Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tun bayan datai sallar Asubahi take jin ciwon Marar ta na taso mata kaɗan kaɗan adaddafe tai sallah ta koma gado ta kwanta tana faman Juyi
"Wai yau ba zaki fita aiki bane Farha? jiya dai baki da lafiya amman yau ya kamata ki fita kada suce kina wasa da aikin ki"
Cewar umma da take tsaye a kanta.
Ɗago idanunta tai wanda yayi jajir sabida azaba Murya can ƙasa tace.
"Umma nai wa ogan waya na gaya mashi bani da lafiya bazan iya fita ba"
Umma tabi ta da kallo tana nazarinta.
"Yaya naji muryarki a haka Ko jikinne?"
Cikin tsananin azabar zafin marar tace mata.
"Umma marata ciwo ji nake numfashina yana fita da ƙyar"
Ta faɗa cikin azaba Umma ta ɗauki wayarta ta soma haska saman sif ɗinta Maganin farha ta lalubo wanda saura ɗaya ya ƙare ta miƙa mata fita tayi waje ta ɗebo mata ruwa lokacin data dawo har ta miƙe zaune.
"Ungo kisha kafin Ikram ta tashi sai ta amso maki wani"
Ta amshi ruwan ta watsa maganin cikin bakinta Tashan ye tana mayar da Numfashin wahala Jim kaɗan ta miƙe tai tsakar gida aguje tana kwarara amai wanda shine ya Tada jama'ar gidan su.
Babarsu Ruƙayya ce ta tsaya akanta tana mata sannu Babarsu Hadiza kuma ta wanke mata Aman Ƙannenta sai sannu suke mata tana amsawa da ƙyara Duk abin Matan gidan da ƴaƴan gidan in abun jaje ya samu suna ƙoƙarin karantawa Amman in tashin hankalin su ne ya motsa ba sauƙi.

A wajan ta kwanta har rigarta na yayewa Ƴan cilli cillin cinyoyinta Suka bayyana a waje Kawu ne ya fito yana kallon ta.
"Wannan kuma lafiya ko jikinne?"
Umma data ke ɗagota Zuwa jikinta tace.
"Ciwon marar tane ya tashi shine tasha magani take amai"
Kawu ya koma cikin ɗakin sa.
Can jimawa ya fito da ɗari Biyu.
"Ga wannan ku tafi asibiti a dubata Allah ya sawaƙe"
Umma tabi Naira Ɗari biyun da kallo tana cuɗa yadda zata musu Kuɗin mota har da ganin likita ba abin kai magana ba yayo maka caa.
"Allah saka da alkairi"
Daga haka ta ɗaga Farha suka nufi ɗaki da taimakon umma ta shirya Suka fito domin zuwa asibiti.
Da ƙyar aka kaisu bakin asibiti a naira ɗari Layi suka tarar sosai a asibitin Farha na zaune tana jin yadda wasu mata suke magana ɗayar ce tace.
"Ai tuni an ƙona gidan radion tun ranar, Naji ance ma an kama mai gidan radion ita kanta yarinyar datai labaran an kamata, Wai gwamna da kansa yace zai ɗauki mataki akansu shi kuma Hasken matasan yace a,a abar shi da kanshi zai ɗauki mataki"
Farha tai tsuru tana jin wannan ƙarya wai an kama wadda tai labarin bayan gata a zaune.
Tana jin yadda matar take ta zabga wa mutanan wajan ƙarya akanta alhalin gata a zaune kuma tana wa Allah godiya abisa rufin asirin dayay mata daya sa babu wanda ya kama sunanta har yanzu.
Haka layi yazo kansu suka shiga ganin likita wanda ya rubuta musu magani Daga asibitin Zage suka shiga Gidan yayar umma anan suka ci abincin rana da ƙyar ma umma ta yadda ta zauna sabida tasan halin kawu da faɗan tsiya.
Ita kam farha bacci ta samu bayan taci abinci wanda Umman zage tace wa umma tabar farha zuwa yamma sai ta tawo gida Haka umma tai wa Umman zage sallama ta tafi gida.

Koda Umma taje Gidan kawu faɗa ya kamayi akan me zata baro masa ƴa a wani waje ta kamo hanya ta tawo umma tasan za'a rina sabida yadda tasan shi mutum ne mai taka tsantsan akan ƴaƴanshi.
Shuru tayi masa ta shige ɗaki sai ya bita yana cewa ta mayar dashi mahaukaci Umma dai bata yi magana ba tazo ta tarar da gidan A bushe ba ai abinci ba inda bata biya zage ɗin ba da haka zasu dawo da yunwa damma ta tarar da Ikram ta tafi gidan fa'iza.
Zuwa yamma Halifa ya kawo garin tuwo kwano Biyu yace a tuƙa sabida yau Mai gidansu yasa an musu kyautar Dubu goma goma Shi kuma nura ya bada dubu biyu yace ayi cefane.
Amman Fafur Babarsu Ruƙayya tai ɗakinta da garin, tace babu wanda zata tuƙawa tuwo da garin Ganin haka yasa itama Babarsu Hadiza ta bada Dubu biyun da Nura ya bata tace  Zuhuriyya ta siyo musu taliya da mai da Kayan miya haka kowacce ta saka tukunyarta tare da ƴaƴanta dama umma tasan za'a rina shiyasa bata fito tsakar gidan ba har wajan Marigaba tana ɗaki Sai da aka kira sallah Ikram ta dawo daga gidan Fa'iza Lokacin data shigo ɗakin Hannunta riƙe da fulas wanda Fa'iza ta ciko shi da awara da naira ɗari biyar tace a kawo wa ummansu.
Kawu ne ya ƙara zuwa bakin Ƙofar Umma.
"Hasiya wai har yanzu fatima bata dawo ba kinga bana son irin haka kada ki ƙara bar min Ƴaƴana a wani wuri"
Umma data zuciyo dama da taƙaicin matan gidan a ranta duk da tasan cewar kawu bai san abin da sukai ba.
"wai kai dan Allah in farha ta zauna acan gutsirar namanta za'ai? ina ba wajan yayata taje ba in ta zauna anan wani abun zaka mata nan maganine aka rubuto mata kazo ka tambayi kuɗin sai aikin tambayar ta dawo"
Bala'i ne ya kaure a tsakanin Umma da kawu abin da bai taɓa faruwa ba haka ya fita ƙofar gida ya tsaya yana sauraran ta inda farha zata fito har ya gaji ya nufi Bakin titi wajan zaman shi sai dai a ranshi ya ƙudiri aniyar sai ya mata arnan duka idan ta dawo gida.

Farha sai Bayan magariba tai shirin dawowa gida bayan sunyi sallama Da umman zage wadda ta bata kuɗin Mota katin ta na wajan Likita daya rubuta mata magani ta ɗauko ta fito daga gidan cikin ikon Allah tana fitowa ta sami abin hawa.

Yau Aliyu bai wunin Office ba yaje wajan visa ɗin sa ta fita chaina wadda yay cuku cukunta yana dawo wa gida kuma ya wuce cikin gidansu mahaifin sa rabon kuɗi yayi Musu kamar yadda ya sanya musa ya rabawa kaf ma'aikatan sa dake kamfanin shi Kuɗi Ya jima wajan ƙannen mahaifinshi Kafin ya fito Yaja face mask ɗin shi ya rufe fuskar shi sabida mutane Ya laluba aljihun shi da ƴan canji Napep ya tare yace masa ɗandago A bakin layin su Farha ya sauka ya shiga cikin layin lokacin gari ya fara duhu.
A ƙofar gidan ya tsaya ba yaron da ya fito daga gidan sai dai Yana jiyo kukan yara da hayaniyar matan gidan ya jima a wajan duk sauro ya gama cije masa jikin shi.
Yarinyar jiya ce ta fito da kuɗi a hannunta daga gani shago zata je yay saurin matsowa kusa da ita.
"Ke ina masifaffiyar yayarki ta jiya?"
Ikram da bata gane ko waye bane sabida abin kare fuskar dayay amfani dashi ta soma ƙifta ido cikin tsoro tace.
"Farha bata nan tana zage"
Ta faɗa cikin sauri tare da tsoro.
Ya nanata sunan
"Farha"
Lallai kam.
"Sunan ta kenan Shi ake gaya mata?"
Da sauri Ikram tace.
"Eh ko kace fatima ba"
Jin Muryar Halifa dake fitowa yasa Ikram ta Nufi hanyar shagon aguje Halifa yabi Aliyu da kallo wanda bai gane ko waye bane Aliyu ma baiwa halifa magana ba ya cigaba da tsaiwar shi a wajan Har Ikram ta dawo daga aiken ta ta shige cikin gida.

Adaidai nan kuma farha ta shigo layin sanye take da hijabi har ƙasa ja Wanda ya rufe mata har tafin ƙafafunta Daga hannunta ma yatsun hannunta kaɗai ake gani.

Tana ƙoƙarin Hawa dakalin gidan wanda bata lura da Aliyu dake tsaye ba Taji yo muryar kawu wanda garin saurin ta shiga gida har faɗuwa tai ta miƙe tana kaɗe hijabin sai dai kafin ta shiga har kawu ya ƙaraso wajan Aliyu yay saurin matsawa daga jikin gidan ya zuba wa Tsohon ido wanda yaji muryarshi yana cewa.
"Fatima sai yanzu kika dawo to ki jira zuwana daga ke har uwar taki data ɗaure miki gindi ni kinsan ba'a yawo a gidana ba zan lamunci wannan ɗabi'a ba Shiyasa na matsu wannan yaro ya turo ni koba lefe aurar dake zanyi"
Takaicin tijarar kawu ya kama farha shi haka yake in yaso cin mutuncin sa a ko ina yi maka yake yanzu meye abin wannan maganar a ƙofar gida damma ba kowa a layin.
Kawu ya juya ya koma titi Ita kuma ta nufi Gida zata shiga.

Da sauri Aliyu ya sha gabanta.
"Kinga shima ya matsu ki aure to mai kike jira ga miji a hannun ki kin samu"
Taji muryar BAWAN ALLAH a cikin dodon kunnenta cikin taushin murya yayi mata maganar.
Yana zare face mask ɗin daya rufe fuskar shi da ita.

Da sauri ta ɗago kai tana kallon shi.........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*15*

Lumshe idanunta tayi ta saki wata irin ɓoyayyar ajiyar zuciya, Yayi mata masifaffan kyau Ƙura masa idanu tayi babu ko ƙiftawa sanye yake da wani irin lallausan yadi Coffee colour wanda ya haska farar fatar jikin sa sai yanzu ta kuma ƙare masa kallo dogo ne sosai dan yadda ya mata tsaye akan ta har rumfa tsayin shi yayi mata Yana da manyan lumsassun idanuwa masu kama dana wanda yake jin bacci Yana da cikakken gemu wanda ya haɗe da ƙasumba ya cika fuskar tashi Sai Ƙaton tabon Abin sallah wanda yay baƙi sosai a saman Goshin sa.
Numfashin ta ne ya kusan ɗaukewa lokacin da taji ya hura mata iskar cikin bakin shi mai ƙamshin Mint.
"Kallon fa?"
Ya faɗa da tattausar Muryarshi.
Tsintar kanta tayi da jin matsananciyar kunyar shi.
A hankali ya furta.
"Do you feel what I feel when you are with me?"
Ya kuma matsowa gabanta ya maimaita mata abin da yace da yaran hausa.
"Kema kina jin abin da nake ji atare dani?"
Matse katin asibitin dake hannunta tayi gam aranta tana cewa.
Wannan Bawan Allah zai halaka ni.
Jikinta ko ina rawa yake muryarta na rawa sosai tace.
"To ka matsa baya sai muyi magana"
Aliyu ya zira hannunshi saman nata hannun ba zato taji ya fisge katin asibitin data riƙe a hannun nata.
Zubawa katin idanu yayi yana gama karantawa ya saki murmushi.
Bai miƙa mata katin ba ya zira shi acikin aljihun shi.
Hannun nashi tabi da kallo wanda yake shinfiɗe da wata irin baƙar suma tai luf kamar ka taɓa jini ya fito.
"How do you feel about your body?"
Ya faɗa yana ƙoƙarin saka ƙwayar idanun shi cikin tata wadda ita kuma taƙi yarda ta haɗa idanun dashi sabida duk kunyar abin da ya gani ajikin katin tagama kamata.
"Shike nan tunda baza'a min magana ba oya shiga gida"
Kamar jira take da sauri ta kama ƙofar gidan nasu zata shiga ciki.
Hannu ya zira cikin Aljihunshi tare da fesar da iska mai zafi.
Tsadaddiyar wayarshi wadda bai cika amfani da ita wajan hulɗa da jama'arshi ba ya fito da ita ya damƙa ta a hannun Farha wadda harta kai da shiga soron gidan nasu.
A hankali ya rage tsayin shi ya Sunkuya daidai kunnenta ya raɗa mata.
"Saura ki ƙi ɗaga wayata, zan kira ki anjima"
Daga haka ya juya ya fice daga soron gidan yabar mata ƙamshin turaren shi.
Gaba ɗaya Jikin farha rawa yake sai faman kaiwa da komowa numfashinta yake Ta kasa jan ƙafafunta zuwa cikin Gida gefe guda ga tsoron wannan waya daya bata Ya cika mata zuciyarta.
Da ƙyar ta aro jarumtar jan ƙafafunta da suka mata nauyi ta shiga cikin Gidan Duk matan gidan da ƴaƴan suna cikin ɗakunan su yanayin sallamar datai ne a hankali yasa ba wanda yaji sallamar tata.
Ta ɗaga labulan ɗakin umma ta shiga ɗakin da sallama, Umma ta zuba mata ido cike da tausayinta zaton umma duk jikin nata ne yasa ta koma haka.
"Sannu farha ina nan ina tunanin ki Yaya ƙarfin Jikin naki?"
Ta damƙe wayar tana Cewa.
"Alhamdulillahi Umma"
Daga haka ta nufi uwar ɗakan su ta aje wayar a saman sif gudun kada Umma ta gani, Ta zare hijabin Jikinta Ta fita tsakar gida banɗaki ta shiga ta gyara jikinta sabida priod ɗinta daya zo mata a yanzu.
Tana shigowa ɗaki taji Muryar yaro yana cewa.
"Wai ina fatima?"
Umma ce ta ɗaga murya tace.
"Shigo mana menene"
A lokacin Farha ta zauna a gefen tabarmar ɗakin yaron ya shigo da ƙatuwar leda a hannun shi fara mai ƙyalli.
"Wai wanine yace in kawowa Fatima amman ya tafi"
Umma tace.
"Wani yaya kamannin sa yake?"
Sabida duk ta ɗauka ko Salim ne.
"Dogo ne sosai fari amman banga fuskar shi ba"
Umma tai jimm dan Salim baƙi ne kakkaura.
"Ka mayar masa da ledar kace ba'a nan gidan take ba"
Yaron yace.
"Ai ya riga ya tafi tunda ya bani"
Daga haka yaron ya aje ledar yayi tafiyarshi.
Ikram ta buɗe baki cike da Ɗaga murya tace.
"Wallahi umma da gaskiyar yaron nan nima tunda kika aiken siyo suga ɗazu na ga Mutumin a ƙofar gida wai yace ina Masifaffiyar yayata, Kuma Umma mutumin kamar balarabe Duk da fuskarshi a rufe take"
Umma tai shuru ta zubawa Farha idanu wadda tai ƙasa da kanta Jikinta na rawa.
"Farha wanene kuma wannan Mutumin kada ki Ɓoye min gaskiya?"
Farha tace

"Wallahi Umma ban sanshi ba nima, Yace min wai a hanyar wajan aiki yake ganina in zan tafi, Amman umma ni ban sanshi ba Allah da gaske nake miki"
Umma ta janyo ledar ta buɗe.
Magungunan da aka rubutowa farha ne masu tsada amman ba a sako katin ciki ba, Sai Kaji manya gasassu Guda Uku da Lemuka masu sanyi.
"Baki san shiba ta yaya kika bashi katin maganin ki? Farha ba zaki jamin Cin mutuncin mahaifin kiba wallahi sai na tattare kayana na bar muku gidan in banda ke da Ikram da tuni na mance da barin wannan gida Salim bai cancanci haka daga gareki ba kada ki bari ruɗin Shaiɗan ya shiga zuciyar ki, Maza ki tattare masa kayanshi Kisan yadda zaki ki mayar masa dasu ni babu ruwana kuma ki kuka da kanki idan mahaifinki yaji"
Farha tahau kuka tana bawa Umma haƙuri.
"Allah umma ki yarda dani shine ya ƙwace Katin a hannuna ɗazu"
Umma miƙewa tayi tabar mata ɗakin.
Farha tasha kukanta Daga ƙarshe ko kallon ledar bata yi ba ta miƙe ta shige ɗaki ta kwanta.
Umma banɗaki ta shiga bayan ta fito Ikram tai musu shinfiɗa a rumfa suka kwanta dama su a rumfa suke kwanciya Farha ce ke kwanan Cikin uwar ɗaka dan komi zafi bata fitowa.
Umma ta jima batai bacci ba tsoron ta Ɗaya shine kada Allah yasa wannan Mutumi ya yaudari Farha ya rabasu da Salim dan so wani bin shu'umi ne Musamman ga zuciyar mace mai rauni.
Cikin baccinta taji Nishin wayar daya bata wadda ita Fushin umma ma yasa ta mance da ita.
Da sauri ta miƙe ta ɗauko wayar ta katse kiran.
Can wani sabon kiran ya kuma shigowa Numbern ba suna sai dai special number ce ta ƙurawa Numbern idanu kafin a hankali ta ɗaga kiran.
Wata irin Ajiyar zuciya Aliyu ya saki ta cikin wayar.
"So kike yau na kasa bacci my princess ina ta kiranki baki ɗaukar Min kirana ba Why?"
Ƙara damƙe wayar tayi tana Zare idanu tsoronta ɗaya kada Umma ta jiyo ta.
"Dan Allah ka rufamin asiri bawan Allah kazo ka amshi Abin da ka aiko kasa ummata tana fushi dani"
Ta faɗi Murya can ƙasa Kamar mai yin raɗa.
Aliyu ya Narkar da Murya kamar zai mata kuka ya soma Gaya mata mayaudaran kalamai wanda shi kanshi bai san ya iya suba Luf Farha tai tana ƙara nutso a saman gado Wayar kare a kunnenta wani irin Baƙon lamari ke bibiyar dukkan sassan jikinta.
Aliyu sai da ya tabbatar ya mata illah a zuciyarta sabida yadda yaji tana sakin Numfashi da alama kokawa take da zuciyarta Manna wa wayar Kiss yayi ya kashe kiran.
Tashin Hankali Farha a zaune ta raba dare ta kasa bacci duk motsi hoton Aliyu da yadda yake mata magiya ne yake mata yawo acikin idanunta zuwa asubah wata irin Mahaukaciyar soyayyar Aliyu tai mata mugun kamu Ko Motsi tayi shi take gani bata kallon ko wani namiji a zuciyarta sai shi taji ta aminta da Salim kawai kula shi take, amman soyayya yanzu ta fara yi da bawan Allah kamar yadda ta raɗa masa dan bata san sunan shiba.

Aliyu kwanciyar shi yayi ranshi fes batare daya ji dukkan wasu kalamai daya yiwa yarinyar yayi tasiri a zuciyar shiba.
Washegari haka ya shiga harkokin sa batare daya tuna da Farha ba Ranar Alhamis wadda ta kama rabon shi da farha kwana uku jirginsu ya ɗaga ƙasar chaina.
Harga Allah ya mance da ita tunda ya je chaina zirga zirga yake akan yadda sabbin motocin daya siya su zo Kamfanin shi wannan tasa baya samun Lokacin kanshi bacci ma baya isarshi sosai tsayin sati ɗaya ya ɗauka a chaina daga nan kuma ya wuce saudiyya.

Tuni soyayya da tunanin Aliyu sun huda dukkan sassan jiki da zuciyar Farha dama tun washegari da bai zoba Umma Ala dole tai amfani da Kajin ta bawa farha magungunan sai dai sam ta daina sakarwa farha fuska maganar aiki ma umma da kanta tace ita gaskiya farha ta haƙura da fita Tunda dalilin fita aikin wani ya fara biyota ita bata son Su shiga haƙƙin salim wannan hukunci yayi wa farha daɗi sabida haka bata ɗagawa kanta hankali ba suma mutan gidan duk sun ɗauka rashin lafiyar farha ne yasa Bata koma aikin nata ba.
Ba abin da Farha take sai aikin kwanciya Sai kuma zubawa wayar data ɓoye ido kullum Tunanin ganin Kiran Bawan Allah take tun tana sanya rai har ya cika sati ba shi babu wayar shi dole tai shahadar kiran layin nashi sai dai baya tafiya haka zata haɗa kai da gwiwa tana kuka ita kaɗai a ɗaki tana Allah wadai da zuciyarta data kamu da son wanda ko sunan shi bata sani ba ƙila ma Ƙarya yake mata yaudarar ta kawai yazo yayi.
"Ni farha meke damun kine? wannan jarababban bacci da ƙunci ke kaɗai ya isheni idan ma dan na hanaki fita aiki ne to kisha Kurumin ki ɗazu Mahaifin Salim ya turo Ƙanin sa nan da jibi zasu kawo kuɗin auren ki"
Farha bata ɗaga kai ta dubi Umma ba Hawaye ne ke gudu acikin Idanunta Ta kife a saman gado ranar wuni tayi kuka da magariba Salim yazo haka ta fita a zuciye duk haushin salim ya cika mata zuciyarta.
Duk maganar da salim ya gaya mata baƙar magana ce take Biyo baya Cike da mamaki salim ya dube ta dan hakan bai taɓa faruwa a tsakanin suba.
"Farha lafiya kuwa kodai wani ya ɓata miki rai ne?"
Ta ɗago a fusace.
"Kaga salim dan Allah ka rabu dani, Kaga in ka takura sai ka aure ni wallahi zan kashe kaina kowa ya huta"
Daga haka ta shige Gida da Ihu wanda yaja hankali mutan gidan tambayar duniya an mata taƙi cewa komai addu'a Umma ta dinga tofa mata zaton umma ko gamo farha tayi

Abin mamaki kwana tayi tana kuka ta wuni Kawu duk zafin sa sai da ya sauko yana tambayar ta Meke damunta.
"Kawu kada ka aura min salim bana son shi wallahi idan aka aura Minshi zan kashe kaina"
Salati Umma dasu Babarsu Ruƙayya suka ɗauka.
Kawu ya miƙe.
"Zan tanaji likkafani da makara wanda ina ɗaura Miki auren zan haɗaki da kaina na kaiki kabari amman ki sani ko gawarki ce sai taje gidan salim Butulu Dama nasan za'ai haka tunda uwarki ta ɗaure miki gindin aiki To duk baku isaba ni ba ƙaramin Mutum bane"
Kawu yabar ɗakin
Umma a zuciye ta rufe Farha da duka tana cewa.
"Ni zaki wulaƙanta to bara na kashe ki da kaina kafin Ki kashe kan naki"
Da ƙyar aka ƙwaci farha a hannun Umma Babarsu Hadiza ta kaita ɗakinta Ranar kowa ya wuni ba daɗi agidan.
Salim durƙushe a gaban Babansu wanda ya kirashi akan Batun kai kuɗin auren shi gidan su Farha.
"Baba ina ganin abar batun kai kuɗin nan"
Baban salim yace.
"Dalilin ka kana son naji kunyar aminina?"
Salim yay ƙasa da kanshi.
"Baba muna jin case a radio da kasuwa na illar auren dole Jiya naje wajan Farha da kanta taci alwashin na aure ta zata kashe kanta"
Subuhanallahi.
Baban Salim ya faɗa yana tafa hannun shi.
"Jeka zan nemeka"
Babar salim dake bakin Ƙofa tahau bala'i
"Tsinannu dama nasan za'ai haka sun gama ta tsar shi shine zasu zugata to Allah ya isa"
Baban Salim ya dube ta.
"Amman baki da hankali In da kin san waye Abubakar akan ƴaƴan sa da baki ce haka ba, Ɗane ka haife shi baka haifi halin sa ba mu dai addu'a zamu yi duk abin da yafi alkairi Allah ya zaɓa bama son ai abin da za'a zo ana kuka"
Baban Salim Mutum ne mai sauƙi wanda halin shi salim ya ɗauko ba irin mahaifiyar shi masifaffiyar mace ba.
A ranar Baban Salim ya sami kawu a Gida bayan sun gaisa yace masa.
"Malam Abubakar nazo ne da maganar yarannan ɗazu salim yace Min fatima tace in ya aure ta zata kashe kanta, To duk maganar haka bata taso ba ka zaunar da ita ta gaya maka wanda take so in yaso sai ayi dashi ƙila rabo ne ke kiranta in aka ja za'a iya rasa rai"
Kawu ya dubi Baban salim.
"Duk wanda aka rasa kwanan shine ya ƙare nifa ba zata mayar dani ƙaramin Mutum ba Munafurci ne nata dana uwarta Sabida haka bama kawo Kuɗi ba gobe gobannan ina son ka turo da sadakin salim na ɗaura musu aure da fatima"
Baban salim yace.
"Nagode nasan duk ƙauna ce ta saka kace haka ni nafi ka hange akan wannan matsalar, saboda haka ayi haƙuri a tuntuɓi yarinyar wa take so a bata shi ni dai nine mahaifin salim to in dai daga wajena Auren shi zai Ɗauru da fatima to na janye Allah ya haɗa kowa da rabon shi"
Duk yadda kawu ya kafe Baban salim yaƙi sabida Yaji tsoron furunci Farha haka sukai sallama da Kawu abin ba daɗi dan kawu ya zuciya haka yayo gidan ya faɗo ɗakin Umma A ranar anga tashin hankali agidan dan kawu cewa yayi umma sai ta bar masa gidan shi ita da Farha da ƙyar su Halifa dasu Babarsu Ruƙayya suka janye kawu Daran Umma kuka Farha kuka Ikram kuka umma taiwa farha dukan da har sai da tai mata tarkaɗe Amman zuciyar farha bata saduda ba zuwa asubah kawu ya tara kaf Matan shi.
Da Ƴaƴan ya dubi farha.
"Na baki daga yau zuwa gobe Kiwa wanda kike so magana yazo gobe da sadaki na ɗaura muku aure idan ya wuce gobe kuma zan bawa duk wanda naga dama sadakar ki Burunku ya cika keda mahaifiyarki"
Daga haka yabar wajan.
Umma bata ko kalli farha ba tayi ɗaki Farha ta rasa yadda zatai Haka ta shige ɗaki taita gwada numbern Shi yaƙi shiga.
Har Yamma abu ɗaya take taƙi fitowa waje sabida tana tsoron Hararar umma.
Kamar da wasa Ana kiran magari ba ta kira Numbern tana ringing amman ba'a ɗauka ba.
Aliyu daya sauka yau da rana tunda ya shiga part ɗin shi da yayi wanka bacci kawai yake bai tashi ba sai la'asar yayi sallah Ya Nufi Gidansu Mami abisa tirsasawar Ammi har Magariba suna tare da Mami yana kallon wayar shi na ringing da tsohon layin shi daya bawa wannan yarinyar wadda ya manta ta kiranta ne ma ya sanya shi tuna ita ɗin wacece yana kallo kiranta yana shigowa amman yaƙi ɗauka sai da yayi sallar magariba sannan ya baro gidan su mami wadda tace cikin satin nan zata dawo ɗakinta.
Yana driving yaga wani kiran nata ya ƙara shigowa wayar shi yayi parking a gefen titi ya ɗauki kiran.
Muryar Farha cikin kuka take cewa.
"Ina ka shiga bawan Allah ka barni cikin bala'i dan Allah ka dawo gare ni"
Kuka ne yaci ƙarfin maganar tata.
Kukan mace yana ɗaya daga cikin abin da yake san yashi Jin rauni fiye da zato.
"Ki haƙuri bari na zo"
Daga haka ya katse wayar ya tada Motar yayi unguwar su a bakin layin su yayi parking Yaja Face mask Ɗin shi ya rufe fuskarshi ya taka da ƙafar shi har bakin Ƙofar gidan ya fito da wayar ya kira ta.
"Gani nazo"
Daga haka ya kashe.
Sum sum Farha ta fito daga ɗakin su tayo ƙofar gida wajan shi da sauri............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar

Please Login or Register in order to submit comment