Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna ta zuba zance"


Salma ita da su Shamsiyya suka tashi suka haɗo musu abincin, duk sun baje a parlour'n suna ci suna ci gaba da hiran su cike da nishaɗi.


Ƴaƴan Hajiya Lailan ne guda biyu maza, Bashir (Abba) da kuma Yaseer suka shigo cikin parlour'n, yanzu haka ko wannen su da iyalan sa, shi Abban ne babban jikan gidan


Gaishe su suka yi cikin girmamawa, su ma suka amsa cike da fara'a da nuna farin cikin su na ganin su, har da tambayan su Baffa da Usman tare da sauran ƴan gida, duk suka amsa musu da "lafiya lau sun ce a gaishe su," daga nan suka wuce ɗakin Mahaifiyar su suka bar su nan suna ci gaba da hiran su


Ɗahira ce ta kalli Fardausi da ta cika su da Surutu, don ita ce ma ƙarfin hiran, cikin tsokana take ce mata, "Ni wlh da an haɗa ku gaba ɗaya Dady ya aurar daku, ko gidan ma sun huta da surutun ki, yarinya ko haɗiye yawu ba ta yi".


Dariya gaba ɗaya aka kwashe dashi


Ita kuma Firdausin gyara zaman ta tayi har da karkace ɗankwalin kanta tana faɗin, "me kuke ci na baka na zuba? Ai wlh marriage is time and I'm here to do, amma wlh bazan yarda a haɗa Ni da Salma ba, dole sai na zauna nima na taɓa ƴan matanci na Ni kaɗai, haka kawai ai bazai yiwu ba".


Hararan ta Salma tayi tace, "dalla yi mana shiru, Ni wlh ban san ma meyasa Dady ya ƙi tilasta miki fiddo da mijin ba, uwar ma me zaki sauna yi musu bayan ba kya cas ba kya as".


Itama dai Firdausin hararan nata tayi tace, "eh naji dai, baza ai mana auren tare ba ƴar baƙin ciki, wlh nima yanda kika fara aiki kafin kiyi aure, nima bazan yi ba sai na soma aiki na".


Tsaki kawai Salma taja tana sake kwaɗa mata harara


Firdausin ramawa ta kuma yi, har da murguɗa baki


Dama sun saba kasancewar saƙo da saƙo suke, bare kuma dama Salma tana jin haushi an ce ta fito da miji a haɗa da na sauran yayyin su biyu maza da za ayi musu aure, ita kuma Firdausi da sauran ƴan matan ba'a ce musu ba, hakan yasa take jin haushi tunda ba'a haɗa su gaba ɗaya ba


Su dai sauran sai dariya suke musu, basu tashi ba sai da aka kira sallan la'asar, sai ma lokacin ne su Ɗahiran suka tuna basu yi azahar ba, ganin ƴan uwa da hira ya shagaltar dasu


Ɗakin su Salma suka wuce, wasu daga cikin su kuma suka koma nasu Part ɗin, sallan suka gabatar kafin Ɗahira ta miƙe tana kallon Firdausi dake zaune kan sallaya, tana latsa wayan ta da aka kira time ɗin tana sallah


"Fido tashi ki raka Ni mukai gaisuwa wajen Granny da ƴar tsohuwar matar sa, tun kafin ma ya aiko".


Ɗago kai Firdausi tayi tana dariya tace, "wlh nima dai naga haƙurin sa da be aiko a kira ki ba".


"Ko dai be san ta zo bane?" Cewar Haneefa dake zaune itama kan dadduman


"He knows, tunda Ni naje na shafa masa labari har ɗakin sa yau za su zo".


Ɗahira ta murmusa tana faɗin, "Let's go. Please, I'm too tired to see him, because I'm missing him."


Salma tace, "oh wa yaga Ɗahira matar tsofaffi, Ni na kula ma tsofaffin nan duk sun fi son ki, Anya ba da ɗaya za ayi ba between Kaka and Granny?"


Dariya suka kwashe dashi sauran cike da shaƙiyanci.


Fadila da Shakira ma duk tashi suka yi suka bi bayan su Ɗahira don su gaida Granny ɗin, a Parlour suka tarar da Yusra dake zaune ita da Hajiya Laila, nan suka yi mata bayanin "za su je gaishe da Granny ne daga nan su je sauran ɓangaren su gaishe su," har da Yusran suka tarkata suka tafi.


Part ɗin Granny suka soma zuwa, lokacin Inna Haja na sallah a ɗakin ta


Koda suka leƙa suka ga tana sallah ne sai suka nufi ɗakin Granny, yana zaune kuwa yana duba ƙur'ani, shima idar da sallan sa kenan, dayake ba ya iya fita sabida ciwon ƙafa da yake fama dashi, duk da ba'a Wheel chair yake zaune ba, kuma yana iya tafiya amma ba me nisa ba


General Isah Basheer Isah (Walid) kenan, tsoho me ran ƙarfe, kai da gani kasan an zuba ƙaƙƙarfan jarumi sanda yake matashi, har yanzu kuma idan ka kalle sa zaka ga zubin jarumtar sa, don daga gani kasan da sauran ƙarfin sa sosai, sai dai kawai tsufa ne da yayi, ga furfura da duk ya cika masa kai, kasancewar sa ba me barin gemu ba shiyasa babu komi a wajen sai ƙananun gashi farare kaɗan-kaɗan.


Shigowar su yasaka ya ajiye ƙur'anin yana ɗago kansa tare da cire medical Glass ɗin sa, fuskar sa yalwace da murmushi yake amsa gaisuwar da suke masa tare da bin su ɗaya bayan ɗaya yana kallo


Cikin tsokana Firdausi tace, "wai kuwa ka gane su Granny? Ko sai na maka bayani tunda naga idanun naka sun tsufa da yawa?"


Dariya yayi kafin yace, "ke kam baki da kirki Nana Firdausi, yo idan har bazan gane su ba kema ai bazan iya gane ki ba".


Gaba ɗaya fashe wa da dariya suka yi, ban da Firdausi da ta kwaɓe fuska tana ma Granny shagwaɓa.


Nan ya soma tsokanar su Ɗahira bayan ya tambaye su mutanen gida, suka zauna suka biye masa suna ta kwasan dariya


Itama Inna Haja da ta idar da sallan, ɗakin ta shigo ta zauna ana yi da ita.


Sai da suka daɗe a nan shashin kafin suka wuce sauran sasukan, suka gaishe da su, a Part ɗin Baba ƙarami suka shantake sukai ta kwasan hiran su.


Washe gari da safe sai ga Hajiya Ikram ta bugo sammako, ita da ƙannin Shamsiyya, sai Babban ƴar ta wacce take aure a Katsinan Aunty Mimi da nata yaran sun taho tare


Zuwa wajen sha ɗaya su Aunty Zulaiha da Aunty Zainab su ma suka zo, gida sai sake cika yake yi kowa ya hallara.


Da yamma sai ga su Aunty Amarya, Hajiya da Umma sun taho, ban da Hajja Fatu, ita zata biyo su Big Dady ne washe gari ranan auren, idan kuma za su koma su Big Dadyn sai su Hajiya su bi su, ita kuma Hajja Fatu za su dawo ranan Lahadi tare da su Ɗahira.


Tunda safe su Ɗahiran ma suka tafi yawon su, babu inda ba su zagaya ba, ba su nan ba su can, ko zama ba sa yi, sai da dare ne ma da suka dawo daga yawon na su suka ga su Hajiya sun zo.


The following day aka ɗaura auren Amarya Salma, sannan aka wuce gidajen Sauran amaren yayyin su aka ɗaura na su


Biki yayi biki, mutane tamkar tsaki, haka suke ta ɓulɓulo wa, su Yusra ma ko ganin ƙeyan su ba ka yi, ana can ana ta shan biki.


Da dare tare da su aka kai amarya gidan ta, sai dai a cikin su babu wacce ta kwana sai Yusra tunda za'a kwanar ma Amarya, tare da sauran dangi da aka bar mata.



Zuwa washe gari da yamma suka yi haraman tafiya, ƙarfe 06:30pm. Suka shigo Kaduna.







*WASHE GARI*


Monday tushen aiki, tunda Ɗahira ta shiga Office ɗin ta yau bata huta ba, sosai take da Patients waɗanda zata duba, shiyasa tunda ta shiga ta duƙufe take faman aiki, gaba ɗaya ta gama gajiya ga shi taƙi huta wa kanta.



Ƙarfe 05:30pm ta tashi, ta fito daga Office ɗin ta tarufe da keey tayi hanyan Lifter, dayake ta gaji sosai shiyasa tafiyan nata ma sai ya sauya salo, dama gata akwai yanga bare kuma yau me lasisi ne, buɗe Liftern tayi ta shige, tana shirin rufe wa sai ga Usman cikin saurin shima ya shigo, be ma kula da ita ba sai da ya shigo ɗin idanun su suka faɗa na juna, da sauri ko wannen su ya janye nashi suna haɗe rai alokaci ɗaya


Ƙofan fita Ɗahira tayi zata fice, don baza ta iya haɗa hanya dashi ba, sai dai kafin takai ga ficewar sai ji tayi ya jawo ta kiiiiiii.. ta dawo baya, ya jefar da ita wanda tuni ta je ta haɗe da jikin Liftern, saboda azaba ta ƙwalla ƙara tana dafe ƙeyan ta da sauri


Ko a jikin sa sai ma danna number da yayi ya rufe ƙofan, sannan ya tsayar da Liftern cak, yana juyowa gare ta fuska a haɗe..



[5/30, 8:44 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓

𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️

𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.



*EPISODE Twenty One*


Wani kallon tsana yake aika mata dashi, sai dai ya kasa magana duk da kuwa so yake yi ya faɗi wani abun


Ɗahira a hankali ta ɗago kanta her eyes filled with tears, and she looked at him, yanda ya haɗe rai yasaka ta kasa faɗa masa magana, illa haɗiye yawu da tayi tana aika masa da kallo me cike da tsana gami da haushin sa


Sake haɗe rai yayi, cikin izza irin ta shi yace, "har ke kin isa ki kai ƙara ta wajen iyayena ko? Kina jin kin girma kin zama macen da zaki iya ja da Usman Noor Al'ameen?"


Ɗauke kanta tayi a kansa tana sake dafe ƙeyan ta


Tsawa ya daka mata da faɗin, "Am I not talking? Uban wa ya baki ƙwarin gwiwan da zaki kai ƙara na wajen iyaye na?"


Sosai Ɗahira ta tsorata da yanda ya daka mata tsawa, nan da nan jikin ta ya soma rawa ta ƙanƙame jikin ta tana hawaye


Matsowa kusa da ita yayi yana saka hannu ya jawo kanta ta yanda za su haɗa idanu, sosai ya matse mata kan, wanda ya sa ta dinga zubar da hawaye tare da rufe idanun ta gam


"This is the first and last time you would do such a thing to me again, domin Ni ba abokin wasan ki bane, idan ba haka ba uhmmm".


Sai ya ci je leɓen sa na ƙasa yana sakin kanta, ya juya ya danna Numban Liftern yaci gaba da tafiya, yana kai su downstairs ya buɗe ya fice.



Ɗahira dake durƙushe a ƙasa tana ta shashsheƙan kuka, ko motsin kirki ta kasa yi sabida baƙin ciki da ƙuncin da ya cika ta, ji take yi tamkar ana tsaga magudanan jinin ta ana ƙara rura wutan tsanar da take yi masa


"Shin ta ya ma zata iya bari wani ƙaton banza ya zauna yana mata irin cin mutuncin nan? Kamar ta? Me ta tare masa ne?"


Ta jima a haka kafin ta share hawayen ta tare da gyarawa eyeglasess ɗin ta zaman sa, ta miƙe ta buɗe Liftern ta fice, a hankali ta taka har gaban motan ta tabuɗe ta shige, ja tayi tabar Hospital ɗin.


Tuƙin take yi amma hawaye na kwaranya a kyakkyawar face ɗin ta, maganganun Usman ne ke dawo mata kwanya, a haka har ta kai gida tayi parcking motan, sai dai ta kasa fitowa sai ma sake fashe wa da tayi da sabon kuka, sosai ranta ke suya da abinda yayi mata, ta rasa meyasa tarasa ƙwarin gwiwan da zata iya mayar masa da martani, alhanin tayi wa kanta alƙawarin baza ta sake barin sa yaci mata mutunci ba, ko kaɗan baza ta iya jure wa ba, shiyasa abinda yayi mata yanzu yayi mugun ɓata mata rai


Kifa kanta tayi saman sitiyarin motan tana rufe idanun ta ruf, tunanin abinda zata yi masa ta huce take yi, but ta kasa, don haka ta ɗago kanta ta share fuskarta tare da gyarawa ta fito daga motan, rufewa tayi ta wuce Part ɗin su.



A ranan sukuku ta wuni ta kasa taɓuka komi, duk idan ta saki jikin ta sai ta tuna abinda ya faru ɗazu, sai kuma gaba ɗaya ta rasa fara'an ta


Aunty Amarya da ta kula da yanayin ƴarta, tayi mata magana, but Ɗahira ce mata tayi, "babu komi". Dole ta ƙyale ta don ta san halin ta akwai zurfin ciki wani lokacin.




Washe gari tana tashi daga barci ta kunna wayan ta, ta soma cin karo da saƙon masoyin ta, yawanci duk complain yake mata a kan rashin reply ɗin ta, kasancewar tunda ta dawo daga aiki ta kashe wayan bata sake kunna wa ba


Murmushi kaɗai tayi ta ajiye wayan ta shige Toilet, sai da tayi wanka kafin ta dawo ta mayar masa da reply ɗin, sannan ta shirya cikin doguwar riga abaya fara me kwalliyan stone da ratsin ja, ta yane kanta da gyalen sannan ta fito


Ɗakin Aunty Amarya ta shiga, tayi mata sallama zata tafi, har ta kai bakin ƙofa ta kira ta tana tambayan ta "taci abinci?"


Dayake Ɗahira ba me yawan yin ƙarya bace don bata saba ba, sai tace mata "a'a but zata ci idan taje can".


Hararan ta Aunty Amarya tayi tace, "yi maza je kici abinci kar in saɓa miki"


Dole ba don ta so ba ta'amsa mata da "to". Sannan ta fice


Kan dainning ta wuce ta zauna ta soma haɗa tea, shi ne kaɗai abinda zata iya saka wa a bakin ta don ba daɗin jikin ta take ji ba, ga kanta dake ta faman sara mata sakamakon kukan da tasha jiya.




Fadila ne ta fito itama ta zauna akan dainning ɗin ta hau haɗa abun karin ta, sai da ta gama sannan ta kalli inda Ɗahira take a karo na biyu tun zuwan ta wajen, tun jiya ta kula da yanayin ta kamar tana cikin damuwa, sai dai kuma miskilanci ya hana ta tambayan ta, yanzun ma ganin Ɗahiran ta tafi tunani ta kasa shan tea ɗin ne ta kalle ta tace, "Sister, are you all right? What's wrong with you?"


Ɗago idanuwan ta tayi ta kalli Fadilan kafin ta kau da kai tana sauke numfashi a hankali, ɗaukan tea Cup ɗin tayi tana bata amsa da faɗin, "nothing, I am thinking something".



Fadila bata sake magana ba duk da kuwa bata gamsu ko kaɗan da amsar ta ba, sai ma ci gaba da tayi da yin breakfast ɗin ta.


Miƙe wa Ɗahira tayi tare da ɗaukan jakanta tayi hanyan fice wa, a Steps ta haɗu da Baffa zai yo Part ɗin su, sai ya tsaya yana kallon ta, yayinda itama ɗin ta tsira masa idanu, kafin kuma ta ɗauke nata ganin yanda yake mata kallon ƙurilla, ɗan dai-dai ta fuskarta tayi tana sakin murmushi tace, "Good morning my brother".


Be amsa ta ba illa jeho mata tambaya da yayi, "What is wrong with you, my dear? What happened to your swollen eyes?"



Har a time ɗin murmushin fuskarta be gushe ba tace, "Yaya babu komi.. it's just that I'm not feeling well"


"Shi ne kika yi kuka?" Ya sake jeho mata tambayar


Shiru tayi tana sauke kanta ƙasa


Sake matsowa kusa da ita yayi yana bin ta da kallo, sosai suka yi kusanci da juna, hakan yasa har suna jin hucin junan su


Da sauri ta ɗago kanta ta zuba masa manyan idanuwan ta, sai tayi saurin ja da baya gaban ta na matsanancin faɗuwa da ganin wasu abubuwa cikin idanun sa, wanda ta kasa fassara su illa saka ta a matsanancin faɗuwar gaba da suka yi, saurin runtse idon ta tayi saboda yanda ƙirjin ta ke sake bugawa sosai, ƙarar sahun takalman da taji yasa ta buɗe ido a lokaci ɗaya


Gaba ɗayan su daga ita har Baffa suka bi Usman da kallo, wanda yake dumfaro wajen su shima idon sa a kansu fuska a turɓune


Ɗahira ɗauke kai tayi daga kallon sa, tana mayar da idanun ta gefe


Lokacin har Usman ɗin ya iso wajen suna gaisa wa da Baffa, iyakan gaisuwa ya haɗa su ya wuce ya nufi hanyar Part ɗin Kaka


Idanu Baffa ya aza kan Ɗahira yace, "meyasa kike son min ƙarya ƙanwata? Kin san duk halin da kika shiga dole ne na gane? Sabida kin kasance mace me fara'a, wanda ba komi ne yake ɓata mata rai ba, kin kasance me juriya me ɓoye baƙin cikin ki ga maƙiya, why kike son nuna gazawan ki?"


Itama idanun ta da suka cika taf da hawaye ta mayar kansa


Ganin ƙwalla cikin idanun ta sai hankalin Baffa yayi mugun tashi, nan da nan ya rikice da tambayar ta yana saka hannu ya riƙo mata hannayen ta


Bata yi yunƙurin hana sa ba, illa lumshe idanu da tayi tana matse bakin ta, buɗe idon tayi cikin rawan baki tace, "How can you tell you what is wrong with me? What have I done? How can Yaya Usman hate me? Meyasa yake son muzguna ma rayuwa ta? Shin na taɓa yin masa laifi ne a rashin sani?" Taƙarishe maganar cike da ɗacin zuciya hawayen na silalo mata daga kuncin ta


Sake damƙe hannayen ta yayi cikin nasa, cike da sanyin murya yace, "Ƙanwata ki dena saka damuwa a kan abinda Usman yake miki, babu abinda kika yi masa, kawai Allah ne be haɗa jinin ku ba, amma insha Allahu wata-rana sai yayi alfahri dake a rayuwan sa, tabbas watarana komi zai wuce my dear, ki saka wannan a ranki zaki ce na faɗa miki, duk inda akwai jini dole ne akwai ƙauna, ke ɗin ƴar uwan sa ce, dole zai so ki kuma zai yi nadamar hakan, Plz ƙanwa ta wannan ya dena ɗaga miki hankali, I'm not happy to see you in this situation. wlh ina ji kamar zan mutu duk sanda na ganki a damuwa, ko kaɗan ba na jin daɗi".


Murmushi ta saki hawayen ta na sake silalo wa, cikin farin ciki tace, "haƙiƙa shiyasa nake sake alfahari da kai yaya, wlh billahi kai kaɗai ka ishe Ni a matsayin Yaya, ina son ka yayana ina matuƙar son ka fiye da yanda kake so na! insha Allahu kuma bazan sake damuwa da ko wani abu da ya nuna min ba, domin kai kaɗai ka ishe ni".


Murmushi sosai Baffa yake yi sakamakon jin zantukan ta, tsaban farin cikin jin kalman so a wajen ta, be san sanda ya janyo ta ya rungume ta ba; duk da kuwa ba yau ya soma jin hakan a wajen ta ba


Sosai Ɗahira ta zaro ido da ganin abinda be taɓa faruwa da ita ba, tayi saurin jan jikin ta tana matsawa da sauri


Sai shima a nan ne ya gane abinda ya aikata, yayi saurin saka hannu yana sosa kai cike da murmushi a face ɗin sa yace, "I'm so sorry Ƙanwata, wlh na manta ne".


Murmushi tayi kawai tana kallon sa, sai kuma ta gyaɗa masa kai


Hakan sai yasa yaji daɗi sosai, don be yi tunani hakan daga gare ta ba, a kullum faɗa masa take yi ba ta ƙaunar irin wannan rayuwan, duk da shi a wajen sa ya saba sosai ga friends ɗin sa da yayi school tare da su, irin wannan rayuwan wayewan shi ne Baffa ya taso dashi, babu ruwan sa don ya rungume mace, amma tun sanda Ɗahira ta soma taka masa birki shima ya rage yi, duk wani halayen sa mara su kyau da yasan za su ɓata mata rai, ya dena su, duk sabida farin cikin ta, shiyasa a kullum sake ji yake yi ƙaunar ta na ƙara wanzuwa a cikin ƙalbin sa, idan har ya same ta a matsayin matar sa kuwa; to, tabbas ya gama dace a rayuwan sa, ita ɗin haske ne cikin rayuwan sa, zai so ya kasance da ita har abada a duniyar sa..


"Yaya mu je kar muyi late". Tayi maganar tana kallon Wrest watch ɗin dake ɗaure a hannun ta


Murmushi yayi kafin yace, "tom dear".


A tare suka fita daga gidan.










⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫



Washe gari aka wayi gari Kaka be da lafiya, zazzafan zazzaɓi ya tashi dashi, sosai hankalin iyalan gidan ya tashi, nan da nan aka ɗunguma aka yi asibiti dashi


Su Ɗahira suna can labari ya riske su, ai nan ko wannen su ya kiɗime, domin ba ƙaramin ƙaunar Kaka suke yi ba, ko kaɗan ba sa son abinda zai taɓa sa, duk da kuwa ya tsufa amma suna matuƙar ƙaunar sa; ba sa son su rasa sa, ga shi be cika ciwo ba shiyasa hankalin su ya tashi da ganin yanda jikin sa yayi mugun zafi.


Gaba ɗaya iyalan gidan sun hallara a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da Kaka, kowa hankalin sa a matuƙar tashe, da yawan su sun kasa zama sai zagaye suke yi, irin su Ɗahira kuwa sun kasa jure wa sai sharan hawaye suke yi.



Su Abbu na ciki su ne masu duba shi, su kansu hankalin su ya gaza kwanciya, sabida halin da suka ga Kaka ya shiga, sun kasa shawo matsalar sai faman zufa suke yi.
[5/31, 12:56 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓

𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️

𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈

\𝗙.𝗪.𝗔📚/

𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.


*NASIHA*
_Sallah tana maganin duk cututtukan da suke samun zuciya. Ita ce haske mai kawar da duhu da zunubai. Abu Huraira ya ce, "Na ji Manzon Allah yana cewa:_
_"Ku duba nan; idan ɗaya daga cikin ku yana da rafi a bakin ƙofar sa kuma yana wanka cikin sa sau biyar kullum, shin wata ƙazanta tasa za ta yi saura?" Sai suka ce, "Ba wata ƙazantar sa da za tayi saura". Sai ya ce, "Wannan kamar salloli biyar ɗin nan ne waɗanda da su ne Allah yake wanke zunuban mu"._
_A sallah ne ake ganin tahƙiƙanin daidaituwa da adalci. Lokacin da Ladan ya yi kira da cewa: "ku yi gaggawa zuwa Sallah, ku yi gaggawa zuwa ga falala. Duk waɗanda sallar ta rataya a kansu, masu arziƙi da faƙirai, manya da yara, sarakuna da talakawa - dukan su za su taru a sahu guda ba wani bambanci tsakanin su, dukan su bayin Allah ne. Za su taru a bisa aƙida guda a ɗakin Allah, suna tuna Allah kaɗai, suna tawali'u gare shi._




*EPISODE Twenty Two*


Wajen awanni biyu da shigar da Kaka, kafin su Abbu su fito, sai dai basu ba ma kowa damar ganin sa ba, sabida a time ɗin sun yi masa alluran barci; yana cikin barci, domin ba sa son ayi hayaniya da zai ja har ya farka daga wannan barcin.



Gaba ɗaya iyalan gidan sun kasa kataɓus a ranan, ko jirgawa sun kasa yi a baƙin ƙofar, sai da su Big Dady suka yi musu magana ne, akan "su tafi gida," sannan ne su Hajiya suka koma gida, yayinda su Ɗahira kuma suka koma bakin aikin su, but

Please Login or Register in order to submit comment