Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan ya Mika Mata nasa tafin Hannun suka Dan tafa sama sama a tsorace Kar Yan sa Ido su ganta,Murmushi yayi Yace cikin muryarsa me Dadi sai nazo gidanku, oh ka Gane gidan ne? Kai ya gyada Mata,to a Ina zaka kwana? Ba ruwanki da wannan,okay kawai tace Suka rabu tana ta murna Wanda ta Rasa dalilin hakan,Shi kuwa bangarensa murna yake zai koma mutum fa shima.








Ina gaisuwa Fans

Sharhi nake bukata ba godiya ba.










AsmaBaffa.
[5/10, 3:16 PM] Sis Asma: 🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠




FREE PAGE





Ga masu bukatar siyen complete Novels Dina dari Uku 300 ne kowanne

RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDU'AR KAWA


Ga me Bukatar Shiga Group din GIDAN GWAURO
Naira dari biyu 200 ne.



ACCOUNT NUMBER
0175487861
Asmau Garba Muhammad
GTBank.


Masu yin Vtu, transfer,ko tura katin MTN ta WhatsApp ga Number ta
08033933642.

'YAN NIGER ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39.









2









Official







By
AsmaBaffa





Page naki ne
AIDA MAMAN TASNIM.










Gida Nabeela ta karasa Bayan ta kaiwa Sa'ad Machine dinsa,Abba ne ya fito Yana cika Yana batsewa ya Fara zuba Mata masifa wato Nabeela duk abinda Zan fada Miki ba Kya ji ko? Kin Mai Dani banza a unguwa,ace yau Ni da idona zanga katon Namiji kin Goya shi ya aza Hannayensa a wuyanki da kafadunki,kin zubar min da mutunci, Baki Bude Nabeela ke kallon Abban nata,fada yaci gaba da yi Kuma harda turo Sa'ad da kayan Miya ya Raina min hankali nasan ke Kika ce yace min haka,Makaho ne ni?Dan Ubanki nace Ni sa'anki ne ko Makaho ne Ni?

Kayi Hakuri Abba wani Business ne ya biyo ta haka,Zaki ga Business wlh kina ji kina gani Zan aurawa wani ke tun da Naga Alama ke Baki da Hankali gaba Daya, da Sauri Nabeela ta kame kamar soja ta daga Hannu saman goshi tare da sarawa tace Yes Sir.....I salute you Abba dama Ni bana so nayi hankali yanzu,Nafi so inta Jin dadina Haka,Dadi nake ji Abba Ina Jin dadin rashin Han....tsawa ya buga Mata rufe min Baki wawiya kawai,Shuru ta tsaya a gefe sai da ya gama fadansa ya shige dakinsa sannan itama taja kafarta ta fada dakinta ita da Kanwarta Nazia wacce ke zaune tana rubutunta a littafi tabbacin Assignment take Yi,Baki Nabeela ta tabe tace indai Boko ne yanzu Kika fara Nazia,Abeg stop reading You are waisting your time,Iliminan Nima nayi shi Amma wacce karuwa Kika ga nayi? Can't you see where it has landed me to? Wannan Abubuwan duk karya ce,katon gardi ne kawai yaci ya koshi ya Rubuta Textbook na karya don ya Dora ku a mummunar akidar boko.

Littafin ta duba tace mugani ahhh Kinga Wai two square Minus 1 square....dariya Nabeela tayi tace ki fada Masa Dan Kan babarsa 2-1 saura 1 Dan gyatimarsa kaji balagaggen malami, yo dama biyu a ebe Daya ai saura Daya,Nazia oya bani littafin Nan naki ta fisge notebook a Hannun Nazia ta Rubuta Dan Kan Uwarka biyu a ebe Daya saura daya,baka iya komai ba jaki.

Nazia Bata da wayo Bata ma San me aka rubuta ba Bata iya karatu sosai yarinya ce sosai,ai kuwa ta rufe Assignment a matsayin yayarta tayi Mata Assignment ta huta gobe zata Yi submitting.
Ruwan Zafi Nabeela ta dafa tayiwa Nazia wanka tare da shafe Mata jikinta da Mai,itama wanka tayi sukayi Shirin bacci bayan sunci abincin dare bacci ya kwashe su,gaskiya Nabeela ba karamin son kanwarta takeyi ba Wato Nazia Yar Shekara Bakwai kacal a duniya.

Washe Gari Nazia a School tayi submitting din assignment dinta Bayan Break Malam ya Fara marking Assignment har yazo Kan na Nazia Hashim da karfi yace what? Nan take ya mike tare da shigewa office din Principal ya nuna Mata irin zagi da cin mutuncin da aka Yi Masa a matsayin Assignment,Pc tace Nazia baza ta iya rubuta Haka ba wannan aikin na Babbar mace ne Amma sa yaro ya Kira min Nazia.
Yaro aka tura Dan jss2 ya Nemo Nazia,Pc ta kalli Nazia tace waye ya Miki Assignment jiya? Nazia tace Aunty na ce Nabeela.

Okay to ga takardar an dakatar Dake da zuwa makarantar Nan har na kwana Uku sai kinzo da yayarki wacce tayi wannan aikin tare da takardar ban Hakuri Kuma yayarki ta jawo miki sai na Zane ki yau ya za ayi taci mutuncin malami,ko Baku da Tarbiyya ne? Pc ta kwalawa Headgirl Kira tace kawo min bulala,wata katuwar Bulala aka kawo,Pc ba Tausayi ta Zane Nazia tayi Mata rudu rudu da jiki sannan ta kore ta gida,Da Kuka Nazia ta shiga gidansu,Nabeela ta f

Washe da safe Alex Yana cikin Yana cikin garin Kaduna Yana tafiya Yana kallon yanda Mutane suke gudanar da Rayuwarsu abin Yana birge shi matuka,Yana ganin komai kudi Ne har yau ya Rasa me akeyi da su Bai Gane ba,Yana zauna kusa da katon Shagon Da ake siyar da kayan gyaran Machine da Keke,Wani matashi ne a ciki Wanda bazai wuce 30yrs ba zai Kai mate din Alex,a kofar shagon Alex ya tsaya Yana ta kallon yanda ake Mika kudade ana karbar Abu,Kasa Jurewa Yayi ya shiga shagon,Matashin Baki ne kyakyawa Dan gayu da shi.

Alex yayiwa magana Malam me za a baka? Murmushi Alex ya saki kyawawan hakoransa Suka sake bayyana farare kanana,Matashin ya tambaya Dan Allah Mene amfanin kudi Kuma me akeyi da su? Matashin yayi tunanin bashi da hankali Amma sai yayi Masa kwarjini ya tsaya tare da Zaro kudade ya shiga nuna Masa yadda suke da Kuma fada Masa duk abinda akeyi da kudi,Mene kudi,ya koya Masa yanda ake kashe su,da Kuma aikin da akeyi Ana samunsu,Farin ciki ya Kama Alex yau ya gane komai akan kudi,Godiya ya dinga zubawa Matashin sannan Matashin yayi Dariya tare da tambaya ya sunanka? Alex ya furta,Matashin yace Ni Kuma Sultan, daga Nan Alex yayi tafiyarsa Bai tsaya ko Ina ba sai kofar gidan su Nabeela,Nazia ya iske a waje tana wasanta an hade ta cikin kana Nan Kaya,Kallonsa tayi ya ganta Kyakyawa me Kama da Nabeela,Gidan ya turata yace Kira min Nabeela.

Da Gudu Nazia ta shige gida lokacin Nabeela tana tsakar gida tana kankare farcenta Nazia ta fada jikinta tace wani yace kije, ba musu sabo da tasan tana da mutane maza masu sallama da ita Haka tasa Hijab dinta ruwan kasa ta fita kofar gida,Mamaki ya kashe ta ganin Alex sanye cikin rigar shadda sea blue,rigar ta wuce gwiwarsa kadan Amma gajeren Wando ne kawai a jikinsa sai rigar,Tasha wanki da guga,Cike da tsiwa ta kalle shi shekeke tare da Furta lafiya? Ya akayi ka Gane gidan mu? Idan ka tuna Pin dinka muje idan baka tuna ba a bar Mana kofar gida baka da amfani a wajena ta furta tana turo Dan bakinta Karami me dauke da jajayen lips dinta,Fuskarsa ba Rahma yace na tuna pin din gaba Daya jiya na dage sai da na tuna,sai lokacin Nabeela ta fadada fara'arta tace to ..to..Bari nazo mu tafi.

Gida ta koma da sauri Kamar zata fadi kasa ta sako wani brown Hijab me Hannu yasha wanki da guga,Nabeela jerawa tayi da shi suna tafiya kowa ya kalle su sai sun birge shi,sun dace da juna,da rigarsa ta shadda ba wando sai Gajere a ciki,ga tafkekiyar Sarkar cross a wuyansa tana sheki da gani me tsada ce,Napep ta tare musu,Rasa ta yanda zai Shiga yayi,Duwawunsa ya Fara turawa ciki,Dariya ta kwacewa Nabeela,Juyawa yayi sannan ya duka ta kasa ya tsuguna sannan da Rarrafe ya shiga ciki tare da zama abinsa ya wani babbake waje,Shigowa Nabeela tayi Itama tare da Sa hannunta tana kokarin janye Hannunsa Daya tare waje,da Sauri ya janye abinsa tare da boye Hannunsa a jikinsa Yana gasa Mata uwar Harara Bai so ta taba Masa jiki,Allah baka Hakuri Nabeela ta Furta tare da Dan samun waje a napep ta zauna gefe can sannan Suka tafi.

Bank Suka karasa ta sallami me Napep a gabansa ta bashi kudi Yana kallo ya sake Gane amfanin kudin Yana ta mamaki,Kallonsa tayi Ido cikin Ido kafin tayi magana ya zaro Atm card ya Mika mata,Karba tayi tare da tambayarsa to yanzu idan An ciro kudin me zaka siya? Gida da mota Zan siya da kayan sawa etc, Atm card ta saka a machine sannan tace fada min pin,Nan take ya Karanto Mata numbers guda Hudu,tana sawa ya bude,Balance ta Fara dubawa,Kanta ne ya kulle tsoro ya Kama ta ganin Miliyoyin kudi ba na Wasa ba a accnt din, To yanzu wayar Hannunka da ita kake transfer? Kai ya daga mata Wai ae,to Yan gidanku Wai basa kiranka? Nan ma ae ya furta,card din ta zare tace muje a Fara samun gidan da zaka siya sai mu shirya komai. Hannaye ya harde a kirjinsa sannan Kamar me Ciwon Baki ya furta Ni a yau nake so na siya gida.

Baki Bude Nabeela tace Lallai kana min yanga kana min yanda kaga dama,ji ba Ni Nabeela kake yiwa Yanga Haka,Sake Hardewa yayi tare da turo Yan jajayen lips dinsa gaba yayi tare da dauke kansa Yana tsaki,Murmushi Nabeela ta saki tare da tsayawa tana faman kallon irin baiwar kyau da cikar zati da Allah yayi masa,sai da ya Gama yangarsa sannan yace muje wurin Abban naki Yau Zan siya gida Ni,Ina so na dawo mutum kina Bata min lokacin,Dariya Nabeela ta shiga Yi tana mamaki Yana Mutum dashi Amma Yana tunanin Zama mutum to wanne mutum zai dawo Kuma.
Muryarsa taji kasa kasa yanda yake magana bazai taba daga murya ba sai dai idan baza kaji me yace ba to ka hakura,yace Idan baza ki taimakamin ba ki barshi ya Furta Yana tsaki,Nabeela Tsakin nasa taji kawai,Kunnenta ta kawo saitin Bakinsa me kace? Da sauri ya matsa gefe Yana kallonta tare da Furta Wai me yasa ku mutane kuke haka? To Ni ba mutum bane ki daina zuwa kusa Dani.

Napep ya tare musu Suka shiga zuwa gidan Su Nabeela,a kofar gida Suka Iske shi Yana saanarsa ta gyaran takalma sannan Yana siyarwa da Nabeela kayan miyar ta,sarkin yawo da maza daga Ina Abban Nabeela ya Furta,haba Abba wannan arziki ne ya kwansa Mana kofa budewa kawai zaka Yi ka karba,bangane ba? ,Gida to yake nema zai siya sabo me kyau,To to ai sai a bincika Masa cewar Abban Nabeela,akwai wani Doctor da ya gina gida me kyau rannan ya tumbume mu idan an samu me siya zai siyar Masa shi Abuja zai koma da Zama baya bukatar gida a Kaduna.

Dan Allah Abba a Nemo Masa yau Muke so a gaba komai akwai kudi kasa,Jin ance akwai kudi Nan take Abba ya dakko wata kwakwurarar wayarsa ya shiga Kiran numbers din mutane Yana tambayar gida,Har Allah yasa akace ai gidan Doctor Yana Nan ba a samu me siya ba,a ranar Abba ya Gama Magana da Doctor tare da ciniki, Doctor yace Idan an siya million Goma Sha biyar ya siyar sabo da sabon gida ne sama da kasa me shegen kyau madaidaici,har garden ne a gidan ko Ina yasha tiles da Interlock,cikin gidan a kasa Dauke yake da Katon palo da 2 bed rooms da toilet ko wanne sai Bangaren Dining kusa da kitchen manne da store,Sama ma Haka take abinda ke kasa Haka akwai a sama gidan yayi kyau komai Golden and milk a wallpaper Dake gidan,Haka katon gate din gidan ma,Parking space kuwa motoci biyar zuwa shida zasu iya Zama a ciki,Alex Kuwa mayen Yana zaune a kofar gidan su Nabeela aka Gama ciki yace a Fara nuna Masa ya gani.

Abba yace ba damuwa Muje gidan a nuna maka,Nabeela ma Fitowa Suka Yi tare da Shiga Napep can Karshen layinsu ne a Nan Unguwar Rimi gidan yake,Baki Alex ya tabe tare da Furta ban son unguwar Nan tayi min kauye da yawa,Kai yaro uban me zaka Yi da gidan Haka da shegen fadin Rai Kai ba Aure ba gidan Gwauro ne fa,Allah ya kiyaye ma ba Mata zaka dinga kawowa ba gidan,to Dan Ubanki Nabeela wlh karki sake na ganki a gidan Tuzuru,Dariya Nabeela tayi tace to Abba.
Suna Haka har suka karasa kofar gidan,tun daga nesa kasan gidan ya Gama Haduwa matuka kaf kusa Babu me kyan gidan,Amma Alex sai cewa yayi zanyi manage Yana tabe Baki.

Cikin gidan Doctor ya shigar Dasu Suka Sha kallo ko Ina,Nan take yace Zan maka transfer,Mamaki ya Kama Nabeela ita dai tasan wayarsa ba layi to a Ina ya samo layin ya saka,kallon ta yayi Suka hada Ido,ya gane mamaki takeyi,Ba zato ya Dan kwada Mata wayar a goshi tare da yin Murmushinsa me tsada kadan ya furta dama da SIM card din a tsohuwar rigata jiya na saka ki daina zaro min mayun idonki.

Caraf Abba yace 'yata son kowa kin Wanda ya Rasa zaka ce mayun Ido gare ta Kai ai Kaine me mayun idanuwa Kai da kake tsohon gwauro,Doctor dariya yayi Yana jinsu,Shi da baya Sallah ma har ya Isa ya kushe min yarinya ta,Ko kulasu Alex baiyi ba suna kallonsa ya karbi accnt number yayiwa Doctor transfer,Nan take bank Suka kirashi a waya Suka tabbatar shine sannan kudin Suka Shiga accnt din Doctor sabo da Babban accnt ne da shi ba irin na Yara bane ,La',ada aka fitarwa Su Abba,Sannan Alex ya kalli Nabeela yace nawa kike so na Baki? Ko nawa ne ki fada,a hankali Abba yace kice talatin,Ashe Abba million talatin yake nufi Nabeela ta fada Amma Bata Gane ba sai tace dubu talatin,Nan take Ya tura mata Mata dubu dari kyauta,sai Murna takeyi tace Abba sai sabuwar Amarya Nan da sati Yar Makkah ta tare a gidanka,farin ciki ya Kama Abba yace Na gode me hankali,ban tabbatar kina da hankali ba sai yau,Nabeela kin San me kike yi,kinfi maza tunani me kyau,Ana cewa maza akwai hankali Ashe duk karya ne Mata ne masu hankalin Ashe ba'a Gane ba to Alhmdllh Allah ya ganar Dani gaskiya,Dariya Doctor da Nabeela Suka dinga Yi har suka karbi takardun gida tare da shedu da komai sannan suka tafi gida.

Suna cikin tafiya Alex yace zai sauka,me Napep ya tsaya ya sauke shi a Hanya yayi tafiyarsa ko sallama Babu,Nabeela tace yake ya karata tunda mun samu rabonmu, Washe Gari da Sassafe Nabeela bayan ta Kai Nazia school ta dawo ta ci Karo da Kawarta wacce Suka Yi secondary school tare Farha Yar gidan Chairman ce na local government me ci a yanzu,Farha Baki ta rike tare da furta oh Nabeela dama Ana ganinki? Kin jefar Dani Kamar ba Kawaye ba,Murmushi Nabeela ta saki tare da furta to ya za ayi lamari ne na duniya,ga duniya yanda ta koma Bata tashi lalacewa ba sai da aka Zo kanmu,Dariya Farha tayi tare da furta har yau dai Nabeela kike sak ba canji,to ya school Kinci gaba kuwa? Ni yanzu a ABU zaira nake karatu Ina level 3,Lallai Allah ya taimaka,Ni naji dadin ganin ki ma Farha,Dan Allah tunda ku masu kudi ne yanzu ko Zaki taimaka ki sa Ummanki ta dauke Ni aikin shara da wanke wanke ko girki Zan na zuwa kullum sai ta dinga biya na.

Mamaki ya Kama Farha tace Haba Nabeela Allah ya kiyaye ki Zama Yar aikinmu ai kinfi karfin Haka kina kawa ta,ai talaucin naku Bai Kai Haka ba,Baki Rasa sutura ba,ga ci da Sha ai kin wuce Nan,idan kudin school ne ko wani Abu Zan sa Daddy ya taimaka Miki da shi Dan Allah ki samu ki Fara makaranta ki koma school kici gaba,ba girmanki bane Nabeela ya kike Abu kamar namiji,ke komai Neman kudi,Hmm kice kawai baza ki bani aikin ba ba sai Kinci mutunci na ba,Kuma ke kin San Halina ba a taimaka min sai dai nayi aiki a biyani nasan gumi na ne idan Mutum yayi Iskanci naci Ubansa la'ada waje da ciki,idan har kina so na kin dauke Ni kawa to a dauke Ni aiki a gidanku Kuma babu ruwanki da karatuna bana so bazan Yi ba Dole ne karatun Boko ko sai da shi za ayi kudi etc.

Ba shiri Farha tace kizo to Zan fada mata zata Baki indai aiki ne sai kiyi ta yi,yanzu nasan ke kawa ce ta kirki zanzo da yamma Inshaallah cewar Nabeela, Haka kuwa da yamma Bayan ta Kai Nazia kanwarta Islamiyya gidan Kawarta ta wuce Farha,Hannu bibiyu aka karbe ta sabo da Babu Wanda Bai San Nabeela ba a gidan har yaran gida,ba bakuwa bace,Bayan sun gaisa Maman Farha tace Nabeela bakya Hajiya da neman kudi Farha ta sanar min sai ki mike Zan kawo Miki wankin kayan Yara ki wanke ki goge musu,Amma kafin Nan na Bude Restaurant katon gaske Farha Restaurant sunansa 24hrs ne idan kina so na dauke ki aiki a ciki tunda Naga kin iya girke girke iri iri sai ki shiga cikin masu girki watarana Kuma har abincin ma Zaki na bayarwa, Zaki je sau Hudu a sati,Fri, Saturday and Sunday Baki da aiki akwai me karbarki kin Amince? Duk wata Zan dinga biyanki dubu goma ya Kika gani? Ba damuwa zanyi na gode ok to Jibi ki dawo ki karbi Uniform Baki kala hudu ne har takalma Banda kazanta pls.
Nabeela wankinta ta karba tayi ta Gama sannan wurin Magrib Hajiya ta sallame ta tare da Bata dubu biyu kudin wanki Dana Napep ta wuce abinta.

Washe Gari da Sassafe ta bar gida ko karyawa Nabeela Bata tsaya tayi ba sabo da Neman kudi direct gidan Hajiya Talan Me Kidan kwarya ta wuce,Hajiya Talan tana dama Koko taji Sallamar Nabeela,Guda tayi Ayyiri yiriiiiii Nabeela kece wata sabon gani,yaushe rabon da kizo a fita Wasa Dake,Ana ta cin arziki Babu ke, harka ta Bude kullum a gayyatar mu ake gidan biki,jiya Nan da kike gani Nabeela matar Dan Majalisa ce ta Kira biki mun Sha ruwan Naira harda turamen atampofi Yan gaske,Baki Nabeela ta washe tare da Furta Kai na cuci kaina wlh kwana biyu Neman wasu kudi ne ya rike Ni Amma yanzu Alhmdllh na dawo da Ni za ayi harkar Nan sosai.

Ko kefa ai muma zaku Fi samun kudi idan da ke ana ganin jar fatar Nan Taki ga kyau ga kyan sura da diri ai sai ruwan Nairori Heeeeeeee Hajiya Talan ta Furta tana me sakin dariya da shewa cikin salo na Yan Bariki,karfe Hudu Nabeela ki fito yau zamuje biki gidan wani Kansila angama Hajjaju sai nazo Nabeela ta Furta tare da barin gidan cikin mugun sauri.
Bayan wasu mintuna masu yawa gab Nabeel take da Shiga gidansu taji wani mahaukacin horn a bayanta,da sauri ta juya tana kallon waye Haka zai fasa Mata dodon kunnen,parking motar taga anyi wasu kyawawan fararen kafafu sun Fara Fitowa sai mutum ya fito gaba Daya,Baki ta bude da sauri Ganin Alex yasha uban shadda me mugun tsada Fara dinkin ya wuce gwiwarsa kasan,samansa yasha Sarkar cross sai Kuna kafafu ba wando a ciki sai tsuran Riga Da boxers.
Kyau ya Sha shi matuka matsalar kawai Rashin dogon wando.

Motar Nabeela ta sake Kallo muguwar Hadaddiyar Benz me shegen tsada Ruwan toka,gashin kansa ta kalla yasha aski me shegen kyau anyi Masa style kamar Bature,sajensa da gemunsa Yan chakwas ta karewa kallo suna ta shining,Hancinsa dogo me kyau tare da lips dinsa jajaye ta kafe da idanu yayin da hantar cikinta ke kadawa,ya Mata kyau ga kwar jini,wani azababben kamshi ne ke fita daga jikinsa,Nabeela a ranta tace Kai Ashe kyawunsa ya zarce hankali ga Naira kudin Dake Accnt dinsa bazan iya lissafasu ba,sunfi karfin Ilimina ai tuna Haka ke da wuya Nabeela ta zube a kasa ta durkusa a gaban Alex tace Sannu Honorable barka da Asuba ya shugaban samari kyawawa na Nigeria,Ya Diamond prince,Golden prince sannu da zuwa,Dariya ta bashi da kyar ya danne tare da Jan tsaki tashi Ya mayyar kudi,Murmushi tayi tare da Mikewa tsaye tace da Sallama Zan maka na manta fa Ashe Kai ba musulmi bane...kafin ta rufe Baki yace Yeah...Baki ta bude zata Yi magana yace shiiiiii Ni bana son surutu idan kin ganni ki daina min surutu indai ba Dole Abu Important ya Kama ba.
Ku Biladama Kun fiye magana da yawa ahhhsh....shi yasa bana son muamula a Cikinku,Yar aiki Zaki Samo min wacce zata na gyara min gida tayi min Abinci,Tun kafin ya Karasa magana Nabeela kamar zata karya wuyanta ta juyo da sauri tare da washe Baki tace gani nice Yar aikin naka nawa Zaka dinga biya na kasan aiki a Gidan Gwauro tsada gare shi sabo da mace a cikin Hadari take Kar watarana Gwauro ya afka mata.

Ke Kika San wani Gwauro da afkawarsa aiki ne idan Zaki Yi Dubu talatin duk wata,Da sauri Nabeela tace zanyi wallahi,irin wannan kudi Yan aikin mu ai dubu biyu dubu uku ake biyansu a wata,Baki Alex ya bude yace okay to ke zan biyaki dubu biyar ai ban San Haka ake biya ba,Murna ce ta komawa Nabeela ciki tace Kai ba fa a cikin mutane na birni nake nufi ba a can kauye,Nan Ma Alex yace Okay to Na fasa kije Aboki na zai Nemo min wata,no Dan Allah zanyi please,Okay dubu goma Zan Baki ba damuwa na Amince to muje yanzu ki Fara,Sai Gobe Zan Fara,to shike Nan na fasa daukanki,No Dan Allah zanje tsaya na sanarwa Abba sai na fito mu tafi,na baki 10mnt.

Gidansu Nabeela ta fada Tana kwalawa Abba Kira,da sauri ya fito tace Abba yau sai dai ka dakko Nazia daga makaranta Ni na Samu aikin Yi kullum da Sassafe zanje sai yamma likis Zan dawo duk wata dubu goma,Murna ta Kama Abba yace kice Ni Aure na Shar Muna da abin rike su,kwarai Abba kaje a Gama komai na Aure,a Ina Kika samu aikin? Gidan Gwauro Abba me kudi Wanda ya siyi gidan Nan.

Fuska Abba ya Bata yace ban Amince ba Nabeela kina mace baliga kusan Shekara ashirin ki dinga zuwa aiki gidan Gwauro Kuma a gwauron ma Arne baya Sallah Haka kawai ya lalata Miki rayuwa,Haba Abba Inshaallah ba abinda zai faru Addua akeyi Kuma kudin Nan Kai Zan nemowa Abba,kana gani baka da sana'a kullum a wahala muke kaga idan na Fara aiki tunda kana so nayi karatu ko kaina ai Zan dauki nauyi nayi karatu,Hmmm Ai ko ba karatu ba Nabeela Aure na rike min Iyali zakiyi,to ka gani ba Abba kawai kayi min Addua,shi kanshi Alex din Nan ba mutum bane Bai San ma komai da mutane sukeyi ba bare ya lalata ni,Baki Abba ya bude yace zaku ci ubanku ya mutum da shi sak kice ba mutum bane to Aljani ne Ni zaku rainawa Hankali,Abba wallahi yace ba mutum bane shi Kuma na yarda,da Allah tafi ki bani waje Allah ya tsare ki rike mutuncinki wlh wani Abu ya faru sai na Tsine Miki Nabeela ki bi a sannu ki rage Neman kudin Nan Kamar zakiyi sata.
Dariya Nabeela tayi ta gyara Hijab dinta tayi waje abinta sai wajen Alex Gwauro Dake jikin mota,Gaba ta Bude ta Shiga shima ya Shiga Suka tafi Babu Wanda yayi wa Dan Uwansa magana.








AsmaBaffa.
[5/10, 3:21 PM] Sis Asma: 🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠





FREE PAGE







Ga masu bukatar siyen complt Novels Dina Dari Uku 300 ne kowanne

RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDU'AR KAWA


Masu bukatar shiga Group din GIDAN GWAURO Naira dari biyu 200 ne.



ACCOUNT NUMBER
0175487861
Asmau Garba Muhammad
GTBank.


Masu yin Vtu,Transfer,ko tura katin MTN ta WhatsApp ga Number ta
08033933642.

YAN NIGER ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39.









Please Login or Register in order to submit comment