Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

me Zan gani yau,Tsoro ya Kama Nabeela ta kalle shi da sauri yace Na Fara Zama Irin mutum nima,Nabeela tace a radio kaji Salatin Nan ka koya zaka wani ruda ni,Zeena ce ta koya min ya furtawa Nabeela, Nabeela
Tace to anji baka da Lada dai musamman daka yarda Zeena fasika ta koya maka,Alex yace ae ta fiki...Kai tafi can Cewar Nabeela,Ke matsa can Cewar Alex shima Wai ya Rama,Nabeela ta sheke da dariya sannan ta zaro harshe tace wullu,Alex yace woooo shima,Nabeela tana ta girkinta kamshi ya cikawa Alex ciki shi Kuma Yana ta yanka ganyen salat Yana gasa namansa,Nabeela ta leka taga namansa tace San min kadan kaji Alex yace Baki da kunya bazan Baki ba,Na daina Dan Allah San min ko Kamar Dan farce na ne, Alex ya yanko Dan mitsili kamar farcen Nabeela ya Mika Mata yace gashi,Dariya ta Kama Nabeela tace Dan wannan? A Bakinsa yasa ya cinye tana kallo ya Gama ya tafi da abincinsa,A fili tace Kan uba Amma Alex Bai da Imani Sam,jullof din taliya tayi Tasha nama taci ta koshi sannan ta nemi food flask ta zubawa Nazia ta tafi da abinta gida.

Abba Hashimu yana zaune a tsakiyar matansa Safiyya da Hajiya Binta yace Ina so ku bani Shawara Yarinya ta gangare Ni Kun San komai ko Tsine Mata zanyi Baza ta bar gidan Nan ba,Kuma baza ta kawo min Mijin Aure ba ya kuke ganin Za'ayi? Hajiya Binta farin ciki ya kamata tana lankwashe Kai tace to Ni ai sai abinda Yaya Tace Amma wlh na tsani Nabeela Allah ya gani Ehe,Safiyya tace Nima ba Kaunarta nake Yi ba ko na Kobo bana sonta Bata da halin kirki,Ni abinda yafi damu na da ita Bata da aiki sai Bin maza kullum tana can cikin kartai a gidan Gwauro,Ai kuwa idan akace mace na Shiga gidan Gwauro to an samu Matsala,kawai farko ka Fara Kulla Mata kayan Miya a Leda kana cika Mata Faranti tana tafiya Talla kaga mun huta ba ita ba zuwa gidan Gwauro sai Talla,Abba ya washe Baki yace Haka za ayi dama na siyo kayan Miya zanci gaba da siyarwa gobe,Saffiya tace to ga dabara,kaga daga can sai ta samo Mijin aure a wajen Talla,Dariya Suka Yi gaba Daya,lokacin da suke Maganar Nabeela tazo zata shigo gidan taji kaf duk abinda suke fada labewa tayi,Sai ta nuna Kamar Bata ji ba ta shigo da Sallama Nazia tana rike da hannunta ta dakko ta daga Islamiyya,Bata kulasu ba tayi wanka abinta Nazia ma tayi Suka shige dakinsu Abincin data taho da shi Nazia taci ta koshi tana Santi tace Aunty Weekend ki je Dani,Allah ya kaimu Nabeela tace Sam Bata cikin Hayyacinta kamarta za a daurawa Talla Amma tunda Abba ne ya zatayi da shi.

Washe Gari da Sassafe suna karyawa Nazia tana school Abba ya shigo yace ke Nabeela Zo Nan Dan Jakar ubanki,Fitowa tayi tace Abba Gani,Katon Faranti Safiyya ta Miko Masa ya Gama Kulla Attarihu tattasai da tumatur a fararen Leda harda Albasa ya jera a tire ya cika shi Dam yace dauki ki zaga ko Ina da shi Kin koma Talla ba Ke ba gidan Gwauro Kuma ki tabbata kin samo Mijin aure a wajen Talla,Hajiya Binta tace ki dinga Turo kirji gaba ko maza zasu ga Baiwar da Allah ya Miki sosai suzo Amma shegen bakin jininki yayi yawa,Nabeela ta galla Mata Harara,Abba yace to kinji dai abinda Hajiya ta tace sabo da Haka kiyi yanda tace ko na Tsine Miki,Nabeela tasa Hijab zata tafu Amma Safiyya ta fito tace munafuka saka hularki ta Yan achaba da mayafi yanda kike Yi,Nabeela ba musu ta saka yanda tace ta daura Farantin Talla a kanta,Abba yace ki bi ko Ina ki zaga lungu da sako kowa ya ganki yawwa,Bata ce komai ba ta fita,Kamar yanda aka Umarce ta Haka Nabeela ta Hankaro kirji Kamar me gantsarwa sabo da Rashin mutuncin Nabeela tayi waje a Haka tana zagawa,Kuma bata Bude Baki tace ga kayan Miya ba,kawai yanda akace ta dauka ta zaga Unguwa Unguwa lungu da sako Haka tayi Wai zagawa takeyi ba ko magana Kuma ko an tsaidata Bata tsayawa Bata kula kowa yawonta takeyi lungu lungu tun safe har yamma,Karshe ta biyo ta layin gidan Alex sai ga motarsa kuwa ya dawo zai Shiga gida ya hango Nabeela kamar zata cire kirjinta sabo da yanda ta masa Tasa mayafi ta rufe jikinta kirji a gaba,Alex dariyar Tafiyar ce ta kamashi ya tsaya Yana kallon ikon Allah har ta karaso Jikin motarsa tana kallonsa Ido cikin Ido,Glass ya sauke tazo ta tsaya kerere kasa daurewa tayi itama ta Fara yiwa kanta dariya,Alex yace Yan Mata kinyi fa na gani Ina so, dariya Sukayi tare Nabeela tace a Ina ka iya magana Haka?,Nabeela tace Muje Ni yunwa nake ji Gidan ta shiga gidan Ta dafa Indomie ta ci sannan ta huta ta dauki kayan miyarta Bata siyar da ko Daya ba ta koma gida.

su Safiyya Suka saki salati tare da kwalawa Hashim Kira yazo yaga yanda ya daurawa Nabeela Talla Haka ta dawo da shi,Abba yace au ba tallan Kika je? Nabeela tace Abba da kuka bani cewa kayi Na zaga lungu da sako kowa ya ganni sannan na nunawa maza baiwata to ai shi nayi dama cewa kayi Na siyar? Takaici ya Kama Abba yace an Gama Nabeela wallahi kin jawa kanki Aure Zan Miki Zaki Sha mamaki,Gobe ki shirya Wanda na yanke hukuncin Zan Aura Miki gobe zaizo zance,Allah ya kawo shi Abba cewar Nabeela ta ajiye tire ta shige Dakinta ta kwanta ta barsu da surutai.

Washe Gari Basu kula Nabeela da Zancen Talla ba suna gani ta fita Harkarta, motar Huzaifa ta karba ta fita tana tukawa cike da nutsuwa Har gidan Alex,Alex Bai San ta iya mota ba lokacin Yana Garden yaga ta shigo a cikin mota ta birge shi,Alex wani haske da kyau yake Karawa kullum Jin Dadi Yana ratsa shi,Zuwa tayi ta gaishe shi Yace muje yau na kaiki kici Abinci a restaurant Ni bazan ci ba Amma Nima irin ta mutum zanyi Ina gani suna Kai Yan Mata,Nabeela banza ta Fadi ta washe Baki tace Allah ja zamaninka Honorable Alex muje,Alex yace me yasa ke bakya sa Kaya masu kyau kina kwalliya irin na Yan Mata Yan gayu?...kafin ya rufe Baki Nabeela tace Talauci ciki Bai Gama koshi ba Ina ake ta gayu,Motar data Zo da ita ya shiga gaba ita tayi Driving Zuwa wani Restaurant Hadadde na manya,Ko da Suka shiga Pounded yam Nabeela ta zaba da Farfesun kaza gefe kuma ta zaba fried rice and chicken aka Mata take away zata tafi dashi gida.

Cokali aka kawo wa Nabeela tace kuje da abinku bazan ci da cokali ba matsiyantan ma'aikata ba abinda kuka iya sai cuta,wato so kuke naci da cokali salon na Dade ban cinye ba har cikina ya cika na bar muku ragowar banza ta Fadi ko to digon Miya bazan rage ba,karku sa Rai zaku karu Dani ku samu sidi ko Almajiri ne sai dai ya maida maitarsa, mutanen Dake wajen Suka dinga dariya shi kuwa Alex ya sata a gaba Yana ta kallonta,Hannayenta ta wanke ta shiga ci duk mutanen dake gabanta ba ruwanta da wata yanga Zagewa tayi ta koshi Lemo Alex ya bude Mata tare da Bata a Baki da kansa Wai shima ya Zama mutum,Ana ta kallonsu sai dai Sarkar Alex ta cross ta nuna da Christian suke tare.

Sai da ta Gama Yana ta Jin Dadi ta sauke shi a gidansa tayi gaba ta maidawa Huzaifa motarsa ta koma gidansu,Bayan Sallar Isha yaro ya shigo yace Wai Ana sallama da Nabeela tazo Inji Aminu Wanda zai Aureta,Nabeela tayi dariyar yake tace je Kace gata Nan,Su Safiyya sai kus kus sukeyi suna dariyar mugunta,a hankali Nabeela ta leka don taga waye Aminu,Wani gajeren mutum ta hango me azabar kiba cikinsa Kato gashi Baki wuluk Yana ta busa Hayakin wiwi,Gida ta dawo ta dauki katon Itace faskare tana fita ta samu kusa da Kan Aminu jikin Katanga ta maka itacen da karfin tsiya,Aminu yayi mugun firgita yayi zaton a kansa ta kwada itacen sai ya dafe Kai Yana wayyo kaina ya mike da Gudu yayi Hanyar gida sai da yayi Nisa ya gano Ashe ba a kansa ta sauke itacen ba,Yace Allah ya so ni Ba ruwana wallahi na fasa bazan aure ta ba ta kashe Ni cikin dare,Nan take ya dauki waya ya Kira Abba ya ci Masa mutunci sannan yace bazan auri yarka ba dama kasan mahaukaciya ce kace naje muga juna,Abba a fusace ya shigo gidansa Yana Kiran Nabeela Yana masifa Akan Aminu ya fasa,Nabeela ta dinga Murna a ranta,Tace sabo da Allah Abba ka Rasa wa zaka turo min sai kwado wannan ai kwadon dawa ne,Abba ya bita da zagi iri iri.

Bayan wata Hudu Rayuwa Babu abinda ya canjawa Nabeela kullum Sallah da Adduoi takeyi tana Rokon Allah ya fitarsu daga halin da suke ciki,Gashi da karfinta tana yaki da Matan Ubanta kullum rayuwa Bata Mata Dadi,Daga wannan sai wancen,Tsakaninta da Alex Kuwa sun sake shakuwa Yayinda Yan bariki kullum karuwa sukeyi a gidan Alex ya kasa korarsu Babu me kulasu abinda suka ga dama suke yi.
Yau Sunday da dare ba kowa a gidan Alex Yana kwance har ya Fara bacci,sai yaji motsin tafiya Kamar a bedroom dinsa Kamar a mafarki ya farka,Bude idonsa ke da wuya yaga mutum katon Gardi ya tsaya a kansa da katuwar wuka Yana son ya caka Masa Allah yasa Alex ya rike Hannunsa da karfi ya murde shi wukar ta Fadi,yasa kafa yayi ball da shi,ya mike yayi Kan Gardin wanda yasa mask ya rufe fuskarsa Dan Kar a Gane shi,Alex ya shiga Naushinsa sosai ya fasa Masa Hanci da Baki Ya fisge face mask dinsa,Wani Mutum ne Christian da Alama shi Igbo ne,Nan take Alex ya kafe shi da Ido sai kwakwalwarsa ta fada tunanin baya a iya Kan mutumin ya tuna sanda mutumin ya kamashi ya daure shi tare da Masa duka yayi tunanin ma Alex ya mutu domin a dajin Kaduna ya daure Alex cikin Kogon dutse,Ai Alex zuciya ta Zo Masa wuya ya tabbata a baya shi mutum ne Bai San me ya faru da shi ba,Gardin wato George da karfi ya kwaci kansa ya fita da gudu Alex ya bishi Amma tuni ta Garden yabi ya Dane saman bishiya sannan ya taka katanga ya Haure waje ya gudu,Alex ya neme shi ko sama ko kasa yace indai bibiya ta kakeyi zaka kashe Ni to Ni Zan kamaka da kaina,A daren Alex kwana yayi Yana Tunani ko zai tuna rayuwarsa ta baya Amma ya kasa sai ma zazzabi Daya rufeshi idonsa yayi jajir ya Fara gurnani kamar Zaki,Allah yasa shi kadai ne ba kowa har yayi ya Gama Gari ya waye ya dawo Normal.
Kwana Biyu a Tsakani Nabeela ta Gama aikinta suna zaune suna kallo wayarsa tayi Kara tunda yake da wayarsa ba Wanda ya taba kiransa yayi mamaki ya daga Hello...Muryar Gardin Nan George yaji Yana Masa turanci yace Idan ka Isa Kazo mu Hadu a daji kusa da Jaji,Alex Ransa ya baci ya mike zumbur da Niyyar gamawa da wannan mugu yace gani Nan zanzo Ni Kuma sai na Gama da Kai,Nabeela tana kallonsa taga Yana Huci ya fice da sauri ya barta tana kiransa tana Alex Alex Amma Ina mota ya fada yayi gaba har gefen Dajin yaje sannan ya fita a motar ya taka a kafa har cikin dajin Yana tafiya sai da yayi mugun Nisa a dajin Sannan ba zato yaji an buga Masa katako a kansa,Kuma Mutumin ya rufe shi da duka ta ko Ina sai da yayi wa Alex jina jina ko tashi ya kasa Yi sai idonsa da yake budewa Yana Nishi sama sama Amma duk da Haka Yana zagin George ,Shi Kuwa George yana ta kyalkyala dariya yace ka tuna waye Ni?

Kwakwalwarka zata iya tuna Emmanuel? Dama mun fada maka sai mun kassara rayuwarka Hahaha ka manta komai ko? Yanzu nasan kana iya tuna wani abin,ba burina na kashe ka ba burinmu mu lalata rayuwarka yanda baza ka Mori rayuwarka ba a duniya kudinka baza kaji dadinsu ba,Ina Daya bank Accnt dinka Wanda kudadenka suke? Wannan kudin sai dai bank su cinye tunda muma bamu ci ba, A yanzu a gabanka Zan kashe Mamanka zaka iya tuna Mahaifiyarka? Nafi so har abada baza ka mantani ba,Nan take Alex yaga wani katon Gardin Ya taho da Mamansa Hannunta a daure da kafafunta, Mamansa Wata Dattijuwa Fara Kamar baturiya ta rame ta fita a hayyacinta tana kuka kanta ko Dankwali Babu,tana ta Rusa kuka tana kallon Danta Alex wani Gardin ya kawota gaban Alex,Nan take Alex kwakwalwarsa ta fada tunanin rayuwarsa da Mahaifiyarsa a baya yanda suke Wasa da juna,tana kula dashi Abinci ma a Baki take bashi,Baya taba cin Abinci da kansa,ita ke gyara Gashinsa,Yanda take raka shi har mota idan zai tafi Office,Ga security ko Ina Ana take Masa baya,Kaf ya tuna rayuwarsa da Mahaifiyarsa yanda yake jin Dadi take ji da shi,Mamansa tana kuka ta Kira Sunan Alex da karfi Tace Asad Dana......Alex cikin Karaji yace Mum.......gashi ya kasa tashi ya CeCe ta,Da kyar ya iya Durkusawa a Gaban Katon George yana rokonsa da shi ya kashe shi ya bar Mum dinsa ta rayu Yana ta bashi hakuri,Amma ba Imani Igbo Nan ya zaro Bindiga ji kake Tas tas tas yayiwa Maman Alex Harbi Uku a cikinta,Alex ya saki Ihu da Karaji tare da kururuwar Kuka,Bai San sanda karfi yazo Masa ba.

Ya Suri George ya maka shi da kasa Ya dauki katako ya shiga Dukansa tare da kwace bindigar Ya Masa Bullet uku shima ya kashe George sannan yaron George Daya kawo Mahaifiyarsa aka kashe ta ya kwasa da gudu zai gudu Alex Ya Harbe shi shima ya mutu Nan ya zube ya dinga kwarara uban kuka Yana ihu Ya Rungume Mum dinsa.

Nabeela ce ta karaso wajen tare da motar Yan Sanda suka shiga dajin tana Kiran Alex,nesa suka ji kukan Alex Suka nufi wajen da gudu,Da kyar ya iya fada musu kidnapping Mum dinsa akayi aka ce yaje ya karbeta yaje Suka kashe ta a gabansa,shi Kuma ya samu nasarar kwatar Bindiga ya Harbe su,Police Sai da Alex ya birge su Suka jinjina Masa,Report Suka dauka da komai sannan Suka tafi da Gawar Arnan Alex Kuma Da Nabeela Suka tafi da Gawar Mum din Alex,Nabeela sabo da Tausayin Alex harda Kuka,Alex yace Mum Dina musulma ce ban San kowa ba ki Kirawo min mutane ayi Mata sutura,Nabeela tace Angama,Haka tabi gidajen Unguwarsu kaf Dattijai da matasan Unguwarsu Kaf ta kirasu anyi mugun cika damkam Musamman abokan Nabeela Cikin mutunci aka sallace ta aka kaita makwanci Alex Yana cikin dakinsa ya kulle kansa a daki Yana ta sharbar kuka,gashi Bai tuna waye Babansa ba da danginsa bare garinsu,Kuma ga cutar dake damunsa,sannan Mum tace Masa Asad Sunan Musulmi Ina ya samo suna Alex har a bank dinsa? Kuma Sarkar cross dinsa me tsada Ina ya samo ta? Ana kaita kowa ya watse Nabeela ce kadai a gidan tayi tagumi.

Sabo da Shishigin Nabeela sai cewa tayi Banga ta tafiya gida ba anyi Mana babban Rashi Haka ai Ni da gida sai anyi sadakar Uku,sabo da Haka Bari a dauko min Nazia Nan kawai,Nan take ta fadawa Usman ba Bata lokaci sai ga Nazia da katuwar jaka kayanta Dana Auntynta sai anyi sadakar Uku zasu koma gida.
Nazia tana zaune tana kallon Nabeela tana ta kuka ita da Bata San Mum din Alex ba Amma sai kuka takeyi,Nazia tace Aunty sai kace Abba ne ya mutu kike kuka,zanci Uwarki Nazia Dole inyi kuka yanzu Wanda ke bani kudi nake ci Ina koshi baya cikin Hayyacinsa idan Bai samu nutsuwa ba ta ya Zan samu damar karbar kudi a wajensa? Gashi jibi zai bani Salary na ga Mum tasa ta rasu Taya Zan Bude Baki nace ya bani kudin aiki na? Wannan mutuwa Ni aka yi wa ita,Yanzu sai sanda zafin mutuwa ya sake shi zai iya bani kudi shike Nan ga matsaloli a gida,Wallahi Allah ya tsinewa Wanda yayi wannan kisa, Allah ya Tsine Masa Albarka ya tare min Hanyar samu na ya cuce Ni,Badan kudi ba yau she zanyi kuka Ni da uwata ta mutu tun Ina Karama maraici wanne ne ban gani ba shi kuwa ya Gama Balaga da Mamansa a kusa gasu da kudi ai sai ya godewa Allah Amma gashi can ya kulle kansa Yana ta faman kuka gashi an Masa dukan tsiya jikinsa ya farfashe ko asibiti yaki zuwa.

Nazia tace ko Allurar tetenus ba ayi Masa ba,Ai zumbur Nabeela ta mike tace wata sabuwa ai Dole ya tafi asibiti ko a Kira Likita idan Tetenus ta Shiga shike Nan ko a yanke Masa Kafa ko hannu ko ma ya mutu Kinga Hanyar samu na tazo karshe bazai yuwu ba Dole na kula da lafiyarsa ban karbi Albashi na ba,Nan Nabeela tayi sama wajen Alex da sauri,Ta shiga buga kofa kamar zata ballata,Yana saman Gadonsa ya shige Bargo Yana uban kuka da zazzabi,Nabeela ta zaro key a jikin kofar Daya room din tana gwadawa kofar Alex ta Bude,Ta Shiga ciki a nutse.

Ayoyin Qurani Nabeela ta Shiga tinowa Wai zata Masa waazi Amma Bata iya fassarawa ba ta hakura gudun Kar tayi sabo,sannan ta tuna ma Arne ne kawai sai tace Bari nayi Masa yarensu tace Sorry...Sorry.... Okay,RIP Mummyn Alex,Komai na duniya hakuri akeyi,muma duk na can ne, lokaci muke jira,ko yau ko gobe ko anjima ko ma yanzu,Addua zaka Mata shi zai bita kabari,Alex ya sake barkewa da kuka kamar mace,Yana cewa a gabana aka Harbe Mum...sai numfashinsa ya shide kamar zai mutu,Nabeela a ranta tace wayyo kudina zai kashe kansa,A fili tace hakuri zakayi Addua zaka Mata Haba Alex Kamar ba Namiji ba,kana so ka dawo mutum Kuma baka yarda da kaddara ba,kayi hakuri ka karbi kaddara shine abinda mutane sukeyi,Rannan kana gani Baban Aliyu ya mutu Amma gashi ya hakura Yana harkokinsa harda shayeshaye to mutum kenan Allah ne ya karbi Abarsa ba yanda zakayi,Nabeela ta tsaya ta shafe tsawon lokaci tana ta Masa Nasiha Kuma sai yaji sanyi ya Dan hakura ya tashi da kyar Yana harararta idonsa jajir,Baki ya turo yace sai ki rike Ni na tashi Baki Bude tace ai kayi nauyi,Asibiti zamu je Dole a kula da ciwonka sai mu dawo yanzu,bani key din motarka,a saman Drower ta dauka,tace Ina gidan Nan Zan kuka da lafiyarka sai ka warke sumul.










AsmaBaffa.
[5/10, 3:23 PM] Sis Asma: 🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠




FREE PAGE



MASU BUKATAR NOVELS DINA NA KUDI DARI UKU 300 KOWANNE COMPLT

RASHIN SA'A
TA GYARU
YAT KWANGILA
ADDU'AR KAWA


GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DIN GIDAN GWAURO NAIRA DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER NA
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA VTU, TRANSFER,KO TURA KATIN MTN TA WHATSAPP KO SMS
GA NUMBER NA
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39








11-15





Official







By
AsmaBaffa







Page naku ne

SERLMERH
BASMAM GLAM
RUKAYYA MUHAMMAD
MAMAN FARUQ









Da kyar yake takawa,Nabeela ta Bude Inda taga Yana Ajiye kudi ta dauki rafar Yan Dubu sukayi waje Suka wuce Asibiti tare da Nazia,private Hospital Suka je me tsada Nabeela ke Driving,Suna Shiga aka tarbesu,Allura akazo yiwa Alex ko motsi baiyi ba aka Yi Masa kala Wajen Uku sannan aka yiwa raunukan Dressing ba aci wani kudi me yawa ba,Kwantar da shi sukayi tare da daura Masa Drip Nabeela tana gefensa a zaune shi Kuma bacci ya kwashe shi,Likitan ne ya fito ya samu Nabeela Yace kwana Biyu ya Dace kuyi sabo da ya samu Hutu ya Dan samu karfi sai ku koma gida,Yanzu karki Bari dare yayi kije ki siyo muku Abinci da sauran kayan bukata,Nabeela tace to ta mike ita da Nazia Suka tafi,Amotar Alex ta koma Gidan Alex ta Iske Yan shaye shaye su Zeena a gidan sun cika Palo,Nabeela ta wuce sama ta dakko Blanket biyu,Kayan sawar Alex biyu da nata kayan Dana Nazia da sauran kayan bukatu,Tana Fitowa ta kalli su Zeena tace to a tashi a fita Zan rufe gidan me gidan ya Aiko Ni an Masa rasuwa Mahaifiyarsa Yana asibiti marasa kwakwalwa a tashi a tafi gidan uba.

Zeena tace munji labari uwar shishigi,To ku tashi ku fita yace na kulle Masa gida ai bana ubanku bane ko Kuna da gado a ciki? Aliyu yace wlh Kinci sa'a yau da sai dai ayi gadon Asibiti Dake,Muazzam yace Dalla ku tashi mu Ware Yarinya ta fiku gaskiya an Masa rasuwa bamu neme shi ba mun Masa Jaje ba muna cin Arzikin mutum Kuma munzo Ana zube kayan Maye wannan Bai Dace ba,ko waye aka Masa Haka bazai ji Dadi ba,Mikewa Sukayi wurin su goma Suka kwashe kayan shansu Suka Yi waje,Nabeela tasa key ta rufe ko wacce kofa Lungu da sako sannan tasa me gadi Akan ya kula sosai ta tafi itama.

Fruits da Hadin salat ta siya tare da gashashen Naman rago da sauran Abinda taga Alex Yana ci,Itama ta musu take Away lafiyayye,Nazia tana kusa da ita kamar jela suka koma Asibitin suka Iske Alex Yana ta baccinsa.
Suna Zaune Sunyi Shuru ita da Nazia sai Yar wayar Nabeela tayi Kara tana dubawa taga Abbanta ne da sauri ta daga,cikin fada yace Naga Kiranki Mene ne? Dama fada maka zanyi zanyi kwana uku ban dawo gida ba Wanda nake aiki a gidansa ne babarsa ta mutu mun zauna zaman makoki,Cikin karaji Abba yace ki Shekara ma acan Amma ki dawo min da Nazia gida,Nabeela tana Jin Muryar Safiyya ta waya tana cewa karta koya Mata karuwanci tun tana karama,Abba yace wallahi Idan minti talatin tayi Banga Nazia ba sai na Tsine miki.

Da Sauri Nabeela ta tattara Nazia da kayanta Suka Shiga Motar Alex,Nazia tana ta kuka tace Wlh Aunty dukana zasuyi ta Yi,Karki damu Sister Zanzo da kaina da safe na kaiki School Kuma gobe Inshaallah Muna tare,Murna Nazia ta Kama Yi 20mnt ta sauketa tare da Abincinta take Away gida ta shiga Ita Kuma Nabeela ta koma Asibiti wurin Alex,Koda Ta koma Har Nabeela tayi Sallar Magriba da Isha Alex Bai farka ba,Sai Wurin 10pm sannan Alex ya farka,Mutuwar Mum dinsa ce ta dawo Masa sabuwa Yanda aka wulakanta Masa Uwa Bai San Sanda ya Fara Hawaye da sheshekar kuka ba,Nabeela tana cin Abincinta taji Kukan Alex,Ido ta zuba Masa Bata ce Masa komai ba Yana ta yin Abinsa,ganin Yaki dainawa sai ta mike ta karasa saman Bed dinsa tare da Zama gefensa kadan,fuskarsa ta leka kadan tace Sannu...Sannu kaji Yi kukanka Dole kayi kuka bazan Hanaka ba Nima da Mamata ta rasu Haka na dinga Kuka Nasha wahalar duniya,duniya tana Tafka ta har yanzu a cikin jarabawa nake,Uwa guda ai Dole ayi kuka,Rashin Uwa shi ya jefa Ni a halin da nake yanzu,ban samu tarbiyya ba,bani da ita sabo da Babu Wanda ya Dora Ni a hanya,Allah sarki Alex dinmu Mum dinka guda.

Alex Bai kula Nabeela ba Kuma Bai daina kuka ba,Abinci Nabeela ta koma tana ci tana yamutsa fuska tace Abincin Nan bana Jin dadin cinsa sabo da Anyi Mana Rashi,Rashin Mum ya jefa mu a wani Hali yanzu Daci abincin kawai yake min a Baki da kyar nake Hadiyewa Tana fada tana yagar Cinyar kaza ta cika Baki da nama lips dinta duk yayi maiko tace kazar ma ba dadinta nake ji Salam kawai ci nake Dan kawai ci ya Zama dole ne Amma da yau kayan cikina sai dai suyi hakuri baza su samu sinadaran aiki ba,Amma tumbi shi bashi da mutunci bashi da hakuri ko na second yanzu idan ban ci Abinci ba sai ya Kama ciwo da kugi,da badan Haka ba bazan ci komai ba Amma ya na iya Nabeela ta sake zuba shinkafa da

Please Login or Register in order to submit comment