Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

3







Official







By
AsmaBaffa







Page naku ne
AUTA
FLOWER
RUKIEY MUAZ









Kida ya kunna Yana jin kidan turawa,Tsaki Nabeela ta ja kasa kasa ta Furta a Haka yace shi ba mutum bane,Suna tsayawa a bakin gate Taga An wangale musu gate da Alama Me Gadinsa ne Daya dauka domin taga yanda jikinsa Yana rawa Yana kwasar gaisuwa,Kallonsa Nabeela tayi kafin tayi magana Alex yace me gadi ne so what? Shuru tayi tana mamaki ya akayi yake Gane Zancen zucinta sai taji ya Bata amsa gefe Daya kuma kallon ikon Allah take Yi ganin motoci har kala Biyar a cikin gidan masu shegen kyau da tsada,Nan ma yace nawa ne ki daina kallon su,ai Jin Haka sai ta rufe idonta a tsorace,Bayan yayi Parking Fitowa sukayi tare da takawa zasu shiga ciki,Shigar su ke da wuya Nabeela ta bude Baki tana kallon Aljannar duniya,Gidan yasha furniture masu uban kyau da Kaya na Haduwa duk wani Abu na Jin Dadi da gayu an zuba a gidan,a tsakiyar Palon Nabeela ta tsaya tace dankari Lallai mutumin Nan yasan Jin dadin duniya,Haduwar duniya..kafin ta rufe Baki Alex ya fada saman lafiyayyar kujerarsa ya nutse a ciki tare da daukan Remote Yana canja Chanel,Nabeela tana tsaye taga wani Saurayi matashi zai Kai shekarun Alex ya fito daga bedroom Dake Palon shi da Wata Budurwa Yar gayu,Kafin tayi motsi wata Budurwar ta fito Tana gyara mayafinta Namiji Yana bayanta shima matashi ne saurayi, ta bayanta taji Shigowar wasu mazan su biyu,da sauri ta juya Suma tana kallonsu.

Nabeela ta Shiga kallon mazan Nan Daya bayan daya da Matan Nan su biyu sun zauna a palon suna ta Hira sun fito da kayan shaye shaye Dana Maye suna korawa ga kida sun kunna,kafin kace me sun turnuke Palon da hayaki ta ko Ina na Shisha da Wiwi,su kuwa Matan syrup suke korawa kawai,Alex Yana kallonsu suna ta zuga shi akan ya Sha Amma yace shi ba mutum bane bazai Sha ba.

Jikin Nabeela ne yayi sanyi Lallai ya tabbata gidan Gwauro to a Ina ya samo wannan mazan da Matan Duk Yan Tasha da su,Daya a ciki ne ya kalli Nabeela yace ya akayi Yan Mata Alex ko Kaine ka samo taka ne? Gaskiya ta hadu kalar da nake so gata Fara gata da kyan sura wannan zata Yi ruwa da Alama,dariya Suka saki suna kallon Nabeela tsananin Kyawun Nabeela shi ya gigita su,Alex Kuwa Bai son Hayaniya ko kadan tashi yayi tare bin steps zai Haura samansa,Nabeela tace to ni baka nuna min aikin ba? Ai kin San Abinda ya Dace ki Fara kawai,ran Nabeela ya baci ta Fara duba gidan da kyar ta gano kayan shara da mopping a bayan kitchen,cikin fushi ta Fara share Palon Ta biyo ta inda Yan shaye shaye suke ba magana ba komai tabi ta Kan kafafun su da shara tana cewa jaraba anzo an cika Mana gida da Yan wiwi,talakawa matsiya ta an ga me kudi an manne masa.

Ko kula Nabeela basuyi ba tana ta fada musu magana me zafi,Daya cikin Yan Matan Khausar ta kwantar da Kanta saman kafadun Saurayinta,Baki Nabeela ta tabe tare da ci gaba da aikinta har sai da ta gyara ko Ina a Gidan Yana kamshi da sheki sannan ko sallama Bata yiwa Alex ba tayi gaba abinta, tana Isa gida Babu Bata lokaci Abinci ta ci tare da Taya Matar Babanta aiki sannan tayi wanka,Nazia ma wanka tayi Mata tare da Shirya ta suna yin Sallar Isha Bacci ne ya kwashe ta.

Bangaren Alex ma shower ya sakarwa kansa ya Dade Yana wanka kafin daga bisani ya fito tare da goge jikinsa da towel,lotion ya shafa me kamshi da tsada sannan ya shirya kansa cikin wasu kayan Bacci masu taushi, Sarkar sa ta cross ya maida wuyansa sannan ya feshe jikinsa da turarukansa masu dadin kamshi ya kwanta a saman bed dinsa ya Shiga tunani Wai shi mutum ne ko ba mutum bane,Maganar zucinsa ce ta fito filo Yana cewa gaskiya ba mutum bane Ni Idan Mutum ne ai duk irin abincinsu Zan na ci to ya akayi Ni ba komai nake ci ba sai Vegetables da nama kawai,Sannan ya akayi nake Jin kamshin mutum me Dadi kamar na cinye mutum musamman Nabeela,To ko dai Ni Dan Shan jini ne? Da sauri ya girgiza Kai tare da furta no way, gashi Kuma na iya turanci a Ina na koya? Mota ma Sai na ji na iya,Abubuwa da dama...kansa ya Dafe Yana Tausayawa kansa kamar maraya a hankali ya furta Ni bani da Kowa kenan Yana Haka bacci yayi gaba da shi.

Washe Gari Da wuri Nabeela ta Taya Safiyya Matar Babanta aikin gida bayan sun karya wanka tayi tare da Nazia,Doguwar Rigar Lace maroon and milk ta saka wacce aka Bata kwancenta a gidan masu kudi da take zuwa aiki,Tayi kyau sosai gashinta me uban tsayi ta gyara ta yafa mayafinta Milk sannan ta Shirya Nazia cikin Kaya Yan kanti farar T-shirt da wando dogo yarinyar tayi kyau gashinta ta gyara Mata sannan ta sa Mata wata hula me kyau kalar rigar ta,Baki Hajiya Safiyya ta tabe tare da Furta Abi duniya a sannu a rage karuwanci,Nabeela ta rigada ta Saba da bakin cikin Saffiyya matar Babanta,Shi yasa Bata ganin mutuncinta ko kadan,idan na Nemo kudin har dake ake cin kudin karuwancin,Kishiya dai kamar anyi Miki Kuma wlh saura sati Daya biki zata shigo gidan nan.

Tsaki Safiyya ta ja tace sai me ayi dubu ma,Nazia ce tace Aunty kyale ta ki tafi Dani wajen aikin naki Dama idan ba kowa dukana takeyi tana zagina,Takalma Nabeela ta sawa Nazia sannan ta rike Hannunta Suka fito,a kofar gida Suka Iske Babansu Abba Hashim Yana gyaran takalminsa gefe Kuma ga Table din kayan Miya Yana siyarwa,Sallama Nabeela tayi Masa tare da furta Abba Mun tafi wajen aiki,Yau da Nazia Zaki tafi kenan? Ae Abba,to a dawo lafiya a kula Allah ya tsare,Ameen Abba cewar Nazia hannunta cikin na Nabeela Suka tafi abinsu Nazia tana ta faman yiwa Nabeela surutun makarantarsu.

Napep Suka shiga zuwa Gidan Alex,Mintuna kadan aka sauke su a bakin gate,me gadi ne ya Bude musu kofa Suka shiga ciki har katafaren Palon Alex,gidan Shuru ba kowa,Nazia tace Aunty gidan Nan Yana da kyau musamman kayan ciki,Bata nemi Alex ba kawai ta shiga gyara gidan tana aikinta ita kuwa Nazia saman kujera ta zauna a palon tana kallon Chanel na cartoon har sai da Nabeela ta Gama gyaran gidan Sannan ta Haura saman Alex shine kawai Bata gyara ba,Abin mamaki tana shiga Hadadden Room dinsa baya ciki Kuma baya toilet,Nan ma fes ta gyara shi Yana fitar da kamshi na musamman toilet din ma Haka,Bayan ta Gama Kitchen ta shige tare da Shirya musu lafiyayyar jullof rice Tasha nama da kayan lambu, Dining ta shirya sannan tayi Sallar Azahar tare Nazia Suka ci abincinsu Suka koshi tare da zabar irin lemon da suke so suka Sha abinsu,Mamaki ya Kama Nabeela na rashin ganin Alex to Ina ya tafi,Baki ta tabe tare da cewa Nazia tashi mu wuce gida,Kafada Nazia ta makale tare da furta ke wai Aunty Muna Shan dadin mu sai kwankwadar lemo da Madara nakeyi Zaki ce mu tafi gida,gidan Nan me kyau na masu kudi Dan Allah mu kwana a Nan ga sanyin AC Ina ta Sha a jikina, Dariya Nabeela tayi tace Dalla tashi kamar wata babbar mace kina tsaro zance,Mikewa Nazia tayi ba a sonta ba Haka ta saka takalminta tare da furta Dan Allah Aunty ki tsaya tunda kince me kyau ne na ganshi ko ya fimu kyau,Baza ki ganshi ba muje gida,Gobe fa Zaki dawo Dani? Tsaki Nabeela ta ja tace muje uwar naci.

Fitarsu compound ke da wuya rantsatsiyar Motar Alex ta danno Hancinta cikin gidan,Shike Driving da kansa,Nazia da sauri ta makalkale Nabeela jikinta Yana rawa tana cewa Aunty Bature zai Kama mu,Fuskarta ta boye wayyo Haskensa Yana kashe min ido,idona zai mutu kyawunsa yayi yawa Aljani ne Aunty.
Dariya Nabeela ta dingayi da shirmen Nazia,Cikin taku na mazantaka ya fito da Ledoji a hannunsa na shopping mall,Cikin salon tafiyarsa na mashahuran maza masu ji da Naira ya tako har gaban Nabeel,Ido Suka hada Yana binta da mugun kallo,da sauri ta dauke idonta a cikin nasa tayi gefe da kanta,Kunya ce ta kamata domin ya kure ta tana kallonsa yanda ya tsula uban kyau cikin Shadda sea blue dinkin nasa na gaske Dan cif cif jikinsa,abinka da farar fata gashi da gani Bai San wahala ba Hutu da Jin Dadi ya Gama ratsashi, Baki ya tabe tare da kashe Ido Daya yace hope kin Gama aikin? Kanta Yana kasa ba tare da ta kalle shi ba tace Ae, let's go naga aikin naki idan baiyi ba sai kin sake,Nabeela Bata San sanda ta jefo Masa tambaya ba Ina Kaje da tun safe Kuma kace ba Wanda ka sani a garin Nan?...bakinta ta toshe da sauri Mene nata a ciki da har zata Masa wannan tambaya,ciki ya nufa Suka bishi a baya Nazia tana ta Jin tsoro cikin rada tace Aunty Arne ne Ashe? Ga cross nan a wuyansa,Hannun Nazia Nabeela ta matsa tare da Furta Ina ruwanki,Arne ne Aunty baya Sallah tab.

Shigarsu ciki ke da wuya ya Fara duba ko Ina ya tabbatar aikin nata yayi sannan ya duba Dining a Nan ya tabe Baki yace kwashe wannan ance Miki Ni mutum ne da zanci wannan? Dama tana son abincin da sauri ta zaro Leda baka ta juye ciki tasa a cikin Jakar ta,You can go ya Furta tare da riko Hannun Nazia,ba shiri ta saki ihu ita tsoron Kyawun Alex take ji,Bai sake ta ba har ta Gama tsoron nata Murmushinsa ya sakar Mata Wanda yayi Sanadin Firgitar Nazia Karo na uku,Ganin jikinta Yana rawa ya saketa yace kin taba ganina Amma kike Jin tsoro na? Nazia tana karkarwa tace yanzu kafi kyau ne shi yasa,Kudi ya zaro dubu biyar ya mikawa Nazia yace kije school da su kinfi Auntynki kyau, Fuska Nabeela ta Bata tare da furta ai wlh na fita kyau ita da Bata kaini gashi da Hanci ba sai ace ta fini kyau,dariya ta Bawa Alex yace Ku Dan Adam Bakin ciki gare ku,your blood sister kina Mata Hassada,a Haka dai kake so ka koma mutum din tana Gama fadin Haka ta juya Suka tafi abinsu.

Shi kuwa Alex saman kujera ya kwanta Yana kallon film Yana kallon me mutane suke aikatawa Yana tunanin dama shima ace mutum ne,a zuciyarsa yace Dole na koma mutum zumbur ya mike ya Shiga kitchen ya iske ragowar Abincin da su Nabeela Suka ci Suka rage,Fara ci yayi da sauri sauri,Cokali uku ya Sha ruwa sai ya Fara kakarin Amai da sauri ya fada toilet ya Shiga kwara Amai, jijiyoyinsa Suka firfito idonsa yayi jajir Nan take zazzabi me zafi ya Kama shi bayan ya Amayar da Abincin tas, Yana kwance Yana numfashi sama sama kamar 30mnt Zazzabin ya sauka sai karfi da yake ji a jikinsa Kamar Zaki, idonsa jajir Yana Huci shi kadai katsam lokacin Nabeela ta manta Yar karamar wayarta ta dawo dauka ta bar Nazia a compound,tun farkon zuwanta Palon take Jin gurnani a hankali ta lallaba tana Hello....zumbur Alex ya mike tare da juyowa suna facing juna,lokaci Daya tsoro ya shige ta ganin ya koma wani red idonsa ma jajir ga wani irin nishi Yana Yi Yana tunkaro Nabeela wanda baya cikin Hayyacinsa, Hakoransa masu matukar kyau ya bude da Niyyar cizon Nabeela,Hawayen Wahala da tsoro ya tsiyayowa Nabeela ta Fara ja da Baya ya dumfaro ta,Dan Shan jini ne Kai? Ta furta tana ja da baya jikinta Yana rawa,da karfi tace Wayyo Abba Dan Shan jini ne ta kwashe da gudu,ya rufa Mata baya Allah yasa tana fita a palon ta garkame kofar,Nazia Kamar Babba tana ganin Nabeela ta fito a tamanin itama ta fita a dari tayi waje,me gadi Yana bakin kofa yaji Nabeela tana cewa ka buya ka buya me gadi Dan Shan jini.

Da Gudu ya fada dakinsa ya banke Nabeela kuwa tuni Sunyi waje Allah yasa sun tsaida me Napep Yana jiransu,suna shiga yaja yayi gaba a sukwane, Alex kasa Bude kofar yayi ya Fadi a kasa ya sume a Nan.
Su Nabeela Basu samu nutsuwa ba sai da Suka gansu a gida sannan ta tsaya a kofar gida ta Kama Nazia tace karki sake ki fadawa Abba abinda ya faru ko Umma Safiyya da kowa ma karki sake indai naji kin fada sai na yanke Miki kunne Daya Kuma sai kin wanke Bishiyar gidan Nan tas da soso da sabulu,Ai bazan fada ba Aunty kin hanani surutu yawwa good girl,tafawa sukayi sannan Suka shige gida ba Wanda yasan me ya faru,Nabeela tana tunanin Yar wayarta tace ai Dole na koma gobe na dakko hakkina,ai ko zai shanye min jini Yar wayata sai na dakko ki nasan dabarar da zanyi.

Sai da Gari ya waye sannan Alex ya tashi fes da shi ya dawo normal,abinda ya faru jiya ya tuna mamaki ya kamashi da sauri ya fada Toilet ya sakko wanka Kamar ba shi ba ya fesa gayu cikin kananan Kaya Designers na manyan Yara yayi uban kyau Yana kamshi,kitchen ya shiga tare da Bude Fridge ya dakko Danyen Mama ya gasa shi sama sama ya hada da ganyen Salad yaci ya koshi dama irin abincinsa kenan baya cin Abinci Kamar kowanne mutum Naman ma Sai Danye danye baya gasuwa.
Halin da yake ciki ne yayi mugun damunsa ya kasa ganewa mutum ne ko ba mutum ba oho.

Nabeela Hular kwano ta aro ta machine ta jibga kayan sanyi a jikinta duk uban zafin da akeyi,safa kafa da Hannu wuyanta ma ta nannade shi Wai Kar fa Alex yasha jininta, Hular kwanonta ta saka ta nufi gidansa da safe zata dakko wayarta,Cikin tsoro ta karasa harda tambayar me gadi ko Oga ya fita? Me gadi yace ban sani ba.
kwankwasa kofar palonsa tayi a hankali,Bai Bude ba Yana ji sai da ta Dade tana knocking sannan yaja tsaki tare da Mikewa ya Bude kofar,ganinta yayi cikin Hular kwano ga jikinta da uban kayan sanyi,Murmushi ya saki ya gane dalilinta,ciki ta shiga tana sanda Kamar Barauniya Yana tsaye Yana kallonta ta dauki wayar a saman center table ta arce da gudu tayi waje,Tsaki yaja tare da kulle kofarsa.

Tana barin gidan Yan barikin Abokansa Mata da maza su shida Suka shiga gidansa za ayi shaye shaye da fasikanci, cikin Matan Sapna tace gaskiya gidan Nan yasha gyara yau kaji wani kamshi,wacce ake Kira da Khausar ta furta wlh yunwa nake ji dama wannan Yar aikin tayi Mana girki ciki ta duba taga wayan,Zeena wacce ke mutuwar kaunar Alex Kamar ta mutu ta mike tare da komawa Kusa da Alex ta rike Hannunsa cikin salo,Hannunsa ya fisge da sauri ya matsa gefe can ya barta dariya Mazan sukayi Aliyu,Muazzam da Saif,baya sonki Zeena gwara ki zauna a wajena wannan yafi karfinki cewar Muazzam,Fada Mata ta sani Alex ya Furta Yana latsa katuwar iPhone dinsa latest.

Kayan shaye shayen su Suka zube a gabansu tari guda Suna ta zuga Alex Kan ya Sha gajiya yayi da Halinsu sun damu ya Sha Bai San me suke ji ba yau dai ya dauki kwalabar Giya zai Fara Sha kenan Sai ga Nabeela ta banko kofa da uban karfi,Bagazam Bagazam ta taho da sauri tare da fisge kwalabar dake Hannun Alex Wanda saura kadan ya Sha,Zage zage Nabeela ta Shiga yi tana masifa,aikin banza sai kace gidanku na Rasa Jarabar da ya kawo ku gidansa Dan Kunga bashi da Iyali to nice Iyalinsa Kun maida Masa gida Tasha bariki,Ku wato kunzo ga gidan Gwauro zaku bararraje to wlh Baku Isa ba ku taka a sannu Kar na dawo gidan Nan da kwana kuga rashin mutunci Yan tsiya kawai karuwai Yan bariki,Zeena ce ta mike ta shararawa Nabeela uban Mari,Kumatu ta dafe ta kalli Alex tace kana gani ta mare Ni ka tashi ka ramamin,Baki Alex ya tabe yace Ina ruwana wannan fadanku ne na Biladama, Nabeela anyi tsokana ga tsoro Bata da karfi,kwafa tayi tace Kinci daraja daya yau Asabar ranar hutun aiki ce Ina hutun dukan mutum wlh da sai na karya Miki wuya,Kuma idan kin cika ke Yar bariki ce kiyi tsirara a Nan,Zeena tayi dariya tace cikakkiyar Yar bariki ce Ni Bari na gwada Miki Dan ki tabbatar,Zeena ta Fara yakice kayanta tana cirewa ba ko kunya.

Saura pant da bra Suma zata cire Muazzam yace Bari Haka Mana Zeena,Ka Bari na gwada Mata ko Ni wace,Nabeela tace ae gwada mu kuwa muga blacj mazaunanki da nankarwa me suffar doya,Zeena ce ta shako wuyan Nabeela ta Fara jibgar Nabeela tana ta ihu ba Wanda ya raba sai da Zeena tayiwa Nabeela lis sannan ta kyaleta,Nabeela ba karfi tace Uwarki Kika duka shegiya shamulallen baya,Alex ne yaji Tausayin Nabeela ya riko Hannunta tare da zaunar da ita a kusa da shi,Zeena wani kishi da bakin ciki ya tokare Mata makoshi,Tace yau sai na karairayaki a gidan Nan ta sake damko Nabeela,Alex ya Fara tunanin me zaiwa Zeena Dan ta takurawa Yar aikinsa a ransa yace Nima Bari na koyi yanda Naga mutane suna yi,iya karfinsa ya dage tare da kwashe Zeena da mahaukacin Mari Nan take ta zube kasa sumammiya.

Ihu su Muazzam Suka saki suna ta mutu Alex,wallahi ta mutu ka kashe Zeena,Muyi ta kanmu Aliyu tun kafin Yan Sanda su zo,Nan Suka mike gaba Daya Suka bar gidan,Daga Nabeela sai Alex sai Kuma Zeena kwance Kamar gawa,Babu Wanda yayi magana har Alex kawai sun zubawa Zeena Ido sai da aka kwashe lokaci me tsawo sannan Nabeela ta ebo ruwan Sanyi ta kwarawa Zeena Amma Shuru,Ganin Haka shima Alex ya ebo tare da shekawa Zeena nasa Amma Shuru,Botiki ya dakko ya ciko shi dam da ruwa ba jira ya juyewa Zeena a jikinta Amma Shuru,Nabeela tace yau mun shiga uku dauketa muje toilet Alex,Kamar jaririya ya sunkuci Zeena zuwa cikin Wani toilet Dake bedroom na Palon kasa,Cikin bathtub ya zaunar da ita Nabeela ta saki shower akan Zeena,shima Alex yace a Kara da wannan ya Murda Kan pampo Akan Zeena shaaaaaaa ruwa kamar Hauka sai ga Zeena ta Fara tari tana shidewa,Farin ciki ya Kama Nabeela tana tsalle da yeeeeee ta farfado,dariya Alex yayi kadan Yana kallon Nabeela yanda take abin Yara sai ta birge shi yaji Dama shine mutum shima.














AsmaBaffa.
[5/10, 3:22 PM] Sis Asma: 🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠




FREE PAGE








Ga masu bukatar siyen Novels Dina na kudi ko wanne complt dari uku 300 ne

RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDU'AR KAWA


Masu Bukatar shiga Group din GIDAN GWAURO Naira dari biyu 200 ne.


ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBank.


Masu yin Vtu,Transfer,ko tura katin MTN ta WhatsApp ga number ta
08033933642.

'YAN NIGER ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39.








4







Official







By
AsmaBaffa






Page Naku ne

Nafeesat Umar Muhammad
Oum Ilham
Rukayya Muhammad
Bk
Basmam Glam.









Shower suka kashe Zeena ta mike da kanta tayi waje Ba tare da ta kalli kowa ba, Nabeela ta juya Suka fita suma,jikinta ne ya gogi na Alex kadan wani Yarrrrr taji har kwakwalwarta abin ya Bata tsoro Bata taba Jin Haka sai a jikin Alex,Maganar zucinta ne ya fito fili ta furta to baya Sallah dai bare kice kina sonsa Nabeela,Bangaren Alex Kuwa da sauri ya matsa gefe tare da Bata Rai Jikin Nabeela ya gogi nasa shi fa ba mutum bane,Tsaki ya ja kadan ciki ciki yayi magana yace ku fa mutane aikinku kenan Namiji ya taba jikin mace Ni karki sake taba min jiki bana son irin wannan nonsense din naku.

Takaici ya Kama Nabeela wacce ta tsaya a Palo tana kallonsa Yana Raina Mata hankali,Hey Hold on Abeg waye ya damu da jikinka? Ka taho ta kofa mu hadu mistakenly kazo kace Ina son taba jikinka A.c ce a jikinka da Zan damu da shi ko kuwa jikinka Gold ne ko Diamond? Tana furta Haka tayi waje abinta a bakin gate ta Tsinci Zeena tana bawa me gadi Umarni Kan ya Kular Mata da Wanda take so Alex,Dan Asabe Dan Allah ka kular min dashi karka Bari wani ya cutar min da shi,Kuma karka bar mace ta kula min Alex na baka Amana,nice Matarsa verysoon,Dan Asabe yace angama Hajiya Amma ai ba musulmi bane ke Kuma musulma ce,Tsawa ta bugawa Dan Asabe Wanda ya haife ta tace Dalla Malam dakata Ni Zan musuluntar da shi to,kayi abinda nace,kudi ta zaro dubu Uku ta mikawa Dan Asabe Yana washe Baki ya amsa.
Nabeela ce ta karaso Inda suke tana murmushi tace Zeena ki taimakawa kanki wannan bayahude ne baza ki iya musuluntar da shi ba,Tsaki Zeena taja tace to uwar kinibibi Ina ruwanki kazama Yar talakawa kalleki kalli kayan jikinki duk sun Gama kodewa Yar aiki Dake har kin Isa kiyi magana Dani kizo gidanmu ki Sha kallo dakikiya.

Nabeela ranta ya baci tace Kinci sa'a yau Asabar Ina hutun dukan mutum da sai na Saki kin wanke min bishiya tas da soso da sabulu...kafin ta rufe Baki Wani uban kamshi suka ji da sauri suka juya inda kamshin ke Fitowa Alex ne Sanye cikin kana Nan kayan Yan gaske White Jean da rigarsa rabinta Dark blue Daya Rabin Kuma white,Takalminsa shine abin kallo fari,Ga wani agogo me tsadar gaske Abin ba acewa komai sai Wanda ya gani,Farar motarsa ya zaba ya Shiga ko kallon Inda su Nabeela suke baiyi ba,Sai da Dan Asabe ya wangale Masa gate yazo fita saitin Nabeela ya sauke glass yace Get in let's go,Nabeela sai ta kalli Zeena tace aje a hau Napep ayi gida Baki da fada wajen Ogan,wa ya Isa ya ja da Nabeela? Wallahi Kika Yi Wasa sai nasa Yan daba sun Miki tsirara a gaban Dan Asabe,abokaina duk maza ne tana magana tana shigewa gaban motar Alex,Tana rufewa ya ja suka wuce Yana Jin kidansa kasa kasa,A sace ya kalli Nabeela yaga ta kwantar da kanta a jikin window tare da lumshe ido.

A kofar gidan su ya ajiye Nabeela yayi parking ba tare da yayi magana ba ta Balle murfin mota tayi waje tare da Furta na gode Oga Allah yasa Ka Zama mutum,Alex Bai San sanda yace Ameen ba,tace Zan dage na taimaka maka,Allah dai ya biya Honorable,Kai ya daga Mata kadan yaja motarsa yayi gaba,Shigarta gidansu ke da Wuya Nazia ta taso da gudu tana cewa sannu da zuwa Aunty kina can gidan me kyau kin barni,Abishirinki Aunty? Goro fari Kal Nazia,Abba ya Kara Aure yau aka Daura Aurensa da Hajiya Binta Yar Makkah,Nabeela ta rangada guda tace da gaske? Wallahi dazu yazo ya fadawa Umma Safiyya ta dinga ta masifa tayi yaji ma ta tafi gidansu dazu,Zama ta dawo ne cewar Nabeela,Baki ci Abinci ba? Ae yunwa nake ji,Nabeela Nan take ta Ajiye hand bag dinta ta daura musu Abinci suna ta murna Abbansu ya Karo Aure zasu huta zasu samu ne kula da su ba irin Safiyya ba matar Babansu.

Bayan Nabeela ta Gama Girka musu Shinkafa da Miya da Salat sun ci sun koshi ta ajiyewa Abba nasa, gidan ta gyara sannan Suka yi wanka,Nabeela ta saka wani skert Dan kanti tare da Wata Yar Riga me siririn Hannu Kamar Vest kasancewar Ana zafi,Nazia kuwa Yar T-shirt tasa Fara da gajeren Wando pink,Nabeela Bata Bari Nazia tasa kayan Hausawa sai na turawa ita a Dole Yar gayu,kuma Kaya masu kyau take siyawa Nazia duk kudinta Akan kanwarta Nazia ke karewa makaranta ma me tsada take biyawa Nazia school fees.



Please Login or Register in order to submit comment