Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan, kasancewar yamma ta soma shiyasa babu wasu mutane sosai a waje, ta inda tasan ma baza ta same su ɗin ba ta nan tabi ta wuce sashin Hajja


Akwai mutane sosai a parlour'n suna zazzaune suna aiki, kasancewar parlour'n akwai duhun magriba har ta wuce ɗakin Baffa babu wanda ya kula da ita, bare ma a shaida ta, bare kuma gidan biki kowa sha'anin gaban sa yake yi.

Keey ta saka ta buɗe ƙofan bayan ta taɓa taji a rufe yake, ta tura ta shiga sannan ta mayar ta rufe, Direct Kan gadon sa ta nufa ta faɗa ta soma rusa kuka, kawai so take yi ta fitar da duk wani ƙuncin da ke damun ta, domin kuwa muddin bata fitar ba, dole ne tayi ciwo. Sosai tayi kukan babu me rarrashin ta, sai da ta gama ta miƙe zaune ta buga tagumi tana me ci gaba da tunanin zuci


"Ita bata ga makusa a jikin ta ba, duk inda mace me ji da class, me ji da kyawu da tsafta, gami da ilmi ta kai, to meyasa har yanzu ta rasa masoya? Meyasaka har yanzu ta rasa wanda zai ce mata zai aure ta? Ta san tana da farin jinin jama'a, kama daga mazan har matan, babu wanda ba ta harka da su, amma kuma babu wanda ya taɓa buɗe baki yace mata ya zo gare ta ne don soyayya, wanda kuma zai kai su ga aure, sai dai su zo a matsayin tana burge su, tunda tana burge su why baza su sanar mata suna ƙaunar ta ba? Ko kuma dama tana da makusa ne wanda be dace ta samu mijin aure ba?"


Runtse idanuwan ta tayi hawaye na sake silalo mata, cikin muryan ta da ya dishe sosai sabida kukan da tasha tace, "Allah gani gare ka, kai kace a roƙe ka zaka amsa, har yanzu bazan gajiya ba, kuma na san cewa kana ji na. Allah ka zaɓa min abinda yafi alkhairi a rayuwa ta, idan har auren nan ne alkhairi a gare Ni, ya Allah ka zaɓa min miji na gari, idan kuma babu alkhairi a tare da Ni, ya Allah zan rayu ina me gode maka, saboda haka ka tsara min rayuwa ta. Zaɓin ka kaɗai nake nema ya Allah, a duk sanda kaso ikon ka a kaina, a lokacin Ni kuma zan amsa ina me godiya a gare ka ya Allah, Allah na tuba ka yafe min". Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan

Ta jima tana yi kafin ta tsakaita tana me miƙe wa, sai hannun ta ya bigi drowan gadon wani abu ya faɗo, kasancewar ɗakin da duhu sai ta saka hannu zata laluba, hakan yasa ta kama wayan da tayar hannun ta na latsa wa a rashin sani, take a nan hasken ta ta kawo


Ƴar ƙaramar waya ce Nokia, wayan tabi da kallo, kamar ta ajiye sai kuma zuciyar ta ta bata umarnin latsa wa, take a nan ta danna ta ta cire ta a keey, nan ya bayyana wajen Text message, kasancewar daga wajen ne ba'a fita ba ta shiga keey


Rawa jikin ta ya soma saboda ganin text ɗin da ake turo mata, take ta koma ta zauna tana ci gaba da karanta wa, tabbas gaba ɗaya text ɗin da ake turo mata ne anan

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Kar dai ace Ya Baffa shi ne Masoyin ta na ɓoye?" Tayi maganar a fili tana ɗaura hannun ta ɗaya dake rawa a baki

"Ya Allah..." Ta sake faɗa tana kai idanun ta dake tsiyayar da hawaye kan wayan, ci gaba da karanta text ɗin tayi, sai kuma ta koma ta shiga ta duba Numban, take a nan taga Numban nata ne

Lumshe idanu tayi tana jin wani irin raɗaɗi a ranta, babu abinda ya faɗo mata a rai sai text ɗin sa na ƙarshe


"Hajja..!" Ta furta a laɓɓan ta tana me buɗe idanun ta

"Why Hajja? Me nayi miki? Dama ke ce kika hana Ni aure a wannan gaɓar? Ke kika raba ni da Masoyi na na haƙiƙa? Me nayi miki da zafi haka?".

Miyau ta haɗiye sabida jin wuyan ta ya cinƙushe da tuƙuƙin baƙin ciki, cikin kuka tace, "Ya Baffa meyasa ka kasa bayyana min kanka a matsayin wanda kake so na? Meyasaka ka zaɓi ɓoye min kan ka? Ashe dama da kai ne nake soyayya ban sani ba? Tabbas da baka ɓoye min kan ka ba, da duk haka be faru ba, ga shi Hajja taci galaban raba mu. Meyasa?.." ta kasa ƙarisa maganar dole tayi shiru

Tun soma maganar nata Baffa ya buɗe ƙofan ya shigo, yana tsaye bakin ƙofan yana jin komi, cikin tsananin ƙaunar ta tare da zallan tausayin ta yace, "Ƙaddara ce Ɗahira".


Saurin ɗago idanuwan ta tayi tana bin sa da kallo, duk da kuwa bata ganin sa sosai, amma hakan be sa ta kawar da idanun ta a gare sa ba

Yaci gaba da faɗin, "Nima sai daga baya na gane nayi wauta, tabbas da na bayyana soyayyar ki a fili, da duk hakan be faru ba, da mutanen gida sun goya mana baya, da Hajja bata ci galaba a kan mu ba. sai dai yanzu kuma babu yanda zan yi, sabida Hajja tarigada tayi min iya ka da hakan, idan har na bari wani yaji, tsinuwar ta shi ne zai ta bibiya ta, ban san ya zan yi ba Ɗahira, amma wlh ina tsananin ƙaunar ki, ke nake so a zuciya ta, kuma har na mutu bazan taɓa dena son ki ba".

Da gudu ta tashi tana toshe bakin ta, ta zo ta wuce sa ta bar ɗakin

Shima be hana ta ba, ko motsi ma be yi ba, illa runtse idanun sa da yayi hawaye na zubo masa kan kuncin sa.




⚫⚫⚫


Direct ɗakin Maman ta tawuce, ta shiga ta kulle kan ta ta hau rusa kuka babu ji babu gani, kukan da ke taɓa mata zuciya, yake ƙara mata raɗaɗin da ke cinkushe a zuciyar ta. Sosai tayi kukan wanda har ya haifar mata da ciwon kai me tsanani


Ita da kanta ta rarrashi kanta tayi shiru, sai dai duk yanda taso ta danne abun da take ji a ranta, ta kuma jure baƙin cikin dake zuciyar ta, ta kasa, gaba ɗaya rauni ne a zuciyar ta, waye zai rarrashe ta? Waye zai kwantar mata da hankali har taji sanyi a ranta? Ya faɗa mata tayi haƙuri haka ƙaddaran ta take?

Lumshe idanuwan ta tayi, hawayen dake maƙale a cikin idanun ta suka zubo saman kuncin ta, ta saka hannu ta share tana me miƙe wa zaune, kanta ta riƙe tana jan majina


"Allah Sarki Mamana, da ace kina nan ke ce zaki share min hawaye na. Meyasa ne Ni kuwa bani da Sa'a a rayuwa ta? Menene aibu na? Shin me na tare wa Hajja da ta tsane Ni har haka? Ya Allah.. ka saka min juriya domin in tsallake wannan jarabawar taka".


Miƙe wa tayi ta wuce Toilet ta ɗauro alwala ta fito, sallan magriba da isha'i ta gabatar, sannan tayi shafa'i da wutri, ta jima tana kwararo addu'a tana hawaye kafin ta shafa ta miƙe


Ta san Abbun ta ba anan zai kwana ba, sabida jama'a masu biki, kuma dama Aunty Amarya ce ke dashi, shiyasa ta kwanta a ɗakin tunda tasan ba ma zai zo Part ɗin ba.


Daƙyar a ranan barci ɓarawo ya ɗauki Ɗahira.





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫



Ranan Saturday 25 March 2021. Aka shaida ɗaurin auren *AL'AMEEN ABUBAKAR AL'AMEEN* tare da Amaryan sa *SA'ADATU ABDULLAHI*


*SHAKIRA ABUBAKAR AL'AMEEN* da Angon ta *SAHABI MAHMUD*


Sai *YUSRA NOOR AL'AMEEN* tare da Angon ta *SULAIMAN HABIB*


*FADILA AL'AMEEN AL'AMEEN* da Angon ta *KHABEER ALH. MUNIR.*


Ɗaurin auren da ya tara dubban jama'a ta ko ina, sai dai mu ce Masha Allah.


Zuwa huɗu ko wacce aka kai ta ɗakin ta bisa umarnin su Big Dady, Fadila aka wuce da ita Katsina da sauran jama'a. Yusra kuma da Shakira duk a nan Kaduna za su zauna, gidan Yusra ma ya fi kusa da gidan su, kuma duk ka su biyun za su ci gaba da aiki a Hospital ɗin su, sabida sai da aka yi yarjejeniya da mazajen nasu kuma sun amince.


Inda Baffa zai zauna kusa da gida ne, gini ne da aka yi musu shi da Usman a gefen gidan su, ga Gate ɗin gidan su ga nasu, sai dai kuma ta ciki a kwai ƙofan da aka yi wanda zai riƙa kai su cikin gidan su, ba sai sun yi wahalan fito wa ta Gate ba, wannan duk tsarin Kaka ne, shi ya siya filin kusa da gida, sabida yafi so iyalan sa su zauna waje ɗaya, har filin Fadil da yake ƙarami akwai shi an ajiye masa, idan ya tashi aure sai ya zauna a nan ɗin


Part ɗin Baffa dana Usman suna kallon juna ne, komi iri ɗaya aka yi musu, ɗakuna uku ko wanne da Toilet a ciki, sai babban Parlour da kichen a ciki da kuma wani Toilet, sannan idan ka fito waje ko wanne yana da faranda a ƙofan ɗakin, komi dai masha Allah, domin ba kaɗan ba an kashe kuɗi a ginin nan, su Big Dady duk suka yi musu komi babu ko ƙwandalan su, kayan ciki kuma suka bar musu su yi da kan su


To Part ɗin Baffa dai ya tsaru sosai, domin zance kuɗi yayi kuka a nan, iyayen Sa'adatu sun kashe mata kuɗi sosai, don ganin sun fito da ɗiyar su, itama zuwa dare aka kawo ta, can babban gidan aka fara kai ta, sai da aka kai ta wajen Kaka yasa mata albarka, sannan su Big Dady suka haɗa su da Baffa suka yi musu nasiha sosai. Daga nan kuma suka wuce wajen Hajja, inda itama tayi wa Baffa faɗa da nasiha sosai, akan "ya riƙe ta da amana, kar taji kar ta gani wajen ya muzguna mata, domin ita ɗin ƴar uwan sa ce, idan kuma aka ce ta kawo ƙarar sa, to wlh sai ta ɓata masa rai".


Shi dai be ce komi ba, har ta ƙarashe faɗan ta ta sallame su, suka nufo gidan su.

Sai mu ce Allah ya ba da zaman lafiya Amare.




⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫


Ɗahira dai taci bikin nan ne ba a daɗin rai ba, domin kuwa fama take yi da matsanancin zazzaɓi me zafi, kowa be san halin da take ciki ba, ko Kaka da take zuwan mishi hira, ƙin zuwa tayi bare ya san me ke faruwa da ita, shima be neme ta ba tunda ya san sha'anin biki ne


Fadila ita ke matsa mata tasha magani, domin sosai take bata tausayi, ita duk a ganin ta tana damuwa ne saboda rashin auren ta, bata san cewa Ɗahira ta kasa jure rabuwan da suka yi ne da Baffa ba, har yanzu abun na cin mata rai, shiyasa dole ciwo ya kamata.


A haka Aunty Amarya ta dawo ta tarar da ita babu lafiya, hankalin ta yayi matuƙar tashi, duba da yanda ta dawo ta ganta gaba ɗaya ta rame a ɗan kwana biyu kacal da ba ta nan, babu wanda ya duba lafiyan ta, har kuka sai da Aunty Amarya tayi, nan ta kira Abbun su take sanar mishi


Shima hankalin sa ya tashi sosai, tare da ɓacin rai da ya nuna a kan Umma, tunda ai ita ce take zaune da su, amma ta kasa kula da ita, ga shi gida ya hargitse da ƴan biki, shi kansa ba kwana a Part ɗin yake yi ba, kuma ko da yana son ganin yaran sa, yawan jama'a bazai bar sa ganin su ba, shi duk a tunanin sa da ita ake bikin

Dole aka ɗaura mata drip, sabida sosai take jin jiki, duk hankalin su Kaka ya tashi matuƙa, irin su Hajja Fatu kuwa murna fal ciki, domin duk a ganin su baƙin cikin rashin auren ta ne ya saka mata damuwa


Su ma su Kaka abinda suke tunani kenan, shiyasa tayi matuƙar ba su tausayi, a ranan Kaka ya zauna da ƴaƴan sa meeting, inda suka yanke shawaran kawai za su haɗa auren Ɗahira da Usman, tunda dai baza su zuba musu idanu suna kallon su sun ƙi aure ba, sai dai babu wanda ya tayar da zancen, sun bari sai nan da kwana biyu, lokacin an gama huta wa da bikin nan da suka yi.


Itama Ɗahiran sosai take samun lafiya, tunda ana kula da ita sosai

Baffa dai sau biyu yana zuwa gaishe ta, yanda Ɗahiran ta nuna masa ne, yasa shi jin daɗi, domin ko kaɗan bata sauya masa daga yanda suke da ba, gaba ɗaya ta nuna masa tamkar wani abu be faru tsakanin su ba, duk da a zuciyarta tana jin ƙaunar sa. Hakan sai ya mishi daɗi sosai, shima sai ya saki jikin sa yana jan ta da hiran da suka saba

A ranan na ukun ne da zai zo, suka taho da Sa'adatu don ta duba ta, amma daƙyar ta taho, don sai da suka yi faɗa da Baffa ɗin, da cewa tayi, "ba ta zuwa" amma da ya nuna mata ɓacin ran sa, dole ta biyo sa

Suna zuwa tayi mata ya jiki ta miƙe zata tafi, sai ta ga Baffa ma gyara zaman sa yake yi be da ninyan tafiya, ta kalle sa tace, "a'a ya haka kuma? Kai da za mu tafi kuma kake shirin zama?"

Kallon ta yayi, sai ya harare ta, sabida akwai Aunty Amarya a wajen, dayake suna zaune a Parlour ne har Ɗahiran. Kawar da kansa yayi ya soma jan Ɗahira da hira

Sai ta ja dogon tsaki tana faɗin, "Da kai fa nake yi ka zauna ina magana?"

A fusace Baffa ya kalle ta yace, "Ni sa'an wasan ki ne wai Sa'adatu? Ni ne zaki tasa a gaba sai ka ce ɗan ki?"

Murguɗa baki tayi ta hau jijjiga jiki, sai dai bata iya cewa komi ba sabida ganin yanda ya taso mata a fusace

Aunty Amarya ce tace dashi, "ya isa haka Miji na, tashi ka tafi tunda baka san me take buƙata ba, ka je kaji ka dawo anjima".


"But wlh Aunty Amarya this girl..."


"ya isa tashi ka je kaji?" Ta katse sa da faɗan haka cikin lallami


Miƙe wa yayi yana kallon Ɗahira da ta kawar da kanta yace, "Sweet sister I'm leaving, I will be back soon, we have something to talk about, Allah ya ƙara lafiya kinji?"


Gyaɗa masa kai tayi, a wannan karon tana kallon sa tayi masa murmushi tace, "to Yaya na, na gode".


Fuuuu Sa'adatu ta wuce ta bar parlour'n


Shima bin bayan ta yayi bayan ya sake yin ma Aunty Amarya sallama


Aunty Amarya ci gaba tayi da ɓare lemon dake hannun ta, a ranta sosai take mamakin abinda yasa Sa'adatu take kishi da Ɗahira, domin tuni ta gane abinda ke zuciyar ta, sai dai kuma bata san cewa da Baffa Ɗahiran tayi soyayya ba

Ɗahira kuwa gyara wa tayi ta kwanta kan two sittern da take kai, tana lumshe idanu tare da faɗa wa duniyar tunani, ita ko kaɗan abubuwan da Sa'adatu take yi ba ya damun ta, amma duk idan ta tuna da yanzu ita ce a makwafin Sa'adatu ɗakin Baffa, abun na mata zafi sosai a zuciya, har ta zubar da hawaye.




⚫⚫⚫⚫


Kai tsaye gidan su suka nufa, Sa'adatu tariga shi isa, inda ta zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun parlour'n ta tana faman karkaɗa ƙafa, sosai ta cika tayi maƙil tsaban kishi, ita ko kaɗan yanzu ba ta ƙaunar Baffa ya raɓi Ɗahira, gani take yi hakan zai saka mutanen gida su san me ke faruwa tsakanin su, kuma ta san ako yaushe za'a iya kawo mata ita a matsayin kishiya, tunda ita ɗin ƴar uwan sa ce, baza su yi la'akari da daɗewan auren ba ko rashin sa.


Shigowar Baffa ne ya dawo da ita daga guntun tunanin da ta afka


Kallon ta yayi kamar yanda take kallon sa yace, "ke wai Sa'adatu wani irin baƙin kishi ne kike son ki shigo min da shi gida na? Wato rashin hankalin naki ya kai har ki shiga tsakani na da ƙanwa ta? A kan me zaki riƙa min haka? Ke fa baki isa ki hana Ni abinda nayi ninya ba, kuma idan Allah yace Ɗahira mata ta ce, wlh daga ke har wacce take ɗaure miki gindin baku isa ku hana ba".


Sai kawai yaga ta fashe masa da kuka, cikin kukan take cewa, "wlh tallahi kamar a kunnen Hajja, wato kana nufin Ni da ita ba mu isa mu hana ka kula wancan yarinyan ba ko? Kenan Hajja bata da mutunci a wajen ka? Da kake cewa kar na shiga tsakanin ka da Ƙanwar ka; ai ba Ni ce na raba ku ba, wlh na gaji da abinda kake min, tunda ba ka gani na da mutunci ƙarar ka zan kai". Tana ƙare zancen nata ta tashi fuuuu ta fice tana ci gaba da kukan ta


Direct cikin gidan ta nufa, inda ta wuce Part ɗin Hajja don Kai ƙaran sa.


Ta bar sa nan tsaye da sakakken baki, sosai ransa ya ɓaci da abinda ta faɗa, "kenan shi be da ikon da zai mata faɗa, sai ta ɗibi ƙafafu ta kai shi ƙara wajen Mahaifiyar sa? Anya zai iya wannan auren kuwa?"











_to ba mu dai sani ba baffa. 🤷_


💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         \𝗙.𝗪.𝗔📚/

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

*TARIHIN FARILTA SALLAH*
'''An farilta sallolin nan biyar ne gabanin ƙaura, watau hijira, da shekara ɗaya da rabi. Sallah ce kaɗai ibadar da aka farilta ta a sama a daren Isra'e, kamar dai yadda aka ruwaito a hadisin nan na Anas. Da farko an umurce shi da Sallah guda hamsin ne; da sannu aka dinga rage su har suka zama biyar a bisa roƙon da shi Manzon ya yi wa Ubangijin sa. Da suka zama biyar, sai Allah ya ce masa su biyar ɗin nan, dai-dai suke da hamsin.
Malamai da yawa sun yi bayanin yadda sallar ma'aikin Allah, mai tsira da aminci, take gabanin Isra'en.
Wasu malaman sun ce, "Gabanin Isra'e, babu wata sallah wadda aka farilta sai sallar dare (Ƙiyamul lail) wadda aka umurci ma'aiki da yin ta ba da iyakataccen lokaci ko adadi ba, kamar yadda yake a suratul Muzzammil, ayoyi huɗu na farko:
"Ya wanda ya lulluɓe! Ka tsayu domin yin Sallah a cikin dare (duka) face kaɗan, rabin sa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi, ko ka ƙara kansa...
Ma'aikin Allah ya kasance yana yin sallar a kashi biyu cikin uku na dare ko a rabin sa ko kuma sulusin sa. Musulmi suka dinga yi tare da shi kamar shekara guda har suka gaji; daga nan sai Allah ya shafe ta don jin ƙan su.
An ruwaito cewa sallar da Musulmi suke yi gabanin tafiyar dare suna yin ta ne kafin faɗuwar rana da kafin ketowarta kamar yadda yake a sallah littafin Almanhalil Azb. Gabanin ƙaurar Annabi zuwa Madina raka'o'in sallah bibbiyu ne, bayan ƙaura ne suka zama hurhuɗu, illa magriba da ta kasance raka'a uku, ita kuma sallar subahi ta tsaya a kan biyu saboda dogon karatun da ake yi cikin ta. Buhari da Ahmad sun ruwaito daga Nana A'ishah cewa, "an farilta sallah raka'a bibbiyu, bayan ƙaura ne aka mai da ita raka'a hurhuɗu, amma an bar sallar tafiya a kan raka'a ne bibbiyu, sai sallar magriba ita ko da ma raka'a uku-uku ce."
Allah ya sa mu dace.'''

.

        *EPISODE Thirty One*

        Tunda Sa'adatu ta shiga parlour'n Hajja, ta tarar da ita zaune, sai ta ƙara volume ɗin kukan ta tana nufan kujera kusa da ita ta zauna

Kankace me Hankalin Hajja ya tashi, nan ta soma tambayan ta ba'asin kukan nata

Sa'adatu ta sanar mata da abinda ke faruwa, daga zuwa gaishe da Ɗahira Da Baffa ya matsa mata tayi, har maganganun da ya faɗa yanzu

"Lallai kam Baffa yana son Wasa Dani a gidan nan, amma bari miƙo min waya ta in Kira sa".

Tashi Sa'adatu tayi ta miƙo mata wayan daga kan Centre table, ta ba ta

Kiran sa tayi ta ba shi umarnin zuwa yanzu

Be daɗe ba kuwa sai ga shi ya shigo parlour'n da sallama

Tsaban tsiya ya ci ran Hajja, ko sallaman ma basu amsa ba, ta hau masa faɗa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba

Ganin abun yayi yawa, sai ya ce, "Hajja wai me tace miki ne da kike min irin wannan faɗan?"

"Uwar ka tace min, nace uwar ka tace min, wallahi tallahi Baffa ka fita ido na in rufe, idan ba haka ba zan mummunan saɓa maka a gidan nan, tunda kake baka taɓa gaya min magana ba, amma a kan wancan shegiyar yarinyan naga alamu kana so ka bijire min, to wlh kar in sake ganin ka raɓe ta, idan ba haka sai na.."

"Hayaniyar mene ne haka nake ji wai?" Cewar Abba da ya fito daga daƙi daga shi sai Singlet da dogon wando, da alamu dai barci yake yi Hajja ta tashe shi da hayaniyar ta

Daga Baffa har Sa'adatu duƙar da kansu suka yi, sun kasa cewa komi, sai Hajja ne da ta cika maƙil da fushi tana shirin magana

Ya katse ta da faɗin, "ya isa, ku tashi ku tafi gidan ku".

Tashi suka yi daga Baffan har Sa'adatu suka fice

Sannan ya juyo kan Hajjan yace, "wai ke Fatima me kike so ki zama ne? Me Baba na yayi miki da kike son hana sa kwanciyar hankali shi da matar sa? Duk abinda kike faɗa ina ji, wlh idan har baki fasa shiga sha'anin auren su ba, to watarana zaki ji kunya, kuma da kike son raba sa da ƴar uwan sa, kar in ji kar in gani, domin zan mummunan saɓa miki kema, wannan ai rashin hankali ne, tukuna ma me Uwata tayi miki ba kya ƙaunar ta?"

Shiru Hajja tayi don bata san me zata ce ba, shaf ta manta da yana ciki da tun farko bata ɗaga muryan ta yaji ta ba

Ƙwafa yayi kafin yace, "ki ci gaba kar ki fasa". Ya juya ya shige ɗaki

Sosai ran Hajja ya ƙara ɓaci, a ranta ta ɗau alƙawarin muddin tana numfashi sai ruwan sha ya gagari A'isha da ɗiyar ta.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

       Ranan Monday Ɗahira ta koma bakin aikin ta, saboda sosai jikin ta yayi sauƙi

Shima Baffa ranan ya koma, tunda sati biyu kenan da auren su

Nan hankalin Sa'adatu ya tashi matuƙa, domin gani take yi, Baffa ya koma bakin aiki ne duk sabida ya ga Ɗahira ta koma aikin ta, kuma tasan a can dole su riƙa haɗuwa, wannan abun duk ya dame ta, taje ta sanar wa Hajja

Hajja tace, "ta bar su, zata saka musu idanu, kuma zata yi wa Baffa gargaɗi sosai" domin ita kanta Hajja yanzu ba ta ƙaunar alaƙar Baffa da Ɗahira, hanya mafi sauƙi take son samu don raba su, sam ba ta ƙaunar su ci gaba da yanda suke kamar da, tunda yanzu a ganin ta yayi aure, hakan zai cuta wa Sa'adatu.

       Baiwar Allah Ɗahira, ko kaɗan ma bata san wainar da suke toya wa ba, babu ruwan ta, abinda ta saka a gaba shi take yi, a ranan ma da ta dawo aiki ta shirya zuwa gidan su Shakira, tunda ko sau ɗaya bata je ba, da biki bata da lafiya, kuma Aunty Amarya ne ma ta matsa mata taje ɗin, kar ace tana baƙin ciki ne mutanen gida su yi wani fassara daban, shiyasa yau da wuri ta tashi a aiki, zuwa ƙarfe ɗaya da

Please Login or Register in order to submit comment