Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce matar aure a gidan, babu me nemo magana sai ita.

         Ataƙaice dai aka sasanta komi, inda Kaka yayi mata faɗa sosai ya kuma ce "kar ta sake zargin Ɗahira da ita ce silan kashe Baffa, idan kuma zata yi hakan sai dai ta zargi kanta tunda ita ce taja komi".

           Bayan an ƙarƙare maganar sai Big Dady yace ma Usman "ya miƙo mishi takardan sakin Ɗahira".

Duƙar da kanshi yayi yace, "Dady kuyi haƙuri a kan abinda nayi muku baya wlh nayi nadama, insha Allahu yanzu zan yi muku biyayya gwargwadon iyawa ta, na yarda zan zauna da ita kamar yanda kuka zaɓa min ita".

Ɗahira da kanta ke cinyoyin ta tana ƙananun kukan ta saboda har yanzu raɗaɗin zafin shaƙan da Hajja Fatu tayi mata be barta ba, bata san sanda ta ɗago a firgice tana kallon Usman ɗin cike da haushin jin kalaman sa ba

Bata kai ga magana ba Big Dady ya riga ta da cewa, "wannan zancen banza zancen hofi kake mana a nan, tunda har ada ka nuna mana bamu isa da kai ba kaƙi zaɓin mu, to yanzu baka isa kace zaka wulaƙanta mu ba, saki ne babu fashi dole ne sai ka sake ta dan uban ka". Ya ƙare maganar nasa a zafafe kamar zai kai mishi duka

Kaka da ya kafe Usman ɗin da ido sai yace, "abinda za'a yi yanzu a bar maganar nan ba yanzu ne ya kamata mu yi shi ba, muna ji da raɗaɗin mutuwa a yanzu mu bari zuwa nan gaba, yanzu kowa zai iya tafiya".

Duk tashi suka yi suna fice wa, inda Ɗahira da duk ta cika tayi fam da jin rainin hankalin Usman, sai bin shi da kallo take yi tana son su haɗa ido, sai dai shi tuni ya yi ƙofa yayi ficewar sa. Da sauri tabi bayan sa tana zuwa ta bangaje shi ta wuce

Sai ya tsaya kawai yana kallon ta cike da mamakin abinda tayi masa

Ita kuma sai da tayi taku kamar uku kafin ta jiyo tana kallon sa ta balla mishi harara cike da haushin sa da tsanar sa tayi gaba abinta ba tare da ta tanka shi ba

Sai abin ma ya bashi dariya ya kasa tafiya har sai da ta ƙule, sannan ya taka ya wuce Part ɗin iyayen sa yana jin zuciyar sa na sake cika da nishaɗi, fuskar shi kuma yalwace da kyakykyawar murmushin da sai ya jima kafin yayi shi, be san meyasa ba duk wani yanayi da yake ji a kanta yanzu yake burin jin sa a ko yaushe, musamman bugun zuciyar sa da sauyin yanayin da yake ji a jikin sa, yana son ya kalli idanun ta yaji tsoron nan dake riskan shi wanda ada yaƙi jini, har dariya yake yanzu yana mamakin wai me ke kawo hakan. Shi fa be taɓa jin yanayin da yake ji a kan yarinyan nan wajen wani ba, shiyasa ada yayi wa abun mummunan fassara, wanda yana ganin idan ba ita mayya bace taya zata riƙa bashi tsoro da faɗar masa da gaba? Har kuma ya riƙa mafarkin ta haka kawai. sai duk ya tsangwami kansa a kan lallai-lallai sai ya raba kanshi da wannan yanayin, wanda kuma yanzu kusantan da suka yi da juna na ɗan zaman nan da suka yi a ƙauyen nan, yasa ya soma saba wa da yanayin har yana jin ya riƙa kansacewa a haka idan har zai ganta kusa dashi.





      _Mu je zuwa._ 🤣







             ⚫⚫⚫


      Ɗahira na zuwa Part ɗin su ɗakin ta ta shige ta zauna a kan gadon ta

Sai ga Aunty Amarya itama ta shigo da sallaman ta

Amsa mata tayi tana kallon ta kamar yanda itama take bin ta da kallon, kana kuma tazo ta zauna kusa da ita

Tace, "meyasa baki sanar min soyayyar dake tsakanin ki da Baffa ba?"

"Mama Ni kaina ban san shi ne wanda muke soyayya dashi ba, sai daga baya na san hakan bayan mun rabu. Kuma naga hakan be da amfani tunda Hajja ta rigada ta raba mu, idan kuka sani baza ku ji daɗi ba".

Ajiyan zuciya Aunty Amarya ta saki kana tace, "haka ne. Amma ba na son ki saka damuwa a ranki ko kaɗan tunda kin san halin kanki, duk wani abu yanzu ki bar shi ya wuce, kuma ki mayar da hankalin ki wajen ibadan Allah kina neman kariya wajen sa, domin Ni yanzu abubuwan tsoro suke sake bani, baki tare wa kowa komi ba ke kuma ba fin su kika yi ba amma maƙiyan ki sun yi yawa Ɗahira".

Murmushi Ɗahiran tayi tace, "insha Allahu Mama zan kasance me neman kariya wajen Allah na, na san shi zai kare Ni".

"Batun kuma Usman kar shima ki saka shi a ranki, babu me miki tilas a wannan lokacin domin su kansu su Kakan ba mara su hankali bane da za su sake saka ki ki koma gidan sa, babu wanda zai tilasta ki sai da yardan ki kinji?"

"Mama idan har da yarda na ne kuwa bazan taɓa koma wa gidan shi ba, ki dena ma zancen nan domin Ni na cire sa a raina tuni wlh, dole ne sai ya sake Ni don bazan taɓa zama dashi ba". Tayi maganar kamar zata yi kuka

Murmushi Aunty Amarya tayi tana shafa kanta, kana kuma ta tashi tsaye tana cewa, "ki tashi ki je ki sake cin abinci don ɗazu ina ganin ki baki ci da yawa ba".

Itama Ɗahiran tashi tayi tana cewa, "to. zan yi wanka ne yanzu zan fito, don Allah Mama ki turo min Fadil yazo min da wayan shi".

Amsa mata tayi Aunty Amaryan tana fice wa

Inda ita kuma Ɗahira ta ɗauko tawul ɗin wankan ta tana shige wa Toilet.







⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫


         An sallami Sa'adatu daga asibiti, sai dai ko da iyayen ta suka so su tafi da ita Legos, Kaka yace, "A'a a nan zata zauna har sai ta haifu sannan zata koma". Dole ba don sun so ba suka haƙura, inda ta dawo Part ɗin Hajja ana kula da ita

While Yusra itama tana gidan sai tayi arba'in zata koma, abun mamaki kuma tunda Ɗahira ta dawo sai kuma duk idan suka haɗu sai tayi mata magana

Da fari hakan ya saka Ɗahira tunani da tsantsan mamaki, amma kuma duk idan taje duba little Baffa sai tayi ta janta da hira, ba ita kaɗai ba har Hajiya, sai duk abin yayi mata banbaraƙwai wai na miji da suna Inna ta Hajara. Duk da a zuci hakan yayi mata daɗi amma kuma da ta tuna ko suna yi ne don ta koma gidan Usman sai ta soma jin haushin su, daga baya sai ta ɗauke ƙafa da zuwa, amma kuma haka Yusra take biyo ta har ɗakin ta wai "ta ji ta shiru bata zo taga Little ba". Tun ba ta kula ta har dai ta saki jikin ta tunda a ganin ta hakan ma sauƙi ne ga rayuwar ta, ace yau maƙiyin ka ya koma masoyin ka

Fannin Usman kuma basu sake haɗuwa da shi ba, kuma ko kaɗan ba ta ƙaunar haɗuwar nasu ma.





             ***********



            Rayuwa taci gaba da tafiya inda har an yi sadakan arba'in ɗin Baffa

Inda ita kuma Yusra ta gama jegon ta ta koma gida itama.

             Sai a lokacin ne Ɗahira ta samu damar koma wa bakin aikin ta, inda taci gaba da aikin ta cikin salama da kwanciyar hankali, sai dai har yanzu kewan Baffa na maƙale a ranta, ta kan tuna sa wani lokacin tayi ta zubar da hawaye tana mishi addu'a, kuma har lokacin bata sake jin ɗuriyan Usman ba, ga shi ba'a sake yin zancen sakin ta ba, itama shiyasa bata sake kula maganar ba, tunda dole ne dai sai ya sake ta, ko kotu ne sai an je babu wanda ya isa ya saka ta ta koma gidan Usman.



             Gefe ɗaya kuma Usman shima ya koma aikin sa, sai dai be taɓa neman Ɗahira domin ya ganta ba, tunda sosai zuciyar sa ke addabar shi da son ganin ta, ba kaɗan ba tunanin ta ya gallabi ruhin sa, tun yana ganin abin da sauƙi, har kuma dai ya kasa jure wa yau ya yanke shawaran zuwa Office ɗin ta ya same ta, ko da ganin waɗannan idanuwan nata ne masu firgitar dashi domin yaji sanyi a ranshi, a lokacin da yake tunanin yana zaune ne a Office ɗin sa yana ta faman murmusawa. Sai kuma ya tashi ya fito ya nufi Office ɗin ta


Nocking yayi


Sai ta ba shi iznin shiga


Ya buɗe ya shiga yana bin ta da kallo


Ɗahira da kanta ke kan files tana duba wa, ƙamshin turaren sa kawai ya ziyarci hancin ta sai taji wani muguwar faɗuwar gaba ta ziyarce ta, da sauri ta ɗago don tabbatar da shi ɗin ne wanda take hasashe


Ilai kuwa shi ne yana tsaye a bakin ƙofan, shi be shigo ba kuma be fita ba idanun shi a kanta


Sai ta ɗauke idanun ta tana jin zuciyarta na ci gaba da bugawan sauri kamar zata faso ƙirjin ta, take a nan yanayin jikin ta ya sauya lokaci ɗaya taji yayi mugun sanyi har tana jin yanda hannayen ta suka soma rawa


"I want to talk to you". Yayi maganar har yanzu yana tsaye a bakin ƙofan be ɗauke ido a kanta ba


Bata motsa ba bare ta sake kallon sa, illa ɗaure fuskar ta da tayi tana me jin baƙin cikin sa da tsanar sa me girma a zuciya


Takowa kawai yayi ya zauna ganin bata kula shi ba, sai da kamar soconni uku suka shuɗe kafin ya buɗi baki yace, "wani alfarma nazo nema wajen ki, na san zaki yi mamaki sosai but ki ɗauka tamkar zan yi hakan ne domin faranta ran iyayen mu, ki amince muci gaba da zama a matsayin mata da miji domin yiwa iyayen mu biyayya kamar yanda suka so tun Farko.."

Be ƙare maganar ba ta ɗago tana kallon sa da idanuwan ta da suka cika fal da hawaye, cikin rawan murya da za'a gane ƙiris take jira ta saki kuka, ba wai don komi ba sai don ƙuncin da kalaman sa suka saka ta, tace dashi, "kai har kana da bakin da zaka zo waje na kace in koma ɗakin ka domin muyi wa iyayen mu biyayya? Kar ka manta tsanar da nake maka ya zarce tunanin ka, kai ka koya min tun ban san kaina ba. har gobe bazan taɓa manta azaba da wahalan da ka bani ba, idanun ka sun rufe saboda tsantsan tsanar da kake min, ka manta cewa Ni ƙanwar ka ce kuma jinin ka, ka gallaza min uƙuban da na gummaci mutuwa ta da rayuwa ta, taya ya kake tunanin zan iya yafe wa har in koma in Yi rayuwar aure da kai? Never wlh. Har abada bazan taɓa manta abinda kayi min ba, yana nan daram a cikin zuciya ta wanda kullum ƙara jin tsanar ka nake yi a cikin ta, I hate you Usman I will never go back to your house .. "

Tsawa ya daka mata saboda jin maganganun ta da suke ƙona masa zuciya da ya kasa jure wa. Sai kawai yaga ta fashe mishi da dariya ga kuma hawaye suna ɗiga a fuskar ta, sai ya saki baki yana kallon ta cike da mamakin ta

Ido cikin ido take kallon sa bayan ta tsayar da dariyan nata lokaci ɗaya tace, "Hi Guy gate out of my office baza ka zo kayi min iko a nan ba".

"Ni kike kora?"

"Eh kai. WHO ARE YOU?"

A fusace ya tashi yana nuna ta da yatsa yace, "zan nuna miki kuwa Ni wane ne, kuma zan tabbatar miki da cewa baki isa kici galaba a kaina ba". Sai ya saki guntun murmushi yace, "gida na ne dai baza ki koma ba har kike furta min munanan kalaman nan ko? To zan ga yanda zaki yi kiyi auren da igiyar aure na, muddin ba gida na kika koma ba baza ki taɓa aure ba wlh, sai dai ki mutu da aure na a kan ki babu wanda ya isa ya saka Ni na sake ki, ba wai don ina son ki ba sai dan in sauke miki wannan iskancin da yake kanki, dole ki koma gida na kuma dole ki amsa sunan mata ta".

Fashe wa tayi da kuka cikin ƙunan zuciya tace, "wlh ƙarya kake yi mugu azzalumi, Ni ba matar ka bace, dole ne sai ka sake Ni".

Dariya ya saki lokaci ɗaya saboda ganin yaci galaba da saka ta baƙin ciki kamar yadda ta saka shi

Lokaci ɗaya ta tsayar da kukan nata ganin dariya a fuskar sa wanda tunda take bata taɓa ganin shi yayi ko da murmushi ne ba. Sai gani kawai tayi ya zagayo ta gefen ta har yana ranƙwafo wa saitin kunnen ta

Yace, "Mata ta ce ke wlh, kuma dole sai kin amsa sunan nan, babu wanda ya isa ya raba aure na dake ko waye.."

Da sauri ta tashi saboda jin tsigan jikin ta ya tashi gaba ɗaya ta rasa sukunin ta, hakan yasa suka yi karo da juna kansu ya bugu, sai duk suka riƙe goshin suna kallon idanun junan su, nata idanun sun yi luhu-luhu suna zubar da hawaye kamar wanda aka kunna famfo.


Hannu ya saka ya...

















_kai na gaji mu haɗu next page sai ku ji ya za'a kaya. Amma ku bi Ni bashi zuwa jibi._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




        *EPISODE Sixty One*

       Hannu ya saka ya janyo ta jikin sa yana kallon ta

Wanda ita lokaci ɗaya ta rufe idanun ta jikin ta ya soma rawa ta soma ƙoƙarin ƙwace kanta

Murmushin mugunta ya saki yana sake manna ta a jikin sa, a hankali ya furta. "Na san baki manta abinda ya faru ba a ƙauyen Baba Jaure. So Kar ki tunzura Ni in sake maimaita wa wlh, ki kama kanki ba na son rashin kunya, ba wai na sauya bane daga hali na bane, sai dai na sassauto ne wanda Ni kaina ban san meyasa tsanar da nake miki na dena ji ba". Sai yayi shiru yana saka hannun sa ya shafi fuskar ta yace, "kina burge Ni yanzu shiyasa. Ki kula". Ya sake ta ya fice abin sa.

       Wani irin kuka me ƙara ta saki tana zame wa a ƙasan wajen jikin ta na ci gaba da rawa. "Allah ya isa tsakani na da kai Usman, ka gama dani wlh ka cuce Ni! bazan taɓa yafe maka ba mugu azzalumi kawai!".

Kuka sosai take yi ta kasa tashi a wurin, ji take yi da zata iya da sai ta faffalla mishi mari ko zata samu sukunin ƙuncin da yake ƙunsa mata.



        Bata tashi a durƙushe a wurin ba sai da taji ana mata Nocking, a tunanin ta ko Usman ɗin ne ya sake dawowa shiyasa ta ɗauke kukan nata cak tana jiran shigowar sa tayi masa rashin mutunci, tana ga hakan kaɗai zai saka ya fita harkan ta, domin ta tsane shi ko kaɗan ba ta son ma wata magana ta sake shiga tsakanin su. But sai taji shiru ba'a shigo ba illa Nocking ɗin da aka ci gaba da yi, dole ta tashi tana share fuskar ta tare da daidaita nutsuwar ta, ta ba da iznin shigo wa tana zama a kan kujera



Ayush da Safra ne suka shigo Office ɗin idanun su a kan Ɗahira da itama ta ɗago rinannun idanuwan ta tana bin su da kallo

Kallo ɗaya da tayi musu ta gane Ayush, sai ta saki fuskan ta kaɗan tayi musu Bismillah

Zama suka yi suna murmushi duk kan su

Ayush tace, "na san baki gane Ni ba ko? Ni ce Dr. Ayush Abdulkarim friend ɗin Dr. Baffa".

Yaƙe Ɗahira tayi tace, "Na gane ki mana. Ai na san ki a Hospital ɗin nan".

"Haka ne. Wannan ƙawata ce sunan ta Safra, mun zo miki ta'aziyya ne, sai kuma taya ku murna a kan dawowar ku".

"Allah Sarki Nagode sosai".

"Allah ya jiƙansa Allah ya gafarta masa". Suka haɗa baki ita da Safran suka faɗa

Ɗahira ta amsa da "Amin Amin". Tana jin idanun ta suna ciko wa da hawaye.

"To zamu tafi, sai kuma mun sake kewayo wa".


Daga nan sallama suka sake yi sannan suka fice.




        Suna fita Ayush ta kalli Office ɗin Dr. Usman, ji take yi kamar ta ganshi ya fito

Safra ta dafa mata kafaɗa tace, "zo mu wuce don Allah, ai komi ya kusa zuwa ƙarshe tunda ga shi Allah ya bayyana su basu mutu ba, so yanzu burin mu zai cika, kar ki soma ko da da wasa ki je Office ɗin sa sai sanda muka cika aikin mu. Yanzu abun da ya kamata mu shiga jikin ita matar tashi, ta hakan ne zamu samu muna shiga gidan su har mu samu gashin kanshi, wannan hanyar shi ne me sauƙi da zamu bi, dole sai mun zama ƙawayen ta".

Murmushi Ayush tayi tace, "gaskiya ne ƙawalli, ziyaran gaba kuma gida za mu kai mata".

"Ashe kin gane. Mu je mu ƙarisa maganar a mota akwai wani Alhaji da na samo miki, na san zaki fi jin daɗin harka dashi yana da kuɗi sosai. Kin san ya kamata mu soma shirye-shiryen biki ma tun yanzu".

Dariya suka yi har da kashe wa suka yi gaba cike da nishaɗi, barin ma Ayush da bakin ta yaƙi rufuwa, tun ranan da bayyanar su Usman ɗin yazo kunnen ta, kullum ba ta iya barci tsaban murna.






⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫


          Fannin Abba kamar yanda yayi ƙudirin sake aure ashe be fasa ba abun na ranshi, har ya sanar wa su Big Dady da Kaka, inda Kaka yaso ƙin amince wa tare da tausan sa "ya haƙura yaci gaba da zama da ita a haka". Amma shi yace, "dama shi yana da burin sake auren, kuma ya rigada ya yi niyya". Dole Kakan ya ƙyale shi tare da saka mishi albarka a kan maganar

To abu kamar wasa sai ga shi Abba ya samo wata bazawara dake cikin anguwan nasu, yaran ta biyu duk ka yara ne, na farkon ma sa'an Fadil ne, mijin ta ya rasu ne wajen shekara biyu, Abokin shi yayi mishi hanyar ta, don haka tuni Abba ya amince da batun nata

Har aka saka rana Hajja Fatu bata sani ba, domin yaƙi sanar mata, sati Uku aka saka, sai da ya rage saura sati ɗaya sannan ne ya sanar mata, shima don taga yana kwashe kayan ɗakin shi yana mayar wa ɗakin Baffa ne, don a ɗakin nasa zai ajiye ta

Nan fa Hajja ta tashi hankalin ta a kan "sai ya faɗa mata dalilin sa na cire kayan shi ya mayar can".

Shi ne yake faɗa mata, "aure zai yi".

Bazan iya fasalta muku haukan da Hajja Fatu tayi ba, tayi borin tayi kukan domin ya fasa auren

Amma sam yace, "bata isa ba tunda yayi ninya".

Wannan dalilin ne ya kawo saɓani a tsakanin su me girma har Hajja tayi yaji ta koma gida. Ko kwana bata yi ba Hajiya Hannatu (Ihsan) ta dawo da ita, tace, "sam wannan shirmen ba dai a gidan ta ba, kuma wlh muddin ta tafi wani wuri yaji; zata haɗu da fushin ta". Dole ba don taso ba Hajja ta zauna a gidan, amma fa fitina yaƙi ƙare wa a dole sai Abba ya janye auren nan

Sai dai kuma babu abinda ya fasu sai ci gaba da bikin ake yi, domin har Kaka ya zaunar da ita ya kwantar mata da hankali amma ta ƙi ji, dole suka zira mata ido tayi ta gaji ta bari.




      Ana saura kwana huɗu bikin ne Sa'adatu ta haifi ɗiyar ta mace ƙatuwa, abun mamaki duk girman cikin nan kuwa, domin har ya zarta wata tara kowa yayi tunanin ƴan biyu ne, sai dai Allah ya nuna ikon sa ashe mace ce. Dole aka ɗaga bikin zuwa ranan suna sai a haɗa ayi tare.

     




                *SUNDAY*
      Ranan biki da ya kasance ranan suna, an raɗa wa yarinya sunan Hajja Fatu, Fatima za su na kiran ta da Zahra

Gida ya cika maƙil tubarakalla, mutane sai dai suka tare a sauran Part ɗin, amma Hajja ta hana kowa shigo mata sashi, Shakira ma bata zo ba saboda tana taya uwar ta kishi

Su kuwa duk yaran gidan suna sashin su Ɗahira, dayake yafi girma nan, a nan suka shantake suna ta hira. har da su Fadila da su Salma ita ma da babyn ta ita da Shamsiyya duk sun zo

Ɗahira na cikin su ana ta washe baki, duk kansu sun yi ankon kamfala doguwar riga me ruwan zuma da ratsin fatsi-fatsi na milk

Yanzu haka ma abinci suke ci shi ne suke ta shewa

Uwar surutu Firdausi ta kalli Ɗahira tace, "wai ke yaushe ne mu kuma zamu dawo musha sunan ɗan mu? Kin wani ƙaƙabe tunda kika shige gidan Yaya Usman kin ƙi sulluɓo mana ɗa".

Dayake su ba su da labarin zaman da suka yi, iyakan iyayen su suka ji labari

Ɗahira hararan ta tayi tace, "sai ranan da kika yi naki auren kika fara sulluɓo ɗanki kafin Ni in diro nawa".

Dariya suka yi

Inda Salma ta amshe zancen da faɗin, "ai wannan rasa kunyan ba yanzu ba, zaki sha wahala kuwa idan kika ce zaki jira ta".

Gyara zaman ta Firdausin tayi tace, "faɗa mata dai, sai kun yi yara bibbiyu ko uku-uku kafin Ni nawa ke tafe".

Su Aunty Zulaiha dake zaune saman gadon Fadila na da, sun yi ɗai-ɗai suna ci a saman, a tare suka haɗa baki ita da Aunty Zainab wajen faɗin, "keee Firdausi kiji tsoron Allah, da gaske kike yi?"

Sai duk ɗakin suka kwashe da dariya

Yusra da ta bigi bayan Firdausin tana cewa, "ai kuwa da kin shiga uku kuwa, kiyi ta zama a gida babu Aure, ko da kuwa da gaske kike yi zan sami Gwaggon namu in kitsa mata ayi-ayi kema kin ƙosa tunda shigowa cikin manya kike yi kina kwasan gulma".

"Oh su Yusra manya, wlh kin daɗe baki ce mata ba, ga ƙuda can zai riga ki". Cewar Firdausin tana fuske wa

Ɗahira tace, "wai ba batun wasa ba da gaske kike yi don Allah?"

"Da gaske ne mana". Tafaɗa tana kai loman tuwon ta

Sai duk suka tsaya suna kallon ta

Shamsiyya da ta miƙe da kwanon tuwon ta, dayake ita kaɗai take ci tace, "kin ga banu kuwa, ki zauna har sai kin tsofe". Ta ƙare maganar da fice wa

Salma tace, "ku kun dauka da gaske ne? Ku dena biye ma wannan wlh an kusa saka mata rana, domin Ni da Daddy muka yi zancen nan kwanaki da naje gida".

Sai Firdausin ta ɗaka mata duka a cinya tace, "wato dama ke kika ziga shi ko? Ashe shiyasa yazo min da zancen in turo Wanda nake so, ga babban muna-fuka a gefe ina tare da ita".

"Kambu... Ni kika duka Firdausi? Dan Allah Ɗahira riƙe min yaron nan wlh sai na rama, zan ga dani dake waye muna-fuka kina so kina kaiwa kasuwa".

"To kaji kun fara ko? Dama babu daman ku haɗu waje ɗaya". Inji Aunty Zulaiha

Ita kuma Firdausi tunda taga ta yunƙuro ta tsame hannun ta cikin tuwon ta ruga aguje tabar ɗakin

Salma na mara mata baya tana cewa, "wlh ko cikin Momy kika koma sai na ƙwaƙulo ki na rama, gwara ma ki tsaya".

Me za su yi ƴan ɗakin ba dariya ba, sosai suke dariya. Inda Aunty Zulaiha take ta kwaɗa wa Salma Kira a kan "kar ta bi ta ta dawo". Amma ina tuni ta fice


Ɗahira dake ta faman dariya tashi tayi tana girgiza yaron Salman tace, "ai gwara ta bi ta ta zane mata jiki tunda Firdausi ta raina ta, kamar ba yayar ta ba".

Aunty Zulaiha tace, "to ai ga shi nan ta bar miki wannan yaron me shegen kukan jaraba, kema ki bi ta wlh duk ya kure mana kunne".

"Haba Aunty. Kema fa kin kusa haihuwar ba'a san ke kuma wanda

Please Login or Register in order to submit comment