Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

runtsa a gidan nan sabida tashin hankali, kowa tunanin yanda mutane biyu aka rasa su a lokaci ɗaya, sai kuma duk tunanin su Big Dady suka koma kan "ko dai Usman ne ya ɗauke ta suka koma can Turkay ɗin?" Wannan tunanin yasa Big Dady safiyar Allah na yi yace, "zai je domin yaci uban sa a can, wlh idan har da gaske ne tunanin nan nasu Usman ya kaɗe a wurin shi," sosai ransa ya ɓaci sai faɗa yake yi


Ganin haka yasa Kaka yace, "kar yaje, Baffa yaje shi ya gano musu".


Wannan dalilin ne yasa Baffa ya shirya aka nema masa jirgi na ƙarfe 10:00am a ranan ya wuce TURKEY.






⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫


          Duk yanda ya so ya buɗe ƙofan motan ya fice ya kasa, har sai da motan ta gama nitsewa zuwa ƙasa, kokuwa yayi ta yi amma ya gaza, ba don Allah yasa ya iya ruwa ba da tuni babu numfashin sa, amma duk da haka yanayin awannin da suka ɗauka a haka cikin motan babu jan numfashi bare iska sai duk ya galabaita, ya rasa ya zai yi har numfashin sa ɗauke wa yake yi kamar zai shiɗe


daƙyar da siɗin goshi ya samu ya buɗe ƙofan motan, har zai fice ya tuna da ita, nan ya dawo ya janyo ta suka fito daga cikin motan, sai dai yanda ake tsula ruwa ya kasa yanda zai yi ma yayi iyo, take a Nan ruwan yayi gaba dasu saboda yanda ruwan yake gudu sosai, ta cikin gadan wajen yabi dasu yay gaba dasu, dayake wajen makwararan ruwa ne na sassa-sassa dake tafiya ya isa babban kogin dake can wani yankin jeji dake cikin Kadunan.


      Tun Usman na sanin halin da yake ciki, har shima numfashin sa ya ɗauke gaba ɗaya


Ita kuwa Ɗahira har yanzu bata farka ba ma bare tasan inda take.


      A haka har garin Allah ya waye, inda wajen hantsi wani Tsohon Mutum yazo gaɓar ruwa zai ɗiba ruwan a tulu, a nan ya tsince su tamkar matattu ruwa ya fito da su bakin gaɓar ruwan, sosai hankalin tsohon nan ya tashi, nan ya nufe su cike da mamakin ganin su, sai da ya gama taɓa su ya tabbatar da tabbas suna da rai, sannan ne ya koma cikin ɗan ƙaramin ƙauyen nasu, ya kira wasu samari suka zo suka taimaka masa ya kai su gidan shi, aka zube su cikin ɗaya daga cikin bukkan gidan


Duk mutanen ƙauyen sun fito sun nufi gidan Tsohon nan me Suna Baba Jaure suna ganin ikon Allah wajen su Usman, sun zame musu kamar t.v, duk da ba wai bambanci ne dasu ba, sai dai su sun kasance ƙauyawa ne futuk makiyaya, kuma garin ɗan ƙarami ne a tsakiyar ruwa take, sannan kuma da jeji a kewaye dasu, Baba Jaure shi ne babba a cikin ƙauyen, kuma shi ne me faɗa aji, tsoho ne sosai kuma be da iyali.


    Sai da Baba Jaure ya kore su saboda sun cika mishi gida sun hana shi ya duba su, sannan ne suka fita suka bar shi, shi kuma nan ya soma bincika su dayake shi masanin magunguna ne, duk sai da ya gama duba su ya gano raunukan da suka ji, kuma da alamu sun sha ruwa sosai domin daƙyar ma ake iya gane suna numfashi


Ita Ɗahira ta sami karaya a duka ƙafafuwan ta, tare da rauni a ƙafan ta na dama


Shi kuma Usman ciwuka kawai yaji, da alama shi be sha wahala kamar ta ba, sai dai tafin hannun sa na dama ta kwaye kamar dai cizon wani dabba haka, tunda har rami tayi, sai kuma a goshin sa nan ma yaji rauni.




    Sai da ya gama duba su kafin ya shiga rumbin ajiye magungunan sa, ya haɗo wanda zai yi musu amfani da shi, nan ya jiƙa na jiƙa wa wasu kuma ya niƙa su da turmi, sannan ya saka musu a ciwon, yayi wa Ɗahira ɗaurin karayan ta, shi kansa sai da ya tausaya mata, domin ba ƙaramin karaya bane taji, da ace idanun ta biyu azaban da zata sha Allah kaɗai zai sani, sai dai har ya gama ko alamun motsi bata yi ba, hakan ya ƙara tabbatar mishi tana cikin wani yanayi wanda farfaɗoWar ta sai Allah ya yi, domin ita ko numfashin ma ba ta yi sai da ya taɓa hannun ta yake ganin jijiya na harba wa.







⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫


      Baffa ya je can Turkay ya dawo musu da labari mara daɗi a kan basu je can ba, wannan labarin ya sake ɗaga musu hankali matuƙa, bare da suka ga kwanaki nata tafiya babu labarin su, yau ga shi kusan kwana shida babu su babu wani bayani daga bakin ƴan sanda


Tuni Aunty Amarya da Kaka sun kasa jure wa sun zube an kai su asibiti, yanzu haka an kasa samun kansu, domin tunda suka sume basu farfaɗo ba, duk wani taimako an basu amma an kasa shawo kansu


Ita kuma Hajiya na gida sai faman kuka take yi, ko abinci ta dena ci saboda halin da take ciki


Bazan iya misalta muku halin da waɗannan bayin Allan suke ciki ba, haƙiƙa sun ga iftila'i a cikin ƙanƙanin lokaci, ɓacewar mutane biyu, ga kuma halin da su Kaka suke ciki, domin shi Kaka ma numfashi ba ya yi a halin yanzu sai da oxygen


Tuni ƴan uwa dangi na nesa dana kusa labari ya kai musu duk sun zo, har Fadila da take cikin halin lalura sai da aka zo da ita, duk da cikin ta yanzu har ya soma girma amma kullum ciwo kamar yanzu ta samu cikin, duk ta rame abun tausayi, yanzu tana lafiya, anjima sai aga jikin nata ya rikiɗe an tafi da ita asibiti, an rasa dai me ke damun ta, likitoci sun ce ita nata cikin haka yake, zuwan nasu ma sai da aka yi mata ƙarin ruwa saboda rigigim ta kwanta ciwo, duk da rashin ganin su Ɗahira ne ya yi matuƙar ɗaga mata hankali, sai kuka take yi, daga nan kuma sai jikin ya rikice.


      Halin da ahalin nan suka shiga sai innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, abin tausayi idan ka gansu.


       Ƴan sanda sun je har asibiti sun yi bincike, dayake akwai ccTV Camera a asibitin, sun duba kuma sun ga tabbas a ranan Ɗahira ta bar asibitin a cikin motan ta, Dr. Said ne mutum na ƙarshe da ta zanta dashi a haraban Hospital ɗin, daga nan ta hau motan ta ta fice


A lokacin shi kuma murmushi yayi yana bin motan nata da kallo har ta fice, kana ya zaro waya yayi waya, duk da ba sa jin abinda yake cewa amma duk rashin gaskiya ya nuna a tare da shi, sai kuma suka ga ya shiga tashi motan ya fice.


     Wannan dalilin ne yasa aka je neman Dr. Said amma ba'a ganshi ba, domin tun ranan da abin ya faru be sake zuwa asibitin ba, hakan ya ƙara ɗarsa zargi daga zukatan ƴan sandan. Sai suka je har Zaria suka cafke shege, da yasha matsa sai ga shi ya faɗi gaskiya


An sha wahala kafin aka kamo sauran mutanen da suka yi aikin tare da taimakon Dr. Sabo tunda shi ne ya sanar musu inda suke, sun yi bayanin komi da ya faru a ranan da suka ɗauki Ɗahira, har wanda ya zo ya taimake ta da kuma faɗa wa ruwa da suka yi


A nan ne aka gane Usman ne tunda sun yi bayanin motan nashi, kuma zahiri shi ne.


        Koda aka je wajen an yi duk wani bincike tsawon kwana da kwanaki, amma motan su kawai aka gani a cikin ruwan, inda suka tabbatar dole su Usman sun rigada sun mutu a ruwan, tunda babban makwararan ruwa ne dake tafiya wani ƙaton tafkin kogi, daga can ma akwai yanki-yankin ruwa dake da alaƙa da wajen, takamaime dai baza a gane inda suke ba a cikin ruwan nan, duk wanda ya faɗa kuwa sai dai mutuwa ne bazai iya fitowa ba


    Wannan bayanin da ƴan sanda suka yiwa su Big Dady sun sake ɗaga musu hankali, domin har kuka sai da suka yi sosai a wannan gaɓar, shikenan an rasa su sun mutu. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Mutuwar da ya girgiza ahalin gaba ɗaya, wanda sanadin haka ne Fadila tayi ɓarin cikin ta lokaci ɗaya, shi kuwa Baffa ranga-ranga aka wuce dashi asibiti yana aman jini, ga su Kaka su ma dake asibitin har yanzu ba'a sallame su ba, ita dai Aunty Amarya ta farka, amma da jin wannan bayanin sai ta sake zube wa a sume, dole aka koma basu taimakon gaggawa, su kansu su Abba sun kasa taɓuka musu komi, su ma suna ji da kansu.


         Su Dr. Said kuwa suna hannu za su girbi abinda suka aikata, domin har an miƙa su kotu babu ɓata lokaci.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




        *EPISODE Fifty Four*

         A Waɗannan kwanakin da su Usman suka yi a wannan ƙauyen, har yanzu suna a yanda suke basu farfaɗo ba, Baba Jaure na ci gaba da kula dasu sosai yana musu magani, inda tuni ya gano suna tare da sihiri gaba ɗayan su biyun, tunda shi mutum ne me saurin gane sihiri, kasancewar sa wanda yayi gwagwarmaya da aljanu, tun farko su suka buɗe mishi idanu har yake bayar da magunguna, sai ya tafi jeji yayi kwana da kwanaki yana haɗo magunguna, shiyasa duk ƙauyen nasu shi ke basu magani, tamkar shi ne likitan su, kuma shi ne kariyan su har suka kasance a cikin ta har yanzu

Wannan dalilin ne yasa yake haɗa musu wasu maganin na karya sihiri yana shafa musu a jiki, dayake akwai nasha sai ya riƙa zuba musu a baki, duk da yana zube wa amma ya san wasu suna shiga cikin nasu.

     Ana haka Usman ya farfaɗo ya tsinci kansa a wannan yanayin da ya kasa banbance a cikin duniya yake ko a maƙabarta? Wurwurga ido kawai yake yi yana zare su a cikin ɗan ƙaramin bukkan da suke kwance, nan idanun sa suka faɗa kan Ɗahira dake kwance tamkar matacciya, da kallo ya bi ta da shi ko ƙyafta wa ba ya yi, yana son tuna me ya faru har yake kwance a nan kusa da ita, be gama dawowa tunanin shi ba yaji motsi a waje, ƙofan yabi da kallo

A lokacin ne Baba Jaure ya shigo da wani kwanon sha a hannun shi, shima ganin Usman zaune sai hakan ya saka shi farin ciki, nan da nan ya yalwata fuskar shi da murmushi yana me ƙarisowa kusa dashi tare da mishi sannu

Amma yanda ka san gunki haka Usman yake bin shi da ido, ko motsi ya gaza yi illa idanun sa da suke juya wa

"Yaro ka kwantar da hankalin ka kaji? Ba cutar da kai zan yi ba, alhmadulillah tunda ka tashi. amshi wannan ka sha". Ya miƙo masa kwanon shan hannun sa

Usman be motsa ba bare ya amsa, a lokacin tunanin sa ya dawo duk ya tuna abinda ya faru, sai kawai yayi saurin saka hannun sa a kanshi yana shafa wa, sai da ya taɓa ɗin yaji zafi ya ratsa shi, yayi saurin janye wa yana bin hannun shi da kallo, lokaci ɗaya ya ruɗe cikin tashin hankali ya kalli Baba Jaure yace, "ina ne nan don Allah? Me ya faru damu ne?"

Baba Jaure be ce komi ba sai da ya zauna yace, "kayi haƙuri ka kwantar da hankalin ka sai in Yi maka bayani".

Shiru Usman yayi yana bin hannun sa da kallo, yanda duk aka barbaɗa mishi wani baƙin abu da babu kyan gani, dashi aka cike ramin da hannun sa yayi, sosai yake jin azaba na ratsa shi har ruwan hawaye ne ke cika mishi idanu, sai dai kuma dauriya irin nashi bazai iya kuka ba, amma sosai yake jin azaba. Da kallo kawai yabi Ɗahira dashi yana kallon ƙafafuwan ta da suke a ɗaure alamun sun karye, shiru kawai yayi ya gaza ɗauke idanunsa a kanta, lokaci ɗaya yaji hawayen dake idanun sa sun zubo, sai yayi saurin kawar da kansa yana saka ɗaya hannun sa ya share

Baba Jaure dai duk yana kallon sa be sake ce mishi komi ba, amma tausayin sa ne sosai a ransa, a lokacin sai yace, "yau kwanan ku goma a waje na sai yanzu da ka samu kai ka farfaɗo, na tsince ku a gefen kogi ne cikin mawuyacin hali, wanda ita ƴar uwan taka ta samu karaya a duka ƙafafuwan ta sai raunuka. kai kuma ka samu ciwo a kanka da hannun ka". Shiru yayi

Usman dake bin shi da kallo tun soma maganar nasa yace, "amma ina ne nan don Allah?".

Murmushi Baba Jaure yayi yace, "kar ka damu zaka sani, nan wani yanki ne dake cikin jeji, kuma zagaye muke a ruwa".

Duk da Usman yana son sake mishi magana amma ya kasa buɗe baki yayi, illa hannun sa da yake tabi da kallo yana cike da raɗaɗin azaba

Ganin yayi shiru be ce komi ba sai yace, "ga magani ka sha".

Still shiru Usman yayi kuma be ɗago ya kalle sa ba

Sai shima be sake cewa komi ba illa tashi da yayi ya koma gefen Ɗahira, a nan ya ɗibi maganin a cikin tafin hannun sa yana zuba mata a baki

Da kallo kawai Usman yake bin shi dashi yana yamutsa fuska, har ya gama yaga ya soma shafa mata magani a raunukan ta

Sai da ya gama yace mishi, "ka sha maganin nan, shi zai taimaka maka wajen rage raɗaɗin da kake ji, kaji ko?"

Gyaɗa kansa Usman yayi, ya amshi maganin ya kafa kai ya sha

Baba Jaure fita yayi, sai ga shi ya sake dawowa da wani kwanon, ya miƙa mishi ya sake ba shi umarnin yasha

Hakan kuwa yayi ya amsa yasha, wannan duk ɗaci amma be ce komi ba har ya gama sha

Sai ya sake fita, zuwa can ya dawo mishi da fura ya bashi

Usman amsa yayi ya kafa kai ya shanye domin yana buƙata

Sai da ya gama Baba Jaure yace mishi "zai fita zuwa jeji, bazai daɗe ba zai dawo".

Shi dai Usman be ce mishi komi ba har ya fice, kana ya mayar da idanun sa kan Ɗahira, kallon ta kawai yake yi kamar ya sami t.v, abinda tunda yake be taɓa mata ko kallon second uku bane, a ƙasan zuciyar shi yana jin wani abu na taso mishi me kama da tausayi, ita yake tausayi ko kuma kanshi yake tausayi ya kasa sani, sai ya ɗauke kai kawai yana mayarwa kan hannun shi, duk idan ya kalli yanda hannun nasa yayi rami sai kawai yaji hawaye suna son cika mishi idanu, "kenan nashi azaban nafila ne a kan yanda ita take ji? Ko ya ya take ji?" Ya yiwa kansa tambayar yana me sake mayar da idanun sa kanta

Kamar zata yi magana haka fuskar ta tayi, sai dai kuma babu inda nata yake motsi, har ta numfashin ma ba ya ganin tana yi

Sai yayi saurin kai hannun sa mara ciwon ya tsinci kansa da aza shi saman ƙirjin ta, memakon yaji bugun zuciyar ta, sai nashi ne tayi wani irin buga wa sabida saukar hannun sa a saman ƙirjin ta. Saurin janye hannun nasa yayi yana ɗaura wa a kan nasa ƙirjin, lokaci ɗaya ya lumshe idanun sa yana me ci je leɓen ƙasan bakin sa, sosai yake jin bugun zuciya wanda yaja tsawon lokaci a haka ya kasa taɓuka komi, so yake yi ya sake ɗaura hannun sa don yaji bugun numfashin ta, domin be ji komi ba sanda ya saka, amma kuma tsoro ya hana shi mayar wa, haka kawai yanayin da yake ji a jikin sa yasa ya kasa buɗe ido bare ya mayar da hannun sa a ƙirjin ta

Tsawon mintuna biyar kafin ya buɗe ido yana bin ta da kallo, shiru kawai yayi shi be dena kallon ta ba; shi kuma be yi abinda yake ninyan yi ba. A haka har Baba Jaure ya dawo ɗakin, a nan ne ya samu kanshi da tambayar Baba Jaure, "ita yaushe zata tashi?"

Baba Jaure da ya sami wuri ya zauna yace, "gaskiya tana cikin wani hali sosai, ta fi ka shan wahala shiyasa zai yi wuya ta farfaɗo yanzu, sabida tasha ruwa da yawa, amma idan an dace tunda ina bata maganin da ya kamata tasha, insha Allahu zata tashi ba da jima wa ba, sai dai mun yi haƙuri".

Usman kallon sa yayi yace, "ina son mu koma gida saboda a bata taimakon gaggawa".

Baba Jaure yace, "yaro ba na tunanin za ku samu barin nan wajen a nan kusa".

"Meyasa?" Yayi masa tambayar har yanzu yana bin sa da kallo

Gyara zama sosai Baba Jaure yayi kana yace, "kamar yanda nace maka ne nan wani yanki ne dake cikin jeji, muna cikin tsakiyar ruwa ne gaba ɗaya ƙauyen namu, kuma gaskiya mutanen cikin ta ba sa fita idan har wannan lokacin ya yi, ma'ana lokacin damina ba ma iya fita zuwa cikin gari, sakamakon yanda ruwa ya tabaibaye mu, sai idan damina ya wuce shi ne hanya zata kafe har mu sami hanyar wuce wa, amma idan muka sake muka bi ta cikin ruwan a cikin kwale-kwale, to, mutuwa ake yi, Ni kaina nasha mamakin ganin ku kun fito daga cikin ruwan ba tare da kun rasa ranku ba, saboda gaskiya ruwan nan duk wanda ya faɗa ko ya sake ya shiga ciki, yana ji yana gani za'a janye shi a nemi gawan sa a rasa, wanda na tabbatar da cewa mutanen ruwa ne suke hana mu fita duk sanda aka ce damina yayi, dole duk wani zirga-zirga muna yin ta ne ba lokacin damina ba, zamu shiga cikin gari mu nemi duk abinda zamu iya buƙata, sabida ana fara ruwa mu da fita har sai damina ta ƙare, to ka ga kuwa fitan ku cikin garin nan sai bayan damina idan muna da rai Zaku yi ta zama har lokaci yayi".

Usman kasa ce mishi komi yayi sabida tashin hankalin dake tattare dashi

Baba Jaure yace, "amma ina son ka faɗa min abinda ya faru da ku har kuka tsinci kanku cikin wannan ruwan? Da kuma alaƙar dake tsakanin ku".

Usman samun kansa yayi da faɗa mishi gaskiya, ma'ana "ita matar shi ce wasu suka sace ta, shi ne ya biyo bayan su wannan tsautsayin ya faɗa musu," duk abinda ya faru dai sai da ya faɗa mishi

Jinjina kansa Baba Jaure yayi cike da zallan tausayin su yace, "haƙiƙa na tausaya muku, kuma Allah yasa da rabon zaku sake tsawon rai a gaba shiyasa har kuka samu kuɓuta. Allah ya kyauta gaba, sai kayi ta addu'a har sanda matar taka zata farka, amma mene ne sunan ka?"

"Usman". Ya sanar mishi a taƙaice

"Ita kuma fa?"

Sai da Usman ya ɗago kai ya kalle shi kafin tunanin shi ya kai ga Ɗahira, a hankali ya buɗe bakin shi yace, "NAFEESA". Sai ya samu kanshi kuma da maimaita sunan a ranshi

Baba Jaure dai fita yayi ya barshi a ɗakin

While shi kuma ya haɗa kanshi da ƙafafuwan shi sai ya hau faman tunani, tunanin kawai yanda zai iya rayuwa a nan yake yi, sai tunanin dangin shi suka faɗo mishi, lumshe idanun sa kawai yayi yana ta tunani cikin ranshi.





                   Tun ranan da ya farka ko ƙofar ɗaki ya ƙi fita bare ya ga yanayin garin, kullum be da aikin yi sai tunani da kallon Ɗahira, a kullum gani yake yi kamar zata yi magana ko kuma motsi, amma dai yanda take har yanzu haka take

Baba Jaure shi ke zuwa ya shafa musu magani, idan yazo yana jan Usman da hira amma shi komi ba ya iya ce mishi, sai dai ya riƙa sauraren shi

Yau ga shi kimanin kwana biyar kenan da farfaɗowar shi, ganin har yanzu Baba Jaure be ce mishi idan zai yi wanka ya fito ba, sai shi yayi masa maganar "yana son yayi wanka".

Baba Jaure yace masa, "idan zai iya to bari ya ɗumama mishi ruwan, dama yana jiye mishi ciwukan shi ne kar ya taɓa ruwa".

Bayan ya ɗumama mishi ruwan ya sanar mishi

Sai Usman ya tashi ya fito, da kallo kawai yake bin gidan, fili ne fetete da aka zagaye shi da kara, sai bukkoki kusan guda shida a jere har wanda suke ciki, sai kuma ɗaya dake can gefe ƙato, da alamu shi ne ban-ɗaki

Baba Jaure ya Yi masa nuni da wajen

Sai ya taka ya wuce ya shiga, tsaban ƙyamƙyami irin na Usman ya kasa yin wankan, duk da babu komi a bayin domin a tsaftace yake. Haka ya wanke fuskar shi da bakin shi, sai kuma ƙafafuwan shi ya watsar da ruwan ya fito, fuskar shi duk babu alamar fara'a, yana jin taya ya ma zai iya rayuwa a nan babu kulawa babu wanka

Baba Jaure da kallo ya bi shi dashi har ya shige bukkar, sai ya saki murmushi kawai yaci gaba da rubutun shi cikin allo, sosai ya gama kula da halin Usman, shiyasa be damu da wannan ɗaurewar fuskar nashi ba, domin tunda ya tashi be taɓa ganin haƙoran shi a waje ba, ko da kuwa magana zai yi ba ya buɗe baki sosai a ciki-ciki yake yi.




        Usman kuwa yana shiga mayar da kayan sa yayi zuciyar sa duk babu daɗi, sai yayi kwanciyan sa a gefen Ɗahira, yayi rigingine yana bin ta da kallo, yanda yake jin zuciyar sa da ya kalle ta sai ya ɗan samu sauƙi, sai kuma tunanin ta suka fara mishi yawo a zuciya, babu abinda yake tuna wa sai rayuwan da suka yi a can Turkay, da kuma abubuwan da yayi mata, sai kawai ya tsinci kansa da tambayar kansa "shin meyasa yayi mata wannan muguwar tsanar da har ya saka shi ya ƙuntata mata da yawa har haka? Anya shi ne kuwa?" Sai kuma wata zuciyar nasa tace, "to wa kake tunanin zai yi mata bayan kai? Ko ka manta tun sanda aka haife ta ka ɗaura mata karan tsana har zuwa kuwa wannan lokacin?" Sai ya lumshe idanun sa yana sake buɗe wa a kanta, a ransa ya furta "amma meyasa yanzu ba na jin tsanar nata sosai kamar yanda nake ji a zaman da muka yi a turkey?" Hasali ma yana jin wani irin tausayin ta ne a ƙasan ransa tare da nadamar abinda yayi mata

Saurin tashi yayi yana tankwashe ƙafafuwan sa, sai ya buga tagumi idanun sa a kanta, the more Yana tuna abubuwan da yayi mata the more Yana jin zuciyar sa na zafi, meyasa ya zama mugu mara tunani a wajen ta? Shi ya ma kasa tuna wani abu ne mummuna da tayi masa da har yayi mata mugun tsanar nan? Ya san dai tun sanda aka haife ta ya kalli cikin idanun ta, faɗuwar gaban da ya same shi tare da wani irin tsoro duk shi ne ya haddasa mishi tsanar ta, ko kaɗan ba ya ƙaunar ya ganta kusa dashi wannan dalilin ne yasa yake muzguna mata ko don ya rage haushin ta a zuciya, sosai ta hana ma rayuwar sa sukuni tun soma girman ta, shiyasa a lokacin da ya gama karatun shi na secondary School shi ya matsa wa Kaka dole ya tura su Turkay karatu shi da Baffa, ba don komi ba sai don nesanta kanshi da ita, sabida har a mafarkin sa zuwan mishi take yi, ba ta da aiki sai tsorata shi da waɗannan idanuwan nata, wanda yake ganin kamar da gayya take yi tunda ta san be son Kallon ta, shi har ya fara mata kallon aljana, sai dai kasancewar shi shima mugu ne shiyasa duk sanda ya same ta yake kiman ta, a cewar sa "ai ko ita aljana ce wlh sai ya rama abun da take mishi a mafarki," duk inda ya same ta duka ke haɗa su, har ya zamo idan ta ganshi ba ta iya zuwa wajen sai idan babu shi,

Please Login or Register in order to submit comment