Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu tawali'u ne."_
    _Watau, Muminai wanɗanda idan sun tsaya yin Sallah sai gaɓoɓin su da zukatan su su natsu, babu wani abu mai shagaltar da su daga ambaton zatin Allah maɗaukakin sarki, to, irin su suke rabban ta. Natsuwa cikin sallah da ƙasƙan da kai ga Allah su ne alamun imani na gaskiya da Tauhidi tsantsa, don kuwa ko yaushe bawa yayi kusa da Ubangijin sa sai ya haɗa jin tsoron sa, musamman ma dai a sallah inda yake ganawa da shi, yake tunawa da girman sa. Allah yasa mu dace._





.

        *EPISODE Thirty Eight*


            *WASHE GARI*

       Tunda aka yi sallan asuba Usman be dawo gidan ba, be kuma bari kowa ya gansa ba ya bar masallacin.

     Ita kuwa Ɗahira tunda ta tashi tayi sallan asuba itama, ta sake komawa barcin, dayake akwai zazzaɓi a jikin ta shiyasa har gari yayi haske bata farka ba, sai da taji hayaniyan ƴan biki da wasu suka zo su sake ganin ɗakin nata, kasancewar a lokacin za su tafi, shi ne ta farka, lokacin 12:00pm.

    Har ciki suka shiga suna ta mata tsiya, ganin ta da suka yi tana ta barci

Ita dai bata ce musu kanzil ba, illa murmushi da take tayi, sai kuma daga baya ta gaishe su.

       Ba su wani jima ba suka yi mata sallama suka tafi.

   Sake koma wa tayi ta kwanta, don sosai kanta yake sara mata sakamakon tashin ta da suka yi, ta rufe ido kenan taji an hankaɗo mata ƙofan ɗaki, da sauri ta buɗe idanun ta tana bin Yusra da ta shigo da kallo

Ita kuwa sai faman taɓe baki take yi tana girgiza jiki, sai kuma ta mayar da idanun ta kan Ɗahiran tace, "baƙar munafuka! burin ki ya cika kin auran min Yaya, to wlh ki saka a ranki, kamar auren nan ya rabu ne, ba ke ba zama a gidan Yaya Usman, domin ba ya ƙaunar ki, ba kuma zai taɓa ƙaunar ki ba, wlh dani dake yanzu ma muka soma ƴar tsama".

Yanda ka san t.v haka Ɗahira take bin ta da idanu, har sai da ta dire Aya kafin ta tashi zaune tana bin ta da kallo sosai, ko kaɗan ba ta jin daɗin Jikin ta, kuma har ga Allah ba ta son ta biye mata, amma kuma gani take yi idan har ta bar ta ta tafi bata mayar mata da martani ba, to, tabbas nan gaba ma zata dawo tayi mata irin wannan cin mutuncin, kuma zata ga kamar tsoron ta take ji, don haka ta saki guntun murmushi tana kallon ta tace, "wa kike da suna? Yusra ko? Ni ba sa'an yin wasan ki bane, tun wuri ki kama kanki, domin shiru-shiru ba hauka bane, wlh ina ƙyale ki ne kawai don Ni ba Kaza bace da zan zauna kullum ina sa'insa da ke, na san mutuncin kaina; na kuma san kima ta, amma wlh muddin kika sake shigo min gida na, kika yi min irin wannan halin karnukan, zan baki mamaki Yusra, zan nuna miki Ni ba'a sha na a warke, domin zan nuna miki ainihin hauka na wlh".

Shewa Yusra ta saki tana tafa hannu tace, "an yi miki duk abinda zaki yi ki yi, ai Ni dama so nake yi ki ɗau mataki sai in San kin cika ke tatacciyar mara mutunci ne, kuma ke baki isa ki hana Ni zuwa gidan ɗan uwa na ba wlh, kin yi kaɗan, nonsense..."

"Wai hayaniyan me nake ji ne? What's going on here?" Cewar Fadila da ta shigo da sauri, dama Breakfast ta kawo musu shi ne ta jiyo kamar hayaniya

Ɗahira tace, "Ask her to come and find me in my room,"

Tsaki Yusra taja tace, "wlh mu zuba dani da ke". Tana faɗa ta juya ta fice.

Ƙarisowa Fadila tayi bakin gadon tana zama tace, "wai me ke faruwa ne? Me ya haɗa ki da ita?"

"Babu komi Fadila, kin san halin ta ba tun yau ba, ban san me na tsare mata ba ita da Yayan ta suka bi suka tsane Ni, ban san me nayi musu ba". Ɗahira ta ƙare maganar cikin damuwan da ya nuna a muryan ta

Ajiyan zuciya Fadila ta sauke, sai kuma tace, "ki yi haƙuri da duk halin su, Ni ban san meyasa Yusra take wannan ɗabi'an banzan ba, amma yanzu ba ta Ita zaki yi ba, ta Mijin ki zaki yi, duk hanyar da ya dace shi zaki bi domin samo soyayyar shi, ke ba yarinya bace Ɗahira, kin san abun kuma da ya dace, batun tsana ko rashin sa duk be taso ba yanzu, yanzu kun zama ɗaya ke da shi, aljannan ki kawai zaki nema, kar ki soma ki biye mishi, na san zaki iya ƴar uwa, haƙuri shi ne zai sa ki cin ma Nasara kinji? Domin auren ku muna fata mutu ka raba ne".

Murmushi Ɗahira ta saki tana jin hawaye na son cika mata idanu, sai tayi saurin kawar da kai tana ɗan rufe idanun ta tare da komar da su

Fadila tace, "yanzu ina Angon naki? Ga abinci can na kawo muku sai ki je ki tashe shi. Amma kin ban mamaki fa".

Kallon ta Ɗahira tayi da son ƙarin bayani

"Kya waro min Ido mana, ji be ki don Allah mana, kin zauna har sha biyu da rabi baki yi wanka kin shirya ba, ta hakan ne zaki dai-dai ta gidan ki?"

Wannan karon dariya Ɗahira tayi, sai ta tashi kawai ba tare da tayi magana ba, domin sosai take jin jikin ta babu daɗi

"To Ni bari in tafi, zuwa anjima zan sake leƙo ki, zuwa gobe insha Allahu duk zamu tarkata, na san ma yanzu su Momy suna nan shigo wa". (Tana nufin mahaifiyar K.B Hajiya Ikram) tunda ta koma can sai ya zamana itama Momy take ce mata kamar sauran ƴaƴan ta, saɓanin a baya da suke kiran ta Gwaggo Rabi.

Har Fadilan zata fice, sai Ɗahira tace mata, "ta zo mata da maganin ciwon kai".

Amsa mata kawai tayi Sannan ta fice

Ita kuma ta shiga wanka, sai da ta fito ta shirya cikin atamfa baƙa da kalan fari da coffee, ɗinkin riga da zani raffer, tayi kyau sosai, sai dai yau komi bata shafa a fuskar ta ba duk da kasancewar ta me son kwalliya, ɗankwalin kawai ta ɗaura ta fito Parlour

Da kallo kawai take bin ko ina, har ta isa kan dainning ɗin, duba abinda aka kawo musu tayi, sai kuma ta juya ta nufi ɗakin da ta gani kusa da na ta, tsaya wa tayi a bakin ƙofa tana tunanin shiga ko a'a, don ta san nan ne ɗakin Usman, sosai gaban ta yake faɗi, don har yanzu bata san wani irin zama za su yi ba

Bismillah tayi kawai ta tura ƙofan da sallama, bayan tayi Nocking ba'a amsa mata ba. Sai dai babu kowa ciki, sai da ta gama ƙare wa ɗakin kallo gunun ban sha'awa irin nata komi da komi, sai dai kayan ɗakin ta ya fi yawa tunda ita mace ce, amma har ta colours ɗin ciki iri ɗaya ne

Fitowa tayi ta koma kan dainning ta hau yin breakfast ɗin ta, sai dai har ta gama a tunani tayi Breakfast ɗin

Ɗaya daga cikin ƙannin K.B suka kawo mata maganin da tace a kawo mata, amsa tayi tasha ta zauna a kan kujera tana faman tunani

A haka sauran mutanen gida sukai ta shigo wa ganin ɗaki, da masu tafiya da waɗanda sai gobe za su tafi, ƴan Maiduguri dai duk yau suka watse

Daga ƙarshe su Shamsiyya da Shakira, Firdausi, Salma da sauran sa'annin ta duk suka cika sashin, suna ta hira

Tun Ɗahira ba ta biye musu har dai ta saki jiki ana ta yi da ita, tuni ta wartsake abun ta

Suna ta tsokanar ta wai "daga aure ango ya tafi ya bar ta," masu kare mata suna yi, har da Shakira Iyayen gulma, ita dai sai dai ta bi su da dariya kawai.

     Sai magriba duk suka watse suka bar ta, ta shiga tayi sallan magriba, sannan ta dawo Parlor, tunda nan ya ɗan fi haske, da wayan ta ta haska tayi zaman ta tana ci gaba da faman tunanin ta, babu abinda ke tsaya mata a rai, sai yanda za su yi zama da wanda ya tsane ta; itama kuma ta tsane shi

Kafin a kira sallan isha'i aka kunna musu gen, tunda duk generator ɗin su haɗe yake dana Part ɗin Baffa

A lokacin ne aka sake kawo musu abincin dare, tana amsa ta ajiye saman dainning ta wuce ɗakin ta ta rufo ƙofa, alwala tayi ta gabatar da sallan isha'i, sannan tayi shafa'i da wutri, ta roƙi Allah buƙatun ta, sannan ta sauya kaya zuwa rigan barci doguwa tayi kwanciyar ta, da haka tana tunani har barci ya ɗauke ta.






             *********

           Kamar jiya, haka ma yau Usman sai ƙarfe 01:00am. Ya dawo gidan. Ko kallon ɗakin ta be yi ba ya shige nasa, wanka yayi ya sauya kaya zuwa na Barci, dama ya rigada yayi sallan sa a masallaci, sai yayi kwanciyar sa, tare da kitsima abubuwan da yake son aiwatar wa, don samun mafita daga wannan kaddararren auren.

     Washe gari haka ya sake tsallake wa ya fice a gidan, shi fa sam ganin ta ne ba ya son Yi ma, shiyasa yake fice wa. Ga shi Big Dady yace masa kar ya soma ya ga ƙafafun sa a Hospital idan har ba two weeks yayi ba.




       A yau duk sauran mutanen da suka zo biki suka watse, dama duk yawanci ƴaƴan Kaka ne su Hajiya Ikram da Hajiya Laila, sai ƴaƴan su wasu  da ba su tafi ba, sai kuma ƙannin Kakan, su Hajiya Baseera da Hajiya Hannatu (Ihsan). Duk dangi na kusa ne. Kuma duk yau suka gama watse wa

Aunty Zulaiha CE kawai ta kai yamma, itama don tana jiran mijin ta ne, da zata tafi sai da tazo har Part ɗin Ɗahira, a nan take ce mata "ta shirya taje Part ɗin su Usman ta gaishe da Hajiya, idan da hali ma ta zauna a can sai zuwa dare ta dawo"

Tana tafiya ta shirya kamar yanda tace mata, doguwar riga abaya baƙa ta sanya, me kwalliya sosai a gaban rigan na flower, sai ta yane kanta da gyalen abayan, ta saka turare a jikin ta tare da takalmi ta fito riƙe da wayan ta

Tana fito wa Part ɗin ta suka haɗa idanu da Baffa dake zaune saman farandan gidan sa, ya haɗe ƙafafu ya ƙura wa Part ɗin nata idanu yana faman tunani. Ganin ta yasa ya sauke ƙafafun ƙasa yana mata murmushi

Sosai taga ya sauya mata, gaba ɗaya ya rame ya rage haske, sai ƙasumba da ta ga ya ajiye, kamar dai ba shi ba ɗan gayen nan

Murmushi tayi masa itama, tana ƙarisa wa inda yake ta gaishe shi

Amsa wa yayi yana cewa, "amarya ba kya laifi.. ko da kin kashe ɗan masu gida".

Dariya tayi tana ɗan rufe fuskar ta tace, "kai Yaya ka dena don Allah ba na so. Ina Sa'ada tana nan mu gaisa?"

"A'a ta fita, tana Part ɗin Hajja".

"To bari inje Yaya".

Daga nan ta wuce tayi ƙofan da zai sada ta da gidan su

Da kallo Baffa yake bin ta dashi, sai ya lumshe idanu yana jin hawaye na cika masa idanu. har yaushe zai jure da abinda yake ji? Yanzu ta zama matar ɗan uwan sa amma soyayyar ta ƙara wanzuwa yake yi a ransa

"Ya Allah ka cece Ni, ya Allah ka bani baiwar Allan nan idan har alkhairi ne ita a rayuwa ta.."

"Da wa kake yi ne haka?" Cewar Sa'adatu da ta tsaya gaban sa tana kallon sa, sai dai bata san me yake cewa ba

Buɗe idanun sa yayi yana kallon ta, sai kuma ya kawar da kai yana miƙe wa ya shige cikin parlour'n su

Itama bin bayan shi tayi fuskar ta tuni ya nuna damuwa, yanzu sam Baffa ya dena kula ta, sai tayi magana sau dubu be amsa mata ba.




               ⚫⚫⚫⚫⚫

     Da sallama Ɗahira ta shiga Part ɗin Hajiya, sai dai babu kowa a ciki, sai ta samu wuri ta zauna tana aza idanun ta kan t.v dake aiki

Kamar shuɗewar mintuna biyar sai ga Hajiya ta fito riƙe da Plate a hannun ta daga kichen. Ganin Ɗahira sai tayi kicin-kicin da fuska ta nufo cikin parlour'n

Da sauri Ɗahira ta zamo daga kan kujeran, ta zauna a ƙasa tana gaishe ta

Sai da ta zauna ta ɗan kalle ta a fizge, kafin tace, "Lafiya".

Jiki a sanyaye Ɗahira ta sake duƙar da kanta ba tare da ta sake cewa uffan ba

Itama Hajiya bata sake kula ta ba, ta soma cin abincin ta.

      Har ta gama Ɗahira bata ɗago kai ba, tunanin kawai yanda zata iya rayuwa da su take yi, da kuma yanda suka tsane ta, nan da nan taji idanun ta sun ciko da hawaye, bata ankara ba taji sun soma zubo wa, saurin saka hannu tayi ta share tana ɗan ɗago kanta tabi Hajiyan da kallo, wanda ta fito daga kichen ajiye Plate ɗin; ta wuce ɗakin ta

Ɗan ajiyan zuciya ta sauke tana me lumshe idanun ta. sallaman Usman da yayi ciki-ciki ne ya saka ta ware ido sai a kan sa

Wanda shima ya sauke nasa idanun yana bin ta da wani irin kallon da ta kasa fassara shi.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_



        *EPISODE Thirty Nine*

     Saurin ɗauke kanta tayi daga kallon sa, ta duƙar da kanta tana jin gaban ta na matsanancin faɗuwa, ko kaɗan ba ta ƙaunar su haɗa idanu, saboda kallon da yake mata sosai yake cutar da ita.

     Takowa yayi ya shige ɗakin Hajiya

Sai a lokacin ta sake ɗago kanta, ta ɗan kalli hanyar da ya bi, sai kuma tayi zugum ita kaɗai a parlour'n, ta rasa me zata yi, kar kuma ta tafi tayi laifi, sai ta tashi kawai ta shige kichen ɗin Hajiyan, duba wa tayi ko akwai wanke-wanke tayi, amma ƴan ƙwayoyi ne. Dayake ɗazu kafin su Aunty Zainab su wuce duk sun wanke.



     Wanke sauran tayi ta kife ta fito tana gyaran mayafin ta, sai kawai idanun ta suka faɗa cikin na Usman dake zaune saman dainning, saurin ɗauke kai tayi tana takowa ciki ta zauna a ƙasa kusa da kujera, bata sake ɗago kai ba bare ta kalli inda yake. Har ya gama tana nan a haka, sai da tajiyo sahun ƙafafun sa ya wuce ya nufi ƙofa kafin ta ɗago kai tabi shi da kallo, ƙare masa kallo kawai take yi har ya fice, kafin ta saki ajiyan zuciya tana ɗago hannayen ta ta soma murɗa su tana tunani

Fitowan Hajiya yasa ta ɗago kai ta bi ta da kallo

Ita Hajiya ma tayi tunanin ta wuce tun ɗazu, shiyasa bata ce mata komi ba tayi ninyan juyawa

Sai Ɗahiran tayi saurin ce mata, "zata tafi".

Kanzil bata ce mata ba ta shige ɗakin ta

Sai jikin ta ya sake yin sanyi ƙalau, miƙe wa kawai tayi ta wuce gidan su, gaba ɗaya ranta babu daɗi, bata san tun yaushe Hajiya ta sauya mata ba, amma da sosai suke mutunci da ita.

     Tana shiga parlour'n suka sake haɗa ido da Usman dake zaune yana latsa waya, ya ɗago kai yana kallon ta

Janye idanun ta tayi da sauri, ta nufi hanyar ɗakin ta

"Zo nan". Yayi maganar tamkar ba da ita yake yi ba, yana ci gaba da latsa wayan sa

Ɗan juyowa tayi tana kallon sa, sai kuma ta taka ta nufe sa, durƙusa wa tayi gaban sa tace masa "ga ta".

Tamkar ba da shi take yi ba, be ɗago ba bare ya kalle ta, sai ma sake tamke fuskar nan nasa da kullum take a haka yayi, ya ɓata lokaci a haka be ɗago ba, be kuma ce mata komi ba

Ɗahira har ta gaji, sabida durƙuson da tayi ƙafafun ta sun soma mata zafi, jure wa kawai take yi, amma gaba ɗaya ba ta jin zata iya jure irin wannan wulaƙancin nasa, "don me ya kira ta kuma yayi banza da ita?" Sai kuma ta miƙe kawai ta nufi ɗakin ta

Bata san cewa yana biye da ita a baya ba, tana isa bakin gadon ta sai ji tayi an janyo ta baya, kasancewar gyalen ta ya riƙe ya shaƙe mata wuya, babu shiri ta waro ido waje tana kallon sa

While shima kallon nata yake yi fuska babu fara'a, cikin izgili da taƙaman sa yace, "kin dai ƙi jin magana ta? Sai da kika shigo gida na ko? To yau zan nuna miki banbancin Ni da kwaratan ki, sai kin gummaci zaman wuta da zaman gida na, domin sai na ɗai-ɗai ta rayuwan ki, sai kin yi dana-sanin zuwan ki duniya".

Tuni Ɗahira ta soma hawaye sabida shaƙan da yayi mata, bata so yin magana ba, sai kuma tace, "meyasaka ka tsane Ni ne Ya Usman? Me nayi maka ne? Ko na tare maka wani abun ne?"

"Uban ki ki kai min! Na ce ubanki ki kai min". Sai ya zaro mata idanun sa da suka juye suka yi ja yace, "na tsane ki! na tsane ki! Na tsani na buɗe ido na ganki, taya ma zan bari kiyi rayuwa a ƙarƙashi na?"

Sosai wannan karon Ɗahira take kuka, jin yanda ya zagar mata uba, babu abinda yafi ƙona mata rai sama da haka, sai ta saka ƙarfi ta janye gyalen ta idanun ta na zubar da hawaye


Bata ankara ba sai ji tayi ya falla mata mari, kafin kace me ya sake sakar mata wani, sai ya tura ta saman gadon yana cewa, "yau sai na kashe ki ko zan huta a rayuwa na".

Sosai Ɗahira ta gigice da marin da yayi mata, lokaci ɗaya ta zaro ido ganin ya nufo ta gadan-gadan, wani ƙara ta saki tana me miƙe wa a saman gadon ta wuntsila can ɗaya side ɗin, sai gata ta faɗo ƙasa tim, duk da haka bata haƙura ba ta miƙe da sauri tana neman wajen ɓuya, gaba ɗaya ta fita hayyacin ta lokaci ɗaya, saboda ba kaɗan ba marin da yayi mata ya gigita ta, har kumatun ta sun kumbura

Sake fashe wa tayi da kuka da ta gansa kusa da ita

Janyo ta kawai yayi ya wurga ta saman gadon, ko kaɗan babu tausayi a lamarin Usman, domin sosai yake sake jin wutar tsanar ta na ƙara ruruwa a zuciyar sa, ji yake yi idan be kashe ta ko ya wulaƙanta rayuwan ta ba, bazai taɓa sukunin zuciya ba

Hawa yayi kan gadon ya soma janye mata gyale

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. me.. me.. kake yi haka? Don Allah kayi haƙuri". Tafaɗa da rawan baki tana son ƙwatan kanta

Falla mata wani marin yayi da yasa dole ta nutsu waje ɗaya, ta saki wani marayan kuka tamkar ranta zai fice

Be dakata ba sai da ya cire mata gaba ɗaya kayan ta, tuni idanun sa sun juye, sai ƙara hautsina yake yi da tsantsan tsanar ta

Ita kuwa numfashi kawai take sauke wa, tana addu'a a zuciyar ta sabida abun da ke shirin faruwa da ita, domin ko kaɗan baza ta iya jure wa ba, ita da take amsar wa ƴaƴa mata haƙƙin su idan aka yi musu fyaɗe, shi ne yau ita za'a yi wa

"Ya Allah ka taimake Ni". Tafaɗa a ƙasar ranta hawaye na ci gaba da kwaranya a fuskar ta tamkar an kunna famfo.

       Tofar da yawu yayi ya mirgina ya tashi, zuciyar sa tamkar ta ƙone sabida baƙin cikin abinda yake shirin aikata wa, bayan yasan ita wace ce, taya ma yayi wannan tunanin gangancin da yake son haɗa jiki da ita?

Tsaki yaja yana kallon ta da jajayen idanun sa, ganin yanda take rufe jiki, sai ya saka hannu ya janyo blanket ɗin yana cewa, "ƴar iska! Uban wa kike son ɓoye wa jikin naki? Bayan da kin gama tallata sa a waje meye kuma yayi saura? Babu abinda zai burge Ni a nan bare inyi sha'awar ki, gwara ma tun wuri ki sauya tunani. Na tsane ki! kuma wlh sai kin yi dana sanin aure na, sai na azabtar dake yanda ko an ce su sake bani auren ki sai sun yi kuka".

Kuka sosai Ɗahira take yi, tana riƙe da blanket ɗin da ya riƙo ƙam, ta hana sa janye wa

Tsaki ya kuma ja ya fice a ɗakin, har ya shige ɗakin sa, sai kuma ya dawo cikin nata ɗakin

Wani irin zabura tayi cike da tsoro tana kallon sa

Shi kuwa ko bi ta kanta be yi ba, ya sanya hannu ya cire keey ɗin ɗakin, sannan ya janyo ƙofan ya rufe ta ta waje

Wani marayan kuka ta saki har da shashsheƙa, sosai ta takure kanta tana ta kuka, tafi awa a haka bata dena kukan ba, sai da taji gaba ɗaya jikin ta ya ɗau zugin zafi kafin ta haƙura. Lallaɓa wa tayi ta sauko daga kan gadon, har ta ɗauki rigan ta zata mayar, sai kuma ta ajiye ta shiga Toilet, ruwa me zafi ta haɗa ta gasa jikin ta, daƙyar take iya yin komi, tana yi hawaye na kwaranya a fuskar ta, sai da ta gama ta ɗauro alwala ta fito, wani doguwar rigan ta saka mara nauyi me ruwan ƙasa, ta saka Hijab ta tayar da Sallan magriba da ya wuce ta, sai ta haɗa dana isha'i

Har ta idar da sallan kuka take yi, ko kaɗan ta kasa yin shiru. Ta daɗe tana roƙon Allah kafin ta sallame sallan, ta kifa kanta a gwiwowin ta taci gaba da rera sabon kukan ta

Maganar Fadila da tayi mata tun ana gobe bikin su, shi ne ya dawo mata a rai. "Ta sani cewa dole ne sai tayi haƙuri da rayuwan auren ta, amma bata taɓa tunanin wulaƙancin da zai mata zai kai haka ba, yanzu har da yunƙurin mata fyaɗe a matsayin ta na matar sa ta sunna kuma ƙanwar sa. Sannan yake jifan ta da munanan kalamai, wai wani irin tsana ne yake mata? Me ta tare masa ne? Me tayi masa?"

Sai ta ɗago kai tana share hawayen fuskar ta da ya gama kumbura yayi suntum, kasancewar ta fara gaba ɗaya tayi jazur sawayen yatsun sa sun fito, cikin rawan murya a fili take cewa, "ga shi tun ba'a yi nisa ba na tuna maganar ki Fadila, amma ba na tunanin wannan auren zan jure azabar shi har na ba wa maƙiya na kunya, wlh bazan iya ba sam". Ta ƙare maganar ta da fashe wa da sabon kuka

Buɗe ƙofan da taji ana ƙoƙarin yi ne, yasa tayi tsit tana bin ƙofan da kallo hawaye na kwaranya a saman fuskar ta, wanda tayi zaton shi ne ya shigo

Shima a kanta ya sauke idanun sa, sosai yaji wani sanyi a ransa duba da yanda ya ganta, ci je leɓe yayi a ransa yace, "kaɗan ma kika gani, sai na wahalar da rayuwan ki, sai na wulaƙanta ki".

Takowa yayi ya isa gaban dressing mirror inda ya ƙilla idanu ya ga wayan ta. ɗauka yayi kawai ya fice a ɗakin, ya sake rufe ta, domin ba ya son ko kaɗan ta gudu ta kai ƙaran sa, shiyasa zai mata horo da haka, kuma nan ba da daɗe wa ba zai san abun yi, domin ba ya so a fuskanci komi sai ya gama gana mata azabar da ya tanadar mata, yayi wa kansa alƙawari sai tayi dana-sanin rayuwan ta.

    Ita kuwa Ɗahira ko ci kanka bata ce masa ba har ya fice, domin wani irin baƙin ciki da zallan tsanar sa ke nuƙurƙusan ta, shiyasa baza ta iya tambayan sa ina zai kai mata waya ba.

     Ta jima a nan zaune tana kuka, gaba ɗaya ta fita hayyacin ta, har wajen ƙarfe 10:30pm. tana nan a haka, zazzaɓi me zafi ya rufe ta, dole ta rarrafa ta isa inda ta ajiye sauran maganin da tasaka a kawo mata jiya, ta ɗauka ta isa ga Fridge ta samu ruwa, sai dai bata sha ba sai da ta kora

Please Login or Register in order to submit comment