Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nata, zazzaɓi ne kawai ke damun ta"

Hankalin Big Dady ya ɗan kwanta, inda ya roƙi Doctor ɗin "da ya kula da ita sosai, kuma kar ya bata sallama da wuri har sai ta warware sosai".

Murmushi Doctorn yayi yace, "ok Sir, dama ba yau zan sallame ta ba".

Daga nan dai sun ɗan sake tattaunawa, inda suka yi sallama. Doctor ɗin ya miƙa wa Usman dake tsaye ya tsare shi da ido wayan sa

Shi kuma ya amsa ya tusa cikin aljihu, be ce komi ba ya juya yayi ficewar sa

Girgiza kai kawai Doctorn yayi a ransa yana cewa, "Dr. Man problems". Sai ya mayar da idanun sa kan Ɗahira dake barci tana fitar da numfashi a hankali, dayake yayi mata alluran barci ne, da alamun dai ta fara jin daɗin yanayin ta sabida yanda numfashin nata yake fita, kau da kai yayi kanta yaci gaba da aikin gaban sa.

       Zuwa dare ta farka, duk da jikin babu sauƙi sosai, amma tunda tana ƙarƙashin kulawar likita ne tafi da, an sauya mata ɗaki ita kaɗai ce.

       Da safe ko da Usman ya zo Hospital ɗin ko zuwa duba ta be yi ba, kasancewar asibitin da yake aiki ne

Doctor Shamel har office ya bi sa yana masa maganar Ɗahiran, da kuma yanda ya ga be je ya duba ta ba

Amma Usman ko bi ta kansa be yi ba, ce masa ma yayi "kar ya ƙara masa magana idan har ba sallaman ta zai yi ba".

Shi dai Doctor Shamel sosai yake mamakin wannan hali na Usman, ya san dai yarinyan tabbas ƙanwar sa ce, duba da yanda suke mugun kama, amma kuma abinda be sani ba "meye ta zo yi nan?" Shi ne abin da ke masa yawo, duk da ya san Usman ɗin ya bar Hospital ba ya aiki, dama yana mamakin dawowar sa da cewan "zai yi two months a ƙasar, that's why ya dawo aiki kafin ya tafi," to amma kuma yana kyautata zaton akwai abinda suka zo yi da ƴar uwan tasa. girgiza kai kawai yayi ya cire tunanin a ransa tunda be shafe sa ba. Sosai yake ba wa Ɗahira kula wa, inda take samun sauƙi a hankali

Gefe ɗaya kuma Big Dady ya kira har sau biyu don yaji jikin ta, amma sai Usman yayi masa ƙaryan "tana barci" don yaƙi haɗa su

Abbu ma ya kira tunda Big Dady ya basa Numban Usman ɗin, shima the same haka yace masa, "she was asleep at the time."

Sanda Big Dady ya sake kira, a lokacin Ɗahira tayi kwana biyu a asibitin, sosai ta samu sauƙi sai dai abinda ba a rasa ba, a lokacin ne Usman yaje har ɗakin nata ya bata wayan su gaisa da Big Dady

Lokacin Ɗahira na kwance ta juya wa ƙofa baya, tana sanye cikin fararen kaya na mara sa lafiyan Hospital ɗin, tunani me zurfi take yi idanun ta a buɗe ta ƙure wa waje ɗaya ido, babu abinda take kitsima wa illa yanda zata gudu daga Hospital ɗin nan a yau

Shi kuwa shigowar sa Direct gaban gadon ya isa, ya tsaya yana bin bayan ta da kallo, sai ya ɗauke kai yana haɗiyar yawu cike da ƙunci a zuciyar sa da ya rasa shi kwana biyu, tamke fuska yayi sosai kana yace, "keee".

Hakan yasa ta ɗan yi firgigit ta dawo hayyacin ta, sai tayi saurin juyo wa tana kallon sa, sosai ƙirjin ta ya buga saboda kawai sauke idanun ta da tayi a kansa, zuciyar ta nan da nan ta sauya bugu kamar zata faso ƙirjin ta tsaban buga wa da ƙarfin da take yi. Ƙyafta idanu ta hau yi sai tayi saurin janye su daga kallon sa, sakamakon kallon da yake sakar mata da yanda take ji

Shima be ce komi ba illa latsa wayan sa da yayi ya kira Big Dady, ya miƙa mata ba tare da ya ce uffan ba

Ɗan ɗago kai tayi ta kalli wayan, kana kuma ta saka hannu ta amsa tana me kara wa a kunne, a lokacin Big Dady ya amsa call ɗin yana faɗin "Hello Daughter"

Kallon sa tayi ganin yanda ya tsaya mata ƙiƙam kamar zai faɗo mata, sai dai ya mayar da fuskar sa na mara sa mutunci, wanda kamar ƙiris yake jira. haɗiye yawu tayi tana sauke kai ta amsa da "na'am Dady". Cikin sanyin murya irin na mara sa lafiya

Nan Dady ya soma tambayar ta jikin ta

She replied, "Very easily Daddy, sai dai missing ɗin ku da nake yi".

Murmushi yayi yace, "kar ki damu Daughter ai kun kusa dawowa, ke dai kawai ki kula da jikin ki kinji? ba na son in sake jin an ce min baki da lafiya, na san halin ki idan kin saka damuwa ne a ranki yake saka ki ciwo, duk idan kin ji wani abu na damun ki just tell your brother kinji?"

Lumshe idanu tayi wasu zafafan hawaye suna zubo mata, lokaci ɗaya ta gyaɗa kanta kamar yana ganin ta, cikin raunin murya tace, "to.." tana datse baki jin kuka na son kufce mata

"Yauwa Daughter, bari in ba wa Abban ki ku gaisa, muna tare da Baba ne (Kaka)".

"To". Ta sake amsa wa cike da murna, domin sosai take son jin muryan kowa a gidan su, musamman Maman ta da Abbun ta, tayi kewar su matuƙa

Gaisa wa suka yi da Abba, inda shima ya tambaye ta jikin ta, sannan yayi mata nasiha sosai a kan biyayya ga miji, tare da ƙara haƙuri a rayuwa

Ita dai jin sa kawai take yi, a ranta tana jin kamar ya san halin da take ciki, "ina ma zata iya sanar da su halin da take ciki?" Amma tsoro da fargaba ya hana ta furta abinda take son faɗa

Daga nan Kaka ya amshi wayan, sun jima suna waya, inda take ta mishi shagwaɓa a kan "ita lallai lallai tana son dawowa gida ta gan shi" sosai take kuka a wannan lokacin domin ta kasa tsayar dashi

Usman dake tsaye yana kallon ta, hannu ya saka ya dalla mata a gefen kumatu

Inda ta saki ƙara tana ƙara ɓare baki

Kaka da duk ya ɗauki abin nata kawai tsaban rigima ne irin nata, sai yayi dariya yace, "ki yi haƙuri Mata ta, duk da kina kewa ta amma na san Real Mijin ki ya fi Ni buƙatar ki, ki yi haƙuri har ku dawo kinji? nima nayi kewar ki sosai, ji nake yi kamar in biyo ki nima". Shima ya ƙare maganar ta sigan wasa

Kuka ta sake fashe wa dashi, tana shirin magana Usman ya ƙwace wayan

Inda ya kara a kunne yana cewa, "wai tsoho meye haka kake saka ta kuka?" Ya ƙare maganar da dalla mata harara

Ita kuwa sake fashe wa da wani sabon kukan tayi

hakan yasa ya saka hannu ya damƙe mata baki tare da hancin ta

Zaro idanu tayi ganin zata shiɗe, nan da nan ta soma kokawar cire hannun sa tana son shaƙar numfashi, amma ina ya saka ƙarfi sosai ya tamke ta yanda baza ta iya ƙwace wa ba, sai uhmmm.. uhmmmm take yi tana dukan hannun nasa, tare da sake ware idanun ta dake tsiyayar hawaye sosai

Tsaki yaja yana sauraron Kakan dake masa tsiya, a daƙile yace, "kar ka cinye min kuɗi na sai an jima". Ya katse kiran ba tare da ya jira cewar sa ba. Maida hankalin sa yayi kanta yana kallon ta da fuska a ɗaure, sai kuma ya janye hannun sa yana sake sakar mata wani banzan kallo

Ita kuwa cikin kuka tace, "wai don Allah me nayi maka da zafi haka da kake son kashe Ni? Idan har ka tsane Ni ne meyasa baza ka ɗauki wuƙa ka daɓa min ba a kan wahalan da kake ba ni?" Cikin tsawa ta sake cewa, "ka sake Ni mana tunda ba ka ƙauna ta, wlh nima ba na son ka ko kaɗan, I hate you more than anyone in this world! Sai Allah ya saka min bazan taɓa yafe maka ba! I hate you so much USMANNN". Ta ƙare maganar da wani irin kuka me ban tausayi

Sosai ransa yayi mugun ɓaci da maganganun da ta faɗa masa, ba kaɗan ba yaji ɗacin yanda take kallon ƙwayar idanun sa take sanar masa ba ta ƙaunar sa, "ita wace ce da ta isa ta kalle sa ido cikin ido tace masa ba ta ƙaunar sa" a zuciye ya saka hannu da ninyan cafke mata gashi, sai wayan sa ta soma ƙara, wanda hakan ya dakatar dashi yana bin wayan da ido

Mahaifin ta ne ya kira, sai ya ja dogon tsaki yana daka mata tsawa.

        
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.

        *EPISODE Forty Six*

        "Wlh idan baki rufe min baki ba sai nayi ƙasa-ƙasa dake a nan, bar ganin kina kwance a nan sai na ɓalla miki ƙasusuwa, mahaifin ki zai yi magana da ke, idan kika sake kika yi wani motsin da zai sa ya gane wani abu.. uhm wlh I will teach you a lesson".

Cak ta tsayar da kukan nata jin ya kirayi mahaifin ta, da sauri jikin ta na rawa ta kai hannu ta amshi wayan da yake miƙo mata, muryan mahaifin ta taji ya doki kunnen ta, sai ta lumshe idanu tana me tsiyayar da hawaye, cike da sanyin murya take gaishe sa zuciyar ta cinkushe da kewar sa

Nan ya tambaye ta jikin nata?

Ta amsa mishi tana faɗin, "taji sauƙi sosai". Kana ta soma jero masa tambayan "ina su Maman ta da su Umma? Har Fadil sai da ta tambaya"

Abbu yace mata, "babu su Fadil kusa, amma ga Maman ta su gaisa".

Jin muryan Maman ta sai ta fashe da kuka tana me kiran sunan ta

Daga can Aunty Amarya tace, "har yanzu dai kin kasa girma ko? Kukan na mene ne?"

"Nayi kewar ku ne sosai Mama, don Allah ki saka baki ya dawo dani".

Aunty Amarya ta gane wa take nufi, sai tace mata, "ke baki da baki ne? Duka-duka yaushe kuka tafi? Idan kin yi haƙuri nan ba da jima wa ba kamar yau ne za ku dawo, Allah ya muku albarka baki ɗaya".

"Amin Mama". Ta amsa ta tana me share hawayen ta da bayan hannu

Daga nan Aunty Amarya sallama tayi mata

While Usman ya amshi wayan sa, sai da suka yi magana da Abbu kafin ya kashe wayan. Ya dube ta fuska a tamke yace, "tashi mu je".

Ko kallon sa bata yi ba, illa sake haɗe kai da gwiwa da tayi ta saki wani Marayan kuka, domin wayan nan da suka yi ba ƙaramin fama mata zuciya yayi ba, sosai take kuka kamar ana yanka ta, har wani shashsheƙa take yi

Hakan yasa ran Usman yayi mugun ɓaci, ya daka mata tsawan da ya razana ta lokaci ɗaya

A dai-dai lokacin ne Doctor Shamel ya shigo ɗakin, da mamaki yake bin Usman da kallo, sai yace, "what's going on?"

"Ka bamu sallama zamu wuce gida yau".

Murmushi Doctor Shamel yayi, cikin harshen turanci yace, "my friend ban da abun ka ka barta mana ta samu sauƙi, ka ga har yanzu da sauran rashin lafiya a tare da ita".

Usman be kalle sa ba ya saka hannu ya riƙo nata, jan ta ya soma yi dole ta sauko a kan gadon tana ci gaba da kuka

Dr. Shamel yace, "Oh Man, leave her. Don't hurt her. You see her crying. Maybe it's her body."

Shi dai be saurare sa ba tuni yayi waje da ita, be sake ta ba har sanda ya isa da ita motan sa, ya buɗe mazaunin gaba ya tura ta ciki, sannan ya rufe ya saka lock

Babu abinda Ɗahira take yi sai kuka tana me tsine masa a zuciya, har ya koma cikin asibitin ya dawo bata dena kukan ba

Yana shigo wa ciki ya daka mata gigitacciyar tsawar da dole ta ɗauke kukan cak a lokaci ɗaya

Be yi magana ba ya kunna motan ya nufi bakin Gate, sosai zuciyar sa take masa ƙunci, gaba ɗaya jin sa yake yi babu daɗi, yanda yayi ta ɗaga mata murya yana mata tsawa sai duk hakan ya saka masa ciwon kai, hakan yasa ransa ya sake ɓaci matuƙa, a wuya kawai yake yana jiran yayi maganin ta

Sai dai Allah be sa ta sake ko ƙwaƙƙwaran motsi ba, illa ajiyan zuciya da take ta sauke wa idanun ta a lumshe, yayinda ta ɗaura kanta saman cinyoyin ta.

     Suna isa gida tana jin ya tsayar da motan ta ɗago kai, sai ta buɗe motan ta fice da sauri, tana jin sanda ya ja dogon tsaki amma ko bi ta kansa bata yi ba, haka ta nufi ciki da sauri, sai dai dole ta tsaya har sai da ya zo ya buɗe ƙofan, jefa mata magungunan ta yayi dake cikin leda, sannan ya buɗe ƙofan, sai da ya tasa ƙeyan ta ciki kafin shima ya shiga

Tuni ta isa wajen kayan ta ta nemi wuri ta zauna saboda har yanzu tana ɗan jin jiri

"Ki gyara min gida tunda ke ƙazamiya ce, daga yau ba na son in sake ganin baki yi aikin da ke kanki ba, sannan wankin kaya na suna nan ki wanke min su na zuba miki a kan gado na, akwai igiyar shanya cikin Toilet ɗina ki shanya a ciki". Yana gama maganar yayi waje ya fice, tare da rufe ta ta waje

Lumshe ido kawai tayi tana me jingina bayan ta da bango, sosai ranta ke suya sai dai babu yanda ta iya, ta san haka zata ƙare da uƙuban sa har sanda Allah zai yi su koma, "yau har akwai ranan da wani zai iya buɗe baki yace mata ƙazamiya?" Sai ta ɗan yi murmushin da yafi kuka ciwo tana me buɗe idanun ta, babu yanda zata yi dole ne tayi masa abinda yace, ko da kuwa wani ciwon ne zai kama ta, domin dai ta san wulaƙancin da zata fuskanta sai yafi halin da take ciki.

      Sai da ta ɗan samu hutu sosai, kana ta tashi ta shiga kichen, tea ta haɗa me kauri ta zo ta buɗe magungunan ta, inda ta cire Waɗan da zata sha, ta shanye da tea ɗin, sannan ta miƙe ta wuce ɗakin sa, gaba ɗaya babu ƙarfi a jikin ta, amma haka ta daure ta kwashe wankin da ta gani a saman gadon, Allah yasa ba masu yawa bane, ta nufi Toilet da su, akwai engine machine a ciki, amma ko da ta gwada yi a ciki ya ƙi yi; domin ya lalace. Sai ta cire ta saka a bucket, komi na buƙata akwai a wurin, haka ta zauna ta wanke masa tas har Singlet da ƙananan wanduna, zuciyar ta na tafarfasa har ta gama, shanya masa tayi kana ta fita ta je ta kwaso nata ta wanke a Toilet ɗin, sannan ta shanya a Toilet ɗin Parlour, tana gama wa ta gyara masa ɗakin sa, duk da babu datti sai dai gadon da ya yamutsa

Bayan ta gama ta share Parlour ta Yi moping, zuwa lokacin gaba ɗaya ta gama gajiya, kamar dai wani zazzaɓin ne ke son kama ta; tunda bata gama warke wa ba, zama tayi ta huta sannan tayi alwala ta gabatar da sallan azahar, kasancewar sauran sallolin da ake bin ta duk tayi su a Hospital, sai ta ɗan kishingiɗa zuwa sallan Asar.

     Sai biyar ta farka, nan kuwa ta sake jin daɗin yanayin ta, wanka tayi tare da Sallah, ta shiga kichen ta yi ma kanta girki sannan taci ta koma tayi shimfiɗa ta sake kwanciya, tana nan tana tunani har magriba tayi, sai da tayi sallah kafin ta soma muraji'ar Al'ƙur'ani, da kai take yi domin bata san inda zata samu ƙur'ani ba, dayake akwai hasken NEPA ko ina, hakan yasa ta ɗan ji daɗin zaman bata ji tsoro ba, sai da aka yi isha'i kafin ta kwanta tayi lamo, yanda tunani ya cika mata zuciya sai ta tashi zaune ta ɗauko ruwa ta sha magungunan ta, sannan ta haɗa dana barci da aka saka mata, sai ta koma ta sake kwanciya, babu daɗe wa barci ya sure ta, dama haka tafi so domin ba ta ƙaunar ya dawo ta ganshi.

     Sai goma na dare kamar yanda ya saba dawowa ya dawo, be bi ta kanta ba ya shigewar sa ɗaki, shima shirin barcin sa yayi ya kwanta abin sa.



            *WASHE GARI*

     Sai da ta bari ya bar gidan kafin ta tashi tayi wanka ta shirya cikin riga da skert na atamfa, sai ta saka Baby Hijab ta shiga kichen, Breakfast tayi wa kanta taci ta koma ta zauna, yanda ta ga babu abinda take yi sai zaman banza da tunani, hakan yasa tayi ta karatun Alkur'ani, kasancewar ta ba ma'abociya son kallo ba, ko kaɗan be dame ta ba, idan har ba wani ya kunna ta zo wurin ba, to ko kaɗan ba ta bi ta kai bare ta tuna dashi

Kuma zaman gidan ma yayi mata daɗi tunda Usman ba ya zama, sai hakan ya saka ta farin ciki ainun, gwara kar ya dawo tayi ta zama ita kaɗai da ta ganshi a cikin gidan.







⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫



              *NIGERIA*
   

       Fitowa tayi daga ɗakin majinyata na yara, kai tsaye ta nufi Office ɗin Hajja Fatu

Ita kuma a lokacin tana shirin fita daga Office ɗin nata

Safna tayi saurin dakata wa tana me ce mata, "Dr yaron nan fa ya farka, yanzu time ɗin ba shi maganin sa ya yi, kuma na duba lockern gadon sa babu komi".

Tsaki Hajja Fatu taja, tana bin Safnan da harara tace, "ke dai wlh baza ki taɓa sauya wa ba, ban san wani irin yarinya ce ba, common dalla shige ki ɗauka ga yi can, Ni Bani da time ɗin ki". Da gama faɗar hakan; sai ta wuce ta tafi

Murguɗa baki Safna tayi tace, "kai wannan Matar kullum jaraba, bazan sauya ba ko baza ki sauya ba? Ni ban san me na tare miki ba wlh".

A Haka Safna take ta mita a ranta har ta ciro maganin cikin wani kwali da ke ajiye tsakar Office ɗin, domin ta duba ma'ajiyar maganin bata ga komi ba, tana buɗe kwalin sai ta ga kamar shi ne, bata tsaya bincika wa ba tayi waje da sauri. Kai tsaye ɗakin yara ta wuce, inda ta je kan wani yaro dake kwance magashiyan Mahaifiyar sa na riƙe da shi, haɗa maganin tayi ta ba shi, sannan tayi masa alluran da ta haɗo dashi, kana tayi wa matar sallama ta wuce gadon gaba, duk sai da ta tabbatar babu wani matsala kafin ta fito ta nufi Office ɗin ta, haɗa kayan ta tayi tunda lokacin tashi yayi, tana fito wa ta wuce Lifter tayi downstairs. A reception suka kusa cin karo da Baffa, tayi saurin matsa wa tana ba shi haƙuri

Be bi ta kanta ba ya yi waje abin sa, motan sa ya hau ya bar Office ɗin, gaba ɗaya idan ka kalle sa duk ya gama sauya wa, tamkar ba shi ba, yanzu kwata-kwata ba ya da fara'a, be son yawan yin magana bare dariya, wuni yana kaɗaita kansa yana faman tunanin Ɗahira, har yanzu yayi iya yin sa ya kasa cire ta a rai.

     Yana zuwa gida kai tsaye ɗakin sa ya wuce ya buɗe ya shige

Ƙaran buɗe ƙofan nasa ne ya janyo hankalin Sa'adatu dake zaune a ɗakin ta, sai ta fito ta nufi ɗakin nasa kanta tsaye, domin yau so take yi ayita ta ƙare; ta gama gajiya

Shiga ɗakin tayi ko sallama

Baffa dake duƙe a bakin Fridge yana shirin buɗe wa domin ɗaukan win ɗin sa, sai ganin ta yayi a cikin ɗakin sa, hakan yasa ya dakata da abinda yake yi yana bin ta da mugun kallo

Ƙarisowa inda yake tayi tana cewa, "Baffa Ni fa na gaji da abubuwan da kake min a gidan nan, na gaji wlh, yau sai dai ka faɗa min matsayi na a wurin ka, don bazai yiwu ina zaune a matsayin matar ka ba amma ka maishe Ni tamkar ba kowa ba, babu wani zaman soyayya, kullum ba na sanin halin da kake ciki, idan ka saka ƙafa ka fita ba ka dawo wa sai sanda ka ga dama, kuma idan ka dawo sai ka ƙule ɗakin ka ka rufe kanka baza ka bar Ni na shigo ba, kai kuma ba ka zuwa ɗaki na, ba ka cin abinci na, wannan wani irin rayuwa ce? In CE dai aure na kake yi ba wani abun ba?"

Da mugun kallo kawai yake bin ta be da ninyan cewa komi, haka ya miƙe ba tare da ya buɗe Fridge ɗin ba yayi bakin gado ya zauna

Hakan da yayi mata sai ta zuciya ta isa gaban sa tana girgiza tace, "wai don Allah me nayi maka ne da zafi da ka dena min magana? Wlh idan har baka sauya ba zan bar gidan nan, tunda kai ba ka ƙauna ta ai iyaye na suna so na".

"To dama na riƙe ki ne? Ki fi ruwa gudu mana, ki fice min a ɗaki da Allah ina da abin yi".

Kuka ta fashe dashi tace, "wlh bazan fita ba, sai ka faɗa min abinda nayi maka ka sauya min, idan ba haka ba ƙaran ka zan kai wajen Abba tunda ka dena jin maganar Hajja".

Miƙe wa yayi ya kama hannun ta ya ja ta zuwa waje, ya tura ta yace, "ki je ki sanar wa Baban Abba ba Abba ba, dama Ni na gaji dake". Ƙofan ya maida ya rufe, har da saka keey

Nan Sa'adatu ta dinga dukan Ƙofan tana kuka tana faɗa masa magana, "wai don ya ga ya gama da ita dole yace zai yar da ita, to wlh sai ta zubar da cikin jikin ta don baza ta haife sa ba".

Yana jin ta amma be tanka ba, illa ma ɗauko win ɗin sa da yayi ya hau kurɓa wa

Har ta ƙarishe fitinar ta ta shige ɗakin ta, harhaɗa kayan ta ta hau yi tana kuka, bayan ta gama ta ja Trolly ɗin zuwa wajen motan ta, "wlh yau sai na bar gidan nan, na gaji da wulaƙancin da Baffa yake min kuma Hajja ta kasa ɗaukar mataki, babu dole auren". Ta faɗa tana ci gaba da kukan ta, tana saka kayan ta ta shige taja motan ta ɗauki hanyar Lagos, duk da ta san dole dare zai yi mata a hanya amma hakan be shafe ta ba, Fatan ta kawai ta isa gidan su ta sanar wa da Momyn ta komi.



          Shi kuwa Baffa be ma san wainar da take toya wa ba, ƙarshe ma da giyan ta bugar da shi; barci ya hau yi, be tashi ba kuwa sai dare, alwala kawai yayi ya nufi masallaci ya gabatar da sallolin da ya wuce sa, inda daga nan ya wuce Part ɗin iyayen sa

A nan Hajja take tambayar sa "ina Sa'adatu?" Domin yau kwata-kwata bata shigo sun gaisa ba

Sai ma lokacin shi ya tuna da ita, sai yace mata, "tana ɗaki".

"To amma dai kana kula da ita ko? Ka san me ƙaramin ciki dole sai ana bata kula wa, kuma har yanzu ƙorafin ta ɗaya ne ka ƙi ka koma yanda kake, kaji tsoron Allah Baffa, wlh akwai ranan da Allah zai tambaye ka".

"Hajja ki dena min irin haka don Allah, ai kullum jin tsoron sa nake yi, da ba na jin tsoron sa da bata kawo iyanzu a ɗaki na ba".

"Au iyeeeee? Me kake nufi to?".

Kumbura baki yayi yana shafa ƙeya yace, "to ke ne ai Hajja da wani magana, ke ma kin san ba na son ta, ban taɓa son ta ba, ga wacce zuciya ta take so can amma kika liƙa min ita".

Hajja tace, "lallai kam wuyar ka ta isa yanka Al'ameen, yau kuma rashin kunya zaka yi min? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibatin.."

Miƙe wa kawai yayi ya fice ba tare da ya sake tanka mata ba

Sai kawai Hajja ta fashe da kuka tana cewa, "eh lallai A'ishah, kin rantse sai kin ga bayan ɗana, yanzu ji be yanda kika mayar min

Please Login or Register in order to submit comment