Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[5/9, 9:55 PM] Sis Asma: 🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠
COPY BY ZAINAB BULATAWA




FREE PAGE







BISMILLAH






1







Official






By
AsmaBaffa








INA GODIYA GA ALLAH DAYA BANI DAMAR SAKE RUBUTA SABON NOVEL,ALLAH YASA MU GAMA LAFIYA.

MASOYANA INA MIKO GAISUWA DA JINJINA ALLAH YA BAR KAUNA.




LITTAFAN DANA RUBUTA SUNE KAMAR HAKA

GASKIYA CE
MARAICIN RAHMA
MA'AIKACIYAR GOMNATI
CIRANIN AMANA
DUK INDA TA FADI
KAMARSU CE DAYA
KASUWANCI NA
JIN DADI SABO
HADIN KAI
ME MAGANI
TUBABBIYA

NA KUDI SUNE

RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDU'AR KAWA.
GIDAN GWAURO.......






Ga masu bukatar siyen wannan novel ko wanne complt dari uku 300 ne.
RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDU'AR KAWA

GIDAN GWAURO
masu bukatar shiga Group dinsa dari biyu 200 ne.

Masu siya ta Bank ga Accnt number

0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gt bank.

Masu tura katin waya ta whatsApp, Vtu ko Transfer ga Number ta
08033933642.

'YAN NIGER ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39.







Wannan page na masoyana ne Wanda novel Dina baya wuce su,Na Gode Allah ya bar kauna Musamman masu
Nemana Ina na shige.










Lokacin Damuna ne Gari yayi Dadi tare da sanyin Ni'ima,Iska tana kadawa kadan Kadan,a wani daji cikin wani Kogon dutse Wani ya fito kafarsa daure da sasarin sarka a Kafafunsa da hannayensa,Cike da rangaji Yana tangadi kamar yasha giya, a hankali yake iya tafiya Kafafunsa sunsha Dauri Har jini suke fitarwa,a hankali ya fito Yana rumtse Ido sakamakon Rana ta haske Masa Ido da yawa,alamar ya Dade Bai ga hasken Rana ba,cikinsa ne yayi kugi alamar yunwa,Ya Rasa Ina zai je a cikin Dajin,Jikin wata bishiya ya koma tare da kwanciya ya lumshe idanuwansa masu matukar kyau,Yana nishin yunwa kamar zai mutu.

Wata tsuntsuwa ce tayi kuka ai da sauri ya Ware daradaran idanuwansa a kanta,cikin Zancen zucinsa yace kwadayinta nake ji,harshe ya zaro tare da lasar jajayen lips dinsa Yana so yaci tsuntsuwa Amma Kash ba halin hakan, kwadayin tsuntsuwa yasa Ya Fara kokarin Balle sasarin dake Hannunsa a Dole sai yaci tsuntsuwa,idonsa yayi jajir sabo da yanda ya dage shi fa sai yaci tsuntsuwa Yana Haka yaji takun wani mutum a bayansa,da sauri ya juyo suka hada Ido da wani Babban Baushe masu farautar namun daji.

Baushen yace Samari waye ya daure ka haka? Daga Ina kake? Kyakyawan Saurayin ne ya bi Baushen da kallo,A zuciyarsa Yana cewa ko wannan sune mutane Yan Adam? To idan sune mutane Ni mene kenan? Baushen Ganin Saurayin Yana Maganganu shi kadai sai yace yaro ya sunanka? Kyawawan hakoransa ya bude jerarru kanana dasu farare tas yana Murmushi me matukar kyau,Baushe yace Kai yaro ko daga kasar larabawa akayi kidnapping dinka? Ko Kai Balarabe ne Wanda suke zuwa Nan aiki aka sace ka? Da gani Kai Balarabe ne sak hasken fatar da komai har gashinka na larabawa ne ya abin yake?

Matashin ya Rasa me zai cewa Baushen yace Ae kawai,Baki Baushe ya washe yace ai da ganinka kalar Hutu da Jin Dadi ne kalar Naira ne,Hannu ya mikawa Baushe alamar ya kwance Masa sasarin dake daure da shi,Ba musu Baushe yasa Karafansa yayi dabara ya sare sasarin har na Kafafunsa,Murmushi Matashin yayi na Jin dadi yace Na gode Sunana Alex,Baushe yace Uhm da ganin Sarkar Dake wuyanka an San Kai ba musulmi bane, ba komai ka mike wannan wannan hanyar zata kaika har babban titin Kaduna.
Matashin tafiya yaci gaba da Yi a hankali Yana tangadin yunwa.

A Haka Yana tafiya har ya Fara hango motoci suna yawo a Kan titi,gashi yaga wani kauye kusa da titin yace wato wannan sune mutane,Cikin kauyen ya shiga Ana ta kallonsa musamman kayan jikinsa masu daukan hankali,farar shadda ce dinki na Yan gayu cif cif jikinsa,Da wata sarka ta cross tafkekiya a wuyansa wannan ya nuna Christian ne ba musulmi bane,a jikin wata bishiya ya zauna Yana faman kallon duk abinda mutane sukeyi Yana Murmushi a hankali ya Furta dama Haka mutane suke abubuwansu gaskiya Nima sai na koma mutum Kamar su,Ruwa ya gani a rijiya Ana ja,har wajen ya taka yaje wani dattijo ne ya zuba a karamin kwano ya Mika Masa yasha ya koshi.

Tun daga wannan Rana Alex yake zuwa cikin kauyen kullum ya Sha kallon yanda mutane suke abubuwan su sai ya koma dajin Daya fito cikin Kogon dutsensa yayi ta gwadawa Yana koyon yanda mutane suke yin komai,Har Sallah yake gwadawa Amma Bai sai me akeyi ba ko ake cewa.
Abinci kuwa sai dai ya Kama tsuntsuwa ya gasa abinsa a dajin yaci,idan Kuma Bai Kama tsuntsuwa ba sai ya shiga kauyen ya tambaya a wani gidan a bashi yaci ya Kara gaba yayi ta Amai,ya rasa me yasa idan ba Nama yaci ba to Amai yakeyi har da Zazzabi,a Haka Har mutane Suka Fara ganowa Alex ba kalau yake ba amma ba Wanda ya kula shi,Yau ma Kamar kullum gani yayi Ana ta cin Abinci da cokali a Majalisa,yaga wasu Kuma da Sassafe suna motsa jiki exercise,ai komawa yayi daji ya dinga gwadawa sai da ya iya,har cin Abinci da cokali Haka ya ya dinga gwadawa da tsinke,har wanka sai da ya koya,Wasa Wasa sai ga Alex ya kwashe wata Biyar Yana koyon abubuwan da mutane suke Yi shima ya iya komai,Yaji kullum Ana Zancen kudi Amma ya Rasa mene kudin Nan da kowa yake magana kudi,sai na Samu kudi,ya gaji da jin Maganar kudi, ya kasa ganewa har ya yanke hukuncin tambayar mene kudi Wai.

Cikin kauyen ya shigo da Sassafe ya Fara tare wani Babban mutum yace Malam Ina da tambaya,Mutumin ya tsaya Yana jiran tambaya,Alex yace Wai Mene kudi ne? Naji Ana ta cewa kudi kudi Mene Wai kudi? Baki Bude mutumin ya kalli Alex lafiyayyen mutum zai Raina Masa hankali,tsaki yaja yayi tafiyarsa,Haka Alex yabi Wani Yana tambaya Babu Wanda ya saurare shi ma sabo da suna ganin ya Raina musu hankali da yawa,Da kyar ya samu wani Almajiri yace Masa malam kudi sune abinda ka siyi Shaddarka da su,kudi ake bayarwa a mallaki Abu,Alex yace mene mallaka? Uwarka ce malam cewar Almajiri,yace wayarka gata Nan katuwa a Aljihunka Ina gani itama kudi ce,Tsayawa Alex yayi Yana magana shi kadai waya Kuma? Aljihu? Yace ya kamata na shiga birni inda ake da wayewa a can Zan samu amsar tambayoyi na sai na koma mutum Nima.
Tsaki Almajiri yaja yayi gaba daga Nan Alex ya dauki Hanyar Shiga cikin garin Kaduna cikin birni Babba.

Dattijo ne ya kwada sallama a gidansa yace Ina Nabeela take Dan Ubanta yarinyar Nan Bata da mutunci Ni wallahi da Zan samu wani tsohon tuzuru Aura Mata shi zanyi,tabi ta Gama zubar min da mutunci a Unguwar Nan,Shekarun ta sun Kai ashiri taki fito da Mijin Aure so take sai kwayayen Haihuwarta sun Kare sun mutu a gida ba Miji,ace ban Isa da yata ba Ni Alhaji Hashimu na Haifi yarinya a cikina tafi karfi na,Kina gani tana Gama makarantar Secondary tace baza ta ci gaba da karatu ba ita Business zata Kama,har jari na Bata Amma ki duba kullum itace gantali da yawo gida gida,to gashi can ta tafi yawo ta bar kayan miyar a tabir dinta akuyoyin makwafta sun Zo sun cinye tumatur da Allayyahu tas, Baki Dattijuwa ta tabe tare da Furta Oh Ni Safiyya da ace Uwar Nabeela tana da Rai da tuni bakin cikin Nabeela ne zai Karasa ta,duk da kishiya ce kar ace na Fadi sharri,kasan Dan da ba naka ba.

Karar machine Suka ji an shigo gidan da Gudun tsiya,Baban Nabeela ne ya kalli me machine din sai ya ga Nabeela ce goye da kanwarta Yar Shekara bakwai a duniya a bayanta ga Kuma Kaya cikin katon buhunta,Babanta baiyi mamaki ba sabo da yasan Yarsa Nabeela ta iya abin Hawa kala kala,ta iya Keke,ta iya machine tun daga su Jin Chen,kanchen bare Kuma wani lifan da mota ta iya a garin yawonta da gwagwarmaya da Shiga cikin maza,Bata da tsinke Amma yanzu zaka ganta saman Machine,Keke ko mota ta mutane abokanta maza sabo da shige chigenta,Har a mota felleliya zaka ganta ciki tana tukawa ta aro.

Sakkowa tayi tare da sauke Yar kanwarta ta ajiye ta a saman Tabarmar da Babanta ke kwance,sannan ta koma ta dakko katon buhun data shigo dashi saman Machine ta ajiye a gaban Babanta tana huro hanci kamar zata doki mutane,Sabo da sun San halinta Babu Wanda yayi mamaki har Matar Babanta Safiyya,Daga tsaye tace yawwa Abba ga fa Shinkifa aiki nayiwa wata Hajiya matar custume kasan akwai Naira,tace kudi zata bani nace Ina ai yanzu ta ciki akeyi a kasar Nan, ya za a ci Abinci kawai shi ake nema,Tace to me Zan Baki a kayan Abinci? Abba me aka Fi ci a kasar Nan? Abba yaga harka zai huta tuni ya manta da fadan da yake faman Yi da sauri yace Shinkafa Yar Abba ai itace abinci gidan talaka da me kudi,Dariya Nabeela tayi tace to shinkafa ce Abba ka canka, kwano goma ce gata Nan nasan zamu Dade Muna ci sai muji Dana cefane, 'ya Daya tamkar da goma an gaisheki Nabeela Ina Nan Ina fada kin bar kayan Miya a waje awaki sunci wani sai Ni na Ebo shi na shigo gida dashi Ana ta zuwa nema za a siya Ashe Yar Albarka kin tafi Nemo Mana Abinci.

Abba yaci gaba da Yabon Nabeela Shi yasa Ni dama can Allah ya Dora min sonki yata,gaki kin gado Mahaifiyarki zam ita Yanda take Kyakyawa Yar fulani Haka kike kema gaki jajir,idan na kalleki sai na tuna da ita,Ai idan Zan auri Mata dari to fa Bazan manta da Aisha Mahaifiyarki ba,Gaki da zafin nema,Nabeela taji Ana ta yabonta ta kwala ihu Eho Abba Dadi kashe Ni,Sanda ta Suro tana ta radar katanga da duka Wai tsuminta ya tashi,Abba Yace Chau chau Yayar Zaina,Nabeela Hularta ta gyara Wata katuwa irin ta Yan achaba tana ta dariya da kyawawan hakoranta reras farare tas, Safiyya matar Abba Baki ta tabe tare da Furta anji kunya mace ba aji sai Abu irin na maza,ba birgewa Kika Yi ba Dan kinyi Bara da maula an Baki shinkafa,Kai Kuma ba kunya kana wani yabo baza ka manta da Uwarta ba munafuki ai sai kaje ka dawo da ita daga lahira algungumi,Nabeela ta kalli Safiyya shekeke tace Bata ke nakeyi ba,ai ke minus ce a gidan Nan,ki duba Abba badan Kaddara ba me zaiyi da ke kafafu hagu a dama-dama a hagu.

Kyaleta Nabeela Hassada ce kwana Nan Zan Mata kishiya,Abba Allah zaka Kara aure? Kwarai kuwa ai rashin kudi ne yasa da tuni na Kara,karka damu Abba Zan tayaka neman kudin wlh sai kayo Amarya,Tsaki Safiyya taja ta shige daki abinta ta bar Nabeela da Abbanta suna ta Zancen Auren da Abba zaiyi suna lissafa nawa za a kashe a bikin,Nabeela tace Abba ka Fara zuwa zance asusu na ya kusa cika ka samo bazawara ta kirki,Aiko Abba yace Ina da ita ma kwanan Nan ta dawo daga Makkah takari ce a gidan larabawa tayi aikin Abinci take musu girki sunanta Hajiya Mairo, Lallai zamu kwashi girkin larabawa a gidan Nan,Abba yace Har tuwon dabino ta iya,Idan ta zuba Miki miyar Habbatussaudat sai kunnenki yayi ringing inda kisan wayar cellular Haka Zaki ga Yana kadawa,Dariya Nabeela tayi tace dole lafiyarmu ta karu tuwon dabino ai ba Wasa ga miyar Habba Tasha nama kaga karyar aljani yazo gidan nan,ai konewa zaiyi kurmus to Habbatussaudat ta ratsa jininmu cewar Abba.

Zaina ta Kama ta mike tayi Mata wanka tare da shiryata da kanta ta kaita Islamiyya sannan Nabeela ta dawo tayi wanka ta shirya cikin Doguwar Riga ta Atamfa Red tare da yafa mayafinta ba dankwali sai Hularta irin ta Yan achaba ita ba pcap ba Bata ta Yan tauri ba,Mayafin Yana kanta ta kifa Hularta sannan ta leka dakin Abbanta tace Abba na tafi nema,Zan Saro kayan Miya a kauye a machine din Saad zanje,to Allah ya kiyaye a tsare mutunci a Kama Kai Dan Allah,Karka damu Abba garau nake Babu Wanda ya Isa ya kawo min hauka kasan yanzu na kafce shi,Babban yatsa Abba ya daga Mata da kyau.
Lifan din ta haye dogon wandonta ya bayyana kadan,Fisgar machine din tayi ta fita a dari,Tana ta Wasa a titi da machine motoci kawai take yankawa tana wucewa,Duk Inda ta wuce sai an bita da kallo tana birge mutane da mamaki mace ke ganganci Haka,a Danger ta tsaya wani ya leko a mota Yace yarinya kibi a hankali,Juyowa tayi tace Iyayena suna min Addua,Lafiya na rabu da uwata babana da Zan fito sai da ya zuba min Addua munafuki Ina ruwanka Dani rayuwarka ce ko tawa dan shishigi,Duniya ce cewar driver,Kai a lahira kake? Dama duniya ce Mana Kai Malam Ni fa ko Tsine min kayi baza ta ci Ni ba,iyakaci kace Zan Sha wahalar duniya to me yayi saura dama a cikin wahalar nake me Kuma Zan gani sabo? Neman da nakeyi da gwagwarmaya Kai wlh bakayi baza ka iya ba ,Driver yayi mukus Nabeela ta fetse shi tas Ana ta dariya,sabo da ya gani ma Bata ji fadansa ba sai ta daura kafa Daya a saman machine dinta tana tuki da kafa Daya Haka take tafiya harda kallon driver tace maganar Ubana kawai nake ji sai Kuma fadan duniya ka Bari duniya tayi min fada Kai baka Isa ba Dan titi Dan kwararo da Kai.

Sai da Tayi nisa sannan ta sauke kafarta dayar ta daidaita zamanta har ta shiga kauyen Kaduna,tana tafiya a cikin gonaki da buhunta na siyen kayan Miya,Matashi Wanda yace sunansa Alex shi ta hango kayansa Sunyi dirty matuka kamar Mahaukaci ga katon cross a wuyansa sai Dan Karan kyau kamar shi yayi kansa fari tas da shi.

A gabansa ta tsaya da machine dinta ko kulashi ba tayi ba Amma kyawunsa yasa ta kasa daina kallonsa,A hankali tace Kai Ina masu gonar Nan? Na'am Uhm me Kika ce? Kai Ina masu gona? Mene gona Kuma? Harara ta Balla Masa tare da Furta kaga kazami da Iyayin tsiya Wai Mene gona,A fusace tace gona nace idan ban saka wankin Bishiyar can ba shegiya nake sai nasa ka wanke katuwar Bishiyar can da ruwa da soso tas, Harara ya watsa Mata tace wannan da gani Dan duniya ne Dry Eyes kawai,Yana tsaye har masu kayan Miya Suka Zo a gabansa yaga ta siya anyi ciniki ta biya kudi abinda yake ta Neman sani me akeyi da kudi yau ya gane me akeyi da su,Rokarta yayi yace pls tafi Dani Cikin city, Bata Yi musu ba ta daura kayan miyar a gabanta shi Kuma ya hau bayanta.

Taja suka tafi da yaji machine ya Kada kamar zasu Fadi sai ya zura hannayensa ta cikinta ya rungumeta,Nabeela tana Jin Haka tace Zan ci Uban yaro da sauri ya janye Hannyensa ya maida su saman kafadunta ya shako wuyanta,idan ban sauke ka ba Allah ya Tsine min kwarto ne Kai? Ko kula ta baiyi ba ya sake Rungume wuyanta Yana Jin tsoro,tana ta faman cewa Zan ci Uban yaro idan Bai sakar min wuya ba,Jin ta Ishe shi da masifa sai ya saki Nan ya koma da hannun ta cikinta,Hannu Daya tasa ta yakushe shi.

Sai ya janye ya koma da shi kirjinta Jin Nan yafi Dadi sai ya kankameta sosai yaki saki,Nabeela ba irin zagi da yakushin da Bata Masa ba yaki ko kulata,Sun Fara shigowa cikin Gari ta tsaya a hanya tace sakko Dan Iska tsohon gwauro a Nan Zan barka,Ba musu ya sauka,Tsaki taja yace pls Ina da tambaya,Tausayinsa taji tace Mene ne? hannu yasa a Aljihunsa ya zaro Atm card dinsa yace ance min kudi ne a Nan pls a Ina Zan Kai na samo kudin? Nabeela sarkin son kudi ganin Atm card sai ta washe Baki tace na Zama kawarka daga yau,Zaka Zama Aboki na? Kai ya daga Mata,Hannu ta Mika Masa tace to Give me five mu tafa,tafin Hannunsa me kyau da laushi ya Mika Mata ai ko Suka tafa tace harkar kudi ba ruwanta da musulmi ko Christian,Atm card din ta karba sai taga ansa sunan Alex Benedy
Nabeela tace ka tuna number din da ake sawa a cire kudin? Pin dinka? Alex yace Ni ban sani ba,bazan iya tunawa ba,murna ce ta koma Cikin Nabeela tace Wai Kai Mahaukaci ne? Ko Dan Shan jini ne? Ko me yasa ka manta komai? Ko Kai ba mutum bane? Da sauri yace yeah Ni ba mutum bane dama burina ya zanyi na koma mutum rayuwar biladama tana birgeni shi yasa Zan koya,Tsoro ya shigi Nabeela ko dai Aljani ne shi, a fili tace ko Aljani ne sai na karu da shi sai na ci kudinsa ba ruwana,shi ma Aljanin ai ana kulla alaka dasu wayo Zan Masa,Abba Sabuwar Amarya ta taho a satin Nan zaka rangado Amarya muci tuwon dabino Malam.

Tana duba bank din taga Gtbank ne, tace hau machine mu tafi Yau ko zaka mutu sai ka tuno pin din Nan,Ba musu ya sake Hawa Bayan machine dinta Yana Murmushi,Dake kudi Nabeela ke so ya dafa kafadarta Amma Bata hanashi ba Bata ce komai ba,Wuyanta ya Rungume da Hannayensa biyu suka bi ta kofar gidan su Nabeela,Abban Nabeela Yana kofar gida Yana aikinsa na gyaran takalma sai ko yaga Nabeelansa da katon saurayi a bayanta ya Rungume wuyanta sun wuce a tamanin fit kamar Walkiya,Dan Kar Abba ya gane ta,Mutane suna ta kallonsu an Gane Nabeela ce ta Fara Zama Yar iska abin nata ya Fara girmama mutane da zargi.
Sai da taje Wajen abokinta Sa'ad ta tsaya tare da sauke Masa Buhun kayan miyar ta tace ka Kai gida a ajiye min kace da Abba Ina office din Yan Hisba sun kamani Ina gudu a wajen Cin abinci inda ake Kama Mata,Kace Masa Kai ka siyo min Kayan miyar ma,karka sake kace da Abba nabi ma ta Nan layin,dariya Sa'ad yayi yace ya fa ganki wlh Yana kofar gida ya uba zai kasa Gane Yarsa,Business ne ya taso min Kai ka sani Dalla kaje ka tsara Abba juyin duniya kace ba Ni bace,kaima Zan baka kasonka wani kudi zamu curo da wannan.
An Gama Nabeela sai Kun dawo cewar Sa'ad.

Machine ta fisga suka Kara gaba da Alex Yana Bayan machine tana ta tsinka gudu tana cewa kayi sauri ka tuna yanda kake cire kudi da,Okay ya Furta Yana ta faman tunani har Suka je wajen Atm machine.

Bayan sunyi parking sai da ta Bari ba kowa a wajen sannan tace muje,Fadi pin din ka tuna? Yace no na kasa tunawa,Wani wuri ta nuna Masa ya zauna tace relax,ka nutsu ka kwantar da hankalinka Zan taimaka maka ka koma mutum irinmu, maza tuno pin din,Mutum da tunani aka sanmu, Allah ya bamu daraja da baiwa yawwa maza ka Lula da kwakwalwarta tunani,Ina Mummy dinka? Daddy fa? Yawwa maza tunanoooooo su maza,tafi ta Fara Yi tana tsalle a gabansu yawwa tuna maza ka tuna kanwarka yanda take Wasa Haka girgiza ta Shiga Yi tana ta tsalle yawwa maza tuno yeeeee.......yiiiiii......da kallo yake binta Yana ta dariya yace Lallai ku mutane abin dariya ne daku, share shi tayi taci gaba da Rawarta da tsalle tana sai ka tuna eh...eh...eh...yawwa maza...pin....ka tuna ma'aikatanka? Wanda kake bawa kudi,Zuwa tayi ta Fisgo Hannunsa ta kaishi jikin Atm machine ta zura card din a ciki ta Kama Yatsansa ta Danna suka ce pls enter you pin,Da Yatsansa ta shiga Danna wrong tana cewa tuno Dan Allah Kar a Kama mu,Ka tuna sanda kake dannawa Haka....ta Kama Yatsansa tana ta dannan keyboard din,Wani dogon tunani ya tafi zirrr sai ya hango can baya lokacin da yake cire kudi,Amma 5 Daya tal ya iya tunanowa,Yace yes na tuna daya 5 a farko,Yesssssss Nabeela ta furta tana dariyar murna harda tsalle za a ci kudin bawan Allah,Biro ta dakko ta Rubuta 5 a jikin wani Yar jotter, yayi yayi ya tuna ya kasa har dare ya musu Dole ta hakura tace,muje marar mutunci Wanda Bai San arziki ba,da gani Dakiki ne Kai a school,Kayi min asarar lokaci da tuni nayi cinikin kayan Miya,Tafi can marar Amfani Minus kawai,Sai muje na nuna maka gidan mu idan ka tuna Pin din ka dawo ka neme Ni,Atm card dinsa ya kwace ya maida Aljihu yayi tafiyarsa alamar yaji haushi ta zage shi,tunawa tayi kudi fa zata samu sai ta bishi da sauri ta riko rigarsa tana bashi hakuri,Fisge rigarsa yayi tare da hankadata ta fadi a kasa,ko kallonta baiyi ba yayi tafiyarsa,tsabar son kudi da gudu ta bishi tana ta bashi hakuri tace na daina wlh bazan sake ba,Zan taimaka maka ka dawo mutum wallahi yanzu da gaske nakeyi ka Zama friend Dina kayi hakuri kaji.

Sai lokacin ya juyo ya kalle ta tare da Furta you sure? Yesss ta Furta da karfi tana murmushi,Hannu ta Mika Masa ya kalleta

Please Login or Register in order to submit comment