Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su tambayo auran mansur Allah ya k'ara maka ni san kwana ba we zan ja da maganar ka ba aa ka duba ka gani kaf ahalin mai zaki ba su tab'a auran bare ba in kayi haka zai iya budai kofa ga yan baya suk'i jinin su su auro bare ya sarkin birnin zaki ka duba magana ta shine d'an ka na fari ba wataran shi zai zama sark'in garin nan ,

Shiru yayi yana sauraran ta kamar ba zai magana ba sai ya ce.

"Ni shugaba ne dole inyi adalci a k'an dauyin da Allah ya dora min mu da su duk al'umma daya ne kuma mu musulmene dan haka aure ba fashi nan da sati mai zowa za a daura aure ki shirya amsar sirik'ar ki zaki iya ta fita "

Mamaki ne ya kusan kashe ta a zaune mai isa yana da kafiya in yace eh to babu mai juya ta ta koma aa cikin kunar rai ta tashi muryar ta na rawa tace,

"Na barka lafiya fucewa tayi ranta in yayi dubu ya b'aci dariyar da maimuna ta saki ce ta sa ta dawo hayya cin ta bata Kula ta ba ta huce domin a yanzu bata da lokacin hajiya maimuna amma a juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe tasa k'afa ta futa direct shashin ta ta huce tana zuwa ta d'auki waya ta shiga kira har ta kusa yanke wa aka dauka aka ce

"Hajiya anni barka da rana
ina toilet ne shiya ban d'auka da huri ba ina fatan lafiya ?"

Kilishi ina ba tun lafiya mahaifin ku ya dage sai wannan yarinyar ta shigo gidan nan ina cik'in ma tsala

"Anni kuma duk abin da malam ya ce a yi k'in yi kuwa ?"

Kilishi na daina kashe kud'i na agun malamai kina ga wancan karon da muka je cewa yayi asiri ko tsafi ba zai tab'a cin sa ba na barwa Allah komai ita ma ance ta na da addu'a kullum sai tayi azk'ar tun da ya dage sai ya aure ta to nan da wata hud'u da auran su zai auri yar gid'an hajiya aina'u aminiyata..........✍🏼

*AFIF*



Oum yasmeen



*My first novel is return black*


_the writer of BINTA YAR JAGALIYA_

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

*____________________________________*

*____________________________________*


Chapter 51-60



" Anni anya kuwa zai yarda ya aure ta kin san halin yaya fa ,


Tsaki tayi tace


"Barni da shi sai ya aure ta kamar yadda mahaifin sa ya yarda ya aure zab'in sa nima sai ya aure nawa yarinyar nan zaliha tana da k'irki ga tarbiya"
Hmm anni kenan kamar ba kisan wace mahaifiyar ta ba kuma fa kinsan tare mukai makaranta da dai kin zab'a mai wata da yafi amma wallahi anni

Ai kafin ta k'arasa abin da tayi niyar fad'a tace ,



"Kilishi yimin shiru in ba zaki fad'i alkhairi ba yi min shiru auran yayan ki da zaliha ba fashi nakira domin ki tayani jimami shine ki ke fad'amin wannan magana ko ita kawo isk'anci da rashin kunya duniya to sai ya aure ta in banda shashanci yana matsayin d'an sarki zai kwaso mana bare ina laifi ko yar wata sarkin wani garin ce ko yar wani basa rak'e ko yar governor aa ba daya yaje karatu Egypt d'an sun sauke shi a gidan su sun k'ar rama shi shima sai ya rama musu


" To, anni Allah ya shege mana gaba,

"Ameen kilishi ta kashe wayar to wannan ke nan bayan sati biyu aka daura auran mamy da abbie tadawo k'asar zaki da zama tun zuwan ta gidan sarauta ta fuskanci kalubale daban daban tana da cikin afif haihuwa yau ko gobe aka aure hajjiya zaliha duk yana daga cikin tsarin anni ko zata had'iyi zuciya ta mutu tun da ance larabawa basa son kishiya gata kumada ciki ko kuma ta tada hankalinta ta sa ya saketa sai dai mamy tana da hakuri ta shiga d'aki tayi kuka fa adadi ko sau daya abin da ake mata bata tab'a zuwa gida ta fad'a ba ta san mutuncin iyayan mijin ta ne zai zub'e duk wani girma da suke gani nasu za sudai na gani hanyar da ta zab'a ita ce


tana fad'awa Allah kukan ta ba wani hin hausa take yi sosai ba dan haka ko sunyi habaici masu zuwa ganin amarya suce zasu zo gaida ita baji take ba ko kuma aina'u ta rako su bata tab'a nunawa tasan da ita suke bayan aure da kwana ukku ta nak'udar Afif ta tashi da tsak'ar dare ga yanzu ta fara rasa hankalin mijin ta cikin a halin ciwo ta d'auko waya ta Kira shi bai dauka ba har sau ukku sai can aka d'aga ganin an daga tace Dan Allah kazo ka k'ai ni a sibiti bani da lafiya ,

"Mwsss banza ki na tunanin zai zo to ni ya bawa wayar domin yace min baki da
amfani agunsa k'inga ma aiki yazu nice a kan duty kinai mi mai kai ki badai mijina ba kit ka keji hak'an yayi dai dai da dauke war numfashi mamy na hucin gadi da k'yar ta iya sai ta numfashin ta ta mik'i ta nufi shashin su inna da kemata aiki bugawa tafara yi jini sai zuba yake

" da sauri inna ta budai tace lafiya hajiya ?"

Dan Allah inna ke taima keni zan mutu
"To, tace ta taima ka mata ta shiga cikin d'aki inna shiga tayi uwar d'akin su ta taso mijin ta daya ke driver ne shi yake kai su unguwa da sauri ya tashi ya fita saita mota ita koma inna ta ruk'eta suka fito prevent asibiti suka nufa da ita hankalin su be kai na suji na masarauta ba domin duk k'an ahalin masarauta anan za a dubashi hakan doka ce suna shiga nurse suka zo da abin d'aukan mara sa lafiya suka shiga da ita babban Dr nadiya sunusi dala ta fara dubata tasha wahala domin jinin mamy ya hau kuma ta kum d'an cikin ta da suka binkice shi yana tare da ciwon zuciya Masha Allah yana da girma sosai kamar shi daya da mamy komai nata ya d'auko b'e biyo masarautar zaki ba bayan an gyara su duk baba ne a kan komai har biyan kudai shi ta bawa ya biya inna ta dubi mamy ta ce,

"Na fadawa malam ya fad'awa alhaji tun da k'inga ba yau za a sallamomu ba ko ?"

Hmmm numfashi ta sauki a cikin sanyin magana tace,

"To, shikkenan tunda kun fad'amai ,

Cikin gida kuwa abbie yana sauri zuwa asibiti sai gA wayar anni da yake agaban zaliha aka fad'amai haihuwar cike da girmamawa ya ce


"Allah ya jada ranki ,

Da hallacan yi min shiru ka jirani mutafi a sibitin tare in zan kai asuba k'ar ka sake ka tafi kuma zata gane kuranta tunda har ta tafi wani asibitin ba na muba tsiyar bare kenan har tafara k'arya mana doka tunka fin ahaife ta haka tsarin yake waya sani koma ba d'anka bane shiya ta tafi wani asibitin domin ai mata komai a cikin sirri wani besani ba to Allah ya to ni a sirinta


" Tamk'ar sauk'ar arado yaji maganar mahaefiyar sa yau in ba anni ba ce ta fad'amai haka ai sai yayi shara'a da mutum mai yasa take biyaiwa san zuciyar ta iska mai zafi ya furzar ya ce


"To, anni insha Allah zan miki biyayah
Kit ta kashe wayar ita kuwa aina'u kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha cikin kissa zaliha ta dubi abie ta ce Dan Allah ina ne man alfarma ina so inje gida hajjah ba tada lafiya tun jiya


" Ransa inya yi dubu ya b'aci yau abu goma da ashirin har yau she ya aka kawota gidan da zata fita yau cik'in kunar rai ya ce,


"Aa k'arki je ,


Haba mai yasa kake min haka mahaifiyata bata da lafiya fa nace maka wallahi sai naje ta buga k'afa ta shige daki mayafi ta d'auko ta yafa da mukullin mota tana k'ar kad'awa ta fita
" be tsaya kulata ba domin in da badan anni ba da yau sai ya saketa


to taci darajar anni waya ya d'auka ya kira mamy ring ta keyi amma ba a d'auka ba a na ukku ta d'auka tayi shiru ba magana cikin sigar rarrashi ya ce ,
"Dan girman Allah kiyi hakuri na san ban kyauta ba da har yanzu ban zo ba ya jik'in ku?"


"Hmmmm baka damu da jik'in mu ba ta shiga fad'a mai duk abin da zsliha ta fad'a mata ta dora da cewa in ka gaji dani to ka sallamai ni kowa ya huta a cik'in mu kuka ne ya kub ce mata ka d'auko ni cik'in gatana ka kawoni garin da ba kowa nawa shine kake so ka hulak'anta ni mai nayin maka mansur duk irin hakurin da nake wallahi na gaji

Tun da yake a rayuwar sa be tab'a ji ta ambaci sunan saba sai yau gaskiya shi kad'ai yasan huk'uncin da zai wa aina'u cikin zafin zuciya ya ce ,


"Dan Allah kiyi shiru wallahi ban sani ba a lokacin data d'au wayata bana gid'an ko kin manta yau ina aikin kwai na kin sanfa ban d'auki hutu ba na bar wayata ne a gida dan girman Allah ki tsaya kiyi tunani har aiko wa nayi a d'auko min waya tace bata ganta ba na rantsai miki da Allah ban sani ba kiyi hak'uri yan Zuma da tuni na zo amma anni tace in tsaya ta zata zo muta fi


"Ajiyar zuciya tayi tuni wani abu daya tokare mata mak'oshi ya huce Allah ya kawo ku lafiya tace mai "


"Kin rad'a mai suna nai ?"
"Aa sai ka zo ,


"K'in ga ban san lokacin da zata zo muta fi ba ki sa mai sunan mahaifina sai ki zab'i alkunyar da za a sa mai ,


" To, amma Dan Allah ka zab'a mai ni bani da wani suna da zan sa mai naka na ke so .


Shiya sa take son asiya ta nada hak'uri da biyaya da sanin ya kamata Allah cikin jindadi yace
"Allah yayi miki albarka asa mai Afif ko yayi ya fad'i hakane domin k'arya shiga hakkin ?"


"Eh yayi cike da kunya tace,


" Dan Allah kayi hakuri na d'aga ka murya wallahi raina ne ya b'aci dan girman Allah ka yafemin k'ar ubangiji ya yi fushi dani ,


Tambas tsakanin mata da miji sai Allah a jiyar zuciya ya saki ya ce ,


"Wallahi ban ruk'eki ba Allah ya yafe
mana baki d'aya ,


Amin ta amsa da shi



Wanna kenan


Wallahi hajjah sai munyi da gaske


" zaliha rabu da su mudai gama da asiya da d'anta sannan mu dawo kan anni ,


Gaskiya fa ki kafad'a domin tana gamawa da ita kaina zata dawo fa
Hajjah ta ce,
Yar lele shiya sa nake son ki akwai Ζ™waΖ™walwa shewa d'auko jak'ar ki muta fi kin sanfa gun da nisa


"To, hajjah ta mai son farinciki na mayafin ta tayafa a kafad'a kamar ba mai aure ba ta suka shiga mota tafiya suke ta yada k'anin wani zaliha ce ta juyo tace,


"Allah hajjah in daba dan buk'ata ta ce ta kawoni ba ba dalilin da zan zo nan ,


" Hmmm kawe hajjah ta ce domin i tama ta gaji tsayar da motar tayi suka fito da waiga gaba na waiga baya ba gida gaba ba gida baya baka Jin motsin komai saina tsintsayai gawani k'atun dotsai mai duhu bishiyu duk sun rufe shi tafiya suke har suka isa gaba dutsan nan ashe da aiki gaban su tattare siket d'inta tayi hakama hajjah ta ruke zanin ta suka haura dutsan nan duk k'afar su ta fashe daya ke ba azuwar mai da da kalmi wallahi da ga yau zaliha na daina rako ki irin wannan huyar haka ,


"Haba hajjah aina'u wannan wanne irin zan ce ne naga kema da buk'atar ki ,
Banza hajjah tayi mata domin tasan halin yar ta yanzun nan zata fad'a mata ba dad'i wa'iyazubillah Allah ka tsare mu da fad'awa halaka ,


Wata dariya aka sake gabaki daya dajin ya amsa jikake ance sannun ku shaid'anu makiya Allah ku shigo da baya juyawa sukai suna tafiya da baya da baya sai da suka zo gaban sa suka juyo dana tsaya na karewa gun wadan da suka zo da k'yar na tsaya saboda munin sa ga gun sai warin yake da k'arnin jini ga cikin sa duk d'aud'a kayansa duk sun yage gashinsa yayi wani irin murd'aiwa saboda d'aud'a da tarowa daya yi gawani bak'in bargo hak'oran sa duk sunyi yellow saboda rashi samin wanki da baya yi yace nasan muk'atar ku tunka fin kuzo aljani cangus ya fad'amin mai kukeso ayi ?"


"Yauwa ina so a kashe shi ,


Hhhhhh hhhhh yasaki wata mahaukaciyar dari yace


Bazai tab'a mutuwa ba domin tunyana ciki ya keshan ayoyin Allah haka lokacin data ke na k'udarshi na tura d'an gusji ya je yad'au ko min shi domin in na samai shi zan shiga cikin duniyar tsafi shine mahad'in aiki na kuma ba mukad'ai ba mutane da yawa suna San sa domin jinin sa tsafin mu yake so sai d'ai ajiya aljanun da mutane suka tora d'auko shi sun k'one sa ka makun karatun Al'Qur ani da takeyi yan zuma haka duk da tana jinin haihuwa ta kunna karatu


" jikin ta na rawa tace to asa ta ta tsanai shi ,


"To angama za mujira lokacin data shiga wajan na jasa musa mata tsanar shi taji ba wanda ta tsana a duniya sai shi sai dai da sharad'in in aikin ya k'aryai kifa mutane zasu tsana kee kuma zaki din ga wari k'uraje sufito miki suna zubda ruwa kuma ya nuna hajjah zaki haukace,


" aa boka a cire ni kaga ni rakota nayi ,
"Ai haka aikin yake k'un yarda?"
"Ba wani tsoro a Zuciyarta ta ce eh na yardah ...


""TO, za ki kawo hantar jariri wanda ya mutu kuma wannan aiki da kan ki zakiyi Hhhhhhhhhhh yasaki wata dariya irin ta arnan daji

cikin tsoro da rud'ani tace,
"a yimin afuwa abawa aljani ya d'auko,
"Dole ne sai kee ce zaki shiga mak'abar ta ki samo sannan kuma anan zaki kwana domin a k'asara miki aikin ki,


"zaro ido tayi ciki da ta shin hankali domin ina zata iya kwana a nan balle a zo da had'a jiki da wannan mutumin da baya wanka ko za a bani wani aikin inyi mijina be sani ba na fito


Hhhhhhhhhh dole sai kin kwana sannan kee kuma hajjiyah aina'u ya ce,


"An fad'amin abinda ya kawo ki kina so ki auri sarki aliyu mijin k'awar ki,
Cike da tsoro ta d'aga mai kai ,


Wata dariya sake duk da jin ya amsa sannan ya ce



"Aikin ki yana da wahala domin ya ruk'e addu'a kuma yana da tsari dan jini jini zaki bawa aljanu ki yanka bijimin sa sann sannan zaki yi lalata da yarinyar da ki ke ruk'o ta d'an uwanki da ya mutu ya bari na tsawan sati ukku ki dinga d'iban ruwan daya fito daga gaban ki kina zubawa a roba da shi za muyi aiki bayan mun gama zata mutu,
Dafa kirji tayi tace ,


"Na shiga ukku dan girman Allah a can zamin aiki ita na ke gani inji dad'i


Hhhhhhhhhhhhh dole ne dole ne
juyo wa tayi taga ba yar ta ba boka


*innalillahi wa'inna ilaihir raji'un*



mai wasu mutane suka dauki duniya sun d'auka gurine na zama ba mutuwa kunga irin masifar da boka ya ke haddasawa yana halaka ya halak'ar ita shirka sab'on Allah ce ya Allah ka shiryai mu


Jikin ta a mace ta tashi ta fara tafiya da baya da baya har ta fito da ga bukk'ar shi sannan ta koma tafiya ta gaba a wahalce ga yunwa a k'ishirwa ta fito bak'in titi bata iya mota ba d'an haka sai da tayi tafiya mai ni sannan ta fara

ganin motoci jifa jifa tafin k'afar ta duk ya fashe saboda ta b'ar ta k'almin ta a mota duk wanda ta tsara ba ya tsayawa sai bayan magariba yasami mota a ka sauke ta a bak'in gate d'in masarauta da yake motar haya bata shiga ciki hamdalah tayi domin ba kowa sai fadawa da suke shawagi da sauri ta huce su sai da tayi tafiya mai nisa sannan ta isa shashin ta a jiyar zuciya ta sauke data jita ta zauna a kan sofa laushin ta ya ratsa ta tace


Hajiya sannu da dawo wa
Dasauri ta d'ago tace


Yauwa had'amin ruwan ka ki kai min


"To, ta ce tashiga d'aki domin a nan ban d'akin ta yake ,


________________

"Washe gari hajiya anni ta zo domin sutafi asibiti Mansur ransa ya b'aci dan dai mahaifiyar sa ce suna shiga dak'in da mamy take anni ta saki salati ta ce shikkenan masur an cuce ka kalli d'an nan da wa yake kama ?"

" A firgice mamy tayar da huk'ar da ke hannuta ganin tana ne ma ta cillar da d'an data haifa yasa mansur sauri ruk'e afif ya rumgume shi lokaci daya ya ji soyayyar dan sa ta dorar mai a zuciya abin da anni ta fad'ane ya dawo da shi duniyar daya tafi ta tunani ,
Bashakkah kin haifi shege kina so ki kashe shi ko ai gashi nan kaf a halin masarautar zaki duk kamar mu d'ayah amma ke gashi kin haifar mana bare dubar mansur tayi tace mai da harshan

oromo na kasar utopia Diirama jech kampitira ma'ana d'ana dole kabi duk'ar da zan fad'a maka


"Dan Allah anni ki hakuri insha Allah komai zai daidai ta ina tunanin gaskia asiya zata aikata kisan k'ai ba kuma d'an data haifa ina tunanin ba lafiya ba
Cikin asalin harshan Amharic na kasar utopia

αˆ˜α‰†αŒ£α‰΅α£ αˆ˜αŠ“α‹°α‹΅α£ α‰αŒ‘α£ α‰αŒ£ Ethiopia αˆ˜α‰€α‰ αˆ yazama dole ka sakita


Cikin rud'ani mamy tace,


Wallahi ban tab'a aikata maka mancin abin da kike fad'a anni kuka ne ya sark'eta ga tare nan ta yanke jiki ta fad'i dasauri ya sunkuya ya d'auko ta wayar sa ya d'auko aljuhun rigar sa ya kira likita domin ahalin yanzu bawa ni tai mako da zai iya bata nurse guda biyu suka shiga go ga likita daya dr sabeer yace


Dan Allah ku bamu guri za mu duba ta


" To,

Suka ce suna fita anni ta huce gurin motor da ta kawo ta domin fitar sirri tayi ko sarki be sani ba,,


Duk wani tunanin sa ya tsaya cak yama rasa mai zaice shawara daya zaibi ya kira maimartaba ya fad'a mai komai domin yana ganin shi kad'ai zai iya sa anni ta janyai k'udirin


wannan ke nan


bayan ya fad'a mai komai yasa ya daka tar da anni yayin da aka sallamo mamy taci gaba da shan magani haka hajiya zaliha itama tana zaune ba dad'i domin mansur baya son ta tana zaune bisa son farantawa anni mamy fata kaunar abinda zai had'ata da Afif ta tsane shi tsana mai muni bayan zaliha abie ya sake aureya auri rumaisa tana da ya'ya hudu da shi akwai salmah da zainab sai Dawud sai Faisal hajiya zaliha bata haihu ba hakane yasa ta hada kai da rumai sa suke kunta tawa mamy afif yana da shekara goma sha hudu mai martaba ya mutu abbie ya mayai gurbin sa duk da kace na can da hakan ya janyo ana zar gin guba aka bashi abubuwa sunwa abbie yawa ganin hak'an ba zai iya kula da afif ba yana sauke Al'Qur ani mai girma ya turashi America yayi karatun akan gynecology yana gamawa suka bashi aiki inda yayi musu aiki na tsawan shekara shiddah abbie yace sai ya dawo be dad'ai da wowa ba anni tace sai ya aure jiddah ba yardah ya iya haka ya aure ta sai dai iya biyayah taimai har ya fara son ta bayan auran su da wata biyar ya tafi

Addis Ababa university yajai ya karanci pharmacy wato ilimin hada magunguna mamy tana da ya'ya biyar bayan Afif akwai yusirah tayi aure tana zaune a London tare da mijin ta da y'ayan su biyu mace da na miji sai abdulraman shima yayi aure sai lamir sai autar su nusaiba yanzu haka tana karatu a jami'ar birnin zaki university tana level one afif baya rayuwa acikin yan uwan sa be shak'u da suba ko yazo hutu garin zaki b'angaran sa daban baya shiga hark'ar kowa domin tun farko suna kana na in yashiga shashin mamy ta dunga duk'an sa in kuwa ya yi wasa da yan uwan sa saboda duka sai ya suma abbie yasa anyi addu'ar Allah ya yai mata abin da ke da munta amma abun tamk'ar turi yana da shekara ashirin da bakwai ya bud'ai babban store a garin zaki ba abin da ba a siyarwa duk kayan k'asar da kake so zaka samu inna zatsa kwatanta muku girman wajan b'ata lokaci ne bayan nan da kud'in daya samo ahark'ar kasuwanci ya bud'ai katafaran asibiti domin al'umma komai kyau ta ne hakan dayayi ya konawa surikin sa rai komai shine agaba tunk'an ahaifai shi suke nai man kud'i lokaci daya yazo yafi su indah yasawa asibitin suna


*KAINUWA HOSPITAL*


"Ajiyar zuciya ya sauke yafi to daga mota kai tsaye resumption ya nufa gaban wani dogon table yanufa ida wata mace tana zaune tana dan na system ina aka kwantar da sarki mansur ?"


"Dasauri ta d'ago domin kamar ta gane muryar kwarjini yayi mata Tai sauri sauke kanta k'asa tace,


"Room twenty-one a royal room amma Dr bai tsaya Jin mai zata ce ba yayi gaba da salma ya shiga tuni zuciyar sa ta k'arye ganin irin na'urorin da suke aiki ajikin abbie yawa ba shi da rai sai ka tsaya kalura zaka gane cewa Zuciyar sa tana har bawa ta jinkin na'urar da aka mak'alamai a girjin sa tuni hawayai suka din GA zarya a idon sa yafa zuciyar maza ta k'arye yanzu abie ne ya ke kwance anan da sauri ya k'ara gun sa ya rumgume shi yafara kuka yawa k'aramin yaro ahankali abie ake d'aga hannu ya ruk'e hannun afif gam yawa za a kwa ce mai shi ,,
AFIF yace


Abie kana jina ko abie Dan Allah ka ta shi kayi min mgn abie na dawo bazan sak'e komawa ba

"Wane yake ne ma ya k'arya doka ta sai dana ce miki k'ar ki bari kowa ya shigo sarai Afif ya gane muryar Wanda yake magana turus yayi ya tsaya ganin afif"
Tashi yayi ya tsaya ya dube shi da rinannun idanuwan sa ya sak'ar mai murmushin sa mai barazana da duk wanda yayi wa ahankali ya tako inda yake yace


Yanzu ba lokacin nuna mamakin ka bane ka a dana shi sai nan gama ina so ganin file d'in abie sannan inaso in baka sak'o ka fadawa abokanan harkallar ka cewa zaki ya dawo ni murucin kan dotsai ne ban fito ba sai da na shirya tunda ku baka duba tsofan ku tun tuni nake muku gargad'i kurik'e girman ku k'ar in taka ku k'unki sannan ya ya fito da abin da ya b'oyai a hannu sa maganin da kake bashi poison ne sai a hankali zai ratsa mutum har ya yi mai illa yayi mutuwar tsayaiiiii

"Sannan ina baka sak'o ka fad'awa wa yannan tsofaffin na majalisar dadtawa ce wa ni yad'in mage ne masoya novels d'in na ina nan ina shirya muku sabon littafina mai suna *YADIN MAGE* k'ar ku bare abaku labari ku ba inda be tab'o ba musam man matsalar rayuwar da a ke ciki yar da masu kud'i suke taka talaka dan bashi da galihu da kuma mutanan da suke bada kud'i indan sun lalata ya'yan al'umma suba da kud'i ayi shiru da baki ,


Ina mai baka shawara ka d'auko min file in kuma ba haka ba ina da yanyoyin ka maka ya dafa mai kafad'a ya tsareshi da idanuwan sa masu kafa da mashi Dr uzairu ka girmana wannan fur furar da ta rufe maka fuska da kai we mai kake ne ma a duniya na farko Dan ka daya sai matar ka kana da kud'i account d'in ka billion goma sannan kana da kadarori duk da nasan ta inda ka same su amma

Please Login or Register in order to submit comment