Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dasu bata ce musu komi ba

Amsar wayan sa yayi ya wuce kan kujera, zama yayi yana ta faman latsa wa

Ita kuwa haɗe ƙafafun ta tayi ta rufe idanun ta, sai ga hawaye, "Allah gani gare ka, Allah ka fitar dani a hannun wannan azzalumin bawa naka, na tsane shi!". Tafaɗa a hankali zuciyar ta na ƙuna kamar ta fashe. Motsin sa taji, sai ta ɗago kanta tabi bayan sa da kallo da har ya shige ɗakin sa, wani ƙunci ne ya sake tokare mata maƙoshi, sai ta lumshe idanu tayi shiru tana sauraron bugun zuciyar ta, bata ƙara motsa wa ba har sanda taji motsin fitan sa. A haka ta wuni har dare bata sake tashi ba, illa sallah da ke tayar da ita, ko abinci taƙi ci a haka har dare yayi ta kwanta, nan da nan yau barci ya ɗauke ta saboda ta tara shi da yawa bata yi ba.

     Bata farka ba sai washe gari ƙarfe 07:00am. Sosai taji daɗin barcin da tayi, sai duk wani gajiya ya saukar mata, sosai ta ɗan ji sauƙin kan nata, miƙe wa tayi ta shiga Toilet ta ɗauro alwala, sai da ta gabatar da sallah tayi lazami sosai har wajen tara da rabi, sannan ta miƙe ta shiga kichen, Breakfast ta haɗa sannan ta ɗaura ruwan wanka, a nan kichen ɗin ta karya tunda a nan take cin abincin ta

Ruwan na zafi ta sake ta kai Toilet, sai da ta sirka shi yanda take so kafin ta fito ta hau tuɓe kayan ta, ta cire riga tana shirin ɗaura zani sai ji tayi ya buɗe ƙofa

Usman ne ya fito cikin shirin sa da ya saba ko yaushe na ƙananan kaya, babu ƙarya ya ƙure wanka yau, sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake yi. Da kallo ya bi ta ganin yanda ta ƙudundune jiki lokaci ɗaya ta tsorata, har tana zame wa ƙasa saboda tsaban tsorata

Ita duk bata yi tunanin yana gidan ba, tunda da safe yake fita shiyasa ta cire kayan a Parlour.

    Shi kuwa tsaki yaja me sauti, ya sake ɗaure fuska tamau ya fice da sauri abin sa.

      Ajiyan zuciya ta sauke bayan ta raka bayan sa da harara, "ɗan iska. Allah ya isa tsakani na da kai". Ta faɗa a fili tana shige wa Toilet. Wanka tayi ta sanya doguwar riga ja, tayi Rolling da gyalen sa, kai tsaye ɗakin sa ta nufa, sai da ta gama share masa tana shirin fita ta hangi wardrobe ɗin sa kamar be gama rufe wa ba, da sauri ta ƙarisa har tana cin tuntuɓe, tana jan shi ya buɗe, washe baki tayi kai tsaye bincike ta soma yi ko Allah zai sa taga keeys ɗin gidan, tunda be taɓa barin wardrobe ɗin sa a buɗe ba, ilai kuwa sai taci Sa'a ta samu keeys da yawa a ciki, har da passport ɗin su a ciki, nan jikin ta ya hau rawa tsaban farin ciki, da sauri ta kwashi keeys ɗin ta fita da gudu, ƙofan ta nufa ta hau gwada mukullan, nan ta samu na ƙofan, sai ta buɗe ta watsar da mukullan a nan, ko mayar masa bata bi ta kai ba, passport ɗin ta na hannu ta wuce wajen kayan ta taja Trolly ɗinta ta fice da gudun ta, domin ba ƙaramin rawa jikin ta yake yi ba, gani take yi kamar kafin ta fita zai iya dawowa gidan.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.

        *EPISODE Forty Nine*

        Tafiya take yi tana waigen bayan ta, duk ta gama tsorata matuƙa, ta san haɗuwar su dashi bazai mata daɗi ba, ita kuma tarigada ta ɗau alwashin sai dai tayi yawo cikin ƙasar nan, amma baza ta taɓa koma wa gidan sa ba, ko bata sami taimako ta koma ƙasar su ba sai dai tabi duniya

Har ta fice a layin gidan, ta yanki hanya ɗoɗar, tafiya me nisa tayi Kafin ta samu wata mata me shago a bakin titi, nan ta tuna da Numban Zakeeya ƙawarta da tayi a cikin jirgi, wani zuciyar tace mata "ta gwada neman taimako ko Allah zai sa a dace". Da sauri ta isa wajen ta tana maida numfashin gajiya, kafin ta ƙarisa wajen ta sai da ta ɗan samu ta daidaita kanta, sannan ta isa tana mata sannu da harshen turanci

Matar kallon ta tayi, duk da ba wani turanci ta iya ba, amma tana ji kaɗan-kaɗan, ta amsa mata cikin fara'a tana tambayan ta "me take so?" Cikin turancin

Nan Ɗahira tayi mata bayanin "don Allah ta taimaka mata da Aron waya, ita baƙuwa ce yau ta sauka, amma wayan ta ya faɗi, ta rasa ya zata yi ta isa gidan da tazo, tana buƙatar yin waya dasu ko za su san inda take".

Matar bata wani tsawaita ba, duba da yanda taga Ɗahiran duk tayi laushi ta wani yamushe, da alamun tana matuƙar buƙatar taimako, nan tausayin ta ya kamata ta, ta ɗauki wayan ta miƙa mata tana bin ta da kallo kamar zata haɗiye ta

Ita kuwa bata damu da kallon da take mata ba, jiki na rawa ta buɗe jakar ta a ƙaramin Zip ta ciro takardan, kofewa tayi a wayan tayi kira, ba'a ɗau lokaci ba kamar ana jira aka ɗauka

Muryan mace taji tayi sallama

Sai Ɗahiran ta amsa mata tana cewa, "da Allah da Zakeeya nake magana?"

"Ita ce. wace ce?".

Cikin Hausa take magana don kar matar taji me take cewa, ganin yanda idanun ta ke yawo a kanta, "suna na Ɗahira, Ni ce wacce muka haɗu dake a jirgi last three weeks, kin tuna Ni? Har muka zauna waje ɗaya muka yi exchanging number".

Cike da ɗoki Zakeeya tace, "Laa Ɗahira ke ce? Wlh nayi tunanin baza mu haɗu ba, sabida yanda nake ta kiran wayan ki ba ya shiga, kuma ke baki kira Ni ba".

"Haka ne. Amma ina buƙatar taimako, don Allah ki taimaka min".

Yanda tayi maganar yasa Zakeeyan ta gane akwai matsala, nan da nan ta tashi hankalin ta tana tambayan ta "me ya faru?"

Ɗahira tace mata, "maganar ba ta waya bace, ki taimaka ki zo ki tafi dani in yaso sai muyi maganar".

"Ok.. ok aina kike yanzu?"

Tambayar matar nan tayi, ita tayi mata kwatancen inda take

Zakeeyan tace, "gata nan zuwa yanzu, basu da nisa da wurin ma".

Sosai zuciyar Ɗahira tayi mata sanyi a wannan lokacin, gani take yi zata iya tsira ba tare da Usman ya sake ganin ta ba. Matar ta miƙa wa wayan tana ta mata godiya sosai kamar zata yi kuka.

      Babu jima wa kuwa sai ga Zakeeya a motar ta, da sauri ta fito ta nufo Ɗahiran

Itama Ɗahiran wajen ta ta nufa domin ta shaida ta

Sosai Zakeeya take ware idanun ta a kan Ɗahira gani take yi kamar ba ita ba, har sanda suka kusanci juna ta gane tabbas ita ce, amma kuma yanda ta sauya mata fiye da tunani, ga baƙi da tsananin rama da tayi, duk ta bushe kamar babu jini a jikin ta. Cikin sauri ta riga ta magana da tambayar ta, "Ɗahira ke ce? Ke ce haka meke faruwa ne?"

"Don Allah mu je sai in Yi Miki bayani, ke kaɗai na sani a ƙasar nan ina buƙatar taimakon ki Zakeeya".

Jiki na rawa kuwa Zakeeyan taja hannun ta ganin har ta soma hawaye, motan ta buɗe mata ta shiga daga ita har kayan ta, itama ta zagaya ta shiga taja motan da sauri. Sun yi tafiya me nisa babu me magana cikin su

Kai tsaye Zakeeya gidan su ta wuce da ita, suna isa suka fito taja hannun ta suka yi ciki

Auntyn Zakeeyan na zaune a Parlour suka shigo Zakeeya na sallama

Amsa mata tayi tana bin su da kallo, ganin ta da baƙuwa sai ta bi su da ido har suka zauna, kana kuma ta soma tambayar Zakeeyan "aina ta samo ta kamar ƴar ƙasar su?"

Zakeeya tace mata, "eh Aunty, ƴar Nigeria ce, domin a jirgi muka haɗu da ita sanda na dawo nan, tana buƙatar taimako ne shi ne ta kira Ni".

"Ok Allah Sarki, Allah yasa dai lafiya baiwar Allah? Sannu ko? Zakeeya kawo mata ruwa tasha naga kamar hankalin ta a tashe yake har kuka take yi".

Zakeeyan bata amsa ta ba illa miƙewa da tayi da sauri ta kawo mata ruwan

Duk da Ɗahira tana buƙatar ruwan domin ta jiƙa maƙoshin ta, amma yanzu ba tashi take yi ba, burin ta kawai abinda ke cikin zuciyar ta ya cika, na ganin ta a ƙasar ta na haihuwa, daga nan ne hankalin ta zai kwanta

"Ki sha ruwa kinji?" Cewar Zakeeya tana dafa mata kafaɗa

Kallon ta Ɗahira tayi lokacin kuma wani sabon hawayen ya Kunno mata, cikin rawan murya tace, "wlh ba na jin zan iya saka wani abu a ciki na idan har ba a ƙasa ta na ganni ba, don Allah don Allah ku taimaka min na koma ƙasa ta, bani da kowa a nan, ku taimaka min da kuɗin jirgi, wlh idan na koma zan tura muku kuɗin ku, Ni dai fata na na bar ƙasar nan".

Sosai kansu ya ɗaure da zantukan ta

Cikin al'ajabi Auntyn tace, "baiwar Allah bamu gane ba? Me ke faruwa ne kiyi mana bayani kinji don Allah yanda zamu fahimta".

Ba ta jin zata iya ɓoye musu komi, sabida tana ganin kamar idan suka ji labarin ta za su taimaka mata, don haka ta basu labarin komi game da rayuwan ta wajen Yayan ta da ya kasance miji a gare ta

Sosai suka tausaya mata, Zakeeya har da hawaye sai da ta zubar mata

Nan Auntyn tace, "za su taimaka mata, zuwa gobe da yardan Allah zata koma gida".

Amma Ɗahira sai ta roƙe su "su taimaka a yau ta bar ƙasar, baza ta iya ko ƙwaƙƙwaran mintuna bane, tunda ta samu ta gudo gwara ta koma ga iyayen ta hakan zai fi mata, su taimaka mata idan za'a samu jirgi ta bar gidan".

Auntyn bata yi musu ba, sai ta kira mijin ta ta shaida masa komi

Nan yace mata, "ga shinan zuwa". Babu jima wa kuwa sai ga shi ya zo, shi ne ma yaje ya nema mata jirgin, sai dai ba'a sami wanda zai je Direct to Nigeria ba dole za'a yi biye-biye wasu ƙasashe, kuma da yamma zai tashi. Direct to Nigeria kuma sai zuwa dare za'a samu

Ɗahira tace, "tana so, gwara ta tafi wani ƙasan, baza ta iya jira har dare ba," wataƙil ma ya biyo bayan ta," abinda take tsoro kenan.

     Haka suka taimaka mata har ta bar ƙasan, sosai Ɗahira take kuka sabida wannan karamci nasu, idan ba Allah na son ta ba, kuma sun kasance mutanen kirki, da bata san ya zata yi ba, sosai tayi musu godiya tana kuka

Amma su sun ce "sun yi mata don Allah ne ba sai ta biya ba tunda suna da halin yi, kuma kasancewar ta ƴar ƙasar su me buƙatar taimako".

Itama Zakeeya sai da tayi kuka da za su rabu, jin ta take yi tamkar ƴar uwan ta, ga tausayin ta da take ji, Allah ne ya haɗa jinin su.




⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

           Usman kuwa be koma gida ba sai dare kamar yanda ya saba, yana taɓa ƙofan zai buɗe yaji ta a buɗe, mamaki ne ya kama sa ya shiga yaci karo da mukullai a bakin ƙofa, da kallo yabi wajen, sai kuma yabi parlour'n da kallo zuciyar sa na hasaso masa faruwar wani abu, da sauri ya isa cikin parlour'n yana faman kiran sunan Ɗahira, shi kansa be san cewa ya san sunan ta har haka ba, domin tunda yake be taɓa kiran sunan ta ba, tun tana ƙarama bare yanzu, sai ji yayi bakin sa na furta wa

Ko ina ya duba a gidan be ganta ba, wanda har wardrobe ɗin sa ya duba, nan yaga babu password ɗin ta, zargin sa ya tabbata guduwa tayi, duk da hankalin sa be tashi ba amma ya kasa haƙura sai da yabi bayan ta ko zai ganta, sosai ya ƙudurta a ransa "muddin ya ganta sai ya ci uwar ta yau ba uban ta kaɗai ba".

Duk inda yabi da mota be ganta ba, ko me kama da ita be gani ba, dole ya isa wajen wani Abokin sa suka nufa airport tare, dayake shi yana da hanya, ya san nan da nan za'a bincika masa idan ta hau jirgi, duk da ba ya tunanin zata iya barin ƙasar da sauri haka, ba kuɗi ne da ita ba bare ƴan uwa

A lokacin ne ma jirgin da zata ɗaga zuwa Nigeria Direct zata tashi, nan abokin ya saka a duba musu list ɗin masu tafiya, amma babu sunan ta, sai ya tambaya "ko akwai wanda ya tashi kafin wanann?".

Nan ne aka faɗa musu "akwai wanda ya tashi ƙarfe 04:00pm. Amma kuma ba Nigeria kaɗai zai wuce ba." Koda aka bincika sai aka samu sunan ta

Usman be iya cewa komi ba illa jan abokin nasa da yayi suka shiga mota suka yi gaba

Abokin na tambayar sa "amma lafiya?" Tunda be san makaman zancen ba

Sai Usman yace masa ,"ƙanwar sa ce yarinyan ya neme ta ya rasa, shi ne yake bincike ko ta koma gida ne".

      Koda ya koma gida kwanciyar sa yayi domin ko kaɗan be saka damuwa a ransa ba, hakan ma shi yafi masa, gwara da ta gudu da ƙafar ta, fargaban sa ɗaya kawai yanda iyayen sa za su ɗau fushi dashi, amma ya shirya musu dama tun farko, kuma yanzu bazai koma gida ba har sai sanda suka huce, in yaso sai ya koma musu tare da takardan sakin ta. zuwa da safe ma zai sauya Simcard don kar ma su neme sa su samu. A haka yayi barcin sa cikin kwanciyar hankali har da munshari, babu abinda ke damun rayuwar sa.




⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

                *NIGERIA*
 
      Kwana biyu su Ɗahira suka yi a jirgin kafin suka isa Nigeria, sun sauka ƙarfe 03:30pm. Amma kasancewar akwai hadari garin; sai ka zata yamma ne sakaliya, kowa sai haraman wuce wa gida yake yi tunda hadari gadan-gadan ne ya taso, dayake farko-farkon damina ne.

     Itama kanta tsaye wajen masu Taxi ta nufa, amma duk wanda ta taya ba sa ɗaukan ta tunda kowa ta kansa yake yi ganin har an fara yayyafi. Sai ta fito bakin titi tana ci gaba da tare wa, zuciyar ta gaba ɗaya ta tsinke burin ta kawai ta ganta a gida

A lokacin da ruwan ya sauko sosai, a time ɗin ne ta samu wani me kirki ya faka ya ɗauke ta, lokacin gaba ɗaya ta gama jiƙe wa sai rawan ɗari take yi

Shi kansa me taxi ɗin har ya wuce ganin ta cikin ruwan ne ya tsaya, koda ya ɗauke ta be jirga a wajen ba tunda ana tsula ruwan ne. Wajen mintina goma sha biyar kuma sai ruwan ya tsaya cak, sai ɗan yayyafi da ake yi jefi-jefi, hakan yasa ya tada motan ya nufi inda ta sanar masa.

    Suna isa bakin ƙofar gidan su kamar an yi mata bishara da gidan aljana, fita tayi tace masa, "zata kawo masa kuɗin yanzu".

Yace, "babu damuwa yana jira".

Ƙwanƙwasa Gate ɗin tayi, gateman ya buɗe mata

Shima be wani gane ta sosai ba, har yace, "baiwar Allah daga ina..?"

Ta katse sa da cewa, "Hamisu Ni ce Ɗahira, don Allah ka sallami me motan can".

"To.. to Hajiya, to sannu da zuwa, sannu an dawo lafiya?". Yafaɗa jikin sa na rawa tsaban murna

"Lafiya lau". Tace dashi tana shige wa da sauri ta doshi cikin gidan

Tun daga nesa ta hangi Mahaifin ta da Big Dady suna tsaye a bakin ƙofan shiga gidan suna magana

Su ma sai suka tsaya kawai suna kallon ta ganin ta jaye da akwati, duk tunanin su sai ya tafi ga Ɗahira ce wannan? Duk da sun hangi wannan ɗin tamkar bata da haske kamar Ɗahira, kuma sun san cewa Ɗahira ba ta ƙasar nan, ba yanzu zata dawo ba bare su ganta a nan, amma kuma sak tafiyan ta da yanayin ta ya basu ita ce.

            Ilai kuwa itan ce don basu gama hasashen nasu ba ta gurfana a gaban su, mamaki zalla ne ya cika su ganin tabbas ita ce, sai suka buɗe baki suna bin ta da kallo ko wanne ya kasa furta komi ganin yanda tayi mugun sauya musu

Ita ko nan da nan hawaye ya wanke mata fuska, cikin rawan murya tace, "Abbu.. Dady.." sai tayi shiru tana me fashe wa da wani irin kuka me shiga zuciya

Sosai hankalin su yayi mugun tashi, lokaci ɗaya kamar an tsikare su suka yo kanta ko wanne yana me riƙo mata hannu da tambayar "me ke faruwa? Ina Usman ɗin? Ya aka yi ta dawo?" Haka suke jero mata tambayoyin ba tare da sun jira ta amsa musu ba.








.


_Mu haɗu jibi don jin ya za'a kaya, idan kuma bani da aiki za ku iya samun update gobe, amma fa sai naga ruwan comments, shi ne kawai zai ɗan saka min ƙwarin gwiwan muku._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.


        *EPISODE Fifty*

          Ganin ta kasa magana sai rusa musu kuka take yi kamar ranta zai fita, sai hankalin su ya sake tashi matuƙa, inda Big Dady ya riƙo hannun ta suka nufi cikin gidan

Shi kuma Abbu ya janyo mata akwatin ta yabi bayan su, zuciyar sa tamkar zata tsinke, gaba ɗaya ya rasa ma takamaiman tunanin da zai kama wanda zuciyar sa ke bijiro masa da afkuwan sa ga ɗiyar sa.

    Kai tsaye General parlour suka nufa, inda Kaka da Fadil ke zaune suna hira, Kaka na shan dariyan shirmen Fadil ɗin da yake ba shi, shigowar su yasa duk suka bi su da kallo, inda Kaka yake tambayar su "lafiya?" Yana kallon Ɗahira don be gane wace ce ba, saboda fuskar ta na ɓoye jikin Big Dady

Sai da suka zauna, Big Dady ya zaunar da ita gefen sa, kana yace ma Kaka, "Baba Ɗahira CE muka ganta ta dawo, kuma mun tambaye ta amma sai kuka take yi, Allah yasa ba wani abun Usman yayi mata ba?" Ya ƙare maganar da ɗacin rai, domin tuni hasashen sa ya ba shi duk yanda aka yi Usman ya muzguna mata, amanar da suka ba shi be riƙe da gaskiya ba, duba da yanda suka ga Ɗahiran ta koma

Shi kuwa Kaka jin furucin Big Dady, sai nan da nan jikin sa ya soma rawa, hankalin sa yayi mugun tashi, ya soma kiran sunan ta yana faɗin, "Mata ta, Mata ta ke ce? Ya aka yi kika dawo? Sanar damu don Allah, wani abun ne ya faru? Zo kusa dani".

Da sauri ta miƙe ta isa wajen sa tana durƙushe wa ta sake fashe wa da kuka, domin yau ji take yi duk wani baƙin cikin da ta ƙunsa na zaman ta dashi suna dawo mata, yau take iya amayar da duk abinda ta ƙunsa, kukan kawai shi ne zai kawo mata sauƙi a gare ta

Duk yanda suka so tayi magana, Ɗahira ta kasa yi, riris take kuka kamar ana yanka ta, har wani shashsheƙa take yi tana faman ajiyan zuciya

Wanda hakan ba ƙaramin ɗaga musu hankali yayi ba, musamman Kaka da jikin sa sai rawa yake yi, sai ma a lokacin yake iya ganin yanda ta koma, ta fita hayyacin ta gaba ɗaya kamar ba Ɗahiran da suka sani ba, kowa ya ganta ya san cewa wahala ne ya mayar da ita hakan

Shi kuwa Fadil tuni ya sheƙa a guje ya garzaya ya sanar wa Aunty Amarya, domin yanda yaga Ɗahiran na yi har kuka sai da ya fashe dashi

Nan da nan itama sai Aunty Amarya ta saki tuƙin tuwon da take yi, gaban ta na matsanta faɗi tayi General parlourn da sauri

Umma na take mata baya ita da Fadil, domin lokacin da Fadil ɗin yake sanar wa Aunty Amarya tana zaune a Parlour tana ji, kai tsaye sai da ta wuce ta shafa wa su Hajja Fatu da Hajiya labarin dawowar Ɗahira, kana suka wuce can parlour'n.

      Suna shiga suka ga yanda su Big Dady suka tasa ta gaba suna rarrashi, a lokacin har da Abba da shigowar sa kenan ya jiyo kuka daga parlour'n, shi ne ya garzayo da sauri don ganin waye ne

Aunty Amarya kuwa ta kasa zama saboda ganin tilon ƴar ta yanda ta koma, nan da nan hawaye suka cika mata idanu zuciyar ta na sake tsintsinke wa, dama tun farkon tafiyan su hankalin ta be taɓa kwanciya ba, kullum da ita take kwana kuma take tashi, sosai taji a jikin ta ɗiyar ta ba ta cikin kwanciyar hankali, a kullum ranan duniya sai tayi mata addu'ar kariya da zaman lafiya ita da mijin ta.

     Su Umma kuwa murna na ciki an kasa fito dashi fili, ko wanne sai zuba idanu yayi yana kallon ta, musamman Hajja da tafi kowa murna, tuni zuciyar ta ta bata aikin Malam ne yaci, kuma tabbas ta san cewa da takardan saki ta taho, dama abinda take burin ya faru kenan, kuma ga shi ya faru, yau tsaban murna ai sai ta zuba ruwa a ƙasa tasha.

      Daƙyar Abba ya rarrashe ta tayi shiru, sai sakin ajiyan zuciya take yi tana shashsheƙa

Shi kuwa Big Dady tuni ya yi kiran wayan Usman amma a kashe ake ce masa, hakan yasa zargin sa ya sake tabbata, shi ne ya sake tambayar Ɗahiran abun da ke faruwa

Sai a lokacin ta samu bakin fallasa musu duk zaman da suka yi, kama daga farkon kai ta tun suna gidan nan, har rayuwar uƙuban da tayi a can Turkey, tana Yi tana wani sabon kukan da ya taho mata ta kasa tsayar dashi

Sosai Aunty Amarya a wannan karon take zubar da hawaye tsaban tausayin ɗiyar ta da kuma raɗaɗin da take ji a zuciya

Haka zalika shima Fadil sosai yake taya Yayar tashi kukan tausayin ta

Su Big Dady kuwa sun kasa cewa komi, ko wanne zuciyar sa tafarfasa kawai take yi da jin abinda Usman ya aikata, haƙiƙa da yana wajen nan ne, yau da sai sun taru sun yi masa ɗan iskan duka, komin girman sa kuwa tunda be wuce duka ba, ƙanwar sa jinin sa ita ce yayi wa wannan riƙon, wanda kashi me ɗoyi ya fita daraja a wurin shi, yanzu da ace bata gudo ba sai ta mutu zai kawo musu gawan ta? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un

Kaka ne kaɗai ya iya yin magana a wannan lokacin, duk da shima ɗin sosai ransa yake a matuƙar ɓace, duk son da yake yiwa jikokin sa, ba ya haɗa su da son da yake yiwa Ɗahira, zai iya ɗaukar mummunan mataki a kan abinda Usman yayi mata da ace yau yana gaban sa. Cewa yayi, "aje a duba ta domin be yarda da lafiyan ta ba, maybe wannan uƙuban da ya bata yayi sanadin sanya mata ciwo, saboda yanda ta koma, idan kuma hakan ya faru, Wlh sai yayi mummunan saɓa wa Usman, domin sai ya ga fushin sa da be taɓa gani ba".

Daga Abba har big Dady su ma faɗan suka hau yi, domin sai yanzu bakin su ya iya buɗe wa tsaban ɓacin rai, Abbu ne kaɗai be iya cewa komi ba, amma baƙin cikin abinda Usman yayi wa ɗiyar sa, har hawaye yake share wa tsaban ɓacin rai, haƙiƙa yau da ba don akwai na gaba da shi ba, da be san me zai yanke a kan Usman ba, sai dai kawai ya bar komi wajen ƴan uwan sa, domin ya san duk matakin da zai iya ɗauka, za su ɗauka a kan shi, kuma idan ma ya ɗau mataki ya nuna ba ya da kara kenan, ƴan uwan sa basu isa da ɗiyar sa ba sai shi.

 

Please Login or Register in order to submit comment