Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan kuma suka haɗu a hanya gudu take yi, sabida muddin ya kama ta dukan mutuwa yake mata. Iyayen su tun ba sa damuwa har dai kowa ya gane tsana ce kawai Usman yake mata, sun yi faɗan sun yi faɗan don ya dena dukan ta amma ya ƙi, shiyasa a lokacin da suka gama karatun su suka dawo, sai Usman ya nemi "a barshi ya koma can yayi aikin sa tunda an yi masa tayi".




To shi kuma Kaka be ja da zancen ba ya bar shi, ba don komi ba sai don ba ya son ya takura wa Ɗahira, saboda a lokacin har ya soma kiman ta duk da da girman ta a time ɗin, su ma sun dawo hutu daga Zaria  lokacin suna karatu a ABU, daga sun haɗa ido da ita a ganin shi na farko da yayi mata, ita kuma tuni ta tsere sabida ganin sa don bata yi tunanin yana ɗakin Kaka ba, shi ne fa ya tashi a lokacin tsam yabi bayan ta, su Kaka duk basu san me ya tayar dashi ba, tunda a ganin su ta girma ta wuce duka a wurin sa

Ashe shi Usman har Part ɗin su ya bi ta ya zaƙulo ta a ɗakin su yayi mata shegen duka, ba komai ya saka shi haka ba sai yanda ta faɗar masa da gaba har yana datse haƙora, ga kuma mugun tsoron da ya riske shi a lokacin, don a time ɗin ta zama ƴan mata idanun nan sun ƙara girma da kyawu

Aunty Amarya ita tazo ta ce ce ta tana tambayar sa abinda tayi masa, kasancewar ta ba me son faɗa da hayaniya ba shiyasa bata nuna ɓacin ranta a kan abinda yayi wa Ɗahira ba

Shi kuwa be ce komi ba ya juya ya fice a zuciye

Fadil ya shafa da gudu ya sanar wa su Kaka. Mafarin kenan Kaka ya amince da komawar sa can Turkay yayi aikin sa, duk da suna da buƙatar sa a nan sabida suna da asibitin su, amma kuma hakan shi ne zai kawo sauƙi wajen Ɗahira, su baza su iya hana Usman ba tunda duk faɗan da zaka yi masa wlh bazai dena ba, abinda yayi ninya kawai shi yake aikata wa, da ace faɗa zai saka Usman ya dena dukan Ɗahira da tuni ya dena, amma ga shi ashe abun gaba yayi ba baya ba.

        Tunda ya tafi kuma sai Ɗahira bata sake saka shi a idon ta ba, a lokacin sosai ya koya mata tsanar shi, bata da maƙiyi a duniya sama dashi, ko da ya dawo hutu to zata bar gidan Idan har lokacin su ma suna gida, ko ta tafi gidan ƙanwar Kaka Hajiya Hannatu (Ihsan) ko kuma ta koma Zaria can Soba dangin Maman ta tayi zaman ta har sai sun koma school, ita da ta dawo gidan sai kuma wani hutun idan Usman ba ya gida, bata ƙara yarda sun sake haɗuwa ba sai dawowar sa gaba ɗaya da yayi wanda kuma sun gama school, lokacin tana ganin baza ta iya juran waɗannan abubuwan da yake mata ba...





           Numfashi Usman yaja sanda yaji muryan Baba Jaure Yana mishi Magana.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.

        *EPISODE Fifty Five*

         Bayanin Farko da aka sanar musu a kan Baffa ya yi matuƙar ɗaga musu hankali, ya kamu da ciwon zuciya, ga kuma shaye-shayen da yake yi wanda yayi mishi illa sakamakon ya sha wanda ya fi ƙarfin shi

Ai hauka ne kawai Hajja Fatu bata yi ba jin wannan bayanin

Su kuwa su Abba basu yarda da result ɗin ba daga farko, domin a cewar su "ɗan su ba ya shan giya, sannan babu abinda ke damun sa da har ciwon zuciya zai kama shi," duk da sun san cewa shi ciwon zuciyan Allah na saka maka haka kawai, jarirai ma da ake haifa suna iya kamuwa da ciwon zuciya, amma da suka yi gwajin da kansu sai suka fi yarda tunda ga result zahiri, ga shi kuma ciwon yayi masa mummunan kamun da ya shiga coma lokaci ɗaya, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, tashin hankali ba'a saka mishi rana, ban san ya zan kwatanta muku halin da suka shiga ciki ba, sai dai kamar yanda suka yarda da Allah sun kuma yarda da ƙaddara, shi ne yasa komi yazo musu da sauki. A yanzu dai Aunty Amarya ita jikin nata da sauki duk da ba dena kuka tayi ba, sai dai tana kukan zuci wanda ba ta jin nan kusa zata dena, ɗiyar ta ɗaya tilo Allah ya amshi abin sa

Kaka kuwa da Baffa ba'a magana a kan jikin su, gwara-gwara Kaka yana iya farka wa amma dai da oxygen yake numfashi.

      Jikin Fadila da sauki shiyasa ana sallaman ta Big Dady yace "su koma da ita gida".

K.B ya wuce da ita, duk da tana ta kuka a kan "baza ta je ba".

                An yi zaman makoki duk da babu gawan su, an yi musu zaman makoki har kwana bakwai aka yi addu'a, sannan kowa ya watse, su kuma su Kaka suna asibiti ana ci gaba da kula da su.

     Alhmadulillah ana samun sauƙi daga Kaka, tunda yanzu har yana iya magana, jikin sa da sauki sosai, sai dai Baffa ne jiya iyau, har yanzu tunda aka kai shi be farfaɗo ba.


⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

         Da sannu da sannu Usman ya saba da rayuwar ƙauyen nan da ya tsinci kansa a ciki, tun ba ya sakin jiki da Baba Jaure har dai yanzu sun saba sosai, ya kan gaji da zama a cikin ɗaki har ya fita wajen gidan ya sha iska, ya riƙa kallon mutanen garin da zirga-zirgan su, duk da ya ƙi sakin jiki sosai da su illa Baba Jaure, don wani lokacin har jeji yana raka shi, amma be cika zuwa sosai ba, babu abinda ke faɗo masa a rai illa Ɗahira, ya kan ji hankalin sa be kwanta ba duk idan zai yi nesa da gidan, sai yaji kamar wani abun zai same ta, shiyasa sai idan ya gaji sosai ne yake iya bin Baba Jaure cikin jejin

Ya zama abun kallo ga mutanen ƙauyen, duk da ba wasu mutane ne da yawa ba, ba samarin ba ba ƴan matan ba kowa so yake yi ace ga shi yana mu'amala da Usman, sai dai ya ƙi sakin musu fuska, wasu samarin idan har suka ganshi a waje har zuwa suke yi su zauna wai "sun zo taya shi hira," ga su da shegen surutu dole sai sun yi mu'amala dashi kamar wasu mayu, duk da wulaƙanta su da yake yi, don idan suka soma mishi zuba ko ci kansu ba ya ce musu, ko abin dariya suka yi sai dai ya kawar da kansa idan yana jin dariyan, daƙyar yake iya murmushi wanda basu san ma yana yi ba, iya kanshi dasu gaisuwa da amsa sallama, su da farko ma abin mamaki yake ba su, ayi mutum ba ya magana ba ya dariya, amma kuma dayake iyayen naci ne dasu sun ga ɗan birni zubin ƙetare, su hakan ma daɗi yake musu tunda sun zauna dashi

Su kuwa ƴan matan ma ko kallo basu ishe shi ba, idan za su wuce sau dubu su gaishe shi ba ya kallon inda suke, amma gobe idan sun ganshi a wurin baza su fasa gaishe shi ba, shiyasa yanzu ma ya rage fita, sai dai yayi zaman shi a cikin gidan wajen Baba Jaure yana kafa mishi idanu yana aiki.

     Abin mamaki tunda Baba Jaure yace mishi ya riƙa shafa wa Ɗahira magani yana bata na shan, be yi masa musu ba, shi yake bata kullum yana kula da ita, wani lokacin ma har yana ɗan wanke mata jiki da tsumma, shi kansa abinda yake yi wlh mamaki yake ba shi tsantsa, be san meyasa ba yanzu kwata-kwata ba ya jin tsanar ta kamar da, hasali ma zallan tausayin ta yake ji

Be san cewa tuni asirin dake tasiri a jikin su an karya musu ba, tsanar da aka saka mishi na Ɗahira tuni Baba Jaure ya karya sihirin, kuma har yanzu be fasa basu na tsari ba, sai dai shi Usman ɗin duk a tunanin shi magungunan raunukan da suka ji ne.



          ***** ****** *******

        Yau ma kamar kullum shi da kanshi yaje ya ɗauko maganin ya soma shafa mata, dayake Baba Jaure ya fice zuwa jeji tun ɗazu, yana yi yana kallon fuskar ta da be gajiya da kallo, har ya rame fuskar nata sosai ko da gani ka san tayi jinya

Motsi yaga kamar tana yi sai ya tsaya yana bin ta da kallo, sai kuma cikin sauri ya soma kiran sunan  ta a hankali yana faɗin, "Nafeesa.. Nafeesa".


Kamar daga sama take jin muryan, wanda daƙyar ta iya motsa hannayen ta jin ƙafafuwan ta sun riƙe sosai ta gaza motsa su, sai kuma ta soma juya kanta a hankali

Ganin haka yayi saurin saka hannun sa yana riƙe nata, ya ci gaba da kiran sunan ta a zaƙe da son ganin ta buɗe idanu, sosai yaji wani irin farin ciki ya tabaibaye shi dashi kanshi be san na mene ne ba, yau har so yake yi yaga waɗannan idanuwan nata masu ba shi tsoro da fargaba, sunan ta ya sake kira yana matsa mata hannun ta da ya riƙe gam a cikin nasa

Idanun ta ta soma buɗe wa a hankali tana sake rufe su, a haka har ta ɗan buɗe su kaɗan tana ganin dishi-dishi, tayi kamar mintuna biyu ba ta iya ganin komi, kafin kuma ganin nata ya soma dawowa, ta soma gane abinda ke cikin ɗakin, kana kuma ta sauke idanun ta a kansa, wanda sai da ta sake rufe idanun ko gizau yake mata, kafin kuma ta sake wartsake su a kanshi, kallon kallo kawai suke ma juna yayinda ta tsayar da idanun ta a kanshi ƙyam

Shi kuwa fuskar shi yalwace da murmushin da ya daɗe be yi ba yake kallon ta, don ya ma kasa yin magana

Wani irin zabura tayi lokaci ɗaya tamkar mahaukaciya tana yanka ihu, ihu sosai take yi tuni ta ɗage ƙafafuwan ta tana son tashi da gudu

Hakan da ya gani ne tuni hankalin sa ya tashi, nan ya saka hannu yana riƙe ta yana faɗa mata "ta tsaya".

Amma ina ihu kawai take yi sosai hawaye tuni sun yi mata caɓe-caɓe saboda azaban da ya ziyarce ta, sai a lokacin ma tabi ƙafafun nata da kallo, ai nan ta sake haukace wa a kuka, ga shi jikin ta babu ƙarfi amma yanda ka san mahaukaciya haka take son fizge jikin ta a jikin sa

Shi duk a tunanin sa haukan ne ya same ta, shiyasa lokaci ɗaya ya ruɗe ya riƙe ta gam yana faman kiran sunan ta da faɗin "ta natsu don Allah". Shi ba komi yake jin mata ba illa ɗaurin dake ƙafafun ta kar ta goce.

    A lokacin ne Baba Jaure ya shigo da saurin sa, domin ihun nata ne ya jiyo tun daga wajen ya taho da saurin, shima ya ruɗe sosai ganin yanda take yi, saurin saka hannu yayi ya riƙe ta yana faɗin, "dakata mana ƴar nan, me kike yi haka? Ki zauna don Allah kin ga akwai karaya a ƙafafuwan ki".

Amma ina azaba ya hana ta jin kalaman Baba Jaure, duk da ta dena motsi da ƙafafun, amma kukan ta sai ƙaruwa yake yi har da su majinu

Baba Jaure duba ƙafan yayi yaga dole sai an sake sabon ɗauri, cike da tausayin ta yace, "amma me ya faru ne da ta tashi a firgice haka? Ka ga dole sai an sake sabon ɗauri".


Usman be iya cewa komi ba, shi dai yana riƙe da ita da tayi lagwab kanta a jikin sa sai kuka take yi sosai

"Yanzu je ɗauko min wani magani a ɗaki na yana nan a kwalba ka kawo min". Baba Jauren yace dashi yana kallon sa

Tashi Usman yayi yana aza kanta a saman shimfiɗan da take kai, yayi saurin fice wa

Shi kuma Baba Jaure sai bata baki yake yi duk da ba ta fahimtar sa, azaba da zugin ciwo ya hana ta saƙat, riƙe mata ƙafafun yayi don kar ta motsa duk da tana son ƙwace wa

Bayan Usman ya dawo da maganin ya miƙa wa Baba Jaure

Shi kuma ya amsa yana taɓa ƙafan ɗaya wanda ya san shi ne ya goce

Sai ta yanka ihu tana janye ƙafan, tana faman girgiza kai da son magana amma ina ta kasa

"Kai Usman sai dai ka riƙe min ita a sake sabon ɗauri, idan ba haka ba ƙafan nata zai yi tsami da yawa".

Gyaɗa kai Usman yayi kamar ƙadangare, ya duƙa ya riƙo mata hannaye gam ya ɗaura kan ta a jikin sa

Duk yanda taso ta ƙwace amma ina ta kasa, azaban da ya sake ziyartan ta tuni ta buɗe baki tana roƙon Baba Jaure yayi mata rai, kuka sosai take har da majinu yayinda ta koma kiran sunan Usman tana roƙon sa "ya taimake ta".

Usman har sai da yayi mata ƙwalla tsaban tausayin ta, shi kansa be san ma yayi ba

Shi kuwa Baba Jaure ya ƙufe sai da ya gama gyaran tas kafin ya ƙyale ta, sannan ya kalle ta yace, "sannu baiwar Allah, kiyi haƙuri kinji? Kuma kar ki sake motsa ƙafafuwan nan tunda kin ga wahalan da kika sha, muddin kika sake gotar wa dole a sake sabon ɗauri idan ba so kike yi ki dauwama a karye ba. Allah ya ƙara lafiya kiyi haƙuri".



Ɗahira wanda tasha azaba tayi sharkaf da zufa, inda majinu da hawaye suka yi mata caɓe-caɓe a fuska, fuskar nan tayi jazur kamar tattasai tsaban wahala, yanzun ma gunjin kuka take yi sosai ta lafe kanta a jikin Usman sai faman sakin numfashi take yi

Shi kuwa Usman ƙam ya riƙe ta yana shafa mata kan alamun rarrashi, ya kasa cewa komi illa tsaban tausayin ta dake cin sa a rai, ji yake yi kamar ya mayar da ciwon jikin sa, sosai yake jin tausayin ta na tsarga masa ta ko ina a jikin sa, yana bin jiki da ɓargon sa, wanda har ji yake yi tsigan jikin sa na tashi.



     Baba Jaure tashi yayi ya fita, sai ga shi ya dawo da fura cikin kwanon sha, ya miƙa wa Usman yace, "ga shi ka bata Idan zata iya sha, ki daure kinji ki sha".


Amsar kwanon Usman yayi

Baba Jaure ya fice a ɗakin

Shiru yayi yana tunanin yanda zai iya lallaɓa ta tasha maganin, kamar mintuna biyar da fitan Baba Jaure sai ya saka hannu ya mirgino kanta yana kiran sunan ta a hankali kamar wanda ke raɗa


Bata amsa mishi ba domin idanun ta ma a rufe suke ruf, hawaye sai sake tsiyaya suke yi, sai ta mayar da kanta ƙasa ta kwantar tana ci gaba da shashsheƙan kuka

Sake kiran sunan ta yayi yana cewa "ta tashi tasha furan".


Duk yanda yaso tayi magana ko ta buɗe idanun ta amma ta ƙi

Ko kaɗan ba ta ƙaunar ta sake tozali da fuskar sa, Da ya san abinda take ji a game dashi da be kusanto inda take ba, da ya san yanda muryan sa ke sauka cikin kunnen ta yana sake ƙara mata wutar tsanar sa da haushin sa da be ci gaba da mata magana ba, da ace zata iya yin magana a yanzu ɗin da ta faɗa masa "ta tsane sa fiye da kowa a duniyar nan! ba ta son ganin sa ba ta son taimakon sa, shi be da wani amfani a duniyar ta," zata faɗa mishi "dashi da dabba a wajen ta ɗaya suke". Sai dai kuma ina baza ta iya ba, baza ta iya buɗe ido ta kalle sa, duk azaban da take ji kaɗan ne da yanda take ji a zuciyar ta, sosai zuciyar ta take tafarfasa tsaban tsanar da take mishi.



     Usman tashi yayi ganin taƙi kula shi, sai ya kai ma Baba Jaure yace mishi "taƙi sha".

Baba Jaure ya dawo ɗakin da furan, sai ya bar Usman a can waje. Zama yayi yana cewa, "ɗiya ta".

Sai a lokacin Ɗahira ta buɗe idanuwan ta da suka kaɗa suka yi jawur

"Kar ki sake gardama idan na baki abu kinji? Lafiyar ki ake nema miki, idan babu abinci baza ki samu sauƙi ba, yau kimanin wata ɗaya kenan kina a wani hali baki farfaɗo ba sai yanzu, mijin ki ya damu ƙwarai, ki daure ki samu lafiya ko shima hankalin sa zai kwanta, bari in Kira shi ya baki".


Cikin muryan kuka tace, "a'a don Allah Baba Kar ka kira shi, wlh mutuwa zan yi, ba na ƙaunar taimakon shi idan har shi zai taimake Ni, shi ba miji na bane". Sai ta fashe da kuka me tsuma rai, da ya san yanda kalman mijin ta ya bugi zuciyar ta; da ko da wasa bazai sake ambata mata ba

Baba Jaure cike da mamaki yace, "ba mijin ki bane? Amma ya ce min shi mijin ki ne?"
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




        *EPISODE Fifty Six*



        "Shi ba miji na bane, bani da alaƙa dashi". Tayi maganar cikin kuka



"To ya isa haka, bar kukan kinji kar ki saka wa kanki wani ciwon, bari in taimaka miki ki sha furan".



Gyaɗa masa kai kawai tayi tana faman sauke ajiyan zuciya akai-akai



Kallon ta kawai yake yi cike da tausayin ta, sai ya gyara mata kanta ya ɗan ɗago ya saka mata matashi, sai da ya bata ruwa ta kuskure bakin ta kafin ya hau kafa mata furan tana sha


Duk azaban ciwo ya ishe ta shiyasa kaɗan tasha tace masa, "ya ishe ta".


Dole ya ƙyale ta be matsa mata ba, sannan ya bata wani magani tasha ya mayar da ita ta kwanta sosai, yace mata, "ta kwanta tayi barci ko zata samu hutu".


Bata ce mishi komi ba har ya fita, sai ta mayar da idanun ta ta rufe har yanzu sai faman ajiyan zuciya take saki, fuskar ta tayi jazur da ita sai hawaye dake kwance sun bushe mata.







              **********

      Baba Jaure kuma da ya fita a can gefe ya ga Usman ya zauna ya haɗa kai da gwiwa, kallon sa kawai yayi sai ya kawar da kansa, be ce mishi komi ba duk da yana son mishi tambayoyi, amma ya bari zuwa lokacin da Ɗahira zata samu nutsuwa hakan zai fi mishi. Ɗaki ya shige abin shi



Shi kuwa Usman be ma san da fitowar sa ba, illa tunani da ya faɗa hankalin sa na ga Ɗahira, zuciyar shi na matsa mishi da tunanin ta amma shi yana son kauce wa, sosai yake ƙaunar taimaka mata saboda tausayin ta da yake yi, ya san ba don ciwon dake jikin ta ba ba ya jin zai ji abinda yake ji a kanta, shiyasa duk wani tunanin da yake nata ya barshi ne a kan TAUSAYI kawai, kuma da zaran komi ya wuce zai dena matsa wa kansa



Sai a lokacin ya ɗago kai yana kallon Baba Jaure da ya fito daga ɗakin sa, sai yayi saurin tashi idanun sa a kansa yace, "ta sha furan Baba?"



Murmushi yayi masa yace, "eh na bata ta sha, amma yanzu na san ƙila tayi barci".



Yana ganin yanda Usman ɗin ya saki ajiyan zuciya har da lumshe idanu, sai yace mishi, "zai fita yaje ya dawo".


Har Baba Jaure ya fice be ce mishi komi ba, koma wa yayi ya zauna yana ci gaba da tunanin sa, gaba ɗaya zuciyar sa ta matsa mishi yaje ya duba ta, ko da fuskar ta ne ya kalla but ya daure ya ƙi zuwa. A nan ya zauna har sanda Baba Jaure ya dawo



Sai yace mishi, "daga yau zaka fara kwana a wancan bukkan kaji?"


Da kallo ya bi shi be iya ce mishi komi ba, sai dai mamaki da ya cika sa


Shi kuma Baba Jaure ya gane sarai yana son ƙarin bayani, amma ya ƙi sake ce mishi wani abun, idan ba tambayar sa yayi da bakin sa ba shi kuma bazai tanka sa ba, sai ya wuce abin sa ya bar shi.




        Har aka kira sallan magriba Usman na zaune a wurin be jirga ba, sai daga baya ya tashi ya ɗauki mazubin ruwa yayi alwala ya fita zuwa Masallaci


Baba Jaure tuni shi ya fice ma, tunda dama shi ne liman.






       Bayan an idar da sallah ya koma gida, kai tsaye ɗakin da Ɗahira take ya wuce, da sallama a bakin sa wanda shi kaɗai yaji kayan sa ya shiga ciki


Idanun ta biyu amma suna lumshe, motsin da taji yasa ta buɗe su a kanshi, sai suka shige cikin nasa


Da sauri ya janye nashi idanun saboda yanda yaji gaban sa yayi muguwar faɗi tamkar zai fito waje, har yana runtse idanu


Sai da ta sakar mishi wani banzan kallo da be san ma tana yi ba kafin ta ɗauke nata idanun, ta mayar dasu ta rufe ruf


Dauriya ya aza wa kansa ya sake kallon ta, ganin idanun ta a rufe sai ya taka a hankali ya shiga ciki ya zauna a gefen ta, shiru ne ya biyo bayan zaman nashi be ce uffan ba illa kallon ta da yake faman yi


Har a cikin jikin ta tana jin irin kallon da yake mata, wanda har ta kasa jure wa ta buɗe idanuwan ta a kansa tana mishi wani kallon da ya kasa fassara wa


Sai dai ba kaɗan ba kallon ya shige sa ainun, sai ya janye nashi idanun ba tare da ya ɗauke su a kan fuskar ta ba, cikin cool voice da be taɓa sanin yana dashi ba yace, "zaki yi sallah ne sai in taimaka miki".



Shiru babu amsa



Sai ya kalle ta yaga har yanzu idanun ta na kanshi tana mishi wannan banzan kallon da ya kasa gane kallon mene ne, sai dai kuma yanda ya daure ya kasa cire nashi idanun a kanta, tuni ya gane kallon tsantsan tsana ne, sake maimaita abinda ya faɗa mata yayi ba tare da ya ɗauke idon sa a kanta ba



Rufe idanun ta kawai tayi kafin tace, "ba na buƙatar taimakon ka har abada, Please ka taimaka ka tashi min a nan wurin saboda kana cutar dani da yawa".


Yanda ka san gunki haka Usman ya koma a wurin, ya gaza ina zai saka kalaman ta bare yayi musu filla-filla ya gane me take nufi, sai dai juya su da yake yi amma kuma ya gaza tunani ƙwaƙƙwara, sai dai zuciyar sa na cike da mamaki tsantsa


Tsawon lokaci yana wurin be iya jirga wa ba, kuma be tashi ya fita ba, amma idanun sa har yanzu suna kafe a kan fuskar ta


Sai ta ware nata idanun a kanshi cike da baƙin cikin kallon da yake mata tace, "dalla ka tashi ka bani wuri a nan, na ce maka ba na buƙatar taimakon ka, wlh gwara na ruɓe a nan da ka taimaka min".


Da yatsa ya nuna kanshi yace, "Ni kike faɗa wa haka Nafeesa?"


Wani irin juya idanu tayi cike da harzuƙa kuka na son kufce mata tace, "who you are?" Na faɗa idan ka so kar ka bar Ni da rai kaji ko?".


Shi sosai kalaman ta suka bashi mamaki shiyasa yaji sa wani iri wanda ya kasa taɓuka komi, jin sa yake yi komi nasa yayi sanyi, memakon kalaman ta su sanya shi baƙin ciki sosai kamar yanda a baya suke saka shi, sai dai kuma wannan karon ko kaɗan ba haka ba, duk da yaji zafin kalaman ta, amma yana ganin ya ƙi mata wani abun ne domin ganin ta cikin lalura, amma da ba don

Please Login or Register in order to submit comment