Daukanta yayi Tare da Daura ta a wuyansa Yana dariya Yace kinyi kyau Baby,Nabeela ta galla Masa Harara ita Bai yabe ta ba,Ganin tana fushi sai ya ajiye Nazia da Hannu Daya ya figi Nabeela tare da daga ta sama da Hannu Daya ya sake ta da karfi ta fada saman kujera,Nazia ta dinga Dariya ita da Alex Yana cewa gashi Nan kema na dauke ki,Murmushi Nabeela tayi tare da Mikewa tace Ga Nazia Nan Zanje aiki, wanne Aiki Kuma? Kidan kwarya zata je cewar Nazia,Alex Yace irin wannan na tsofaffin Banzar ke kadawa? Nazia tace ae Kuma yanzu ba a fiye Yi ba Dj ke tashe,Alex ya tabe Baki yace muje to mu kaiki gidan daga Nan Naga irin kidan naki,Gidan mutane zaka shiga ka jawo min masifa salon kace Sai an baka Zakara kaci Ni wlh gwara kayi zamanka,Ba dama a zauna Lafiya sai kace zaka ci Dan zakara bazan iya da rayuwarka ba,Ka biya Ni Salary kazo kana fanshe kudinka a Kan Zakara.

Allah sai munje cewar Alex ya dauki Key Suka fita gaba Daya,su Zeena ne Suka shugo gidan, Da sauri Nabeela ta koma ta kulle ko Ina a Gidan ta dawo gabansu tace yau ba Harka a tafi idan kunyi zuciya ku siyi gidanku na Badala Nan Babu Hanya,Zeena ta Kalli Alex tana son Alex a duniya tace Bamu key Alex ai gidan ba nata bane,Alex yace wannan maganarku ce mutane Ni ba mutum ba Ina Zan shiga cikin matsalarku, Gwalo Nabeela tayi musu Suka Shiga Mota Nabeela Harda Zama a wajen tuki ita tayi Driving ta Yo Kan su Zeena da mota Suka watse da gudu ta wuce Suka tafi,Dole Suka bar gidan suma.

Su Nabeela kuwa tana waya da Ladi tana gwada musu gidan Har Suka Isa can Gidan ya Hadu ba karya 'Yan Mata ne na gani na fada zuka zuka masu kyau da Aji,Sun ci gayu na karshe Ana ta Iyayi Ana Daga manyan wayoyi Dj ya Gama kidansa sun tafi yanzu filin na su Nabeela

Please Login or Register in order to submit comment