Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

me layi layin Baki da wandonta yayi kyau,Nabeela ma Irinsu ne nata me gajeren Wando,Wani English Novel Asad ya Rike da Hannu Daya Yana karantawa,Nabeela tana kwance rabinta a kirjinsa Hannunsa daya Yana shafa gashin kanta a hankali Wasa take Yi da abin jikin Rigarsa, saman Wuyanta ya maida Hannunsa tare da rungumo ta,Cike da Shagwaba tace Muyi Bacci ni gaskiya,Murmushi ya saki tare da furta tunaninki hankalina Yana Kan Novel din Nan ne? Gaba Daya kin Hana Ni komai ban san Mene ma a ciki ba kin Gama dauke hankalina My wife,Jikinki Dadi ne da shi ya furta tare da kwantar da kansa a saman gashin kanta,cikin lankwashe murya Nabeela tace gobe da wuri fa zamu tafi wajen me magani inji Abba Wai wani kauye ne kaga gwara muyi bacci,Asad yace Allah yasa a Dace Kuma Allah yasa ba masu shirka bane,Ameen Nabeela ta furta suna Hira kasa kasa har bacci ya kwashe su.

Washe Gari da wuri ta hada musu Breakfast lafiyayye Bayan sunci gidan suka gyara tare da Yan aiki sannan Nabeela ta shirya kanta cikin Arabian Gown Blue me kyan gaske,Asad Kam cikin Shadda fara ta shirya shi suna ta murna Allah yasa ya warke,Nabeela ce tayi Driving Zuwa Gidan Abba,Abba Yana fitowa cikin wani yard me kyau Brown ka rantse wani Babban Alhaji ne yayi kiba yayi kyau,Nabeela bani wajen na tuka ke koma baya kusa da Asad,Haka kuwa akayi ta koma Baya Abba yaja mota suka wuce kauyen.
Sai da suka Yi tafiya ta Hour guda da rabi sannan suka Isa Gidan me magani,Mutane suka samu da yawan gaske Malam Yana ta ganinsu Daya Bayan Daya,Abba ne ya Shiga layin su Nabeela suna mota har Layi yazo kansu aka Shiga da Asad,Abba ne ya karantawa Malam komai har zuwa rashin lafiyar Asad,Bayan Malam ya Gama ji ya gyara Nadin rawaninsa da katon carbinsa Yana magana Yana ja,Ganin Kalar su Nabeela masu kudi sai Malam yace Lallai aikinsa Babba ne, bakaken Aljanune suka Shiga jikinsa idan Kuma aka sake ba a dauki mataki ba to zasu shafi Matarsa ma,Nabeela Bata San sanda tace kaji karya,Malam ya daka Mata tsawa keee....ya hakuri Malam da zuciyata nake ce min tayi bazai warke ba mu bar wajenka shi yasa Ni Kuma na fada Mata Karya take Yi,Oho yanzu naji Magana Malam zai Fara magana kenan duf sai aka dauke nepa yace mutanen Nan Basu da mutunci kullum basa bamu wuta suna kawo ta sai su dauke,Nabeela tace Malam gashi kana duba mutane ka gano komai nasu ai ya kamata ace kasan Sanda za a dauke Nepa a kawo ta,da sai ka fada Mana kace yanzu za a dauke Nepa,Malam ya kwalalowa Nabeela Ido,Abba ya bige ta kadan,Malam yace kudi dubu Hamsim za a Baku tubutu zai Sha ya shafe jikinsa har na tsawon Kwana Uku da ikon Allah zaku ga ya mike,Nabeela tace Malam zamu baka dubu Ashirin idan ya warke sai muzo wallahi ko nawa ne zamu baka,Amma bazai yuwu mu zuba adashin da ba dauka ba,Malam ya nuna Nabeela tare da cewa ke dai baki gaji arziki ba,inda arziki yake Baki biyo ta Hanyarsa ba,da a ce danke Zan ba da Magani bazan Baku ba,Asad yace Malam kawo account Nan Malam ya bayar Asad yayi Masa transfer cash dubu Hamsim suka karbi Dan rubutu Dan kadan a kwalaba,Nabeela ta daga kwalabar tace a Kan Dan wannan har anci dubu Hamsim Abu kamar ma Fitsarin jaka,Malam ya fusata yace sai na Mai dake Kwandala idan kikayi Wasa,Nabeela tace yo ba sai a siyi Alawa da Ni ba Yara su shanye,Bayan sun Fita Abba ya lullube ta da fada har Suka je Gida.
Magani aka Fara aikatawa har kwana Uku Yanda Malam yace Amma Shuru Asad ko alamar warkewa Bai ji ba.

Ba a Dade ba Abba ya dauko su Kano wani kauye Nan ma aka ci Kudinsu a banza,Wasa Wasa sai da Suka gaji da zuwa Wajen masu magani iri iri baza su Irgu ba kudi kawai suke kashewa a banza,karshe Nabeela tasa Suka koma na Asibiti aka Yi duk wasu gwaje gwaje ba a ga komai ba,Nabeela wahala ta Mata yawa ga zuwa school ga kula da mijinta ga Kuma Taya shi wasu ayyuka na Office Yana koya Mata watarana ma da shi suke zuwa Office abinsu shar,Kamar Kullum Nabeela da wuri tana kitchen tana Hada musu Karin safe ta tuna Asad time din tashinsa yayi da sauri ta wanke Hannunta tare da komawa Bedroom dinsa ai kuwa ta Iske ya farka,Kallonta yayi tare da sakin Murmushi Itama ta sakar Masa tare da furta Barka da Asuba, Toilet ta tallafa ta kaishi sannan ta kulle Masa kofa tare da kawo Masa duk abinda zai bukata kusa da shi,Kayansa ta cire Masa sannan tace Bari na koma kitchen kafin kayi wanka,Cike da so tare da Tausayi ya kalli Nabeela ya furta na gode,Hararar Wasa ta gasa masa Akan me zai Mata godiya,Kitchen ta koma taci gaba da aikinta,Bayan ya Gama ta koma ta Masa duk abinda ya Dace sannan ta jingina shi jikin Bed ya Dan zauna,Abinci ta kawo musu tana bashi a Baki Yana ci ita ma tana ci har suka koshi.

Wanka tayi ta shirya Har Office dinsa ta kaishi ta wuce School,2pm tayi wa Asad take Away na lafiyayyen fried rice da kaza ga Hadin Salat da lemuka,a Office dinsa Suka ci tare da gabatar da Sallah ta koma school tana Gama lecture ta koma ta dauki Asad Suka wuce gida.
Nabeela ta koma Sam Bata da Hutu ko kadan Nauyi ya hau kanta da yawa dan ma Jaruma ce.

Sunday kuwa ba Aiki gidan wani me magani Suka tafi a can Takai Kano state,tun safe suke Kan layi sai Yamma suka samu damar ganin Malamin,Bayan sunyi wa malam Bayani kamar gaske yace a bashi Dubu biyar,Nan take Suka bashi ya Basu wani garin magani za a Sha kullum a cikin fura ko Kunu na tsawon sati Daya,Nabeela sai Murna takeyi da Alama ta yarda maganin zaiyi aiki,Ai kuwa Har Asad ya shanye Shuru Bai warke ba,Nabeela ta saki kuka tana zagin Masu magani,Tana kallon Asad tace macucin Malami ne ka duba duk katuwar alkyabbar Daya sha Ashe maganin baya aiki harda wani sa Alkyabba wacce ko guga Baku,Asad Yana dariya yace Ni dama Haushinsa nake ji Baki ga yanda yake ta kalle min ke ba,kwalelensa Dan Ubansa me zanci da shi Nabeela ta furta cike da takaicin maganin Malam baiyi ba.

Safiyya kwance take a palon Kanwarta murja tana kallo a wata akwakwun tv Yar karama Sharp irin tsuhuwar Yayi,Murja ta tabe Baki tare da Furta ya kamata gaskiya kiyi aure yo Sabo da Allah kya Zo ki tare kina kwana a nan,Safiyya tace ki godewa Allah ma Murja har za a Zo gidanki a zauna,Tsaki murja ta ja suna ta yiwa juna Habaici Mijin Murja ya shugo Yana zare idanuwa,Akwatinsa ya dakko katuwarl, Murja tace Ina zaka tafi Kuma? Yace tafiya ce ta taso min zuwa Lagos akwai wani aiki da zanyi a can Zan samu kudi kiyi Addua kawai,Murja tace Allah ya tsare,dubu Biyar ya bawa Murja yace Zan yo Miki aike idan naje can,Okay Allah kaika lafiya.
Tunda Mijin Murja ya bar gida ba a sake Jin labarinsa Har ya kwashe wata Uku Murja lokacin Basu da Abinci na ci sai dai ta Shiga makwafta tayi Maula a Bata ,Ranar Juma'a 11am Murja sun Fara bacci Ita da Safiyya katsam Suka ji Ana buga musu gida,Murja tana Bude kofa taga Mijinta Shehu tare da Wata mace matashiya,Baki Murja ta tabe tare da tambayar wacece wannan Kuma? Kafin ta rufe Baki Shehu Yace sabuwar Amarya ta ce,a lagos Muka Hadu na musuluntar da ita shine na taimaka Mata na Aure ta sabo da Haka ki kwashe kayan ki na wancen dakin zata sa kayanta a ciki,Murja kamewa tayi a tsaye.

Safiyya ma abin ya daketa,ba abinda suka Isa Yi a Daren suka kwashe kujerun Murja kaf tare da maida su Soron gidan aka jibge su tare da lulluba musu Ledoji sabo da Kar suyi Dirty.
Amarya tana wani yanga ta wuce Shehu ya taimaka Mata su Murja suna kallo suka sa katuwar katifa Tasha bedsheet da sauran tarkacenta,Murja tace Kan uban Nan wallahi da Gaske yake Yi,Safiyya tace kema tsafinki ya karye Murja,Murja gashinta ta Bude ta zaro layu guda biyu a cikin gashinta,ta Bude damatsanta ta cire wani Guru na tsafi,Hips dinta ta Bude ta zare wata jigida ta boka,Safiyya tana dariya tace ya Kika cire? Basu da amfani aikinsu ya Kare,ai tunda Kika ga Shehu ya Karo Amarya to Basa aiki sun tsaya,da yatsa ta nuna layun tana zaginsu Dan Ubanku Ni zaku yiwa Haka,Kuna gani tawa ta Kare yau Rana ta baci sai dai yanzu nayi Biyayya kawai Gudun Kar ya kore mu daga gidan mu koma kauye

Tunda Amarya ta shigo ta Fara cin uban Murja Amma Murja bata iya ramawa Dan Kar mijinta ya sake ta,Amarya Zaleeha ce tace Shehu ya Bata kudi zata je saloon,A gaban Murja ya zaro dubu Uku ya bata sannan ya kalli Murja tare da tambaya ko Kar a Bata? Da sauri Murja tace na yafe a Bata Mana,Murmushi Shehu yayi yace Good,Haka ya dinga dannewa Murja hakki suna magana Kuma yaci Ubansu yace zai sake ta,Murja duk ta rame tayi Baki wahala take sha,miji yayi mata itama Amarya ma tayi musu cin mutunci idan Suka maida martani ta dauki tabarya tace zata kashe su.

Yau fada ne ya Hauke tsakanin Murja da Zaleeha suna ta zagin juna,Zaleeha tace shegiya Yar talakawa lokacin da aka Kai lefen aurenki ai ance Babanki tsabar lalacewa a shago saman Dan Benchi aka karbi kayan,Murja tace na fiki dai ke ranar Daurin aure fa Ubanki da Gajeren wando da Singlet ya karbi Sadakinki,Safiyya tace Kuma Uwarki Kosai take soyawa a gindin Bishiyar Giginya,Kuma Bishiyar ginginyar ce ta Fado Mata ta mutu.
Kuka Amarya Zaleeha ta saki,Shehu ne ya shigo da sharbebiyar Bulalarsa da Shirin Zane Murja da Safiyya suna ganinsa Suka fada daki tare da Sa key,Shehu yace zaku fito ne sai na farfasa muku jiki matsiyata.

Abba ne ya samu wani Malami Wanda ance aikinsa bada maganin cututtuka,Koda suka je Nan ma ba a Dace ba,Nabeela tace mun hakura zamu koma Addua da kanmu Allah ya kawo Mana maganin cutar,Haka Nabeela taci gaba da dawainiya da Asad har suka kwashe wata Biyar Asad ba labarin warkewa,Hakura sukayi kawai suka dage da Addua,Nabeela tana kasan center carpet Asad Kuma Yana kujera a kwance tana cike wasu Takardu na Office tana Mikawa Asad Yana signing,Tausayin mijinta yasa Nabeela har Bata San sanda Kuka ya kwace Mata ba,shesheka kawai Asad yaji tanayi,Hankalinsa ba karamin tashi yayi tunaninsa ko Nabeela gajiya tayi da wahala da shi,Cikin kasalalliyar muryarsa ya Kira sunanta a hankali,Fuskarta gaje gaje da Hawaye ta dago tare da zuba Masa Idanunta Wanda suka Yi ja sabo da kuka,a hankali ya furta come,Gefensa ta zauna,ya daga Hannunsa dakyar ya Dan kwantar da kanta saman Kirjinsa Yana shafa Mata gadon baya da kyar yake iya hakan,magana ya Fara cikin lafazi me taushi da sanyaya zuciya,kiyi Hakuri Nabeela na fiki damuwa da wahalar da kike Sha,ban San da me Zan saka miki ba, da wata ce wlh da tuni ta guje Ni,yatsa Nabeela ta daura a saman lips dinsa jajaye masu taushi sannan tace Ni ba wannan bane ko zamu dawwama a Haka bazan gajiya da maka ko Mene ba,Kawai Ina tausaya maka ne shine Abinda ya dameni,Murmushin karfin Hali yayi tare da furta na gode Allah ya biyaki a gidan Aljanna Allah ya Miki Albarka My wife, Ameen na ta amsa tare da cewa kaima Allah baka lafiya yace Ameen.

Idan na warke me Zaki Fara bani sabo da farin ciki? Asad ya tambayi Nabeela,Nabeela tayi fari da Ido me Jan hankalin me gida sannan ta rufe Fuskarta da tafukan Hannayenta tace Bental Uba Mana,Dariya sukayi yace Nima tunanina kenan kullum da shi nake kwana nake tashi,Hannnunsa ta kamo tare da Sa yatsan tsakiyarsa a bakinta tana tsotsa suna Hira kasa kasa yace
Wai Nazia baza ta dawo bane? Asad ya tambaya,Nabeela tace Abba ne yace ta zauna a can sabo da Kar nauyi yayi min yawa,Gaskiya ban yarda ba a dawo min da Kanwata yau wata nawa ko zuwa Nan Hutu Abba ya Hanata,zanje na dauko ta ne sai na Samu time,Okay Magrib tayi ki min Alwala cewar Asad,Okay Nabeela ta Furta tare da Mikewa ta Shiga Toilet.

Washe Gari da yamma Maryam me Awara ta kawowa Nabeela ziyara,tare da duba Asad duk kuwa da cewa Maryam tana yawan zuwa duba Asad sabo da Kawarta,Maryam tana Kora ruwan Lemo a kujera me zaman mutum Daya,Asad Yana 3seater Nabeela ma tana gefen Kafafunsa a zaune,Maryam tace su Nabeela manyan Mata,Iskanci naki ya motsa Kuma? Maryam tace hmm ai kin Zama Babbar Hajiya ne kin ganki kuwa Nabeela wlh kamar Yar India Ana ganinki an San ba Karya Asad ya iya kiwo,Asad sai da ya Dan kalli Maryam Jin surutunta itama irin Nabeelan tasa ce,Nabeela tace ki daure kiyi auren Nan Maryam ko Kya huta da Awara,Babu Mashinshini ya zanyi Nabeela ko so kike na dauki speaker Ina magana a Gari Azo a aure Ni? Za ayi Reunion na makarantar Secondary dinmu ki tura dubu biyu za aje ayi zumunci,ban da time cewar Nabeela Maryam tace na biya kudi Ni zanje Hannun jari na zuba zanje ko na Samu Dan saurayi a wajen mu samu mu gangare daga ciki,Da ace Dan school ne bazan je ba Ina da dalilin zuwa,dariya Nabeela ta dingayi Har Asad, yanzu baza kije Dan Allah ba? A banza Zan dauki har dubu biyu jarin Awara ta na wani tafi Allah ya kiyaye ai Ni Jari na zuba Zan samu riba idan na Dace.

Bayan Maryam ta tafi Almajiri ne ya kwala Bara a gidan,Nabeela tana ji sama sama tana daga kitchen ta cewa me Gadi ya Bude Almajirin Nan ya shugo,Almajiri ya shugo dauke da robarsa da Allonsa a Hannu, Nabeela ta cika Masa kwano da Abinci tace yaro malaman naku basa koya Muku bada magani ne? Dan yaro yace mun san wasu dai kadai,To Ina bara a wajenka Dan Malam Dan Allah ko akwai wata Aya da zaka rubutawa miji na? Ya Dade da Lalura ko motsi baya iyawa,Almajiri yace ajiye min Abincin Bari Naje na dakko tawadar rubutu,Da Gudu yaron Ya fita Bai Dade ba sai gashi ya dawo da tawadarsa ta rubutu,Nan take ya zauna yayiwa Nabeela wani Dan rubutu kadan a Allo ya Bata yace ki wanke ki bashi ya Sha kawai,Nabeela dai har ga Allah karba tayi Amma tasan sunje wajen shahararun malamai nasu baiyi ba bare wani rubutun Dan yaro,Dubu Daya ta mikawa yaron da abincinsa ya tafi Yana murna.

Asad ta samu Yana kwance a kujera yana kallon sama Yana ta tunanin duniya,Nabeela ta fadada fara'arta ta zauna kusa dashi,Hannunsa ta riko tare da Furta Mene kake tunani My Heart? Ba komai ya furta tare da share kwallar data zubo Masa,Nabeela tace ga wani magani mu gwada,kansa ta dago yanda take bashi magani ta bashi rubutun
Yayi Bismillah ya shanye tas,Kwantar da shi tayi ta koma kitchen tana aikinta,Asad Yana kwance bacci ya kwashe shi me karfi Bai farka ba sai 5pm,wani mugun karfi yaji a jikinsa,Kamar Wasa yaji ya daga kafarsa daya,Ta biyun ma ya daga ai cikin wani mugun karfi Daya ji ya shige shi Bai San Sanda ya yunkura tare da Mikewa tsaye,Kafafunsa ya taka da karfi ya gwada tafiya farin ciki yasa ya dinga godewa Allah harda Sujjadar shukur,Nabeel ya Shiga kwalawa Kira ta fito da gudu daure da Towel a jikinta, jikinta duk kumfa sabo da wanka ta Fara,Mamaki ya kamata ganin Mijinta na tafiya,Ihu ta saki Tana tsalle da Murna,Hannaye ta daga sama tare da Furta Allahu Akbar sau uku,Cikin so da kauna Ya Rungume Nabeela tare da kankameta a jikinsa Suka dinga Tsalle tare suna Yee...Yee..Yee..suna zagawa,Nabeela ta Fara cashewa ba kida Asad ganin tana rawa ba kida ya Fara Mata kida da Bakinsa tana ta uban rawa.
Yace Yau sai Bental uba.
Sai da Suka Gama Murnarsu sannan suka dinga Kiran wayar Yan Uwa da abokan arziki suna fada musu Ana ta Taya su Murna.










AsmaBaffa.
[1/17, 12:20 AM] Sis Asma: 🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠



NA KUDI NE










81-85


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment