Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai dai kuma yanda yake jin wani iri kamar an manne masa idon cikin nata ya kasa ɗauke su a kanta


Illa ita ce da tayi ƙoƙarin fizgar kanta sa'ilin da ta gama tantance a jikin wanda take, wani irin fisga tayi wa kanta saboda haushin ganin ta a jikin sa da saura ƙiris ta gurɗe ta zube ƙasa


Sai ya ƙara azamar riƙo ta da sauri yace, "ke kina da hankali kuwa?"


Wani kallo ta sakar masa cike da baƙin ciki ta kasa ce mishi uffan, ta sake yinƙurin janye jikin nata da ƙarfi duk dan ta raba kanta dashi


Yana shirin sakin ta ganin abinda take so kenan, sai sandan ta ɗaya ya faɗi, dole ta ɗage ƙafa ɗaya don baza ta iya ba da ƙarfin ta a ƙafafuwan gaba ɗaya ba, tuni hawaye sun cika mata ido saboda azaban da take ji tayi saurin ƙanƙame mishi hannu, shi kuma sai ya duƙa ya ɗauko mata sandan


Yaran wajen tuni hankalin su ya dawo gare su sun tsaya suna ta kallon su kamar wasu t.v

Su kuwa basu san ma suna yi ba, domin tuni Ɗahira ta bizge sandan nata ta daidaita su ta soma ɗingisa wa a hankali


Yanda take yi ne kamar zata sake faɗi sai yayi saurin kawo hannu zai sake tare ta yana cewa, "Please kiyi a hankali manaaaa". Ya ƙare maganar cikin jan kalman ƙarshen in a cool voice

"Kar ka sake taɓa Ni?" Tayi maganar hawayen idanun ta na sauko mata a kunci. Sai ta sake janye jikin ta sosai kafin tace, "ko kaɗan ba na buƙatar taimakon ka. Ko ka manta a baya ma baka taimaka min ba sai yanzu? So please zan iya da kaina ba tare da taimakon ka ba, kar ka sake yinƙurin taimaka min na roƙe ka".


Kalaman ta sun ba shi haushi sai yace, "kina tunanin zaki iya wani abun ne ba tare da taimako na ba? Idan da ban taimaka miki ba babu yanda za'a yi ki kawo yanzu a raye. Waɗannan mutanen da suka ɗauke ki da tuni yanzu sun aikata nufin su a kanki da ban amso ki a wajen su ba, so ki iya bakin ki Please ba na son cika baki, kar kuma ki ga ina kula ki ki ce komi ne zaki riƙa faɗa min". Yaja dogon tsaki yayi gaba abin shi fuuuu kamar ana tunƙuɗa shi


Ita kuwa da kallon banza ta bi shi hawaye na sake kwaranya a fuskar ta kamar an kunna famfo, tana jin zuciyar ta na mata ƙuna da maganganun sa. Shiyasa ko jirgau ta kasa yi duk da kuwa yanda yaran nan suka mamaye ta suna bin ta da kallo sai surutu suke yi, amma ba ta jin su illa bin hanyar da yabi da kallo da take yi ta kasa ɗauke idanun ta..





"Nafeesatu lafiyan ki kuwa? Me ya fito dake waje?"


Maganar Baba Jaure da yayi ya dawo da ita tunanin ta. Saurin kallon sa tayi


Sai ya sake cewa. "Subhanallah.. kuka kike yi lafiyan ki me ya faru? Ina Usman ɗin?"


Duk bata iya amsa mishi tambayoyin ba illa hannu da ta sanya tana share hawayen ta

Yaran ya kalla yace, "kai ku tafi kuyi wasan ku kunji ko?"

Hakan yasa suka dare a wajen sai dai basu tafi ba sun tsaya suna kallon Ɗahira

Shi kuma hannu yasa ya gyara mata sandan da kyau yana cewa, "zaki iya tafiyan dai ko?"

Gyaɗa mishi kai tayi sannan ta soma tafiyan a hankali yana biye da ita a baya.





      Suna shiga gidan ya nufi ɗakin da Usman yake kwana ganin be ganshi a waje ba


Yana ciki kuwa ya kwanta idanun sa a rufe, sai dai tunani ne fal cikin ransa da kuma haushin Ɗahira da yake ji, sosai ransa yake a ɓace

Nan Baba Jaure ya ɗaura masa da faɗan "barin ta da yayi ta fita ita kaɗai".

Kanzil be ce mishi ba har ya gama ɓaɓatun shi shi kaɗai yabar wurin.





     Itama Ɗahira tuni ta shige ɗaki ta zauna tana ci gaba da zubar da hawaye, baƙin ciki ne sosai ke nuƙurƙusan ta na rashin mayar mishi da martani har ya tafi, ga tsantsan tsanar shi dake ƙara rufe ta, ta tsani ta buɗe idanun ta ta ganshi kusa da ita, babu abinda ke tuna mata illa rayuwar ƙuncin da tayi sanadiyar shi, da kuma azabtarwan da yayi mata. Ita a yanzu burin ta su koma gida su Kaka su amsar mata takardan sakin ta. Nan kuwa kewan ƴan gidan su ya cika ta, ta kwanta nan tana ta murƙususu tana faman tunani.



      A kwana a tashi kamar yau ne suka zo cikin wannan ƙauyen, sai ga shi sun shafe kimanin watanni shida a karkaran, wanda ciwon Ɗahira ne ya tsayar da su har wannan lokacin domin tuni an samu hanya, shiyasa tana warke wa suka yi haraman tafiya



Inda sosai Baba Jaure ya nuna rashin jin daɗin sa, domin ba kaɗan ba ya shaƙu da su a wannan watannin da suka yi tare da shi, bare shi ba me kowa ba, shiyasa rabuwar nasu zai yi masa ciwo, sosai yayi musu nasiha a kan riƙe addu'a domin shi ne takobin mumuni, duk wani halin da suke ciki su dage su riƙa kare kan su da addu'a don suna da maƙiya masu bin su da sharri, sannan yayi musu nasiha kan zamantakewar aure da ya taɓa musu zuciya ainun, kuma yace "idan da hali su zauna su sasanta su riƙe auren su hannu bibbiyu, duk wani saɓani dake tsakanin su su yi ƙoƙarin ganin sun daidaita kan su, domin ba ƙaramin dace wa suka yi da juna ba".


A sanda yake faɗan wannan kalaman nasa har ɗago kai Usman yayi yana kafe Ɗahira da ido, inda yake son ganin abinda yasa Baba Jaure ya faɗi hakan, a kuma ƙasan ranshi yana jin wani nishaɗi da be san na mene ne ba, ko kaɗan memakon maganar tashi ta ba shi haushi sai be ji hakan ba, har yana ji a ransa a yanzu zai iya yin ma iyayen sa biyayya ya riƙe ta a matsayin matar sa ba tare da ya sake ta ba, wanda kuma a ganin sa Nasihan Baba Jaure ne ta taɓa masa zuciya ainun har yayi wannan tunanin

While ita kuma Ɗahira ko kaɗan bata yi tunanin wai zata iya ci gaba da rayuwa da shi ba, ta rigada ta saka wa ranta zaman su ya ƙare har abada, shiyasa ko ɗar bata ji ba a zancen Baba Jaure, kamar yanda yake shiga ta wannan kunnen haka yake fita ta wancan kunnen, har ya kuma gama ɗin. Sai dai zuciyar ta fal da kewar sa da za su yi, har a ranta ta ƙudura wata rana zata kawo mishi ziyara ko da ita kaɗai ce.

       

     Sun fito inda Baba Jaure yayi musu jagora suka yi sallama da mutanen ƙauyen, daga nan aka ɗauke su a motan ɗiban kaya aka fita dasu har titin da zai kai su cikin gari, inda aka sauke su suka sami abin hawa suka miƙa gida, zuciyar ko wannen su cike da wani irin farin ciki da murna na ganin yau za su koma su haɗu da ahalin su. Ɗahira tsaban zumuɗi bakin ta ya ƙi rufuwa sai wani zillo take yi ta kasa zama waje ɗaya

Inda Usman kawai kallon ta yake yi yana sake jin wani irin nishaɗi a ranshi


Dayake waje ɗaya suke zaune kuma motan a cike take fal, ita tana ƙarshen baya; shi kuma yana kusa da ita, sosai suka matsu da juna


Amma hakan be sa Ɗahira ta damu ba, ta ma manta shaf illa tunanin gida da take yi da ƙosawan su kai


Sai shi ne da zuciyar sa ta hana sa sukuni, da kuma yanayin da yake ji sanadiyyar haɗuwar cinyoyin su wuri ɗaya, lumshe idanu kawai daga ƙarshe yayi yana amsar baƙon yanayin da ya zo mishi, wanda ya kasa fassara ko mene ne, tare da tunanin abinda ya kasa ɓace mishi a rai.




     _Fans ku sanar dashi idan kun sani._







⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫



      Kwana biyu kenan da farfaɗowar Baffa, wanda ya sanya ahalin farin ciki matuƙa, duk da jikin sa babu daɗi sosai amma kuma sun ji daɗi matuƙa. Haka aka ci gaba da kulawa dashi sosai kuma alhmadulillah yana samun sauƙi, tunda har ya soma magana kaɗan, sai dai abin mamaki babu abinda yake faɗi sai sunan Ɗahira, maganar tashi kenan Ɗahira.  Ɗahira, wanda hakan ya ɗaure wa su Big Dady kai, "ko dai ya san ta mutu ne?" Tambayar da suke wa kansu kenan

Ganin abin nashi gaba yake yi kullum maganar nasa kenan,  sosai hakan ke ƙona ran Hajja Fatu, cike da haushi kuwa tace dashi, "gwara ma ya cire ta a ranshi, idan ba haka ba sai dai shima ya mutu yabi ta".

Maganar nata ta taɓa shi, duk da yana jin jiki haka ya ɗago yana tambayar ta fuskar shi sharɓe da hawaye, "don Allah Hajja meyasa kike wannan maganar? Yanzu kenan kina nufin baza ki bani damar auren ta ba ko da Usman ya sake ta?"


"To wa ya faɗa maka an gansu? Ai ina ce ɓacewar nata ne ya sanya ka wannan halin? To yanzu haka kimanin watanni shida kenan ba'a samu inda suke ba, mu har mun yi jana'izar su tuni..."


Tarin da ya sarƙe shi ne ya tsayar da ita daga maganar ta. Yanda yake yi tuni hankalin ta ya tashi ta ruɗe lokaci ɗaya tana kiran sunan shi


A lokacin ne su Big Dady suka shiga dai-dai da lokacin da ya fara aman jini


"Subhanallah.. innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. what's going on?" Inji Abbu da duk ya ruɗe shi ke riƙe da Baffan


Hajja Fatu da duk ta ruɗe ta karaɗe ɗakin da kuka, hakan ya jawo hankalin Abba dake waje yana amsa call be shigo ba, shima nan ya faɗo ɗakin yaga halin da Baffa ke ciki, sai sambatu yake yi yana kiran Ɗahira. Dole suka soma ba shi taimakon gaggawa cike da ruɗewa ganin yanda yake yi. Daƙyar suka samu suka tsayar da jinin suka saka mishi oxygen don ba ya iya numfashi da kyau


Al'amarin da ya ƙara ɗaga hankalin su kenan, duk sun shiga damuwa suna murna ya samu sauƙi ashe zai koma gidan jiya


Inda gefe ɗaya Hajja sai faman kuka take yi, tana dana-sanin sanar mishi da abinda ke faruwa, ga shi itama zata rasa ɗanta.





          Kwanan sa ɗaya ya samu ya farka, sai dai jikin babu sauƙi ko kaɗan, lokacin su Big Dady duk suna kanshi suna sake duba shi


Sai ya soma musu kuka yana tambayar su "da gaske ne Ɗahira ta mutu?"


Sosai suka yi mamakin ya aka yi ya sani


Nan Abba tunanin sa ya ba shi Hajja ce ta sanar mishi, ranshi ya ɓaci sosai amma babu yanda zai iya yace, "kayi haƙuri ka san duk me rai mamaci ne, ƙaddaran su kenan kuma babu me tsallake wa.."


Big Dady katse shi yayi yana cewa, "haba Abubakar ka dena maganar mana, ka ga ashe shi ne silan tashin ciwon shi me zai sa ka riƙa mishi bayan kana ganin halin da yake ciki?"


Baffa dake riƙe da gefen ƙirjin sa yana kuka kashirɓan yace, "wlh nima bazan iya rayuwa babu ita ba a duniyar nan, ina son ta Abba don Allah ku nemo min ita, bazai yiwu ace Ɗahira ta ta mutu ba. Tana raye don Allah ku nemo min ita Kar in mutu". Sai ya fashe da wani sabon kukan yana cewa, "Hajja ta cuce Ni ta raba Ni da ita, amma yanzu bazan iya haƙura ba sai na aure..." Sai ya fara tari be ƙarisa ba, nan da nan jini ya soma zubar masa ta baki




Tashin hankali ba a saka mishi rana.





    Duk taimakon da su Abba suka so ba shi amma abin ya citura, tuni zuciyar sa ta gama bugawa lokaci ɗaya numfashin sa ta ɗauke daga jikin sa, wanda hakan ya tabbatar musu da Baffa ya rasu, ya tafi ya bar duniyar.




           Sai suka daskare kawai ba tare da sun san meye next abinda za su yi ba, amma tuni hawaye ya wanke musu fuska


Barin ma Abba da shi ya kasa tsayuwa waje ɗaya, sai kai komo yake yi cikin tsantsan tashin hankali, ƙwaƙwalwan sa ta kasa yarda Baffa ya rasu, sai ya taho kawai ya sake taɓa shi yana son tabbatar wa, cikin raunin murya yake cewa, "Baba na.. Baba na Ka tashi mana don Allah ka tashi.. Ɗahira tana raye bata mutu ba, ka tashi kaji Ni zan baka ita babu me raba ka da ita, da ka sanar min tun farko ai da tuni na aura maka ita, ka tashi kaji don Allah ka tashi".



Da su Abbu suka fahimci sambatu ne kawai yake yi sai suka kama shi suka zaunar suna tausan shi, inda gaba ɗaya hawaye suke yi kashirɓan, sun kasa fita su sanar wa mutanen gidan dake bakin ƙofa suna jiran su.




Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. kullu nafsin za'ikatul mauti 😭😭



Bazan iya fasalta muku halin da ahalin nan suka shiga ba sanda labarin mutuwar Baffa ya riski kowa. But think for yourself.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




        *EPISODE Fifty Nine*


       Motar na sauke su suka hau keke napep ta nufi dasu gida, har suka kai babu me magana a cikin su, kowa tunanin da yake yi daban dana ɗan uwan sa.




         Tun sanda suka doso layin gidan su suka ga mutane cike fam, wasu a zaune a cikin rumfa wasu kuma a tsaye, wasu kuma cikin motocin su inda gaba ɗaya wajen cike yake da ababen hawa



Al'amarin da ya soma tayarwa su Usman hankali kenan, duk suna tunanin abinda ke faruwa a ƙofar gidan su mutane suka taru haka. Daga gate ɗin su har babban Gate ɗin gidan duk an buɗe mutane nata ɓulɓulowa, wasu na shiga wasu na fita.




         Shima me napep ɗin da yaga ya kasa kutsa motar tashi sai ya sauke su a wurin, inda tuni Ɗahira tayi gaba tabar Usman da biyan kuɗi, shima sai ya biyo bayan ta yana bin mutanen wurin da kallo, duk yaga waɗanda ya sani cikin dangi, amma dayake wurin maƙil ne ba kowa yake kula dasu ba, bare kuma yanda duk suka sauya duk kan su.




          Ƙwaƙwalwan su fa ta kasa ɗaukar abinda kunnuwan su suke jiye musu wajen mutanen dake gaisuwa, don tuni maganganun wasu mutanen ya faɗa kunnen su inda suke gaisuwa suna faɗin sunan Baffa


Tuni Ɗahira ta ƙara sauri tana ƙoƙarin shigewa gidan


A lokacin ne kuma su Big Dady dake zaune a rumfar ƙofar gidan suka hange su, gaba ɗayan su tashi suka yi suna bin su da kallo, tabbas su Ɗahira suke gani, su ne suka dawo basu mutu ba


Usman dake shirin shiga gidan shima ya hange su nan yayo wajen su yana ɓashe baki



Sai suka tsaya kamar gunki suna bin shi da kallo sun kasa kataɓus, mafarki ne ko gaske shi ne abinda suke son sani, Waɗanda suka cire rai da tsammanin dawowar su; su ne yanzu suke gani a gaban su.






            *******

       Ciki kuwa Ɗahira sanda ta shiga ta sake tabbatar wa da tabbas zaman makokin Baffa ake yi, inda ta zo shiga Part ɗin su taji Aunty Zulaiha na kuka tana buga waya tana sanar wa wasu daga cikin dangin mijin ta, tana ce musu "har an yi jana'izar sa yanzu aka dawo ma".


Cak ta tsaya a inda take tana jin wani abu ya tsarga mata, so take yi ta ƙarisa inda Aunty Zulaiha ke tsaye ta juya baya amma ina ƙafafuwan ta sun gaza ɗaukar ta, saboda ruɗu da tashin hankalin da ya riske ta, sai kawai ta zube a wajen ta faɗi a sume.




     Wanda yayi dai-dai da juyowar Aunty Zulaiha tana shirin koma wa ciki, ganin mace zube bata tabbatar da ko waye ba sai ta nufe ta da sauri, ta mirgino da fuskar ta sai fuskar Ɗahira ya bayyana gare ta. Wani irin ja da baya tayi muryan ta tana rawa tace, "Ɗa..hiraa". Sai kuma ta tashi da gudu ta shige part ɗin tana ihun kiran mutanen gidan da son sanar musu "Ɗahira ta gani".




             Gidan mutuwa fa ya rincaɓe da ganin dawowar su Ɗahira, don tuni su Abbu su ma sun shigo tare da Usman, lokacin an wuce da Ɗahira ɗakin Aunty Amarya, sai dai duk wani taimako da aka bata bata farfaɗo ba. Hankula sun ƙara tashi, dole aka bar zancen bin ba'asi zuwa dare lokacin an nitsa da shigowar jama'a.




         Sanda Ɗahira ta farka kuka tay ta yi; domin ba kaɗan ba mutuwar Baffa yayi mugun taɓa ta, ko magana ta kasa ma kowa sai kuka, abinci ma taƙi ci duk ta fita hayyacin ta, sai dai rarrashin ta da ake ta faman yi.




       Sai dare jama'ar gidan suka taru gaba ɗayan su har da su Hajiya Laila Hajiya Ikram da yaran su, da duk wani me ruwa da tsaki sai da suka cika General parlour fam, kowa so yake yi yaji labarin abinda ya faru dasu


Usman ne ya basu labarin komi, don ita Ɗahira har yanzu ba ta iya magana, tana jikin Aunty Zainab sai zubar da hawaye take yi wanda suka kasa tsaya mata tun farkawan ta, har yanzu gani take yi ƙarya ne Baffa be mutu ba, ji take yi kamar zata ganshi cikin jama'ar parlour'n, shiyasa sai ware ido take yi tana kallon mutanen ciki.




         Sosai aka tausaya musu da wannan iftila'in da ya same su, barin ma Ɗahira ita da ta shiga mugun yanayi, karaya har biyu a ƙafafu wanda tasha jinya ba kaɗan ba, sai sannu suke mata suna "ta auna arziƙi Allah ya kyauta gaba". Sai dai su Aunty Zulaiha su amsa amma ita ko uffan ta kasa cewa.




      Da haka aka tashi a taron, duk yanda Kaka yaso ya gana da Ɗahira sai dai ya haƙura kasancewar ba ta cikin mood ɗin ta, ranan mutane da yawa basu runtsa ba a gidan nan, kar ma ace Hajja Fatu, domin mutuwar Baffa ya taɓa ta ainun, tasha kuka har ta gode wa Allah, duk tayi yaushi itama maganar ma ba ta iya yi


Yayinda Sa'adatu tana can asibiti ana jinyan ta, tunda tun sanda aka sanar musu rasuwar Baffa ta zube, ga tsohon cikin ta haihuwa ko yau ko gobe, duk da watan sa takwas ne amma yayi mugun girma, wasu ma cewa suke kamar ƴan biyu zata haifa saboda girman cikin, sai dai dayake likitoci ne gidan tuni an bincika an ga ɗa ɗaya ne a ganin su.




         Washe gari kuma sai aka tashi Yusra babu lafiya, naƙuda gadan-gadan yazo mata, ba'a ma kai ga kaita asibiti ba ta silliɓo ɗan ta namiji. Kowa ya yi murna duk da ana cikin baƙin ciki.




       Ranan bakwai ɗin Baffa da ya kasance kwana shida da haihuwar Yusra aka yi sunan ɗan nata, kasancewar duk wasu za su tafi a ranan ne, Sulaiman yayi musu kara inda ya saka wa yaron sunan Baffa. Al'ameen. Za su na kiran shi da Little Baffa.




         Fannin Ɗahira kuwa gaba ɗaya ta sauya har ciwo sai da ta kwanta sabida damuwa, sai da Aunty Amarya tayi da gaske kafin ta soma shawo hankalin ta, sannan ta koma tana cin abinci har tana iya magana


Yau ma ce mata tayi "taje ta yiwa Hajja Fatu ta'aziyya tunda bata je ba," ga shi dama Hajjan ba lafiya ne da ita ba


Shi ne ta tashi ta fita, sai da taje wajen Kaka kafin ta wuce Part ɗin Hajja, lokacin da ta shiga babu kowa kasancewar kowa ya watse, har Shakira ta koma gida, dayake yau kwana takwas kenan


Bayan tayi sallama taji babu kowa sai ta wuce ɗakin Hajja Fatu, sai da ta sake sallama kafin ta shiga ciki


Hajja dake kwance saman gadon ta duk ta wani rame sai kace ba ita ba, mutuwar babban ɗa kamar Baffa ba wasa ba. Tana ɗago kai taga Ɗahira ce sai tayi kicin-kicin da fuska zuciyar ta na ƙuna


Ita kuma sai ta taho ta zauna a kan drowan gadon tana gaishe ta tare da mata "ya jikin?"


Ai kuwa tuni Hajja ta yunƙura ta cafke wuyan Ɗahiran ta maƙure ta, cikin hayagaga take cewa, "kutumar uban ki dake da jikin matsiyaciya annamimiya, burin ki ya cika kin raba Ni da ɗana shi ne ke kika dawo ko? To wlh kamar yanda ya mutu kema wlh sai kin bi shi bazai taɓa yiwuwa ki kashe min ɗa ke kuma ki dawo ki ci gaba da rayuwa ba, wlh baki isa ba".


Idanun Hajja fa sun rufe sai zagin Ɗahira take yi kamar zata kashe ta


Gaba ɗaya idanun ta sun fito waje taji shaƙa tana neman taimako


Amma Hajja taƙi sakin ta sai ƙunduma mata zagi take yi ta uwa ta uba tana faɗin "itama sai ta kashe ta".


Hayaniyar su ne ya shigo da Abba ɗakin, domin shigowar sa kenan Part ɗin ya jiyo zagin da Hajja take ƙunduma wa, yana shigowa yaga abinda ke faruwa sai ya nufe su da mugun sauri ya ɓanɓare Hajja Fatu yana falla mata mari. "Baki da hankali ne Fatima kashe ta zaki yi? Me tayi miki?" Sai kuma ya koma kan Ɗahira da ta faɗi ƙasa tana ƙaƙarin amai kamar zata mutu, gaba ɗaya fuskar ta ya jiƙe sharkaf da hawaye domin ta ma kasa kukan. Ɗago ta yayi yana mata sannu


Amma Hajja ta soma faɗin, "wlh tallahi sai naga bayan ta babu wanda ya isa ya dakatar dani tunda tayi min sanadin mutuwar ɗana, sai na kashe ta nima".


Tsiya fa sai ya kaure daga ita har Abba sabida jin kalaman ta da take faɗa wa Ɗahira


Lokacin ne Hajiya ta shigo taga me ke faruwa, domin hayaniyar har Part ɗin ta dayake sun fi kusa. sai taje ta sanar wa Big Dady, kankace me gida ya ɗauka da abinda ya faru, har an kai maganar wajen Kaka


Shi kuma Abba dole sai da ya matsa Hajja ta faɗi abinda yasa take son ganin bayan Ɗahira, tunda ya gane ta san komi, kuma dama ya ƙyale ta ne tun ba yau ba domin a fice taron jama'a, yana son tambayar ta ta sanar mishi alaƙar dake tsakanin Ɗahira da Baffa da har basu sani ba


Dole da ta ga bala'in sa ta faɗi gaskiya ita ta hana Baffa ya auri Ɗahira wanda sanadin haka ya faɗa shaye-shaye sannan ya kamu da ciwon zuciya


Da jin haka sai Abba ya miƙe ya kife ta da maruka har uku, duk yanda su Big Dady suka so su dakatar dashi amma ina ya gagara, be jira wata-wata ba yace, "ya sake ta".


Tashin hankali kenan da ba'a saka mishi rana, yau ga Hajja Fatu a tsaka me wuya, domin lokaci ɗaya ta kurumce gidan da ihun ta saboda abinda bata taɓa zaton zai faru bane.















_So ku yi manage please._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

          *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.

             *EPISODE Sixty*

            Take a nan Kaka ya saka shi ya mayar da ita ɗakin ta, kuma yayi mishi faɗan saurin ɗaukar fushi abin duk be kai haka ba duk da tana da laifi, amma Allah ne ya ƙaddara wannan hanyar ne silan mutuwar Baffa

Ba da son ran Abba ba ya mayar da Hajja Fatu, amma a ranshi ya ƙudura aniyar sai ya ƙaro aure, don bazai yiwu ya ci gaba da zama da ita a matsayin mata ba tana ƙunsa mishi baƙin cikin ta, ita kenan kullum haɗa mishi jaraba sai kace ita kaɗai

Please Login or Register in order to submit comment