Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi ba har yanzu. Nan gaba ko yace kar tayi wani abun; to baza ta tsallake umarnin sa ba".

     Tana ganin ya fita, sai kuma ta tashi ta nufi kichen ɗin, dube-dube ta hau yi, wasu abubuwan duk bata taɓa ganin su ba, amma dayake tana karanta wa sai ta gane amfanin su, nan tazaƙulo indomie ta dafa, daga mai sai gishiri ta saka, saboda duk sauran kayan girkin su ba iri ɗaya bane, ta san ko da ta saka ba daɗi za su yi mata ba, sai dai a hankali zata soma gwadawa ta ga ko zata iya ci, amma yanzu yunwa take ji baza ta zauna tayi abinda baza ta iya ci ba.

        Tana gama wa ta fito Parlor tayi zaman ta tana ci, sai da ta gama sannan ta koma ta wanke komi ta mayar muhallin sa, still ta sake koma wa Parlour tayi zaman ta, tunanin rayuwa kawai take yi tare da kewar gida, ga shi babu waya a hannun ta bare ta sa ran zata kira su, shiyasa ta yanke shawaran yana dawowa zata ce "ya bata wayan ta", tunda dai ba nashi bane.


      Ganin duhu ya soma yi ta duba agogon hannun ta taga magriba tayi, sai taje tayi alwala ta dawo, ta tayar da sallan ta, tana idar wa ta duƙufa addu'a, ta jima a wajen har lokacin isha'i yayi, ta gabatar. Ga duhu ko ina dole ta soma jin tsoro, tunda ba inda ta saba da shi ne ba, nan ta ƙudundune a kujera ta rufe idanun ta ta hau karatun Alqur'ani a hankali da muryan ta me tsananin daɗi, a haka har ta soma jiyo motsin buɗe ƙofa, tayi shiru tana buɗe ido tare da kallon wajen

Usman ne ya shigo riƙe da wayan sa yana haska wa, tunda ya shigo ya ƙyalla hasken kanta idanun sa suka sauka cikin nata idanun, yanda ya ga idanun suna wani ƙyalli sun sauya kala sai yayi saurin ɗauke kansa gaban sa na matsanancin faɗi, rufe ƙofan kawai yayi ya nufi ɗakin sa, domin so yayi tun yau ya soma mata tijara, amma ganin ƙwayan idanuwan ta bazai iya zuwa ba

Yana shige wa ta rufe idanun ta, "wai da gaske dai mutumin nan be da imani anan zai bar ta ta kwana?" Tafaɗa a ranta. Numfashi taja ta gyara kwanciyar ta tana sake ƙudundune wa, bata sake motsi ba illa tunani da take ta faman yi, sai daga baya ta samu barci daƙyar ya sumfice ta.


            Washe gari ta farka a makare, ƙarfe 07:00am. A lokacin, shaf-shaf tayi alwala ta gabatar da sallan ta, ta zauna nan tana ta lazimin safe, sai da gari yayi haske sosai kafin ta miƙe ta nufi kichen, a tunanin ta ko ya fita ne tunda bata ji motsin sa ba, ga shi har sha biyu tayi, amma haka nan ta soma haɗa musu Breakfast har da shi, ruwan tea ta haɗa sai arish da ta soya, ta kwashe ta kai saman dainning, ta zo ta sake duba kichen ɗin ta ɗauko kayan haɗa tea ɗin, duk ta kai kan dainning ɗin. Sai da taje tayi bruch kafin ta zo ta haɗa tea ɗin ta sha da arish ɗin, tunda babu ko bread bata gani ba

Bayan ta gama ta tashi ta je ta ɗaura ruwan zafi, yana ɗumi ta sake tayi wanka ta shirya a Toilet ɗin, yau ma riga da skert ta saka na kanti, rigan t.shirt ne me gajeren hannu ja, ta zauna mata ɗas ta yi mata matuƙar kyau, sai ta saka skert Robber light green, irin me tsagin nan ta baya, sai da ta ɗan yi kwalliya kaɗan tunda sabon ta ne, gaskiya tayi mugun kyau matuƙa, musamman yanda take kyakykyawar nan. murmushi kawai tayi tana zaro siririn gyale ta yafa a kanta zuwa wuyan ta, sai ta zauna a kan kujera, a ranta tana tunanin ko ta tashi ta gyara parlor'n ne?

     Buɗe ƙofan da Usman yayi na ɗakin sa, shi ne yasa ta ɗago manyan idanuwan ta ta sauke a kanshi, tare da dakata wa daga miƙewan da tayi ninya

haka zalika shima kallon ta yake yi, lokaci ɗaya ya ɗauke kai yana cin magani, da alamu dai fita zai yi saboda a cikin shirin sa yake

Takowa yayi ya isa wajen kujerun

Duƙar da kanta tayi kawai tana jin gaban ta na faɗuwa

"Keee". Yayi maganar a maƙoshi yana ja

Ɗago kai tayi tana kallon sa, yanda ya tsare ta da ido da fuskar sa tamkar hadarin kaji, daga gani ba mutunci a tare dashi, hakan yasa ta ɗauke kai itama tana shan kunu, domin bata san da me ya zo ba

Zama yayi be sake cewa uffan ba, don be san ma ta ina zai fara ba tsaban miskilanci, ga shi matsanancin haushin ta yake ji, tare da sake jin tsanar ta me ƙarfi a ran sa, "ko uban wa zata yi wa kwalliya?" Ya faɗa a ransa yana sake kallon ta

"Ki tashi ki je ki ɗauko min Trolly ɗin ki". Yayi maganar tamkar ba shi ba

Sai da ta kalle sa kafin kuma ta ɗauke kai tana me mamaki. Amma bata ce komi ba ta miƙe ta nufi wajen kayan ta, janyo wa tayi ta kawo masa har gaban sa

"Buɗe shi". Ya sake bata umarni

Ita dai bata ce uffan ba sai mamaki da ke son kashe ta akan "me zai yi mata da kaya?"

Tana buɗe wa ya sake ce mata "ta fito da duk komi dake ciki".

Hakan kuwa ta sake yi

Ɗaya bayan ɗaya ya saka ta tana ɗaga kayan, don shi bazai iya saka hannun sa ya taɓa kayan ta ba

Idan ta ɗaga sai ya ce "ta ajiye gefe," wani kuma yace "ta mayar cikin akwatin". Karkatakaf sai da ya gama zaɓe ƙananun kayan dake ciki, sai atamfa da Abaya kaɗai da yace ta zuba cikin akwatin

Ita dai duk yanda yace tayi hakan take yi, arziƙin ta ɗaya bata biye wa miskilancin sa ta fito da under-Wears ɗin ta ba, da yanda ya saka take ɗai-ɗai da kayan ta; da ta sha kunya

"Waɗannan kaɗai kike da damar saka wa a gida na, nan ba gidan karuwan ki bane da zaki zo kina saka min ƙananan kaya, and daga yau aikin gidan nan gaba ɗaya ya dawo kanki, ko ina na cikin gidan nan kullum Ina son ki share shi tsab, ko alamun datti ba na son gani, zan bar miki keeys ɗin ɗakunan, kuma daga yau inda nace ki koma nan zaki koma, kar in sake ganin ƙazantaccen jikin ki ya zauna min a cikin parlor. sauran aiki ya rage naki, ki bi ko kar ki bi, idan ba haka ba zan baki mamaki Wlh".

Tun sanda ya soma magana ta ɗago kai tana kallon sa, sakin baki kawai tayi tana bin sa da ido domin mamakin sa ma ya kusa kashe ta. Ganin yana shirin tashi tace, "ban gane me kake cewa ba fa? Ni fa matar ka ce ba baiwar ka ba. fine naji aikin gidan zan yi tunda dama aiki na ne, amma meye haɗin ka da kaya na da sai ka zaɓa min waɗanda zan saka? Kuma da kake cewa ba gidan karuwai na bane, amma ai naga Gidan Mijina ne, kuma idan ma nayi karuwancin iyawa ne, kasan da haka ka aure Ni, so ba abun damuwa bane".

Sosai yayi mamakin furucin nata

Ita kuwa ƙarfin hali ne ta azawa kanta har ta iya faɗan waɗannan kalaman, domin ba ƙaramin tsoro ne cike a zuciyar ta ba, amma kuma tana gani idan har taci gaba da shiru ba ta mayar masa da amsa, tabbas ya samu damar kullum yana sakar mata magana yana cusa mata baƙin cikin sa.

       Kallon ta yayi da idanun sa da suka soma sauya kala, domin maganar nan ma da yayi me yawa ba ƙaramin dauriya yayi ba, amma kuma tsaban rashin mutunci irin nata take maida masa martani, "ke nan baza ta bi umarnin sa ba?" Ci je leɓen sa yayi yana bin ta da kallo, sai kuma ya ɗan saki guntun murmushi yace, "me yi ba ya faɗa, don Allah idan kin cika ke ƴar uban ki ne, ki tsallake umarni na".

Sosai ranta ya ɓaci da zagin uban ta da yayi, sau biyu kenan hakan ke faruwa. Shiyasa cikin ɓacin rai da baƙin cikin sa tace, "ba dai uba na ba wlh, domin ya fi ƙarfin ka har da zaka zauna kana zagin sa.."

Bata ajiye numfashi ba ya ɗaga hannu ya falla mata marin da sai da taga taurari suna shawagi a idanun ta, ɗif tayi kawai ta dena gane abinda ke duniyar.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

_SAƘON GAISUWA GARE KU MASOYA NA *Usman Aliyu Ahmad, Adama Aliyu, Nana Aliyu, Prencess Teema, Maryam Muh'd, Hafsah, Amina Umar Abdullahi, Zainab Muh'd Hussain, Fatima Bintu Muh'd, Sadiya, Asma'u, Lawisa, Rahma,* da ma waɗanda ban lissafo su ba, duk ina gaishe ku, kuma ina godiya da soyayyar ku gare Ni._

.

        *EPISODE Forty Three*

     
        Bata gama dawowa duniyar gigitan da ta shiga ba. ya duƙa a gaban ta ya shaƙo mata wuya, cikin ɓacin rai yace, "idan har na sake magana kika mayar min da martani makamancin haka, Wlh sai na binne ki da ranki a gidan nan, idan kin isa ke tatacciyar mara kunya fitsararriya ce ke, ki sallake umarni na, zaki ga yanda zan yi biji-biji dake a gidan nan.." sai ya datse harshe ba tare da ya gama faɗin abinda yake son faɗa ɗin ba, miƙe wa kawai yayi bayan da ya dungurar mata da kai. Har ya taka zai fice, sai kuma ya dawo yana kallon ta da ɗaurarriyar fuskar sa da ba mutunci, cikin tsawa yace da ita, "biyo NI da kayan nan". Ya nuna kayan ta dake zube a ƙasa

Ɗahira da gaba ɗaya duniyar ta juya mata sabida tsaban gigicewan da tayi da marin da yayi mata, tuni hawaye sun gama wanke mata fuska, tana me riƙe da kumatun ta da ta kasa saki. A tsorace ta tashi tabi umarnin sa kamar yanda yace mata ɗin, domin gani take yi kamar zai sake mata marin nan da yayi mata, ko kuma fiye ma da hakan, domin ko kaɗan bata ga alamun ɓurɓushin imani a tare da shi ba.

     Kai tsaye cikin ɗakin sa suka wuce, inda ya nuna mata cikin wardrobe ɗin sa ta zuba kayan, sannan ya rufe da keey ya ɓoye keey ɗin

Ita tuni ta fice da gudu ta isa inda ya nuna mata makwancin ta, wani irin rushewa da kuka tayi tana me haɗa kai da gwiwa ta soma rera wa, zuciyar ta na wani irin tafarfasa da ƙara jin tsanar Usman a ranta.

     Shi kuwa tuni ya nufi ƙofa ya ficewar sa, ya kulle ta ta waje, domin ya san cewa zata iya guduwa, tunda ita ba yarinya bace, kuma ita ba jahila bace.

      Kuka sosai Ɗahira take yi kamar ranta zai fita, gaba ɗaya idanun ta sun juye sun yi jazur sun kumbura, haka ma fuskar ta da inda ya mare ta ya kumbura suntum, sai shatin yatsun sa da suka fito raɗo-raɗo, haka fuskar ya sauya kamanni, abun ku da farar mace ya sake yin ja

A zuciyar ta babu abinda take yi sai Allah wadai da shi, tare da ƙara rura wutar tsanar sa.

      Har dare Ɗahira na zaune a wurin tana ta kuka, babu abinda ke tashin ta sai Sallah, kuma duk idan tayi sallan sai ta roƙi Allah ya saka mata, ya kuma fitar da ita cikin hannun sa, sosai zazzaɓi ya rufe ta saboda kukan da ta sha, nan ta nannaɗe da zani tana ta rawan ɗari.

     Usman kuwa be dawo ba sai wajen sha biyu, kuma ko kallon inda take be yi ba ya wuce ɗakin sa.

    A haka Ɗahira ta kwana a mawuyacin hali.

         Washe gari haka Usman ya tsallake ya bar gidan ba tare da ya damu da ya bi ta kanta ba

Wannan abun ya tabbatar mata da cewa, tabbas Usman ba shi da ɓurɓushin imani, be da ɗigon imani ko kaɗan, kuma ba zai taɓa tausaya mata ba, duk da tana jin jiki, amma hakan be sa ta ƙi bin umarnin zuciyar ta na guduwa ba. Sai dai kash bata san cewa ya rufe ƙofan ba, tunda ta jijjiga yaƙi buɗuwa ta hau rusa kuka kamar ranta zai fita, nan wani sabon ciwon ya sake kama ta, da ƙyar ta isa ɗakin sa ta hau dube-duben inda zata samu keey, amma duk ta duba babu, dole ta zo ta kwanta a makwancin ta, taci gaba da kukan ta.

     A ranan ma sai dare Usman ya dawo

Sanda ya shigo, daƙyar ta iya buɗe idanun ta da suka yi mata nauyi tsaban ciwo tana bin shi da kallo, dayake akwai hasken NEPA, ko motsin kirki a lokacin ba ta iya yi, hawaye kawai ke tsiyaya a face ɗin ta. Ganin zai wuce ɗaki be kalli inda take ba, sai ta buɗe baki murya na rawa tace dashi, "Please.. Please.. help.. me".

Kallon inda take yayi, sai ya kawar da kai ya shigewar sa ɗaki, ko kaɗan be ji tausayin ta ba, illa ma manta shafin ta da yayi yaci gaba da harkokin sa.

      Ita kuwa tuni ta sake sakin wani sabon hawayen me tsananin raɗaɗi da baƙin ciki, "Allah gani gare ka! Allah kai ne gata na, Allah ka fitar dani hannun wannan azzalumin". Kuka kawai taci gaba da yi a wannan halin da take zaton mutuwa zata yi, domin azaban da take ji baki ma bazai iya faɗa ba. Daga ƙarshe ma da jikin nata ya sake rikice wa, sai ta hau kwarara amai daga kwancen da take, amai kawai take kwarara wa kamar zata zubar da hanjin cikin ta, domin kuwa babu komi a cikin nata, babu abinda taci tun marin da yayi mata jiya

      Yanda take kwarara aman har ɗakin sa sai an ji, amma dayake tuni yayi barci be ma san tana yi ba

Tuɓus jikin ta yayi, wanda tuni ta fita a hayyacin ta, tamkar dai ba ta numfashi haka ta koma. A haka har washe garin Allah yayi.



⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

             *NIGERIA*

     Kamar yanda Hajja suka tsara za su koma wajen Malam, sun koma, inda ya sake musu sabon aiki bayan ya caska kuɗin sa wajen Hajja, "aikin dai a ƙara rura wutar tsanar da Usman yake yi wa Ɗahira ne, a haddasa musu rashin zaman lafiya, kullum ya riƙa ganin ta kamar baƙar kumurci, babu abinda zai riƙa shiga tsakanin su illa cin mutunci da zagi, daga ƙarshe ya koro ta da sakin wulaƙanci", inda ta sake bayar wa aka yi mata aiki akan Aunty Amarya, sai dai suna baro wa wajen, Hajiya Sa'ima ta koma ta sauya sabon aiki, kuɗin da za'a yi wa Aunty Amarya aikin, ta saka aka yi wa ɗiyar ta, sannan ta ƙara masa kuɗi me yawa, a haka suka rabu akan zai yi mata aikin da Usman da kansa zai zo wajen ɗiyar ta neman auren ta, ba shi da wata mata a duniya illa Zeena

Hajiya Sa'ima ta tafi tana farin ciki, ta koma gida ta ba wa ɗiyar ta labari. Nan itama ta hau murna da farin ciki, tana ganin burin ta nan ba da jima wa ba zai cika.


            ***********

     A fannin su Kaka kuwa, sun soma shiga damuwa da jin har yanzu Usman be kira ya sanar musu saukar su ba, haka ma Aunty Amarya da Abbu sun fi kowa damuwa, saboda jin shiru daga ɗiyar su, babu wani waya, ga shi duk an kira layin su be shiga, Numban da Usman ɗin ke amfani dashi idan ya je can an kira shima ba ya shiga

Kaka duk ya ɗaga musu hankali, abu kaɗan yace, "har yanzu Matata bata neme Ni ba?".. "Shin matata ta kira kuwa? Ko kuma Fodio be kira ba?".. ga shi a lokacin jikin sa duk ya ƙi daɗi, shiyasa suke dangana wa ga zafin ciwo ne, saboda yanda ya matuƙar damuwa akan "yana son jin halin da Ɗahira take ciki"

Babu yanda za su iya su Big Dady, sai dai kwantar masa da hankali da suke yi, suna ƙara ba sa haƙuri a kan "za su kira, ƙila wani abun ne ya dakatar da su".




⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

              *TURKEY*

      Fitowar sa kenan daga ɗaki cikin shirin sa na kamar kullum, idanun sa akan ta suka faɗa, hakan yasa ya tsayar da saka link ɗin rigan sa da yake yi yana sake kallon ta, lokaci ɗaya sai ya ɗauke kai yana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki na shigan sa, tare da wani tashin zuciya na taso masa, sakamakon ganin ta cikin amai da yayi. Rasa me ma zai yi yayi, sai kuma ya taka ya nufe ta tamkar zai haɗiya zuciya ya mutu tsaban baƙin ciki, yana zuwa inda take ya sanya ƙafa ya tokare ta yana faɗin "Keeeee" cikin tsawa

Sai dai bata san ma yana yi ba, domin tuni ta sume ba ta ko numfashi

Ganin bata motsa ba, sai ya mayar da idanun sa kanta yana noƙe hanci har da saka hannu ya toshe hancin nasa, sake tokarin ta yayi, sai ya ga alamun ba ta numfashi, tsaki yaja me ƙarfi yana juya wa ya shiga Toilet ɗin parlour'n, ruwa ya ciko cikin bucket, yana fito wa ya sheƙa mata a jiki

Lokaci ɗaya ta kawo wani irin numfashi a matuƙar firgice tana kiran sunan Maman ta

Ƙafa ya saka ya taka nata ƙafan Yana murzawa

Wannan dalilin ne yasa ta dakata daga kiran sunan Maman ta da take yi; sakamakon zafin da ya ziyarce ta, nan ta buɗe idanun ta da suka gama rine wa suka yi wani irin kore tamkar dai ba na ɗan adam ba, saboda yanda ƙwayan idanun nata suka kasance ba baƙi ba, ta zuba masa su kamar zata cinye sa

Hakan yasa lokaci ɗaya tsoron da ya saba ji ya tsarga masa fiye da yanda yake ji a ko wani lokaci idan ya kalle ta, nan ya janye idon sa tare da ƙafan sa ƙirjin sa na faman dukan uku-uku

Ita kuwa kuka ta fashe da shi da ɗan sautin muryan ta da ya rage mata, sosai take kuka wanda ke fita a hankali yana yi yana ɗauke wa

While shi kuma yana jin kamar ana sake tsaga zuciyar sa ne ana ƙara masa wutar tsanar ta, kukan nata na shigan kunnen sa kamar wuta, yana sake jin wani tuƙuƙi a zuciyar sa tare da wani nauyi, ji yake yi tamkar idan be mata dukan tsiya ya ɗaiɗaita ta a lokacin ba, bazai samu sukunin zuciya ba, sai dai kuma ko kaɗan ba ya son sake kallon inda take, hakan yasa ya juya ya nufi ɗakin sa da sassarfa yana kame kansa da ya soma sara masa

Lumshe idanun ta tayi tana jin wani irin zafi dake ruruwa a ko ina na sassan jikin ta da zuciyar ta, yayinda take jin numfashin ta na son ɗauke wa, hakan yasa ta buɗe ido tare da ƙwalalo su waje tana sakin nishi da sauri da sauri, tamkar wacce tayi tseren gudu ko me athma, yanda take fizgar numfashin kamar zata shiɗe, lokaci ɗaya kuma ya fizge mata ta sake sume wa gauu...



                   ****

   Shi kuwa yana shiga ɗakin sa ya zauna bakin gado yana riƙe da kansa, abinda yake ji a zuciyar sa baki ma bazai iya misalta shi ba, gaba ɗaya ya yamutsa gashin kansa ya rasa sukuni, idanun sa kuwa duk sun yi jazur kamar an yi masa duka, lokaci ɗaya ya saki kan nasa ya miƙe a firgice ya nufi ƙofa zai fice...




_babu yawa. Manage Please._
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.

        *EPISODE Forty Four*

       Yana sake koma wa wajen ta ya ga alamun ta sake sume wa, juya wa kawai yayi ya sake ɗibo ruwa ya watsa mata

Hakan yasa ta farfaɗo numfashin ta ya dawo, sai dai idanun ta suna rufe ta kasa buɗe wa, illa kuka da take yi ƙasa-ƙasa tana riƙe da kanta, sai faman rawan sanyi take yi haƙoran ta na karkarwa

Ko kaɗan ba ya jin zai iya taimaka mata saboda zallan tsanar ta da yake ji a ransa, juya wa ya sake yi ya koma ɗakin sa, magani ya ɗauko mata ya zo ya jefa mata, cikin kausashshiyar murya da zaka gane yana a cikin ɓacin rai, wanda daƙyar ma maganar take fita yace da ita, "ki gaggauta tashi ki gyara min gida. Kar in dawo na ga baki gyara nan wajen ba, kar na dawo baki cire min ƙazantar nan naki ba na maimaita miki.. "sai yayi shiru yana juya wa ya yi waje ya fice

Ɗahira bata motsa ba tana nan yanda ya bar ta, illa kuka da take tayi, sosai take kukan har da su shashsheƙa, ta rasa meyasa Usman ya tsane ta, mene ne tayi masa a rayuwa da yake nuna mata wannan zazzafan tsanar? Tana a cikin halin mutuwa ko rayuwa amma shi ko kaɗan ba ya tausayin ta, shin yaushe ne zai tausaya mata? Har yaushe ne zata fita a cikin wannan uƙuban nashi? Me yake nufi da ita ne? Idan so yake yi ya kashe ta meyasa bazai kashe ta a lokaci ɗaya ba sai ya gana mata azaba haka? Ba ta jin zata iya yafe wa Bawan Allan nan, har ABADA! Baza ta taɓa yafe mishi ba domin ya cutar da ita.

     Ta shafe fiye da awanni uku bata iya motsa wa daga inda take  ba, sabida ko kaɗan bata da ƙwarin jiki, ga tsananin ciwon da take fama dashi, amma don kar ya dawo ta fuskanci wulaƙancin sa, tana kuka ta yunƙura ta tashi daƙyar, jikin ta gaba ɗaya ya tsume sai karo da haƙori take yi tana ƙanƙame jiki, hawayen nata ma sun kafe illa kukan zuci kawai da take yi, daƙyar da jan jiki ta isa Fridge ta sanya hannu ta buɗe ta ɗauki ruwa, maganin da ya ajiye mata ta ɗauka tasha ko don wai zata samu sauƙin ciwon da take fama dashi, sai ta sake rarrafa wa ta isa inda gaba ɗaya ruwa ne sharkaf da aman ta a wajen, kallon wajen take yi tana tunanin ta ina zata fara, baza ta taɓa iya wa ba saboda zazzaɓin da take fama dashi, daga ƙarshe zube wa tayi nan ta dinga sheƙa wani aman, ga tsananin yunwa dake addabar ta, jikin ta sai faman rawa yake yi, majinu na tsiyaya ta hancin ta

Sake rarrafa wa tayi ta kwaɓe kayan jikin ta gaba ɗaya, ta sauya wani rigan daƙyar, rufe kanta tayi ta ƙudundune tana ci gaba da rawan sanyi, gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi ta rasa inda zata saka kanta, addu'a kawai take yi a ranta Allah ya kawo mata mafita, tunda take bata taɓa shan wahala makamanciyar irin ta yau ba. Runtse idanun ta tayi tare da tamke bakin ta zuciyar ta na ƙuna, duk second ɗaya tsanar Usman na sake ruruwa a ranta, tana jin har abada baza ta taɓa yafe masa ba, sai Allah ya saka mata.

      Wasa-wasa har dare Ɗahira tana cikin wannan mawuyacin halin, ta kasa taɓuka komi, a haka ta wuni zurr komi bata saka a cikin ta ba, ta kasa ma tashi bare ta samu abinda zata saka a cikin ta, tana jin sai dai ya kashe ta domin baza ta iya yin komi ba.

         A haka ya

Please Login or Register in order to submit comment