Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana kallon ikon Allah Kamar ubanta,Amma tsoron Alex da kwarjininsa yasa tace Nima ganinsa kawai nayi na Isa na Fara kula samari ai sai da amincewarka,Ni din banza na kula samari bayan baka bani dama ba ai sai abinda kace Daddy Asad,Harara ya watsa Mata tare da furta karki ganni kamar sakarai nasan me nake,Dan bana iya tuna wani abin ba shine zai sa ki maidani sakarai ba ki kiyaye Kar na kuma ganin Namiji yazo min gida,Ni yanzu a gida na kike ni zan Baki tarbiya daga yau kinji Ni? Da sauri Nabeela ta kame kamar soja tare da Sa hannu a goshi ta Sara tare da furta yes sir,Alright ya furta sannan yasa Hannayensa masu matukar laushi ya goge Mata hawayen Dake Fuskarta yace I'm sorry kin jawo na mareki ki kiyaye gaba.

Ina matar Auren tawa? Nabeela ta turo lips gaba tace anjima bayan Sallar Isha,an Dace ta Amince? Ya tambaya yana Binta da mayen Kallo, Nabeela tace ta Amince na karbo number wayarta tace ku Fara sms chat kafin ku Dan saba sai ka Kira ta ku Fara waya daga Nan sai ta baka dama a Kai kudin Aure,Asad ya murmusa yace wayar ma baza ayi ba sai sms chat,Bata WhatsApp ko wani Abu? Iyayenta baza su barta ba,To Nan da yaushe Zan Fara Jin Muryarta? Nan da sati daya yanzu sms kawai zaku Fara,Good bani Number,Nan take ta bawa Asad number dayan layinta Wanda tasan Bai da shi sai Murna yakeyi zai Yi aure ya koma mutum,Nabeela tace yau kayi Sallah kuwa? Asad yace ae Mana kin San Wani Abu? Sai ka fada,Na tuno cewar tun farko Ni musulmi ne Kuma Kamar yanda Mum ta fada kafin ta rasu suna na Asad,Kuma na tuna Sunan Daddy na,Da Sauri Nabeela tace ya sunansa? Usman Benedy sunansa,Asad Usman Benedy ake kirana,shike Nan ka tuna? Asad yace na tuna Yanda ake Sallah,karatun Addini na ya dawo Ina tuna komai,Sai me Kuma? ae shike nan Sun Dan tattauna kafin Nabeela tace saura wannan cutar da kake komawa Kamar Zaki ya kamata mu gwada yanda Ranka zai Kai karshen baci ko kaci irin abincinmu mu gani ko ka warke ko? Ae Asad ya furta Bari su Zeena su tafi.

Girki Nabeela ta daura suna Hira sama sama da Asad ya karba yankan Cabbage Yana tayata,Har tayi miyar cabbage ta Sha kifi da pounded yam,Har su Zeena duk ta kawo musu sunci sun koshi,Asad yau shine yaja su Mu'azzam Sallar Isha da Magriba suna ta mamakin iya Qiri'ar Qurani Haka da Asad yayi,Yana da Ilimin Addini matuka sun tayashi murna sosai,Wurin 9pm su Zeena Suka tafi gaba dayan su,Nazia tana bedroom tana game wacce Asad ya siya Mata,Baki na tafiya Nabeela ta kulle ko Ina ta kawowa Asad Pounded yam, Sannan ta kunna Camerar wayarsa zata dauki video idan cutar ta motsa yaga abinda yakeyi,Ai kuwa ta saita waya tare da ajiyeta, tace start,Nan Asad ya Fara kwasar girki,Kafin yayi Loma Biyar idonsa ya Fara canjawa,Sai ya Fara karkarwa idonsa yayi jajir,a hankali ya Fara gurnani, ga karfi yazo Masa ya Fara Nishi da gurnani kamar Zaki,Ganin Haka Tsoro ya Kama Nabeela ta kwashe da gudu ya bita a tamanin tayi samansa tare da Bude Bedroom dinsu ta fada tasa key,Allah Nazia tayi bacci tuni,yayi bugun duniya Yana Hargagi shi Daya,Tausayinsa ya Kama Nabeela ta Fara zubar da Hawaye tana jinsa Yana ta Yi har ya gaji ya Fadi a wajen Yana wani nishi Bai San me yake ba har ya Fara Amai ya Amayar da duk abinda yaci sannan ya dawo Hayyacinsa a wajen Bacci ya sace shi.
Nabeela Kam Bata fito ba sai da Gari ya waye tangar sanann ta fito tare da lekawa Bedroom din Asad ta Ganshi Yana ta baccinsa Alamar yayi wanka ma ya canja Kaya,gidan tabi ta gyara ko Ina tayi Masa irin abincinsa ta dafa musu kalar Nasu sannan tayi wanka tare da Nazia Suka fito Dining,Nazia dama Sunyi hutun makaranta.

Asad da wani Nishadi ya farka a bacci sai yunwa data Dame shi a gurguje ya sake sabon wanka ya fito cikin Shadda me tsada light blue fadin irin kyan da yayi Bata Baki ne,Kasa ya sakko zuwa Dining sabo da yasan Nabeela ta hada Masa abincinsa,a dining ya hango su suna ta ciye ciye,Nabeela tace Good morning Sir,Nazia ma ta gaida shi ya amsa da fara'a,Wayarsa Nabeela ta Mika Masa ya duba yaga farkon sanda ya Fara gurnani idonsa yayi ja,Kamar zaiyi kuka ya kalli Nabeela yace ke Daya Kika San sirri na don Allah karki fadawa Amaryar da Zan aura,Idan ta gani Baza ta Aureni a wannan halin ba,Nabeela tace ba damuwa ko ta sani baza ta gujeka ba,ae duk da Haka Kar ta sani please, Inshaallah cewar Nabeela,Nazia tana ji Bata San me akeyi ba ma.

Bari na fara Mata Sms yau ko? Ae ka Fara idan ka iya soyayya da wuri zaka sace Zuciyarta,Asad yace na iya Ina kallar yanda akeyi a film da wajen mutane,Okay to Fara yanzu kaga Safiya ce sai ayi Mata zazzafar morning Text.
Wayarsa ya Fara latsawa,Nabeela ta dauki wayarta itama Kamar me duba abu,Shima ya Fara rubutu kamar Haka,Nabeela a ranta sai dariya takeyi Asad Bai San ita ce Budurwar ba.






Sharhi fans






AsmaBaffa.
🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠






FREE PAGE









Masu son shiga group din Gidan Gwauro dari biyu ne

Account number
0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank

Vtu ko katin MTN ga number da zaku tura
08033933642

'Yan Niger Ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39


31-35








Official






By
AsmaBaffa






Page naku ne

Page Naki ne MUMMY











Rubutu ya Fara Kamar Haka Yana wani Murmushi Kamar ya San matar tasa
Morning is not only sun rise
but
A Beautiful Miracle of god
that defeats darkness and spread light.
This may be a very beautiful day for you Inshaallah.!!Good morning Angel.
From Handsome Asad.
Yana Gama typing ya tura.
Bugul Silently message ta shigo wayar Nabeela ba tare da Karar ringing ba,Budewa tayi ta karanta abin ya Bata dariya har da wani Cewa Handsome Asad ya wani yabi kansa,Murmushi take zubawa Alex Yana satar kallonta tayi Masa kyau da yawa,yace ki daure ki Nemo miji kema har yau ba mashinshini,jinin farin jini ne Dani ke Kam bakin jini Kika gada,Nabeela tana typing Bata kulashi ba,minti biyu sai ga reply ya shugo wayar Alex,da sauri ya bude yaga an sa

Morning Dear,Always be Happy and make others too.
Yana karantawa yace Good,ki kular min da kanki,Sai ga repyly Nabeela ta tura itama Kamar Haka
Gaskiya kana sa min nutsuwa, Zamansa ya gyara yana Murmushi ya rubuta Ke Haske ce a zuciya ta tunda har Kika so ni Kika Amince Dani.
Nabeela ta tura ka godewa Nabeela itace ta fada min kyawawan Halayenka shi yasa na Amince,Asad yana gama karantawa ya kalli Nabeela tare da daga Mata Babban yatsa irin na jinjina Murmushi tayi itama Suka ci gaba da chat abinsu ta waya,Kamar Wasa Suka Fara chat kullum Safe Rana dare sai Suka Saba sosai Suka Kara shakuwa matuka ba tare da Asad ya San Nabeela ce ba, tunda ya samu budurwa suna chat shike Nan Bai damu da wata Nabeela ba,a cikin gidan Kowa harkar gabansa yakeyi shi a Dole wata ta dauke Masa hankali.

Wasa Wasa sai Asad ya kamu da son wacce suke chat matuka,Bangaren Nabeela ma hakan take Alex ya Gama shiga Zuciyarta Har Bata iya bacci idan Bata ga Text dinsa ba,shi kuwa ya matsu ta bashi dama su Fara waya Amma Har anyi sati Biyu da Fara chat Taki Amincewa suna waya.
Nabeela ya iske a palo waje ya nema tare Zama sannan Yace Ki Mata magana ta Bari mu Fara waya Mana sai kashe Ni take da zafafan Kalamai banji Muryarta ba,Ni ko sunanta ma Baki fada min ba Maryam din ce Kika samu ko wata? Nabeela ta murmusa tace ai sunan mu Daya da Ita Nabeela sunanta itama ,Asad ya wani Dafe gefen zuciyarsa tare da Furta a farko sunanki Bai min Dadi ba Amma tunda Iri Daya ne da wife Dina to sunan yafi ko wanne suna Dadi a duniya.

Nabeela tace Lallai kana sonta da yawa,jiya har mafarkinta nayi tana min zazzafan kiss kamar Kar na farka a bacci Amma Kash sai na farka ban Gama Jin dadin ba,Gashi ance ba a son idan Ana Neman Aure a bi wata Hanya ta banza matukar Ana so Auren yayi Albarka gashi ban karasa Jin dadin ba ya za ayi kenan? Ko kece Zaki Karasa min yanzu? Nan take Nabeela ta fashe da dariya ta Gama gano wayon da Asad zai Mata,To Nima Wanda nake so Zan adanawa abinsa kamar yanda baka so ka lalata taka matar,Tsaki Asad yaja tare da cewa ke bakya ganewa ita rayuwa ai cude ni incude ka ne,Nabeela tana ta faman dariya tace to nidai baza ka cudar min jiki ba,ka dauki Hakuri har kayi Aure ko kaje wajen Amaryar Taka kuyi bada Ni ba,Asad ya ja kwafa Yace Zaki ga Rashin mutunci kuwa yarinya kina Nan gidan za a kawo min Amarya muyi ta love a gabanki muna sa Miki Rai ke ko Baki da ko Saurayi Kuma duk Dan Iskan da Kika kawo min gida zakuyi zance sai nasa anyi Raga Raga da shi Zaki sani ne,Nabeela ta kasa rike dariyarta tace In sani din Mana.

Asad yaji Haushi ya Kama masifa Ke Dan ance ma Ana son Kiss dinki har wani kyau ne da ke,idanuwansa masu mugun kyau ya zarowa Nabeela tare da furta ki kalle Ni Sarai,In Banda dariya ba abinda Nabeela keyi mamakin Iya Maganar Asad take Yi,Na fasa siyo Miki kayan gayun tunda baki da mutunci,Bakin naki ma da za ayiwa kiss Yana Ina? Ni da wahala ma zan sha ba sai na maida bakina Kamar kugiyar Ciro guga Ina lalabu lips ban samu ba Dan mitsili da shi.
Nabeela tace a Haka kake so dai na baka Kuma Haramiyarka.
Kitchen Nabeela ta shiga tana gyarawa Text din Asad ya shigo wayarta tare da furta Baby kinki fada min sunanki Nabeela ta fada min sunanku Daya,Nabeela tana karantawa ta tura Masa Ae gaskiya ta fada Sunan mu Daya da kawata Nabeela,Nice Name cewar Asad,yaushe zamu Fara waya? 10pm ka kirani yau zaka Fara Jin Muryarta na gamsu da Kai kana da halin kirki I love you So much,Love you too cewar Asad.

Haka kuwa da Dare Nabeela,Nazia da Asad suna ta kallon Nigerian movie Amma Asad agogo kawai yake dubawa,Nabeela tana satar kallonsa 10pm nayi ya mike zai tafi Maganar Nabeela ta tsaida shi,Tun yanzu zaka Yi bacci ka Bari mu Gama Film din Mana,Gobe ki bani labari da safe Ina da aikin Yi,Yana Tafiya Nazia tace Bacci zatayi itama ta koma Bedroom aka bar Nabeela Ita Daya a Palo tana kallo tana jiran kiran wayar Asad.
Minti biyu tsakani sai ga Kiran Asad ya shigo wayar Nabeela,a hankali Nabeela ta daga tana magana kasa kasa tare da canja murya ta koma irin ta masu Iyayi Asad Bai Gane Nabeela bace a saman bed dinsa yayi wani juyi tare da Rungume pillow Kam a jikinsa,Jin Muryar ya Haifar Masa da wata muguwar kasala tare da Sha'awa me karfi,a hankali Yace Barka da dare Ranki ya Dade My Queen,Nabeela tana ta dariya kasa kasa yanda bazai ji ba tace My King Ya gida ya aiki? Lfy Alhmdllh,Kamar yanda kawata ta fada min kyawunka to Haka muryarka ma take,sai yanzu nake Jin Haushi kaina da ban Bari mun Fara waya da wuri ba Ina Jin wannan murya taka me matukar Dadi tare da Sanya duk Wanda ya jita Nutsuwa.
Kece tauraruwa ta Queen,muryarki tafi tawa ai kinji yanda tsigar jiki na ta tashi Yarrrrrrr Dana ji muryarki,kin San yanzu ji nakeyi Kamar na sato ki nayi bacci a Kyakyawan jikinki,Nabeela tace ka Kara hakuri saura kadan na zamo mallakinka Baki daya Nabeela ta Rubuta Masa tana wani Gyara kwanciyarta a saman kujera wani Dadi da sanyi take ji,Son Asad ya Dade da kamata Ashe, Bata tabbatar ba sai yau,Bangaren Asad kuwa Yana waya da Matar Aurensa Amma a zahiri zuciyarsa gaba Daya tana Kan Nabeelan Nazia ya Rasa dalili,sai da Suka raba dare suna waya da juna har bacci ya kwashe su ba tare da sun sani ba.

Washe Gari da Sassafe Asad ya dawo daga Motsa jiki sanye cikin kayansa na motsa jiki farare tas,Kitchen ya Shiga ya dauki Fresh milk yasha tare da Fitowa zai Haura sama ya iske Nabeela tana ta baccinta a saman kujera alamar a Nan ta kwana,Murmushi yayi tare da furta kallo yayi Dadi da kayan jikinta tayi bacci a Palo,Tsugunawa yayi a gabanta ya kafe Fuskarta da kallo Kamar zai cinye ta,Babu dankwali a kanta gashinta ya karewa kallo me matukar kyau da santsi ga wani duk ya kwanta a saman goshinta,Hancinta ya kalla ya birge shi tare da gashin idonta da girarta,jajayen lips dinta ya Shiga karewa kallo,Hannunsa yasa a saman gashinta ya shafa kadan sannan ya daura Yatsansa a saman Lips dinta ya shafa suna birge shi,Doguwar Rigar Atamfa ce Batik a jikinta brown color,Kirjinta ya karewa kallo, wani irin yanayi ya Fara tsintar kansa,Mikewa yayi ya Haura sama tare da shigewa toilet domin watsa ruwa a jikinsa.

Nabeela da Asad Haka Suka kasance ko yaushe daga sms chat sai Waya sun Shaku da juna sosai Asad Bai San Nabeela bace,Waya iPhone me tsadar gaske latest da Computer laptop sai wayar Samsung me tsada ya siyo,Nabeela ya iske a bedroom dinsu tana Gyara kayan Nazia, manyan Ledoji ya ajiye a gabanta ya zaro iPhone sabuwa dal da laptop Yace gashi na Budurwar da Zan Aura ki Kai Mata,Ga Kuma Taki wayar Samsung tunda Baki da Saurayin da zai siya Miki ,Murmushi tayi tana ta Masa Godiya Asad Yana Mata gorin Saurayi,washe Gari da wuri Nabeela ta shirya ta dauki Phone da laptop ta fita a zuwan ta tafi kaiwa Budurwar Asad,Gidansu ta wuce Direct ta Iske Safiyya tana kwance a gindin Bishiyar Gidan tayi wani malaho kamar Almajira da Alama yunwa ce ta sa hakan,Duk ta wani Rame ta bushe ta sake yin Baki sosai,Hajiya Binta kuwa tana dakinta ta kwanta saman kujera tayi Shuru tana tunanin me zata samu ta sa a bakin Salati,Nabeela kallon Safiyya tayi tace Umma Nkeci ya Naga gidan naki kayau ne? Hajiya Binta ce ta fito da sauri tace Dan Allah ki bamu kudi ko Garri da sugar mu Sha,yau wajen sati Daya kenan bamu dora tukunya kullum sai dai mu Sha Garri watarana ma garin bama samu,Gashi Hashimu kin San bashi da sana'ar rike mu,wlh an cuceni dama an San baza a iya rikeni ba aka Aureni? Da gata na da komai,Safiyya duk masifarta Shuru tayi ta cikinta takeyi,Tausayi Suka Bata musamman Abbanta tunda tasan da shi ake Wahalar,Nabeela tace Ina ruwana kufa kuka ce akan na ciyar daku gwara Kun Sha Garri yanzu Kuma zaku Zo ku dameni,to ba wannan ne ya kawo Ni ba ragowar kayana nazo dauka,Abba ne ya fito daga Bayi,Shima lakwas yayi kamar zai Fadi sabo da yunwa,Nabeela Tausayinsa yasa ta zaro dubu Ashirin Cash ta mikawa Abbanta,ba tare da ya kulata ba ya karba,Dama Albashinta ne Asad ya Bata ta kawo Masa Tasan Yana wani Hali,Tafiyarta tayi tare da kallon Safiyya tace Nkeci Kinga rayuwa ko? Ai yunwa ba Kanwar Murja bace Kanwar ki da zata daga Miki kafa ita yunwa Bata da hankali kuma Dole kici arzikina ko yunwa ta hallaka ki tana fadin Haka tayi waje abinta Basu ce Mata komai ba yunwa ta cinye su.

Ajiyar laptop da wayar Nabeela ta kaiwa wata tsohuwa Iya me koko,suna shiri da Nabeela har tarin kudi Nabeela ke Yi a wajenta,Nan ta Kai Mata ta ajiye sannan ta koma Gidan Asad,tana Zuwa ta Iske Asad da Nazia suna ta kallon Kaya sababbi English wears da dogayen riguna readymate etc takalma da sauransu Asad ya Siyawa Nazia akwati biyu masu tsada,Nabeela Tasha kallo kuma taji Dadi sai Godiya take wa Asad yace akwai wasu na Hausawa na bayar a dinka Mata suna wajen tela tare Muka je aka Auna ta,Nazia tace Aunty Kala Sha biyar Atamfofi da lace harda shadda da materials,Nabeela tace Masha'allah Zaki Sha wanka Nazia,Asad yace ya kin Kai Mata ta yaba? Nabeela tace sosai ma tace Gobe ka Fara zuwa zance Amma gidanmu zaka je a can zata Yi zance kasan makwafta ne gidansu ba wajen yin zance,Asad Yana murna yace Allah ya kaimu.

Washe Gari da wuri Nabeela ta dauki Nazia Wai zasu je gida gaisar da Abba,Da Yamma 5pm Asad yasha wanka cikin Sabuwar shadda ta gaske ka rantse Ango ne,Motar ma da zai hau sai da ya kaita aka sake wanke ta,Ya fito Yana zuba Kamshi cike da Nishadi,A hankali yake tukinsa har ya Karasa gidan su Nabeela yayi parking,Lokacin Nabeela Tasha sabon Dinkinta lace sea blue takalmi da mayafinta iri Daya da kayan taci kwalliyar da Bata taba Yi ba tayi kyau karshe,a waya ya Kira Budurwarsa da zai Aura Nabeela ta daga Kiran Kirjinta na dukan uku uku,Safiyya tsoro ya kamata karfa a hankali Nabeela ta sake dawowa gidan taga tana ta zuwa ko yaushe,Tsaki Safiyya take ja tana jefarwa da su Nabeela maganganu,Wayar Asad Nabeela ta daga cikin Muryarta da take canjawa ita a Dole Wata ce ba ita bace,My King ka karaso? Ae Ina kofar gidanku,Nabeela mayafi ta yafa kirjinta na dukan uku uku ya zasu Kare da Asad idan yasan ita ce? Haka ta Daure ta fita har jikin motarsa.

Asad yasha mamakin ganin Yanda Nabeela Tasha wanka Haka tayi kyan da Bata taba Yi ba a duniya,kasa dauke Idonsa yayi daga kanta Yana Jin wani irin yanayi a jikinsa,a hankali ya sauke glass din motarsa yace kinyi kyau fa Yan Mata Kira min sanyin Idaniya ta,Nabeela tayi Murmushi tare da jajircewa tace Nice Ai Budurwar taka,nice na Dace dakai sabo da baka san waye Kai ba,baka San danginka ba,Babu wata me Iyaye wacce Kuma Iyayenta ke sonta zasu Bari ta aure ka,sai Ni Nabeela Hashim sabo da nice dai dai Kai,Ina da Uba Amma Baya Sona,Bai damu Dani ba,na tabbata ko waye na Kai Masa matukar musulmi ne Bashi Ni zaiyi tunda dama ya gaji Dani baya bukatar ganina kusa dashi, Hawaye ne ya kwararo saman kumatun Nabeela,Tace bani da gata tunda Har Ubana ya iya barin mace baliga iri na zauna a gidan Gwauro Wanda baida Mata bare iyaye,gidan da ake kawo Mata Ana shaye shaye,Na zauna daga Ni sai Namiji Wanda cikon namu shedan ne,Hawayenta ta share tare da Furta Asad ba Wasa nake ba wallahi nice Budurwar taka,Boye maka nayi sabo da mu Dan Shaku da juna.

Idan Baka so na Zaka iya fada min Nima dama ba damuwa nayi ba,kawai Naga da Zaman Da nake tare da Kai a banza gwara na Aure ka tun kafin Shedan ya shiga tsakaninmu,Asad Murmushi ya saki sannan yace ai nasan kece Matar Nabeela,tunda Kika fada min kin samo matar nake bibiyar me kike Yi,Ban tabbatar kece ba sai da Kika bani Number akan Muna chat da ita na Fara zarginki,Watarana kina kitchen kin manta wayarki a Palo lokacin na gwada Kiran wacce muke chat da ita abin mamaki sai wayarki tayi Kara kusa Dani,sai da na gwada Kiran sau Uku na tabbatar wayarki ce,na dauka nayi searching Text naki Naga chat din da mukeyi,kyaleki nayi Naga iya gudun ruwanki,Amma ko Dan gaba Ki sani Asad ba sakarai bane,Duk da Ina cikin wani Hali na lalura ki kula Asad na daban ne.

Sannan ki sani Nabeela ba Haka kawai Zan aure ki ba kawai Ina sonki ne ko sanda Kika ce Zaki hada Ni da kawarki naji haushinki sosai sabo da Ni ke nake so ba kawarki ba,Karki ji komai Kuma a shirye nake da a daura Mana Aure sabo da Haka sai ki daina wahalar da kanki shugo mota mu tafi gida Amma yanzu ki fadawa Abbanki jibi za a kawo kudin Aure.

Shuru Nabeela tayi kunya da mamaki sun cika ta,tana tunanin ta rainawa Asad hankali da yawa Ashe shine ma yafi Raina Mata hankalin..
Gidansu ta koma ta samu Abba a dakinsa Allah yasa ba kowa tace Abba na Samu Mijin Aure jibi Asabar zasu kawo kudin Aure,Babu tambayar waye bare bincike Abba yace Allah ya kawo su na bada ke na huta ki daina sintiri a gidana,Karaf Safiyya dake labe tana Jin komai tace Waye Zaki Aura Mene aikinsa?

Wayon Safiyya taji wa Nabeela zata aura Idan me kudi ne ta tafi gidan Malam ta sa a raba su,Kamar Nabeela ta sani ta ambato Baban Safiyya Mahaifi tace Isyaku me Kifi shi Zan Aura,Safiyya ta Bude Baki ta Fara zage zage,Nabeela ta mike zata bar gidan tace Kinci kin koshi ne shi yasa Amma jiya Dake kin kusa mutuwa da yunwa ai Baki ce komai ba,to na fada Isyaku me Kifi Shi Zan Aura Kuma naje nayi kishi da Uwarki Asabe tayi waje tabar Safiyya a tsaye Kamar wata bishiya.

Asad tabi tare da Nazia Suka koma gida Babu Wanda yayiwa Dan Uwansa magana har suka je gida,Tun daga wannan Rana su Nabeela Suka ci gaba da chat dinsu har waya kuma suna gida Daya tare suke yini ma.
Da Yamma suna Palo Kamar kullum suna kallo Asad ya kalli Nabeela yace kowa ya shige room dinsa muyi waya,Nabeela tana Dariya ta mike tayi cikin room dinsu,Asad ma ya shige room dinsa aka bar Nazia ita Daya a Palo tana kallo,Asad ne ya Kira Nabeela Suka dinga waya Har sai da lokacin Sallar magrib sannan Suka hakura,Cikin dare Kuma kusan kwana sukeyi suna chat,Asad Yana kwance a saman Bed dinsa Ya turawa Nabeela text Kamar Haka
Fito mu hadu a Palo,hijab ta saka tare da fitowa ta gashi shima ya fito ,guri Suka samu tare da Zama,Asad yace Yau fa an Kai kudin Aure dubu Dari,Nabeela tace Haka Abba yace dazu naje gaida shi,a Ina ka samu Iyayen da suka Kai? Baban Aliyu da Mu'azzam ne Suka Kai Amma Abba yace shi Ranar Asabar zai daura Auren Kinga ko sati fa baza mu Kara ba mun Zama Mata da miji,Nabeela tace Hmm kuma kasan bazai min Kayan daki ba Bai tanaji komai ba sabo da bani da gata shine za a daura kawai a barni ko cokali baza a siya min ba Nabeela ta Furta tana kuka tace an sa Ranar Aure kwana Biyar ban taba jin Haka ba sai a kaina marar gata,Ba abinda za a Yi min ko gyaran Amarya babu.

Tausayi ta bawa Asad sosai ya Shiga Bata hakuri Yana nuna Mata muhimmancin iyaye da hakuri Har ta daina kukan,yace je kiyi bacci Good night Nan suka rabu kowa ya tafi makwancinsa.
Kafin biki Alex ya canja komai na gidan ya dawo sabo Dal har furniture ya Sa komai na Alfarma na gani na fada,Babar su Aliyu ya bawa kwangilar hada lefe,Sai da aka Hada Akwati guda Tara cif aka Kai Gidan su Nabeela,Biki saura kwana biyu Nabeela Suka tattara ta koma Gidan Abbanta a dakinsu ta zauna,Asad kudade masu yawa ya Bata na gyaran jiki da duk abinda zata siya,da kayan da zata sa a biki,Su Safiyya sai bakin ciki sukeyi komai Na Nabeela abin birgewa,Gashi Basu Isa su taba komai ba Inno yayar Hashim sunzo da su ake komai.
Su Zeena duk dasu cikin kawayen da aka gayyaya Wedding Dinner,Nabeela ta gayyaci kawaye masu Uban yawa,Haka Asad ma su Aliyu sun gayyato nasu masu Uban yawa sai

Please Login or Register in order to submit comment