Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mata Fresh milk din a baki tare da dafe kanta da hannunsa Yana Bata tana kwankwadewa sai da Tasha da yawa ya dauke Abarsa shima Yana Sha,Ina zaka fita a Haka? Idan Nazia tana Palo fa?

Murmushi Asad yayi yace tana makaranta fa nasa a kaita Ayi Mata Interview da komai,Aha Nabeela ta Furta tana karewa Wandon Asad kallo ya Dame shi ga abar Bental Uba Kaya guda,Nabeela tace Dan Allah kaje ka saka Kaya Abu ba kyan gani Haka,Kallonta yayi tare da dage Mata gira Daya,A saman Kujera ya baje Nabeela tana gefensa,Kafa yasa Yana ta shafa cikinta da Kafafunsa,Ni Allah ka takura min,Yana latsa waya ya zuki madararsa ko kula ta bai ba ya mike sosai a kujera harda dawo da kafarsa a saman Cinyarta.

Harara Nabeela ta watsa Masa kafarsa ya daga tare da Daura ta a fuskar Nabeela,Tasa Hannu ta cire,Babban yatsan kafarsa ya sake daurawa a saman Lips dinta,Shagwaba ta Fara Yi ya takura Mata,tana Bude bakin ya Sa yatsan a ciki,cizonsa tayi ba shiri ya janye kafarsa.
Ihu da zage zage suka ji a cikin gidan gaba Daya Ana ta Hayaniya,Asad yace lafiya naji Hayaniya,Nabeela Mikewa tayi ta leka compound,ma'aikatan gidan ta hango an Tara su wuri Daya securities suna ta cajesu tare da zazzage kayan kowa Dake Dakin kwanan su,Ana neman takardun da Nabeela ta Kwashe,Daki Daki ake searching,Nabeela ta dawo tare da bawa Asad Labarin Abinda ake nema Amma Bata sanar Masa suna wajenta ba Shuru tayi ta koma wajen da ake abin tana ta kallo har aka Gama Searching ba a gani ba,Kan Yan Gidan Cyndia ta koma aka Fara searching Komai na Uche shima ba a samu a wajensa ba,Haka Sylvester da Damy,Ichichi ma har ita ba a samu ba.

Part din Asad aka taho da Wasu Securities da wasu Yan aikin tare da su Ichichi,ba magana ba komai Suka Fara searching ko Ina suna zage zage ba aga komai ba Dole suka Hakura tare da barin part din,Suna tafiya Nabeela ta kyalkyale da dariya,Asad yace lafiya? Ba komai ta furta tare da Jan Hannunsa tace Zo muje ka gani,Binta yayi zuwa Bedroom dinta,Katifa ta Bude Bedsheet din sai ga yanka katuwa a katifar cikin yankar ta Sa Hannu tare da Zaro Takardun tace ka gani Ni na kwaso su na boye, Asad yace Katifar Kika yanka da wuka kenan,kinyi dabara Kinga ba Wanda zai gani,takardun ya duba yaga duk kayan Abbansa ne Daya mutu ya Bari,Murna yayi yace good maida su ki boye,Nabeela ta maida su ta Adana sannan ta bawa Asad Labarin komai yanda ta samu takardun,yaji Dadi Kuma ya jinjina Mata .

Kamar yanda ya fada 5pm Nabeela Tasha wata Doguwar Riga ta kasar Qatar Ruwan toka,Taji Ado Golden tayi kyau ta yafa Dan gyalen rigar sai walwali take zubawa da Sheki,Takalmi tasa me shegen Tsayi Golden da jakarsa,ka rantse balarabiya ce,Asad Kam kana Nan Kaya yasa Wandonsa creazy Silver color da Rigarsa milk itama Creazy ko Ina a farfashe take sai kayi zaton tsohuwa ce Amma duk Wanda ya ganta yasan wanka ne kawai,Ba karamin kyau ya Tsula ba,Ga agogonsa kalar Wandonsa Haka takalmin ma,a Palo ya Iske Nabeela tana jiransa ,Kallonta yake Yi kamar zai cinye ta ta Gama Haduwa,wankan ya dire,Wayarsa ya gyara ya shiga kashe ta da Hotuna zafafa ya koma Yana Mata Video,Yana karasowa ya daura Hannunsa saman kafadunta ya mannata a jikinsa,fuskarsa ya manna a jikin Tata ya Shiga Yi musu Selfie,Suna Haka sai ga Sylvester ya shugo wajen kawarsa Nabeela,Asad ya wani Hade Rai Yana kallar Masa kwalliyar Mata a banza,waya Nabeela ta mikawa Sylvester tare da cewa Yi Mana pics, Sylvester Yana ta Jin Haushi ya dinga daukan Asad da Nabeela Hotuna,kala uku ya a musu ya Mika Mata wayarta Cikin fushi ya bar part dinsu Yana sake sake a ransa ya zai raba Asad da Nabeela.

Shi kuwa Asad Hips din Nabeela ya wani Rungume tare da gyara Mata mayafinta da kansa yace muje,A Haka suka fito compound,Yan aiki sai kallonsu akeyi sun birge mutane ko Ichichi da zata shiga mota ta hango su taji Sunyi karshe,Damy kuwa tana waya Bata San sanda ta saki Baki galala ba tana kallon kyau da gayu.
Uche Dake jikin window din bedroom dinsa sai da ya sake Miko dogon wuyansa, Sylvester Kam Naushi ya kaiwa Iska lokacin zai shiga motarsa.

Gaban mota Asad ya budewa Nabeela ta Shiga sannan ya rufe tare da zagawa ya Shiga mazaunin Driver Suka fita,Fitarsu ke da wuya wani matashi shekarunsu Daya da Asad abokinsa ne,duk Jos bashi da Abokin Daya wuce Sufyan,Sufyan dan me kudi ne shima ba laifi Kuma lecturer ne, ya taba Aure Matarsa ta rasu wajen Haihuwa,Bata Haihu ba ta rasu da Cikin gaba Daya.
Shine Wanda Asad ya bashi Nazia ya kaita makaranta yayi Mata duk abinda ya Dace,sai da ya Gama Mata komai sannan ya dawo da Nazia gida,Ganin ba kowa a part dinsu tasan Lallai sun Fita tunda Nabeela ta fada Mata zasu je Unguwa,shike Sufyan gida ya wuce abinsa.
Wanka Nazia tayi taci Abinci sannan ta koma dakinta tare da Sa key tana ta kallon cartoon a makekiyar plasma tv din Dake room dinta.

Asad kuwa Tsohuwar Unguwarsu ya Kai Nabeela,Nabeela Bata manta unguwar ba kasancewar tana Nan yanda take sai chanji da aka Dan samu na sababbin gine gine da wasu gidajen da aka canja musu fasali,Yanda Gidan su Asad yake a baya Haka yake sai tsufa da yayi tare da komawa tsohon yayi,Baki Nabeela ta Bude tace na tuna unguwar Nan ai na fada maka mun taba zama a Jos to a Nan kofar gidan aka so Yi min Fyade wallahi wani ya taimakeni kamar ma sunanku iri Daya Asad yace min lokacin da ya kaini gidanmu dake Tasha,Allah Kuna Kama na kalle shi sau daya Amma fa Kamar ma ya fika kyau.
Murmushi Asad yayi kawai ya ja mota Suka Kara gaba,Tasha ya Kai Nabeela tsohon gidansu da Suka taba haya wanda a yanzu an maida shi shaguna manya,Nabeela ta Bude Baki tace tsohuwar Unguwarmu ce wlh,Ga Inda Abba yake Zama a Majalisa Kai Allah sarki duniya,a Nan Jos fa Da Dan Gada Gada ake Kiran Abba,Asad ya Gama Tabbatarwa Nabeela ce wacce ya taimaka,Yace to yarinya Nine Wanda na taimakeki za a Miki fyade,nine Asad din wlh,Kuma kece wacce nake ta nema dama.

Asad Yana jira yaji Nabeela tace tana sonsa ko yaga alamar Jin Dadi a Fuskarta sai yaga akasin hakan,fuska ta murtuke tare da Furta to An gode da Taimako, a hankali ya furta I love you Nabeela,Nabeela baki ta tabe tace kake son dai Yarinyar da ka taimaka Amma ba Ni ba,yanzu da ace yarinyar da ka taimaka ba Ni bace da tuni ka koma wajenta ka auro min ita,itace zabinka to Ni bana sonka ka maida Ni gida Kuma yawwa Ehe.
Kai da kace itace burin ranka wato Ni bani kake so ba,to ai kuwa Ni ba abinda ya dameni,Asad yace tab abinda Zaki min kenan?wallahi Baki Isa ba sai kin so ni Dole,kuma Ni Bari kiji in fada Miki nafa gaji da jiranki Yau sai kin bani hakki na bazan iya jira ba na gaji,tunda bakya so na kije Amma Ni Ina sonki Kuma Ni Hakkina Zaki bani ba ruwana da wani sonki ko ki,Nabeela tace sai ka kwata mu gani,banyi niyya ba bana so kuma idan ka matsa min sai na fita daga motarka Kuma idan Naga dama na bar Jos gaba Daya,Okay to fita ki tafi na gani idan kin Isa,Murfin mota Nabeela ta Balle ta fita tayi tafiyarta Asad Yana kallonta cike da mamaki.

Takaici yasa shima yayi zuciya tare da fisgar motarsa zuwa gida,Yana tafiya Nabeela tace wayyo kaga marar mutunci ya tafi kuwa wallahi Ashe da gaske yake Yi, yanzu idan na tafi Ina zanje? Asiri na ya rufu inci Isha in saka sutura ta Alfarma ga son Asad ya Gama ragargaza min Bargo,Ai Nabeela tace Ina ga inda zanci shinkafa in koshi inyi abinda nake so ba inda zani,Taxi ta shiga ta koma Gidan su Asad.










AsmaBaffa
🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠






NA KUDI NE



DAN GIRMAN ALLAH KARKU FITAR DA NOVEL DIN NAN.








61-65








Official






By
AsmaBaffa









Page naku ne

MAMAN KHAIRI
MAMAN ILHAM
BESTYNBEELAT
BK
NANA MAHMUD
SAADATU TIJJANI
MUM NAWAAZ











Kafin Asad Ya koma gida Nabeela ta Riga shi komawa,Asad kuwa Direct gidan Abokinsa Sufyan ya wuce cike da bacin Rai Sufyan ya ga Asad ya shugo Yana Huci,Sufyan dake wance saman Bed dinsa,Tashi yayi zaune Yana tambaya lafiya Asad? Tsaki Asad yaja tare da Zama a saman bed din Yace Sufyan idan aka ga Zan Kara Aure Kar a ji Haushi na ko a ga Laifi na,Yarinya Yar karama sai Raina min hankali takeyi akan ance Ana sonta,Allah zanyi mummunan lafazi idan aka sake,Sufyan ya tuntsire da Dariya sosai,ka Dade fa kana fada min kana son Nabeela sannan yarinyar da kake nema idan ka ganta baza ka Aure ta ba Kuma baza ka rabu da Nabeela ba, yanzu Kuma kazo kana maganganun Banza abinda baza ka iya ba,Kai banza ne ai Yarinyar Dana ke baka labari Ashe Nabeela ce,Kuma ko da Bata kasance Nabeela ba bazan so ta ba wlh,Nafi son Nabeela ta,Tsokanarta nakeyi da Zancen kishiya shine ta dauka da zafi.

Sufyan ya gyara Zama tare da furta kaga inda ka kashe kanka Kai da kace zaka sa ta fada sonka shine kaje kana Mata Zancen kishiya,ko Shekara dari kuka Yi da mace matukar zaka Mata Zancen kishiya Kun Bata kafin ta dawo normal zaka Dade,Yanzu sai ka koma kayi ta nuna Mata so da kyautatawa har ta fahimta da gaske kana sonta,Hadiye ta take so nayi a Haka baza ta Gane Ina sonta ba? Kwangiri ce ita? Ko dusa ce a kanta da baza ta Gane ba Asad ya furta Yana masifa,dariya Sufyan ya dinga Yi,Yace Asad wlh Abinda kake birge Ni da shi Iya Hausa kamar a wajen Tsohuwa ka girma,har mamaki nake Yi Ina kake samo Kalmomi haka,Tsaki Asad ya ja tare da furta kaji da shi ya mike yayi tafiyarsa ko sallama babu.

Gida ya wuce Direct Baiyi zaton Zai ga Nabeela ba Amma Yana shiga Palo ita ya Fara gani tana kallo ta wani kyalkyale dariya,fasa shugowa yayi ya tsaya Yana kallonta kawai yanda Dariyar tayi Mata kyau,duk bacin Ransa sai ya yaye har shi kanshi da Bai San me take wa dariya ba ya Fara tayata a gefe Yana wani Murmushi marar dalili kamar wani dolo.
Palon ya Shiga da Sallama dauke a Bakinsa,Amsawa tayi tare da maida kanta ga tv tana kallonta,Haushi Asad ya ji Bata ce Masa Sannu da zuwa ba,cikin fushi yayi sama abinsa Yana Jin Haushin Nabeela Yana cewa me take so nayi Mata ne yarinyar Nan,Sai da yayi wanka ya canja cikin Kaya Marasa nauyi sannan ya dawo Palon da take kallo,Kamar daga Sama yaji tace Sannu da dawowa,ta gefen Ido ya kalleta kawai tare da furta yawwa,Lokacin ya samu dama Yace kinci Abinci kuwa?

Mamaki Nabeela tayi a ranta,gwada shi tayi tace banci ba sai anjima idan na Gama kallo zanci,Kallo yafi lafiyarki kenan? Tashi ki zubo,Nabeela cike da Shagwaba ta dauke kanta can tana Shure Shure Ni Kyuya nake ji,Okay ya Furta tare da Mikewa ya nufi kitchen da kansa,yana tafiya Nabeela tayi dariya harda tsalle tace Ashe Haka Safiyya ke ji shi yasa ta dinga wahalar da Abba Nima na koma Safiyya,Asad ya duba kitchen dinsu ba komai,waya ya Kira Shugabar masu dafa Abinci ta gidan Gaba Daya Yana Balbala masifa Yace ya Zaki bar min matata da yunwa? Me za a kawo Mata Sir? Gashi an Gama pounded yam with Egg source,Okay a kawo yanzu bana son jira,Yana tsaye sai gashi an kawo,gaban Nabeela yasa suka ajiye kyawawan flasks din,kusa da Nabeela ya zauna jikinsy yana gugan juna.

A hankali ya furta gashi Nan an kawo Miki kici,kallonsa tayi sannan ta Furta thanks tare da komawa kasa ta dire gwiwoyinta ta rankwafo tana serving kanta,Rigarta me siririn Hannu ta wani Zame Rabin Boobs dinta duk a waje suke suna sheki,Asad Yana ta Shan kallo harda Harde kafafu ya kwanta sosai a cikin Kujera,Yana ta kallo tana zuba abinci,Ta Gama Yace Serve me Dan yanga tana kokarin gyara zamanta kallonsa zai Kare,Haka ta zuba Masa Bata San me yakeyi ba,zata mike kenan Yace zubawa Nazia Mana,Nabeela tace maybe tayi bacci fa,idonsa Yana kirjinta Yace ki zuba Mata Ina ruwanki,Haka Nabeela ta zuba na Nazia,Yace ga ragowar Nan zubawa me rabo shi ma idan Allah ya kawo wani yaci,Baki Bude Nabeela take kallonsa sai tayi Shuru ta zuba ta me rabo,Zata mike tace na Gama Asad Yace to a yanda kike zuba abincin Nan a Haka Zaki ci abincin Nan,Nabeela ta Fara zargin wani Abu sai ta kalli idonsa ta ganshi gaba Daya kirjinta yake kallo,a ranta tace ohhh na Gane shi,Sai ta duka sosai yanda zai gani hankali kwance tayi wani goho tana ta cin Abincinta a Haka,shi kuwa mayen ko Kyafta Ido baya Yi.

Cikin magagin kallonsa Yace Wai ke kuwa Lafiya kike Yar Nan? Nabeela ta dinga Dariya tace Malam na Gane ka fa kallo ba tabawa ba kayi ta Yi idonka ke aiki,Idan ba tsoro ba ki cire Rigar Mana tunda kince kallo kawai,a gidan Nan ana zaluntata gaba Daya Babu me so da kaunata cewar Asad,Ban Gane ba? Nabeela ta Furta,yace ga su Cyndia sun sani a gaba ke Dana kawo Zaki kula Dani kin ma fi kowa tsanata, idan akayi Wasa Uban yaranki kwana Nan zai Fara Neman Mata ko na Fara Shan giya abina,Nabeela tana dariya ta mike tsaye tare da komawa gefensa ta zauna tace Ina Nan ai bazan Bari ba,Asad ya jinjina Kai yace to kuwa Zan Hadiyi Zuciya na Mutu kawai, ki ci gaba da cusa min bakin ciki kina kallo mijinki zai Mutu ki koma bazawara gaki Baki Haifi yaro ba bare ki samu gado Karshe ma su Cyndia ne zasu koreki daga gidan Nan.

Da sauri Nabeela ta rufe Masa Baki da tafin Hannunta tace Dan Allah idan zaka Yi magana ka daina min zancen zaka mutu kana mutuwa Nima Zanyi fut na Mutu,Ina ji da Kai ai Kaine kace zaka min kishiya kana neman wata ba Ni ba,Da sauri Asad yace Ni Wasa nake Miki tsokanarki nakeyi kawai Don Naga kishinki ko kina so na,Amma ai ka nemi yarinyarka daka taimaka,to ba gashi ke bace sabo da kece ma shi yasa nake sonta,Ko ba Ke bace wallahi nafi sonki da ita Kuma nace bazan iya Miki kishiya ba ni sai Idan bakya min abinda nake so,ta ya Zan yarda? Nabeela ta Furta Zaki gani da idonki ai,Alright Ina zuba Ido Nabeela ta Furta tare da daura kanta a saman kafadarsa tana cin Apple,Hannunta ta saka a cikin nasa tafin Hannun shi kuwa ya damke tare da lumshe ido.

Zaki Fara University verysoon,Nabeela ta Bata Rai tare da Furta Ni Allah bana son karatun Bokon Nan sai dai Dole kawai nayi,Ae kiyi hakuri kiyi Haka ba course me wahala ba kina farawa Zaki ga kin Gama,shi wahalar karatu a Fara sai na saki a private University inda baza ki wahala ba,Amma fa Ni bazan Yi aikin Gomnati ba sai dai idan ka Bude min wani abin Business din,To wanne irin Business za kiyi? Shagon Boutique zaka Bude min da bangaren jaka da talkalma na Mata insa yaro me kula da wurin Ni Kuma Hajiya me wajen sai dai sanda Naga dama na Shiga dalleliyar mota naci gayu da glass Dina naje waje Ina taku kwas kwas tare da karkada mukullin mota yanda Yan karya keyi, wata ma da kyar ta samu kudin zuba Mai sai taje waje tana famkama da mukullin mota,Asad yace to ke baza kiyi ba,me shi Baya fada sai dai a gani a fada,Ai Allah Nima sai naji Dadi na nayi,sai na Rama nayi Kara'i,wani abin ma Sai naje Kaduna ko Kano a can Zan Rama karyar da aka dinga Yi min.

Suna Hirarsu Sylvester ya banko kofa kamar Mahaukaci,Nabeela ya nuna da yatsa Yana cewa bincike ya nuna cewa ke Kika dauki Documents sabo da Haka kiyi gaggawar dawo da su,Nabeela ko kallon Sylvester Bata Yi ba sai ma juyawa da tayi tana ta yiwa Asad Labarin Suka maida shi wani banza Yana ta magana shi kadai,Tsaki yaja yace You will see,ya juya zai tafi Nabeela tace to see Uwarka,cak ya tsaya tare da kallon Nabeela yace you are in Hot Soup,Nabeela tace You are in Hot Kamu and tuwo,Stupid Girl I will teach you a lesson Sylvester ya Furta Yana Huci,Nabeela tace Abomination, I'm intelligent I knew A.B.C.D to Z, I can read and write,which kind Lesson Kuma?,as you see me so you can't teach me anything Never,Over my Death body, Sylvester Nan ya gane Nabeela ba karamar shegiya bace ta nuna kamar ta kirki ce, kwafa yayi ya fice.
Asad Yana jinsu Suka Gama cecekucen su.

Sylvester direct Meeting ya hada Cyndia, Ichichi,Damy,Uche sai shi Kansa suka zauna a palonsa,Bayani ya Fara musu Kan tsafinsa ya nuna Masa Nabeela ce ta sace Documents,Ihu Cyndia ta saki tare da Furta Ewooooo...that stupid young lady? Ichichi tace Jesus,Nan ya Basu labarin fadansu da Nabeela,Uche yace I Hate that Girl Die.
Cyndia tace mun bar komai a Hannunka my son Ta nuna Sylvester da yatsa Do as you wish.

Bayan kwana buyu Asad Ya sa Nabeela a makaranta tana karanta Biology, Nazia ma tuni tana zuwa makarantarta da Islamiyya yayin da Asad ke nunawa Nabeela kulawa da so Amma har yanzu Nabeela bata wani ko Taya shi kwana,shi Kansa ya cire Rai, Yau Tuesday Nabeela tana da lecture yamma sai 6pm Asad yaje da kansa ya dakko ta,Sun dawo zasu Shiga part dinsu kenan Suka ji uban kidan Makkosa Yana tashi a speakers,Sunyi knocking har sun gaji ba a Bude musu ba,Ta Window Asad ya tsuguna Nabeela ta Dane saman wuyansa sannan ya mike tsaye ta leka ta window sai ta hango Nazia ce ita kadai tana ta rawa tana Murguda Duwawu irin na Yan Makkosa.
Nabeela Baki Bude tace Nazia ce ita kadai tana ta Rawa,Asad ya sauke Nabeela ya leka shima yaga Nazia tana ta cashewa ita kadai harda sa pcap.

Da karfi Nabeela tace Naziaaaaaa.....zanci Ubanki,Sai lokacin Nazia taji Maganar ta kalli window inda taji magana r tana Ganin Asad da Nabeela ta Bude kofa da gudu ta Haura sama ta boye,sai da Suka shiga sannan Nabeela ta kashe kidan,Asad ya Zama bawan mace Haka ya dauki mayafin Nabeela da Jakarta Suka Haura Sama,Bedroom dinsa ta bishi yau da sabon salo tazo,saman bed dinsa ta haye ta kwanta Wai bacci zata Yi,Asad yasan kwalele zata Masa kawai ya Fara zare kayansa yayi tumbir sannan ya daura Towel Nabeela ta rufe idonta da sauri karta gani sai ma ta rufe kanta cikin Bargo tana dariya a hankali,Wanka yayi sannan ya fito ya Gama kalailaitarsa ya shirya cikin Riga Armless da gajeren Wando farare ne tas Yana zuba Kamshi Yace Yunwa nake ji,Nabeela tace Bari na tashi nayi girkin Hutawa nakeyi,Kiyi baccinki zan sa a kawo ya furta Yana me ficewa.

Yana fita ta mike ta shige toilet dinsa a Nan tayi wanka ta saka Wata farar T-shirt dinsa har cinya ta kawo Mata fitowa tayi tana kamshi irin nasa,tunda ya hango ta Yana Dining ya kasa dauke idonsa,Kujera taja itama ta zauna Kanta tayi Serving Fried rice ta sake zuba wata Yace ke da wa Zaki ci? Ta me rabo ce,Dariya yayi ya tuna sanda ya fada Yace ai ba a Haka Zaki zuba na me rabo ba Zo ki gani,Mikewa Nabeela tayi zuwa gabansa tana dariya,Saman Cinyarsa ya daura Nabeela ta zauna daram sannan Ya dauki Abincin data zuba gaba Daya ya maida cikin flask har nasa Yace to ayi Serving dinmu harda plate din me rabo,Yanda Yace Haka Nabeela ta zuba harda na me Rabo,Zata mike tsaye Yace a zubawa Nazia a rufe Mata itama,Dariya Nabeela ta dinga Yi tace bazan tashi a cinyarka ba Dan Allah Kar a lalata abincin Nan akan Haka,Ban yarda ba ni dai cewar Asad.

Tana saman Cinyarsa a Haka suka ci abincinsu Nabeela wani mugun Sha'awa da Son Asad takeyi tana so ko Romancing juna su Fara Yi Amma Bata so ta nuna hakan,Dabara ce ta Fado Mata sai da Suka Gama cin Abinci tace daukeni mu kwanta a saman kujera,Asad ya gano kwana biyu yanda Nabeela take makalewa a jikinsa,dannewa kawai yake Yi,Yace kujerar ai tayi Mana kadan,Ni dai a Haka zamu kwanta,idan Nazia ta fito fa? Nazia ai ta waye kuma idan zata damu mutum sai ta tafi Kaduna wajen Abba tunda an kusa Hutu,Asad Ido ya zaro Yace Yau da kanki kike cewa Haka? Murmushi tayi kawai Suka kwanta a haka,Nabeela ta shige jikinsa wuyanta yake shafawa da gashinta a hankali sai lumshe Ido take yi tana so ya gangara da Hannunsa zuwa kirjinta Amma sabo da muguntar Asad sai yaki yarda,Nabeela a ranta tana Ka Kara gaba...ka Karasa wajen Amma Ina Asad yaki.
Juyowa tayi Suna facin juna Lips dinsu suna gaf da na juna Amma Asad yaki kissing nata,tsaki taja tare da Sosa gashinta,mutsu mutsu ta koma Yi tana shagwaba Nan ma Bata Yi Nasara ba sai ma gani tayi Yana Shirin yin bacci,Nabeela ta turo Baki tace Ni dai gaskiya karka Yi bacci Kai komai bacci Bacci baza ayi Hira ba,Yana sani Yace na gaji da yawa ne, Ya rufe idonsa Yana baccin karya,Remote ta jawo da Hannunta ta Fara bubbugawa a kusa da kunnensa idan ya Bude Idonsa sai ya rufe abinsa,takaicin duniya ya damu Nabeel Haka Har lokacin Sallah yayi.

Bayan Sunyi Sallar Isha lokacin Nabeela da wuri tayi Shirin Bacci cikin Wasu sababbin Kayan Bacci,wata Yar yagwalgwalar Riga ce kusan kamar tsirara Haka mutum zai fito komai ana gani,Nazia kuwa kunya takeyi an kamata tana Rawa abincin ma Sai dakinta Nabeela ta Kai Mata.
Asad shima yayi Shirin baccinsa kenan Yana fesa turare yaga Nabeela ta shigo,kawai karfin Hali yakeyi Yana danne sha'awarsa,Nabeela ta Baya ta Rungume shi tare da lafewa a jikinsa,Asad ajiyar Zuciya ya saki ba tare da ya shirya ba Amma a fili sai yayi Kamar Bai ji ba,Yace Good night Kika zo Yi min? No a Nan Zan kwana yau,Asad a ransa sai da yayi Ihun murna Amma fili Yace Okay kawai ba murna ba komai,jikin Nabeela yayi sanyi fa,ko baka so ne? Ina so Mana barka da zuwa ya Furta Yana shareta,Light ta kashe da kanta tare da hayewa saman bed,Kwanciya yayi nesa da ita,da kanta ta dawo jikinsa ta Rungume shi,Sai mutsu mutsu takeyi tana tsaki Asad yaki nuna ma yasan me take nufi,Kuka yaji Nabeela ta barke da shi Harda cewa Wayyo Allah na Shiga Uku Abba...Har ga Allah Asad ya zaci wani Abu ne ya same ta da sauri ya juyo Yana tambayarta lafiya,Kasan bed ta koma tana jama'a ku taimakeni wayyo Allah Ni ba a so na,Mijina jama'a baya kauna ta ya juya min baya,Da sauri Asad ya toshe Mata Baki Jin zata tare Masa mutane.

Me nayi Miki Nabeela? Sai yau taji ya taba Kiran sunanta a duniya,Wulakanta Ni kake Yi Dan kaga Ina kulaka yau kwana nawa sai shareni kakeyi,Asad Yace ke fa Kika ce Baki yarda da son da nake Miki ba sai kin yarda tukun Kuma

Please Login or Register in order to submit comment