Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abubuwa sun yi min yawa dole zan taƙaita labari na daga nan, ba wai don ya ƙare ba, amma dai na san kowa na son jin ƙarshen labarin shiyasa zan taƙaita.


      An kai ruwa rana kafin Ɗahira ta yarda ta koma gidan Usman, a lokacin cikin ta ya shiga wata na biyar ne

Sai da aka sake shagulgula isu-isu ƴan gidan kafin ta tare, inda aka gyara mata ko ina

A ranan dai Usman yayi kwanan farin ciki, yau ga shi ga Ɗahiran shi cikin sukuni, domin ta rigada ta sallama tuni ta yafe mishi komi ya wuce, tunda ta koma kuma biyayya take mishi kamar yanda aka santa, hakan ya ƙara jawo shaƙuwa me ƙarfi da ƙauna a tsakanin su

Inda Usman ɗin ya so su wuce TURKEY yayi hutun amarcin sa da ya ɗauka

Amma Kaka ya hana, ya ce, "dole sai ta haihu".

Ba don ya so ba ya haƙura

Ita kanta Ɗahiran ma ba ta son zuwa sabida idan har suka je rayuwar da tayi a can ne zai dawo mata, amma bata ce mishi komi ba.



        Cikin ta na wata shida Aunty Zulaiha ta haifi ɗan ta na miji, an yi suna inda yaron yaci sunan mahaifin mijin ta Aliyu, za su na kiran shi da Aiman.



     Fannin Hajja Fatu kuwa don dole tayi ladab yanzu, domin ba kaɗan ba Abba yake gasa mata aya a hannu, duk wani jin daɗi yanzu yayi ƙaura a wajen ta.


Matsalan da Shakira take fuskanta wajen mijin ta Sahabi, zama dai ya ƙi daɗi, domin ashe har yanzu be dena bata ƙwayoyin hana samun ciki ba, ko ɓatan wata bata sake yi ba, sai da dubun shi ta cika ashe Allah ya bata ciki, daga baya da ya gane sai ya je ya siyo magani ya bata, ciki ya zube lafiya lau, duk a tunanin ta Allah ne ya ƙaddara hakan, domin yanda Sahabin ya nuna damuwarsa tsantsa dole ta cire tunanin komi, sai daga baya kawai ta kama shi yana waya da abokin shi, inda yake faɗa mishi komi "shi ne yake bata maganin hana ɗaukan ciki, don shi wlh be ƙaunar haihuwa yanzu sai nan gaba," sanadin da aka yi ta fitina kenan, daga ƙarshe dai aka raba auren dole duk da rai be so ba, amma su Big Dady sun ce, "dole sai ya sake ta, ya je can ya auro wacce ba ta son haihuwar". Ita kanta Shakiran hakan ya fi mata, domin burin ta yanzu kenan ta samu ciki, tunda ga shi duk ƴan uwan ta da yaran su, Fadila ma yanzu tana ɗauke da nata cikin, sai dai be kai wancan matsala ba, haka ma itama Aunty Zainab.



                Ɗahira ta haihu lafiya ta samu Baby Boy, inda yaro yaci sunan Abbun ta, sunan Kaka kenan, Al'ameen, za su kira shi da sunan A'sim


An yi shagulgula an gama lafiya.



           Sai kuma a lokacin ne aka yi bikin Firdausi ita da sauran ƴan uwan ta jikokin Granny, sun je sun kwana sun raɓashe.



            Sai da Ɗahira tayi arba'in kafin suka tafi Turkay, satin su uku a can suka wuce Saudiya suka yi umra, sannan daga can suka wuce Dubai, sun yo wa ƴan uwa siyayya kala-kala inda suka dawo gida. Zaman su sai son barka, domin ƙauna tsantsa suke nuna wa junan su, gefe kuma ga ɗan su dake ta wayau tubarakalla.



         Kwatsam sai aka wayi gari Kaka be da lafiya, ciwon kwana ɗaya don har ya samu sauƙi ma, ashe ciwon ajali ne, inda ya ce ga garin ku nan, mutuwar da ya girgiza ahalin nan gaba ɗaya, wanda sun daɗe basu manta bawan Allan nan ba.



       Bayan wasu shekaru, yanzu Ɗahira har ta sake haihuwar ɗiyar ta mace me sunan Hajiya, Asiya, suna kiran ta da Huda.



     Itama Fadila yanzu tana goyon ɗan ta na biyu ne me sunan Abbun su, duk ka yaran ta maza ne. Yusra ma ta sake haihuwar har da tsohon ciki yanzu. Shakira ta samu miji ta yi aure, sai dai a Zaria yake, kuma yana da mata ɗaya da yara biyu, suna zama lafiya babu wani hayaniya tunda yana da shi, kuma ya barta tana ci gaba da aikin ta. Itama Sa'adatu yanzu tayi aure a can Legos ɗin, har ta dawo da Zahra da tayi wayau Masha Allah, kamannin ta da uban ta sai ƙara fito wa yake yi, duk wanda ya kalle ta sai ya tuna da Baffa, Allah sarki rayuwa kenan.




      *TAMMAT BILLAH... ALHMADULILLAH.. ALHMADULILLAH.. ALHMADULILLAH... Duka-duka a nan na kawo ƙarshen littafi na, abun da na faɗa dai-dai Allah ya bani ladan, kuskuren da nayi kuma Allah ya yafe min*



_saƙon gaisuwa ga masoya na bazan taɓa manta ku ba, na gode sosai da nuna min ƙauna da kuka yi, Allah ya bar mu tare har a aljanna, Love You fisabilillahi.. taku JIKAR LAWALI_ 🤩👄💘❤️💓



*DEDICATION to the family of GOMA'S Family, and to every family, joy and happiness be with them. Happy family❤️👨‍👨‍👧‍👧👩‍❤️‍👨*



_Mu haɗu a sabon book ɗina me suna *ABUL KHAIRI (LABARIN DEEBIZAH RETURN)* kar ku bari a baku labari._









                  *ƊANƊANO*




            *ABUL KHAIRI*

                 Lumsassun idanuwan sa da suke cike taf da barci ya ware su a kan ta

Tana kwance gefen sa, hannun ta ɗaya saman ƙirjin sa da babu riga, barci itama take shararawa wanda yayi wa cuty face ɗin ta kyau matuƙa.



     Idanu kawai ya zuba mata cike da takaicin ganin ta kusa dashi, sake ware idanuwan sa da suka sauya kala zuwa ja yayi, ya mayar dasu kan hannun ta dake ƙirjin sa, dogon tsaki yaja kafin ya saka hannayen sa biyu ya riƙo hannun nata ya sauke kan jikin sa ya yarfar dashi

Wanda hakan sai da yasa taji zafi sosai cikin barcin ta, babu shiri ta farka tana zare idanu ba tare da ta motsa ba

Shi kuwa tuni ya ma sauka akan gadon, yana gyara rigan zuwa jikin sa, tare da ɓame bottles ɗin gaban rigan da suke a buɗe gaba ɗaya

Kallon sa kawai take yi tana karantan yanayin sa, sai da ta gama ƙare masa kallo har ya gama abinda yake yi, ya zari makulle zai fice ba tare da ya sake kallon ko inda take ba, ai kamar ƙiftawar ido ta dira daga kan gadon tasha gaban sa da sauri, har da saka hannu tana kare sa alamun bazai wuce ba

Sauke idanun sa yayi akan ta cikin ɓacin rai da ya nuna a face ɗin sa, sai dai be iya ce mata komi ba illa kallon ta da yake yi yana sake haɗe rai

Ita kuma yatsina kyakykyawar fuskar ta tayi, kafin ta kafa masa manyan idanuwan ta tace, "Wai ina zaka je ne ka bar Ni bayan kasan me ya kawo Ni wajen ka? Bie babu inda zaka je wlh sai mun tsayar da maganar mu, tunda ka ƙi ɗaukar waya ta to na biyo ka". Sai kuma taja numfashi tana ci gaba da faɗin, "Wlh idan har baka yarda da buƙata ta ba Bie, na rantse da Allah zan nemi mafita kamar yanda na faɗa maka, kasan kuma Ni ɗin ina da waɗanda suke jira na in Kai musu kain..."

"ZIYA.." Yafaɗa da ƙarfi cikin tsananin ɓacin rai da ya ninka wanda yake ciki, lokaci ɗaya farar fuskar sa ta sauya kala tayi jazur, haka ma jijiyoyin kansa sosai suka fito raɗau

Ƴar siririyan dariya ta saki tana kallon yanda gaba ɗaya ya sauya lokaci ɗaya, hakan kuma sosai ya faranta mata don tafi son yayi zuciya yabi ra'ayin ta, cikin yatsina tace, "kar ka yimin tsawa Bie, kasan bazan ɗauka ba, kuma kabar tunanin bazan iya rabuwa da kai bane, wlh akan haka sai mu raba hanya.."

Damtsen hannun ta da ya damƙe ƙam, shi ya hana ta ƙarisa maganar ta, domin sosai zafin ya shige ta

Matso da fuskar sa kusa da nata yayi yana huci, idanun sa sun sake yin jazur fiye dana da, cikin amon muryan sa me haɗe da fushi yace, "Wlh kinji na rantse miki idan har kika ba ma wani daman riƙe hannun ki; ba shiga jikin ki ba ma, wlh wlh sai kinyi dana-sanin sani na a rayuwan ki! bazan hana ki rabuwa dani ba, sannan bazan hana ki aikata duk abinda kike so ba, fine ki aikata kinji ko?" Yaƙarike maganar da girgiza ta yana ware mata jajayen idanun sa, sai kuma ya janye ta daga gaban sa ya nufi ƙofa dasauri ya fice

Duk da ba wani jan ta yayi ba sai da ta faɗi ƙasa, sabida rashin ƙwarin jiki, ƙofan tabi da kallo cike da tsoro a ranta, babu shakka tasan Kishin da yake mata zai iya aikata komi, idan tace komi tana nufin komi zai iya yi a kan ta, sai dai kuma ba ta tunanin zata nuna tsoro ko gajiyawa da buƙatan ta, domin baza ta zauna dashi ba ya biya mata buƙatan ta ba, sannan kuma ya hana ta zuwa inda za'a biya mata, tabbas zata ci gaba da tunzura sa don ganin ta cin ma burin ta

Itama miƙe wa tayi ta zura Takalman ta, sannan ta ɗau gyalen ta; ta rataya a kafaɗa tafice dasauri.




             ▪️▪️▪️

      Motan sa ya gangarar da ita gefen titi, babu abinda zuciyar sa ke yi sai suya, iska kawai yake faman fesar wa daga bakin sa yana riƙe da sitiyarin motan, ya rasa meke masa daɗi a lokacin, sabida kalaman ta daga jiya zuwa yau sai kai komo suke masa a rai

Hannu ya saka ya soma hargitsa gashin kansa cike da tsagwaron KISHI dake cin sa, sai kuma ya kwantar da kansa jikin kujeran yana lumshe kyawawan idanun sa, ya jima ahaka be ɗago ba illa numfashi da yake sauke wa yana faman ci je leɓe, daga ƙarshe kuma yayi wa motan keey ya fige ta da gudu yayi gida.

      Gate man na buɗe masa Gate ɗin gidan ya kutsa motan ciki, a parcking space yaja birki yana kashe motan, sai dai be yi yunƙurin fitowa ba illa ma gyara zaman sa da yayi yana dafe kansa.




▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

        Eyeglasess ɗin fuskarta ta sake gyara masa zama akan cikakkiyar kamilalliyar farar fuskar ta, murmushi yalwace a fuskar ta take kallon su tana magana, "Ba na son ku je ku zauna acan har in kira waya, idan kuwa kuka bari na aikata hakan, to Ni da ku ne, don kun san bazan sake barin ku zuwa ba".

Da sauri Batool ta dafa gwiwowin ta, har da ranƙwafo da kanta tana faɗin, "Wlh Mamy baza mu daɗe ba, idan muka je ma muna gaishe ta da jiki zamu dawo".

Jinjina kanta Mamy tayi kafin ta maida idanun ta kan Maimuna tace, "je ki kira min Aƙilun zan ba sa saƙo ne".

Da sauri Maimuna ta tashi tafice daga ɗakin Mamyn, da gudu ta nufi hanyan parlour, ta buɗe ƙofan fita tana shirin saka kai waje taji tayi karo da mutum, kafin ta tabbatar da wanda suka ci karon, sai ji tayi an janye ta da ƙarfi an yi wurgi da ita gefe, ai babu shiri ta saki siririn ƙara jin ta faɗa a saman hannun ta, da sauri ta ɗago kanta tana bin sa da kallo idanuwan ta cike fal da hawaye

Shi kuwa be ma bi ta kanta ba, ya taka yashige fuskar sa a ɗaure tamau kamar be taɓa dariya ba

Bata dena kallon sa ba har ya shige ɗakin Mamy, sai taja majina tana matse idanunta hawayen ciki suka samu daman zubo wa, jiki babu ƙwari ta tashi tafice don kiran Aƙilu drever'n su.



        Tura ƙofan yayi da sallama ciki-ciki

Mamy da Batool suka amsa mishi duk kan su suna juya wa ga ƙofan, dasauri Batool ta miƙe tanufi ƙofan tana mishi sannu da zuwa

Be amsa ta ba, ita kuma tafice abun ta

Tako wa yayi ya zauna a kan kujeran dake cikin ɗakin, hakan yasa yake fuskantan Mamy dake zaune gefen gadon ta tana kallon sa

"Baba na lafiya kuwa?" Ta tambaye shi cike da kulawa sabida sauyawan da tagani a tattare dashi

Sakin faukar sa yayi sosai yana ƙoƙarin dai-dai ta kansa, cikin ƙwaƙulo murmushi yace da ita, "Mamy lafiya ƙalau me kika gani?"

Hakan yasa tasaki murmushi wanda ya zame mata ɗabi'a, koda yaushe fuskar ta a sake yake cike da annurin fara'a, sake tsare sa da idanu tayi tace, "Baba na kana son ɓoye min halin da kake ciki ko? Jiya haka ka wuni da ɓacin rai, yanzu ma ga shi ka dawo a yanayin, but kana son ɓoye min, Why?"

Sosa Kansa yayi cike da basarwa yace, "Mamy babu komi fa, ki yarda dani, idan da akwai ke ce ta farko da zan sanar ma wa".

Mamy ta murmusa cike da ƙaunar ɗan nata, shi dai daban yake cikin ƴaƴan ta, koda yaushe a zurfin ciki yake, idan har abu ba yayi tsamari bane, ba ya iya fitowa fili ya sanar musu su da suke iyayen sa, ya dinga ƙumbiya-ƙumbiya dashi kenan a ransa, sai dai wuni yana cikin ƙunci da ɓacin rai, wanda hakan ya jawo ba kasafai zaka ga yana shiga cikin jama'a yana walwala ba..



"Mamy har yanzu Abba be dawo bane?" Maganar sa ta katse mata guntun tunanin ta

"Be dawo ba, lafiya dai ko? In ce dai ba wani abun ka samo zaka bashi Ni ka hana Ni ba?". Tayi maganar cike da barkwanci

Hakan ya saka shi sakin yalwataccen murmushin da yafito da jerin haƙoran sa

Sanyi taji aranta ganin ya ɗan saki ransa fiye da ɗazu ɗin, hakan yasa taci gaba da jan sa da hiran tsokana don dai tadawo mishi da walwalan sa

Shiyasa sau tari yafi ƙaunar kasancewar ta kusa dashi fiye da kowa a duniyar nan, tabbas uwa daban ce, a duk sanda yake cikin matsala, ita ke fara gane damuwar sa fiye da kowa dake gidan, that's why yake tsananin ƙaunar mahaifiyar shi fiye da komi da kowa dake cikin duniya.




         ▪️▪️▪️


      Koda Maimuna tadawo kiran Aƙilu drever, zaman ta tayi a Parlour batare da tayi yunƙurin komawa cikin ɗakin Mamyn ba.

       Tana zaman itama Batool tafito tazauna gefen ta tana tambayan ta, "shin ta kira Aƙilun?"

Kafin ma taba ta amsa Aƙilu ya shigo yana baza idanuwa cikin parlour'n, hannun sa ɗaya riƙe da aswakin da yacire daga bakin sa ya ƙariso cikin parlour'n, ya zube ƙasa yana faman washe baki tare da yiwa Batool kirarin da ya saba

Ita kuwa nan ta biye masa suna kwasan dariyan Aƙilun daga ita har Maimuna, kasancewar sun fi saba wa da Batool ɗin, kullum suna cikin surutu da junan su, ita kuma Maimuna koda yaushe dama nata ido ne idan suna yi, sai kuma ta dara idan abun ya bata dariya, idan kuma sun sako ta sai ta tsulmiya baki, dayake ita ɗin ba me yawan surutu bane, bata da hayaniya ko kaɗan.



         Lokacin ne Mamy da ABUL KHAIRI suka fito daga ɗaki

Kai tsaye ABUL KHAIRI hanyan ɗakin sa ya wuce ko kallon inda suke be yi ba




Mamy ne taƙariso cikin parlour'n ta zauna tana amsa gaisuwar Aƙilun, sannan ta kalli Maimuna tace, "Maimuna tashi ki haɗa wa yayan ku abincin sa ki kai masa".

Amsa mata tayi da "Toh". tana miƙe wa tsaye, ta kalli Batool tana mata alama da ido tabiyo ta

Maƙe kafaɗa Batool tayi tana mata dariya ƙasa-ƙasa

Sai Maimunan ta marairaice fuska tasoma tafiya, har da haɗe hannayen ta biyu alamun roƙo

Amma ƙiri-ƙiri Batool taƙi motsa wa, sai ma gwalo da tabi ta dashi

Babu yanda ta iya haka tanufi kichen jiki a sanyaye, tasan halin Yayan nasu yanzu abu kaɗan zaka yi masa kuskure yaci uban ka, bare ma shi da ya tsane ta fiye da kowa dake gidan, ko kaɗan bata san meyasa ba ya ƙaunar ganin ta ba, shiyasa ba ta son ma a aike ta wajen sa bare tayi kuskuren abun da zai haɗa su.




       Ita Mamy tuni ta maida hankalin ta kan Aƙilu tana bashi saƙo, sai kuma tajiyo tana kallon Batool ɗin tace, "ke baza ki je ki shirya bane kin zauna? Ai kuwa idan Abban ku ya dawo ya hana ku fita babu ruwana, ki zauna kasa kunne kina ji na kar ki tashi ki wuce".



Ai kuwa dasauri Batool ɗin ta tashi tayi hanyan ɗakin su tana faɗin "wlh Mamy Ni ban ma ji me kuke cewa ba".

Itama Mamy bata tanka ta ba tamayar da hankalin ta ga Aƙilu tana sallaman sa.



      Lokacin ne Maimuna ta fito daga kichen riƙe da Faranti a hannun ta, kanta tsaye tanufi ɗakin ABUL KHAIRI ta soma Nocking a bakin ƙofan, sai dai har ta gaji babu amsa, dole ta haƙura ta tura ƙofan ta shiga da sallama.

     Yana zaune a bakin gadon sa idanun sa kafe a kan ƙofan, ashe duk yana jin Nocking ɗin but yaƙi amsa wa

Shiyasa tana shigowa idanun su suka haɗe cikin na juna, saurin sad da kanta ƙasa tayi gaban ta na matsanancin faɗuwa, ko kaɗan ba ta ƙaunar ta haɗa idanu dashi sabida kwarjinin da yake mata, shi kaɗai ne mutumin da idan suka haɗa idanu dashi take jin daban a cikin rayuwan ta, tana shiga wani yanayi da har yanzu ta kasa fassara shi

Jiki a sanyaye ta ƙariso cikin ɗakin, tanufi gefen sa inda Centre table ke ajiye gaban gadon da yake zaune, akai ta ajiye farantin muryan ta na ɗan rawa ta soma gaishe shi, tare da son isar da saƙon abincin daga Mamy

Amma kuma ko ci kanki be ce mata ba

Don haka ta juya da ninyan fice wa batare da ta kalle sa ba, sai jin saukar dakakkiyar muryan sa tayi yana faɗin, "Kee Ina zaki je da wani dogon goshin ki anan wajen? Wa kika bari ya zuba miki?"

Saurin juyowa tayi kanta a ƙasa ta duƙa ta soma zuba masa abincin a cikin Plate, sai da ta gama sannan ta zuba masa Coke cikin Cup; tunda tasan yana so sosai, kuma ko ta tafi zai iya dawo da ita, shiyasa tayi gwanintan zuba masa kar tayi laifi

Mi ƙe wa tayi da zumman tafiya, sai ji tayi an riƙe ta.






      _wannan salon labarin na daban ne, ku kasance dani don jin cikakken labarin._

Zaku iya samu na a WATTPAD ɗina UMMUDAHIRAH. Please kuyi following ɗina na gode. 🤝


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment