Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka ba...


           Muryan Baba Jaure ne ya dawo dashi tunanin sa, "Fito mana Usman mu je Masallaci".


Be ce komi ba ya tashi ya fice, har yayi Sallah be da wani kuzari


Ko da ya dawo zama yayi a waje ya haɗe kai da gwiwa


Baba Jaure da ya shigo ya soma tambayar sa "me ke damun sa?"


Amma sai yace mishi "babu komi".


Yace, "ka wuce wancan bukkan ka kwanta kaji? Ka tashi a waje ka ga garin yana kaɗa wa".



Be yi musu ba ya miƙe ya nufi ɗakin da ya nuna masa, ya shige yayi kwanciyar sa, sai dai ya gaza hana kansa tunani, be san meyasa ba kalaman ta kawai suke dawo masa, duk inda ya juya muryan ta yake ji ya rasa ya zai yi, duk da ya san cewa komi zata iya masa sakamakon abubuwan da yayi mata a baya



Ƙarshe tashi zaune yayi ya sake haɗa kansa da ƙafafu yaci gaba da tunanin sa, yana jin sanda ruwa ya ɓarke kamar da bakin ƙwarya amma be motsa ba, ga sanyi dake shigan sa saboda rashin rufa da be yi ba.




           A haka har garin Allah ya waye Usman yana zaune digirgir, wanda shi kansa ya sha mamakin wannan al'amarin, domin duk yanda ya so ya hana kansa tunani ya samu barci ya gaza, haka ya tashi jiki babu ƙwari ya fita yayi alwala suka wuce masallaci shi da Baba Jaure, sai da ya dawo ne ma ya samu barcin ya ɗan sure shi cike da mafarkai kala-kala.









⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫



         Sanda labarin mutuwar Usman ya riski Ayush hauka ne kawai bata yi ba, tayi kuka sosai kamar baza ta dena ba, wanda har sai da ta kwanta ciwo ranga-ranga domin ba ƙaramin shigan ta mutuwar yayi ba, dole iyayen ta suka ɗauke ta suka wuce da ita asibiti, kwanan ta biyar sannan ta soma samun sauƙi, sai dai sauƙin a jikin ta ne amma ba a zuciya ba, zuciyar ta ta rigada tayi tabon da baza ta taɓa warke wa ba, bata shirya rasa Usman a rayuwar ta ba, ko kaɗan bata taɓa kawo wa kanta zai mutu ba tare da ta cika burin ta a kanshi ba, ita kanta bata san soyayyar da take mishi ya kai haka ba sai da ya mutu, ƙarshe dai ko da aka sallame ta suka koma gida ta dena walwala gaba ɗaya ta rame, mahaifyar ta tayi-tayi ta faɗa mata abinda ke damun ta amma ina taƙi, sai dai kullum tana cikin tunani da kuka, ko abinci ta dena ci, kuma ta dena zuwa aikin ta.




       Safra har gida tazo ta duba ta, itama ta bata baki sosai amma Ayush taƙi jin ta, har tace mata, "idan har wani saurayin ne wanda ya fi Usman zata samo mata, amma yanzu ta cire damuwa a ranta tana cutar da kanta".


Ayush kallon ta tayi tana zubar da hawaye tace, "baza ki gane bane Safra, na rigada na saka shi can cikin zuciya ta da fitar shi zai yi wuya a gare ni, har yanzu ji nake yi a jiki na be mutu ba, na kasa yarda wlh, taya Usman ɗina zai mutu ba tare da na aure sa ba? Taya? Gaba ɗaya rayuwa ta na tsara ta ne dashi, abubuwan da nake gani a mafarki na yanzu duk sun rushe baza su gasgata ba".


"Hmm Ayush dole ki yarda ya mutu tunda iyayen sa ma sun yarda, batun kuma ki cire sa a ranki wannan kuma me sauƙi ne, sai dai idan ke ce kika ƙi hakan, duk da na san na ɗan lokaci ne dole ki manta shi, akwai waɗanda suka fi Usman komi a duniya zaki same su, kar ki hana wa kanki jin daɗin rayuwa a kan ɗan ƙanƙanin abu Ayush, ki manta shi please, ke Kinga yanda kika koma ne?" Ta ƙare maganar tana sake bin Ayush ɗin da kallo


Numfashi kawai Ayush taja ba tare da ta sake cewa uffan ba, domin ta san duk abinda zata faɗa Safra baza ta taɓa gane wa ba, gwara tayi shiru ta ƙyale ta zai fi


"Zan tafi muje ki raka Ni, amma wlh ki sauya tunani tun kafin ki naƙasa kanki, aikin da kike matuƙar so ga shi har kin dena zuwa saboda wannan damuwar taki, idan baki yi wasa ba zaki rasa komi naki wlh". Cewar Safran tana tashi tsaye


Itama Ayush tashi tayi ta bi ta suka fita


Mahaifiyar Ayush dake zaune tana tankaɗe Safra tayi mata sallama sannan suka fice


Har ƙofar gida ta raka ta sannan suka rabu, Ayush ta dawo ciki, ita kuma Safra ta shiga motan ta taja ta tafi.







⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫


        Kaka ya samu sauƙi har an sallame sa, sai dai abinda ba a rasa ba, inda za'a ci gaba da kula dashi a gida ana ba shi magunguna, duk ya koma wani iri kullum maganar sa ɗaya Ɗahira, mutuwar ta ta shige sa ba kaɗan ba, duk da ba ita kaɗai ba har Usman ɗin, amma ya fi jin mutuwar Ɗahiran.




        Shi kuma Baffa har yanzu ba ya sanin su waye a kanshi, jiya iyau ake har yanzu


Babu wanda ya kai Hajja Fatu shiga damuwa, ta koka ta koka har ta gaji, duk da ta san mutuwar Ɗahiran ne ya saka ɗanta shiga wannan matsanancin halin, amma bata yi nadama Ba, ji take yi da Ɗahira zata dawo duniya a yanzu haka; wlh da babu me ƙwatan ta a wurin ta, domin tasha alwashin sai ta salwantar da rayuwar ta me munin gaske, har yanzu kuma bata fasa tsine mata a zuciya ba, kullum da ita take kwana take tashi, gaba ɗaya ta sauya wa Aunty Amarya fuska, ko gaisuwar ta ba ta amsa wa, har habaici take mata, ta kasa ɓoye ƙiyayyar ta yanzu a fili, ƙiri-ƙiri take faɗa mata "ɗiyar ta ne tayi silan shigan Baffa a wannan halin, kuma wlh idan be tashi ba ta rasa shi sai taga abinda zata yi mata, daga yanzu babu mutunci a tsakanin su".


Aunty Amarya takan bi ta da kallo ne kawai, tun abun yana bata mamaki tana ganin kamar wasa ne, sai kuma taga eh lallai Hajja Fatu da gaske take yi, sai kuma abun ya soma damun ta, "meye haɗin Ɗahira da Baffa da zata yi silan shigan sa cikin wannan halin har ya sha giya? Ta san dai babu soyayya a tsakanin su, shaƙuwa ce kawai wanda kuma Allah ne ya haɗa jinin su, tunda tana ganin ga shi jinin su ya haɗu, amma kuma Allah da ikon sa ba sa shiri da Usman, to taya ya zata ɗaura wa ɗiyar ta wannan zargin?" Ta kasa jure wa sai da ta sanar wa Abbu


Shi kuma Abbu sai yace mata, " ta ƙyale ta tayi ta kanta, kuma duk abinda zata ce kar ta soma ta kula ta".


Da wannan maganar na Abbu Aunty Amarya tayi amfani, duk wani haushin karen da Hajja Fatu take yi ba ta kula ta, iya kan nata ido ne.













_ku yi haƙuri babu yawa, so kuyi manage._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




        *EPISODE Fifty Seven*




       *AFTER THREE WEEKS*

        A wannan kwanakin da suka shuɗe Ɗahira ta sha wahala sosai, bazan iya misalta muku azaban da ta fuskanta ba, tabbas karaya babu daɗi, barin ma ita da take mace me rauni, kuma har ƙafafu biyu, duk juriyan ta ta kasa jure wa, sai da ta sake goce ƙafa ɗaya Baba Jaure ya sake gyara mata, azaban duniya ta sha shi har suma tayi, tasha kuka kamar zata tsiyayar da hawayen ta, domin a ranan ma kwana tayi tana kuka taƙi cin komi


Daga Baba Jaure har Usman sun kasa rarrashin ta, shi Usman ma har sai da yayi mata hawaye, sosai yake jin tausayin ta na tsarga mishi ta ko ina a jikin sa, yana jin dama zai iya da ya dawo da ciwon jikin sa.

     A haka Baba Jaure yake ta rarrashin ta yana bata bakin "ta jure idan ba haka nan ba sai dai a yanke mata ƙafafun muddin basu warke ba".


A haka kwanaki suke ta shuɗe wa Ɗahira na a wannan halin, amma duk da zafin ciwon nan ba ta bari Usman ya taimake ta, idan har ba Baba Jaure ne zai taimaka mata da wani abun ba, to, ta gwammace kar tayi, gaba ɗaya ta tsani ma ganin sa kusa da ita, baza ta taɓa manta abinda yayi mata ba, shiyasa duk idan ta ganshi sake jin tsanar sa take yi a zuciya, ya riga ya dasa mata tsanar shi me girma a rai, wanda duk duniya ba ta jin akwai mahalukin da tafi tsana idan ba shi ba, da ace za'a bata bindiga da tuni ta harbe shi


Shi kansa Usman yana mamakin wannan halin da take nuna mishi, duk da azaban da take ciki amma haka take iya nuna masa tsana tsantsa, ya kula ko kaɗan ba ta son ta buɗe ido ta ganshi, duk maganar dake bakin ta haka take yaɓa mishi ba tare da taji shakkun shi ba.

          Baba Jaure dai da yaga abun yayi yawa sai ya kira Usman zuwa ɗakin da Ɗahira take kwance, yace mishi "ya zauna".


Bayan ya zauna ya dube sa yace, "wai ya alaƙar ku da Nafeesatu ne? Ina son in San tsakanin ku?"

Shiru Usman ɗin yayi, sai ya kalli Ɗahira wacce ta rufe idanun ta tayi kamar bata san dasu ba a ɗakin


"Faɗa min mana ina magana? Ko ba kai kace min matar ka bace?"


"Eh Mata ta ce". Yayi maganar bayan ya mayar da idanun sa kan Baba

"Amma ya aka yi ke Nafeesatu kika ce min ba mijin ki bane? Kuma na kula kwata-kwata ba kya son ya taimaka miki, idan be taimaka miki ba a wannan halin da kike ciki wane ne zai taimaka miki? Kina buƙatar taimako sosai domin ke abar tausayi ce, Shin ko wani abun yayi miki?"


Buɗe idanun ta tayi da suka soma tara ruwan hawaye, ga zuciyar ta dake mata ƙunci da jin kalmar da Usman ya faɗa, shiyasa sai da ta kalli Usman ɗin ido cikin ido kafin tace, "Baba shi ba miji na bane, ban san shi ba, bani da wani alaƙa da shi a rayuwa ta".

Usman tsimi yayi ya kasa ɗauke idanu a kanta, ko kaɗan be ji daɗin abinda ta faɗa ba, sai ya lumshe idanun sa kawai yana haɗiyar yawu


Shi kuwa Baba Jaure jinjina kansa yayi yana sake kallon ta da kyau, sai kuma ya kalli Usman ɗin yace, "yanzu maganar wa zan yarda? Kai kace min Mijin ta ne, ita kuma tace min bata sanka ba. Amma ya aka yi kuke kama da juna, daga ganin ku kuna da alaƙa da juna?".

Usman da ya buɗe ido yace, "Baba wlh ita Mata ta ce kuma ƙanwata, jini na ce ita.."


Cikin kuka Ɗahira ta katse shi da faɗin, "wlh Ni ba miji na bane shi, sam Ni ba na ƙaunar sa ko kaɗan, na tsane sa fiye da komi a duniyar nan! kuma takardar saki na zai bani".

Kamar zuciyar sa zata ƙone a wannan karon sabida jin kalmar tsana a bakin ta, sosai yaji ciwon kalmar, shiyasa a harzuƙe yace, "to Ni nace miki ina ƙaunar ki ne? Ko cewa nayi bazan sake ki ba? Idan ba don laluran ki ba baki isa ki zauna kina gaya min wannan maganar ba ban yi ƙasa-ƙasa dake ba".


"An faɗa maka kai waye? Ka sake Ni yanzu ba sai anjima ba, banza kawai.."


Hannu ya kawo zai wanka mata mari jin zagin da tayi masa, saura ƙiris hannun sa ya kai fuskar ta sai ya dunƙule, cike da wani irin fushi yake kallon ta yace, "Ni kike zagi.. Ni?" Ya nuna kansa da hannu idanun sa jawur har jijiyoyin kansa suna tashi


Sosai Ɗahira ta tsorata har tana janye jikin ta, domin ta manta ma da wani karaya a ƙafan ta, lokaci ɗaya ta saki azababben ihu

Salati kawai Baba Jaure yake yi domin ya kasa komi illa kallon su da yake faman yi, sai da yaga Ɗahira ta saki kukan ne nan ya matso yana cewa, "subhanallah mene ne me ya same ki? Kin taɓa ƙafan ko?"


Yanda take kuka kamar ana yanka naman jikin ta sai duk jikin Usman ya soma rawa, shima ya matso kusa da ita sosai amma ya kasa cewa komi illa kallon ta da yake yi


"Kun gani ko ba kya jin magana, ban ga ranan da zaki bar ƙafan nan su warke ba sai kin ja ma kanki, kai kuma Usman da girman ka kake biye mata?" Sosai Baba Jaure yake bala'i kamar zai ari baki, sai da ya haɗa su tass yayi musu masifan kafin ya kalle ta yace, "ba na son shashanci daga yau kar in sake ganin kin goce ƙafafun nan, kuma duk wani taimako da ya kamata zai riƙa taimaka miki tunda Ni ba zama nake yi ba, kinji ko kar in sake ganin kinyi wani abun da kanki?"

Gyaɗa kanta tayi tana shashsheƙan kuka

"Mu je waje Usman". Yace dashi yana fice wa


Shima bayan sa yabi ya fita


Ita kuma Ɗahira kamar an kunna ta sai ta ɓare baki taci gaba da kuka sosai


Daga waje suna jin ta amma babu wanda ya tanka, sai dai sosai kukan ta ke shigan Usman, ji yake yi kamar ya shiga ya rarrashe ta amma ya san hakan bazai taɓa yiwuwa ba, baza ta taɓa mishi kallon arziƙi ba, shi kansa har tsoro take ba shi saboda bala'in ta, "ko dama haka take?" Yake tambayar zuciyar sa. "ko kuma zafin ciwo ne ya mayar da ita hakan ba". Wata zuciyar tace mishi haka.




     Daga ranan dole Ɗahira take bari Usman yana taimaka mata da wani abun idan babu Baba Jaure, sai dai ko magana ba ta mishi, shima haka, sun zama tamkar kurame, ko shekara za su yi a wuri ɗaya baza ta tanka shi ba, ko ya tambaye ta tana buƙatar wani abun ba ta kula sa, ta gummaci ta zauna har Baba Jaure ya dawo


Abun da ke ba wa Usman haushi tun sanda ta soma ba-haya (kashi) dayake ba'a bata komi sai Nono gudun kar ta riƙa ba-haya, sai ta bari Baba Jaure na nan sannan zata nuna tana buƙatar yi, shi ke taimaka mata, ta gummaci shi ya taimaka mata da Usman ya taimake ta, shiyasa abun ya soma ba wa Usman haushi, yana a matsayin mijin ta ai shi ne ya kamata yaga jikin ta ba wani ba, shiyasa da abun ya dame sa wajen kwana huɗu da bata yi ba, sai kawai ranan na biyar ɗin dai ya cire baki ya tambaye ta "ko tana jin Kashi ko fitsari ne ya taimaka mata?"



Sosai tambayar ya baƙanta mata rai, sai ta kalle sa kamar zata make shi tace, "ba na ji ko dole sai nayi?"

Tsaki yaja yace, "na san kina ji tunda kin kwana biyu baki yi ba, sai dai idan Ni ne ba kya son na taimaka miki sai Baba Jaure".



"Allah ya kiyaye na nemi taimakon ka, abubuwan ma da kake min da zaka fasa da nafi kowa murna, ba na ƙaunar ganin ka wlh ko kaɗan a kusa dani, ji nake yi kamar zan haɗiye zuciya na mutu, mugu azzalumi kawai".

A zuciye yace, "Nafeesa Ni kike faɗa wa haka? Wato kina ganin ina ƙyale ki shi ne yasa kike faɗa min duk abinda kike so ko?"

"An faɗa ɗin, ka kashe Ni ka huta shi ne zan san ka isa". Ta ƙare maganar tana sakar masa kallon tsana


Hannun sa ya saka ya murɗe mata baki yana cewa, "bakin zan fasa ko zaki dawo hankalin ki kisan da wa kike magana, Ni ba sa'an wasan ki bane, ina ƙyale ki ne kawai domin ina tausaya miki".

Kuka ta fashe dashi jin ya murɗe mata baki sosai


Ganin tana kuka sosai sai ya sassauta riƙon amma fuskar sa a ɗaure yace, "ke ki shiga hankalin ki kisan da wanda kike magana, Ni ne Usman kuma na san baki manta halina ba, wlh bar ganin kina halin lalura biji-biji dake zan yi".



Bata iya cewa komi ba illa kuka da take faman yi


Ganin haka sai yaja tsaki yana tashi zai fice


Ƙasa-ƙasa tace, "mugu azzalumi Allah zai saka min wlh, kuma kashi ne bazan yi ba, kuma ma ina jin yi har da fitsarin ma".

Dariya taso ba shi sai dai be juyo ba yayi ficewar sa


Ita kuma taci gaba da kukan ta tana yi tana tsine masa a ranta


A haka har Baba Jaure ya dawo, yana shigo wa ya ganta tana kuka ya tambaye ta ba'asi

Sai tace mishi, "Usman ne ya murɗe mata baki sannan ya falla mata mari". Har da riƙe kumatun ta tana me fashe wa da wani kukan

Salati kawai Baba Jaure yake saki yana faɗin, "ashsha.. be kyauta ba, wannan ai mugunta ne, ba ya ganin halin da kike ciki ne?". Sai kuma ya koma kwaɗa wa Usman ɗin kira


Usman dake waje duk yana jiyo ƙaryan da Ɗahira ta shirga mishi, ci je leɓe kawai yayi yana jinjina kansa, sai ya miƙe ya nufi ɗakin ba tare da ya amsa ba, yana shiga idanun su suka shige na juna


Sai ta balla mishi harara tana kawar da kanta

Shi kuma fuskar nan a ɗaure kamar ko yaushe yake sauraron faɗan Baba Jaure ba tare da ya ɗauke idon sa a kanta ba, duk da kuwa ba kallon sa take yi ba, "zan kama ki ne yarinyan nan zai fita ai, zan mare ki sai ki sami faɗa mishi da hujja tunda ke baki da mutunci". Yayi maganar a ranshi


Sai da Baba Jaure ya gama mishi faɗan kafin yayi ficewar sa be ce komi ba

Ita kuma sai a lokacin ta dawo da kallon ta ga Baba Jaure tace mishi, "tana buƙatar zata yi fitsari".


"To kuma sauri nake yi ina da rubutu a gaba na, meyasa baki ce Usman ɗin ya taimaka miki ba?".


"Baba na Ce mishi amma yace bazai taimaka min ba, shi ne dalilin da yasa ya mare Ni".


Baba Jaure yace, "be kyauta ba kuwa, bari in taimaka miki to, zan yi masa magana daga yau bazai sake ba".


Taimaka mata yayi ya ɗan ɗaga ta ya saka mata wani Robber me faɗi, sai ya koma bakin ƙofa har sai da ta gama ta gyara kafin ya dawo shi kuma ya gyara mata kwanciya ta yanda baza ta motsa ƙafafuwan ba.




     Duk abinda ta sake faɗa a kunnen Usman ya faɗa, kaɗa kai kawai yayi ya yi ficewar sa a gidan, ransa babu daɗi duk haushi ya cika sa, haka kawai yake jin haushin Baba Jaure Wanda be San dalili ba, "don me shima zai yarda ya riƙa taimakon ta bayan ga shi shi ne mijin ta? Ai wannan ma cin zarafin sa ne da kuma keta mishi haddin aure". Sosai zuciyar sa ke a ɓace shiyasa ya nufi jeji kansa tsaye don keɓe kansa, amma wani zuciyar nasa tana faɗa masa, "kai meye naka na jin haushi bayan sakin ta zaka yi? Ko ka manta ka tsane ta ne? Sannan ma Baba Jaure ai kamar Kaka yake a wurin ta, halin lalura ne ya kawo haka dole sai an taimaka mata". Dogon tsaki kawai yaja a fili ya furta, "to Ni ina ruwa na.. yayi mata wanka ma idan zai iya be shafe Ni ba".
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




            *EPISODE Fifty Eight*


           Sannu a hankali Ɗahira ta soma jin sauƙi, domin babu laifi yanzu tana iya ƙoƙarin ta wajen jure wa da zaman nata, ba ta motsa ƙafafuwan kullum kaffa-kaffa take yi, a haka rayuwa taci gaba inda kusan watanni huɗu kenan da soma jinyan nata, yanzu har ta soma taka wa


Baba Jaure ya haɗa mata sandan nan guda biyu da zata riƙa dogara wa


Tun ba ta iyawa da taimakon Usman da Baba Jaure ya saka shi yana koya mata tafiyan, har yanzu tana iya fita zuwa waje wani lokacin ba tare da taimakon shi ba, zaman jinya ba wasa ba, gaba ɗaya ta sauya tamkar ba ita ba, tayi wani irin haske kamar mara jini a jiki, sai kuma ƙara ramewa da tayi a fuska, sai kuma ɗan kumbura da tayi a jiki, sai dai jikin nan nata luwai-luwai kamar ka taɓa jini ya tsiyaya, saboda zama wuri ɗaya da ta jima tana yi, duk ta sauya dai. Yanzu haka har wanka tana yi da kanta, inda Baba Jaure ya samo mata itama kayan su na Fulani tana sauya shiga.



              Ga shi yanzu har sun gabatar da azumi a wannan ƙauyen, sai dai ita Ɗahira bata samu tayi ba saboda halin da take ciki, an yi sallah an gama lafiya kuma sun yi farin ciki matuƙa kasancewar sun fita sun kalli wasan sallan mutanen ƙauyen.



                Duk da gefe ɗaya kuma gaban su da Usman kullum daɗuwa take yi, kusan kullum sai sun yi faɗa, ita bakin ta bazai yi shiru ba babu ranan da baza ta sanar mishi ta tsani ganin shi a rayuwar ta ba


Shi kuma hakan na mishi zafi sosai, sai ya biye mata suyi ta yi tana ƙara ƙona mishi rai, shi kuma a ganin shi yana ƙyale ta ne don halin lalura, ba don haka ba zane mata jiki zai yi, amma duk da haka tsaban mugunta be fasa mangare ta ba ko kuma ya kwaɓe mata baki idan tana gaya mishi maganar da yayi mishi ɗaci a zuciya.



Yau ma tana zaune a waje tana shan iska


While Usman na zaune can gefe ya buga tagumi yana bin ta da kallo, sai dai a baɗini tunani ya faɗa be ma san idanuwan sa na kanta ba


Ita kuma ganin yaƙi dena kallon ta tun ɗazu sai taja tsaki tana yinƙura wa zata tashi

Tsakin nata ya dawo dashi hayyacin sa, sai ya bi ta da kallo kawai har ta miƙe, ganin ta nufi ƙofar gida zata fice sai yace, "ina zaki je?"


Bata juyo ba bare ta tanka shi, taci gaba da ɗingisa wa a hankali zata fice


Shima sai be sake ce mata komi ba ya kawar da kansa gare ta, ya ɗaura tunanin sa daga inda ya tsaya.



              Ɗahira na fita ta soma bin garin da kallo, tun ranan sallah da ta fita sai yau ta sake saka ƙafafuwan ta a wajen, shiyasa kawai take ta bin ko ina da kallo, yanda ko ina yayi kore sharr da bukkokin gidaje sai ya bata sha'awa, tamkar dai babu kowa a garin haka wajen ya ɗaɗe, takawa ta soma yi tana ci gaba da tafiya tana kallon ko ina, jefi-jefi kuma ta soma ganin Mutane, yara a waje suna wasa da kuma hayaniyar mutanen cikin gida


Yanda suke wasan ne sai ya ɗauke mata hankali ta shagala tana kallon su


Suna ta wasan ƴar gala-gala ne maZan su da matan su, sai dai sun raba ne idan mata suka yi sai maza su yi, kowa yana son ace su ne gwani. Duk basu lura da ita ba duk tsayuwar ta


Har ta soma gajiya tana shirin juya wa sai sandan nata ya gurɗe zata faɗi, sai ji tayi an tare ta ta faɗa jikin mutum. Da sauri ta ɗago kai tana kallon sa zuciyar ta na wani irin bugawa a lokaci ɗaya da nashi, waro ido tayi kawai tana kallon shi tana ɗauke numfashi tsamm sabida yanda taji wani abu ya tsarga mata a cikin jikin ta wanda baza ta iya fasalta shi ba

Shima haka zalika abinda taji shi ya ziyarce shi, shi nashi ma har wani nauyi zuciyar tashi tayi mishi tare da tsantsan tsoron da ya saba ziyartan shi a duk sa'ilin da ya haɗa ido da ita,

Please Login or Register in order to submit comment