Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zo ya tarar da ita zaune cikin ruwan aman tana ta rawan sanyi. Tunda ya shigo ya sauke idanun sa a kanta ya haɗe giran sama dana ƙasa yana jin zuciyar sa na sake ƙunci, take ya nufe ta gadan-gadan yana cewa, "baki ji abinda nace miki bane kafin in fita? Ke me taurin kai baza ki yi abinda nace miki ba ko?"

Ta ma kasa yin magana illa kallon sa da take yi, domin ji take yi idan ma ta tanka sa tabbas zuciyar ta zata buga da baƙin ciki, shiyasa ta rufe idanun ta tana jiran abinda zai yi mata

Tsawa ya daka mata yana cewa, "ki tashi ki gyara min gida ko in ci uwar ki a gidan nan".

Sosai ta tsorata da tsawan da yayi mata, ta zabura zata tashi, sai dai ta kasa sabida rawan da jikin ta yake yi, da zaran ta yunƙura zata miƙe sai ta zame ta bugu a tyles ɗin parlour'n, hakan yasa ta fashe da kuka tana rawan baki, tana son furta masa baza ta iya ba amma ta kasa

Hannu yasa ya janyo ta kiiiiiiiii... ya ingiza ta cikin Toilet ɗin

"Maza ɗauki mopper ki gyara min gida ko in Yi biji-biji dake yanzu". Ya sake daka mata tsawa

"Me..yasa.. ba ka da tau..sayi ne wai? Me.. me nayi maka.. ne? Ka bar Ni na koma ggida tun..da.." sai ta kasa ƙarisa wa saboda kukan da take yi

Idanun sa jawur ya aza kanta yace, "ai baki ga komi ba daga abinda na shirya miki, Ni dai kika aura ko?" Sai ya karkaɗa kai kafin yace, "Wlh daga ke har waɗanda suka aura min ke sai na sa ku kun yi dana-sani, kamar yanda kika ƙuntata min rayuwa, ke ma sai na ƙuntata miki". Sai ya juya da ninyan fice wa, har ya fita ya dawo ya sake nuna ta da yatsa yace, "ki gyara min gida a karo na ƙarshe.." ya juya ya fice da sauri. Direct ɗakin sa ya wuce ya shige Toilet, shower ya kunna ya shiga ruwan na zubar masa daga sama zuwa ƙasan shi, zafin da yake ji a zuciyar sa ji yake yi kamar ana ƙara masa icce yana ruruwa, duk da ruwan sanyin dake dakan jikin sa, amma ji yake yi ko kaɗan babu sauƙi, dauriya me dauriya ya gwada yin sa amma ina, kawai sai ya fashe da kuka, domin ji yake yi idan be je ya kashe ta tsaban tsanar da yake mata ba, bazai taɓa sukuni ba, abinda yake ji tun ɗazu kenan amma ya kasa daure wa

Nan tunanin addu'a ya faɗo masa, ya soma lalubo abinda zai faɗa, daƙyar harshen sa yake iya faɗin, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..." Ya ƙame ƙam a wajen yana ci gaba da karanta wa a ƙasan zuciyar sa, ya daɗe a haka kafin ya soma jin abunda ke zuciyar sa yana lafa masa, daƙyar ya tuɓe kayan jikin sa ya yi wanka ya fito, a haka ya zube kan gadon sabida rasa inda yake masa daɗi a jiki.

      Ita kuwa baiwar Allah Ɗahira tunda ya bar ta take kukan ta, sai da tayi ma'ishi kafin ta yunƙura ta tashi, a duƙe- a duƙe ta soma kwatanta aikin ko zata iya, har dare ya tsala tana abu ɗaya, gaba ɗaya ta gama jiga ta, har faɗi take yi tsaban wahala, sai ta tashi taci gaba, aikin da zai ɗauke ta mintoci, sai ga shi ta shafe tsawon daren tana yi, daga ƙarshe ta zube a ƙasa tare da rufe jikin ta, taci gaba da rawan sanyi, bata ko runtsa ba sabida azaban ciwo, a haka safe ya cin mata, zuwa lokacin baza ka taɓa gane Ɗahira ce ba, sabida yanda gaba ɗaya ta zabge tayi wani irin muguwar rama, idanuwan nan nata sun sake fito wa sun koɗe sun yi zawur, dama ga ta ba auki ba haka ta sake sirance wa gunun tausayi, tamkar wata ƙaramar yarinya ce a kwance a wajen

Har haske ya gama fito wa bata iya tashi ba, yunwa ke addabar ta amma ta kasa yanda zata yi ta nemi abinci, jikin ta yayi zauu kamar garwashin wuta, sai karo take yi da haƙora.

        A haka Usman ya fito da shirin sa, tunda ya kalli inda take sau ɗaya ya tabbatar da ta gyara wajen, sai ya ɗage kai yai ficewar sa.

   Lumshe idanuwan ta kawai tayi tana sake lafe wa a ƙasa, bata san wani tunani ya kamata tayi ba, bata taɓa tunanin akwai wani rayuwa da zata iya shiga har taji tana ƙaunar mutuwar ta ba, sai a wannan gaɓar, tayi dana-sanin amince wa da auren nan, tabbas da tasan irin azabar da zata tarar kenan; da tayi guduwar ta, da dai ace ta zauna da wannan mara tausayin, ko kaɗan bata taɓa tunanin ƙiyayyar da yake mata ya kai har haka ba, da ya gummaci ganin mutuwar ta da rayuwar ta, tabbas yau tana kaico da rayuwar ta da ta kasance a ƙarƙashin maƙiyin ta tana me neman lahirar ta, kuma bata da hanyar da zata iya kufce wa hakan

Sai ta sake fashe wa da wani irin kuka me ban tausayi dake fito wa daga can ƙasar zuciyar ta yake ƙara mata raɗaɗi da ƙunci me ciwo, tuna wa da tayi da iyayen ta, sai dai ga shi tayi musu nisa babu yanda za'a yi ta fita ta koma gare su, suna can ba tare da sun san halin da take ciki ba. Tasha kukan ta ma'ishi babu me rarrashin ta, inda ta wuni curr a kwance bata san inda kanta yake ba, domin kuwa wani sabon zazzafan zazzaɓin ne ya sake rufe ta, abun ka da bata saba da damuwa a rai ba, haka ta wuni zuciyar ta na mata zafi kamar ana soya mata, daƙyar take iya numfashi, har dare kana wani wahalallen barci ya sure ta, wanda be da maraba da suma, domin kuwa gaba ɗaya numfashin ta ba ya fita da kyau, idan ta ja numfashi sau ɗaya; sai ta shafe fiye da second biyar kafin ta sake jan wani.



             ***** ***** *****

           Sai wajen ƙarfe 10:40pm. Usman ya shigo gidan, be kalli inda take ba ya wuce kai tsaye ɗakin sa, zama yayi gefen gadon sa yana zare Cumbas ɗin ƙafafuwan sa haɗe da socks ɗin, yana gama wa ya cire wrest watch ɗin hannun sa ya ajiye, sannan ya miƙe ya kwaɓe kayan sa ya shige Toilet, wanka yayi ya fito ɗaure da alwala, sallan isha'i yayi da be samu yayi ba, sai ya koma kan sofa ya zauna yana latsa laptop ɗin sa, har yayi kamar mintuna biyar, ko me ya tuna ya miƙe ya ɗauko wayan sa dake ajiye gefen bed side, ya soma latsa wa, kai tsaye WhatsApp ya shiga yana bincike a kan sakon da Friend ɗin sa ya turo masa, a nan tunanin mutanen gida ya faɗo masa, sai ya ɗan dakata yana kame goshin sa, shaf ya manta da wani kiran gida a rayuwar sa, ga shi har suna son wuce sati ɗaya da barin gida ba tare da ya kira ba, tabbas ya san akwai matsala, domin ya san yanzu haka suna nan sun damu, duba da yanda ba shi kaɗai bane ya taho. Tsaki yaja yana fita daga WhatsApp ɗin, shiru yayi yana tunanin Numban wa zai kira

Still tsakin ya kuma ja tuna wa da yayi ba Numban sa da yake amfani bane a wayan, tabbas ya san sun neme sa ba su same sa ba, Kai tsaye Numban Hajiya ya rubuta ya kira

Tana ɗauka abin da ta soma tambayar sa, "shin ina ya shiga tsawon wannan lokacin be kira su ba?"

Be bata amsa ba, sai ya soma gaishe ta a daƙile kamar yanda ya saba

Amsa wa tayi tana sake jeho masa tambayar farko

Sai yace mata, "wai be samu time bane, sabida ya koma Hospital ɗin da yake aiki yana ci gaba da zuwa har sanda za su dawo".

Ajiyan zuciya kawai ta sauke, ko kaɗan bata damu ta san halin da Ɗahira ke ciki ba, sai ce masa tayi "to yaushe kenan kake sa ran dawowa?"

"Kamar nan da Two months".

Dogon tsaki taja, cike da ɓacin rai tace, "wato ta shanye ka shi ne zaka kai har wannan lokacin baka dawo ba? Uwar me kuke yi da baza ka dawo ba sai ka kai lokacin nan?"

Shiru yayi mata be tanka ba

Kamar yanda itama bata sa ran zai tanka ɗin ba, amma sai ta sake cewa, "ina magana kayi min shiru, ko cin amarcin ne har yanzu baka gama ba sai zuwa nan da two months ɗin?".

"Momy na ce miki aiki na koma shiyasa". Yayi maganar kamar zai yi kuka

"Mtsww! dalla rufe min baki, meye amfanin aikin tunda ka ajiye? To, Ni ban amince ka kai tsawon wannan lokacin ba, yarinyan da ba ka so meye kuma na zuwa da ita wani waje? Ka gaggauta shirin dawowa tun yanzu domin hutun ya isa haka, kuma ka kira Dadyn ka yanzu domin suna ta neman ka su ma basu same ka ba, ga Kakan ku can har rashin lafiya ya yi amma baka da labari".

"Ok". Kawai yace mata saboda be da abun cewa, ba kuma wai don ya yarda zai yi abinda take so ɗin bane na game da dawowar sa

Sallama suka yi, inda ya mayar da akalan kiran ga Mahaifin sa, ringing biyu ya ɗauka, gaishe shi ya soma yi

Amma Big Dady be amsa ba, sai ya fara jeho masa tambaya kamar yanda Hajiya tayi masa, "me ya tsayar dashi tsawon lokacin nan ba tare da ya kira gida an ji sun sauka lafiya ba?"

Be da amsar faɗa masa, illa shiru da yayi

Nan kuwa ya dinga mishi faɗa, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, sannan daga ƙarshe yace masa "ya ba wa Ɗahira wayan".

Duk da maganar ta bugi Usman, amma hakan be sa ya nuna akwai wani ruɗe wa a tattare dashi ba, illa gyara murya da yayi ya ce masa, "uhmmm Dady tana barci yanzu haka, sabida nan dare ya soma nisa"

"Ok ka tabbatar gobe idan ta tashi ka haɗa Ni da ita".

"To". Ya amsa masa

"Ka kira wayan Kaka sabida yanzu ba na gida bare na faɗa masa ka kira". Cewar big Dady

Amsa mishi yayi, sannan suka yi sallama. Inda ya kira Kaka. A lokacin Fadil ke zaune dashi tunda jikin nasa da sauƙi, sai abinda ba a rasa ba

Nan Kaka yayi murna da jin suna lafiya, ya tambayi Ɗahira yace, "a bata wayan"

Sai ya faɗa masa yanda yace wa Big Dady.


      Koda suka gama wayan tsaki yaja fuska babu walwala, ya ajiye wayan, kasa ci gaba da aikin yayi sabida ransa duk a ɓace yake, ya tashi ya sauya kaya zuwa gajeren wando da Singlet ya kwanta.


            *WASHE GARI*

        Da safe da ya tashi, zuwa ƙarfe 09:00am. Ya gama shirin sa, ya fito Parlour, inda Ɗahira take kwance ya kalla, sai ya kawar da kai yana tamke fuska kamar an aiko masa da saƙon mutuwa, kai tsaye kichen ya nufa, ya haɗa coffee ya shanye a kichen ɗin, sannan ya fito ya nufi ƙofan fita, har ya buɗe ƙofan; ko me ya tuna ya dawo da baya ya nufe ta

Tana nan kwance kamar yanda ta kwanta tun jiya, tun barcin da ya ɗauke ta a yammacin jiya bata ko motsa ba, kallo ɗaya kayi mata zaka gane tana shan matuƙar wahala, daga gani ba barcin lafiya bane, duba da yanda take haɗa gumi tana fitar da numfashi da ƙarfin gaske, kuma duk da uwar gumin nan da take yi amma hakan be hana jikin ta rawan ɗari ba.

       Yana zuwa kusa da kanta, ya sanya ƙafa ya bugi kan nata

Wani irin zabura tayi tana sakin ƙara, lokaci ɗaya ta buɗe shanyayyun idanun ta da suka kaɗa suka yi jazur suka shige ciki tsaban kumburan da suka yi, dafe kanta tayi saboda sara matan da yayi lokaci ɗaya, sai wani jiri da ya kawo mata mamaya lokaci ɗaya ta koma yanda take tana me runtse idanun ta da suka soma ruwan hawaye, ko kaɗan ta kasa buɗe ido balle ta kalli inda yake, duk da kuwa ta san shi ne a kanta sabida ƙamshin turaren sa da ta jiyo, kuma ta san babu wanda zai mata haka sai shi

"Get up and sit down". Yayi maganar kamar ana masa tilas, sai dai yanda muryan nasa ta fita hakan zai saka ka gane a cikin ɓacin rai yake

Bata motsa ba don bata da ƙarfi ko na sisin kobo, kamar dai an zare mata laka a jikin ta take ji, kamar kuma ana yayyanka naman jikin ta saboda mugun ciwon da yake mata, ga rashin sabo na kwanciyar ƙasa, duk ya bi ya haɗe mata ya saka mata wani irin ciwo me wuyan fassara, ji take yi tamkar dai ta mutu ta huta

Tsawa ya daka mata yana sake bata umarnin tashi

Babu yanda ta iya dole ta soma yunƙurin tashi, hawaye na ambaliya a fuskar ta tamkar ana tsiyayar wa daga famfo, gaba ɗaya jiri take ji, hakan yasa daƙyar ta tashi zaune tana ƙanƙame jikin ta, komi ganin sa take yi bibbiyu, ba ma tasan takamaiman inda yake tsaye ba, domin ba ta gane komi, ga hawayen da ya cika mata ido fal

Shi kuwa wayan sa ya zaro cikin aljihu, sannan ya latsa yana kallon ta yace, "za kiyi waya da mutanen gida, ko kaɗan ba na son ki nuna wani alama da zai saka su gane halin da kike ciki, idan kuwa kika yi haka.." ya ci je ƙasar bakin sa yana sake tamke fuskar sa, "wlh summa tallahi sai na binne ki da ranki a gidan nan, kuma kar kiyi tunanin idan kin faɗa musu kin sha ne".

Wayan ya miƙa mata bayan ya kira Numban Big Dady, sannan ya bata umarnin ta amsa

Jiki na rawa ta miƙa hannu tana laluba inda zata ji wayan, nan ta cafke wayan da hannun sa

Da sauri ya zame nasa hannun saboda jin wani abu da ya tsarga masa daga kwanyan sa har  ƙafafun sa, har wani ƙanƙame jiki yayi yana lumshe ido saboda jin yanayin abinda da ya kasa fassara mene ne

Ba don Allah yasa ta rigada ta riƙe wayan ba, da tuni tasha ƙasa. Kara wayan tayi a kunne jin muryan Big Dady na faɗin, "Hello.. Hello".

"Hel..llo.. Daddddy..". Tafaɗa da wani irin murya tana me fashe wa da kuka lokaci ɗaya.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.


        *EPISODE Forty Five*

           Zaro mata ido Usman yayi, lokaci ɗaya ya damke dantsen hannun ta tare da matse wa da ƙarfi yana caka mata ƙumba; ta yanda zata ji zafi

Sosai kuwa taji zafin da har yasa ta saki siririyan ƙara tana hawaye

Sake zare mata idanu yayi yana ɗaura hannun sa saman baki alamun tayi shiru

Kallon sa kawai take yi tana tsiyayar da hawaye ba tare da ta amsa tambayoyin da Big Dady yake jero mata ba, Sai da ya sake kiran sunan ta a karo na uku kafin ta amsa shi tana faɗin, "na'am Dady. I miss You so Much!" Tayi maganar cikin rauni tana ci gaba da hawayen ta

"What's the matter, daughter? What's wrong with you? Did I hear you? Did you tell me if there was a problem?"

Still idanun ta suna kallon Usman da ya kasa ya tsare yana mata gargaɗi, gaba ɗaya ya ɗaure fuskar sa alamun babu imani. Hakan yasa taji tsoro sosai, domin ta san ko ta sanar wa Dady dole ne yayi mata abinda yayi ninya, tunda ba kusa suke ba, kafin su koma gida ya gama aiwatar da duk abinda yake so, ƙarshe ma ta ƙara wa kanta uƙuba, don haka sai ta daure still cikin raunin murya na wacce take jin jiki sosai tace,"Daddy, it's all right, okay,"

"I don't agree. Let me know if there's a problem, ko akwai abinda yake miki ne?"

Girgiza kanta tayi kamar yana  ganin ta, wasu sabbin hawayen suna sake sauko mata, murya a matuƙar sanyaye tace, "Daddy I'm not feeling well".

Big Dady yace, "subhanallah... Garin ya? Ya aka yi be kai ki asibiti ba? Ba shi wayan.. ba shi wayan".

Bata ce komi ba ta cire wayan a kunnen ta ta miƙa masa, a lokacin sosai wani kukan ya taho mata, sai tayi saurin saka hannun ta ɗaya ta rufe bakin ta tana shashsheƙan kuka me fita da sauti kaɗan-kaɗan, kasancewar ɗaya hannun nata yana riƙe dashi ya ƙi saki sai sake matse mata yake yi, wanda shi tuni ma ya manta da hakan, daɗi da taushin skin ɗin ta ya shagaltar dashi, har ya mayar da abin kamar wasa yana ta faman matsa mata dantse, while ita kuma zafin hakan take ji

Big Dady ce masa yayi, "yayi maza-maza ya kai ta asibiti, idan har be kai ta ba wlh sai yayi mummunan saɓa masa". Ce masa ma yayi "suna zuwa asibitin ya haɗa sa da doctor ɗin".

Hakan da Usman yaji ne yasa yace mata "ta shirya su je" da ya gama wayan, sannan ya tashi ya fice

Ita kuma daƙyar ta iya miƙe wa jiri na ɗiban ta, bango ta dafe sannan ta soma bin bangon har ta kai bakin ƙofa, ko bi ta kan ta rufe jikin ta bata yi ba, sabida ba ta cikin hayyacin ta, daga ita sai doguwar rigan less me ruwan Powder, kanta kuma babu ɗankwali illa gashin ta dake ɗaure da ribom baƙi, amma duk ya tuttuge ya mitsitstsike kamar na mahaukata

Tana fita ta tsaya tana faman haki, sabida gani take yi kamar zata faɗi idan har ta rabu da bango, kuma ga shi dole sai ta rabu da bangon zuwa haraban gidan, hawaye kawai take saki tana gunjin kuka

Usman dake cikin mota yana faman jiran ta, nan ya danna mata horn da ƙarfi yana faman kallon ta daga cikin mota, kuma duk a yanayin halin da yake ganin ta hakan be sa ya ji tausayin ta ba, yana gani kamar wannan shi ne dai-dai da hukuncin da ya kamata ya ɗauka a kanta, babu tausayi a tsakanin su bare taimako, ko wani hali take ciki ita ta ja wa kanta

Daƙyar a duƙe- a duke ta soma taho wa wajen motan, sosai ta sake fashe wa da kuka sabida yanda take ji, kafin ta kai motan sai dai ta ƙarisa da rarrafe, sabida ƙafafun ta sun gaza ɗaukar ta, tana isa ta dafe motan sannan ta buɗe ƙofan baya ta shige

Be ce mata komi ba ya ja motan ya nufi kan titi, kasancewar gidan babu Gate sai compound da ƙaramin ƙofa me raga-raga, kuma motan nasa na fake ne a ta wajen ƙofan a ɗan ƙaramin haraban wajen

Ƙudundune wa tayi sosai tana rawan sanyi, coz yanda motan ta ɗau sanyi sabida a.c, sai karkarwa take yi da haƙoran ta tana faman sakin sauti me ƙara

Tsaki yaja a daƙile yace da ita, "ki yi min shiru a wajen nan".

Tamƙe bakin ta tayi, amma duk da haka haƙoran ta karo suke yi, sai dai sautin na fita a hankali, kuma ya sauya ƙara, tamkar dai wacce aka toshe wa baki tana gunjin ceton rai

Be sake ce mata komi ba har suka kai wani kyakykyawar asibiti da babu nisa da su, fita yayi ba tare da ya tanka ba

Itama sai ta saka hannu ta buɗe ƙofan ta fita, a duƙe take tafiya kamar zata faɗi tana sake sabon hawaye sabida azaba

Shi tuni yayi gaba abin sa

Hakan yasa wata nurse da ta hango ta, ta taho da sauri ta taimaka mata, tana tambayar ta, "are you sick?"

Ɗahira bata amsa mata ba, illa kuka da ta saki me tsuma ran me sauraro, domin tamkar dai jira take yi dama ayi mata maganar; ta fashe da kuka

"Sorry! Sorry!". Abinda take ta faman ce mata kenan har suka shige cikin Hospital ɗin

Usman dake tsaye bakin wani Office yana jiran shigowar ta, nan ya hange su da nurse ɗin, har ta zo nurse ɗin zata gibta shi domin bata san tare suke ba, sai yace mata "ta tsaya".

"Doctor are you together?" Cewar nurse ɗin tana kallon sa

Fuska babu fara'a ya ɗaga mata kai yana shige wa cikin Office ɗin

Hakan yasa Nurse ɗin ta taimaka mata suka bi shi ciki tana me mamakin halin sa, duk da kuwa dama sun san haka yake, "they were sick together but he came and left her outside?" Take tambayar kanta a ranta

Suna shiga ciki, Doctorn dake gaisa wa da Usman ya kalle su, sai kuma da sauri yace, "Beha what's wrong with her?"

"I don't know Sir, but they seem to be together".

Sai Doctor ɗin ya kalli Usman yace, "Doctor, are you together?"

Fuska a ɗaure Usman yace, "Yes. I brought her to check on her".

"Ok. Beha help and calm her down".

Kamar yanda yace ɗin, haka Nurse ɗin tayi, ta nufi kan gadon dake cikin Office ɗin ta kwantar da ita, sannan ta ɗauki excuse wajen doctor ɗin ta fice.

"Doctor Man amma ya aka yi haka ka bar ta har ciwo ya yi mata zafi haka? daga gani tana shan jiki, kai fa doctor ne". Cewar Doctor ɗin cikin turanci dake tsaye yana kallon Usman

Gajeren tsaki Usman yaja yace, "Please ka duba ta, ba surutu nace kayi min ba". Shima ya maida masa da turancin

Doctor ɗin be ce komi ba, illa kaɗa kai da yayi ya nufi gadon da Ɗahira ke kwance, ya san halin abokin sa sarai, shiyasa be yawaita binciken ba ya ƙyale sa. Fara duba ta yayi, duk wani taimako na gaggawa ya bata, domin ya ɗau tsawon mintuna arba'in yana duba ta, inda daga bisani ya ɗaura mata drip ya dawo kan kujeran sa ya zauna, kallon Usman dake ta latsa waya yayi kamar babu abinda ke damun sa a rayuwa, kana yaja numfashi yana ɗaura hannayen sa da ya haɗe su waje ɗaya a saman table ɗin sa, cikin harshen turanci yace, "Amma doctor ya aka yi ka bar pation a tare da kai ta shiga wannan mummunan yanayin baka kawo ta Hospital ba? Yarinyan tana cikin wani mawuyacin hali, zazzaɓin jikin ta yayi tsanani sosai, ga kuma damuwa dake damun ta matsananciya a zuciyar ta, wanda hakan zai saka ta samu matsala, domin idan taci gaba da zama a haka da yawan damuwa a ranta, tabbas komi zai iya faruwa, kuma duk baka ɗau mataki ba, why?"

Ɗago Kai Usman yayi yana kallon sa da fuskar sa kamar kullum, cikin miskilanci irin nasa yace, "wannan be shafe ka ba, tunda ka duba ta shikenan, zaka iya ba mu sallama mu wuce".

"Sallama kuma? Kana jin fa abinda na faɗa, jikin ta yayi tsanani da yawa sosai Doctor, dole zata zauna a nan har ta warware, baza mu iya bata sallama ba".

Miƙe wa Usman yayi yana saka wayan sa cikin aljihun wandon sa, kana yace, "fine. Sai ka riƙe ta har sanda ka so, Ni ka ga tafiya na bani da time ɗin ku".

"But doctor Wai ba ƙanwar ka bace? na ga kun yi kama sosai, amma yanda kake nuna wa kamar da akwai matsala". Cewar Doctorn cike da mamakin Usman ɗin

Shiru Usman yayi yana kallon sa, sai kuma ya juya zai fice don a ganin sa be da lokacin sa, har ya kai bakin ƙofa sai kuma ya dawo yana ciro wayan sa ya kalle sa, "Please Doctor Shamel I will call my Daddy, he will ask you about this girl, Please and please I don't want you to tell him anything, just tell him her body is easy ".

Sosai mamaki ya sake cika Doctor ɗin, sakin baki kawai yayi yana bin Usman da kallo cike da al'ajabin halin sa

Miƙa masa wayan yayi bayan ya kira Big Dady

Inda Doctor ɗin ya amsa ya kara a kunne yana me gaishe da Big Dady cike da girmamawa irin nasu

Nan Big Dady yake tambayar sa halin da Ɗahira ke ciki

Inda Doctor ɗin ya sanar masa "da sauƙi jikin

Please Login or Register in order to submit comment