Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da munir ba zan taba iya rabuwa dashi ba''kuma nasan ba aurena zaiba''tun da abin da yakeso ya samu'' to kenan ya zanyi'' ta fada a cikin zuciyar ta.


TUNATAR WA.___

Kunji fa''yan uwana mata'' hakan kenan yana nuna''rayuwar da ta dauka''ba me bullewa bace'' ita da kanta take tunanin abin da take ba daidai bane'' ''yan mata dayawa ayanzu'' wanan abin shike damunmu a kasa'' saurayi ba sonki yake ba ya nuna miki yana sonki'' ya cuceki a banza'' idan son gaskiya ne mana ya aureki''sai kuyi abin da zakuyi'' amma nan kinzo'' yazo ya zauna ya tsaraki da kalaman sa masu dadi''kin fada ruwa kin yadda'' wataran kuma sai kiji ya kai kudi'' yasamu me tarbiya ''ba ''yar iska irinki ba''to wallahi duk macan da tabari sharrin namiki''ya rudeta''wallahi ta zama kwandem'' dan sai dai nace sharrin namiki''amma ba sharrin shai dan ba dan wallahi kece shaidaniyar kanki'' Allah ya kiyaye'' yashirya'' ya tsare mana imaninmu ameen''.

Pege 5

****cigaban labari''
Munir kam yan barin guri'' yanufi gidan su abokinsa'' domin yadade be kai masa ziyara ba''yana zuwa me gadi ya bude masa get ya shiga'' parking din motar sa yayi sannan'' ya shiga ''dasallama dauke a bakinsa ya shiga falon'' Momy ce a zaune a falon'' sai anisa'' saikuma Hajiya adama'' dake tsaye ta rike kugu tana faman surfawa Momy kwan don bala'i'' .

Momy ce ta amsa sallamar''ita ko Hajiya adama'' ko kallo be isheta ba '' balle ma yayi tunanin zata amsa'' munir kuwa'' tsugunawa yayi ya tai da Momy ''' sannan ya juya ya gay da adama'' cikin masifa tace'' bansa Ni ba tsohon mubafiki'' daban wuni ba kaganni garau'' wallahi uban ka zanci'' daga kai '' har wancen munafikin abokin maka'' dannasan komeye kai kake zugashi'' shashashai kawai'' Momy kam gani tai bala'in bazai kare ba hakan ne yasa''ta kalli munir tace'' munir tashi ka je abokin naka yana sama'' Allah ya muku albarka'' ameen yace'' sannan ya mike ya nufi saman benan'' dakin Habib ya shiga ,yayi sallama'' afalo'' ya sameshi a zaune'' ya hada kai da gwywa sai huci yake'' sallamar ma ya gagara amsawa'' shiko munir karasowa yayi kusa dashi ya zauna'' ya zuba masa ido'' daga bisani kuma yace'' bross meyake faruwa ne?" Naga gaba daya yanayin ka ya sauya ba yadda na saba ganin kaba ?"Please waye ya taba min kai ?"hmm dan Allah munir ka keleni da abin da ya dameni''wai har Ni mace zan na fada tana fada'' metstsssss yasa ki tsaki''ya daki hannun kujerar sa da karfi'' yace oh my god'' munir Ni?" Am sorry bross kada wannan abun ya dameka'' kaine haba daya bakason harkar wayewa'' danine tuni abinnan ya huce'' a gurina''kaga abokina kwa kwantar da hankalin ka'' bari na kira wata baby ta ''ta yaye maka da muwarka'' me kace'' mace''kuma Ni?"Ni ba dan iska bane'' kai kasani kai ma da kakeyi kaji tsoran Allah'' uhm haba bross baza ka gane ba''kaganta kuwa ta hadu komai nata''me kayau ne'' bari fa ka ganta'' hmm habib yayi kwafa ya juyar da kai'' munir dai duk da haka be kyale Habib ba'' ya dakko wayarsa'' ya bude'' yashiga neman hotunan Safiyya a wayar sa'' ko minti aya ba ayiba sai gashi ya nemo hoton safiyya'' nuna wa Habib yashiga yi amma Habib ya ki kallo yayi masa banza'' da ya gajima,sai ya tun kudar da wayar ta fadi kasa'' ta tsage'' agigice'' Habib ya sa hannu ya dakko'' yana bawa munir hakuri'' sannan ya juyo da gaban wayar nan take idonsa ya yi tozali da kekkewar fuskar safiyya''fuskar da bazai taba mantawa da me ita a rayuwarsa ba''bakinsa har rawa yake yace'' munir kasan ta ne?" Uhm nasanta mana baby na ce'' itace wadda nake cemaka zata kaudar maka da damuwarka'' murya a sanyaye'' yace'' wannan din'' to idan baka sani ba wannan yarinyar itace silar shiga ta wannan bacin ran'' kuma wallahi bazan gushe ba har saina koya mata hankali'' ashe ma karuwa ce'' ''yar tasha'' shine zata kalli tsabar idona tace min'' watakila ma kashin kare yafini'' daraja'' ashe ay gwarani da ba zina nake aykatawa ba'' munir dan Allah inason ka hadani da wannan yarinyar domin ina wulakanta rayuwar ta'' wallahi sai mahaukaci tafita kyaun gani a idon duniya'' munir taya zan samu wannan damar''


Pege 6

Nisan tawa munir yayi'' sannan yace hanya daya ce'' bross'amma gaskiya banjin zaka iya ba'' fadamin munir koma mene zanyi Indai zanga rayuwar ta a wulakance'' uhm to kawai ka auteta''takoma karkashin ikon ka ''dagan kuma saika yimata duk wani hukuncin da zakai mata'' inyaso sai ka saketa''uhmm shawara me kyau'' da feyde'' nayi niyar na biya wani kudi yayi mata'' nasan zataji ciwo sosai an rabata da budurcinta'' ashema ''yar kwaltace'' idan ma nayimata haka amemakon taji babu dadi sai dai taji dadi'' shikkenan''yaushene zaka kaini gidan su?" Yauma idan a shirye kake zan rakaka'' okay babu damuwa, kabari sai gobe ,yau zanyiwa abban mu magana, gobe idan yaso sai aje a nemamin aurenta, sanan adaura auren a lokacin, dan har na matsu na fara azaf tar da yarinyar, hhhh munir yayi dariya ya ce kai abokina, wallahi duk wan da ya tsokano ka ya san me ya tsokano, Ni yanzu zan huce'' gida, okay'' babu damuwa ka gay da su umma'' Tom zata ji ya mike har yaje bakin kofa ''sann ya juyo yace'' bross ya zakai da Anty Adama kasan dai Anisa tana sonka'' kuma sabi da kai ta dawo gidannan da zama '' wallahi da matsala fa sosai'' dan da nashigo na iske anty Adama a falon'' kasa'' tana ta surfa masifa'' .

Metstsssss'' yayi tsaki yace dan Allah munir kabar wanan zancen'' nifa banason Anisa'' na fadamata amma ta kasa ganewa'' kuma ina ruwana da masifar mahaifiyar ta'' kaga munir wallah duk abin da nace zanyi sai nayishi hankalina zai kwanta'' sai dai duk abin da za,ai agidannan ayi . okay tom shikenan ni dai kaga tafiya ta ''kadaiyi tunani sosai ...yana fadar haka ya fice daga dakin..

Shima Habib sauka yayi ''kasa be ga kowa ba a falon'' da alama dai Anty Adama ta tafi'' kai tsaye dakin momy ya nufa'' ya kwankwasa'' kofar ''daga ciki aka bashi izinin shiga'' ya murda kofar,bakinsa dauke da sallama ya shiga'' cikin Muryar Dattako Abba ya ce'' Wa, alaikumussalam'' ya amsa'' Habib shiga yayi'' ya samu guri a kasan kafet ya zauna'' yayi shiru bece komai ba'' momy ce ta kallacrshi tace'' Abee kashigo kuma kayi shiru'' meyake damun kane''kwanan nan'' uhm momy dama ''uhm dama nasamu matar aurene'' ya fada yana sosa kai'' wacece ita'' momy zan kawota ku gysa'' abee Wai ba dai kacemin Ba Anisa bace'' eh momy ba ita bace'' what to wacece''. Wallahi baka isaba'' abee ''sokake kasa adama'' ta zo tayimana hauka a gidannan'' ''yar ta kafe ta ki aure tace sai kai shine zakace mana kai baka sonta'' ita waccan wadda ka keso'' 'lyar gidan uban wace'' a garinnan'' waye ubanta abee har da zaka ki ''yar,uwarka akanta'' haba Fateema'' Meyasa kukeson yiwa yaronnan dolene''yace baya son ita Anisa din'' ba''sai ku hakura ba'' yanzu ko mace an daina yiwa auren dole, ballantana namiji'' shekara nawa muna son yayi aure amma ya ki yayi'' saiyanzu Allah ya kawo kuma sai ki hana a,a''. abee yaushe kakeson muje munema maka autenta'' Am abba gobe na keso'' sanan agiben nakeso a daura auren''to gobe kuma abee ''to Allah ya kai mu Allah ya sa albarka aciki'' bari sai na kira kawunka na masa magana '' a sawo goro da alewar daurin aure'' ke kuma fateema ki tashi ki sanar wa hjy zee ta yo mana Odar kayan daga kasar waje ''sanan kice agobe da safe muke bukata'' ita dai momy bata sake cewa komai ba sai Tom ......


Abba ne ya sake kallon Habib yace'' tashi katafi abee Allah ya maka albarka...





Pege 7


____tun a rananr da munir ya bar gurin Habib ''ya huce'' kai tsaye inda suka saba haduwa da Safiyya'' ba ,a fi ''yan mintina ba sai gata ta iso gurin'' tana zuwa ta zauna a bakin gadon shima zama yayi''ya dan kwantar da Muryar sa yace'' safiya'' tambayar ki nakeso nayi ,ina so ki fadamin tsakanin ki da Allah'' insha Allah zan fadamaka gaskiya koma meye'' muddum nasani'' okay ya fada tare da dakko wayar sa a aljihu'' ya budeta''ya shiga hotuna'' ya dakko hoton Habib ''sanan yace'' kinsan wanan?" Karbar wayar Safiyya tai tace'' gaskiya bansan shi ba Ni ban taba ganin mekama da wanan mutumin ba ko a film''ay ina tunanin irin wadannan mutanen ganin su sai ancike Form'' kokuma kaje kasashen waje'' munir kam tun da Safiyya ta fara magana'' ya gane cewa tabbas ba ita ce ta yiwa Habib ''rashin kunya ba''to kenan idan ba ita bace wace'' saliha ce'' dagowa yayi ya sake kallon Safiyya yace''kincemin kanwarki tana da tsiwa sanan bata da kunya'' ko?"ehy'' anyi haka tabbas saliha bata ragawa kowa'' uhmm yayi murmushi yace'' am Safiyya''bakece kuka hadu da Habib ba''salihace'' yanzu zancen da nake miki Habib ya kamu da soyayyar ta'' gashi ita kuma bata da kunya'' shi kuma bayason raini'' ko zaki taimaka mana akan wanan lamarin'' tunanin tafada'' tashig nazarin maganar munir'' azuciyar ta tana cewa''tabbas bazata bar damarnan ta huce ''yar,uwar taba'' dolema tayi wani abu akai'' dontasan muddum salula taji maganar nan ba yarda zataima'' murmuushi tayi daga bi sani kuma tace'' na'amince zan taimaka muku'' amma me kukeson na yi akai'' anna take munir ya fadamata duk abin da zatayi'' sanan ya sanar mata yana bukatar adaura auren agobe'' Da taso taki yarda amma daga bisani kuma sai ta amince da maganar sa'' sukayi sallama ta huce gida''.


A lokacin da ta shiga gi da bata ga saliha ba'' hakan ya na nuna mata alamun'' tatafi islamiyya'' Umman su kuma tana daki'' daman bata ga fitar taba'' batasan kalar kayan da tasaba'' wani mayaudarin murmushi tayi'' ta shiga dakin'' ta rike kugu tace''umma ina Safiyya take?" Wallahi sai nama yarinyar nan rashin mutunci'' umma kema da kinsa dagama ta kafa kawai nake''sabi da tarigani sha)ar iskar duniya'' da sauri umma ta mike zaune tace''haba saliha ke dan Allah bake gajiya da masifa ne''kidaina yi mata irin wanan bikiga yayar kice bane'' dan Allah kirage wanan halin naki gidan wani zaki'' murmushi Safiyya tayi ''jin yadda mahaifiyar su'' bata gane taba'' cikin salo irin na ''yan duniya tace'' uhm umma daman yanzu nake shirin fada miki'' kinyi siriki'' baki umma ta rike tare dacewa to rasa kunya'' wato har wani cemin kike kinyi saurayi ko''nasan da safiya ce bazata yi haka ba'' cigaba ina jinki''uhm umma abin fa babbanne'' dan dangidan hamshakin me kudine''wallahi umma mun warke da talauci'' wai yace aya asanar da magaba tana gobe zasu zo da magaba tanshi'' za,a daura aure'' kai dan Allah dagaske cewar umma ta zaro ido'' Tom kirawomin baffanku'' a waya'' jikin safiya harrawa yake tashiga'' kiran numbar baffanku'' bugu biyu ya daga'' umma ce ta karba'' tayi sallama ya amsa suka gaisa'' sanan ta shiga sanar masa abin da Safiyya tace mata'' babu laifi yayi murna sosai'' sanann yace insha Allah gobe da da safe zamu zo'' gidan domin a daura auren'' daga haka sukayi sallama'' tashi safiya tayi ta futa'' daga dakin tabar umma sai murna takeyi'' tana futa'' tashiga'' tsalle ganin cewa tayi nasarar yiwa Ummansu basaja'' ban daki tashiga'' ta watsa ruwa ta dauro zani a kirji ta shigo dakin'' jiki a sanyaye tace'' umma dazu naji''kunata murna da ke da saliha lafiya kuwa me yafaru'' anan umma ta kwashe komai ta fadawa Safiyya'' bakin safiya kamar ya tsare dan dariya'' daga bisani kuma tace'' umma yanzu ina salihar take?" Yanzu tafito ina tunanin tayi gidan su hafsane'' ko tahuce makaranta'' okay ''tafada tare da hucewa ta zauna a gefenta'' ...


Suna zaune a dakin sai ga saliha nan ta shigo ''dauke da qur'ani a hannunta'' shiga dakin tai ta zauna ''tana yatsine fuska tace'' kash umma nagaji wallahi'' san samu school dinan dana ke zuwa ace ina da motata wadda nake tafiya aciki'' uhm saliha kenan kwana'' daga yaufa shikkenn'' sai dai mijinki yadinga kaiki a motarsa'' ke da zama ki auri danmasu dash'' cewar umma'' what ''me umma ni nace muku nashirya aure ne'' Ni da ko saurayi ma bana dashi'' bangane inda kuka dosaba'' idan ma wasa kuke'' Ni banason irin wannan wasan'' tafada tare da hade girar sama da ta kasa'' afusace umma tace kajimu da shashashar yarinya nuzaki rainawa hankali'' ki mai dani karamar mace'' wallahi''idan ma wani abun. Ne yashega kanki tunwuri'' ki dawo hayyacinki ''dazunnan kigama cemin gobe za azo a daura aure'' yanzu Kuma ki nunamin baki san zancen ba''kull wallahi saliha kikiyayeni'' ko kinki ko kinso sai an daura auren nan gobe'' dan da hannunki kika kira baffanku'' a waya'' na sanar kasa'' Kuma kinsan baya magana biyu''


Pege 8

hannu saliha tasa aka ta tusa ihu ''ta fashe da kuka ta ajiye qur'anin ta watsa a guje'' bata tsaya ko ina ba sai gidan su hafsa'' Hafsah tana zaune da ita da mahaifiyar ta a tsakar gida'' kawai sukaga saliha ta shigo gidan tana rusa ihu'' gaba dayansu ta shi sukai suka rukota'' suna tambayar ta menene'' saliha lafiya mene ya faru?"ko ummace bata da lafiya''ki fadamana meyafaru kin tadamana da hankali?" cewar umman Hafsah'' kuka take kamar ranta zai fita tana koramusu bayani tana cewa''dan Allah Hafsah kintaba ganina da saurayi a tsaye?"a,a meyafaru ?"wai ummace tace gobe za,a daura mana aure da wani wan da Ni bansanshiba''what'' aure kedawa kuma'' yaushe akai haka?"anan saliha tafada musu duk abin da ummanta tace mata'' mamaki cike afuskar umman Hafsah''tace amma fa wannan abun da abin mamaki yake'' anya kuwa'' ko dai Safiyya ce ta fadamata bakeba''wallahi umma zata iya yiwuwa itace'' sabi da aduniya safiya ta tsaneni' bansan me naimataba'' amma kuma ay ummanmu'' tana ganemu'' Meyasa takasa ganewa yanzu?"dan Allah kufadamin mezanyi asan bani na kawo mijin aure ba'' uhm Hafsah tayi kwafa tace'' kije kisamu Safiyya ki tambayata''kuyi maganar fahimta dake da ita ''idanma itace zata fada miki'' sannan kada kimata rashinkunya fa domin nasan hali'' uhm tom shikenanan na gode tana gama fadar haka ta fice zuwa gida''


Tana shiga gidan abin ka da me hali baya fasa halinsa'' ta rufe Safiyya da masifa ta in da tashiga'' batanan take fitaba'' tana cewa'' safiyya Meyasa zaki min haka'' ashe har tsanar da kikaimin takai haka''to bari kiji tun wuri kisa asoke wannan bu kowallahi na manta da girmanki a matsayin ki na yayata na miki duka a gidannan'' me saliha nikike fadawa wadannan maganganu''hmm Nagode ''kuma kije wallahi Indai rashin kunya ce'' jurar ki wataran sai ansamu wan da zai koya miki hankali'' ki rike wannan a zuciyarki'' domin nasan komai daran dadewa zakituno da abin da na fadamiki'' tana gama fada mata haka''ta shige dan kwangon dakinsu'' ta barta a tsaye tana huci'' zama tayi a gurin ta saka kuka'' tana ta tunane tunane kamar wadda zatai hauka''.... Atakaice dai saliha anan gurin ta kwana dan ko runtsawa batayi ba sai dai bacci barawo idan ya dauketa''...


To washe gari su baffanta suka yo sammako suka taho daga kauye'' tun karfe 7suka taho basu isoba sai misalin karfe 2na rana '' suna zuwa suka tarar da har magabatan Habib su iso harma da Habib din'' yasha farar shadda'' sai washe baki yake da alama dai akwai wata makarkashiya dayake kullawa' masha Allah yau take ranar juma'a inda ake shaida daurin aurena Saliha Usman aliyu'' da angonta Habib Alhasan madaki''akan newa dubu dari 2''lakadan ba ajalan ba''masha Allah.

pege 9

Lokacin da sanar War daurin hauren tazo kunnen saliha'' sai da ta gigice'' dajin sunan habib ''hakama Hafsah wadda tasan komai a tsakaninsu'' innalillahi wainnailaihirraju un'' Hafsah nashiga uku'' Habib ne ,nasan ya aureni ne domin ya wulakanta rayuwata innalillahi wainnailaihirraju un... Tana tsaka da yin salatin nan sai ga baffan ta yashigo'' yana zuwa yace'' Saliha ,tace na'am baffa'' maza kije mijinki yana son magana dake'' jikin Saliha na rawa zuciyar ta na dukan uku'uku ta mike jiki babu kwari'' tafuta kofar gida'' tana fita sukayi idon hudu'' dashi ya sakar mata wani mayau darin murmushi wan da ita kanta batasan me murmushi yake nufiba'' ahaka dai ta daure ta kara sa inda yake''ta tsuguna zata gaisheshi yayi saurin dakatar da ita yace'' au ashe daman kina da tarbiyya'' ay nazata iya masu tarbiyya ne suke iya gaishe da wan da kashin kare ya fisu daraja'' walhi sai na koya miki tarbiyyar da kika yi missing dinta a baya, sai na nuna miki Ni Habib dan duniya ne nafiki duniyan ci'' kuma daga rana irin tayau kifara irga'' ranakun mutuwar ki'' Ni bani zankasheki ba amma wahala zata kasheki'' yana gama fadar haka yayi tsaki ya ce karuwa kawai me bin mata'' daganan kuma yasa hannu a aljihu ya debo bandir din kudi ya mika mata ''dakamar bazata karba ba '' sai tajuya taka duk idon mutane akansu yake'' hakan yasata sa hannu ta amsa'' ta juya zata tafi'' yace kuma ki shirya anjima za,a zo adaukar mini ke amarsuna ,yayi murmushi ya kashe mata ido daya ya bargurin''....

Tsayawa tai tabi bayansa da kallo''tana nazarin abin da Habib zai iya aikata mata'' tabbas tun yanzu tafara gasgata maganar Safiyya''datace in dai rashin mutuncine zata samu ubanta ''ay ko gashi tasamu tunkan taje ko ina.

Gajiya tai datsaiwa a gurin don idan tacigaba da tsayuwa hawaye zai iya zubomata abin da yafi sauki ta koma gida tanemi shawarar hafsa''

Shiga tai gidan'' ta samu hafsa'' a zaune ta yi tagumi''karasawa tayi ta kamo hannunta suka fito waje'' tafiya suka shigayi har sai da suka isa wani lungu inda babu kowa sannan saliha tace'' Hafsah nashiga uku'' bana fadamiki ba''Habib bazai aureni ba sai da wata munifar'' dan Allah ki bani shawara'' yazanyi ne'' hafsa'' kodai na gudune?" Me ki gudu idan kika gudu ina zaki'' haba saliha kidai sake tunani'' uhm,to ya kikeso nayi dan Allah Hafsah ki taimaka kifadamin yazanyi'' idan kuma bazaki iya taimakona ba gwara na gudo'' don wallahi Habib bazai barni ba kasheni kawai zai'' hmm saliha ,naam hafsa'' tayi magana cikin kaguwa'' inason ki saurareni kiji mezan fada miki'' wannan fa abu da kika ga ya faru ''daman can Allah ya tsara haka saita faru arayuwarki ''allah ya tsara dole sai kin zama matar Habib ''karki wani saka damuwa a zuciyarki kawata'' inason ki dake kamar yadda nasanki baki da tsoro to inason idan Habib ''ya cemiki (A)kicemasa (Z)don billahillaxi da alamun Habib akwai abin da yatama''kada kiji wani tsoro'' wuya bata kisa'' ko da kin mutu'' a dakin mujinki kika mutu ba adakin wani katon ba''yanzu idan kikace zaki gudu'' bafata nake miki'' ba ,ki hadu da wasu mugayen suyimiki fayde ko su illata ki'' inga ya sun cuceki'' to ko kinga da wannan gwra zaman gidan Habib'' ko banza zakici ki sha'' kimore'' habama sai na koyamiki abin da zakiyi sai kace ba kike islamiyya ba ''kinga mukoma gida kada azo ana nemanki'' .uhm saliha tayi ajiyar zuciya ta goge hawayen ta'' suka koma gida,...


*Anisa Anisa, meyasameki haka'' fadamin kukan mekikeyi'' yanaganki da jakar kaya niki__niki kodai fateeman ce ta koroni?" Anisa a guje tasaki jakar ta fada kan kirjin Hajiya Adama ta rungumeta'' tasaki kuka me sauti''zuciyarta na tukuki'' hankalin adamane ya tashi sosai'' tarasama mezatai'' bakinta har rawa yake daker ta iya buda baki tace'' wai Anisa lafiya me akai miki'' kifadamin kinkasa magana'' ko wani abunne ya samu Habib''...?

Mami'' sun cuceni'' sai da suka bari nayi nisa akan soyayyar shi'' Meyasa za,ayimin haka ''mami menarasa na ''ya mace''mene bani dashi?" Dallah Malama ki fahimtar dani meyake faruwa ban gane ba'' suwaye'' suka cuceki'' zaki fadamin ko saina ci ubanki a gidannan'' mami yau aka daura auren yaya Habib da wata, what ''hajiya Adama ta zazzaro ido tace'' kan kutumar uban can'' ammafa za a maimaita yakin Badar '' me aurefa wai dagaske kike ko dai fada kikayi Anisa ,anya kuwa kinji daidai'' za,ayi auren Habib dinne bansani ba''wallahi Allah mami da gaske nake miki'' tarkashi ayko yau '' za ayi yakin duniya a gidan Alhassan'' Ni za aywa tijara '' Ni Adama '' toni ba,a taboni bama hawa nake ballantana an tabani'' jar uba'' Anisa'' huce'' muje gidan wallahi basu isa su wulakanta min zuri aba'' nafisu dabbanta wallahi marabar mu da tinkiya wajan hauka'' Ni mutumce'' ita dabba, mota suka shiga ''suka figa'' har cikin gidan su Habib'' ko motar bata tsaya ta gama parking ba ''tafigi hannun Anisa tayi cikin gidan tana kwallawa Fateema'' kira'' kina ina bakar munafuka'' Fateema'' kufito ayita ta kare'' don wallahi yau ''mutuncin ma bansan shiba'' Fateema''munafuka ki fito ko na shigo ciki na koya miki hankali...


Pege 10

Dasauri Hajiya fateema ta fito ''tana bata hakuri dan tasan za,a tuna''dan Allah kiyi hakuri Adama abi abun asannu'' bazan bi asannun ba'' anki abi adun asannu'' Ni zaku raina wa hankali'' walhi daidai nake da kugun ku daga ke har dannaki'' ''yartawa zaku wulakan ta'' to wallahi ko yasaki'' waccan ''yar matsiyatan ya auri Anisa,ko kuma yanzu na nunamuku Anisa na da gata'' aykin banza sai da kuka bari ta gama zama ta wahalar da kanta taki kowa tace saishi''sanan kawai rana daya ku aurar da danku ga wata.....

Dan Allah Adama kiyi hakuri''komai kikaga yafaru akwai sila''daman Allah ya ruga ya tsara Anisa ba matar Habib bace'' dallacan tafi can''kirifemin baki''ay komai daman yafaru akwai sila Kuma kece'' idan da kince ''yar,uwarsa zai aura ai da bazai kiba'' sabo da tsabar bakin hali irin naku na ''yayan talakawa'' ay tun da yaya ya auro diyar talaka munta samun talakawa a zuri'ar mu'' ke adama !!!ya daka mata tsawa ya hade rai'' tare da karasowa gurin yace'' Adama matar tawa kike fadawa wadannan maganganun?" Ashe dama baki da hankali'' haba yaya ni baka ga abin da tamin ba'' sabo da tsabar rashin adalci tasan Anisa nason Habib amma takasa hanashi auren waccan ''yar talakawan''Ni ban ma yadda da wanan matar takaba idan aka bibiya ma ''yar uwasu ce'' dan nasan kaf danginsu babu masu kui bal...... Aykafin ta karasa maganar ta taji saukar wani gigitaccen mari a kuncinta'' hagu da dama'' Waye Abba ne'' afusace adama ta daga ido tana kallonta, dan tun da take da dan,uwanta betaba sa hannu ya mareta ba sai yau'' jiki asanyaye'' tace yaya Ni kamara''?" Akan na fadi gaskiya'' namareki Adama kiyi duk abin da zakiyi''akai badai akan Habibu bane ''yace bayason Anisa ''gawadda yakeso sai na hanashi abin da yakeso ''to bari kiji ko mace an daina yimata auren dole ballakuma namiji'' namijin ma dana '' idan yazama dole sai jinina zata aura''tajira dawowar juneid muddum ya nuna yana sonta'' nikuma na amince zan auramata dana juneid''

A gigice Fateema''ta kalli Abba tace'' alhj juneid fa kace'' habibu ma be aure Anisa ba sai juneid da ya shiga gari ya zagaye kasashen ketare yaga ''yanmata kala da ban da ban'' banjin zai amince da auren Anisa''

Hajiya Adama kam bata karacewa komai ba''taja hannun Anisa'' suka fuce daga gidan''

Tun da suka koma gida Adama ke kaiwa da kawowa'' tana tafa hannu, Anisa na zaune agefe tana bin ta da kallo'' jiki babu kwari Anisa tace dan Allah mami kiyi hakuri''nasan duk wannan abin Ni naja miki ''har Abba ya mareki''idan akan yaya Habib ne na hakura, no Anisa'' badai ance za ajira dawowar juneid ba '' mujira ya dawo dan wallahi bazakiyi dakon banzaba'' A,a mami bana tunanin ya juneid zai soni'' tun da Habib besoni ba juneid bazai taba sonaba , saboda yafi Habib komai na rayuwa ''hatta kyau da duri da tsarin halitta Habib mummuna za,a kira shi agaban juneid ''kuma wasa kukeyi''kawai ku bari na hakura'' walhi bazai yuwuba '' don yanzu aka fara wasan'' dole sai Habib ko juneid

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment