Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rabi ta dawo

Wanka kawai tayi ta shirya cikin farin Less me ɗige-ɗigen baƙi, riga da skert aka yi mata, wanda yayi mata cif a jikin ta, ya kuma ƙara haska mata white skin ɗin ta, sai ta yafa baƙin gyale bayan tayi ɗaurin ɗan kwalin ta normal, sai dai fuskar nan ya sha make-up, sabida Ɗahira ba baya ba wajen son gayu, musamman na kwalliya, takalmi me tudu tayi amfani da shi fari, ta ɗau HangBag ɗin ta ta rataya ta fito

Umma ce kaɗai zaune a parlour'n

Tace mata, "Umma zan je gidan su Shakira ne".

Sai Umma ta wangale baki tace, "ahh to Masha Allah, yau kenan zaki leƙa su? To ki gaishe su".

Murmushi Ɗahira tayi tace, "insha Allah Umma za su ji". Tana gama faɗar haka ta shige ɗakin Maman ta

Taɓe baki Umma tayi tana kawar da kanta daga kallon bayan Ɗahiran, a ranta tace, "gulma ajali! ba ma asan me zaki je yi ba, Allah dai ya tsare min ɗiya ta ba a nan kusa take ba bare ace za'a je mata". Sai kuma ta miƙe ta nufi cikin gidan inda zata je kai wa Hajja rahoto.

     Ɗahira na shiga tace ma Aunty Amarya "ta shirya zata tafi".

Shi ne take tambayan ta "baza ta ci abinci bane?"

Tace mata "sai ta je can, zata ci a gidan su".

Daga haka Allah ya kiyaye hanya Aunty Amarya tayi mata, ta bata saƙon gaisuwa, sannan ta fito. Motar ta ta hau ta bar gidan.

            Gidan Yusra ta soma zuwa, tunda babu nisa da su, babu ƙarya gidan ta ya haɗu matuƙa, babba ne sosai tunda mijin ta yana da kuɗi sosai, Costume ne shi, ya taɓa aure kuma sun rabu da matar tuni, har ɗiya yana da ita, sai dai tana wajen Mahaifiyar sa ne

Horn tayi, me gadi ya leƙo, sai da ya zo wajen ta tayi masa bayanin kanta, kafin ya buɗe mata ta shiga ciki, tana yin parcking ta fito tayi cikin gidan

Tun daga haraban gidan komi ya burge Ɗahira, da ace ita baƙauyiya ce, ko ba su da shi a gidan su, da har zilalan yawu sai tayi lokacin da ta shiga parlour'n Yusra, sai dai kasancewar ta wayayyiya kuma masu shi, shiyasa sama-sama tayi ma komi kallo, a ranta kuma sosai komi ya bata sha'awa, tana ganin Yusra ta more da komi, domin tayi Sa'an muhalli.

        Fitowar wata babbar mace da kaya haɗin gambiza a jikin ta, ya tabbatar wa da Ɗahira ƴar aiki ce, a ranta tace, "su Yusra uwar son jiki! Har an soma ajiye ƴar aiki".

Matar iso wa wajen ta tayi, ta zuƙuna har ƙasa ta soma gaishe ta

Saurin yalwata fuskar ta da fara'a Ɗahira tayi, tace da ita, "don Allah Mama ki tashi, Ni Yakamata in gaishe ki ai ba ke ba".

Murmushi matar tayi tace, "ai babu damuwa ɗiyar albarka, idan na gaishe ki ma girman ki ne, don daga gani ke ƴar uwan matar gidan ce, kinga kuwa be kamata naƙi gaishe ki ba".

Itama Ɗahiran murmushi tayi tace, "amma ai kin girme Ni Mama, don Allah kar ki sake zuƙuna min kinji? Ki ɗauke Ni tamkar ɗiyar ki".

"To babu damuwa, insha Allahu. bari in Kira miki Hajiyan". Matar tafaɗa da fara'a, a ranta sosai taji ƙaunar Ɗahira sabida mutunta ta da tayi, har tana jin da ita ce Uwar gidan nata.

     Har tayi nisa kuma ta juyo ta tambayi Ɗahiran "wa zata ce mata ta zo?"

Ɗahira ta sanar mata da sunan ta

Ita kuma ta juya ta shiga ciki.

     Kamar shuɗewar mintuna biyar sai ga ta ta dawo, tace mata "ga ta nan zuwa"

"To Mama na gode". Ɗahira tafaɗa tana murmushi

Itama murmushin tayi tace, "babu damuwa ɗiyar albarka".

Daga nan juya wa tayi taje ta kawo mata Drinks kamar yanda ta saba tarban baƙi idan sun zo, sai dai na Ɗahira har da abinci ta sawo mata, tunda tana ganin ita ɗin ƴar uwanta ce, be kamata ta tarbe ta da Drinks kaɗai ba, kuma abincin na Mijin ne tayi masa cus-cus, tunda shi ya fi so kuma yace ayi masa. To ta ga bata rigada ta sauke sauran abincin ba, shiyasa ta ɗibo mata nashi.

      Matan tana barin wajen, sai ga Sulaiman ɗin ya fito, da fara'an sa ya zauna suka gaisa da Ɗahira, har yana tsokanar ta da "sai yau za su ga idon ta, gaba ɗaya ita tayi wuyan gani, dole sai an cike Form me tsada ake iya ganin ta, da biki ma ko ganin ta be yi ba"

Ɗahira na murmushi tace dashi, "Allah Sarki Yaya Sulaiman, wlh ciwo nayi shiyasa kwata-kwata ban fita waje ba, kayi haƙuri".

"Eyya Sorry! But ban ji labari ba ko kaɗan wlh, domin dai Yusra bata sanar min ba, ai da mun shiga mun gaishe ki, Allah ya ƙara lafiya, yasa kaffaran zunubai ne".

"Amin Amin Yaya Sulaiman, na gode sosai".

Murmushi yayi yace, "ki dena godiya Auntyn mu, mun rigada mun zama ɗaya Yanzu".

Murmushi kaɗai tayi ita dai

Yace, "sai fa kin yi haƙuri da wannan ƙanwar taki, tana shirya wa ne amma yanzu zata fito".

"A'a babu komi wlh".

"To bari in ɗan fita waje, zan haɗu da Maƙoci na ne, idan ta fito ki ce mata yanzu zan dawo".

Amsa mishi tayi cikin murmushin da ya zame mata jiki

Shi kuma ya tashi ya fice a Parlour'n

Ajiyan zuciya Ɗahira ta sauke, tana ɗauke kai daga hanyar da yabi, sai kuma ta kalli Centre table ɗin da me aiki ta shirya mata abinci da drinks, hannu ta sanya ta ɗauki Robbern fanta, ta buɗe ta tsiyaya a glass cup ta soma sha. Abu kamar wasa har tsawon mintuna 15 suka shuɗe babu Yusra babu dalilin ta, don haka ta zuba cus-cus ɗin ta soma ci, kasancewar sosai take jin yunwa

Tana cikin ci ne, sai Yusra ta fito cikin takun ta ɗai-ɗai tana faman taunan cwhingum

Da kallo Ɗahira tabi ta dashi tana mamakin ganin ta da Shimi da dogon wando, babu alamun dai shirya wa ne ya tsayar da ita, koda yake da ta tuna ba shiri suke yi ba, tasan komi zata iya mata, don haka ta tsayar da cin abincin da take yi tana kallon ta fuskar ta cike da fara'a, ganin yanda tayi mugun sauya mata, tamkar dai ba satin su biyu ne da aure ba, tabbas aure ni'ima ce, Allah yasa mu dace.

      Yusra dai tunda ta ƙariso wajen taga abincin da Ɗahira ke ci, sai ta sake ɗaure fuskar ta tamau fiye da yanda ta ɗaure, tana faman fiffizge kai tana taunan cwhengum ɗin ta har da su ƙas-ƙas-ƙas

Ɗahira ita ta soma mata magana, tare da gaishe ta cikin fara'a

Sai da ta zauna ta gama yamutsa fuskar ta kafin tace, "Lafiya. Dama ke ce?"

Murmushi Ɗahira tayi tace, "eh".

"Yayi to". Tafaɗa tana sake taɓe baki

Shiru ne ya biyo bayan maganar ta, don ita kanta Ɗahira bata san me zata ce ba, domin kawai yanda ta amshe ta ɗin, sai jikin ta duk yayi sanyi, tamkar ma ta ƙaro wulaƙanci ne, ga shi sai mata kallon banza take yi kamar dai ta ga kashi..

Numfashi taja sabida maganar Yusran da ya dawo da ita hayyacin ta

"Wai Husband ne yasa a kawo miki abincin nan?"

Shiru Ɗahira tayi tana kallon ta, don bata san me zata ce mata ba, tunda bata gane ma manufar ta ba

Guntun tsaki Yusran taja tana ɗaga murya ta soma kiran matar nan, "Marka.. Marka".

"Na'am yallaɓiya, gani". Cewar matar da ta fito da gudun ta

"Wa ya baki damar zuba mata abincin Husband?"

Shiru matar tayi tana zazzare ido, ta kalli Ɗahira ta kalli Yusran

Sai da ta daka mata tsawa da faɗin, "ba dake nake yi ba?"

"Kiyi haƙuri Ranki ya daɗe! Gani nayi ƴar uwan ki ce, shiyasa na zuba mata tunda yanzu na ɗaura sanwa, kuma zata..."

"Dalla rufe min baki". Ta katse ta da faɗar haka

Jiki a sanyaye matar tayi shiru tana sad da kanta ƙasa, zuciyar ta cike fal da mamakin uwar ɗakin nata

"Wlh duk sanda kika sake ɗaukar abincin Miji na kika ba ma wata, a mean ba ita ba ko waye ma, wlh ranki sai ya ɓaci! baza ki sake zamar min a gida ba, ba na haɗa Miji na da ko wani tarkace kina ji ko?" Tayi maganar cikin isa da gadara

"Eh naji ranki ya daɗe! amma wai da naga ita ɗin..."

"Shut up I say".

Gum Matar tayi jikin ta na rawa, sabida sosai tsawar ta ya shige ta

"Ki kwashe ki mayar min dashi kichen, idan kin girka wancan sai ki zubo mata".

"To". Matar ta amsa da sauri tana nufan Centre table ɗin, ta ɗauki Plate ɗin kacokan ta wuce kichen, zuciyar ta gaba ɗaya babu daɗi, sosai taji tausayin Ɗahira har tana sake waigo wa ta kalle ta da zata shiga kichen ɗin

Ɗahira na zaune dai tana kallon ikon Allah, har a ranta sosai da sosai abinda Yusra tayi mata ya bata mamaki da tsoro, "shin wani irin tsana ce take mata da har zata yi mummunan wulaƙanta ta haka? Tana a matsayin ƴar uwan ta?". Sosai ta danne ɓacin ranta da komi, cikin juriya ta ƙirƙiro murmushi kafin tace, "Allah ya huci zuciyar ki! wlh nima bansan abincin Mijin ki bane, da ban ci ba". Sai ta miƙe kafin taci gaba da faɗin, "Ni zan tafi, su Umma da Mama suna gaishe ki". Ta ƙare maganar da yin gaba ta nufi ƙofar fita

Taɓe baki Yusra tayi tana faman kaɗa ƙafa, a fili ta furta, "dama ba gayyar ki nake yi ba".

     Ɗahira na fita ta saka hannu ta share hawayen da suka zubo mata a fuska, ta saki wani irin numfashi tana jan majina, lumshe idanu tayi tana haɗiyar wani abu da ya tsaya mata a maƙoshi

"Lafiya Ɗahira? Why are you crying?" Cewar Sulaiman dake tsaye gaban ta ba tare da ta san da zuwan shi ba.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

               *HADHISI*
_An karbo dga Aisha Allah ya ƙara yarda agareta tace " Manzon Allah s.a.w ya aureta tana da shekara shidda,kuma yatare da ita tana da shekara Tara,kuma Allah ya karbi ransa tana er shekara sha takwas. Muslim ya ruwaito_

.

       *EPISODE Thirty Two*

         Ɗago kanta tayi tana kallon sa, sai tayi saurin ƙirƙirar murmushi tace, "No, I'm not crying, abu ne ya faɗa min a ido shiyasa".

Duk da be yarda ba, sai yace, "Eyya sorry! Amma dai ba tafiya zaki yi ba?"

"I'm going Yaya Sulaiman, har da gidan Shakira zan je, and Mama says" I'll be back soon ".

"To babu damuwa, ki gaida mutanen gidan don Allah".

"Insha Allah, they will".

Hannu yasa cikin aljihu ya fito da kuɗi yana faɗin, "amma shi ne Yusran bata zo ta taka miki ba?"

Bata ce mishi komi ba, tunda bata san me zata ce mishi ba

Sai ya miƙa mata kuɗin har 20k Yana faɗin, "ga shi babu yawa kiyi haƙuri".

Girgiza kanta tayi tace, "a'a wlh bazan amsa ba, ka bar shi Yaya Sulaiman". Tana faɗan hakan ta wuce sa ta bar wurin

Da kallo ya bi ta da shi har ta kai wajen motan ta, kafin yaja numfashi yana mayar da kuɗin cikin aljihun sa, ƙofan ya buɗe ya shiga ciki da sallama

Yusra dake zaune har yanzu a inda take, tana faman karkaɗa ƙafafu tana latsa waya, ɗago wa tayi tana amsa sallaman nasa idanun ta a kansa

Shi kuwa a kan Centre table ɗin ya sauke idanun sa, zuciyar sa sosai take ɗarsa masa tabbas Yusra ce tayi wa Ɗahira wani abun, domin ya san cewa Yusra ba ta shiri da ita, tunda sau nawa take faɗar magana a kanta, kuma sannan ba ta son ko kaɗan yayi maganar ta a waje, idan yayi kuma ta dinga kushe ta kenan

Kallon ta yayi yace, "meyasaka Ɗahira ta tafi tun yanzu?"

Taɓe baki tayi tace, "can ta matse mata nima ban sani ba".

Waro ido yayi kanta yana sake gasgata abinda ke ransa, sai kuma ya juya yana kwaɗa wa me aikin nasu kira. Tana fitowa ya tambaye ta "ina abincin nan da na ga Ɗahira tana ci? Yanzun nan daga fitan ta har kin kawar da Plate ɗin?"

Jiki na rawa matar tace, "wlh ranka ya daɗe! Uwar ɗaki na ce ta sanya Ni na ɗauka na mayar tunda abincin ka ne".

"Kina nufin tana zaune a nan ta saka ki kika ɗauke?"

Jiki a sanyaye ta duƙar da kanta ƙasa saboda uwar hararan da Yusra ta banka mata, ta amsa mishi da "eh. Amma a gafarce Ni yallaɓoi, ba laifi na ba.."

"Je ki abun ki Baaba".

Da sauri ta wuce ta koma kichen

Sai ya mayar da idanun sa kan Yusra dake ci gaba da karkaɗa ƙafafun ta, tamkar ma bata damu da abinda yake tambaya a kai ba, yace da ita, "Yusra wai Ni shin in tambaye ki? Ɗahira ba ƴar uwan ki bace?"

Ɗago kai tayi tana kallon sa, sai ta turo baki ta soma magana

Ya katse ta da faɗin, "amsa nake so".

"Ƴar uwata ce mana".

"Ok ƴar uwan taki ce ta zo gidan nan, kika wulaƙanta ta ko? Shin kin san kuwa abinda kike yi? Da kuka fa ta bar gidan nan".

Shiru tayi masa

Cike da ɓacin rai yace, "yayi miki kyau! ki ci gaba da abinda kike yi, Ni babu abinda ya shafe Ni, amma ki sani ranan da zaki yi nadama na nan zuwa". Yana gama faɗar maganan nasa yayi cikin ɗaki da sauri

Tsaki taja kafin ta miƙe tabi bayan sa.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

           Murza sitiyarin ɗin motan take yi zuciyarta na ƙuna, sosai take jin ƙunci da abinda Yusra tayi mata, numfashi kawai take sauke wa duk socond baƙin ciki na ƙara wanzuwa a zuciyar ta, nan da nan kanta ya soma mata ciwo sabida damuwa da tuno abinda tayi mata ya haifar mata, sosai take dana-sanin rashin amayar mata da ƙuncin da ta saka mata, sabida ta san ita zai cuta, amma kuma ta ga ita ta kawo kanta shiyasa be kamata ta biye mata har wani saɓani ya shiga tsakanin su ba, but she promised she would never see her again in her home.

Ta so koma wa gida, sai kuma ta ga be dace taƙi zuwa gidan Shakira ba, can ta wuce duk da bata san gidan ba, sabida kwatancen akwai wahala sosai in dai ba ka taɓa zuwa bane, dole ta kira Baffa ya sake mata kwatancen gidan kafin ta gane

Itama gidan nata babu laifi tunda ita kaɗai ce, amma kuma na Yusra yafi girma da haɗuwa, mijin ta Sahabi aiki yake yi a Companin wutar lantarki.

       Sanda ta shiga gidan da sallama, Shakira na zaune a Parlour tana cin abinci tana kallo, ganin ta yasa ta tashi da fara'an ta ta rungume ta

Murmushi Ɗahira tayi, cikin sanyin murya tace, "ƴar uwa nayi missing ɗin ki sosai da sosai".

Dariya Shakira tayi tace, "ai wlh baki kai Ni ba sister, tun sanda Hajja ta kira Ni tace kina nan zuwa na zauna a nan zaman jiran ki, meyasa ma kika fara zuwa wajen wancan mara mutuncin? Tunda kin san ba shiri kuke yi ba, Allah yasa dai ta amshe ki hannu bibbiyu bata miki wulaƙacin da ta saba ba, ba Ni nasha don Allah ya kuka kwashe?". Ta ƙare maganar har da gyara zaman ta tana zuba wa Ɗahira idanu

Shiru Ɗahira tayi, nan maganar da Fadila ta faɗa mata ya faɗo mata, hakan yasa ta saki murmushin yaƙe tace, "ke dai Shakira, daga zuwa baza ki bari na huta ba sai ki soma min gulman wata?".

Hannun ta ta watsa saman cinyoyin ta tana faɗin, "ai wlh ke dai bari Sister, na damu dake ne wlh, domin nasan halin Yusra yanda ta tsane ki, ruwan gidan ta ma baza ta bari ki sha ba".

"Uhm to babu abinda ya faru tsakanin mu, ta amshe Ni hannu bibbiyu, har abinci na ci".

Ƙure ta da ido Shakiran tayi, sai ta taɓe baki kamar dai ba haka ta so ba, tace, "na ji ki amma dai ban yarda ba, domin wlh ina ji a jiki na akwai abinda ya faru a gidan ta, uhm Ni zan faɗa miki wace ce Yusra a kan tsanar da tayi miki".

"Ya isa don Allah, Ni dai ba na son zancen nan, wlh kai na ciwo yake yi, daƙyar ma na ƙariso". Ɗahira ta ƙare maganar da dafe kanta, sosai take takaicin wannan sabon halin da ta gano na Shakira, "meyasa ma tun farko ta kasa gane ita ɗin me fuska biyu ne? Yanzu da ba don Fadila ta faɗa mata halin ta ba, haka zata zauna tana bugan ruwan cikin ta, tana nuna tamkar ta damu da ita, amma kuma a baɗini ba haka bane, Allah ya kyauta ya ƙara nuna mana maƙiyar mu a fili..

Maganar Shakiran ne ya dawo da ita guntun tunanin da ta afka

"Bari in sawo miki abinci ki ci".

Har ta miƙe Ɗahira tace da ita, "bar shi kawai, Ni bazan iya cin komai ba".

"Kenan dai da gaske ne Yusran ta cika miki ciki da abinci?" Shakiran ta faɗa cikin dariya, sai dai a zuciya baƙin ciki ne tamkar ya karta

Murmushi Ɗahira tayi tace, "ina mijin naki mu gaisa tunda rowan sa kike min?".

Dariyan ta sake kwashe wa dashi tana faɗin, "wlh kuma kin yi rashin Sa'a ne, domin yanzu ya fita, shaf kuma na manta ban ce masa ya tsaya zaki zo ba, sai ku gaisa".

"Haka kawai ki tsayar da shi don zan zo? A'a gwara ma da baki yi ba, wataran zamu haɗu ai, nima ba daɗe wa zan yi ba yanzu zan tafi".

Hararan ta Shakira tayi tana miƙe wa tace, "kan bu..! Wlh babu inda zaki je yanzu, daga zuwan ki? Ki bari zuwa anjima don Allah". Ta ƙare maganar sanda ta isa gaban Fridge ɗin ta, drinks ta ɗauko mata, ta haɗo da Cup ta kawo gaban ta ta ajiye akan Centre table da ta janyo, tsiyaya mata tayi ta miƙa mata

Ɗahira bata yi musu ba, ta amsa ta soma sha

Ita kuma ta koma ta zauna tana ce mata, "ɗazu muka yi waya da Fadila ai, take tambaya na baki zo ba har yanzu? Shi ne nace mata ai yau Hajja ta kira Ni ta sanar min zuwan naki".

Murmushi kaɗai Ɗahira tayi tana ci gaba da sipping Juice ɗin ta, a ranta jin ta kawai take yi, kuma ta san manufar ta, shiyasa ma ko magana ba ta son Yi, Allah-Allah take yi ta bar gidan ma, sabida gaba ɗaya haushin Shakiran take ji, ga kanta dake faman sara mata zuciyar ta duk babu daɗi, duk surutun da Shakiran take mata ba ta tanka ta, har dai ta gaji itama ta dena, sai suka koma zugun suna kallo

Nan Ɗahira ta tashi tace mata "zata tafi," har waje ta rako ta tana bata saƙon gaisuwa wajen mutanen gida. Motan ta na fita ta koma cikin gida da sauri ta wawuri waya don kiran YUSRA.


                 ⚫⚫⚫

         Sanda Ɗahira ta isa gida, tana shiga parlour'n su ta tarar da Aunty Zulaiha da Fadil zaune, da fara'an ta ta isa kusa da ita tana faɗin, "laa Aunty kin zo ne?"

Itama cikin fara'an tace da ita, "wlh kuwa, ina zuwa ai Aunty Amarya tace min kin fita zuwa gidan su Shakira da na tambaye ta"

"Wlh kuwa Aunty, Ina Ilham ɗin?"

"Tana wajen Kaka, kinga wanda ya kaita nan ya bar ta can".

Kallon Fadil tayi tace, "To je ka ɗauko min ita".

"Kai Aunty Ɗahira ki bari mana zuwa anjima in ɗauko ta, yanzu fa kika dawo".

Hararan sa tayi sai dai bata ce komi ba, ta tashi tsaye tana faɗin, "Aunty bari in rage kayan jikina sai in zo dai muyi hira, bari in shiga ɗakin Mama".

Tun kafin ma ta ƙarisa Fadil yace mata, "tana kichen ai".

Kichen ɗin ta wuce, ta sanar mata ta dawo, ita kuma tayi mata sannu da zuwa, sanann ta wuce ɗakin su ta sauya kaya zuwa jan doguwar riga me taushi mara nauyi, sannan ta sake fitowa, nan ta zauna sukai ta zuba hira da Aunty Zulaiha

Itama Aunty Amarya da ta fito zama tayi tana taya su hiran, lokaci bayan lokaci tana zuwa dubo girkin ta

Tashi Ɗahira tayi tace, "bari dai in je ɗauko ta tunda yaron nan ba zuwa zai yi ba". Ta ƙare maganar da dungure wa Fadil kai

Turo baki yayi yana cewa, "Kai Aunty! Kai Aunty! Ki bari to yanzu zan je ɗauko ta".

"A'a ba na so bar shi, ai ina da ƙafa ko?".

Aunty Zulaiha na musu dariya tace, "ai nima yanzu zan yi haraman tafiya, dama duba ƙanwar Baban Ilham ɗin ya kawo Ni, to shi ne na biyo gida".

"Eyya kina nufin Maman Sumayya?" Cewar Ɗahiran tana kallon ta

"Wlh ita fa, har a asibiti an kwantar da ita, ai asibitin mu ne ma aka kwantar da ita, baki sani ba ashe?"

"Wlh kuwa ban da labari, wani ciwo take yi?"

"Ciwon ƙoda ne take fama dashi, amma yanzu an sallame ta ai".

"Allah Sarki! Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne".

"Amen amen". Daga Aunty Zulaiha har Aunty Amarya da ta fito daga kishen yanzu suka amsa.

       Ɗahira fita tayi ta wuce Part ɗin Kaka, inda ta same shi a ɗakin sa yana Sallah, Ilham kuma na wasa a ƙasa da kayan wasan da Kaka ya zube mata, dayake ba ya rasa kayan wasa a wajen sa, sabida ita da Jinior ɗan wajen Aunty Zainab, duk idan sun zo suna kawo masa su, sai ya zube musu kayan wasan saboda kar su riƙa masa kuka.

       Ɗaukan ta tayi, ta hau mata wasa tana shilla ta tare da mata rawa

Lokacin da Kaka ya idar ya kalle ta yana murmushi yace, "dayake ai akwai me gadon zinare waje na, ga shi kin biyo ta". (sunan Umma Ilham ɗin taci, Bilkisu, kuma sunan Mahaifiyar Kaka ne dama Umma taci)

Dariya Ɗahira tayi tana tashi daga kan kujeran ta dawo gefen gadon sa, tunda dama gadon ya fi kusa da wheel chair ɗin sa, tace dashi, "kai Kaka.. dama ai ina zuwa duba ka, kwana biyu ne kawai ban samu na shigo ba, amma yanzu ɗin ma ai sabida kai na zo".

Murmushi yayi yace, "naga alama ai".

Dariya ta sake yi tana cewa, "baka yarda ba ko?"

"Na yarda Matata, to ya ƙarfin jikin?"

"Alhmadulillah Kaka, ai yanzu na samu lafiya har na kere ka ma".

"Ah Masha Allah Abu yayi kyau, fata na kenan dama Matata ta fi ni lafiya". Ya faɗa yana dariya

Itama tana taya sa

Lokacin ne Aunty Zulaiha ta shigo tana faɗin, "Mata da Miji sun haɗu waje ɗaya, hira ba ya ƙare wa, to na zo ɗaukar ɗiya ta zan wuce".

"Kai Aunty yanzu fa na zo". Cewar Ɗahira tana ɓata fuska

Shi kuma Kaka yace, "Ja'ira ko kunya ta ma ba kya ji kin zo ɗaukar ɗiyar ki ko?"

Dariya ta kwashe dashi tana cewa, "Kaka wani kunyan ka zan ji? Tafiya fa zan yi, amma idan kana so in bar maka ita, ai Ni abu me sauƙi ne a waje na, wlh sai in tafi in bar maka, gaba ta kai Ni wai gobaran titi a Jos".

"To ban ce ba, ɗauki ɗiyar ki ki tafi, me zan yi da wannan mummunan ɗiyar taki?".

Dariya suka saka gaba ɗaya, ganin yanda Kaka ya taƙume fuskar sa yana kallon Ilham kamar ya ga kashi

Aunty Zulaiha tace, "ai Kaka kai ta biyo wlh, kaima ka sani, kar ka wani tsine ta. Kuma Maman ka ce babu ruwana".

Taɓe baki yayi yace, "jaaa can da Allah! Ki ɗauki ƴar ki ki wuce kin ji, duk kin cika min kunne da surutu".

"Shikenan Kaka, kora ta kake yi ko? Babu damuwa ai, dani kake zancen wlh". Cewar Aunty Zulaihan tana ƙarisa wa ta ɗauki Ilham tana saɓa ta a baya

Dama sun saba irin haka sosai, kusan a jikokin gidan, Kaka da Aunty Zulaiha sun fi wasan jika da Kaka, idan suka haɗu waje ɗaya bakin ɗayan su ba ya shiru.

Tashi Ɗahira tayi, tace wa Kakan "zata je ta raka ta". Sannan suka fice tare.


⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

           *WASHE GARI*
                *12:30pm.*

             Shigowar motan Usman ɗin cikin asibitin, yasa Ayush buɗe motan Safra tana leƙa wa, sai kuma ta juyo ga Safran dake latsa waya tace da ita, "Ga shinan ya shigo".

Ɗago

Please Login or Register in order to submit comment