Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Suka ce tazo suje taga gidansu yaran Attajirai ne na gaske a hamshakiyar Unguwa suke ta masu fada aji a kasar,Nabeela da son kudi tabi su Suka je Hadaddiyar GRA Tasha kallo har Bata San dare yayi ba sai ji sukayi Ana kiran Sallar Isha suna can suna ta Wasa tare da yaran masu kudin a cikin gidansu,A firgice Nabeela ta fito zata tafi gida ga duhu,Tana tafiya tana tsoro har ta shigo inda ba gidaje wasu maza matasa Christians Suka hango ta ai ko Daya Yace Yau mun samu banza zamu rage zafi ga wata Yar kaza can ku kamota mu baje harka,Nabeela ganin mutum biyu sun taso ta kwashe da gudu ta koma baya inda ta fito nufinta ta koma gidan kawayenta ta kusa zuwa Amma karfinta ya Kare sai ta Fadi Nan mutanen Nan Suka kamata ga uban duhu,Ihu ta Shiga kwalawa Amma Haka Suka cire Mata kayan jikinta tas sai pant, Wani matashi ne ya fito daga wani arnen gida sai Mari da naushi Suka ji ta ko Ina,Da Gudu Suka arce Suka bar Nabeela a kwance tana kuka daga ita sai pant,Matashin cikin muryarsa me Dadi yace Allah ya taimakeki Basu Yi Miki komai ba,uban waye ya fito Dake yanzu? Nabeela tana kuka ta fada Masa dalilin da yasa tayi dare,Kayanta ya kwaso ya Bata yace saka Kayanki,Tana kunya tana boye kirjinta,Baki ya tabe yace Baki da komai a kirji kina min Iyayi,Kiyi sauri ko na tafi na barki.

Jiki na rawa Nabeela ta maida kayan jikinta,Matashin mota ya koma ciki ya dauko,Ta shiga Gaban mota Suka tafi Bata kalle shi ba shima Haka Babu Wanda yasan ya wani yake a cikinsu,ko ba komai ga duhu ba wani haske,Kwatancen gidansu tayi Masa ya kaita har kofar gida,Fita tayi a motar tana Masa godiya tace Dan Allah Uncle ya sunanka? Asad ya Bata amsa tare da Jan motarsa yayi gaba ita kuma tayi cikin gidansu.
Bayan ta Shiga duk abinda ya faru ta fadawa Mamanta ai ko ta Sha fada wajen Aisha.

Bayan wata Tara Aisha ta Haifo Nazia anyi duk abinda ya kamata har Nazia tayi wata uku Lokacin Aisha ta kamu da Ciwon Koda Allah ya Mata Rasuwa,Nabeela da Hashimu sunsha kuka,Bayan komai ya lafa Nabeela ce ke kula da kanwarta Nazia,mutuwar Aisha itace tasa Hashimu gaba Daya Allah ya shirye shi ya daina halin banza,Aisha Bata Dade da Rasuwa ba Iyayensa Suka rasu sakamakon ruwan sama da ya rushe gidaje gini ya Fado musu Hakan yasa Hashim ya sake sanyi Har ya samu Safiyya Yar Kano ya Aureta.

Tunda ya Auri Safiyya take ganawa Nabeela da Nazia azaba da wulakanci Amma duk abinda take musu tana Basu Abinci,karshe Abba ya samu kudi ya siyi gida a cikin Kaduna state Suka koma can da Zama,Nabeela Allah ya Sa Mata son kudi zafin nema ne da ita,ta wani bangaren Kuma ta gaji Mahaifinta a masifa,Ga kula da Nazia da Nabeela ke Yi,gajiya tayi da halin Safiyya ta kwaci yancinta ta karfi da masifa har Nazia ta girma Wanda yanzu gasu karfi ya kawo.

Nabeela kyakyawace ta gaske Fara Amma ba Kar ba, doguwa,me diri me kyau akwai diri,Round face ce da ita me dauke da Hanci zarkadede Dan bakinta cut pink,Girarta a cike gata da manyan idanuwa masu haske da kyau,Sai gashinta me tsayi da santsi ko kitso baya Yi sabo da santsinsa,Jikinta kalar Hutu,Hakoranta kanana masu kyau suna sheki sabo da Tsafta ba kazanta a tare da Nabeela.
Alex Kuwa Fari ne sosai Gashinsa Baki wuluk dogo dashi Amma ba tsayi can ba,Gashi ba Ramamme ba Kuma ba me kiba ba,fuskarsa ba doguwa ba sannan ba round ba gata Nan gwanin birgewa Hancinsa Dan dogo, idanuwansa farare manya lumsassu dasu kamar me Jin bacci,kalarsa gaba Daya ta larabawa ce,Abin sai Wanda ya gani,ga iya daukan wanka,komai kyau yake masa idan yayi,iya kallonka baza kaga muninsa ba.

Ci Gaban labari

Ganin Zeena ta bisu sama sai Nabeela ta juya tayi kasa tare da
Ficewa daga gidan direct ta nufi gidansu sabo da yaune da yamma Tarewar Amaryar Abba,Yan Uwan Abba su biyu sunzo Inno da Indo suna ta aikin dafa abincin saukar Baki ita kuwa Safiyya tana daki da kanwarta suna ta bakin ciki da gulmace Gulmace, Kanwar Safiyya tace wlh daga yau karki sake dagawa Nabeela kafa ki taka shegiya ita da kanwarta,Safiyya tace ki barsu kawai wlh sai na hada musu tuggun da sai an kore su daga gidan Nan Baki daya Baki San yanda na tsani yarinyar bane ki kyale su zasu ga masifa.
Yamma likis bayan an Gama aiki an gyara gidan fes Nabeela Wanka tayi ta shirya Nazia itama ta shirya Suka ci kwalliya cikin Wata Atamfa Dark blue and black Sunyi kyau sosai kamar ba Nabeela ba,Su Inno suna ta Mata tsiya sai ga Abba ya shigo ya Sha Shadda Yana kamshi yace fatan dai an Gama komai ga Amarya Nan suna Hanya mota biyu na tura Inno tace mun Gama komai munci wanka,Safiyya ma ta cakare cikin Lace dinta Tana yatsina fuska tana cewa Ahaf me Amaryar ta Isa ta nuna min Azo a Iske mune Matan wlh.

Ba Wanda ya kula Safiyya sabo da an San zafin kishi ne,Abba fita yayi wajen abokansa na Unguwa Ana Angonci,Motoci ne guda biyu Suka tsaya kanana na daukan Amarya Mata Suka Fara shigowa Ana guda,Hajiya Binta Dattijuwa ce Kyakyawa da ita me nutsuwa da hankali,Nabeela ta mike tsaye tana guda aka shige da Amarya dakinta bayan tayi Addua,kayan dakin Hajiya Binta masu kyau na gaske,Safiyya a dakinta ta fashe da kuka Jin da gaske Amarya ta shigo,Kanwarta Murja tace Haba Yaya Safiyya ai sai a Raina ki,Kinga share Hawayenki na taho miki da guzuri,Jakarta Murja ta Bude tare da Dakko wani Dan Garin magani kamar toka ta mikawa Safiyya tace Kinga wannan to idan dare yayi ki fita tsakiyar gida ki zuba a tafin hannunki ki Kira Sunan mijinki Hashimu sau uku ki Busar a iska to wallahi Hashimu bazai taba saduwa Da Hajiya Binta ba,duk sanda ya shiga dakinta bazai taba lafiya ba sai a dakinki,Safiyya Bata San sanda ta fashe da dariyar farin ciki ba, Murja tace to Bari kiji ga wannan ita Kuma laya ce Rami Zaki Haka ki binne sannan ki daura dutse akan layar Nan amfaninta Hajiya Binta da Nabeela baza su taba shiri ba,Hajiya Binta zata tsani Nabeela sannan Zaki mallaketa sai abinda Kika ce shi Hajiya Binta zatayi da Hashimu sai yanda Kika Yi dasu,Kinga idan kika tabbatar magani yayi sai kisa Hashimu ya Aurawa Nabeela ko misaki ne, karki sake ya aura Mata me hankali ko me kudi,sannan ki hada ta da Nazia su tarkata su bar Miki gida shike Nan kin huta Amma matukar Nabeela tana shiri da Ubanta to yarinya ce me kwazo da wayo zata kula da Mahaifinta Kinga ko ya saki Hajiya Binta zata sa ya Auro Miki wata.

Safiyya tace ai bazai ma Yi Mata aure ba idan na bari tayi Aure ai taci gaba ai kawai ya koreta ita da kanwarta,Murja tace Allah yasa daga can ta fada karuwanci Kinga 'ya ta gaji Ubanta tunda dama shima Allah ne ya shirye shi a baya ai Dan bariki ne.
Yan kawo Amarya sunci sun Sha aka maida su gida suna ta murna Hajiya Binta ta Dace,fitarsu ke da wuya su Inno da Nabeela suna dakin Nabeela Ana ta hira Safiyya ta fito tayi duk abinda Murja ta Umarce ta Babu kuskure ta koma dakinta tana zuba Murmushi,Wurin karfe Goman dare Abba ya shigo tare da shigewa dakin Amaryarsa Yana Zumudi,Shigarsa ke da wuya kansa ya Sara sai ya Fara zazzabi Yana rawar Sanyi,Sama sama Suka Gaisa da Hajiya Binta,kazar taci tayi wanka da kyar Abba ya iya tashi bayan yasha paracetamol ya danyi wanka yazo yaci kazar shima,Hajiya Binta tana ta faman Yi Masa sannu suna Gama shirinsu na bacci Suka kwanta Abba Yana ta zazzabi har Gari ya waye.

Da Sassafe Safiyya tace baza tayi girki ba Dole Nabeela ta fito ta dafa shayi ta soya kosai,sai Amarya kuma ta soya Mata Doya da kwai har Palon Hajiya Binta ta Shiga ta tsuguna har kasa ta gaisheta,Hajiya Binta Bata amsa ba sai tsaki da ta ja,da Sauri Nabeela ta kalle ta,Hajiya Binta Haka kawai ta Rasa dalili taji duk duniya Babu wacce ta tsana irin Nabeela da Nazia,Kuma babu wacce take so da tsoro sai Safiyya kishiyarta,Abba ne ya fito Palo yaga Nabeela tana hadawa Hajiya Binta shayi Tsaki Shima Abban yaja yace uban me ya kawo ki ne Munafukar yarinya da Sassafe ko sa ido Kika zo? Nabeela mamaki ya kamata tace Haba Abba Ni me kaunarka fiye da kowa yaushe zanwa Mahaifina munafunci Allah ya kiyaye Abba.

Shayin ta mikawa Hajiya Binta tsawa Hajiya Binta ta bugawa Nabeela Wanda Nabeela ko a jikinta Dan tsawa Bata tsoratata tace Ajiye ki tashi ki bar min daki Uwar shishigi ko ke nake aure? Wlh Hashimu ya kamata ace ka aurar da wannan yarinyar Banga amfaninta ba.
Nabeela tana ji tace na Miki Uzuri Hajiya Amma wlh ki kiyaye ba a takani bani da wannan hakurin Ko Abba ya sani,Abin mamaki sai ga Abba ya wanke Nabeela da Mari abinda Bai taba Yi ba,Dafe kumatu Nabeela tayi tace Abba nice fa Nabeelanka,Nabeelan banza to Nabeelan taci Ubanta tashi ki bani waje Abba ya furta cikin karaji,Nabeela Hawaye ya kwararo Mata Amma ta goge Hawayenta ta fito jiki a sanyaye tana mamaki,tana Fitowa Safiyya tana labe tana Jin komai sai ta dinga kyalkyala Mata dariya,Gashi su Inno sun tafi gida da Sassafe sun tafi garinsu,Nabeela Bata damu ba ta gyara ko Ina na gidan har Dakin Safiyya da Amarya ita ta gyara musu ta wanke Toilet ta shirya Nazia itama zasu tafi Gidan Gwauro aiki sai ko Safiyya tace gidan ubanwa Zaki je ai kin Zama Yar aiki yanzu ke Zaki dinga komai a gidan Nan kuma wlh a samu Musaki a aura Miki,Hajiya Binta ce ta fito tace gaskiya Kika fada Yaya ai Wannan aikin gida ne ya kamace ta,Abba ne ya shigo gidan Yana gasawa Nabeela Harara yace gidan ubanwa Zaki je? To bake ba fita a gidan Nan,Nabeela ta tsaya sororo tana kallon ikon Allah ta kasa Gane Kan abin tunda Abbanta yace baza ta fita ba sai ta hakura ta zauna ita tayi komai har abincin dare,Wasa Wasa kullum abin gaba yake Yi har takai ga Abban ya daina kulata ita da Nazia ko sun gaida shi Baya amsawa,Ga Mugunta da zagi cin mutunci da Matan Abba suke musu salo salo,Hajiya Binta sai yanda Safiyya tace takeyi Bata da yanci sai abinda Safiyya tace, Haka Abba ma kowa baya gabansa sai Safiyya sai Amarya Binta,Wulakanci da Bauta Nabeela takeyi a gidan sun hanata fita gashi duk kudinta ya Kare kaf ita ke siyo duk abinda za a ci a dafa a gidan,Abba sai gyaran takalma ba wani Abu yake samu ba,rashin fita Neman kudin Nabeela yayi sanadin dawowar talaucinsu sabo Dal,Ita ke nemowa kuma an hanata fita,jarin kayan miyar ma ya karye,Duk Wanda yasan Nabeela da yawo sai yaga baya ganinta gashi abokanta maza masu tallafa Mata Abba ya hanasu zuwa gidansa.

Alex Yana ta zuba Ido gidansa yayi dirty da yawa Amma Nabeela Bata zuwa Bai San dalili ba,kullum zuba Ido yake Amma Shuru,Ba Abinci ba kudi a gidan Abba sai zallar wahala da suke Sha da yunwa watarana ba a daura Abinci sau Daya ake ci duk sun rame sun lalace kowa ya gansu yasan a wahala suke,Nazia ma da kyar Nabeela ta roki Usman Alfarma akan ya dinga zuwa Yana Kai Nazia school Yana dakko ta sabo da babu kudin Napep,Kowa yaga Nabeela sai yayi mamaki tana daga musu kafa sabo da Matan Babanta ne ko ba komai Kamar iyayenta suke Amma basa gani,Wasa Wasa har aka kwashe fin wata Daya Watarana ma ko tukunya ba a daurawa Abbanta ya rame ya lalace,Nabeela tana Tausayinsa ta tabbata ba lafiya ba akwai wani Abu a kasa Kuma Safiyya ce ta Haddasa.

Watarana Nabeela ta Gama gyara gida ba abinda zasu dafa kowa yunwa yake ji,Hajiya Binta ta fito tana masifa tace an San baza a iya rikeni ba aka Auro ni,da arzikina da komai an maidani wata kamar Sanda na fige ko wata Biyu banyi ba sai wahala Dana ke Sha mijina Bai taba saduwa Dani ba,ke Dama uban naki bashi da Lafiya Amma ya Auro Ni kullum sai dai zazzabi a dakina, wannan Mene Haka dutse ce Ni eh nace dutse ce Ni,Safiyya tana dariyar mugunta tace wlh ai jiki ba katako bane Ni kuwa baya zazzabi wannan ya nuna baya sonki sai ki dau hakuri,Nabeela Tana jinsu suna ta tonawa Abbanta Asirin Shimfida Hawaye ya zubowa Nabeela tace wallahi Baku Isa ba ku dinga ciwa Ubana mutunci ba,Ke Hajiya Binta na daga muku kafa ne sabo da Kuna Auren Abba to wlh daga yau na daina,Hajiya Binta ta nuna da yatsa tace kin bani mamaki Dama Makkah da Kika je Ashe ba ka'aba Kika gani ba jikin bango Kika shafa Kika dawo? Kin bani kunya daga Yi Miki asiri har ya kamaki da Alama Zam zam din da Kika Sha fitsarar shi Kika Yi a banza,Ina kallonki Hajiya... Hajiya Ashe Arfar ma Baki samu kinje filinta ba? Aikin Bauta kawai Kika yiwa larabawa Kika dawo,Ina ta murna Abba zaiyi aure mu samu lafiya Ashe Annoba ya dakko Sam Baki da Alkhairi Baki Zame Mana Alkhairi ba,shi yasa ake son komai kayi Addua akan Allah yasa ya Zama Alkhairi, Safiyya ta nuna da yatsa tace ke Kuma kiji tsoron Allah wallahi Zaki mutu kibi duniya a sannu,Dariya Suka sakar wa Nabeela tare da shewa Safiyya ta mikowa Nabeela Botiki tace Shiga makwafta ba ruwa a pampo ki ebo Mana ruwa,Kafa Nabeela tasa tayi Ball da bokitin yayi raga raga ya farfashe,Tana Hura Hanci tana kumbura ta juyo tace ko Abba zai koreni wlh na daina raga muku nayi na Allah,ke Safiyya kin sanni bani da mutunci inda yake ma banbi Hanyarsa ba ku har Kun Isa.

Ke...ke..ke...Abba ya shigo Yana yiwa Nabeela tsawa Amma Nabeela Bata fasa ba ta samu Butar Amarya tayi ball da ita ta daki jikin bango ta fashe,Kayan data wankewa Safiyya da Binta Amarya ta kwaso a saman igiya ta tumurmusa su a kasa tare da tattaka su tace daga yau zaku San wace Nabeela Billahillazi sai Kun yabawa Aya zakinta tayi waje abinta tare da buga musu kofar garam kamar zata balle ta,Hajiya Binta tace yau Naga Tsinau dama Haka take tab,Abba yace ku kyaleta kuyi hakuri zanyi maganinta,kaji Yar iskar Yarinya Wai Makkan danaje bango na shafa ba ka'aba ba,Wai Fitsarin zam zam nayi Bai bi jikina ba,Safiyya ta Kara da karya tace Wai harda cewa Da Kika jefi shedan Ashe ramawa yayi,Binta tana dariya tace banji ma wannan ba dama Haka tace zata dawo ne.

Nabeela Bata Yi zuciya ba wajen Abokanta maza taje tace ya akayi ne ya dai Usman Gari fa ya tsaya cik,Usman yace a Haba Naga duk kin rame Nabeela kinyi duhu kadan,Tafka ce wallahi tafka nake sha iya tafka shinkafa tayi karanci ta Kare,Dole aji jiki bani abinda zaka bani na wuce,dubu biyu Usman ya Bata ta wuce wajen Huzaifa ta samo dubu Daya,Haka ta hado kudade Bata Yi fushi da Mahaifinta ba ta siyi kayan Abinci komai ta Dan hada Wanda zaiyi musu kwana biyu tana Kan machine din Usman ta shiga gidan Suna zaune har Abba suna Hira sai gani sukayi Nabeela ta shigo da machine tana bashi wuta Yana bulbula Hayaki da kafa ta jefo musu kayan abincin a cikin Buhu ta sake bashi wuta ta fisga tayi waje,Binta ta Bude Baki tace Amma anyi Yar iska a Nan.
Abba yaga Abinci sai Murna yace a tashi a daura Mana yau muci mu koshi,Safiyya taja tsaki tace ke Binta tashi ki dafa Mana muci,Hajiya Binta jiki na rawa ta Dora Abinci.

Nabeela Bata tsaya ko Ina ba sai gidan Alex tun a compound taji kida Yana tashi tasan Yan Mata ne da samari fasikai, Machine dinta tayi parking sannan ta shiga Palon dauke da Sallama a bakinta ba Wanda ya amsa Mata itama Bata damu ba ta Haura sama dakin Alex,A zaune ta Iske shi tsakiyar bed Yana kallon film a laptop dinsa,Sanye yake da 3qutr da T-shirt me gajeren Hannu maroon color yayi kyau,damatsansa Nabeela ta kalla da gani akwai karfi,Barka da yini Ranka ya Dade Yawwa Zo kiga wani Abu Wai me maza sukeyi da shi ne? Kamar abin arziki Nabeela ta leka kanta Alex yace baza ki gani ba sai kin Hauro saman bed kadan ta hau tare da lekawa taga Matan turawa mawaka da Nicki minaj Hips Kamar zai fado kasa,Alex yace me akeyi da wannan? Naji su Aliyu sunce maza na sonsa,Kunya ta Kama Nabeela ta bar saman Bed din ta zauna a kasa Yana saman Bed.

Alex yaja tsaki yace ki fada min Mana sai wani rufe Ido kike Yi ko na tambayi Zeena? Ko Kuma naje mutane su fada min na biya su kudi,da Sauri Nabeela tace nawa zaka biya na fada maka? Dubu Daya Zan Baki,Nabeela tace kacal zancen fa Iskanci Zan fada ai ya kamata kudin Sufi Haka Oga,Alex yace dubu Biyar to,Yawwa yanzu Zan fada maka, Ina Ina ta Fara tana uhmmmm..Ahmm...ahh....la...la....da sauri ta rufe idonta cikin Sauri tace Lagutse shi akeyi to miko min kudin, Nan take Alex ya Bata dubu biyar yace ban Gane Mene Lagutsewa ba meke nufi? Da sauri tace shafawa...murzawa tayi waje da Gudun tsiya,Na Palo suna ganinta da Gudun gaske Suka mike da Gudu Suma Sunyi tunanin abin tsoro ne, Suka Fara tureriniya a jikin kofa Ana rige rigen fita.

Machine suka ga Nabeela ta hau Bata tsaya ba sai a cikin gidansu,ta bar Yan shaye shaye da kunyar gudunsu ba dalili, ta shiga kwalawa Hajiya Binta Kira ba mutunci ba komai tace Binta Takari.....Takari...ke Takari,Hajiya Binta tace tab wato yau ba Hajiyan Abba ba Amaryar Abba sai Binta Takari Lallai Nabeela Baki da mutunci,Nabeela tana saman machine tace to aikin Hajji Kika sauke? Aiki fa Kika je gidan larabawa,ai ko kinyi aikin Hajji to Bai karbu ba,Kina jifan shedan ya Rama,Ka'abar ma ba ita Kika shafa ba bangon masaukinku Kika shafa Kika dawo shi yasa Ana Miki asiri ya kamaki,Abba ne ya fito Yana Zaki ci ubanki wallahi,Nabeela machine dinta ta bawa wuta Yana bulbula Hayaki sannan ta sakko ta mikawa Abba dubu biyar ba kunya ya karbe Yana harararta ita kam ta fita abinta a machine ta barsu,Bata tsaya ko Ina ba sai makarantar su Nazia.






Sharhi fans.








AsmaBaffa.
[5/10, 3:23 PM] Sis Asma: 🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠





FREE PAGE






NOVELS DINA NA KUDI KO WANNE COMPLT DARI UKU 300 NE

RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDU'AR KAWA


MASU BUKATAR SHIGA GROUP DIN GIDAN GWAURO
NAIRA DARI BIYU 200 NE


ACCOUNT NUMBER NA
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

GA MASU BUKATAR YIN VTU, TRANSFER,KO TURA KATIN MTN TA WHATSAPP GA NUMBER TA
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39








6-10







Official






By
AsmaBaffa







Page naku

Nana Khadija Muhammad
Beauty Boss
Ummin Saddeeq











Tana zuwa lokacin an tashi su Nazia tana ganin Auntynta da gudu ta taho ta Rungume ta,Kawayen Nazia Yaran masu kudi sabo makarantar su Nazia ta masu kudi ce ai Suka dinga zuwa suna gaishe da Nabeela,Nazia ta Dane Bayan machine suka wuce gida,sai da Nabeela ta maidawa Usman Machine dinsa sannan Suka karasa gida a kafa.
Zuwan Nabeela gida ke da wuya Abba ya fito Cike da Masifa yace koma inda Kika fito ki bar min gida,Nabeela tace Abba Dan Allah Wai me mukayi maka ne Haba Abba...wallahi idan Baki bar min gida ba sai na Miki dukan kawo wuka,To Abba Zan tafi Amma ga Nazia ita ta zauna tunda yarinya ce,Nazian Banza ku tattara ku bar min gida tunda Baku da tarbiyya,Hawaye ya zubowa Nabeela tace wallahi Abba Ko kashe mu zaka Yi baza mu tafi ko ina ba,baza mu bar gidan Uban mu ba,Kasan Haka ne me yasa aka Haife mu,wlh bazan tafi ba tana fadin Haka taja Nazia Zasu Shiga gidan Abba ya fisgo Hannun Nabeela,Nabeela ta rike jikin kofa tana ja tana tirjewa Abba Yana janta shima,Nabbela tana Haki tace Nazia Wuce ciki zanji da kaina,Nazia ta shige tana Kuka Safiyya ta tare Nazia tare da fyalla Mata Mari,Nazia ta barke da sabon kuka,Jin Haka Sai Nabeela ta saki Hannunta ba zato ga Abba ya rike ta sosai ya Gama tabewa kamar za a Harba kibiya,Abba ya tafi Luuuuu rigijif a kasa ya Fadi da karfi,Nabeela tayi kansa tana Bashi hakuri sannu Abba Dan Allah kayi Hakuri ban San zaka Fadi ba,Nabeela ta Kama Abbanta ya mike tsaya ta shige gida da gudu ta Iske Safiyya tana dukan Nazia, Nabeela Kawai itace ta dakko Tayo Kan Safiyya ai Safiyya ba shiri ta shige Dakinta da gudu ta kulle kofa lokacin Hajiya Binta Bata Nan taje Unguwa.

Abba Yana ji Yana gani Nabeela da kanwarta Suka Yi zamansu Kuma suka ci suka koshi ba yanda ya iya Haka Safiyya ma Sai kallo sai Harara,Da Yamma Hajiya Binta ta dawo bayan Sallar Isha Nabeela tana yiwa Nazia Assignment Hajiya Binta ta kwalawa Nabeela Kira Nabeela....ke Nabeela....suna ji Nabeela ta amsa Na'am Takari gani Nan,Abba ya bude Baki yace Iyyeee to Dan ubanki na Baki sati Daya Ki fito da mijin Aure ko wallahi na aura Miki Wanda Naga dama,Nabeela tace yo Abba ai Takari ce Nan tace ta iya miyar Habbatusaudat da tuwon Dabino,har nayi zaton ta iya dambun Hulba Ashe ko miyar Zaitun Bata iya ba Ashe a Tabuka can Kan dutse ta Kare rayuwarta wajen da akayi yakin Tabuka,Kuma Saurayi Bai Zo ba Abba Taya Zan fito da shi nayi Aure,To kuwa wallahi Zan Baki mamaki Zaki Gane kurenki.

Nabeela mantawa tayi da Umarnin Mahaifinta taci gaba da rayuwarta tana Zuwa aikinta Gidan Alex da sauran wajen Neman kudinta taci gaba da daukan nauyin gidan ga zagi da masifa Iri iri, Tana gidan Alex yau Yan shaye shaye Basu zo ba Tunda ta gyara gidan neat Yana ta kamshi Bai baci ba,Alex Yana kitchen zai Fara girkinsa Itama Nabeela yunwa ta kamata ta Shiga kitchen zata dafawa kanta Abinci Suka hadu a kitchen kowa da tukunyarsa suna girki ba Wanda ke kula wani,Nabeela ta Bude fridge zata dauki Abu Shima Alex yazo gaf da Nabeela Kamar zai hade jikinsu,Kunya da tsoro ya Kama Nabeela Kamshin Alex ya Gama ruda Mata tunani,jikinta ya Fara Rawa,Alex yace karki sake ki dauki Kalar Naman Nan,Nabeela ta juyo suna facing juna ta turo Baki tace to Ni shi nake so,Gidanki da Zaki Zo kina yanda Kika ga dama? Ai wannan gidan a wajena inda kasan Na Abbana Hashimu Haka nake ganinsa abinda nake so zanyi,Ido ya kafe ta dashi Nabeela tace ka daina kallona baka Sallah ba sonka zanyi ba,Nafi karfinka Nabeela ta me rabo ce,Fuska ya Bata tare da Jan tsaki yace Ni an fada Miki mutun ne da Zan soki? Harara Nabeela ta galla Masa tace wa ya sani Abu da duhu,Ni dai nafi karfinka ehe .

Kanwarki nake jira ai ta fiki kyau lokacin da zata girma na Zama Mutum sai na Aureta lokacin kin tsufa ke kin Zama Goggo,Nabeela taji Haushi tace wa zata Fi kyau ai wlh....tukunya taji ta Fara konewa Ta koma wajen Gas cooker da sauri ta zuba sanwa tare da Daukan wuka Alex yace bani wukata na Riga ki Mika Masa tayi ba musu a hankali ta Furta masu gida manya.
Tari Alex yayi har sau biyu mamaki ya kamashi ya saki salati ba tare da yasan yaushe ya Iya ba yace La'ilahaillallahu

Please Login or Register in order to submit comment