Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannu babu maganar zuwa kotu, saki ne dai dole ya bata idan ya gaji bata koma ba".

"To amma ai ita daughter za'a cuta zata yi ta zama da auren shi a kanta".

Kaka yace, "kowa ya tashi ya tafi in yaso sai muci gaba da tattaunawa da ku ko?".

Duk fita suka yi suka bar su Big Dady.




            ⚫⚫⚫⚫⚫


     "Ba dai kuka kike yi ba Ɗahira?"

Ɗago kai tayi tana kallon Maman nata, sai ta saka hannu ta soma share hawayen ba tare da ta iya magana ba

Ajiyan zuciya Aunty Amarya ta saki tana zama kana tace, "Ɗahira ba na son kina saka damuwa a ranki, Ni abinda nake gani kiyi haƙuri ki koma gidan Usman tunda ya nuna yayi nadama yanzu, har ga Allah ina ganin soyayyar ki a idanun shi, tunda kuma ga abinda yace kiyi haƙuri ki yafe mishi ki koma ki zauna a ɗakin ki, hakan zai fi miki sutura ke da abinda ke cikin ki, Allah ma ana mishi laifi ya yafe bare ɗan Adam".

"Mama ko na yafe mishi ni bazan iya zama dashi ba wlh, har yanzu ina ganin abubuwan da yayi min na kasa manta wa, shiyasa nake jin bazan iya sake zama a ƙarƙashin sa ba, idan har na koma gidan shi bazan taɓa jin daɗin zama dashi ba domin zuciya ta cike take da tsanar shi". Ta ƙare maganar cikin kuka

"To ki yi shiru ai ba na ce ki koma bane tilas, babu wanda zai tilasta miki Ɗahira sai da yardan ki, Kinga ga Abbun ki can na Kira na bari inje, ki dena fa kukan nan na faɗa miki".



"To". Ta amsa ta tana koma wa ta kwanta

Ita kuma Aunty Amarya fita tayi, ganin babu shi a Parlour sai ta wuce ɗakin ta, a nan ta ganshi zaune a kujera, ta ƙarisa ta zauna tana cewa, "Ga Ni Abbun Zulaiha. Ina ɗakin Ɗahira ne muna magana".

"Maganar me kuma?"

"Ka san bazai wuce na abinda ya faru ba, ta koma ɗaki tana ta kuka tunda abun kuka ba ya mata kaɗan ita".

"Allah Sarki Mama na. Ni a gani na gwara ta bar abun nan ya wuce ta koma ɗakin ta hakan zai fi ai, tunda ɗan Adam ajizi ne Allah ma muna mishi laifi ya yafe bare mu Mutane, yanzu maganar da muka gama kenan da su Baba, Amma shi sam Yaya Noor yaƙi yarda".


"Haka ne. nima abinda nake sanar mata kenan, tunda ka ga Usman ya furta hakan tabbas yana ƙaunar ta yanzu, kuma na tabbata duk abinda yayi mata a baya bazai sake aikata wa ba".


Murmushi Abbu yayi yace, "ai maganar ƙauna ma bata taso ba yanzu tunda ga rabon jika mun samu, dama mata da miji sai Allah tunda ga shi a faɗan nasu ne suka sama mana jikalle". Ya ƙare maganar yana dariya


"Kai Abbun su har da kaima?" Aunty amarya tafaɗa tana dariyan itama


"Eh mana. To ai gaskiya ce, kawai dai abinda zamu yi muyi ta tausan ta har ta amince ta koma, kin san ɗiyar taki halin ki ta biyo, wlh kuna da sauƙin kai, tunda ke kika manta abubuwan da ya yiwa ɗiyar ki kike son ta koma, itama na tabbata da ace zamu bata umarnin koma wa baza ta taɓa mana musu ba, sai dai na san hakan da cutarwa gwara mu lallaɓa ta har sanda taji don kanta zata iya koma wa, idan kuma mijin nata shi yayi ƙoƙarin shawo kanta shikenan, amma kar mu goyi da bayan ta wajen raba auren nan tunda be da wani amfani, Allah shi yaga abinda ya gani har ya kawo wannan cikin a tsakanin su, ni ina ga shi zai zame musu alkhairi".


"Haka ne Abbun su, to Allah yasa mu dace".


"Amin ya Allah. Yanzu ki kira min ita in tambaye ta kan wayan da tace take so".


"Ka bari sai gobe mana tunda naga yanzu kamar ta kwanta ai".


"To Allah ya kai mu, bari in duba Bilkisu ina dawowa". Yayi maganar yana tashi ya fice.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_





        *EPISODE Sixty Five*

        Usman dai tunda ya fita gidan shi ya wuce kai tsaye, gaba ɗaya duniyar tayi mishi zafi ransa duk ya gama ɓaci, shi a ganin shi don yace "bazai sake ta ba ne". Suke mishi haka, to su riƙe ta kar su barta ta dawo, shi kuma wlh bazai sake ta ba har sai sun gaji sun kawo ta da ƙafafuwan su, barin ma ƙasar zai yi tunda don suna ganin shi ne shiyasa suke mishi haka, tunda ya basu haƙuri ya ce zai zauna da ita meye kuma laifin shi a nan? Ko albarkacin cikin shi ai be kamata su raba auren ba. Wani zuciyar tashi tace, "amma ai kaima baka kyauta ba, ko kai ne a madadin ta zaka guje wannan auren, tabbas ka bata wahalan da in dai tana da hankali dole ta guje ka gaba ɗaya".

"Amma to ai na bata haƙuri, kuma na gane kuskure na bazan sake ba". Yayi maganar a fili yana hawaye. Sai ya mirgina kwanciyar sa yaci gaba da tunanin zucin shi dake ƙara mishi ƙunci da raɗaɗi, duk tunanin Ɗahira ya addabe shi ya rasa ya zai yi

Yau dai rana ɗaya ya tashi domin neman agaji a wurin Allah, abin da be taɓa yi ba, domin idan har ka ga Usman ya tashi da dare yana Sallah to tabbas yana cikin ƙunci ne sosai, yau dai ga shi haka ya tashi yayi ta jero salloli yana neman biyan buƙata wajen Allah, da kuma neman ya yaye mishi duk damuwar shi, Allah ya gani yanzu yana ƙaunar Ɗahira, yana jin son ta kamar ya kashe shi yanzu, be san ya aka yi ya faɗa wannan mugun son nata ba,  shiyasa gaba ɗaya sallan duk a kanta yayi

Be dena ba sai da kusan uku tayi, sai ya jira har aka yi sallan asuba yayi a wurin don bazai iya zuwa Masallaci ba, yanzu ɗin barci yake ji sosai, shiyasa yana gama wa ya kwanta.

        Be tashi ba sai wajen goma na safe, wanka yayi ya shiga kichen daga shi sai gajeren wando ya haɗa tea ya zauna a Parlour Yana sha, duk gaba ɗaya tunanin sa ya tafi ga hukuncin da zai yanke

Bayan ya gama ya tashi ya mayar da kofin kichen, ya wanke kafin ya koma ɗaki, kayan shi ya soma haɗa wa a Trolly har ya gama, sannan ya shirya cikin ƙananan kaya farar riga me wuyan V da gajeren hannu, sai wando jeans blue colour crazy, gaban mirror yaje ya gyara gashin kansa kafin ya feshe ko ina na jikin sa da turare, ya ɗauki agogo ya ɗaura a hannun sa sannan ya zira takalman sa sandal da ya zaro su daga ƙasan gadon shi, ya ɗan share kasancewar da akwai ƙura yaja Trolly ɗin sa ya fito, sai da ya kashe komi kafin ya fice, kai tsaye wajen motan shi ya nufa yana shirin saka wa a Boot

Hajiya da ta fito ta ƙaramin ƙofan gidan su ta hange shi, kwaɗa mishi kira tayi tana nufo shi

Sai ya juyo yana kallon ta fuska babu fara'a, gajeren tsaki yaja yana ƙarisa tusa Trollyn cikin Boot ɗin sannan ya rufe, ya nufe ta ba tare da ya amsa kiran nata ba

"Ina zaka je haka da kaya? Ba dai tafiya zaka yi ba a kan maganar nan?"

Sai da ya ƙumshe baki ya saki iska kaɗan tare da sake haɗe fuska yace, "tafiya zan yi Mom, idan sun gaji da jira na sai su aiko min ita".

"To a tunanin ka kana ganin hakan shi ne maslaha a wurin ka? Kar ka manta ita yarinyan nan ba ƙaunar ka take yi ba, memakon ka zauna ka gyara alaƙar ku a wajen ta shi ne kake son sake jagula lissafin ko? Kai a tunanin ka su Dadyn naka za su aiko maka da ita? to, ka dawo hankalin ka tun wuri ka sauya tunani ba na son shashanci kaji ko. Ka je Dadyn ka na kiran ka". Daga haka ta juya ta wuce ba tare da ta jira jin ta bakin shi ba

Shi kuma yana tsaye ƙiƙam yaƙi jirga wa sai bin bayan ta da yake yi da kallo, har ta ƙule wa ganin shi be motsa ba, sai ma ya saka hannayen sa cikin aljihu yaci gaba da tsayuwar sa a wurin. Sai da ya mula dan kanshi kafin ya taka ya nufi hanyar da ta biyo, kai tsaye Part ɗin su ya wuce ya shiga da sallama

Big Dady na zaune a kujera yana kallon labarai a t.v, dayake yau Saturday ne basu da aiki, duk da ba hutu suke ɗauka ba amma ba sa zuwa Hospital ɗin sai yamma ko kuma duk sanda suke so, idan kuma ana buƙatan su suna zuwa su duba mara sa lafiya su dawo, sun dai ɗauki weekend ranan hutun su ne sai an buƙace su tunda akwai likitoci kala-kala.

       Amsa mishi sallaman yayi ba tare da ya kalle shi ba

Shi kuma ya tako ya zauna a ƙasa jikin kujeran dake kallon wanda Big Dady ya zauna, be ce komi ba ya sadda kansa ƙasa

"Ina zaka je da Mom ɗin ka ta ganka kana saka akwati a mota?"

Shiru yayi ya kasa magana

"Da kai nake magana".

"I'm traveling".

"Ok to bani takardan nata tunda dai baza ka tafi da auren ta a kanka ba. I spoke and remained silent".

"Dady don Allah kuyi haƙuri ku yafe min don Allah Dady, wlh ina ƙaunar ta yanzu bazan iya rabuwa da ita ba, ku sake bani dama Please zan je in nemi afuwar ta, na yarda idan har ba ta ƙauna ta zan rabu da ita dan girman Allah Dady kaji?" Ya ƙare maganar da rarrafo wa gaban Dadyn yana me riƙe mishi ƙafa hawaye na tsiyayan mishi

Duk ya kashe mishi jiki shiyasa yayi shiru kawai yana kallon shi, har ga Allah yana ƙaunar su ci gaba da zama a tare amma kuma shi yana yin hakan ne domin amsar mata haƙƙin ta, Usman ya zalunta mata be kamata ayi shiru a bar shi haka ba, sai dai tunda ya ce haka; zai ba shi dama ya je ya nemi amincewar Ɗahiran, idan har ita taga zata iya zama da shi shikenan, idan kuma tace a'a dole ne sai ya amsar mata takardan sakin ta

"Ya isa haka". Yace dashi ganin yanda yake ta mishi magiya

Shiru Usman ɗin yayi kanshi a ƙasa amma hawaye be dena fita a idanun sa ba

Numfashi Big Dady yaja kafin yace, "tun farko Usman ba ka jin magana, mu iyayen ka mu zaɓa maka abinda muke ganin ya dace da kai amma ka nuna mana bamu isa ba, yanzu wa gari ya waya? Wlh Allah ne ya saka mata tun yanzu domin ka gane ɗan Adam ba abun wulaƙanta wa bane, a matsayin ta na ƙanwar ka jinin ka amma ka gallaza mata wannan azabar. Dama ɗaya tak zan iya baka kaje ka nemi amincewar ta, idan har ta yarda zata koma wajen ka falillahil hamdu, idan kuma tace a'a ka san baza mu taɓa mata tilas ba, ka tashi kaje".

Lumshe idanun sa yayi jin abinda Dadyn yace, zuciyar sa cike da murnan da be san iyaka ba yace, "thanks Dad". Sannan ya miƙe zai fice

"A haka zaka fita baka share hawayen naka ba?"

Ɗan juyo wa yayi yana murmushi ya saka hannu ya share hawayen, yana cire hannun sa suka haɗa ido da Hajiya dake bakin ƙofan ɗakin ta tana mishi murmushi, still shima murmushin yayi zai juya ya fice

Sai Big Dady ya sake cewa, "ina kuma zaka je baka yi Breakfast ba? Dawo ka karya zan aike ka Office ka ɗauko min saƙo dana manta da shi".

Usman ɗin be ce komi ba ya juya ya nufi dainning ɗin, bakin sa bazai iya faɗin "a ƙoshe yake ba" shiyasa kawai yabi umarnin sa ya zauna don yaci abinda zai iya

Hajiya ƙarisa wa tayi ta zauna tana haɗa mishi Breakfast ɗin tana tsokanar shi

Shi kuma murmushi kawai yayi, da yaga zata haɗa mishi da tea yace, "ta bar shi ya sha".

Big Dady dai na jin su be ce komi ba yaci gaba da kallon shi.




       Har sanda Usman ɗin ya gama ya dawo wurin shi ya amshi keey ɗin office ɗin, tare da faɗa mishi abinda zai ɗauko mishi, shi kuma ya wuce ya fice

Bazai iya tafiya be ga fuskar Ɗahira ba shiyasa kai tsaye ya wuce Part ɗin su.




           Duk suna zaune a parlour'n ban da Ɗahira dake kichen tana ma kanta faten tsaki da take sha'awan sha

Tana jin muryan Usman ɗin sa'ilin da yayi sallama yana gaishe da su Abbu, sai da gaban ta yayi muguwar faɗi tayi saurin dafe ƙirjin ta tana ƙwalalo ido, "kar dai ace wannan ɗan iskan ya zo maimaita min abinda yayi min ne jiya?" Tayi maganar a fili tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudun tsere

Jin kamar hiran su da Abbu ne yasa ta matsa da sauri ta leƙa kanta, ta hange shi yana zaune a kujera sai dai ya juya wa ƙofan kichen ɗin baya, sai Umma da Fadil a wajen, Aunty Amarya kuma ta tashi ta wuce ɗaki

Ajiyan zuciya ta sauke sai kuma taja gajeren tsaki ta wuce taci gaba da abinda take yi, sai dai duk bata da cikakken nutsuwa domin har ta yanke shawaran zama a kichen ɗin idan ta gama sai tasha faten nata tunda taji kamar be da alamar tafiya. Ta gama kenan tana zuba wa a Plate sai ganin shi tayi a kichen ɗin, kafin ma ƙamshin sa ya shigan mata hanci har ta ga dogayen ƙafafun sa a gaban ta, da sauri ta ɗago kai tana ware manyan idanun ta a kan shi da suka yi fari tarr babu ko kwalli

Wanda kallon nan ba ƙaramin sagar mishi da jiki yayi ba, sai da ya wani lumshe idanu ya buɗe su daƙyar ya sake aro jarumta wajen kallon ta

Ita kuma tuni ta janye idanun ta ta sake haɗe rai tana zazzare idanun, a ranta tana mamakin rashin kunya irin na Usman, ko dama haka yake? Ya zai shigo mata kichen ya baro su Abbu a Parlour? tana son mishi magana amma kuma haushin sa yasa tayi gum don taga iya gudun ruwan shi. Tana gama zuba faten a Plate ɗin ta rufe sauran a tukunya ta sunguma na Plate ɗin zata fice

Sai yayi saurin saka hannu ya damƙe nata yana matsa wa gaban ta, cikin sanyin murya idanun sa na kanta yace, "Nafeesata babu gaisuwa haka ake yi? Ko don na zama maƙiyin ki shiyasa har yanzu bazan samu arziƙin da za'a iya gaishe Ni ba? Domin ki fa nazo".

Da ya san yanda take ji da kasancewar su waje ɗaya da ko kaɗan be zo inda take ba, gaba ɗaya har raunin ta yana shirin fito wa sai dai sosai tayi Jarumtar dakewa, daƙyar ma take iya numfashi saboda yanda take ji a jikin ta, saurin janye hannun ta tayi ba tare da ta kalle shi ba tayi ƙofa ta fice da sauri

Shi kuma yabi bayan ta tana saka ƙafa a ɗakin ta shima yana saka wa

Dayake tuni Abbu ya fice wajen Kaka shi da Fadil, wannan dalilin ne ya samu ya biyo ta kichen. Ita kuwa Umma tana zaune ta hange su sun wuce ɗin, sai ta kama haɓa kawai ta saki wani ashar da ya suɓuce mata bata shirya ba.





              Ɗahira dake shirin zama a ƙasan ɗakin sai ganin mutum tayi a gaban ta. Da sauri ta ajiye Plate ɗin tana faɗin, "lafiya wai? Ka san dai be kamata kana biyo NI ɗaki na ba ko?"

"A kan me? Ba ke matata bace?"

Tsaki taja tana cewa, "ka dena ma tunanin wannan tun tuni na tashi a matsayin matar ka, Please Malam fitan min a ɗaki kaji ko?" Ta ƙare maganar tana nuna mishi hanya fuskar ta a tamke kamar bata taɓa sanin mutunci ba

Sai yayi guntun murmushi ya kawo hannu zai shafa fuskar ta tayi saurin matsar da fuskar, "hmm kin yi min kyau sosai Sweety, meyasa kike son min tsaki ne ki dena kin ji ba na so? Kuma na zo ganin baby na ne ko kar in zo?"

Jin haka sai tayi shiru ta zauna ta saka hannu a faten ta soma sha a hankali, duk da a takure take amma bata ko nuna hakan ba a fuska, nuna wa ma tayi tamkar ma babu shi a wurin

Shi kuma sai bin ta yake yi da kallo yana sake ƙare wa jikin ta da ya tafi dashi kallon tsab

Dayake tana sanye da riga da skert ne ƴan kanti Robber, rigan me wuyan V irin nasa fara, amma nata kamar vest ne don ya fi taushi sosai, sai skert ɗin me santsi ja da Flower's da aka yi da kalan fari, kanta sanye da hula na kayan

Sosai yanda yake bin ta da kallon yake shiga har can cikin jikin ta, gaba ɗaya ta rasa sukunin ta, duk yanda taso ta daure amma ta kasa sai ta ɗago kai tana bin shi da kallon harara cike da haushin kama sa da tayi yana mata wannan kallon maitan

Shi kuma sai a lokacin ya wani ajiye numfashi yana ware idanun sa da suka ƙanƙance suka soma sanja kala

Ranta duk a ɓace tace, "don girman Allah ka fita ka bani wuri kar wani yayi tunanin wani abu kake yi a nan, tunda kai baka da kunya Ni ina dashi".

Sai kawai taga ya zauna a gaban ta, daƙyar ya furta, "nima zan sha". Kafin ma ta ba shi amsa ya tsulma hannu a ciki ya soma kaiwa baki

Tsaban takaici da ya cika ta sai ta yunƙura zata tashi

Yayi saurin janyo ta ta koma ta zauna daɓas

Da kallo ta bi shi kamar zata yi kuka jin sai da ta bugu da ta koma ta zauna. "Wai kai ba ka iya sukuni ne sai kayi mugunta?" Tayi maganar a fusace tana banka mishi harara

Be ce mata komi ba illa ci gaba da yayi da shan faten, sai dai yana riƙe da hannun ta be saki ba

Fushi tayi ta kasa motsa wa bare tasha faten zuciyar ta sai tafarfasa take yi da haushin Usman ɗin, gaba ɗaya ya takura mata har hawaye sun soma taruwa a idanun ta, sosai ta kumbura tayi fam jira kawai take yi ta mishi bala'i, amma ganin yaƙi ce mata uffan ya zaƙe sai shan faten shi yake yi ya bar ta da tsinkewar yawu, sai da ta kalle shi kafin ta kalli Plate ɗin, sai ta saka ɗaya hannun nata ta janye tana faɗin, "wannan ai mugunta ne, ya za'a yi ka zauna kana shanye min faten ko kai ne me cikin?"

Sai kawai taga ya saki dariya yana kallon ta

Itama sai ta bi shi da kallon tana sake haɗe rai, idan yana dariya sosai yake mugun kyau sabida ba kasafai yake yin sa ba, shiyasa yake fita daban, ita kanta sai da yayi mata kyau, amma kuma tsaban neman magana irin nata sai ta dangwali faten ta shafa mishi a fuska babu zaton sa, a ranta tana faɗin, "yau zan yi maganin ka sai nayi maka rashin mutunci zaka fita a harka ta".


Zaro idanu kawai yayi ganin abinda tayi mishi


Ita kuma tuni ta sake dangwalo wa zata shafa mishi a ɗaya kumatun


Sai ya riƙe hannun nata caraf ya haɗa su duka biyun, lokaci ɗaya ya haɗe rai yana shirin magana


Ta riga shi da faɗin, "wlh idan baka fita a nan ɗakin ba sai nayi maka wanka dashi gaba ɗaya a jikin ka, dama ai Ni ƙazamiya ce ko ka manta? So zan nuna maka ƙazanta na yanzu wlh, sakar min hannu".


Murmushi yayi yace, "to kuwa zaki bi jikin nawa ki lashe shi tass, idan har kin shirya Bismillah". Ya sakar mata hannun yana bin ta da kallo


Sai ta miƙe kawai tana shirin fice wa


Ya janyo ta ta faɗa jikin sa sai ga ta ɗare-ɗare a cinyan sa


"Ina zaki je kuma baki lashe abinda kika saka min ba? Wlh sai kin kwalɓe shi ko kuma in miki abinda baki yi expecting ba".
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_





        *EPISODE Sixty Six*


        "Baza kiyi abinda nace miki ba? Ina nan fa dake har sai kin saka harshen ki kin shanye shi, idan kuma ba haka ba kin ji dai Aunty na kiran ki ko. Kuma kin san ƙarshe zata shigo ne tunda zata yi tunanin na tafi, tazo ta ganki a cinya na". Ya ƙare maganar da dariya

Ita kuma ta sakar mishi harara kamar zata yi kuka, ga shi tana son ta tashi amma babu hali ya kanannaɗo hannayen sa ta bayan ta ya riƙe ta gam, gaba ɗaya jikin ta yanzu babu ƙarfi sai rawa yake yi, ko kaɗan baza ta iya jure abinda take ji ba sai ta kalle shi kamar zata yi kuka tace, "dan Allah ka bar Ni.." sai tayi shiru ta kasa ƙarisawa

Lumshe idanun sa yayi yana matso da faukar shi kusa da nata, sannan ya buɗe yana kallon ta a hankali yace, "lashe min".

Lokacin har hawaye sun soma zubo mata tace, "a'a bazan iya ba".

"To Ni zan iya, ba na son ina ganin hawaye a fuskar ki, sabida yanzu Ni ba mugu bane a gare ki kinji ko?" Ya ƙare maganar da kai nashi bakin babu zato ya soma lashe mata hawayen

Da saurin ta ta janye fuskar baki na rawa tace, "meye haka wai? Ni fa.." sai ta kasa ƙarisawa saboda yanda jikin ta ke rawa ganin ya sake manna ta a jikin shi, da ƙarfi ta furta, "na shiga uku na". Sai ta fashe mishi da kuka tana son ƙwace kanta da ko ta halin ƙaƙa

Shi kuwa be saurare ta ba yaci gaba da kai bakin sa jikin ta duk inda yake so

"Wayyo Allana.. wayyo Allana Yaya Usman dan girman Allah ka dena na tuba Dan Allah wani zai zo". Tayi maganar tana kuka sosai gaba ɗaya ta rasa nutsuwar ta

"Dalla matsoraciya wlh ba komi zan miki ba, ƙamshin jikin ki nake so sai mu gaisa da Baby ko?"

Bata kai ga magana ba suka ga an buɗe ƙofan, gaba ɗayan su ƙofan suka bi da kallo suna bin Umma da ido kamar yanda itama ta hangame baki tana kallon su

Usman janye nashi idanun yayi tuni ya sake manne Ɗahira a jikin sa, har da ɗago ta ya matso da ita sosai jikin sa

Umma tace, "to Ɗahira fito Maman ki na ta faman kira kin zo kin maƙale a jikin miji".

Da sauri Ɗahiran ta kalle shi kamar zata nitse a wajen, still tana hawaye cikin sanyin murya tace, "don Allah ka sake Ni bari inje kaji?"

Idanun sa da suka kaɗa ya buɗe yana kallon ta yace, "to zaki dawo?"

Kan ma ya ƙarisa ta soma gyaɗa mishi kai da sauri

Murmushi yayi mata yana sakar mata kiss a laɓɓa, sannan ya sake ta

Sai a lokacin Umma ta juya ta tafi tana buga salati tare da tafa hannu, "yau mu dai mun shiga uku a gidan nan muna ganin iskanci ƙuraratan".

Ɗahira kuwa tuni ta fito ta wuce ɗakin Maman ta da sauri

Shima a lokacin Usman ɗin ya fito sabida ya san tunda ta tafi baza ta taɓa dawowa ba, yana jin abinda Umma ke faɗi be ce komi ba ya saka kai ya fice

Sai ta sake sakin salati tana cewa, "amma wlh Usman ba ka da ɓurɓushin kunya ko kaɗan, ka zo har sashin mu kace zaka nemi matar taka don jaraba? Bari dai Abbun su ya shigo dole fa a san abun yi, don bazai mayar mana da gida kantin karuwai

Please Login or Register in order to submit comment