Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

   A ɗakin kaka aka duba Ɗahira, sannan aka sanya mata drip, bisa umarnin Kaka, domin yace, "babu inda za'a matsa mishi da ita, a barta ya riƙa ganin ta ko zai samu kwanciyar hankali da raɗaɗin da yake ji a zuciya". Dole a ɗakin zata zauna, domin har alluran barci an yi mata domin samun hutu, tunda sun ga matsananciyar damuwar dake zuciyar ta na barazanar kawo matsala ga zuciyar ta, ga kuma ulcer da suka gano tana fama dashi, wanda ada bata dashi ko kaɗan

Hakan ya ƙara ɗaga wa su Big Dady hankali, haƙiƙa Usman ya cutar da ita, kuma tabbas maganar sa ya tabbata, tunda har ya ce "sai sun yi nadamar aura mishi ita da suka yi" to, tabbas yau sun yi matuƙar nadama, haɗin zumunci be amfana musu komi ba sai tsantsan nadama da dana-sani a rayuwa, haƙiƙa sun cutar da Ɗahira wanda ba sa jin za su iya yafe wa kan su har sai ita ce ta yafe musu, me ake yi da irin wannan auren na ƙaddara, sun ɗau duk wani laifi sun ɗaura wa kan su, duk wani abu su ne sila.

     Aunty Amarya ta kasa fita a ɗakin Kaka, ko kaɗan ta kasa jirga wa wajen ɗiyar ta, duk dauriyan ta, da kuma kawaicin ta yau ta gaza ɓoye abinda ke ranta, domin daga baya ma kuka sosai ta dinga yi, dole Abbu ya koma rarrashin ta, ƙarshe dai Umma ta koma ta ƙarisa musu girkin daren, domin Aunty Amarya bata da juriyan ƙarisa wa, ta ɗiyar ta take yi a yanzu ɗin.

      A wannan ranan mutanen gidan sun kwana cikin ƙunci ne matuƙa, sai dai ƙalilan su da suka kwana cike da murnan abinda ya faru, ko Hajiya sai da taji ɗanta be kyauta ba, domin abinda yayi sai dai mara imani, bata taɓa tunanin ƙiyayyar da yake mata zai iya aikata mummunan abu makamanciyar haka ba, duk a ganin ta suna zaune lafiya, kawai son zuciya ne ya saka ta take nuna kyara ga Ɗahiran, da kuma zigi da yayi tasiri a zuciyar ta, wanda ada ko kaɗan ba ta jin tsanar ta, amma lokaci ɗaya ta ɗaura mata karan tsana, ga shi abinda ɗanta yayi ya fi komi muni, haƙiƙa har kunyan kanta take ji, "shin da wani ido zata sake kallon iyayen Ɗahira?" Yau sosai take nadama ga bin son zuciyarta. Kuma tunda ta koma ɗakin ta take kiran Layin Usman amma a kashe ake sanar mata, tayi kiran har ta gaji don kanta ta bari.



           Washe gari sanda Ɗahira ta farka, gaba ɗaya yaran gidan ta gani a ɗakin Kakan har shi, illa Fadila da ba ta wajen, itama taji labarin komi, domin tuni Umma ta kira ta ta shafa mata, kuka sosai tayi tsaban tausayin ƴar uwan nata, tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a kusa da ita, amma babu hali.

      Baffa ne ke zaune gefen ta ya riƙe mata hannun da ba'a yi mata ƙarin ruwa ba, su ma su Aunty Zainab da Aunty Zulaiha suna kan gadon zaune, sai Shakira dake kan drowan gadon, Kaka kuma yana can ɗaya side ɗin zaune a saman Wheel chair ɗin sa, ya zuba tagumi yana ta faman kallon ta. Inda Yusra ke zaune a can kujera, ita kanta duk taurin ranta yau dole ta tausaya wa Ɗahira, har tana jin zuciyar ta na karye wa tsaban tausayin ta, kamar ba Ɗahiran su ba, Ɗahira ƴar gayu wacce idan ma ka ganta tsaban haɗuwar ta baza ka taɓa cewa zata taɓa ƙasa ba, ita ce ta zama haka, ta zama tamkar wata almajira tsaban lalacewar da tayi, duk farin ta tsaban wahala sai da tayi baƙi, har da ƙuraje suka feso mata a fuska, wanda ada bata dasu ko ɗaya, gaskiya ta sha wahala tunda har ta koma haka kamannin ta suka sauya.

       Yusra daga ita har Shakira suna da ciki, Sa'adatu ce kaɗai nata ma ya fi ƙanƙanta, don ita ko watanni biyu be kai ba, itama Fadila tana can tana fama da nata, ciwo sosai ma take yi har yanzu

Ita Sa'adatun tunda taji labarin dawowar Ɗahira ƙin zuwa tayi, tana ganin sanda Baffa ya fice amma ko bi ta kansa bata yi ba, taci gaba da kallon ta.

     Baffa shi ya soma ganin farkawan ta, don haka ya sake riƙe hannun ta sosai cike da jin daɗi yana kiran sunan ta

Hakan ya ankarar dasu, sai duk suka bi ta da sannu ko wacce tana murna

Ita kuma Ɗahira kallon su kawai take yi ta kasa furta komi, duk da a ƙasan ranta daɗi ne ya cika ta

Duk sannun da suke mata ta kasa amsa wa

A lokacin ne Fadil ya shigo ɗakin, ganin ta farka sai ya fita a guje don sanar wa da Aunty Amarya, tunda dama ita tace masa, "idan ta farka ya zo ya sanar mata domin ta kawo mata abinci". Tare suka dawo ɗakin da Fadil ɗin, ya riƙe mata coolarn abincin

A lokacin har Ɗahiran ta tashi zaune da taimakon Baffa, har ta buɗe baki tana amsa musu gaisuwar nasu tana murmushi

Kaka sai tambayar ta inda ke mata ciwo yake yi, "idan da akwai ta sanar mishi sai a sake duba ta?"

Murmushi tayi masa tana kallon sa tace, "tsoho me ran ƙarfe, babu abinda ke damu na yanzu, tunda har na ganku kusa dani hakan ya fiye min komi Wlh".

Sallaman Aunty Amarya suka amsa da suka shigo a yanzu ɗin

Taƙarisa ta zauna inda Baffa ya tashi ya bata wuri, a nan take mata "ya jikin?"

Ɗahira ta kalle ta kamar zata yi kuka tace, "da sauƙi Mama na, babu abinda ke damu na".

"To shagwaɓa ya tashi ko? An ga Mama". Cewar Aunty Zulaiha tana dariya

Su ma sauran duk taya ta suke yi, har Ɗahiran da idanun ta suka cika da ƙwalla

Aunty Zulaihan ta sake cewa, "amma fa kar kiyi kukan don Allah kin ji ƴar ƙanwa ta?"

Gyaɗa mata kai tayi, tana kai hannu ta share hawayen tace, "to bazan yi ba".

Kaka yace, "ai idan akwai ki dole sai kin saka ta kuka, sai dai idan ba Zulaiha bace ke".

Dariya duk kan su suka yi

Aunty Zainab ta amshi coolarn daga hannun Fadil ta zuba mata abincin

Sai da Shakira ta taimaka mata ta shiga Toilet ɗin Kaka ta wanke bakin ta, kana ta soma cin abinci ana zuba hira, ita dai bata sake magana ba sai dai ta riƙa bin su da murmushi

Kaka sai da ya kore su a kan "suna damun ta" amma sun ƙi tafiya

A lokacin ne Hajiya itama ta kawo nata abincin, tayi mata "sannu da jiki?"

Yanda Hajiya ta saki fuskar ta ne, sai duk Ɗahira taji daɗi, a ranta tana mamakin sauyawan ta, wani zuciyar nata kuma tace mata, "ƙila tausayin abinda ɗanta yayi miki ne". Gyaɗa kanta tayi kamar da wani take yi

Abincin Hajiyan duk kowa ya ɗiba suna ci ana ci gaba da hira, ita dai Hajiya tuni ta juya ta fice

Babu daɗe wa su ma su Big Dady suka shigo, sai a lokacin ne wasu suka rage suka koma Parlour

Sannu da jiki suka yi mata cikin kula wa sosai

Ɗahira ta amsa su cike da fara'a

Big Dady yace, "Daughter babu wani abinda ke damun ki yanzu ko? Kina jin ƙarfin jikin?"

"Eh Dady, alhmadulillah babu komi".

"Ok to ga Maganin ki sai ki sha yanzu, idan kin gama Baffa kayi mata wannan alluran barcin, don ya kamata ta samu hutu sosai, in yaso idan ta tashi sai tayi sallolin da ake bin ta, amma yanzu kam hutun ta ake buƙata, ku ma ya kamata ku bar ta haka ta huta".

Abinda Big Dady yace hakan suka yi, duk suka fita suka bar ta. Inda Baffa ya anshi maganin da alluran ya riƙe domin idan ta gama ya bata.

      Bayan ta gama cin abincin sai ya bata maganin, sannan yayi mata alluran, babu jima wa kuwa barcin ya sure ta.



        Zuwa yamma kuma duk su Aunty Zulaiha suka wuce gidajen su.

💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




        *EPISODE Fifty One*


       Washe gari Hajja Fatu ta tashi da tashin hankali ne, tun sassafe aka kira ta da wayan Shakira aka sanar mata bata da lafiya, a lokacin tana tsaka da shirin tafiya Office ne, domin har Abba ya wuce, nan ta zari mayafi jiki na rawa tayi gidan Shakira ba tare da ta sanar da kowa ba


Koda ta Isa ta cidda ƙanwar Sahabi ne ita kaɗai da Shakiran, dama ita ta kira ta tafaɗa mata rashin lafiyan da ta zo ta tarar da Shakiran a mawuyacin hali, ga shi Sahabin ba ya nan ya fita tun safe shima, a lokacin ne ciwo gadan-gadan ya taso mata, Allah ya jeho ƙanwar Sahabin ta biyo ta gidan domin ta amsa kuɗi wajen Yayan ta sai ta wuce school.


      Sosai hankalin Hajja Fatu ya tashi da ganin Shakiran na ta zubar da jini, gaba ɗaya ta gama fita hayyacin ta. Nan ta saka ƙanwar Sahabin ta taimaka mata suka kai ta cikin motan ta, sannan taja suka nufi asibiti, yayinda ƙanwar Sahabin kuma ta koma gida don sanar da mahaifiyar su.


       Suna isa asibiti a rikice Hajja taje ta kira nurse's, aka ɗauke ta a Wheel chair, emergency Ward's aka wuce da ita aka soma bata taimakon gaggawa


Hajja duk ta rasa tunanin da zata yi ma, sai faman goge gumin dake tsatstsafo mata a goshi take yi, duk da kuwa garin babu zafi luf-luf ne kamar za'a yi ruwa ma. Ruɗun da ta shiga be bari ta sanar wa kowa ba


Sai Baffa ne da yazo wuce wa ya hange ta a wannan yanayin, sai faman sintiri take yi tana kaɗa hannaye, nan ya iso wajen ta yana tambayan ta abinda ke faruwa ya ganta a nan? Tunda ya san ba nan ne Office ɗin ta ba


Kallon sa tayi kamar zata yi kuka tace, "Shakira CE babu lafiya, an kira Ni na je na ganta a mawuyacin hali tana ta zubar da jini, tamkar ma bata da rai". Sai ta fashe da kuka tsaban shiga tashin hankali, fatan ta kawai Allah yasa ba wani abu bane zai sami ɗiyar ta, su kenan mata su biyu, idan ta rasa ta bata san ya zata yi ba


Jin abinda Hajjan ta faɗa sai shima hankalin nasa ya tashi, nan ya soma tambayar ta "to garin ya hakan ta faru? Ina Mijin nata?"


"To wa ya san inda mijin nata yake, ƙila yana wajen aiki ne, amma Ni da naje babu shi".


"To bari in faɗa ma su Abba, ina zuwa". Yafaɗa da sauri yana yin gaba.




      Sanda likitan dake duba Shakira ya fito, sai duk suka nufa wajen sa, kama daga kan su Abba har su Yusra duk suna wurin, sai kuma mahaifiyar Sahabin ita da ƙannin sa biyu maza, tambayar sa "jikin nata suka yi?"


Likitan yace, "yanzu babu wani matsalan dake damun ta su kwantar da hankalin su, ɓari tayi shi ne yaja mata zuban jinin, amma da zaran ma ta farka komi normal ne sai abinda ba'a rasa ba".


Kowa alhmadulillah yake faɗa, ba kamar Hajja Fatu da duk ta fi su shiga tention


Nan Doctor ɗin yace, "za su iya shiga su ganta". Kafin nan yace, "yana son ganin su Abba a keɓe".


Su ukun duk ka suka bi shi, sai da suka shiga Office ɗin nasa suka sami wuri suka zauna


kafin likitan yace, "am.. DOCTOR'S gaskiya yarinyan nan ba haka kawai cikin jikin ta ya zube ba, naga kun yi yawa ne shiyasa ban faɗa muku matsalan a waje ba, akwai ƙwayoyin da tasha su wanda su suka zubar mata da cikin, ba don Allah ya tsare an kawo ta da wuri ba wlh da an sami matsala, domin ƙwayoyin suna da illa sosai, saboda suna aiki a jikin mace in two minutes, ƙarfin sa yana sa mace ta sami matsala a mahaifar ta, ko kuma wasu matsalan dai wanda ba ma fatan hakan".


Duk shiru suka yi da jin bayanin likitan


Inda yaci gaba da faɗin, "amma ya kamata ta kiyaye gaba, domin idan ta sake amfani dashi abinda ake gudu zai faru ne".


"Ok mun gode Dr. Bashir, babu matsala yanzu zamu iya tafiya?" Cewar Abbu kenan yana kallon sa


"Eh babu komi, duk wasu magunguna mun rigada mun bata tasha, da zaran ta tashi zata farka da kuzarin ta insha Allahu".


Sallama suka yi masa suka fito, babu wanda ya sake tayar da maganan har suka je suka duba ta suka fito, Office suka wuce tunda a lokacin tana barci ne. Sai bayan ta tashi ne Big Dady da Abbu suka dawo a tare, a lokacin babu kowa wajen ta sai Hajja Fatu


Don haka Big Dady bayan sun yi mata sannu da jiki sai yace da ita, "ke Shakira tashi zaune zamu yi magana".


Tashi tayi kamar yanda yace mata, kanta a ƙasa ganin yanda suke bin ta da kallo, har wani zillo gaban ta yake yi domin gani take yi tamkar tayi laifi ganin yanda suka ɗaure fuskar su


Hajja dai itama shiru tayi tana jiran jin abinda zai faru


Big Dady yace, "ya aka yi kika sha maganin zubar da ciki? Dama ashe baki da hankali bamu sani ba?"


"Zubar da ciki kuma?" Inji Hajja Fatu tana bin su da kallo, kana kuma ta mayar da idanun ta kan Shakiran don itama taji amsar nata


Ita kuwa zare idanu tayi tana ƙifƙifta su, sai kuma ta fashe da kuka sosai kamar an yanka ta


Hakan yasa Abbu yace, "bayani zaki yi mana ba kuka ba, ba ma son sakarci kinji ko? Yanzu da ba don an kawo ki asibiti da wuri ba; bamu san matsalan da zai same ki ba, sai dai Allah ya rufa asiri ya tsare babu abinda ya faru dake, amma kin rasa cikin tunda hakan kika fi so".


Cikin kuka tace, "wlh wlh Abbu wlh ku yarda dani ba Ni ce na sha maganin zubar da ciki ba, wlh sai dai idan Sahabi ya saka min a wani abun nasha, amma wlh ban sha komi ba".


Hajja Fatu da tsaban takaici ya cika ta na jin an zubar mata da cikin jikan ta, tace, "Dan uban ki taya Sahabi zai baki maganin zubar da ciki ki sha? Idan ba ke ce kika san irin magungunan ba shi Sahabi taya zai baki ki sha?"


"Wlh Hajja shi ya bani, dama can ba ya son cikin, yayi-yayi in zubar amma naƙi na ce masa ina son Abu na, Amma sai da ya san yanda yayi ya zubar min".


Big Dady yace, "to ya isa haka, kiyi shiru, but yau kin sha wani abu ne da safe da kika tashi?".


Gyaɗa masa kai tayi sai tace, "eh nasha fura dana tashi, lokacin ina sha babu jima wa naji ciki na yana murɗa wa, daga nan ne na fara jin ciwo".


Jinjina kai suka yi kafin suka sake mata sannu tare da kwantar mata da hankali sosai, sannan suka fice.



     Suna fita Hajja ta soma mata faɗa a kan "meyasa tun farko da yace zai zubar da cikin bata zo ta sanar mata ba? Ai da tayi wa tufkar hanci, amma ga shi yanzu ya cuce su ya zubar da cikin".


"Hajja wlh ban yi zaton abun zai kai haka ba, da fari da ya tayar da fitinan sai an zubar faɗa muka yi tayi dashi, daga ƙarshe yace min ya haƙura, tunda mun yi hakan dashi ne tun lokacin da cikin yake ɗan wata ɗaya da muka gane ina da ciki, ashe wayau yayi min akwai abin a zuciyar sa har yanzu". Ta ƙare maganar tana me fashe wa da sabon kuka


Hajja rarrashin ta ta hau yi kawai tunda me afkuwa ya riga da ya afku, sai dai kuma a koke gaba.




         Mutanen gida duk sun zo tunda labari ya je musu Shakira na asibiti, Ɗahira ne da Kaka kawai basu samu damar zuwa ba, Ɗahira na fama da nata jikin, tunda yanzu sosai zazzaɓi ya rufe ta, ko kaɗan ba ta jin daɗin jikin ta, ƙarin ruwa ake ta mata, duk da yanzu alhmadulillah ba kamar jiya da ta kwana dashi ba.





       Har yamma yayi babu Sahabi babu labarin sa, kuma duk ƴan uwan sa suna ta zuwa gaishe ta, zuwa dare aka sallame ta tunda jikin da sauƙi babu wani abu, kai tsaye su Big Dady gida suka wuto da ita, sun yanke shawaran baza ta koma ba har sai Sahabi ya zo ya same su.


       Be zo ɗin ba sai washe gari da rana, lokacin duk suna Hospital, Hajja Fatu ce kawai bata je ba ta zauna kula da Shakiran, wajen Kaka ya soma zuwa ya gaishe sa


Kaka ya amsa shi kamar babu wani abu tunda shima be nuna komi ba, illa neman gafara da ya nema a kan rashin zuwan sa a jiya ya duba ta, wai "akwai babban abinda ya tsayar dashi ne."


       Waya Kaka ya ɗauka ya kira su big Dady ya sanar musu da zuwan Sahabi wai "ya zo ɗaukar matar sa".


Tare da Abbu da Big Dady suka taho, don shi Abba ƙin zuwa yayi, suna zuwa suka tarar dashi har yanzu yana tare da Kakan, har an ajiye masa abin motsa baki. Bayan sun gaisa dashi


Sai Big Dady yace, "Sahabi abinda yasa muka nemi ganin ka kaima mun san ka sani, jiya matar ka ta yi ɓari har ta kwanta a asibiti amma ka kasa zuwa ka duba ta, Dalili kuwa shi ne saboda baka ɗauke ta da wani muhimmanci ba, sannan kuma saboda kai ne ka jawo musabbabin ciwon nata, kar ka manta mu nan gidan likitoci ne da ko wane fanni mun san matsalar sa, a tunanin ka idan har ka zuba mata magani a abun sha tasha cikin ya zube baza mu gane bane? To, kayi wa kanka ƙarya, don me idan ba ka son ciki zaka bari ku ɗauka? Idan da wani matsalan ya sami ɗiyar mu wato ba ka da asara ko?"


Gumm Sahabi yayi kansa a ƙasa, har gumi ya haɗa domin be yi tunanin sun gano shi ba, ga shi kai tsaye suke tuhumar sa da shi ne ya saka mata, be da kuma da yanda zai yi


Abbu ya amshe maganar da cewan, "ai Yaya babu maganar yana so ko ba ya so, tunda har yayi aure to dole ne ya haihu kamar yanda Annabi yace mu hayayyafa domin yayi alfahari damu, idan be son haihuwar babu dole sai ya sakar mana ƴar mu, idan ba haka ba wata rana zai je ya naƙasa mana ita kuma shi be da halin biyan mu, kayi magana ka tsaya ka sunkuyar da kai? Amma wlh ka bamu kunya bamu zaci haka a gare ka ba, ka watsa mana ƙasa a ido".


Kaka dai duk yana sauraron su be ce komi ba


Haƙuri ya soma basu Sahabin yana cewa, "insha Allahu bazai sake ba, wannan ma kuskure ne amma wlh yana son matar sa". Duk ya gama haɗa gumi ya nuna musu nadamar sa a fili


A nan ne Kaka ya saka baki, inda yayi mishi nasiha me ratsa zuciya, kafin yace, "ya tafi zuwa gobe sai ya zo ya tafi da matar sa, amma yau dai ya bar ta a nan tunda zata fi samun kulawa".


Godiya sosai yayi musu kana ya miƙe ya bar gidan, be ma nemi ganin Shakiran ba ya wuce.



        To al'amarin haka dai ta faru, zuwa gobe Shakira ta koma gidan ta.





      Inda rayuwa taci gaba da tafiya sannu a hankali, kwana na wuce wa haka satikai, har ga shi yau wata ɗaya da dawowar Ɗahira daga Turkey, kuma har yanzu babu labarin Usman gaba ɗaya, wayan sa ma ba ta shiga. Zuwa yanzu Ɗahira ta samu lafiya sosai, ta koma kamar ba ita ce ta dawo ƙoɗai-ƙoɗai ba, ta murje tamkar bata yi wani ciwo ba, tunda tana samun kulawa sosai, yanzu haka ma har ta koma bakin aikin ta duk sabida ya ɗebe mata kewa, tunda ko yaushe neman hanyar da zai ɗebe mata kewa suke yi, su Abbu sosai suke iya ƙoƙarin su wajen sun saka ta cikin nishaɗi, alhmadulillah kuma komi na tafiyan mata normal, don ita har ta manta ma ta taɓa yin aure, ko Usman ɗin ba ta tuna wa bare auren dake kanta, jira kawai take yi yanzu ya dawo mata da takardan sakin ta, aure kuma ta cire sa a ranta tuni, ko idan zata sake aure ba yanzu ba.




       Yanzu sosai suka sake jone wa da Baffa, don shaƙuwar su ta yanzu har tafi na da.



         Hajja Fatu sai dai ta zuba musu idanu babu yanda zata yi dasu, domin dai duk faɗan da take masa ba ya sauraron ta, shi a ganin sa kusantar Ɗahira na rage masa raɗaɗin da yake fama dashi, tunda har giyan nasa ya dena sha sosai, duk yanda ya lalace ya bar ƙasumba a fuskar sa yanzu duk ya gyara, ya koma ɗan gayen nan nashi da duniya ta san shi, burin sa yanzu kawai Usman ya dawo ya bata takardan sakin ta, a lokacin shi kuma zai fito ya nuna wa kowa shi zai aure ta, ya shirya tsaf ko wani irin Fitina ne ma a yi.




      Ana haka sai ga Usman ya dira a ƙasan, ba da sanin kowa ba ya hayo taxi ta kawo sa gida, ana sauke sa ya nufi gidan su, ta Gate ɗin gidan ya shiga, har ya isa Part ɗin sa babu wanda ya ganshi ba ya ga me gadin da ya buɗe masa Gate.




    Gaba ɗaya Part ɗin yayi ƙura sosai, kusan wata biyu babu wanda ya sake shiga tun tafiyar su, be bi ta kai ba ya wuce kansa tsaye ɗakin sa, wanka ya soma yi ya fito ya sanya jallabiya ya soma ramukon sallolin sa, yana idar wa yabi lafiyan gado sai Barci, da zummar idan ya farka sai ya je gidan su ayi duk abinda za'a yi, ya shirya wa ko ma meye ne, bare ma ya san cewa yanzu sun sauka daga fushin da suke yi dashi, cikin kwanciyar hankali yake barcin sa babu abinda ke damun ruhin sa.














_Yanzu aka soma wasan fa, ku gyara zama kawai._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

          *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




              *EPISODE Fifty Two*


         Bayan ya tashi daga barcin alwala yayi ya gabatar da sallan la'asar da ake kira a lokacin, bayan ya idar sai ya shirya cikin ƙananan kaya kamar yanda ya saba ko yaushe, riga baƙa da blue ɗin wando jeans, kayan sun haska shi sosai domin sosai suka yi masa kyau, komin sa yana yi ne a natse a kuma sanyin yanayin sa, turare ya feshe jikin sa dashi kana ya ɗauki wayan sa ya saka a aljihun bayan wandon sa ya fito daga gidan, hannayen sa zube cikin aljihu yana bin yanayin garin da kallo, da alamu hadari ne ke son haɗuwa domin har an fara yayyafi kaɗan-kaɗan duk da akwai rana be gama shige wa ba, murmushi kawai yake saki wanda samun ka ga yayi sa aiki ne, yana bala'in son wannan yanayin na damina, a ransa yana jin daɗin dawowar sa a dai-dai, ya san yanzu can kafin daminan su tayi nisa nan sun sha ruwa sosai


Tafiyan sa a natse yake yi har ya isa cikin babban gidan su, kai tsaye Part ɗin su ya wuce, yana tura ƙofan da sallama a bakin sa


Hajiya dake ƙoƙarin zama a kan kujera domin fitowar ta kenan daga ɗaki ta idar da sallah, da zummar idan ta huta ta tashi ta ɗaura girkin dare, sai jin sallaman ɗan nata tayi kamar a mafarki, hakan yasa tabi sa da kallo don ta kasa

Please Login or Register in order to submit comment