Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fada Dakin Asad tana shiga ta Iske Asad Yana ta sheka Amai ba ji ba gani Aman ya wuce a Kira shi da Aman zazzabi,sai ga wasu ganye Green suna Fitowa ta Bakinsa shima Yana Gama Aman tas ya zube a wajen baya ko motsi,Nabeela ta daga Hannu a sama ta saki Ihu....A gigice ta fada Kan Asad tana ihun kuka da Kiran Sunan Allah tana Dan Allah karka mutu ka barni wallahi Nima mutuwa zanyi Abba...Wayyo Abbaaaaa....na








Fans Naga Adduarku a gareni ta Allah ya bani lafiya.
Naji Dadi matuka Kuma NA GODE
NA GODE
NA GODE
ALLAH YA SAKA.



Banyi Group me Dadin Gidan Gwauro Gp ba,Ana magana Ana Sharhi Ana rakashewa Ana Shan BENTAL UBA a wannan group Allah ya bar zumunci.
😅😅😅😅







AsmaBaffa.
[1/13, 10:22 PM] Sis Asma: 🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠




NA KUDI NE

DAN ALLAH KAR A FITAR DA NOVEL DIN NAN ZUWA WASU GROUPS







71-75







Official







By
AsmaBaffa








Page naku ne

FATIMA
FATEE AHMAED
UMMEE KABEER
UMMUSALMA MUSTAPA











Nabeela tana Kuka taji Su Cyndia sun Fado part dinsu a haukace Cyndia tana ihu da takardu a Hannunta da yawa,Ichichi tana tausarta cikin Harshen turanci Kan Dan Allah karta Fadi abinda take Shirin furtawa,Nabeela inda Asad ya Bata ta gyara fes tana kuka kamar ba ayi wani Abu ba,kayanjikinsa ta cire tare da canja Masa Jallabiyya,waya Nabeela ta dauka da Niyyar Kiran Abonkin Asad Sufyan, A hankali Asad ya Bude idonsa tar a Kan Nabeela yace karki kira kowa,A firgice Nabeela ta katse Kiran tana ihun murna,Cyndia ce ta banko kofa tare da shigowa Uche da Damy suna Bayanta,Cyndia Takardu ta zube a gefen Asad tare da Mika Masa wani file hade da Envelope,Ihu ta sake saki tana furta I will Confess,Fatalwar Nmamdi ta sake gani a gabanta Yana cewa confess,Nabeela ta karba cikin turanci tace na mene wannan? Cyndia tana kuka ta durkushe a kasa ta Fara magana tana kuka tace
Kamar yanda kuka sani Dukkan yarana Dana Haifa ba Yan Uwan Asad bane ko Wanne Ubansu daban, Sylvester Babansa tsohon saurayi nane dake Enugu Nmandi sunansa,ganin Doctor yace bazan iya Haihuwa da Daddyn Asad ba Alex gashi Yana da Kudi Ina tunanin Zan ci gado, Ina da Aure nake zuwa wajen Nmandi muna tarayya har na samu cikin Sylvester,Bayan na Haifi Sylvester ya taso cikin gata da Jin Dadi ya girma sai Nmandi yace Lallai sai na bashi dansa ko ya Tona min asiri,Gudun hakan yasa Naje wajen wani Boka nasa aka kashe Nmandi Gudun Kar asiri na ya tonu,yanzu Fatalwar Nmandi ke fito min Yana cewa na Fadi gaskiya ko ya kashe Ni,gashi Nan a gaba na, Cyndia ta saki Ihu again taci gaba da cewa

Bayan Sylvester ya Fara school nayi sabon Saurayi shima Igbo ne Dennis na Samun cikin Uche da shi a tunanin Alex Baban Asad dansa ne, Lokacin Kuma Alex Baban Asad ya koma Kasar waje Yana Business sai dai yazo ya ganmu ko muje can,A can ya Hadu da Maman Asad musulma Yana sonta shi yasa shima ya musulunta aka musu Aure,Kafin Shekara Daya da Aurensu ta samu ciki,Ni Kuma lokacin na Haifi Uche,Mun Sha Kuka da bakin ciki da muka tabbatar Alex ya musulunta musamman Babarsa Ichichi Bata kaunar musulmai da musulunci,A cikin Christian ma Ichichi ta daban ce a Zalunci.
Haka Ichichi ta sa Dole Usman ya dawo Nigeria tare da Matarsa Muka zauna,Munyi Mata sharri da mugunta iri iri ta Sha wahala a hannunmu duk Dan ta rabu da Usman Amman abin ya gagara,Har ta Haife ka Asad ka taso cikinmu Wanda kaima tun kana yaro muke zaluntarka Dan ka Mutu a huta,Har Guba munsha sa maka a Abinci Amma sai a kaika Hospital ka warke har ka girma Cikin gata da soyayyar mahaifinka da mahaifiyarka.

Muna wannan Rayuwa Usman ya kamani da Kwarto wato Ola Yoruba ne shi shine Kuma Wanda na Samu cikin Damilola da shi,Lokacin Usman ya gano Ina tarayya da mazan banza,ya kasa yarda da yaran Dana Haifa ya kaimu Hospital ta karfi aka Yi DNA test aka tabbatar Kai kadai ne dansa,hakan yasa yace Lallai sai na bar Masa gida ya sake Ni,Ichichi dama Haushinsa take ji ya musulunta ta tsane shi akan danta yayi musulunci gwara ya mutu,gashi Ichichi tana so na da yarana duk da kuwa tasan Ba yaran Danta bane tace Akan Asad yaci gadon Danta gwara Ni da su Uche muci tunda mu Yan uwanta ne a addini,Muna Haka Ka Gama Degree dinka a UK ka dawo Ka sake komawa Masters,Gaka da Girman Kai da Izza baka ganin kowa da kima a lokacin sabo da Babanka Yana ji da Kai Yana Shagwaba ka, kana gamawa Usman ya tattara dukiyarsa ya baka Asad komai mu zamu tashi a zero,gashi muna ta yi maka tsafi yaki kamaka,Sai kawai muka hada Kai Dani da yarana gaba Daya Har Ichichi Muka je can Kauyen Abia state wani Boka yace ko me za ayi maka baza ka mutu ba sai dai a fidda ka a gidan,Haka Kuwa aka Yi Da sa Hannun Ichichi da yarana da Ni kaina Cyndia aka yiwa Mahaifinka Usman tsafi ya mutu sai tashi aka Yi aka ga gawarsa ba dalili.

Bayan komai ya dawo Hannunka Asad kana juya komai Kuna fantamawa da mahaifiyarka Muka koma da Ni da Ichichi aka maka tsafi ka koma kamar ba mutum ba zaka dinga Jin Kai ba mutum bane,sannan abincinka ma daban da komai ma,Sannan Ichichi tace ayi maka Wanda zaka koma Arne Dan karka samu damar yin Addininku tsafin mu ya karye,Haka a baya duk Yan Matan da zaka aura sai muje mu Hada munafunci mu rabaku,har ka hadu da Ihsan shine Ranar wedding dinner aka sace ka, sannan muka sa ka koma Arne,Haka kuwa akayi da kanka ka siyo Sarkar cross ka saka,duk tsafin da Muka maka ya kamaka kawai gidan ne kaki barinsa.

Hakan yasa Ichichi ta sa Kaninta Wanda ya kashe mahaifiyarka a gabanka suka Yi Kidnapping naka aka kaika daji tare da barinka cikin kogon dutse,Uche zuciyarsa tana da Dan tausayi shine yasa aka baka Atm din Accnt din Babanka da wayarsa sabo da Kar wahalar duniya tayi maka yawa zaka iya samun Kudi, shine bayan an daureka a logon dutsen aka sa maka su a Aljihu.
Haka Kuma muna bibiyarka mun San a halin da kake ciki har haduwarka da Nabeela,Kanin Ichichi ke bibiyarka har ya ja ka daji inda ya kashe Mum dinka a gabanka sabo da mun Masa Alkawarin kudi masu tsoka Amma sai kaima ka samu nasarar kashe shi da Yaronsa.

Tunaninmu Idan mun karya Asirin dake jikinka zaka ji ka tsani Nabeela sabo da ka dawo Hayyacinka sai ka rabu da ita sabo da munga zata Mai daka mutum,sai gashi an samu aka si bayan mun bari ka warke sai ka koma kazo da ita,Ganin Nabeela tana baka Shawara ka Fara Business da kudin Hannunka mun tabbata zaka Zama me kudi ka fimu hankalina ya tashi a Duniya bana so wani ya fini a rayuwa ko Dan uwana ne Bana kauna a fini Ballatana Kai Dan Kishiya ta Asad,Bana kaunarka Asad Bana son Mamanka da ta mutu.

Kan Nabeela Cyndia ta koma tace kinyi ganganci,kinyi sauri Nabeela Baki San Mene a cikin tukunyar Tsafin Sylvester ba,Dariya Cyndia tayi tare da furta na yarda a kamani a kashe ni,Amma ki sani dalilin Fasa tukunya da Kika Yi tsafin da akeyi komai na Asad ne,Boka yace indai aka fasa tukunya idan Asad Bai mutu ba to zai samu Rashin lafiya me tsawo Wanda bazai warke da wuri ba sannan Dana Sylvester Kuma zai mutu,idan kuma aka fasa tukunya Sylvester Bai mutu ba to shi zaiyi Jinya ta shekaru masu tsawo sannan Asad ya Mutu,sabo da Haka Nabeela Asirinmu ya karye gashi da kaina na fada Muku gaskiya sabo da Fatalwar Nmandi nake gani,ki daina Murna na rantse yanda Asad yake a kwance bazai iya yiwa kansa komai ba sai magana da kallon mutane,Nabeela ta fashe da Kuka Asad kuwa Dama Hawaye ne ke shatata a idonsa,Cyndia ta fashe da dariya,Ichichi tace Nabeela rashin hakurinki ya ja Miki kinyi sauri kin fasa tukunya ba tare da kinyi bincike kin gano Illar hakan ba,ga Dukiyar Asad kaf an Baku komai sannan Asad yasan inda komai yake na Mahaifinsa Amma Bazai amfani kudin nasa ba sabo da wannan cutar data kamashi ba Lallai ya warke ba,Maybe a Haka zai mutu,Nabeela Kuka kawai take rusawa Nazia tana gefe itama tana kuka.

Suna Haka sai ga Ola Baban Damy ya shugo da Yan Sanda masu Uban yawa,Dama Already sunzo gidan Suna bakin kofa sunji duk maganganun Cyndia da abubuwan da Suka aikata,ai Nan gaba Daya Suka tattara su Ichichi suka tafi da su can police station,Asad Yana kwance zazzabi ya rufe shi Baya iya komai sai idanuwansa da Bakinsa da suke aiki,Gabbansa da kyar yake Dan motsa su,Dole Yan Sanda Sai Nabeela suka sa a gaba aka tafi da ita tare da Daukan Gawar Sylvester gaba Daya,Bayan sun rubuta Report da Komai Kotu aka tura su,Ga labari ya watsu a Gari har gidajen gidan radio da Jaridu,Haka har da Nabeela akayi Hira da Cyndia a gidan tv,Cyndia Bata Musa ba ta bayyanawa duniya Komai,Abban Nabeela Yana samun Labari cikin dare ya Kira Nabeela tana Kuka tana bashi labarin sai lallabata yakeyi,yace Ku taho Kaduna Nabeela,Nabeela tace Abba sai na Gama komai zamu taho,Babu damuwa Nabeela ayi hakuri,to Abba ta furta.
Nabeela Wasa Wasa
Itace take yiwa Asad komai da taimakon Sufyan abokinsa,baya iya Yin komai da kansa sai an rikeshi yake iya takawa yaje toilet,Nabeela tace na godewa Allah ma da ba paralyze bane Yana iya motsa gabbansa idan an Rike shi,Kuma tsarki da wanka ma Yana iya yiwa kansa sai dai kawai a rikeshi yaje toilet.
Zama Uku sukayi a kotu Alkali ya yankewa Ichichi, Cyndia da Uche hukuncin kisa,Damy kuwa kasancewar ba a kamata da laifi ba sai aka bawa Babanta Ola ita ya tafi da Yarsa Dama Ola talaka ne na gaske Damy sai kuka takeyi ta koma Gidan Talauci ga Yan Uwanta kaf Za a sheka su Lahira,Kayanta ta kwashe kaf har na Mamanta abinda zata iya Mora ta bar gidan Asad,Nabeela Ma'aikatan gidan ta samu duk ta sallame su,sai wasu masu kirki musulmai ta zaba Mata biyu maza Namiji daya ta barsu Suka ci gaba da aikinsu.

Bayan komai ya lafa Nabeela ta duba takardun da Cyndia ta basu gaba Daya na kadarar Baban Asad ne da ya mallaka,Daya File din kuma data duba Atm card din Asad ne da layikan wayarsa a cikin Envelope,Asad Yana kwance a saman Bed cike da Tausayawa kansa da Nabeela ya kalleta yace Nabeela duk wannan takardun da komai da Kika sani nasan kansu nasan Kuma Kan aikin,sabo da tunda Muka dawo Nan Ina zuwa Ina bincikar duk abinda ke tafiya na Business,Karki damu kanki ma'aikatanma na Companies etc kaf basa goyon Bayan su Cyndia,sun bani sirrin komai a Kai riba na Samu fiye da baya,kin San Igbo sun iya Business Kudina Bunkasa sukayi sabo da Haka Idan Zaki Iya Zaki ci gaba da kula da komai kafin na Samu lafiya,Nabeela Hawaye ya shararo Mata tace Inshaallah zanyi Mijina Allah ya baka lafiya,Hannunsa Asad ya Rike tare da Furta gobe ki shirya zamu koma Kaduna gaba Daya abinda Muka Zo Yi Nan mun Gama,school ma Zaki ci gaba a can,wannan Gidan da duk abinda nake dasu a garin Nan Na siyar da su Na Kai kudin gidan marayu, Na koma da Office Dina Kaduna sabo da Haka ma'aikatan Dana Aminta da su zamuyi aiki da su a Building Dina inda Office Dina yake Kaduna,Sauran Companies kuwa dama Babu a Jos daga Cross rivers,Rivers State,Abuja Etc,Bani da Business a Jos,Barin garin zamuyi Baki daya bana bukatar sake rayuwa a cikinsa.
Nabeela tace Nima wlh bana so mu zauna inda zamu dinga Tunawa da su Cyndia,Amma a Ina zamu zauna a Kd? Karki damu Zaki Sha mamaki na Dade Ina Target Dina fada Miki ne banyi ba.

Haka kuwa washe Gari Suka Shirya,Nabeela ce ta shirya mijinta tsaf motoci su kaf da duk kayansu na sawa da abin bukata an kwashe a motoci an tafi dasu Kd,an bar gidan da Furniture Wanda ya siya shi lafiya Lau.
Ranar da su Asad suka bi flight ranar Aka zartar da hukuncin su Cyndia,Damy Tasha kuka an kashe iyayenta.
Suna sauka a Kd Airport Sufyan ne ya daukesu zuwa rantsatsiyar sabuwar Unguwarsu ta masu kudin gaske,sai ka Isa sannan zaka zauna a Unguwar,Layin Daya Fi ko wanne tsaruwa Nan Nabeela taga sun shiga tare da tsayawa a wani Hadadden tangamemen mansion gidane Wanda Bata taba ganin irinsa ba ka rantse a turai kake,Asad Yana gefenta a kwance yaganta tana ta mamaki tace Wai yaushe ka gina wannan gidan? Murmushi Asad ya saki yace tun sanda na Fara ganewa Ni mutum ne na dawo hayyacina lokacin na Fara Gina Mana wannan gidan,Nazia sai tafi tayi tace Yaya Asad ka Gama Birgeni a duniya gaskiya,Kaga Harda Swimming pool,ga Garden,Laaaa Harda wurin tsuntsaye daban,Nabeela suka fito santin gida yasa suka manta da Asad a mota Suka dinga zagaye gida duk wani abin more rayuwa akwai a gidan,Ga motoci sababbi na Alfarma sun Kai Bakwai,Sufyan Yana ta nuna musu sai da Suka Gama da Compound sannan zasu shiga cikin paalon part dinsu wasu Numbers ya Danna a jikin kofar kamar Yana Danna Atm Machine sai ga kofa ta glass ta Bude suuuuu,Sanyi da kamshi ya doki Hancinsu,Komai na part din Golden ne da Silver color,, furniture sune Suka haukata Nabeela,suka Shiga ko Ina suna Shan kallo, Bayan sun Gama kallon part dinsu, part din Baki Suka je tare da kashe kwarkwatar idonsu ciki komai Ruwan kasa ne, kasa da Sama Suka Gama kallo sannan Suka Shiga bangaren masu aiki Mata su kuwa Milk ne and Grey color,Sai kusa da gate da akayi dakuna biyu kowanne da toilet masu Aiki Maza,hakan ya nuna Asad bazai dauki maza aikin gidansa da yawa ba baza su wuce mutum biyu ko uku ba.
Gidan yasha flowers ko Ina da Interlock,bangaren pool kuwa Grass carpet ne,gida ya Kai gida na gaban kwatance Kitchen gasu Nan ko wanne part akwai nasu da store,Bayan sun Gama kallonsu Nabeela ta dawo wajen Asad tana ta murna shi kuwa Dadi yake ji ya farantawa Nabeelansa Rai,Sufyan ya rikeshi Yana takawa da kyar nauyinsa kaf a Kan Sufyan yake, Har bedroom dinsa ya kaishi,Nabeela tana bayansu Bayan Sufyan ya fita tace Wai har Office naka ka kammala? Asad yace sosai ma Sufyan zai kaiki ki Sha kallo ya Hadu fa da sauran masu aiki a karkashina duk an musu Office Zaki ga Building din,Gobe masu tayaki aikin gidan Nan zasu Zo Mata buyu Wanda Kika zaba na Jos, Maza Kuma mutum Biyu ne, Dan Asabe me Gadi Wanda Kika sani a gidan Dana Bawa Abba,Okay na Gane,sai me kula da Compound,Flowers,Garden da pool etc.
Nabeela tace Allah ya Kara Budi Ameen,Nazia Kuma na canja mata school ta wannan unguwar Kinga ba nisa da gida ba sai an kaita ba da kanta zata dinga zuwa tana dawowa,Islamiyya ma na Gama komai a layin Nan namu take,School dinki ma na canja Miki private a Nan tana da kyau da tsada,kina school kina taimaka min a Office,Nabeela tace wato Dama Kamar kasan hakan zata faru kana ta tsarawa,Allah ne ya Tsara Nabeela Kawai tunda na dawo Hayyacina na Gane komai sai na Fara planning komai,Cyndia tana tunanin su kadai ne masu Basira Bata San Nima da Target Dina ba,So yanzu Nabeela mijinki Yana da aikin Yi,sai dai Kuma Bai da lafiyar morar harkar Ina tausayinki Nabeela Asad ya furta kamar zaiyi kuka.

Hannunsa Nabeela ta Rike tace karka damu My Heart son da nake maka ya wuce tunaninka ko wanne Hali ka tsinci kanka Zan zauna da Kai,kaddarar mu ce karka damu ko Har abada a Haka zaka dawwama Ina tare da Kai bazan taba gudun ka ba,sabo da Haka Jaruma ka aura duk abinda kake so ni Nabeela shi zanyi,Wlh da ace nasan Wannan cutar zata sameka bazan fasa tukunyar ba,no gwara da Kika fasa ta Yan Matana gashi komai ya karye sun tonawa kansu asiri dare Daya Allah yayi maganinsu Haka Allah yake dare Daya zaiyi fata fata da mutum.

Nabeela ta kwantar da kanta a kirjinsa tana shafa Dan sajensa ta Furta Bari na fadawa Abba suzo ganin gida,sai dai kuje da Nazia Amma Abba yasan komai munyi waya dashi karshe ma gidan Nan shi ya kula da gininsa Ni na hanashi ya fada Miki nace mamaki Zan Baki,Amma har Office shine akan komai na Ginin,shike kula da Ma'aikatan,Kafin muzo Kuma Matarsa Hajiya Binta da Dan Asabe sune Suka gyara gidan Nan yake shining da kamshi.

A baya Burina muna yin Bental uba Zan nuna Miki a matsayin tukwicinki Amma Kash Allah Bai nufa ba gashi yanzu Banda lafiyar Yi Miki komai,Nabeela cike da sigar lallashi ta shiga bashi hakuri tana lallaba shi,Sufyan Kuwa ko da ya tabbatar basa bukatar komai ya Gama aikinsa shiri yayi ya wuce Jos abinsa kasancewar aikinsa bana hutu bane.
Nabeela da kanta ta Kama Asad da kyar yake iya takawa kamar zasu Fadi Dan ma tana da karfi,Toilet ta kaishi sannan ta rufe Masa kofar ta fito Allah yasa Hannunsa Yana aiki Amma bada karfi ba Haka dai da dabara yake yin komai Bai gagare shi ba,Har waya Yana iya Danna Abarsa sabanin yanda Cyndia tace bazai iya motsa komai ba.
Sai dare kayan su Nabeela Suka Zo a mota,a dare ta shirya kayan sawarsu da komai yanda take so Bayan tayi musu girki sunci,Asad Yana ta Binta da kallo Amma ba damar yin komai,a fili yace Allah ya Isa Cyndia gaskiya an min asarar Bental Uba,shi yasa aka ce kayi amfani da damarka kayi amfani da lafiyarka Amma Kika ki yarda ai gashi Nan,Nabeela tana ta dariya shima Haka.

Washe Gari Kuwa maza biyu Dan Asabe me Gadi da Tijjani me kula da gida Suka Zo da Jakar kayansu kowa da dakinsa da Toilet,sun Tausayawa Asad,Dan Asabe harda Kuka,da Yamma kuwa Mata Dattijai masu kwari ne Suka karaso su biyu Kasancewar Nabeela tace Mata biyu sun Isheta a gidan Bilkisu da Harira,Suma suna part dinsu sannan a part dinsu zasu dinga dafawa kansu Abinci suna bawa mazan su Dan Asabe.
Haka Nabeela ta Gama settling komai.

Bayan kwana Uku wanka taci cikin shegen Lace dinta Red,itama Nazia tayi kwalliya cikin Atamfa Riga da skert zasu je gidan Abbansu,Asad kuwa Nabeela Cikin Shadda Sea Blue ta shirya shi fes idan baka San Asad Bai da Lafiya ba baza ka taba ganewa ba,wani kyau da kiba ma ya Kara sabo da Nabeela tana gyara abinta,Kamshi sukeyi sosai,mota Nabeela ta Bude tasa Dan Asabe ya Kama Asad suka Isa Har mota ya zaunar da Asad a gaban mota,Nazia ta shiga baya da tsarabar da zasu kaiwa Abba,Nabeela kuwa kulle part dinsu tayi ta shiga mazaunin Driver cikin felleliyar motar da zasu fita taja Suka wuce cike da Nishadi.
Asad Hannu yasa tare da shafa wuyanta kadan,kallonsa tayi kadan tare da maida hankalinta Kan tukinta tana Dariya tace karfa ka sa na bigi trailer yace Allah kiyaye.

Suna parking a gidan Abba Nazia tayi ciki da Gudun Gaske,Abba ya fito da sauri Nazia ta fada jikinsa tana Murna,Abba yace Auta Nazia ki godewa Allah Ubanki ya warke ya dawo Hayyacinsa da a baya ne Baki Isa ko yatsana ki dangwala ba Yar Bantan Uba da tuni na Sumar da ke,Nazia tace ai Safiyya ta tafi,Abba yace Fadi da ihu ki Kara da wayyo Nazia ta,Ta bar Jin Dadi kullum da safe da Madara nake jika makoshi na,na goge Hakorana tas da Naman Zakara sannan nayi wanka da sabulun ruwa me kamshin jar flower,Nazia ta kyalkyale da dariya tace Abba muma Haka muke Yi a can,Abba ya zaro Ido yace ke Nazia da badan Tsufa ya shigeni ba da Balarabiya Zan Auro yanda kudi Suka ratsa ni,Nazia tace Abba ga Hajiya Binta Nan,Ke rabu da waccen kullum bana cin Abinci akan lokaci sai ta yini a kitchen tana dafa shinkafa da Miya,shi yasa furfura ta kullum Kara fari takeyi sabo da Rashin cin Abinci akan lokaci gata da kirki Amma Sam wajen dafa Abinci Bata da mutunci.

Nabeela ce ta kamo Asad Suka Shigo Abba Yana kallo yaji Tausayin Asad sosai,Nabeela Kamar zata fadi tana Nishi tana Abba Kama min ka tayani,Abba yace Uhm Uhm Nabeela maza kwashi Lada,Lada Zaki samu,ai ko kafadarki ce ta goce a Kan wannan bazan tayaki ba Nabeela sabo da Lada kike samu,Sannu Ana ta Rubuta Miki Lada Nabeela maza, ya sake furta Nabeela sannu Allah ya bashi lafiya,Abba yace Bazan Nemo magani da wuri ba Nabeela gwara ki Bari ki samu guzurin Alkiyama
Duk da Halin da Asad ke ciki sai da ya dinga dariyar Abba.

Hajiya Binta ce ta fito Abba yace Ahaf ka ganta Nan tun Rana ta Shiga kitchen har yanzu Bata Gama Hada Abinci ba,Nabeela tace Abba kana Shan wahala indai Haka ne,Asad ne ya Dan bigi Nabeela tayi Shuru suka gaisa aka Yi Hira har Hajiya Binta,ta kawo musu Ruwa da Da lemo sai Danwake me Dadi gaske,Ga Fruits da Dambun Nama.

Abba ya Ebi dambun Nama ya yafa a Baki Yana ci yace ga iya girki Amma ba a ci a Kan lokaci dariya sukayi gaba Daya,Abba ya kalli Asad yace Kai da gani Nabeela tana maka da wuri gaka Nan bul bul,Asad yace Abba 12pm muke cin abincin Rana,2pm muci makulashe,5pm mu Sha fruits etc dare muci Abinci me Dadi,Abba yace kaji magana Malam,wata kulawar sai yaran zamani,Binta kuwa kanta Gaba Daya kunu ne a ciki a daskare, a Haka larabawa Wai duk wata suke biyanta Riyal Dari,Hajiya Binta dariya takeyi kawai itama tasan rikicin Abba.
Hira suka Sha sosai sannan Suka Fara cin Abinci,Nabeela tana Jin kunyar bawa Asad Abinci a Baki Abba yace ke baza ki bawa mijinki ba? Ya Ina yabonki Sallah Zaki kasa Alwala Ni akidar Yan Boko ce da Ni duk da banyi Bokon ba Nan gidanku ne ku saki jikinku.
Hajiya Binta da Abba Suka ja Nazia Suka koma sama Sai Nabeela da Asad,Nabeela taga ba kowa tace kayi hakuri,Asad ya Mata Hararar Wasa sannan ya Bude bakin ta Fara bashi a Baki suna hirar soyayya abinsu cike da Nishadi.

Sai 11pm Suka fito zasu tafi wannan karon Abba ne ya Kama Asad yace yasa shi a gaban mota Suka Masa sallama,Nazia tace baza ta koma yanzu ba sai Nan da 7days idan zata Fara zuwa school Nan Suka barta.
Komawar su Nabeela gida ke da wuya ta kokarta Suka shiga bayi,Da kanta ta Fara yiwa Asad wanka Yana zaune a wata chair me kyau ta Yan gayu masu kudi,Nabeela ma ta rage kunyarsa a gabansa takeyin wankanta,Tazo Daura Masa towel ta kalli Hajiya Babba tace kinga kawanki ta furta tana dariya,Asad ya gane me take nufi shima dariya yasha, suka fito tare da yin Shirin Bacci.








AsmaBaffa.
[1/15, 10:46 PM] Sis Asma: 🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠




NA KUDI NE

DAN GIRMAN ALLAH KARKU FITAR DA NOVEL DIN NAN ZUWA WASU GROUPS.









76-80








Official








By
AsmaBaffa








Page naku ne

AISHA MOHAMMED
AIDA MAMAN TASNIM
MAMAN SAMHA
UMMIN SADDEEQ.
RUKEY MUAZ












Rigar baccin Asad Fara ce

Please Login or Register in order to submit comment