Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma kuma babu hali, but tun farko da ya faɗa mata da wuri tun jiya ya kamata taje cikin gidan tayi wuni tare da yin ma kowa sallama cikin natsuwa. Amma kuma Allah ya haɗa ta da murɗaɗɗen mijin da babu me iya saka shi bare hana shi, ita gaba ɗaya ma tsoro ya kamata don bata san me zai faru ba idan suka je inda babu kowa nata, yanda yake da baƙin halin nan bata san ya zaman nasu zai kaya ba.









.





_To mu ma zamu bi ku muga ya za'a kaya. Shin wani irin zama zaku yi a can ɗin? Meye a zuciyar Usman?_



_wanda yaga yana da kuɗin jirgi sai ya biyo mu ato, don Ni ba Ni dashi gaskiya, bazan iya biya muku gaba ɗaya ba._ 😜🤣🤣
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.


        *EPISODE Forty One*

            Kafin jirgin su ta sauka, tuni Ɗahira da Abokiyar zaman ta sun zama ƙawaye, domin sosai suka sha hira a tsakanin su, inda har suka yi sauyin number, Ɗahira ta amshi Numban nata cikin takarda kasancewar babu wayan ta a hannu

Ita yarinyan ne ma ta rubuta mata a wani memo ta bata, sai ta kwashe nata cikin wayan ta. Matashiyar budurwan wacce zata yi sa'anni da Ɗahira, tana karatu ne a can Turkey, kuma tana zaune ne wajen Sister ɗin ta dake aure a can tare da Mijin ta, sunan ta Zakeeya. Kasancewar ƙasa ɗaya za su je shiyasa hiran nasu tayi tsaho har suka zama kamar sun san juna.



             Jirgin na sauka a ƙasar Turkey, cikin birnin Istanbul, sallama suka yi akan za su nemi juna bayan sun natsa, in yaso sai su san muhallin juna su riƙa ziyartar junan su, duk da ita Ɗahira bata sanar mata asalin abinda ya kawo ta ƙasar ba, hasali ma ko ce mata su biyu ne tare da Mijin ta bata sanar mata ba

Koda suka sauka jirgi ma, ita Zakeeyan ta soma mata sallama ta wuce, har tayi mata tayin tafiya a motar su, amma tace, "a'a suna tare da wani ne". Da haka suka yi sallama.


           Ɗahira jan Trollyn ta tayi ta isa inda Usman ke tsaye yana tare Taxi, shi be ce mata komi ba duk da ya ga yarinyan da suke ta hiran, motan kawai ya hau, itama ta shiga baya suka zauna waje ɗaya, babu me motsin kirki cikin su har suka isa muhallin Usman ɗin, Plate ne gidan ƙarami na zaman mace ɗaya, kuma mallakin Usman ne, tunda anan ya sauna lokacin da yake aiki.


         Fita suka yi suka shiga gidan, Ɗahira na biye dashi ita dai tana ta kallon abubuwan burge wa, gaba ɗaya anguwan ya tafi da imanin ta, shiru babu wani hayaniya, zai yi wuya ka haɗu da mutum ma, dama ita Ƙasar Turkey Yana ɗaya daga cikin ƙasashen dake matuƙar burge ta, musamman mutanen ciki ma'abota addinin musulunci, da shigan da suke yi.





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

             Tunda Hajja Fatu ta dawo tacid da mummunan labarin nan na tafiyan su Ɗahira ƙasar waje, sai hankalin ta yayi mugun tashi, domin bata da labari ko kaɗan, ko su su Big Dady da suka sanar wa matan su da safe Kaka ya faɗa musu, lokacin sun je gaishe shi. To sai suka dawo suka sanar wa matan su, yayinda Abba kuma ya wuce Hospital, tunda ya san cewa Hajja Fatu tuni ta tafi asibitin, kuma da ya je can be samu ya sanar mata ba har sai da suka dawo, lokacin su ma sun ji labarin har sun tafi, sai sukai musu fatan alkhairi kawai.

         Kai tsaye ɗaki ta wuce sanda Abba ya sanar mata a parlour ya fice, wayan ta ta ɗauka jiki na rawa ta kira Ƙawar ta Hajiya Sa'ima, nan take shaida mata abinda ke faruwa

Itama Hajiya Sa'ima baƙin ciki kamar ya karta, ta ma kasa yin magana

Hajja Fatu tace, "yanzu ji be abinda ke faruwa, mu da muka je neman taimako waje Malam ya hautsina musu zaman auren, daga ƙarshe ya yi mata sakin wulaƙanci, amma kin ga sakamakon tafiya ma suka yi, ta ya idan ya tsane ta daga yin aure zai ɗauke ta wai fita hutun amarci, anya kina ganin aikin Malamin nan yana ci? Ki duba fa ki gani, ita kanta Mahaifiyar ta da na saka ayi min aiki a kanta, shiru kake ji babu wani hayaniya a tsakanin su da zai nuna min suna faɗa".

Ajiyan zuciya Hajiya Sa'ima ta sauke, kana tace, "Wlh nima abinda nake tunani kenan, amma kuma Wlh Ni na yarda da aikin Malamin nan tabbas yana ci, sai dai kuma idan akwai maƙarƙashiya ce, ke da kanki kin ce itama uwar ba zaune take ba, to kin ga baza muyi mamaki ba da abinda za mu gani, amma Ni nan nake ganin aikin Malam, duk da Ni ban taɓa zuwa wajen sa ba sai a wannan lokacin, ƙawata da nake raka wa ina ganin yanda take watayawa a gidan mijin ta, kuma kin san kishiya ce da ita, amma yanzu tuni ta bar gidan duk sabida aikin da Malam yayi mata, yanzu ita take juya gidan, duk abinda tace shi Mijin nata yake yi".

"To yanzu ya kike ganin zamu yi?"

"Ai zama be gan mu ba, koma mishi zamu yi, idan ma akwai matsala a sake sabon aiki, domin muddin kika zauna ke ruwa sai sha".

Hajja Fatu tace, "haka ne. Amma ki bari zuwa gobe idan na fito aiki sai mu je".

"To shikenan Allah ya kai mu rai da lafiya".

Da haka sukai sallama. Inda Hajja Fatu ta miƙe ta nufi sashin Hajiya don sake jin ƙwaƙwaf tare da zigin da ta saba.

Oh Allah ya raba mu da halin Hajja Fatu, HASSADA mugun ciwo.



                  *********

             Hajiya Sa'ima kallon ɗiyar ta Zeena tayi, tace, "kin gani ko? Dama nace zata kira Ni, amma kuma maganar tafiyan nan nasu ya girgiza Ni fa".

"Hmm Mama ke ya girgiza ko Ni? Wlh baki ji yanda ƙirji na yake suya ba da jin zancen". Cewar Zeena tana kumbura fuska kamar zata yi kuka

"To ki kwantar da hankalin ki, ai yanzu za'a sake sabon aiki, kin ga mun yi da Malam dama in sake karkato ta ta dawo, to ga shi ita da kanta ta neme Ni, duk kuɗin da zata bayar ayi wa uwar aiki, sai a mayar dashi kanki, zai miki aikin da shi da kanshi Usman ɗin sai ya zo ya duƙa yana kuka ki aure sa, ita kuma matsiyaciyar can (tana nufin Ɗahira) watan wahalan ta ne ya kama, da ƙafan ta zata gudo saboda azaba, daga nan kin ga shikenan tana dawowa iyayen suka san halin da ake ciki za su ce ya sake ta, kin ga burin mu ya cika, da zaran ya sake ta ke kuma zaki bayyana a wajen sa kamar yanda Malam yace, faƙaɗ".

Dariya Zeena ta saki tace, "Wow har kin sa naji Daɗi Mama, Wlh ina mugun son Bawan Allan nan, muddin ban aure sa ba to mutuwa zan yi".

"Ba ma za'a kai da haka ba ɗiya ta, aure babu fashi dake dashi, idan har Ni mahaifiyar ki ce, to, Wlh ko zan yi yawo tsirara ne sai na cika miki burin ki. Ke kaɗai ce fa dani, idan ban miki ba wa zan ma?"

Farin ciki ne sosai ya cika Zeena, tana ji a ranta da kalaman Maman ta tamkar ta cika burin ta ne, "waiii! Wa ya ganta gidan Dr. Usman Noor Al'ameen, a gaskiya sai ta zuba ruwa a ƙasa tasha ranan don murna. Hohoho!".





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

          Itama Ayush ta shiga tashin hankali jin labarin tafiyan su Usman wani ƙasa, su da suke burin raba auren don me zai tafi ya ɓata musu aiki? Ga shi ba su ji sakamako ba a kan Hotunan da suka tura masa, duk da suna kyautata zaton aikin su yana yi, amma kuma tafiyan nan ya rusa mata gaba ɗaya lissafin ta, dole ta nemo Safra ta sanar mata komi

Itama kanta Safran abun ya girgiza ta, domin tun sanda suka biya wani saurayi yayi musu aikin haɗa hoton nan suka aika, sai ta koma Zaria school ɗin ta, shiyasa bata san wainar da ake toya wa ba, duk da suna waya da Ayush ɗin, but bata taɓa tunanin shirin su zai ƙi tasiri a ƙanƙanin lokaci ba, ga shi kuma tsaban rashin samun nasara har tafiya suka yi tare, a ranta tana tunani "an ya ma Usman ɗin ya buɗe hotunan ya gani?" Domin ta tabbatar babu namijin da zai ga matar da zai aura a wannan mummunan yanayin be rabu da ita ba, ko da son ta shi ne ajalin sa ƙariƙon mamaye masa zuciya.

             Ce ma Ayush ɗin tayi, "ta shirya idan ta samu lokaci ta zo Zarian su je wajen Malamin, tunda dama ce musu yayi "idan aka yi auren alokacin ne zai raba, ita kuma Ayush ta shiga". To yanzu tunda aikin su be yi ba za su koma masa, da fari ma ya soma saka soyayyar Ayush ɗin a zuciya tun wuri Usman ɗin ya san da ita, kafin a raba auren.


         Washe gari Ayush shiri tayi da wuri ta wuce Zaria, domin ko wajen aiki ba ta jin zata iya zuwa idan bata je ta san matsayan ta ba.


      Koda ta sauka masaukin Safra, sai da ta huta taci abinci sannan suka ɗauki hanyar da zata fito da su Zaria, daga nan kuma suka karya kwana har zuwa gidan Malam

Suna isa bakin Bukkan yayi musu iso zuwa ciki. Bayan sun zauna sun kai gaisuwa wajen sa

Ya amsa yana bin su da kallo, sai yace, "kun dawo kenan?"

"Eh Malam.. yanzu aikin muke so sosai Malam, Dan Allah ko nawa ne zamu biya domin kayi mana aikin me kyau". Cewar Ayush cikin damuwa

Dariya ya saki yace, "kee yarinya dama wa yace miki ba na aiki da kyau? Ki ajiye kalaman ki wataƙil zai miki amfani a can gaba amma ba anan ba".

"Ran Malam ya huce". Cewar Safra tana ɗaga masa hannu alamun jinjina

Be ce komi ba ya soma musu aiki, sai can kamar mintuna 20 ya dube su yace, "ina ga aikin nan fa yana da sauƙi a waje na, amma a wajen ki yana da wuya, idan kuma kika aiwatar da abinda nace miki; tamkar shan ruwa ne zaki same shi". Sai ya ja numfashi yana miƙo mata wani baƙin kwalba, sannan yaci gaba da cewa, " riƙe wannan zaki je ki zuba jinin farkon saduwa dake da za'a yi, idan kin zuba sai ki nemi gashin kansa da naki sili ɗaya kacal, ki ɗaure su waje ɗaya, sannan ki saka shi cikin jinin, idan kika yi haka to sai ki dawo min da kwalban, Ni kuma zan saka aljanu su kai min tsaunin da mutane ma ba sa shiga, za su birne shi a ƙasan teku. Daga ranan babu wata mace da zai taɓa so idan ba ke ba, ke har mahaifiyar shi sai da amincewar ki zai nuna mata so, ke kaɗai zai ƙaunata kamar hauka, kuma daga ƙarshe Son ki shi ne ajalin shi. batun kuma rabuwa da matar sa, da zaran kin aikata abinda nace auren su zai warware". Hhhhh ya ƙare maganar yana ɓaɓɓaka wani mahaukacin dariya

Daga Ayush har Safra tsimi suka yi suna kallon sa, babu wacce tafi ruɗe wa sama da Ayush, domin kalaman Malamin ba kaɗan ba ya gama hautsina ta

Safra tace, "amma Malam kamar ya ka ce "Son ta zai zame mishi ajali?"

Dariyan ya kuma saki, kafin yace, "ki adana kalaman ki har sai kin ga irin mahaukacin ƙaunar da zai mata, a nan ne zaki gane tabbas son ta shi ne zai zamo ajalin sa". Ya ƙare maganar yana ci gaba da dariyan sa

Sai alokacin Ayush ta ɗan ƙifta idanu, kamar ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, cikin rashin kuzari tace, "amma ban gane ba Malam, idan mun yi aure da shi ne zan samu jinin bayan ya kusance Ni Ko kuwa?"

"Ba shi nake nufi ba, taya zaki aure sa idan baki aikata abinda nace miki ba? Bari kiji; yarinyan dake tare dashi tamkar wata garkuwar shi ce, akwai bala'o'i da yawa da ake jifan sa dashi, amma kuma albarkacin ta yana zuwan masa da sauƙi, ya rage naki ki je duk wajen wanda zaki je ya kusance ki baya ga shi".

Zata sake magana Safra ta katse ta da faɗin, "to babu damuwa Malam, insha Allahu zaka ji mu ako yaushe, yanzu ba ya gari, za mu ɗau lokaci kafin mu sake dawo wa".

Gyaɗa kansa kawai yayi yaci gaba da surƙullen sa

Sai Safran ta kalli Ayush ta raɗa mata "ta fito da kuɗin a ba shi".

Babu musu ta zuge jakan ta ta fito da kuɗin ciki gaba ɗaya, dubu ɗari biyu ne, ta ajiye masa

"Ranka ya daɗe! Ga kuɗin, muna godiya sosai".

Ɗago kai yayi ya kalli kuɗin, sai kuma ya kalle su yace, "za ku iya tafiya. Fatan Nasara".

Tashi suka yi suka fice, inda babu me magana har sanda motan su ta fito daga hanyar ƙauyen suka hau titi

"Yanzu Ni ya zan yi? Kai na ya ƙulle Wlh, ta ya zan aikata Zina abun da ban taɓa yi ba? Sannan kuma taya zan je gidan sa ba da budurci na ba?"

Dariya kawai Safra tayi, sai dai bata ce komi ba taci gaba da tuƙin ta

Hakan yasa Ayush ta sake kallon ta tace, "kin yi shiru? Don Allah ki bani shawara, ga kuma wani babban aikin; wai tsigo gashin kansa, mutumin da ba shi a ƙasa, ko yana nan ma ta ya zan tsigo gashin sa?".

A wannan karon ma dariyan Safra ta sake kwashe wa dashi, sai kuma tace, "ashe har yanzu baki waye ba? Wlh duk ɗauka na ke fa bugaggiyar wayayyiyar nan ce".

Sake juyo da kanta sosai Ayush tayi tana kallon ta, sai dai ta kasa cewa komi

"Ke yanzu don kawai yace miki ki je ki kusanci wani shi ne ya zama abun tashin hankali? Ina ga fa ba abun ɗaga hankali bane, kuma gashin kansa duk yanda za'a yi mu samo ai dole ne zamu samo, sai dai dole sai mun bari ya dawo nan, sabida ko mun je can bamu da dabaran da za mu iya aiwatar wa bare mu samu, amma anan akwai hanyoyi da dama, kar ki damu ƙawalli zan taimaka miki har sai burin ki ya cika, tunda jini na ya haɗu dake Wlh ko me kike so zan taimaka miki, ki share batun nan, duk sanda aiki ya tashi da zaran ya shigo gari zan haɗa ki da alhazawan da sai kin jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, domin sai wanda ranki ya kwanta dashi zaki darza, sannan kuma uhmmm kuɗin da zaki samu ko? Hhhhh ba'a magana, Allah lokaci ɗaya zaki faso gari, daga ranan ma kin samu sana'ar yi, ke da kanki zaki koma neman su, ga ki kina auren The Young handsome Guy, ga kuma kuɗi ya zauna miki, kin zama Hajiyan kan ki, Allah zaki ce na faɗa miki".


Shiru Ayush tayi a wannan lokacin ma, sai dai tana kallon Safran, tambayar dake yawo a ranta "ita meyasa bata nemi mazan ba sai ita zata haɗa ta da su?" In fact ma ta sha jin tana cewa "Maza ba sa burge ta" sannan ma bata taɓa jin tayi maganar namiji ba in ba yanzu ba, ashe tana da alaƙa da su? Duk da tasan Safra ƴar gata ce tana wadaƙa da kuɗi, amma bata san muhallin da zata ajiye ta ba, iyayen ta ne masu kuɗin? Ko kuma samari take bi suke ba ta? Shi ne bata sani ba.








.




_🤷 Ni ma dai ban sani ba, amma bari fans su baki amsar ki, don na san su akwai su da tunanin hasasowa. 😂_
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

               *TUNATARWA*
'''Manzon Allah mai tsira da aminci, ya yi mana bayani a kan sallah da abin da Bawa yake iya samu. Cewa ya yi, "Yana yiwuwa mutum ya kawo sallah ga baki ɗayan ta amma a ba shi lada wadda ba ta wuce sudusin ta ko ushurin ta ba." Abin da yasa haka kuwa shi ne  rashin nutsuwa cikin sallah.
   Allah yasa mu dace.'''


.


        *EPISODE Forty Two*

         Kyakykyawar parlor'n tabi da kallo, a ranta tana ayyana tsantsan kyawun sa da tsaruwan sa, duk da ba kaya ne me yawa a ciki ba, saboda kun san yanayin tsarin tura wa, basu cika saka karikitai kamar mu a gida ba, amma haɗuwar sa sai kin yi kamar zaki zubar da yawu tsaban kallo. Hotunan sa ne har guda uku a ƙusurwa-ƙusurwa na ɗakin, babu me cewa shi ne sai idan ka yi masa kallon tsab, sabida mugun haɗuwar da yayi, tamkar dai ɗan ƙasan; ba ɗan Nigeria ba, uwa uba ga shi da skin irin nasu, ga kyawu da ya haɗa, ga kuma kayan da ya saka duk nasu ne.


      Ɗahira ta saki baki tana kallon Parlor tamkar wata ƴar ƙauye. Sai jin takun takalman sa tayi daga bayan ta, da sauri ta waiga tana kallon sa

Ba ita yake kallo ba, da alamu ma har ya shiga ɗakin sa, duba da har ya cire rigan saman Jikin sa; yana sanye da Singlet da dogon wandon da ya zo da shi, fuska babu walwala ya nemi wuri ya zauna a ɗaya daga cikin tsararrun kujerun parlor'n

Ɗauke kai tayi tana haɗiyar yawu a hankali sabida jin maƙoshin ta ya bushe, tsayuwan taci gaba da yi a inda take, tunda be ce mata ga inda zata shiga ba, sabida ba wani ɗakuna ne da yawa a gidan ba, daga ɗakin sa sai irin sa na baƙi, sai kuma kichen me haɗe da store har biyu da ƙofa ta baya da zai kai ka Garden ɗin gidan, sai kuma Toilet a parlor'n guda biyu shima.

       Tana nan tsaye ya ƙi ya ce mata komi, dole ta ajiye wani ƙyaliya nata ta kalle sa tace, "ina ne ɗakin da zan zauna?"

Uffan be ce mata ba, ya ci gaba da latsa wayan sa, har sai da ta cire rai da zai yi magana, sannan ya ce, "baki da muhallin zama a gidan nan, taimako ɗaya zan miki". Sai ya ɗago kai yana kallon ta, hakan yasa suka haɗa idanu, kallon kallo kawai suke wa juna, ko wanne na cike da juriyan kallon ɗan uwan sa, domin yanda gaban su ke wani irin bugawa a tare sai ka ɗauka suna jin bugun zuciyar junan su, shi nashi har da wani tsoro ne ya mamaye sa, wanda duk idan dai ya kalli ƙwayan idanun ta masu Colour'n nan, to sai hakan ya ziyarce shi

Wani irin ɗaure fuska ya sake yi, sai tayi saurin sad da kanta ƙasa, domin itama ta kasa ci gaba da kallon sa

"Ga lungu can, nan zaki riƙa kwana". Ya nuna mata wajen kichen da hannun sa, sannan ya ci gaba da magana, "ko a parlor'n nan ban yarda in ga ƙafafun ki ba".

Sosai zuciyar Ɗahira ke suya da maganar nan nasa, sai dai ta kasa cewa komi illa sake duƙar da kanta da tayi, take hawaye suka soma sintiri a saman kyakykyawar fuskar ta sabida jin rainin hankalin sa da baza ta iya ɗauka ba, "wai me yake nufi ne? Ni ce zan riƙa kwana a can kamar almajira?"

Shi kuwa tuni ya miƙe ya shige cikin ɗakin sa, ko a jikin sa. Wanka ya shiga yayi ya soma rama sallolin da ake bin sa. Tunda kwana suka yi a hanya.

        Tamkar gunki haka Ɗahira ta ƙafe a inda ya bar ta, ko motsin kirki ta gaza yi, lumshe idanu kawai tayi hawayen ta na ci gaba da zubo mata. Har ya fito tana nan tsaye a wajen bata jirga ba

Kallon ta kawai yayi ya taɓe baki, sai da yaje kichen ya haɗa tea kafin ya dawo cikin parlor'n, zama yayi yana harɗe ƙafafu, sai ya ɗauki wayan sa ya soma latsa wa yana sipping coffee ɗin.

     Babu daɗe wa aka yi Nocking a bakin ƙofan, sai ya bayar da iznin shigo wa

Wani matashi ne ya shigo, shi ne me kula masa da gidan, kuma shi ne ya gyara gidan tun da ya kira sa yace "zai zo" har girki shi yake masa

Gaishe sa yayi bayan da ya durƙusa a gaban sa alamun girmamawa

Cikin miskilanci tamkar bazai yi maganar ba ya amsa mishi, kana ya ƙara da cewa, "daga yau ka zauna ka huta, ina da me aiki". Yayi maganar cikin turanci

"Ok sir thank you".

"You can go".

"Ok sir". Ya sake faɗi yana me miƙe wa tsaye ya fice.

             Ɗan ɗago kai yayi ya kalli setting da Ɗahira take, sai ya taɓe fuska yana ci gaba da sipping coffee ɗin sa, kamar shuɗewar mintoci a ƙalla goma, ya ajiye Cup ɗin a saman table, kana yaci gaba da latsa wayan sa. Daga ƙarshe ma kwanciya yayi saman kujeran yaci gaba da abinda yake yi.


      Yanda ƙafafun ta ke zugi nan da nan suka soma rawa sabida gajiya, dole ta janye ƙafafun ta ta isa inda ya nuna mata, ajiye Trollyn ta tayi a wajen, sannan ta buɗe ƙofan da take kyautata zaton Toilet ne, ta shige. Zama tayi a ciki tasha kukan ta ma'ishi, kana ta share hawayen ta tare da ɗauro alwala. Tana fitowa babu shi cikin parlor'n, ƙarisa wa tayi wajen Trolly ɗin ta ta zuge ta ciro Hijab, sannan ta zare gyalen da tayi Trollyn dashi ta saka Hijab ɗin, cikin parlour'n ta ƙarisa ta soma sallah saman tattausan carpet ɗin dake shimfiɗe a wajen, rama sallolin da ake bin ta tayi. Har ta idar ta soma kwararo addu'a tana kai wa Allah kukan ta, bayan ta ida sai ta shafa tayi zaman ta a wajen, ta jima tana zaune a wajen ga zafi ya ishe ta, dayake ba'a kunna masa Gen ba, sai ta tashi ta cire Hijab ɗin ta ninke, ta nufi Trolly ɗin ta taja shi zuwa ɗakin kusa da nashi, sai dai a kulle yake, hakan yasa ta tsaya tana tunanin mafita, domin baza ta iya kwana a inda ya nuna mata ba tamkar wata almajira, ko bata da gata sai haka

Juya wa tayi ta mayar da akwatin, sannan ta shige Toilet ɗin, wanka take son Yi Amma babu ruwa me zafi tunda babu wuta, sai ta fito ta nufi kichen inda taga ya bi ɗazu, tana shiga kuwa ta sami komi a dai-dai, ta kunna gas ta matsa ruwa a famfon kichen ɗin; ta ɗaura. Sai da yayi zafi ta sake tare da sirka wa, har ta koma ta shige Toilet bata sake jiyo motsin sa ba, wanka tayi ta fito. Ta duba kayan ta cikin Trollyn ta ta koma Toilet ɗin ta saka, riga da skert ne ƴan kanti, sun yi mata kyau sosai sun lafe a jikin ta, kasancewar bata da jiki

Ta rasa yanda zata yi da kayan da ta cire, sai ta fito dasu ta ninke ta mayar cikin akwatin nata, janyo akwatin tayi ta nufi cikin parlour'n, tayi zaman ta kan kujera, sai dai gaba ɗaya tunani ya addabe ta, ga yunwa da ta soma ji, amma rashin jin daɗin yanayin yasa baza ta iya girki ba.

       Tana nan zaune kamar mintuna 20, sai ta jiyo buɗe ƙofa, sai dai bata motsa ba tunda ta san shi ne

Kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai, ba tare da ya ce komi ba ya sanya ƙafan sa ya fice, a ransa yana murmushin mugun ta, "tabbas zai koya wa yarinyan nan hankali, bata san waye

Please Login or Register in order to submit comment