Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min uzuri. Mahaifiya ta ta haramta min zuwa gare ki, domin ta ce "idan har na aure ki bata yafe min ba," ta rigada ta zaɓa min matar da zan aura, don Allah! Kiyi haƙuri domin ba'a son Raina zan bar ki ba, sai don bin umarnin mahaifiya ta, amma ki sani ina matuƙar ƙaunar ki, har in koma ga mahalicci na bazan taɓa dena son ki ba."_

_A.A.A. Masoyin ki._✍️



Lumshe idanuwan ta tayi, hawayen dake tsiyaya akan kuncin ta tun soma karanta text ɗin; suka ci gaba da kwaranya, wani irin ƙunci ne ya tokare mata maƙogwaro, wanda daƙyar take iya haɗiye yawu


Dauriya dai me dauriya sai da ta gwada yin shi, amma ta gaza, dole ta zube kan gadon ta hau rusa kuka, kuka take yi sosai zuciyarta na mata zafi tamkar zai faso ƙirjin ta


Taya ma zata iya jure wannan halin da take ciki, meyasa zai mata haka? Meyasa zai tafi ya bar ta a lokacin da take buƙatar sa cikin rayuwan ta? Ya tafi ba tare da ta gansa ba, ya tafi ba tare da tasan sunan sa ba, dama ashe ba son ta yake yi ba? Meyasa to ya koya mata ƙaunar sa?...


Fadila ce ta shigo ɗakin, ganin Ɗahira a wannan halin, sai tayi saurin ƙarisowa wajen ta hankalin ta a tashe, ta hau tambayan ta "lafiya?"


Cikin kuka Ɗahira ta bata amsa,
"He is gone ..! Wlh I really love him, ban taɓa son wani ba sai shi, meyasa zai tafi ya bar Ni?.." ta kasa ƙarisa wa illa kukan da taci gaba da yi, hawaye na ambaliya a kyakykyawar fuskar ta


Sosai Fadila ta tausaya mata, riƙo ta tayi tana faɗin, "ki nutsu Ɗahira, tell me what happened, shin wane ne shi wanda ya tafi ya bar ki?"


Ɗago idanun ta da suka kaɗa suka yi jazur tayi ta aza akan Fadila, cikin raunin murya take faɗin, "wanda muka yi alƙawarin aure dashi, ya ce min Mahaifiyar sa ta haramta masa aure na, me zai saka yayi min haka? Me zai sa in ba aure na zai yi ba ya zo ya koya min son sa? Meyasa tun farko ya zo wuri na?" Taƙarishe maganar cikin kuka


Da mamaki take kallon ta, sabida ta san babu wanda ke zuwa wajen ta, tunda take bata taɓa ganin Ɗahira ta kawo baƙonta gidan nan ba, "shin aina shi kuma wannan suke haɗuwa?" Tayi ma kanta tambayar, sai dai babu me bata amsa, dole ta kawar da zantukan daga ranta ta soma rarrashin ta. Ta daɗe tana rarrashin ta, amma Ɗahira ta kasa yin shiru, dole ta haƙura ta bar ta, ta miƙe tabar ɗakin.


Kuka sosai Ɗahira tayi, kukan da ke fitowa daga zuciyar ta. Tunda take bata taɓa yin soyayya ba, koda da rana ɗaya bata taɓa son wani ba, amma kuma ta rigada ta kamu da ƙaunar wannan bawan Allan da bata san ko shi waye ba, bata san sunan sa ba, ko kaɗan baza ta iya juran rasa shi ba, soyayyan gaskiya take mishi, taya lokaci ɗaya zai tafi ya bar ta a lokacin da take matuƙar buƙatar sa? Wannan amsoshin su suke yawo a zuciyar ta, wanda ya ƙara haddasa mata cinkushewar baƙin ciki a ranta


Allah ya gani ita baƙuwa ce a soyyayya, ko kaɗan baza ta iya juran wannan yanayin ba.


Har Fadila ta sake dawowa ɗakin Ɗahira na kwance tana kuka


"Wai don Allah Ɗahira baza ki dena wannan kukan da kike yi ba? Taya kuka zai miki maganin matsalan ki? Ke fa ba ƙaramar yarinya ba ce". Cewar Fadilan tana kallon ta daga bakin gadon ta da ta tsaya


Ɗahira bata ce komi ba, illa miƙe wa da tayi ta shiga Toilet, alwala tayi ta fito ta soma gabatar da sallan isha'i da aka daɗe da yi, har ta idar tana zaune a wajen ta kasa tashi, sai ma haɗa kanta da gwiwowin ta da tayi; tayi shiru tana tsiyayar da hawaye


Fadila dake kwance tana faman latsa waya, ta kalle ta tace, "I forgot I didn't tell you, Aunty Amarya is calling you".


Shiru Ɗahira tayi mata


Ita kuma bata sake bi ta kanta ba, taci gaba da charting ɗin ta ita da K.B, tana yi tana sakin murmushi.


Sai da kusan mintuna goma suka shuɗe sannan Ɗahira ta tashi ta fice, babu kowa a Parlour, kai tsaye ta wuce ɗakin Maman ta. Sai da tayi sallama aka ba ta iznin shiga sannan ta shige


Aunty Amarya na zaune akan sallaya, shi kuma Abbu na gefen gado zaune yana waya, da alamun wayan me muhimmanci ne shiyasa gaba ɗaya attention ɗin sa ya ba wa wanda suke wayan ne


Durƙusa wa gaban Aunty Amarya tayi, cikin dashashshiyar muryan ta na wanda tasha kuka tace mata "ga ta".


"Ya naga kamar kin yi kuka? What's wrong with you?" Aunty Amarya asked her this question keeping an eyes on her


Sake sunkuyar da kanta ƙasa tayi, in a weak voice and said, "nothing".



Shiru Aunty Amarya tayi na ɗan wani lokaci, sai kuma tace, "je ki kici abinci, kar ki kwanta da yunwa kin ji ko?"


Gyaɗa mata kai tayi tana miƙe wa ta fice


Aunty Amarya tabi ta da kallo cike da tausayin ɗiyar ta ta, tabbas ta san akwai ɗinbim damuwa a tattare da ita, kuma ta gane kuka tayi, amma kuma ba ta son ta dame ta da tambaya a wannan lokacin ne har sai ta samu sauƙin damuwar nata..


"Har kin sallami Maman nawa ne?"


Maganar Abbu ya katse mata tunanin ta, sai ta juyo tana kallon sa, ta ce, "eh, na ga ai kana waya ne, kuma bata ci abinci ba shi ne nace ta je taci. Ko in Kira ta ne?".


"No. Let her eat her food."


Koma wa Aunty Amarya tayi ta zauna, don har ta rigada ta yunƙura zata tashi.







⚫⚫⚫


Ɗahira na fita bata ci abincin ba ta koma ɗaki, domin baza ta iya saka komi a bakin ta ba, ko da taci kuwa, baza ta ji daɗin sa ba.


Tana shiga ta haye kan gadon ta ta kwanta, sai dai ta daɗe kafin ta samu barci ya ɗauke ta, gaba ɗaya tunani ya hana ta sukuni, sai daƙyar ta samu tayi barci.



Washe gari da zazzaɓi ta tashi, dole ta sake komawa ta kwanta bayan ta yi sallan asuba, har gari ya waye bata farka daga barcin da ya ɗauke ta ba.



Kowa ya hallara wajen Breakfast amma ban da ita


Aunty Amarya tambayan Fadila tayi "where is she?"


Sai ta faɗa mata, "she was sleeping, she didn't wake up".



Har ta ce "taje ta taso ta sabida kar tayi lattin zuwa wajen aiki"


Amma Abbu ya ce, "su bar ta".


Har suka gama Breakfast ɗin, shi da Fadil suka fice, Umma ta shige ɗakin ta, yayinda Fadila kuma ta koma cikin Parlour ta zauna abun ta tana aikin latsa waya


Aunty Amarya har ta koma ɗaki, sai kuma ta kasa jure wa, don tasan Ɗahira sarai, tunda ta kwanta ba lafiya ba, bare yanda take son Aikin ta, haka kawai yau ranan aiki ba zata ƙi fitowa ba in babu Dalili


Ɗakin ta wuce kanta tsaye don ta duba ta. Tana shiga ta hange ta saman gado ta rufe kanta da blanket, da sauri ta ƙarisa wajen gadon ta saka hannu ta yaye saman kanta, fuskar ta take kallo tana kiran sunan ta


A hankali Ɗahira ta buɗe idanuwan ta da suka yi ja, ta aza su kan Maman ta


"Baki da lafiya ne, me ke damun ki?" Ta jero mata tambayar a yanayin damuwa


Cikin matuƙar sanyin murya da ciwo yake cin ta tace, "zazzaɓi ne ya rufe Ni Mama".


Cike da tausaya wa take mata sannu, kana tace mata, "ta tashi tayi wanka, inyaso sai ta sha magani bayan taci abinci".


Babu yanda ta iya haka ta miƙe, da taimakon Aunty Amarya har ta ƙarisa Toilet


Ita kuma Aunty Amarya ta fice haɗo mata Breakfast don ta kawo mata har nan cikin ɗakin. Bayan ta haɗo mata ta kawo mata ta zauna zaman jiran ta.


Kamar shuɗewar mintuna sha biyar Ɗahira ta fito a Toilet, ɗaure take da towel me tsawo iya ƙasan gwiwan ta, sai ta saka wani da ya rufe mata kanta zuwa kafaɗun ta


Tana fitowa Aunty Amarya tace, "yi maza ki shirya ki zo ki karya ki sha magani, kina likita amma kina wasa da shan magani, wataƙil ma tun jiya da kika yi kukan naki zazzaɓin ya kama ki amma kin zauna baki sha magani ba".


Kallon ta Ɗahira tayi da sauri, sai kuma ta kawar da kanta cike da sanyin jiki ta kariso gaban Sip ɗin kayan su, buɗe wa tayi ta ciro doguwar rigan atamfa. Sai da tagama shirya wa kafin ta iso gaban aunty Amarya dake bakin gadon ta, a ƙasa ta zauna ta tanƙwashe ƙafa ta soma shan tea ɗin da ta haɗa mata, tana yi tana haɗa wa da bread kamar yanda Aunty Amarya ta umarce ta, sai dai tana cin ɗaya biyu taji kamar zata yi amai, ta kalli Aunty Amarya ta marairaice fuska kamar zata yi kuka tace, "zan yi amai bazan iya ci ba".


"To shanye tea ɗin ki sha maganin".


Ajiye bread ɗin tayi da ƙwan, ta sha tea ɗin, har sai da takusa shanye wa kafin ta amshi maganin ta kora da sauran


"Ina jin ki, Why are you crying? What's wrong with you?"




Sunkuyar da kanta Ɗahira tayi don bata san me zata ce mata ba


"Ina magana kin yi shiru, meyasa zaki zauna ki saka damuwa a ranki har kiyi irin wannan kukan da ya haddasa miki ciwo? Bayan kin san halin kanki abu kaɗan ne yake haddasa miki ciwo idan kin saka damuwa?".


Matso hawaye Ɗahira tayi, har yanzu ta kasa yin magana tunda bata san yanda za'a yi ta faɗa ma Mahaifiyar nata matsalan ta ba


"Ko sabida ya ƙi zuwa ne kike kuka?"


Ɗaga mata kai tayi, kafin ta cire kunya ta sanar mata komi


Ajiyan zuciya Aunty Amarya ta sauke, cike da tausayin ɗiyar ta tace, "ki yi haƙuri haka Allah ya so dama ba shi ne wanda zaki aura ba, Allah ya musanya miki da wanda ya fi shi, amma ki dena saka damuwa a ranki kinji? ki fauwala wa Allah komi, ai Kakan ba cewa yayi zai zaɓa muku wani ba idan baku kawo wanda zaku aura ba, don haka ki dena saka maganar auren nan na damun ki".


Gyaɗa mata kai tayi


Sai da ta sake tausan ta kafin ta fice ta bar ta


Sosai maganar Maman ta ya sanya ta jin sanyi a ranta, dama ita yanzu damuwar ta yanda kowa zai kai zaɓin sa, amma ita ban da ita.


A haka ta saki jikin ta a ranan taci gaba da walwalan ta, sai dai bata je aiki ba ta bar wa gobe.
[6/3, 5:48 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓

𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️

𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.




*EPISODE Twenty-Five*


Kamar yanda Hajja Fatu tace zata kira Hajiya Amina su yi magana, hakan kuwa tayi, sun gama ƙulle-ƙullen su a waya, kafin suka yi sallama akan zata turo Sa'adatu gobe-goben nan kamar yanda ta buƙata, yanzu ɗin ma don ba ta kusa ne da sun yi waya.


Washe gari zuwa yamma sai ga Sa'adatu ta dira garin Kaduna


Hajja Fatu zuwa tayi har ɗakin Baffa ta tasa shi gaba akan "lallai-lallai sai ya je ya ɗauko Sa'adatu a airport".


Ba da son ransa ba haka ya tashi ya saka riga a saman Singlet ɗin dake jikin sa, ya fito ya wuce ya shiga motar sa ya bar gidan, a cikin mota in banda tsaki da yake saki babu abinda yake yi, kaso mafi rinjaye na zuciyar sa yana ga Ɗahira, ya rasa meyasa zuciyar sa ta kasa nutsuwa da halin da ya saka ta, yana ji a jikin sa tabbas tana wani hali a sanadiyar Text ɗin da ya tura mata, amma ya zai yi? Bazai iya zuwa ya same ta ba, bazai iya jure ganin damuwa a kyakykyawar fuskar ta ba, ya gummaci ƙaurace mata har sanda komi zai dai-daita. Lumshe idanuwan sa yayi yana buɗe wa sai ga hawaye sun zubo masa a kunci, hannu ya saka ya share yana jan numfashi cike da takaicin Mahaifiyar sa, zuciyar sa sosai take mishi ƙunci fiye da tunanin mutum, yana ji a ransa bazai iya jure wa ba, bazai iya auren kowa ba face Ɗahira, dole ya sake yi wa mahaifiyar shi magana, ko zata iya tallafa wa rayuwar sa, Allah ya gani ba ya ƙaunar yarinyan nan da za'a liƙa masa, sannan kuma bazai iya zuwa ya tunkari wata ɗiya mace da sunan so ba, bare har ya iya auren ta, ita dai Ɗahiran da Hajja ba ta so ita zuciyar sa ke so..



Be fasa tunanin sa ba har sanda ya dangana ga airport ɗin, tunda ya faka motan ya hange ta, sabida kasancewar ta doguwar mace, idan har ta tsaya cikin mutane nan da nan ake iya gane ta, ga ta fara kuma tana ƙara wa dana kanti


Ya ɓata lokaci cikin motan kafin yaja numfashi ya buɗe ya fito, yana hangen ta sai faman waige-waige take yi tana duba agogon dake ɗaure a tsintsiyan hannun ta. Lumshe idanu yayi ya sake buɗe wa a kanta, kamar bazai taka ya isa wajen ta ba, sai kuma ya daure cike da baƙin ciki ya nufe ta, fuskar sa babu ko alamun walwala


Sai da ya dangana ga inda take tsaye, sannan ne ta hange sa, ai nan ta saki murmushin da ya bayyana haƙoran ta, wanda da gani kasan tana cikin tsantsan farin ciki, kiran sunan sa tayi tun kafin ya ƙariso


Sai ya kau da kai yana sake ciccin magani, ya tsaya cak a wajen


Ɗaukar jakar ta tayi ta nufo sa tana sake washe baki, tana iso wa wajen sa ta soma gaishe sa cike da fara'a, amma yanda ya amsa mata ne sai walwalan ta ya ragu


"But yaya lafiya dai ko?" Tayi masa tambayar tana kallon sa


Be ce mata komi ba ya juya ya nufi motar sa


Sai ta tsaya kawai tana kallon sa baki sake, duk da ta san ba ya son ta amma ai suna mutunci sosai ba kamar yanda ya nuna mata haka ba, "so what's wrong with him?" Tayi wa kanta tambayar har yanzu tana tsaye a inda take. Sai da taji horn ɗin motan sa kafin ta ankara, taja akwatin ta ta nufi motan, buɗe bayan tayi ta saka akwatin kafin ta shiga gaban motan ya ja suka bar wajen.



A cikin motan ma babu abinda yace mata, duk da kuwa ta sake tambayar sa abinda ke damun sa, amma yayi mata banza, har suka kai gidan ya sauke ta yaja motar sa ya bar gidan


Tsaye tayi a wajen tana bin motar har ya ɓace wa ganin ta, sai kuma jiki a sanyaye taja Trolly ɗin ta tayi cikin gidan, duk wanda ta gani a hanya gaishe sa take yi har ta isa Part ɗin Hajja Fatu


Sosai Hajja Fatu tayi murna da ganin ta, nan tayi ta nan-nan da ita har ta cika mata gaban ta da kayan ciye-ciye


Ruwa kawai ta ɗauka tasha, sannan ta kalli Hajja Fatu tace, "Hajja where is Shakira I didn't hear her movements?".


"Ai kuwa Shakira tana wajen Yusra, amma yanzu zaki ga ta zo tunda ta san an tafi ɗauko ki".


Gyaɗa kai Sa'adatu tayi, kafin ta sake cewa, "Hajja is something happened to Yaya Baffa? na ga tunda muka zo be ce min komi ba ne?"


Murmushin yaƙe Hajja tayi tace, "bar shi nan yanda kika ganshi, shi ya san me ke damun shi".


Langaɓe fuska tayi tace, "eyya Hajja taya zan bar shi bazan damu ba? kinga fa shi ɗin Yayana ne, wlh baki ga tunda muka biyo hanya duk na gama damuwa da halin da na ganshi, ko dai Ni ce ba ya son gani?".


Hajja tace, "Taya Zaki ce haka? Ina ruwan shi dake da zai ce ba ya son ganin ki? Kin San tunda nayi masa maganar bazai auri yarinyan da ya zaɓa bane, shi ne ya dena min magana, ko abinci ma ba ya ci a nan, ya dena walwala gaba ɗaya, Ni kuwa bazan yarda ya aure ta ba bayan ga ki kina son shi, muddin idan be kawo wacce yake so ba, to ke ce matar sa da yardan Allah kamar yanda muka tsara".


Washe baki Sa'adatu tayi, cike da farin ciki tace, "Allah ya amsa bakin ki Hajja ta. Amma to wace ce wacce ya ke so ɗin?".


"Kar ki damu ba sai kin san ta ba, don ba na son ma maganar tariƙa tsawo azo kuma a samu matsala, maganar ta faɗa kunnen wani".


"Haka ne Hajja, amma ai Yakamata ki sanar dani tun wuri, don wlh har na ji tsanar ta a raina, kinga kuwa gwara in santa in San yanda zan yi zama da ita koda watarana na ganta".


Taɓe baki Hajja Fatu tayi tace, "ai kin ma santa tunda ba wata ƴar nesa bace, Ɗahira ce ta nan gidan".


"What ..! But wlh Hajja I hate this girl so much, God forbid that you forbid her, Allah yasa gwara da kika hana, don wlh wannan yarinyan idan ta aure sa babu ke babu ɗanki, domin irin su ne masu raba uwa da ɗan ta, sai dai ki riƙa hangen sa daga nesa".


"Ai nima shi na gani, ya rasa wacce zai aura sai ita, ba ga shi ba muna gani a wajen uwar ta, yanda take juya Al'ameen, Bilkisu kuwa ta zama abun kallo kamar ba ita ce matar sa ta farko ba, sai abinda tace za'a yi, ke wlh in gaya miki duk iyayen nasu maza sun fi ƙaunar ta, idan har wani abu zai fito daga hannun su to ita suke ba ma wa, ko Kaka shima idan zai yi shawara da matan gidan ita yake kira, komi yace A'isha, uhmmm wlh abun yana baƙanta mini Rai, shiyasa na matuƙar tsanar ta sabida gaba ɗaya Kaka ya rage nuna min kula wa kamar baya, burina kawai ta bar gidan nan tunda Innar ku Safiyya bata aure sa ba, to nima bazan samu kwanciyar hankali ba har sai na kora ta ta bar gidan nan. Mu dai bar maganar nan ki ci abinci tukunna".


"Ok Hajja". Sa'adatu tafaɗa tana saka hannu ta buɗe coolarn


Daga nan sauya hiran suka yi, inda Hajja take tambayan ta mutanen gida da basu gaisa ba.






⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫


Gaba ɗaya a kwanaki biyun nan da suka wuce Ɗahira ta sauya, ba komi ya sauya ta ba illa kewar masoyin ta, a kullum ranan duniya zata ɗau wayan ta sau babu adadi don ganin ko zata ga message ɗin sa, sai dai kuma har ranan ta wuce baza ta ga ko me kama da Numban sa ba, ta kasa haƙura har kiran Numban tayi, amma kuma a kashe ne kamar ko yaushe, duk ta rasa nutsuwar ta ta saka wa kanta tunani, kullum bata da aiki sai tunanin sa, idan ta je Office ma zama take yi tayi ta faman tuna sa, har mafarkin sa tana yi wai ga shi sun haɗu, tabbas sosai take son bawan Allan nan da ya guje ta, ta kasa cire sa a ranta ta saba da rashin sa, ga shi ya tafi ya bar ta koda sunan sa ne bata sani ba, illa kawai A.A.A. da ya rubuto mata a ƙarshen text message ɗin da yayi mata na ban kwana, kuma duk iya tunanin ta na ganin ta gano ma'anar A.A.A ɗin ta kasa, haka zata zauna ta saka wannan sunan ta saka wancan sunan don ganin ta ba shi suna, amma ko wanne ta saka sai ta ga be dace ba.


Ga shi tana son tayi magana da Baffa, koda zai ba ta shawara ne, amma kuma ta kasa ganin sa shima, shi kaɗai ne wanda zata iya faɗa masa damuwar ta amma kuma duk idan taje office ɗin sa ba ta ganin sa, dole yau bayan ta shirya zata wuce aiki, sai ta fara wuce wa Part ɗin su ta duba sa, wataƙil akwai abinda ke damun sa ne ba ta ganin sa a Hospital, Tabbas tana ji a jikin ta ba ya zuwa ne, idan da yana zuwa dole zai neme ta.


A time ɗin su Hajja Fatu duk sun tafi aiki, illa Sa'adatu dake zaune ita kaɗai a Part ɗin, tana Parlour ne tana Breakfast tana latsa wayan ta, sai ta jiyo sallaman Ɗahira da ta shigo parlour'n, ɗago kai tayi tana kallon ta, sai ta ɓata fuska tana kau da kanta


Ita kuwa Ɗahira fara'a ta saka a fuskar ta tana cewa, "ah ah yau Sa'ada ce a gidan na mu? Saukar yaushe ba mu da labari?"


Sa'adatu bata ɗago kai ba, sai tsaki da taja tana kai loman abinci


Hakan sai ya sanyayar wa da Ɗahira jiki, bata sake cewa komi ba tayi hanyar ɗakin Baffa


"So, Ma'am, where are you going?"



Juyo wa Ɗahira tayi tana kallon ta, hakan yasa suka haɗa ido


Sai Sa'adatu ta banka mata harara tace, "dama kin bar wahalar da kanki a kan Ya Baffa, domin kuwa shi ɗin nawa ne Ni kaɗai, ba'a yi macen da ta isa ta ƙwace min shi ba, don haka idan ma zaki nemi mijin ki a can wani wajen ki nema, domin dai Baffa nawa ne, nima kuma tashi ce".


Baki sake Ɗahira take bin ta da kallo, a haƙiƙanin gaskiya Sa'adatu ba wai haushi ta ba ta ba, illa dariya da maganar nata ya bata, wanda har sai da ta murmusa, a ganin ta in ba hauka ba, Taya ma zata ce ta zo wajen Baffa ne domin neman soyayyar sa, bacin ta san da cewa shi ɗin yayan ta ne, ko kaɗan bata taɓa kallon Baffa a matsayin wanda zata iya aure ba, ba wai don wani abu ba, a'a, sai dai tana mishi kallon wanda suka fito ciki ɗaya, duk yanda mutane suke fassara su bata taɓa koda kallon abun hakan ba, "to meyasa su suke wannan tunanin?" Ta tambayi kanta idanuwan ta akan Sa'adatu tamkar da ita take yi, sai dai yanda tayi maganar a hankali babu wanda zai iya ji bare ya bata amsa. Ajiyan zuciya ta sauke sannan ta juya taci gaba da tafiya zuwa ɗakin nasa, don a ganin ta ɓata lokaci ne ta zauna tana biye wa Sa'adatu, tasan ciwon kanta, duk da a girme dai baza ta girmi Sa'adatu ba, amma kuma za su yo sa'anni da juna.



Tana zuwa ƙofar ɗakin ta cinma a rufe yake, bata yi ƙoƙarin buɗe wa ba duk da kuwa tana tare da keey ɗin ɗakin shi a cikin nata, tunda tasan shi dai ta zo nema ba wani abun ba, shiyasa ta juya ta wuce tabar Part ɗin baki ɗaya, ko kallon inda Sa'adatu take zaune ma bata yi ba. Motan ta ta hau ta wuce Hospital, tana isa ta fara zuwa Office ɗin Baffa, amma kuma babu shi sai dai Office ɗin a buɗe yake, kai tsaye lefter ta hau ta koma Office ɗin ta, ta soma duba Patients ɗin ta, tunda a time ɗin har sun soma zuwa.
[6/4, 11:48 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎


Please Login or Register in order to submit comment