Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

raka shi da harara wanda be san ma tana yi ba, lallaɓa wa tayi ta tashi a hankali ta isa ƙofan ta tura shi, kana ta koma ta kwanta a shimfiɗar ta, ta ɗan jima tana tunanin da ya zame mata jiki, wanda ba komi bane sai tunanin mutanen gidan su, sai kuma daga baya tayi addu'a ta shafa ta juya kwanciya tare da rufe idanun ta, babu jima wa kuwa barcin ya fizge ta.







            ******

      Fannin Usman kuwa tunda ya fita sai yayi tsayuwar sa a tsakar gidan ruwa na ta dakan shi, sai da yayi sharkaf wanda ya ɗau kusan mintuna goma a cikin ruwan, kafin ya samu ya wuce ɗakin kwanan shi, kayan jikin shi ya cire ya sauya da wani riga da wando farare na Fulani, sai kuma ya kwanta yana ta faman tunani, gaba ɗaya zuciyar sa ta hana shi sukuni babu abinda yake tuna wa sai Ɗahira, da sanda lokacin bata farfaɗo ba yana wanke mata jiki, har tunanin sanda ya ganta babu riga a can Turkay sai da ya faɗo mishi, shi kansa be san yana murmushi ba tsaban nishaɗin da yake ji a ranshi.




      Duk yanda yaso ya jure abinda yake ji game da feeling ɗin ta amma abun ya citura, bare yanda ruwa ya dake shi duk tsigan jikin sa ya gama tashi. ƙirr idanun sa sun kasa barci, dole ya miƙe ya bi umarnin zuciyar sa a kan zuwa ɗakin ta, shi kansa be san meyasa ba amma yana son zuwa gare ta ko da kallon fuskar ta ne ya riƙa yi, ya san a yanzu tayi barci shiyasa ya lallaɓa ya wuce ɗakin nata kanshi tsaye

A hankali ya tura ƙyauren ya shige, akwai fitilan aci bal-bal da bata kashe ba, da sanɗa ya ƙarisa kusa da ita ya sauke idanun sa a kan fuskar ta. Ajiyan numfashi ya sauke yana matsawa kusa da ita ya sanya hannun sa a hankali ya soma shafa mata fuska

The more Yana shafa mata fuska the more Yana ƙara jin feeling ɗin ta. Duk yanda yaso ya daure ya koma tunda yayi mintoci a ɗakin yana ƙare mata kallo, amma ina tuni zuciyar sa ta ingiza shi yin abinda be taɓa tunanin mata ba. Wanda ya kasa controling zuciyar sa da gangan jikin sa ga abinda suke muradi a halin yanzu.



     Kamar a mafarki haka take amsar saƙonnin nashi, tun tana iya jurewa domin a zaton nata lallai mafarkin ne, but a lokacin da ta farka tuni yayi nisan kiwon da bazai taɓa jiyo ta ba, duk yanda taso ta ƙwaci kanta amma ina ta gaza, haka take kuka tana roƙon shi saboda bata shirya zuwan ma wannan ranan ba, kuma ga wanda zuciyar ta ke cike da zallan tsanar sa, amma ta kasa cin nasara, dole tana ji tana gani ya raba ta da budurcin ta ba tare da ta iya ƙwatan kanta ba....





        Kuka ta fashe dashi a sanda tazo nan a tunanin ta

Da sauri Yusra ta buɗe ƙofan bayin tana kiran sunan ta. Sai ta ƙarisa wajen ta tana riƙo ta ganin ta a zube a ƙasa. Duk tambayoyin da ta jero mata a kan sanin abinda ke damun ta, amma taƙi ƙo motsa wa bare ta tanka ta, dole ta kamo hannun ta suka fito

Duk ƴan ɗakin da kallo suka bi ta ganin yanda hawaye ke zuba a saman fuskar ta. Kuma duk tambayar da suka yi mata sai dai tace musu, "babu komi". Sai gaba ɗaya tunanin su sai ya tafi a kan bayyanar cikin ne, duk da babu wanda ya kawo wani zargi wanda kowa zuciyar sa cike take da amince wa da cikin Usman ne, amma tabbas abun da ciwo a gare ta, kuma kowa ya gane abinda take ma kuka

Aunty Jamila ce kawai da bata gama sanin abinda ke faruwa ba, duk da ta san akwai saɓani a tare da su. Ita take ta faman rarrashin ta

Su Abbu dai fita suka yi a ɗakin. Inda Yusra ta mayar mata da ƙarin ruwan.




            Mutanen gidan basu koma ba har sai da bayan sallan isha'i yayi, inda suka tafi tare da Ɗahiran tunda an bata sallama.



           Suna koma wa Big Dady ya nemi Usman yazo ya same shi a part ɗin su. Nan ya titsiye shi a kan ya ba shi takardan sakin Ɗahira

Amma Usman babu kunya yace ma Big Dadyn, "shi fa yana son Matar sa yanzu bazai sake ta ba, bare kuma yanzu tana ɗauke da cikin ɗan sa, be ga wanda ya isa ya saka shi sakin ta ba".

Marin shi Big Dadyn yayi saboda jin kalaman sa

Daga Usman ɗin har Hajiya dake zaune tana sauraron su sai da suka shiga shock sabida zallan mamakin sa. Maganar sa ne ya dawo da su hayyacin su

"Mutumin banza mutumin hofi, har kai ka isa ka faɗa mana abinda ya kamata? Da can meyasa baka ɗauke ta a matsayin matar ka ba sai yanzu? Tunda kai mara kunya ne duk abinda kayi mata kace zamu bar ka haka, a kan daughter babu abinda bazan iya maka ba in dai in ƙwato mata haƙƙin ta ne..."

Da sauri Usman ɗin ya tashi tun kafin ya gama jin zantukan nashi ya fice yana zubar da hawaye.




      Hajiya da itama hankalin ta yayi ƙololuwar tashi a kan abinda Big Dadyn yayi, tace dashi, "haba Dadyn Zainab meyasa baza ka tausaya wa yaron nan ba? Wlh tunda har kaji ya buɗe baki ya ce yana son zama da matar sa, to, har zuciyar sa ne, kuma..."

"Ki yi min shiru Asiya baza ki koya min abinda zan yi ba, bari kiji wlh kema duk sanda na sake magana irin wannan kika sako min baki zaki ga abinda zan miki, tunda ke kike ɗaure masa gindi yake son mayar damu mutanen banza. Aure ne kuma babu fashi sai an raba shi". Sai ya tashi fuuu ya wuce ɗaki ya bar ta a nan.






             ***********

        Kai tsaye Part ɗin shi ya wuce, ya buɗe ƙofan ya shige sai kan gadon shi ya faɗa riƙe da kumatun shi har Yanzu, idanun sa na tsiyayar da hawaye kamar ba shi ne Jarumin nan me dakakken zuciya ba, samun ka ga hawaye a kyakykyawar fuskar sa sai an jima, amma yau sai ga shi a kan abinda be shirya masa ba yana zubar da hawaye, shi dai ya san cewa har zuciyar sa yanzu yana matuƙar jin ta, kuma bazai iya rabuwa da ita ba domin babu macen da ta cancanci zama dashi sai ita, ita kaɗai yanzu yake ganin ta dace da shi, ba zai taɓa iya zama da kowa ba sai ita, shiyasa kawai yake son daidaita komi ya wuce, amma kuma yana ganin ba sauƙi ne abun ba. Ya zai yi?

Ya jima a haka a wannan mawuyacin halin da ya kasa controling ɓacin ransa, babu abinda yake muradi yanzu illa ya saka ta a idon sa, amma kuma yanda yake ji bazai iya ko da motsa wa bane a wurin.




       A wannan daren daƙyar barci ɓarawo ya sace sa. Be farka ba sai ƙarfe 09:00am. Komawar sa bayan sallan asuba

Koda ya tashi wanka ya soma yi fuskar sa duk babu walwala, har wani kumbura tayi fuskar saboda damuwa da rashin barci da be samu yayi ba

Yana shirya wa ya fice yayi Part ɗin su Ɗahira, da shigan sa da sallama

Aunty amarya da Umma dake karin safe suka amsa mishi suna bin shi da kallo cike da mamakin ganin shi

Shi kuwa be damu da kallon da suke mishi ba, daƙyar ya saki fuskar sa ya gaishe su yana tambayan Abbu?

Umma ce ta ba shi amsa da faɗin, "yanzu ya fita shi da Fadil ai".

Sai ya ɗan shafa kansa yace, "Nafeesa fa?"

Sai duk suka tsaya suna kallon sa don basu fahimci da wa yake nufi ba

Tunanin ko Ɗahira ce yake nufi da Aunty Amarya tayi, shi ne tace mishi, "bata tashi daga barci ba".

"Ok bari in duba ta". Yayi maganar yana yin gaba ya shige ɗakin ta

Sai suka saki baki kawai suna bin shi da kallo cike da zallan mamakin rashin kunyan sa.




      Shi ko, ko a jikin sa. Yana shiga ya ganta kwance daga ita sai doguwar riga mara nauyi me taushi da aka yi kwalliyan Flower's a jiki, kalan fari da Green. Ba barci take yi ba tunda ta tashi tun ɗazu har tayi wanka, kawai koma wa tayi ta kwanta sabida ba ta jin daɗin jikin ta, ga tunanin cikin nan ya hana ta sukuni, tana tuna wa sai hawaye. Bata ji shigowar sa ba sai jin mutum tayi yana shirin hayo wa kan gadon. Kan ta farga ya haye abun shi. A firgice ta ciro kanta dake ƙarƙashin matashi saboda ba ƙaramin tsorata tayi ba, bata taɓa tunanin shi zata gani ba shiyasa ta saki baki zata kurma ihu sabida tsaban kiɗima

Take ya rufe mata baki da nashi yana janyo ta jikin shi

Duk iya mutsu-mutsun da take yi wajen ƙwatan kanta amma ina ta kasa, lokaci ɗaya hawaye ya wanke mata fuska tare da fashe wa da kukan da ba'a jin muryan ta sai gunjin kukan, sabida tsaban takaici da ya cika ta ta kasa motsa wa ma

     Shi kuma sai da ya gama tsotsan bakin ta son ransa, sai da ya ga zai iya rasa tunanin sa kafin ya janye bakin nashi yana ajiyan zuciya idanun sa har sun sauya kala

Tuni ta tusa kanta a pilow ta saki wani kuka me cike da ƙunci da baƙin cikin abinda yayi mata

Kallon ta yake yi kawai be iya cewa komi ba, ba don dai ya san a part ɗin su yake ba babu abinda zai hana shi maimaita abinda yayi mata a baya, sai dai sosai ya daure ya zamo ta jikin ta har yana sakin mata nauyin sa ya sauka kan gadon. Sai da ya ɗan gyara gashin sa da rigan sa kafin daƙyar yace, "kiyi haƙuri kinji? Dama ganin baby na nazo Yi na kasa haƙura, tashi zaune mu gaisa".

Ko motsi taƙi yi illa sautin kukan ta dake ƙara yawa

Ganin haka sai ya saka hannu kawai yana ɗaga rigan ta zai saka hannun sa ya shafa cikin ta yana faɗin, "to Ni bari in duba lafiyan Bab..."

Be ƙarisa ba da sauri ta tashi tana janyo hannun shi ta kama ta gantsara mishi cizo da ƙarfin ta

Ihu ya saki da ƙaramin murya yana ware ido, da sauri ya fizge hannun yana yarfe wa

"Mugu azzalumi ka fita a nan ɗakin ko in maka abinda ba ka zato". Tayi maganar cikin ihu da hayagaga wanda ita kanta bata san cewa tana da irin wannan fushin ba

Sai ya saki baki kawai yana kallon ta

"Ka fita nace".

"Ashe kin iya faɗa haka? To babu inda zan je tunda ke matata ce".

Fashe wa da wani sabon kukan tayi da gudu ta tashi ta shige Toilet ta garƙame ƙofan

Duk yanda yaso ta buɗe ƙofan amma taƙi sauraron sa, illa kukan ta da yake jiyo wa kawai, sai ya wuce ya fice

Umma ce kaɗai a parlour'n, don tuni Aunty Amarya ta shige nata ɗakin saboda baza ta iya ganin abin kunyan nan da Usman yake shirin musu ba, tunda duk wani maganar su suna jiyo wa, sai dai basu fahimci me suke cewa ba illa hayaniyar su

Umman na ganin ya fice ta tashi ta shigo ɗakin Ɗahiran, ganin bata a ciki sai kukan ta da take ji a Toilet, sai ta taɓe baki tana bin gadon da kallo. "Oh dama wannan yaron haka kake ba ka da kunya?" Sai ta nufi kuma bakin ƙofan ta soma buga wa tana kiran sunan Ɗahira

But tana jin ta taƙi amsa wa


Dole ta fice ganin ta ƙi buɗe wa, a ranta tana faɗin, "muna-fukai zaku yi bayani ne daga ke har shi ɗin, ƴan iska kuna so kuna kaiwa kasuwa".

      








_Barka da sallah FAN'S. Da fatan an yi sallah Lafiya? Allah ya maimaita mana. Amma dai ban san cewa gaskiya baku so na ba sai yanzu, Ko ɗan cin-cin ɗin nan babu wanda yace "Ummu Ɗahirah ga naki". Babu komo ai_ 😭
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




        *EPISODE Sixty Four*

        Sai da tasha kukan ta son ranta kafin ta wanke idanuwan ta ta fito, a hankali ta taka ta isa kan gadon ta hannayen ta a saman fuskar ta, kwanciya tayi tana sake cusa kanta a jikin gadon, gaba ɗaya ta rasa me ke mata daɗi, Usman yana son zame mata matsala a Rayuwa, shin me yake nema da ita ne yanzu? Ada ba ya ƙaunar ta amma yanzu yana nuna wa duniya yana son zama da ita? Shin ko dai wani abun ne yake son sake aikata mata? Shi ne ta kasa gane wa

"Allah ya fi ka Usman baza ka taɓa cin nasara a kaina ba, duk yanda zan yi sai na bi domin rabuwa da kai". Tayi maganar a fili tana share hawayen da suka soma sintiri a fuskar ta.




        Tana nan kwance sai ga Aunty Amarya ta shigo jin ta shiru da tayi

"Lafiyan ki kuwa Ɗahira?"

Ɗago kai tayi tana kallon ta, sai ta gyaɗa mata kai tana cewa, "eh Mama".

Ɗan ƙura mata ido tayi ganin yanda fuskar ta duk ta sauya idanun ta suka kumbura, kowa ya ganta ya san tayi kuka, amma ta san cewa hakan na da alaƙa da zuwan Usman ɗin, ba dai tace mata komi game dashi ɗin ba, sai cewa tayi, "ta fito ta yi Breakfast". Sannan ta fice

Itama tashi tayi tabi bayan ta, saman dainning ta zauna ta zuba arish da egg ɗin dake wajen a cikin Plate, sai dai gaba ɗaya ta gaza kaiwa baki saboda kawai ƙamshin be mata ba, gajeren tsaki taja tana miƙe wa

A lokacin Aunty Amarya ta fito ɗaki tana kallon ta tace, "ina kuma zaki je baki ci ba kin zuba zaki tafi?"

"Mama bazan iya cin komi a wurin ba".

"Saboda me? Ko tea ɗin baza ki haɗa ki sha ba?"

"Mama bazan iya sha ba wlh, na san ina sha zai saka Ni amai".

Da kallo kawai Aunty Amaryan take bin ta, sai kuma tace, "to me zaki ci sai na dafa miki tunda baza ki zauna da yunwa ba?"

"A'a Mama bari zan yi da kaina".

"To ki kula". Tayi maganar tana juya wa ɗaki

Ita kuma Ɗahiran ta wuce kichen, kai tsaye inda suke ajiye ƙullun koko ta wuce ta ɗiba kaɗan, sai ta ɗaura ruwan zafi. Wake ta samu ta sirfe ta zuba kayan miya ta markaɗa a blender, lokacin har ta dama kokon ta ta sake a jug sannan ta gama haɗa ƙullun ƙosan ta, sai ta ɗaura mai a wuta ta soma soya ƙosan, tun a wutan tana tsame wa take haɗiye shi da zafi-zafin shi. Kafin ma ta gama ta cinye sai ɗan kaɗan da ta bari, ta zuba kokon a Cup ta zauna nan ta cinye sauran da kokon

Umma ce ta shigo ta same ta a kichen ɗin, sai ta dube ta tana murmushi tace, "a'a yau kuma kwaɗayin koko da ƙosai ake ne babu tayi?"

Murmushi Ɗahiran itama tayi tace, "eyya ai ban san zaki ci bane shiyasa na cinye, amma akwai raguwan kokon".

"A'a wasa nake miki, ci abin ki ai ke ce me lalura".

Duƙar da kanta Ɗahiran tayi bata ce mata komi ba, ta ƙarishe shanye kokon tana miƙe wa ta fice ta bar ta a kichen ɗin.




          Ɗaki ta koma ta sanya Hijab ƙarami a jikin ta ta fito ta wuce ɗakin Maman ta, ce mata tayi "zata je wajen Kaka".

"To ke da baki da lafiya kuma meye na yawo?" Inji Aunty Amarya

"Don Allah Mama bazan daɗe ba wlh, zamu yi magana da shi ne".

"Ok sai kin dawo".

Fita tayi ta wuce wajen Kaka. Tana shiga da sallama

Ya amsa mata cike da fara'a

Sai da taje har gaban sa ta ja mishi Gemu kafin ta zauna a gefen gadon shi tana faɗin, "My Kakus Ina kwana. Ya kuma tsufan?"

Dariya yayi yace, "ai na bar miki Mata ta, ke ce kike fama dashi, Ni kuwa kin ganni sumul ba kamar ke ba da kullum kina rashin lafiya. Ya jikin naki to? Iyayen ki ɗazu suke faɗa min abun farin ciki".

Kwaɓe fuska tayi tace, "Ni Kaka ba wannan ba, Ni don Allah yaushe za'a raba aure na da Yaya Usman? Ka ga har yanzu ina ta zaune da auren shi yaƙi saki na".

"Abinda kike so yanzu kenan?" Yayi maganar yana kallon ta

"Eh Kaka".

"Shikenan kar ki damu zuwa anjima zan tara ku mu yi maganar".

"Yauwa Kaka na, na gode". Tayi maganar tana sakar masa kiss a hannun sa

Murmushi kawai yayi mata yana shafa kanta be ce komi ba

Sai ta ɗago ta kalle shi tace, "Kakus baka da wani abun motsa baki ne a ɗakin?".

Dariya yayi yace, "ina dashi mana, Jiyan nan Dadyn ku ya kawo min kayan marmari suna nan a Fridge ki ɗauka".

"To bari in duba in gani ko akwai abinda zan iya sha". Tayi maganar tana tashi tsaye tayi wajen Fridge ɗin, lemo ɗaya kawai ta ɗauko ta dawo ta zauna

"Shikenan abinda zaki sha?".

"Eh. Ya ishe Ni wannan kar in shanye maka".

"Haba dai, tunda Ɗana yake so yasha ai babu damuwa, sai in saka ma yanzu a ƙaro miki idan kika shanye".

Shiru tayi kawai bata ce komi ba taci gaba da ɓare lemon da hannu

Shi kuma Kaka sai yayi ta mata surutu duk a kan cikin nata, da idan ta haihu in dai na miji ne sunan sa za'a saka

"Kawai ina jin ka ne Kaka, amma ba daɗin zancen nake ji ba, kayi shiru don Allah".

"Yo ko laifin Baban shi zai shafe shi ne?"

Ɓata fuska tayi tana tashi tsaye tace, "Ni dai na tafi. Sai anjima". Bata jira cewar sa ba ta fice abun ta

Shi kuma sai kwaɗa mata kira yake yi yana faɗin "ta dawo".

Dawowa tayi ta leƙo daga bakin ƙofan tace, "Kakus bazan sake zuwa ba yanzu sai kana ajiye min abun daɗi, tunda Babyn naka abun da yake so kenan".

Dariya yake yi yace, "to shikenan, ai kuwa zan riƙa ajiye miki kar ki damu".

"To byee na tafi zan dawo anjima ai". Tayi maganar tana dariya ta fice

      Shima still dariyan yake yi zuciyar sa cike da farin ciki. "Usman da baka yi wannan abun tsiyan ba ai da farin ciki na sai yafi haka, amma kuma ka rigada ka ruguza komi, duk da haka dai ina da rabon ganin ɗan ku tare, ko ba komi dole wata rana ku dena nuna wa junan ku ƙiyayya tunda kuna da ɗa a tsakani".





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫


          Tunda yaje Office ya kasa sukuni, duk abinda yake yi tunanin sa na gare ta, babu abinda ke dawo masa a rai sai abinda ya faru tsakanin su ɗazu, shiyasa abu kaɗan sai murmushi kamar wani zautacce, sosai yake kewar ta tabbas yana buƙatar matar sa a halin yanzu, meyasa baza ta yafe mishi komi ya wuce ba tunda ya bata haƙuri? Tun sanda abun nan ya faru a ƙauyen Baba Jaure yake dana-sanin furucin da yake mata na ɓatanci, da kuma kallon ta da yake yi a matsayin mazinaciya, haƙiƙa yayi dana-sani mara misaltuwa, wanda har ya ɗau alƙawarin duk wanda ya kawo mishi pictures ɗin nan da ya sake dagula mishi lissafi a kanta dole ne sai ya fuskanci wulaƙanci me muni, bazai taɓa barin ko waye bane sai ya ɗau mata fansa, idan da ba shi ne aka ba wa hotunan ba shikenan za'a riƙa tunanin tabbas ita ce.



        Shiyasa sai da yabi diddigin inda aka yi hoton, a can ne ya samu bayani a kan mutumin da ya zo aka yi mishi hoton, dayake sananne ne tunda ya saba zuwa wajen ana mishi, da ya kamo shi yaci uban sa kwanan sa biyu a rufe yana gana mishi azaba, inda kuma yayi mishi barazana a kan sai ya danƙa shi wajen hukuma muddin be nemo mishi waɗanda suka saka shi aikin ba. Wannan dalilin ne da yasa aka kamo su Ayush. Shi mutumin yayi musu wayau ne ya jawo su hotel ɗin a kan "baya ta haihu.." da suka zo kuma sai ya bugar da su daga ƙarshe ya ɗaure su....




                 Ajiyan numfashi Usman ɗin ya sauke yana ɗaukan wayan shi ya soma laluben numbobi, yana son jin muryan ta ko zai samu sukuni amma be san wa zai kira ba, be da Numban ta bare na Maman ta da zai iya kira, nan dai ya tuna dana Fadil sai ya danna mishi kira

Koda ya ɗauka sai yace mishi, "ya je ya kai wa Nafeesa wayan".

Jiki na rawa Fadil ya soma inda-inda don be gane da wacce yake nufi ba

To abun ne ai yazo musu da sabon salo tunda dai kowa da Ɗahira yake kiran ta, babu wani me kiran ta da sunan ta, shiyasa wani lokacin ma suke manta sunan ta, amma shi da iyayi irin nasa dole sai ya bambanta kanshi da kowa

"Ka kai mata wayan ka tsaya kana min shirme". Yayi maganar cike da ɗan tsawa

"Yaya ai ban gane wacce kake nufi ba".

Tsaki yaja yace, "stupid.. Ɗahira".

"Ai Ina school ban dawo ba.."

Be jira sake jin wani zancen nashi ba ya katse wayan yana ajiye wa cike da takaici, ba don ya so ba yaci gaba da aikin da yake yi, sai kuma ya tashi ya fice ya tafi duba patiens ɗin da yake da su.





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫


        Da dare Kaka ya sanya a tara mishi jama'an gidan, bayan kowa ya hallara sai yayi musu magana a kan "sakin da Usman zai yiwa Ɗahira ne, yanzu ya kamata ace ya bata takardan ta kowa ya huta".

Big Dady yace, "nima nayi mishi maganar jiya, amma dayake shi fitsararre ne yake faɗa min maganar ma da bazai yiwu ba, wai "bazai sake ta ba a bar shi da matar shi".

Kaka kallon Usman ɗin yayi da kanshi ke ƙasa. yace, "ai sakin ta ya zama dole kuwa Fodio tunda mu baza mu sake mata tilas ba, tunda ita take buƙatar a raba auren nan babu me matsa mata ta zauna da kai a wannan karon, tun farko abun da muka hango muku kenan sha'awar zaman ku tare har muka haɗa ku, amma kuma sai kayi watsi da umarnin da muka baka kaƙi mana biyayya, hakan yasa ka je ka gallaza mata son ranka, sai ga shi Allah ba azzalumin bawan sa bane kaima yanzu kana son zama da ita, to, ai ita ba jaka bace da zamu sake baka kaje ka sake maimaita mana abinda kayi a baya, maganin kar ayi kar a fara Allah ya haɗa kowa da rabon shi kaji ko? Yanzu ga ta nan ba sai ma ka sha wahalan rubuta wa ba sai ka sake ta kowa yaji, yaron ka kuma idan Allah ya sa ta haifa maka zata raina har zuwa yayen shi kafin ta baka kayan ka".

"Kaka kuyi haƙuri da abinda nayi muku a baya wlh nayi nadama bazan sake ba, bazan iya sakin ta ba saboda ina son zama da ita, ko don abin dake cikin ta be kamata a raba mu ba.."

"Abun cikin ta ɗin uwaka? Usman kar ka ja mu kai maganar nan kotu wlh, idan har Daughter Bata yarda zata koma ba rashin sakin ta bazai hana mu baka ita ba, sai dai mu je kotu a raba". Cewar Big Dady kenan cike da haushin Usman ɗin

Tashi Usman ɗin yayi yana faɗin, "Allah na rantse bazan sake ta ba, duk abinda za'a yi sai dai ayi baza a mayar min da ɗana Maraya ba". Daga haka ya fice da sauri daga parlour'n ranshi a ɓace

Su kansu maganar Usman ɗin ta ba su dariya, wai Maraya

Abba ne yace, "abi komi a

Please Login or Register in order to submit comment