Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dashi, gaba ɗaya ya dena min biyayya kamar baya, ko kaɗan yanzu ba ya jin kunyan faɗa min duk abinda yake so; duk a dalilin ɗiyar ki, Allah ya isa tsakani na dake A'ishah, insha Allahu sai kema kin ɗanɗana abun da naji, kuma wlh Al'ameen ya fi ƙarfin ki har abada, bazai taɓa auren ɗiyar ki ba, da yardan Allah zan tashi masa tsaye sai dai duk wani sharri ya koma miki. Kai kuma mu zuba dani da kai zan gyara maka zama, Allah ya kai mu goben har gidan naku zan zo in ci uban ka hankali kwance".







             **** ***** *****

       Baffa kuwa yana koma wa gidan su, kai tsaye ɗakin sa ya wuce, be duba ko Sa'adatun tana nan ba, ko ta aikata abinda tace zata yin na tafiya gida ba, shi dai be bi ta kanta ba tunda dama tuni ya daɗe da fita shirgin ta, ɗakin sa ya shige, sai da ya kora kamar yanda ya saba sannan ya haye gadon sa, haka yake ta sambatu yana kiran sunan Ɗahira har barci ya sure sa.





28/6/2021.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.

        *EPISODE Forty Seven*

       Washe gari Hajja Fatu da ta gama shirin ta na zuwa Office, sai ta biya ta gidan su Baffa, sai dai kuma bata cid da Sa'adatun a ɗakin ta ba, kai tsaye ƙofan ɗakin Baffa ta hau buga wa, domin a zaton ta suna ciki tunda ta ga motan Baffan be fita ba, kuma ko kaɗan bata kula da babu na Sa'adatun ba; tunda ta san babu inda zata je

Kiran sunan sa take yi daga shi har Sa'adatun

Baffa dake kwance be gama wartsake wa daga giyan da ya sha jiya ba, shiyasa yayi lattin tashi, sai hayaniyar Hajja ce ya farkar da shi, dole ya miƙe yana saka riga a jikin sa, ƙofan ya nufa yana ɓame bottles ɗin rigan, guda uku kacal ya saka ya buɗe ƙofan yana faɗin, "wai Hajja lafiya? Me ke faruwa ne?"

"Biyo ka nayi in ci maka mutunci, ina ita Sa'adatun? Ta fito duk ta faɗa min abinda kake mata, Wlh idan ka sake naji mummunan abu wlh yau Ni da kai ne. ka kira min ita mana ka tsaya kana kallo na".

Wuce ta yayi zai nufi ɗakin Sa'adatun

"Ina kuma zaka je? Ba tana ɗakin ka ba?"

Gajeren tsaki yaja kafin yace, "ba ta ciki tana ɗakin ta".

"To ba ta ciki; na duba ban ganta ba, me ke faruwa ne? Ina zata je da safen nan ba tare da ka sani ba? Yanzu ma na kula kamar ba motan ta a waje".

"To Ni Hajja ina Nasan inda zata je?"

Zata yi magana wayan ta ta soma ringing, ciro wa tayi cikin jaka tana cewa, "ka nemo ta wlh ko inci ƙaniyar ka Baffa, ban son shashanci". Wayan ta amsa ganin sunan Dr. Zubairu

"Hello".

"Dr. Na iso na ga Office ɗin ki a rufe".

"Eh ban fito ba wlh, yau nayi late na tsaya yin wani abun, amma ka jira Ni yanzu zan taho ai kayan naka suna office ɗina".

"Ok to ba damuwa, sai kin zo".

Daga haka suka gama wayan, inda tabi bayan Baffa da ya shige ɗakin Sa'adatu don duba ta.

    Sai dai kuma gaba ɗaya sun duba Part ɗin babu ita, dole Hajja ta ɗauki waya ta kira Numban ta, sai dai ba'a amsa ba har sai da tayi Three missed calls, memakon taji muryan Sa'adatun, sai muryan Mahaifiyar ta taji

Hajja tace, "Amina ya aka yi wayan Sa'adatu ya zo hannun ki? Me ke faruwa ne wai nan mun neme ta ba mu same ta ba?".

Cike da faɗa Hajiya Amina tace, "ina kuwa zaki sani Yaya tunda yaron ki be faɗa miki ba, to Sa'adatu ta dawo gida domin ta gaji da abinda yake mata, kuma na gode da abinda kika min Yaya na gode, babu damuwa". Tana gama faɗar haka ta katse kiran ba tare da taji me Hajjan zata ce ba

Juyowa Hajja tayi ta kalli Baffa tace, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Baffa yanzu me kayi mata da har ta tafi gida? Me ya haɗa ku?"

"Hajja babu abinda ya haɗa mu, nima ban san sanda ta tafi ba".

"Dalla rufe min baki, ashe ban isa da kai ba? Yanzu har sai da kayi sanadin da Sa'adatu ta tafi gida? Ka nuna min ban isa ba ko? To wlh yau na baka ka je ka ɗauko ta tun wuri tun kafin mutanen gida su ji zancen nan, idan ba haka ba zan mummunan saɓa maka". Daga haka ta fice fuuuu ranta a ɓace tayi gida, tana zuwa motan ta kawai ta ɗauka ta fita.

     A hanyan layin gidan ta haɗu da Shakira a cikin motan ta, nan Hajja ta danna mata horn tana faka wa

Itama Shakiran dayake ta gane motan Hajjan, sai ta tsaya tana me fito wa ta nufi motan

Lokacin har Hajjan ta fito tana bin ta da kallo tare da tambayar ta "me tazo yi da safen nan bata wuce asibiti ba?"

"Hajja wlh yaji na yo".

"Innalillahi... Yau na shiga uku na, yaji kika yo kamar ya Shakira? Kina nufin kin baro gidan mijin naki? To uban me yayi miki?".

Baki a zumɓure tace, "wlh Hajja na gaji da abinda Sahabi yake min, kullum be da lokaci na, yanzu ya kai har wulaƙanci yake min, ko yaushe yana waya da mace, kuma idan nayi magana ya dinga min faɗa kenan, yau har mari na yayi don kawai na tanka masa saboda na ga an turo masa text, kuma mace ta turo masa da daren jiya, wai ya fito su haɗu, shi ne ya mare Ni, wlh Hajja bazan koma ba dole sai na ɗanɗana masa azaban da ya ɗanɗana min".

"Uban azaba zaki ɗanɗana masa, angaya miki ana wa namiji haka ne? To wlh idan wani ne zai ce sai dai ki shekara a gida baki dawo ba, kuma da kike tunanin zai biyo ki sai dai ki ji ya sake wani auren ya bar ki banza kawai, dalla ki kama hanya ki tafi, wlh kar ki soma ki shiga gidan nan idan ba so kike mutanen gida yau su yi min dariya ba, ina fama dana Baffa ke kuma kin dawo, ki kama hanya ki tafi ko". Ta ƙare maganar da daka mata tsawa

"Wlh Hajja babu inda zan je, sun daɗe ba su yi miki dariyan ba, ina faɗa miki mari na yayi kina ce min za'a miki dariya, babu inda zan je wlh". Wuce wa tayi wajen motan ta zata shiga

Sai Hajjan tayi saurin ƙarisawa wajen ta tace, "yi haƙuri to, yanzu mu wuce Hospital in yaso sai in sama mana mafita, amma ba na son ki shiga gidan nan a san abinda ya faru, ki kwantar da hankalin ki Sahabi kamar ya dawo tafin hannun ki ne, dani yake zancen".

Da wannan kalaman Hajja ta shawo kan Shakira, sanna suka shiga mota suka wuce Hospital, Kai tsaye Hajja Fatu Office ɗin ta ta wuce, tana shiga ta ciro wayan ta ta danna wa Hajiya Sa'ima kira, nan ta sanar mata "anjima kaɗan tana nan zuwa ta raka ta wajen Malam".

"To babu matsala, sai kin zo". Cewar Hajiya Sa'ima

Suna gama wayan Dr. Zubairu ya shigo Office ɗin

Hajja Fatu tace dashi, "to ga kayan naka nan, amma dai ka san yanda zaka yi ka fita dashi Hospital ɗin nan ba tare da an ganka ba, ka san mutane yanzu sai ace magungunan asibiti ka sata".

Dariya Dr. Zubairu yayi yace, "ai bani da matsala dacta, ba ma yanzu zan fita da shi ba sai zuwa magriba idan an shiga Masallaci, sannan zan dawo in ɗauka, yanzu Office ɗina zan kai".

"Yauwa hakan ma yayi, sai na ji ka zuwa anjima, yanzu ina son na gama duba patiens ɗina ne domin akwai wurin da zan je".

Yace, "to shikenan, dama akwai maganar da zamu tattauna, idan kin samu lokaci sai ki kira Ni kawai".

"Ok".

Da haka ya fice

Ita kuma ta ɗauki wasu files ta fice, kai tsaye patiens ɗinta taje ta duba, bayan ta gama ta dawo Office, waya ta ɗauka ta kira Safna, tana zuwa tace mata "taje ta ba wa Maman yaron nan takardan sallama".

Amsa tayi Safnan tana shirin fita

Sai kuma Hajja ta kira wo ta tace, "zuwa anjima ina ga shima ɗayan yaron na kusa dashi za'a sallame sa, so bazan daɗe ba idan kinga jikin nasa da sauƙi sosai sai ki ba shi sallama".

"To". Safna tace da ita tana fice wa.

      Awanni biyu Hajja Fatu ta ƙara a asibitin kafin ta wuce gidan ƙawarta, kai tsaye bata zauna ba suka wuce wajen Malam, inda Hajja ta zube masa kuɗi don ayi ma yaran ta biyu aiki, ko kaɗan ba ta son a sake samun ɓaraka a tsakanin su, ita Shakiran a kama mata Sahabi sai yanda tayi da shi, shi kuma Baffa a saka mishi ƙaunar Sa'adatu a rai su zauna lafiya kar wani abu ya sake faruwa.

    Daga nan gida kawai ta wuce bata koma aiki ba.

   Ta dawo babu daɗe wa Abba ya shigo a rikice, cikin tashin hankali yace da ita, "ke ɗauko gyalen ki mu wuce Hospital".

Hajja tambayar sa ta soma yi "lafiya?". Itama duk hankalin ta a tashe

Tsawa ya daka mata yana faɗin, "baza ki ɗauko mu wuce ba ko kuwa? Idan mun je can kya ji".

Jiki na rawa Hajja ta rataya gyalen ta tabi bayan sa, a motan sa suka nufi asibitin, be sake ce mata komi ba har suka kai Hospital ɗin. Kai tsaye Office ɗin Big Dady suka wuce, a nan suka ga mutane cirko-cirko har da ƴan sanda, ga Safna durƙushe sai kuka take yi

Da kallo Hajja take bin su dashi hankalin ta a matuƙar tashe, "shin me ke faruwa?" Tambayar dake yawo a ranta kenan babu me amsa mata

"Yauwa officer wannan ita ce me kula da yaron". Cewar Big Dady yana kallon ASP

"Ok". ASP yace yana kallon Hajja, sai kuma yace, "kin gane waɗannan?"

Sai a lokacin ma Hajja ta kalli inda wasu Mata da miji dake tsaye suke, macen na kuka sosai itama. Ta gane matar sarai, sai ta gyaɗa kanta domin ta kasa magana

"Ok sun kawo ƙara da cewan sanadiyar ku ɗanta ya mutu, domin bincike ya nuna an ba wa ɗan ƙwayoyi a matsayin magani, wanda hakan yayi sanadin mutuwar sa, ko da suka koma gida sai ciwo rigigim ya kama ɗan, sun kai sa asibiti mafi kusa dasu domin ceto yaron su, a can aka gano an ba shi ƙwayoyi, kuma ita wannan ( ya nuna Safna) ita ce wacce ta ba shi magani a jiya kenan, in ji Mahaifiyar yaron, ita kuma tace "a Office ɗin ki ta ɗauko maganin." Yanzu binciken da muke yi ya aka yi ƙwayoyin maye masu bugarwa suka shiga Office ɗin ki har aka ba wa yaro ya mutu a sanadin haka?"

Yanda jikin Hajja Fatu ke rawa baza ka ce ƙafafuwan ta za su ɗauke ta ba, sosai ta zaro idanu waje lokaci ɗaya ta jiƙe sharkaf da zufa, ta ma rasa me zata ce illa gaban ta dake faman buga wa kamar zai faso ƙirji

"Baza ki yi magana ba kin tsaya kina kallon Mutane? Ya aka yi ƙwayoyi suka shigo asibitin mu?" Cewar Abba yana daka mata tsawa

Sai kawai Hajja ta fashe da kuka tsaban rikice wa

Cike da baƙin ciki Abba zai sake magana, sai Abbu ya ce da shi, "yi haƙuri don Allah Yaya, a bi komi a hankali".

ASP yace, "Amm... Ina ga fa dole sai dai mu wuce Station; don maganar nan baza ta yiwu a nan ba, wannan matsalan babba ce ya kamata mu wuce can, akwai yiwuwar a kulle Hospital ɗin nan gaskiya domin babu abinda zan iya".

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Abinda su Big Dady suke faɗa kenan. Gaba ɗaya hankalin su ya tashi, ba wai kullewan ba, kar a ɗaga wa mahaifin su hankali, tunda sun san yanda yake matuƙar ji da asibitin nan, wannan babban matsala ne, kisan kai ta hanyar ƙwaya? A matsayin magani?
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.

        *EPISODE Forty Eight*

      Kai tsaye Police station suka wuce gaba ɗaya, inda a can ne Hajja Fatu tayi bayani dalla-dalla, ta yanda ƙwayar suka kasance a asibitin, ta taimaka wa Dr. Zubairu ne wajen shigo da su tare da magungunan asibitin

Nan Abba yayi kamar zai make ta sabida faɗa, sosai ya zuciya ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba

Sai da Big Dady da Abbu suka yi ta tausan sa kafin ya haƙura

Nan aka tura ƴan sanda domin su je su kamo Dr. Zubairu, amma sai dai ba'a same sa ba tuni ya gudu, illa ƙwayoyin da aka kwaso a Office ɗin sa.

      ASP yace musu, "za'a kama Hajja Fatu a matsayin wacce ta taimaka domin yin safaran ƙwayoyi, wanda yayi sanadin kisan kai, ita kuma Safna an sake ta domin bata da laifi". Sai dai sosai suka ja mata kunne a kan sakacin ta ne duk da haka ya ja wannan abun, tana a matsayin likita amma ba ta lura da abinda zata iya ba Patients ɗin ta

Shi Abba tunda ya ga abun ya zo da sauƙi tunda an sasanta baza a kulle asibitin ba, ya wucewar sa ya tafi, be damu a saki Hajja ko kar a sake ta ba

Inda su Big Dady su suka tsaya kai da fata suka yi ta cukui-cukui har suka shawo kan matsalan, to, abin ka da akwai kuɗi, komi a ƙasar mu idan kana da kuɗi to zaka iya yi, nan suka samu aka ce za'a saki Hajja tunda ba ita ce asalin wacce ta shigo da ƙwayoyin ba, kawai da taimakon ta ne hakan ya faru.

      Kafin ma a sallame su har an kamo Dr. Zubairu, sosai yaji kunya sanda suka haɗu da su Abbu, musamman ma Big Dady tunda shi ne  abokin sa ƙwarai, haka yake ta sissinne kai kamar muna-fuki

Su kuwa basu bi ta kansa ba suka ficewar su. Kai tsaye gida suka wuce, sai da suka koma ne suka sanar da Kaka duk abinda ya faru

Gaskiya be ji daɗi ba, domin ya nuna ɓacin ran sa matuƙa a kan Hajja, wanda su kansu sun sha mamaki, duba da yanda Kaka yake son Hajja Fatu sosai, kasancewar ta ɗiyar abokin sa kuma ɗiyar ƙanwar sa, amma kuma sun san yanda yake matuƙar ƙaunar asibitin sa ba ya son ko kaɗan wani abu ya faru, yanzu idan duniya suka ji shikenan za'a fara ma asibitin baƙin fenti. Sosai yayi mata faɗa daga baya ya haɗa su yayi musu nasiha sosai ganin Abba yana ta kumbura da shirin ya aikata wani abun

Abba dai be bar wajen ba sai da ya kafa mata sharaɗi, domin yace "dole sai ta bar aiki," amma Kaka ya hana sa, shi kuma yace, "to idan haka ya sake faruwa wlh dole ba ita ba aiki a ko wani asibiti ba Asibitin su kaɗai ba, idan kuma tace a'a sai dai ba a ƙarƙashin sa take ba, tunda da sa hannun ta ake son ganin bayan asibitin su, da goyan bayan ta ake shigowa da ƙwayoyi tare da maganin asibiti, nan gaba ma da ita za'a haɗa baki da maƙiyan su don ganin bayan asibitin".

Abba fa ya shaƙa sosai, ba don Kaka ba babu me tanƙwara shi, sai dai su rabu da Hajja Fatu. Tunda shi Abba duk a cikin su ya fi su zafi, yana da sauƙin kai matuƙa, amma idan ya tashi faɗa ba ya ji ba ya gani, duk wani rashin son raini irin na mahaifiyar su shi ya biyo ta, ba ya shiga harkan mutum, to, kaima kar ka shiga nasa, yanzu zaka ga haukan sa matuƙa, shi kuwa Abbu sak Kaka ne babu ruwan sa, yana da sauƙin kai, haka ma Big Dady, shi kam ya fi su haƙuri, duk da shi ne babba yana da haƙuri matuƙa, idan ka ga yana faɗa kawai yana yi ne domin gyaran ƴaƴan sa, amma duk abinda zai faɗa zai yi wuya ya aikata shi a zahiri, idan ma kayi masa abu kafin zuwa anjima ya manta ransa yayi sanyi, sai dai idan zai ɗaure maka fuska domin ka koki gaba, shima sak halin Ummin sa ya biyo babu ruwan sa.

           Da haka magana ya watse, ranan dai Hajja ta ga banu, domin a zaune ta kwana, sosai hankalin ta ya tashi, ƙarshe ma washe gari ƙin zuwa aiki tayi.

    A ranan ne shi kuma Baffa suka dawo da Sa'adatu, tunda tun jiya da Hajja ta ba shi umarnin zuwa ya ɗauko ta be je ba sai sakaliyan yamma, to, a can ya kwana yau suka dawo.

       Fannin Shakira ma tun a asibiti Sahabi yaje ya bata haƙuri suka koma gida

Wannan dalilin ne yasa Hajja ta ɗan samu sukuni da matsalolin ta, tana ga kamar aikin Malam ya ci tunda ga shi komi ya zama normal Kan yaran ta, sai dai matsalan yana ga Abba, domin tun abin be sake kallon inda take ba, ya ƙi mata magana ya dena cin abincin ta, hakan yasa tayi tunanin why not ta Kai shi wajen Malam domin magance mata matsalan ta, wannan tunanin zuciyar nata tabi ta wuce kanta tsaye wajen Malam ko bi ta ƙawarta bata yi ba, shi ne kaɗai wanda zai iya mata maganin matsalan dake shirin afkuwa ita da mijin ta, wanda tana ganin ɓaraka ne babba da rashin yarda yake shirin Kunno Kai a tsakanin su, wanda kuma hakan ne babban tsaiko ga rayuwan ta, yardan Miji ya fi komi a rayuwar aure.





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

            *TURKEY*

       A kwanakin nan da suka shuɗe, Ɗahira tayi rayuwar ƙunci ba ni da ƙunci ba, ko kaɗan ba ta da walwala, ta zama tamkar wata wacce bata da gata, ta rame tayi baƙi kamar ba ita ba, bata da aiki kullum sai kuka da saka damuwa a ranta, ta kasa saba wa da halin da take ciki, komi na gidan ita take yi, da ta tashi da safe zata gyara gidan tayi wa kanta abinci domin shi ko bi ta kanta be yi bare tasa ran idan tayi abinci zai ci, bare kuma bata taɓa kwatanta hakan ba, ta gummaci ta girka ta zubar da tayi masa girki, ita take masa wanki da gyara ɗakin sa ko ina, idan ma bata yi ba ranan ya dinga caɓa mata magana kenan, kuma yace "idan bata yi ba sai yaci uban ta". Kalman cin uban ta shi yake matuƙar ɓata mata rai ainun, sai ta zauna tayi kukan ta son ranta ta share hawayen ta, haka zata yi masa wankin ta shanya masa a Toilet ta gyara masa ɗaki ko ina, domin ba ta son ko kaɗan ya sake taɓa lafiyan jikin ta, a haka take ta ƙare wa tana ciwo a tsatstsaye, kullum fama take yi da kanta sakamakon damuwan da ta kasa cire wa a ranta, kuma tun ranan da ya bata waya suka gaisa da ƴan gidan su be sake bata ba, sosai take buƙatar jin muryan ƴan gidan su amma ba hali, dole ta haƙura domin ko magana ba ta ƙaunar tayi masa bare ta tambaye sa wani abun

Duk idan taje gyara masa ɗaki, sai tayi binciken ko zata samu keey ɗin ƙofa, amma duk inda ta duba bata taɓa cin karo dashi ba, haka zata mayar masa da komi a muhallin sa ta gyara masa ta koma inda ya zame mata ɗaki, kusa da kichen. Idan damuwa yayi mata yawa sai dai tayi ta karatu, da dare kuma ko ishashshen barci ba ta samu illa sallah da take faman yi ko yaushe tana kaiwa Allah kukan ta

Rashin zaman Usman a gidan ya fi mata komi daɗi, tunda idan ya fita tun safe ba ya dawowa Sai dare, wani lokacin ta ɗan sami barci ya fizge ta, wani lokacin kuma idanun ta biyu zai shigo, ita yanzu har ta saba da duhun gidan, domin sabida tsaban mugunta irin nasa ya lalata komi na na'uran gidan, ko NEPA babu a gidan, bare dama ita ba gwanar kallo bane bare ya ɗebe mata kewa, haka take rayuwar ƙunci da duhu a gidan, koda da safe ne gidan babu wani haske sosai, sai idan ta yaye cootin, wani lokacin kuma sanyi ya addabe ta ta rasa yanda zata yi, dole ta mayar ta rufe.


           Yau ma tana kwance kamar kullum, ko kaɗan ba ta jin ƙwarin jikin ta, daƙyar take iya taɓuka wani abun saboda rashin ƙarfin jiki, ga ta ba auki ba

Tunda ya fita take kwance ta kasa yin komi, ko karya wa ta kasa, tunani ne kawai ta afka tana ta faman yi. Can kuma sai ga hawaye ya silalo mata a kunci, sai ta yunƙura ta miƙe ta nufi kichen kamar zata faɗi, ruwa ta samu ta dafa ta haɗa tea me kauri, shi ne ta samu ta ɗan sha ko zata samu ƙwarin yin aiki

Tana gama wa ta dawo parlour'n tana bi da kallo, ganin ba wani datti ne ba sai ta wuce kanta tsaye ɗakin sa, nan ne yayi mutsu-mutsu da gadon sa, duk ya jefar da kayan sa, haka ta tattare sannan ta gyara gadon, ta wuce Toilet ta wanke masa, wankin sa dake shanya tun jiya da tayi masa ta kwashe ta ninke, sai ta ɗaura masa a kan gado, kana ta koma Parlour ta shiga wanka, tana fito wa ta zira riga da skert ko lotion bata shafa ba, rabon ta ma da shafa wani abu a gidan nan tun lokacin da tayi ciwo, komi yanzu ya fitan mata a rai

Tana zaune tana gyara kayan nata tana mayar wa cikin akwati, sai ta jiyo motsin buɗe ƙofa, tsayawa tayi kawai tana kallon ƙofan, ta san ba ya dawo wa da rana shiyasa tayi mamaki

Shi ne kuwa ya shigo ciki, wani saurayi na biye dashi a baya. Be bi ta kanta ba ya shige ɗaki, yayinda saurayin nan sai bin ta yake yi da kallo, sai kuma ya gaishe ta da harshen turanci

Amma ko ci kanka bata ce mishi ba, illa ɗauke kai da tayi fuskar ta babu fara'a taci gaba da abinda take yi.

     Usman ne ya fito da Trolly  babba ya miƙa wa saurayin, dayake shi yake ba wa gugan kayan sa, duk kwana uku zai haɗa masa kayan ya zo ya amsa da safe kafin ya fita, yau kuma be zo ba sai yanzu, shi ne ya kira sa ya sanar masa zuwan sa, wannan dalilin ne Usman ya dawo domin ba shi kayan.

    Saurayin fita yayi da Trolly bayan sun Yi sallama, shi kuma ya koma ɗakin sa.

     Sanda Ɗahira ta gama gyara kayan nata, sai ta rufe Trolly ta janye sa gefe, kana ta koma ta jingina da bango ta lumshe idanuwan ta, ta hau tunanin da ya zame mata jiki, ko ta so bari ba ta iya wa.

      Can sai Usman ya fito da waya ya nufo inda take

Takun takalman sa dake tafiya da ƙarin bugun zuciyar ta, shi yasa ta buɗe idanu da sauri ta sauke su kansa

Fuskar sa ɗaure tamau ya miƙo mata wayan ba tare da ya ce uffan ba

Kamar kar ta amsa, sai kuma tayi tunanin ko gida ne, da sauri ta miƙa hannu ta amshi wayan, ilai kuwa gidan ne, mahaifin ta ne a kan layi.

     Yana kanta be tashi ba har ta gama wayan da mutanen gida

Itama ko kallon sa bata sake yi ba, kuma bata yi wani abun da zai saka yayi mata magana ba, bare ya sauke mata tijara, iyakan gaisuwa ya haɗa ta

Please Login or Register in order to submit comment