Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, idanun mu suyi ta ƙone wa a banza".





           ********

      Ita kuwa Ɗahira da ta shiga ɗakin Maman ta, sai ta fashe mata da kuka tana faɗin, "wlh Mama zan bar gidan nan bazai yiwu Yaya Usman yazo yayi ta.." sai tayi shiru tana sake fashe wa da kuka tsaban takaici ya cika ta

Aunty Amarya kamar bata san komi ba tace, "wani Usman ɗin ba tun ɗazu ya fice ba?"

"Ina fa Mama, ɗaki na ya shiga, don Allah Mama Ni dai zan bar gidan nan bazan zauna kullum yana biyo NI ba".

"To ki je ina kenan?".

Sai ta matso hawaye tana cewa, "zan je gidan Kakalle (Baseera ƙanwar Kaka mahaifiyar Umma) ko kuma gidan Aunty Zulaiha ne".

"To kema kin san bazai yiwu ba tunda ba lafiya ne dake ba ko?"

"Amma Mama ai su ma za su iya kula dani, kuma naji sauƙi wlh babu abinda ke min ciwo".

"To Ni dai ban aike ki ba, idan kin tambayi Abbun ki ya barki shikenan". Inji Aunty Amarya tana ci gaba da ninke kayan da take yi

Ɗahiran bata ce komi ba ta wuce Toilet ta wanke hannun ta tare da fuskar ta, sannan ta fito ta haye kan kujera ta kwanta har da juya bayan ta, take nan komi ya soma dawo mata, sai tayi saurin buɗe idanun ta tana jan dogon tsaki, jinta take yi kamar yana jikin ta har yanzu

Aunty Amarya dai na jinta bata ce komi ba taci gaba da abinda take yi.




       Sai ga Abbu ya shigo ɗakin

Aunty Amarya ta amsa mishi sallaman da yayi

"Ah ah Mamana lafiya kika zo nan kika kwanta?"

Da sauri ta tashi tana faɗin, "lafiya lau Abbu, dama kai nake jira".

"To gani Mamana Allah yasa dai ba wani abun bane?" Yayi maganar yana zama a gefen ta saman kujeran

Murmushi tayi tace, "dama zan tambaye ka ne ina son zuwa gidan Kakalle ko gidan Aunty Zulaiha in Yi kwana biyu".

Ɗan ware ido yayi yace, "kai kai ban aike ki ba, ke da baki da lafiya?"

Cikin marairaice fuska tace, "Please Abbu wlh na warke kaji?"

"To shikenan, amma sai dai ki je gidan gwaggon nawa domin gidan Zulaiha yayi nisa da yawa, gwara can zata fi kula dake".

"Yauwa na gode Abbu bari inje in shirya yanzu". Tayi maganar cikin farin ciki tana tashi ta fita da sauri

Aunty Amarya tace, "ai da baka barta ba".

"Kin san ba na hana Mamana abinda take so, ki barta taje hakan ma zai sa ta samu hutu kwana biyu, kin san idan tana nan zata ce zata koma wajen akin ta, amma yanzu can ba lallai Gwaggo ta barta ba, zan ma kira ta a waya in faɗa mata".

"Haka ne". Cewar Aunty Amarya tana tashi da kayan da ta gama ninke wa ta nufi wardrobe ɗin ta don zuba wa

Shi kuma tuni ya tashi ya fice.




               ******

        Ɗahira da ta fita sai ta wuce wajen Kaka ta sanar mishi zata je gidan Hajiya Baseera tayi kwana biyu

Shima sai da yayi mata faɗan, "bata da lafiya be kamata taje ba".

Amma takalallame shi da daɗin bakin ta tuni ya yarda, har yana bata saƙon gaisuwa

Fadil shi kuma nan ya maƙale mata sai ya bi ta, inyaso zuwa anjima shi zai dawo

Tace mishi, "ya biyo ta su je".

Part ɗin su suka wuce, suka shirya, ita da kayan ta a ɗan jaka suka fito, Ali drever'n su shi ya tafi kai su tunda Aunty Amarya ta ce kar ta sake tayi tuƙi.






⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫


         "Suhail kira min Auntyn ka a ɗaki". Cewar Abba da ya fito daga ɗakin shi yana saɓa malin-malin

"To Abba". Inji Suhail ɗin yana tashi da sauri bayan ya ajiye remote ɗin hannun shi

Shi kuma ƙanin shi me suna Abdulra'uf da suke kiran sa Abdul; da sauri ya tashi ya nufi wajen Abban yana faɗin, "Abba na nima zan je".

Hannun sa ya riƙe suna zama, da murmushin sa yace dashi, "a'a Abdul, ai ba nan kusa bane inda zamu je, kuma ɗaurin aure zamu je. Ka bari dai zan yi muku tsaraba ko?"

Gyaɗa kansa yayi cike da murna

"To kaima kira min Maman ka a ɗaki".

Abdul ɗin na tafiya, shi kuma Suhail ɗin ya fito da kuka, Direct wajen Abban ya nufa dake tambayar shi "me ya faru dashi?"

Cikin kuka ya sanar mishi "Hajja ce ta duke shi".


"To kayi shiru kaji? Kayi haƙuri baza ta sake ba". Abba yafaɗa duk ransa babu daɗi yana shafa mishi kai

Aunty Jamila da ta fito daga ɗaki ita da Abdul ɗin tace, "ah ah kukan me kake yi kai kuma?"

Be iya ce mata komi ba tunda kukan yaci ƙarfin shi

Sai ta kalli Abba tana ce mishi, "har ka fito Alhaji?"

"Eh na fito, ki rarrashe shi don Allah bari in zo". Yace hakan yana tashi ya wuce ɗakin Hajja Fatu. Yana shiga ya ganta kishingiɗe tana sakace. Da kallo ya bi ta ranshi a ɓace yace, "Wai Fatima me kike so ki zama ne? In aiko yaro ya kira ki shi ne kika dake shi?"


Kallon shi tayi itama da fuska a haɗe tace, "kai baka da ƙafan zuwa ka kira Ni ne sai dai ka aiko min agola ɗaki? To wlh duk ranan da ya sake shigo min ɗaki; wlh tallahi sai na farfasa mishi jiki".

"To idan kin fasa don Allah, tunda zaman lafiya ne ba kya so, to, ina dai-dai dake kar ki fasa kinji? Sannan idan kin so yau ma kar in dawo in tarar baki yi abinci ba, wlh ranki idan yayi dubu sai ya ɓaci, duk iskancin dake kanki zan sauke miki". Yana gama faɗar haka ya fice da sauri

Tsaki ta ja ƙasa-ƙasa tace, "kaɗan ma ka gani, ai ka auro wacce zata yi maka amma ba Ni ba, daga yau ita sai ta ɗauke maka duk abinda nake maka". Sai ta sake jan dogon tsaki tana ɗaukar wayan ta ta hau kiran layin Hajiya Sa'ima.





           ********

      Abba na fita sallama yayi wa Aunty Jamila ya fice

Ita kuma sai taja yaran nata suka shige ɗaki tunda babu abinda za su ɗauka a parlour'n, dama haka suke yi sabida baƙin halin Hajja Fatu.




          Tana shiga Abba ya dawo da ninyan ɗaukan keey ɗin motan shi, ɗakin sa ya shiga ya duba be gani ba, sai ya tuna jiya a ɗakin Hajja ya sauka, kuma ya tabbata ya bar shi can, sai ya wuce can ɗin don ya ɗauka, amma yana shirin buɗe ƙofan ya jiyo maganar ta, dayake ba a hankali take maganar ba kasancewar ta san ya fita

A dai-dai lokacin take faɗin, "Ni ba wannan ba Hajiya Sa'ima, maganar wancan matsiyaciyan da nake son a raba ta da Usman, gaba ɗaya na dena runtsa wa tunda yaron nan ya fara nuna yana son komar da ita ɗakin shi, kenan buri na bazai cika ba na mayar da ita bazawara?.." sai tayi shiru tana sauraron Hajiya Sa'iman. Kafin kuma tace, "so nake yi yanzu mu koma wajen Malamin nan ya yi min aikin da ya fi wancan, wlh muddin ina numfashi nayi alƙawari bazan taɓa bari A'isha da ɗiyar ta su yi rayuwar jin daɗi ba, ada naci wannan alwashin bare yanzu da suka yi min sanadin mutuwar ɗana da nake matuƙar so, a kan shi duk na rasa wata ƙima ta a gidan nan, shikenan min ɗana na miji amma na rasa shi, dole ne in sake sanya mummunan gaba da tsana a tsakanin su, ta yanda ko ya ƙi ko ya so sai ya sake ta, su kuma burin su na son su ga sun daidaita su bazai taɓa cika ba, har ita Hajiyan ma wannan karon sai na haɗa ta da Malam tunda ta nuna yanzu ta dawo da son tsinanniyar...."



Daga nan Abba ya dena ji ya juya da sauri jikin sa na rawa, gaba ɗaya jin sa yake yi a wani irin yanayi, cike da ɓakin ciki da tsantsan ɓacin ran da kalaman Hajjan suka saka shi, sai ya wuce kanshi tsaye ɗakin Kaka


Inda suna zaune su uku, shi da su Abbu suna zaman jiran Abban ya zo su wuce ɗaurin Aure.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_





        *EPISODE Sixty Seven*


          Yanda ya shigo musu ranshi a ɓace sai duk suka hau tambayar shi

Nan yake sanar musu da komi abinda yaji Hajja Fatu tana faɗi

Gaba ɗaya su kansu hankalin su ya tashi, "shin tun yaushe Hajja take wannan ɗabi'ar ba tare da sun sani ba? A ganin su dai suna zaune lafiya da Aunty Amarya, me ya jawo wannan mummunan tsanar?" Duk kan su sun shiga damuwa da rashin jin daɗin abun

Sai Kaka yace wa Abban, "ya je ya kira wo ta".

Abba juya wa yayi ya koma can Part ɗin nashi, inda ya cidda ita tana wayan har yanzu bata gama ba, tsamo-tsamo ya kama ta tana wayan kansacewar ya bankaɗo ƙofan ne ya shigo

Sai duk ta daburce ta rikice ta rasa inda zata saka kanta. Yanda ta ga idanun sa sun kaɗa sun yi ja sai ta sake daburce wa, domin ta sadakar ma ya gama jin ta, tana shirin mishi magiya har ta duƙa a ƙasa

Sai ya dakatar da ita daƙyar ya furta, "ki ajiye kalaman ki ki biyo NI mu je". Yana faɗa ya fice ya bar ta a wannan mawuyacin halin

Bata da tsimi bare dabara dole ta tashi tabi bayan shi zufa na keto mata, ta rasa ma wani addu'a zata kama tayi sabida tsaban tashin hankali, idan kuwa tabbas Abba ya ji abinda take faɗa ai ta kaɗe, shikenan asirin ta ya tonu, "wayyo Allah na na shiga uku Ni Fatu". Bata sake rikice wa ba sai da taga sun shiga ɗakin Kaka

Kaka ransa a ɓace yace, "ashe ke mutumiyar banza ce Fatima? Duk Nasihan da muka yi miki ashe baki saduda kin zama mutumiyar kirki ba? Duk abinda ke faruwa tsakanin Usman da Nafeesa ashe duk ke ce kika jawo? Kina kuwa so ki gama da duniya lafiya? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. har wajen Boka kike zuwa a kan kin ga kin muzguna wa bayin Allan nan wato? Shin ina hankalin ki yaje Fatima? Wlh yau ina tirrr da halin ki, ina tirrr da kasancewar ki ɗiya a wuri na". Sai ya kalli su Big Dady yace, "kai ku kira min gaba ɗaya mutanen gidan nan domin kowa ya san me ke faruwa, wannan ba abun ɓoye wa jama'a bane tunda abinda kika zaɓa wa kanki kenan, har ita Ihsan ɗin ku kira min ita". Kaka ya ƙare maganar cikin matuƙar ɓacin rai da zafi

Su kansu duk sun sha jinin jikin su ganin yanda Kaka ya nuna tsantsan fushin sa, abun da rabon shi da shiga irin wannan halin su kansu baza su iya tuna wa ba, ko kaɗan be da nuna fushi sosai ko da kuwa ranshi a ɓace ne, bare kuma duk sun san yanda yake son Fatima sosai, shi ne silan auren ta da Abba, don shi ya zaɓa mishi ita domin su cika burin su na son haɗa yaran su aure shi da Abokin shi kuma aminin shi Haidar, wato mahaifin ita Hajjan

Shiyasa ita kanta ta gama ruɗe wa sai kuka take yi, bata taɓa jin cewa akwai ranan da asirin ta zai tonu ba nan kusa sai yau, kuma bata taɓa tunanin zata yi nadama da sauri haka ba, gaba ɗaya jikin ta rawa yake yi ta san yau ta ƙare mata, raguwar igiyar auren nata ma duk za su ƙare.




               A cikin mintoci har sun gama taruwa gaba ɗaya, har da su Shakira da aunty Zainab da kuma Yusra, Aunty Zulaiha CE kawai babu ita sabida ta fi su nesa shiyasa ba a kira ta ba, sai kuma Hajiya Hannatu mahaifiyar ita Hajjan da kuma Hajiya Baseera mahaifiyar Umma, tunda har ita an kira sun dawo ita da Fadil, Ɗahira kuma na can

Sai Usman shima da sai yanzu ya dawo daga aiken da Big Dady yayi masa.
        



                 Nan  Kaka ya sake sanar musu da duk abinda Hajja Fatu tayi, inda ya ɗaura da cewa, "ba don ƙasa ta rufe min Aboki na ba; wlh wlh baki isa ki sake zamar min a gida ba, duk da ke ɗiyar ƙanwa ta ce yau da sai na raba auren ki da Babana, sai dai ina tuna girman Amintar mu da Haidar, wanda ina ganin kamar na ci amanar shi ne idan yau na wulaƙanta ki, Fatima kin ci arziƙin ke ɗiyar aboki na ne ba ɗiyar ƙanwa ta ba, shiyasa a yau zan bar ki kici gaba da zama da ahali na, idan kin tuba don kanki, idan kuma kina ganin hassada dake cikin ranki zai kai ki kici galaba a kan A'isha da ɗiyar ta, to, mu zuba ga ki ga duniyar nan, Allah yana kallon ki, shi ne kuma yake nuna miki ishara a duk abinda kike yi, idan zaki hankalta tun yanzu ya kamata ki yi tunda ga shi Allah ya ɗauke miki ɗan ki ɗaya a kan wannan baƙin halin naki, kaɗan ma kika gani, bazan hana Babana ɗaukan mataki a kanki ba, sai dai ban yarda ya sake ki ba sabida albarkacin wanda kika ci, amma ki sani wannan shi ne damar ki ta ƙarshe Fatima".

"Yaya wlh ban ji daɗin abinda kayi ba, ka bar ta ya sake ta shi ne kaɗai maslaha, zaman Fatima a gidan nan be da wani amfani, tunda ita abinda ta saran ma kanta kenan, wlh kin yi asara kin kuma bani kunya, bazan miki baki ba amma kaɗan kika gani, kuma in Allah ya yarda yanzu zaman Usman da Ɗahira aka fara, duk sharrin da kike bin A'isha da Ɗahira sai dai ya koma miki, da Allah suka dogara kuma baza su taɓa taɓe wa ba".

Gaba ɗaya parlour'n tsit suka yi suna sauraron faɗan Hajiya Hannatu da take tayi ba sassauta wa, in  banda kukan Hajjan babu abinda ke tashi

Daga baya ma Hajiya Hannatun ita da Hajiya Baseera sukai ta mata faɗan tare, sai da suka wanke ta soso da Sabulu

Kaka ne ma ya tsayar da su ya ce, "ya isa haka".

Sai a lokacin Abba yayi magana, inda ya ce, "daga yau ya soke aikin Hajja Fatun baza ta sake zuwa aiki ba ko da kuwa wani asibitin ne, kuma ya raba ta da Hajiya Sa'ima, idan har ta sake mu'amala da ita ya sani, to, daga ranan shi ya yanke alaƙar aure da ita".

Babu wanda ya hana shi kuma a kan hukuncin nasa, gani ma suke yi kaɗan yayi mata, domin ba don da Kaka ya hana sakin ta ba; da tuni ta tsufa a gidan su

Haka kowa ya tafi yana tirr da halin Hajja Fatu, inda ita kuma ta sha kunyan duniya

Usman haka ya tafi duk ranshi a ɓace, ya so ya tanka amma ya san sai dai ran kowa ya ɓaci a wurin, shiyasa yayi shiru. Shi ya ɗauki su Hajiya Hannatu ya tafi da su, domin so yake yi idan zai kai Hajiya Baseera ya gano Ɗahira tunda ya ji suna faɗin, "tana can".






             ********

      Ɗahira na zaune a Parlour tun fitan su Hajiya Baseera ta tashi ta ɗauko lemo Mountain Dew ta hau sha, sai da ta kusa shanye wa kafin taje ta ɗauko mata madara na gari ta sake sauran lemon a Cup, sai ta dinga zuba madaran tana juya wa har sai da yayi kauri sosai, kafin ta saka cokali ta hau shanye wa

Dama kafin su fita ita da Fadil sun girka faten dankali sun ci tare, suna gama wa ne aka aiko kiran Hajiya Baseera shi ne suka koma tare.




             Tana gama shanye wa sai da ta lanɗe kofin tass kafin ta kai kichen ta dawo ta kwanta a doguwar kujeran ta, kamar zata yi barci sai kuma ta sake jin kwaɗayin girka shinkafa, haka ta wuce kichen ta haɗa shinkafan ta me manja da ya ji daddawa da yaji zaƙwai, ta dawo Parlour ta ware ƙafafu tayi ta tusa wa a cikin ta, duk da ta ƙoshi amma tsananin kwaɗayin girkin ya hana ta sukuni, haka take ci tana jan majina saboda azaban zafi dana yaji, amma bata saurara mishi ba har sai da ta kusa cinye wa tass ya rage saura loma biyu

A lokacin ne su Usman suka shigo parlour'n da sallama, gaba ɗaya kallon ta suke yi ganin yanda take ta faman haɗa gumi ta warware ƙafafu Plate a gaban ta tana ta siɗe yatsu

Itama kallon su tayi, lokaci ɗaya ta haɗe rai ganin har da Usman, sai tayi saurin janye nata idanun tana saka hannu da sauri ta kwashe sauran ta cinye tana miƙe wa tsaye, da Plate ɗin ta wuce kichen ta je ta ajiye Sannan ta je Toilet, sai da ta wanke hannun ta da baki sannan ta ɗauraye fuskar ta kafin ta fito tana zama can kujeran dake kallon wanda suka zauna a tare, tace, "har kin dawo Kakalle?" Tayi maganar idanun ta a kan Hajiya Baseeran

Ita kuma sai da ta sauke numfashi kafin tace, "iy na dawo, na tsaya ina ganin ikon Allah ne Ɗahira, yanzu ba da zan fita ba kika gama cika cikin ki da abinci ba?"

Ɓata fuska tayi tace, "Kakalle wlh kamar ban ci komi bane, kuma na ga ai kun daɗe da fita".

"Eh na ga alama ai, tunda ga shi nan daƙyar kike numfashi". Hajiya Baseeran ta faɗa tana kallon Ɗahiran dake ta faman gyara zama ta gagara zama waje ɗaya don daƙyar take iya nishi, sai jan skert ɗin ƙasa take yi saboda ya tamke mata cikin

Shi Usman ma dariya ta ba shi, shiyasa ya kasa jure wa, domin tunda ya shigo da kallo kawai yake ta bin ta yana ganin ikon Allah

Ganin yana murmushi sosai sai ta tsargu ta kalle shi ta balla mishi harara tana tashi zata wuce ɗakin da ta sauka

"Ah ah Ina kuma zaki je? Ko sannu ma baki yiwa mijin naki ba kuma Kinga tare muka shigo?"

"Ina zuwa Hajjaju bari in cire wannan skert ɗin ya matse min ciki". Tayi maganar tana shige wa ɗakin

Dariya Usman yayi yana kallon Hajiyan itama da take taya shi, yace, "wai lafiyan wannan yarinyan ƙalau, ko dama haka masu cikin suke da cin tsiya tun ba'a kai ko ina ba?"

"To ai ka san kowa da irin nashi, wani sai yana ƙarami ne ka ga ya fi cin abinci, wani kuma sai ya girma, to ƙila nata haka yake, ga ta nan fa har raman nata ya shige, har ta fi kyan kallo ma yanzu wlh, da kam kamar a hure ta, ko kai ai zaka fi jin daɗin ta a haka mata tubarakalla".

Murmushi kawai yayi yana zaro wayan sa cikin aljihu jin an yi masa Text.




        Lokacin Ɗahira ta fito ta sauya shigan ta cikin doguwar riga fara me gajeren hannu, tana da taushi sosai don kamar na Barcin nan ne, sai hula da ta sanya a kanta shima fari me tuntu a tsakiyar kai. Zama tayi tana faɗin, "me ya faru da aka kira ki Kakalle? Allah yasa dai lafiya?" Tayi maganar hankalin ta duk a kanta tana jiran jin abinda zata faɗa, don dama har da jiran ta take yi domin taji abinda ke faruwa, tunda ta so ta bi ta tace mata, "a'a baza ta je ba". Kuma ta san ba lafiya ne ba, ba don haka ba da tuni ta shige ɗaki domin baza ta dawo ta zauna ba tunda ta ga da Usman suka zo

"To gagarumin abu ne dai ya faru, yau dai asirin Fatu ne ya tonu, ayi yarinya sam ta fita daban da ƴan uwan ta, wannan wani irin tsana ne haka?" Nan dai ta kwashe komi ta sanar mata, kana ta ƙara da faɗin, "Ni ina ga Ɗahira ba laifin mijin ki bane, a gani na gwara ki koma gidan ki ku ci gaba da zama tunda gaskiya ta bayyana, duk abinda yayi miki ba a cikin hankalin shi bane, taya ma kina a matsayin jinin sa zai nuna miki wannan rashin imanin? kema zaki gane tabbas ba a hankalin shi yake ba, abun da nake roƙon ki da shi ki manta komi ya wuce domin ki ba ma mara ɗa kunya, duk sharrin da take bin ki da shi ki nuna mata Allah ya fi ta, kar ki taɓa bata damar da zai saka ta cin ma burin ta".

Ɗahira da take ta faman kuka tun jin labarin komi, sosai zuciyar ta ke mata zafi, "meyasa Hajja Fatu ta tsane ta? Me tayi mata a rayuwa?" Abinda take ta ambata a ranta kenan tana ƙara Volume ɗin kukan ta

Hajiya Baseera rarrashin ta ta hau yi tana faɗin, "Ke yanzu ba kuka zaki yi ba, yanzu kuka ya ƙare tunda kin gano musabbabin abinda ke faruwa, mijin ki kawai zaki riƙe gam kinji ko?"

"Amma Kakalle ai tun kafin Hajja Fatu ta shiga tsakanin mu ya tsane Ni, meyasa ya tsane Ni tun ina ƙarama ta? Ki tambaye shi meyasa? Ina son in sani. Idan har be faɗa min ba bazan taɓa ganin farin shi a idanu na ba". Ta ƙare maganar tana kuka sosai

Usman da duk zuciyar sa ta karye da kukan da take yi, cikin raunin murya na wanda juriya ne kaɗai ya hana shi shima ya koka yace da ita, "na san nayi miki laifi Ɗahira amma kiyi haƙuri kinji? bani da hujjar da zan iya kare kaina a wajen ki, amma ina roƙon ki da ki sake bani dama, ki manta komi ya wuce, zan gyara Laifuka na nima, zan kuma mantar dake duk wani baƙin ciki na da kika ƙunsa, zaman mu tare ne kaɗai zai sa ki yafe min sannan ki manta komi a rayuwar ki, ina son ki Ɗahira! Ina matuƙar ƙaunar ki! bazan iya rabuwa dake ba ki yafe min kinji?"

Yanda Kalaman sa suke ratsa mata kunnuwa dole ne zuciyar ta ta karye, tana ji a ranta tabbas ta yafe mishi, sai dai baza ta iya buɗe baki tayi masa magana ba, baza ta iya ce mishi ta amince da zama da shi ba, tana ganin ya dace ta sake yarda dashi a karo na biyu? Har yanzu zuciyar ta bata gama yarda da shi ɗari bisa ɗari ba, tana ga kamar yaudaran ta yake yi, mutumin da ya tsane ta tun tana tsumman goyo har girman ta; kuma yanzu ya dawo ya ce yana son ta? Duk bakin da ya furta tsana ko da ya dawo ya furta so; to, kar ka taɓa amince wa da shi, domin ƙarya yake yi akwai manufa a zuciyar sa. sai ta sake fashe wa da kuka tana tashi da gudu tayi hanyar ɗaki ta shige

Da kallo suka bi ta har Usman ɗin domin ya kasa ma motsa wa, "Why can't she forgive him?" Ya tambayi zuciyar sa, sai kawai ya lumshe idanu hawayen ciki suna sauka a dandamalin fuskar sa

Hajiya ce tace mishi, "ya bi ta ɗakin ya rarrashe ta, tunda shi saɓo-tumaki ne da zai zauna yana mata kuka, kar ma ya fito ɗakin ba tare da sun daidaita ba". Sannan ta tashi ta wuce nata ɗakin



Shima kuma sai ya miƙe yabi bayan Ɗahiran, sai da ya tura ɗakin ya shige kafin ya rufo ƙofan har da saka keey.







_Nima dai na ware tunda an bar Ni a parlour._ 🙄
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




        *EPISODE Sixty Eight*


          A taƙaice please. Kuyi haƙuri sabida

Please Login or Register in order to submit comment