Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasara ce Kuma gwamnati zata ɗauki mataki akan shugaban Gidan radion dan zata binciko shi harma wadda tai labaran.

Bayan ya gama jin jawabin gwamna yayi godiya sai dai yace wa gwamna yabar Batun tuhumar mai gidan Radion shida kanshi zai Bibiyi Lamarin dan ya ɗauki matakin daya dace sosai sukai magana da gwamna kafin yayi masa sallama bayan yace ga Jami'an tsaro nan ya Turo masa dan su kare lafiyar shi data iyalin shi yayi Godiya ya katse wayar.

Yawan ƴan jaridar dake ƙofar Gidan ya kai ya kawo dan ƴan jarida kamar su fasa gidan su shiga su ɗauko rahoto haka suka taru ga jama'a kota ina wannan tasa aka rufo gidan ma gaba ɗaya ya zama ba shiga ba fita daga gidan Madaki ma sosai ƴan uwan su Aliyu suka girgiza nan da nan Baba Usman Ƙanin Mahaifin Aliyu ya saka malamai aka hau sauke alkur'ani mai girma.

Mami kuka take tana kiran layin Aliyu dan hankalinta gaba ɗaya yana kanshi Ko kaɗan bata yarda da wannan labari ba sabida tasan waye Mijinta har ya fita damuwa akan asarar Cikin da suke yi Suma gidansu Mami sai rufe Ƙofa sukai sabida Yadda jama'a ke dafifin shigowa jaje.

Yana rangaji ya miƙe da sauri Ammi ta taimaka masa ya haye saman shi ya faɗa saman gado yana Lumshe idanunshi Ammi ta rufo masa ƙofar Ta nufi sashin sa da ƙyar ta rarrashi su sajeeda waɗanda suke Kukan abin da aka wa yayan nasu.

Wayar shi dake Ringing a karo na ba adadi ya laluba ya ɗaga Muryar mami ke sauka cikin kunnen shi.
"Yaya dafatan kana lafiya? wallahi ni na yarda dakai Mijina sabida haka ka kwantar da hankalin ka wannan shiri ne na maƙiya"
Da.
"Umm"
Ya amsa mata ya kashe wayar yayi shuru yana sauraran Bugun zuciyar shi.

Ƴan jarida da sauran jama'a gajiya sukai suka bar ƙofar gidan har zuwa dare ba aji ɗuriyar shiba amman an tabbatar yana cikin Ƙoshin lafiya dama shi haka tsarin sa yake in yana cikin damuwa shuru yake In yana cikin ɓacin rai shuru yake ya killace kanshi wannan tasa Ammi bata sake komawa wajan shi ba tasan yana tunanin mafita ne na wannan matsala data afko masa.

***********

Gaban Farha ne ya faɗi sanda taji kawu na Allah wadai da Wannan tasha ta garkuwa wadda ta ɓata sunan Aliyu Matan gidansu kuwa masifa suke suna kumfar bakin cewa baƙin ciki ne yasa akai masa sharrin ba wani abu ba Ƙara jan abin rufa tai tana Sakin Hamdala da Allah yasa babu wanda yasan a tashar take aiki kuma ba sunanta a labarin sannan bata can aka ƙona gidan rediyon kamar yadda taji labarin a tsakar Gida cewa an ƙona gidan rediyon.
Damuwar ta ɗaya wannan sharrin data ja gaba wajan yaɗawa Ina zata sami wannan bawan Allah ta roƙe shi gafara tsananin tsoro da damuwa sune suka ƙara haddasa mata zazzafan zazzaɓi zuwa dare Jikin Farha ya ƙara rikice wa wanda hatta Ƴan gidansu sun tsorata dan kuka take tana cewa umma ta yafe mata mutuwa zatai Duk zafin kawu sai da ya ruɗe Salim ne ya kirawo Nurse aka saka mata ruwa aka mata Allura Wanda bacci yayi awon gaba da ita.

***********
Daran ranar Aliyu bai bacci ba yadda yaga dare haka yaga rana, Ba abin da yake sai sallah yana ƙara neman gafarar Allah akan dukkan laifukan sa tare da neman tsari da kariya daga dukkan sharri sai da yayi sallar asubah sannan ya sami bacci Ƙarfe goma ya farka ba laifi ya sami nutsuwa sosai harya fito Parlou yana amsa jajen ma'aikata yana kuma ɗaga wayar mutanen sa masu yi masa jaje.
Ƙarfe sha ɗayan safe Musa ya ƙaraso Parlon nashi bayan sun gaisa ya dubi Musa........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
          
           *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *12*

Muryar shi a kausashe wadda ta nuna zallar Ɓacin ran daya kwana dashi.
"Musa ina son lallai a yau ka gano min  inda mai gidan radio ɗinnan yake inda hali katafi da jami'an tsaro cikin fararen kaya, su Kama min shi tabbas sai ya gaya min meye nufin shi akaina zan nuna masa ni ɗin wanene in aka shiga gona ta"
Ya faɗa yana fesar da numafashi mai ƙarfi.
"Sannan ita ma yarinyar datai labaran lallai ina son sanin wacece"
Ya faɗa yana jingina kanshi a jikin kujerar da yake kan ta a zaune.

A hankali ya furta.
"i will not leave them"
Ya ɗago ya kalli side ɗin da musa yake ya furta.
"kuma a yau nake so ka ai watar da komai ba sai gobe ba"
Musa daya tsorata da yanayin mai gidan nashi jiki na rawa yace.
"I will do my best for that"
Daga haka ya ɗaga ma Musa hannu yana cewa.
"Thank you very much Musa"
Da hannu ya dinga cakuɗa sumar data ke kanshi Duk ranshi a ɓace yake mai yasa mutane suke haka tabbas inda sun san girman laifin da sukai masa da idan ance su ƙara ma wani irin sa baza suyi ba.
Ya cije baki.
ya tashi ya koma bedroom ɗinshi yau ko wajan Ammi bai leƙa ba yana jin wayar shi na ringing bai bi takanta ba.

Musa yana tafe yana tausayawa Mai gidan radion sanin waye Aliyu Sarƙa ne faɗi kirikice Sarƙa ne mai rikicin gangan Dangin zaƙi ne Layin zuma.

Direct police station ya nufa sannan ya buƙaci a bashi ƴan sanda Guda biyu Batare da sun saka uniform ɗinsu ba Haka suka nufi Gidan Radio Ɗin Abin yayi matiƙar bawa musa Tsoro na yadda yaga an ƙona gidan Radio ɗin Ƙurmus ba wani abu na mora aciki Wajan ba kowa sai Mai gadi wanda su Musa suka ƙarasa wajan sa yana zaune a saman Banchi su musa suka ƙarasa suka mai sallama.

Mai gadin Irin Iyamuran nan ne Bayan sun gaisa bai da hausa sosai ya dubi Musa yana tambayar shi.
"What do you need here"
Ɗaya daga cikin Police ɗin ya kalli mai gadin yace masa.
"We will ask you a few questions"
Mai gadin ya zuba musu ido sabida dama tun jiya a tsorace yake dandai kawai son kuɗin shi na albashi shine ya zaunar dashi Kowa yasan ƙabila akwai riƙo da aiki baya wasa dashi.
"I hear you,what is your quesion?"
Ya faɗa yana kallon ɗan sandan daya masa magana.
Musa yaɗan dube shi.
"Gidan mai wannan gidan radion muke son ka nuna mana?"
Mai gadi ya zaro idanu cikin hausar da bata ishe shi sosai ba sabida yana jin hausar sosai amman Mayar da amsar ne take basa wiya.
"i don't know his house"
Ya faɗa yana mayar da radion shi kunnen shi ganin zai Ɓata musu lokaci yasa Ɗaya daga cikin Jami'an tsaron ya buga Masa tsawa tare da Nuna masa Id card ɗinsa Jikin mai gadi ya soma rawa Zufa tana karyo masa Nan da nan ya miƙe yana cewa.
"Let me show you"
Suka bi bayan shi Sai da suka hau Adaidata sabida da ɗan tazara daga nesa da gidan ya dakata ya nuna musu da ya tsansa yana cewa.
"That house with a black gate"
Daga haka ya juya da sauri, Suma basu wani takura mai ba suka nufi Inda ya nuna musun Gidan a rufe yake sai da suka buga Da dutse Md ya Fito yana cewa.
"Waye?"
Musa ya maƙale Murya kamar ta mata yace.
"Nice Hafsa"
Md yayi tsuku daga ciki kafin ya zare sakata caraf Ƴan sandan suka damƙe shi batare da sun masa magana ba suka tura ƙeyar shi Titi suka sami adaidaita suka tafi dashi station Gaba ɗaya Md zare ido yake Jikinsa na rawa wata irin nadama ce ta rufeshi dama tunda ya shiga Gida hankalin shi ba a kwance yake ba Burinshi yaranshi su taso daga Islamiyya ya tarkatasu su gudu Matarshi ta fita Ɗauko yaran duk zaton shi itace ma dayake sunan nata kenan Hafsa wanda Musan yaci sa'ar Ambata shiyasa ya buɗe Iya azaba Md yaji a wajan jami'an tsaron Amman Amsar shi ɗaya ce wallahi ba wanda ya saka shi ƙirƙirar labarin shidai kawai yayi ya saki ne dan tashar sa ta sami Suna.

D.p.o ya dube shi.
"Wato irin kune ɓata gari masu tada zaune tsaye acikin al'umma kawai dan son zuciyar kanka da biyan Buƙatar kanka zaka Ƙirƙiri labarin ƙarya dan ka sami ɗaukaka a tashar ka"
Ya kalli ɗan sanda guda ɗaya yace.
"Officer ku shigar dashi Bayan kanta har sai ya bamu amsar abin da muka nema a wajanshi ta yaya za'a ce babu wani dalilin shi na fitar da labarin kuma an tabbatar shine mai tashar"
Md cikin magiya yake cewa ai masa afuwa.
Musa bai bar station ɗin ba sai bayan sallar magariba Kai tsaye Waya ya kira Aliyu ya tabbatar masa da cewa an kama Mai gidan Radion an ɗamƙawa hukuma.
"Ita yarinyar fa?"
Cewar Aliyu.
Shaf Musa yama manta da wannan Sabida haka komawa yayi cikin station ɗin ya nemi daya ga Md.
Bayan ya shiga Inda Md ɗin yake tambayar shi yayi ina ne inda Wadda tai labaran take matar aure ce ko budurwa.
"Wallahi Ranka ya daɗe nina tirsasata bata da laifi yarinya ce ƙarama"
Musa ya buga masa tsawa.
"Ba wannan na tambayeka ba kwatancan ta kaɗai na tambayeka?"
Md yace.
"Gaskiya ni bazan ce ga inda ta fito ba amman Yarona daya taɓa min aiki ɗan nan ƙofar nasarawa ne duk inda ka tambayi gidansu Gali anan layi na Biyu cikin ƙofar nasarawa za'a nuna maka gidansu Tare da ƙanwarshi ya kawo min su tun last week"
Musa yace.
"Na fahimta"
Ya miƙe ya fita daga Wajan kanshi tsaye adaidaita ya kuma hawa sabida yadda Aliyu ya bashi tsoro ne yasan ya ko mota bai ɗauka ba Ƙofar nasarawa ya sauka yaci wiya kafin ya sami gidan wanda Ya sami Gali zaune da matasa a ƙofar gida ana hira Hannu ya bashi suka gaisa sannan yace.
"Da Allah ina son ganin ƙanwarka"
Gali bai kawo komai aranshi ba ya shiga gida ya kira Shema'u duk zaton shi Ko Musa saurayin shema'u ne.

Shema'u cike da mamaki ta ɗauki Hijabinta tabi bayan Gali Jingine da bango taga musa ya ƙaraso suka gaisa tana masa kallon rashin sani.
"Na san zaki mamakin ganina, Sunana Musa ɗaya daga cikin yaran mai Kamfanin Madaki Motors Kuma amintaccen yaron shi"
Shema'u tai jimm dan sunan ya kwanta mata musa yace.
"Ehemm Ina nufin special adviser na gwamna a ɓangaran matasa"
Zabura shema'u tai da sauri sabida ta gano nufin sa yanzu.
"To meye ni nawa acikin case ɗinsu tunda bani nai labaran ba,itama farha duk Nacin danai kada tayi gashi nan son zuciya ya kaita tayi abin zai zama masifa"
Musa ya fito da wayar shi ya saita recording.
"Ko zaki iya gaya mana gaskiyar abin da ya faru?"
Shema'u cikin tsoro tace.
"MD ya nemi ɗaya daga cikinmu akan tai labari akan Shi SA na gwamna ɗin wai muce duk cikin da matarshi ke samu shine yake dalilin zubewarshi ta hanyar bawa matsafa cikin, Ni direct nace bazanyi ba sabida ina gujewa kaina matsala sannan ni ƴar ƙofar nasarawa ce nasan waye shi tunda ina jin labaran alkairan shi a wajan mutane Ƙawata Farha ita tace zatai ba yadda ban da itaba daga ƙarshe ma har faɗa mukai da ita"
Musa ya gyara tsaiwa tare da cewa.
"Ita ƴar ina ce Farha, Kuma budurwa ce ko matar aure?"
Shema'u tace.
"Tare mukai karatu da ita indai ka shiga Lungun Ɗandago kace Gidan Malam Abubakar mai Bulo ba wanda baze kaika gidansu ba, ko kace Gidan cida kai ko gidan yawa Budurwace amman an kusa bikinta a yadda take gaya min akwai wanda yake sonta tun tana ƙarama"
Musa ya mayar da wayarshi Aljihu yana mata godiya.
Shema'u da gudu tai cikin Gida kai tsaye sai banɗaki ta fara fesa gudawar tsoro.
Musa bai koma wajan Aliyu ba sai da ya Je Ɗandago ya sami wanda ya nuna masa har Ƙofar Gidansu Farha sannan ya nufi wajan mai gidan Nashi.
Sai da Musa yasha zaman Jiran Aliyu sabida ƴan uwan mahaifin su da suka cika ɓangaran nashi domin suyi masa jaje Har sai da Aliyu ya sallamesu sannan Musa ya sami damar shiga parlon nashi.
"Musa yaya?"
Ya faɗa yana ɗage girarshi.
"Yallaɓai Mun sami nasarar cafke mai gidan radion duk da yana ƙoƙarin guduwa ne yabar garin, yanzu haka yana wajan ƴan sanda"
Aliyu ya cije baki yace.
"Da kyau musa"
Musa ya ɗauko wayarshi ya kunna yadda sukai da shema'u Aliyu ya Mai da Nutsuwarshi yana sauraran mai shema'u take faɗa.
Murmushi yayi na mugunta bayan ya gama sauraran abin da shema'un take faɗi.
"Yallaɓai gaskiya yarinyar ƴar talakawa ce Irin waɗannan shari'a dasu ma akwai wiya dan in za'a kasheta ba lallai a sami mai belinta ba"
Aliyu ya wara idanunshi.
"Waya ce maka shari'a zanyi da ita musa? ba kace an kusa bikinta ba?"
Musa ya jinjina kai.
"Yawwa Musa ka shiryan tafiyar sirri Gobe In sha Allah zuwa gidansu Yarinyar"
Ya faɗa yana wani irin Murmushi.
Musa daya camfa murmushin uban gidan nashi dana mugunta ya miƙe yana cewa.
"Angama ranka ya daɗe"
Aliyu ya tura hannu cikin aljihun wandon shi ya nufi saman shi bayan sunyi sallama da Musa.
*********
Washe gari Farha ta miƙe da ƙwarin Jiki har Mutan gidansu suna tsokanarta na yadda taita neman yafiya Jiya Tun magariba ta tsala kwaliya sabida salim yace mata zaizo Burinta yazo yau ɗin suyi maganar aurensu tunda dai yanzu ba batun aiki sabida an ƙona gidan radion tasu bababn tashin hankalinta ma shine yadda zata sanar da umma cewar an dakatar da ita a wajan aiki wanda faɗin hakan shine mafitarta, dan kota sha giyar wake bazata dangana kanta da gidan radion da aka ƙona jiya ba, gwara tai aurenta ta huta.
A wayar Umma salim ya kirata akan tai haƙuri baze sami damar zuwa ba jifa tai da wayar tana tura baki gaba.
Umma ta dube ta.
"Ai sai ki tashi ki tafi makaranta tunda baze zo ba"
Takaicin Salim yasa taja hijabin ta tai waje ko jakar makaranta yau bata ɗauka ba.
Adaidai wannan Lokacin Aliyu ya fito cikin Shirinsa jallabiya ya saka Brown Colour wadda tai masifar yi masa kyau ya fesa turare ya Rufe fuskarshi da face mask.
Ya fito compound ɗin gidan musa yana cikin mota yana jiranshi yana shiga motar musa yaja suka bar Gidan masu gadi suka buɗe Musu gate.
A bakin layin su Farha musa yay parking sabida motar ba zata shiga cikin layin ba, Aliyu ya fito daga cikin Motar yana mamakin ƙanƙantar cikin layin ko ina dumɗum ba wutar nepa Musa na gaba Aliyu yana binshi Daga nesa musa ya nuna masa ɗan ƙaramin gidan su farha.
Aliyu ya ƙarewa gidan kallo ya taɓe bakin shi lallai yarinyar nan tai gangancin shiga Hurumin shi dan sai ya tarwatsa mata dukkan wani farin cikinta kamar yadda tai silar shigar shi damuwa shida dangin shi da dukkan masoyan shi.
"Musa koma mota ka jirani"
Da mamaki Musa ya koma Da baya duk da bai san Ƙudirin Uban gidan nashi ba amman Lamarin ya bashi mamaki.
Aliyu ya ƙarasa ƙofar gidansu Farha Adaidai wannan Lokacin ta sako kanta ta fito Ƙofar gidan Ikram ta biyo ta tana cewa
"Yaya Farha umma tace ga jakarki"
A zuciye ta juya.
"Dan ubanki sai ki kai min ita aji munafuka"
Ta faɗa batare data lura da Aliyu dake tsaye a wajan ba ya zuba mata ido yana kallonta tsananin ƙanƙantar Yarinyar ita tafi komai ɗaure masa kai sai dai ya kula ƴar bala'i ce ta a mutu, Taɓe baki yayi yana nazarin yadda take surfawa wadda ta biyota masifa Ikram ta juya gida a guje sabida yadda Farha ta kawo mata duka.
Adaidai nan kuma Farha ta Juyo zata cigaba da tafiya ƙafarta ce tai mata nauyi sabida wanda tai arba dashi a tsaye a gabanta ya zuba mata ido babu Ko ƙiftawa............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*RABO YA RANTSE...!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*13*

luuu ta tafi zata faɗi Aliyu yayi saurin tarota jikinsa da faffaɗan hannunshi Ya wani rungumeta a cikin ƙirjinshi Ƙifta idanu Farha take tana Ƙoƙarin zamewa gaba ɗaya Jikinta rawa yake sosai tunda take a rayuwa ba namijin daya taɓa raɓata da jikinshi sai wannan bawan Allah da bata san kowa ye shiba.
Cikin Nutsuwa ya zamar da ita daga jikinsa yana sakar mata mayaudarin Murmushi.
Da sauri ta tattare Ƙasan skirt ɗinta zata Koma gida da gudu Aliyu ya kuma saka hannunshi a karo na biyu ya janyota gabanshi.
Ko Rabin tsayin shi bata kai ba ganinta yayi ƴar ƙarama a gaban shi Ya Sunkuyo sosai gabanta ya rage tsayin shi ya ƙura mata idanunshi waɗanda ya lura Suke mata kwarjini a tare dashi fiye da komai.
Lumshe idanu Farha tai Jikinta yana rawa ƙirjinta yana bugawa bata taɓa Ganin Halitta Mai kyau kamar ta wannan Bawan Allah ba, Dan ko kaɗan bata ɗauka ma bahaushe bane.
"Amincin Allah da rahmar sa su tabbata agare ki My princess"
Muryar Aliyu mai taushi ta doki dodon kunnen Farha.
Ƙara raɓewa tai Duk jikinta yayi sanyi atake anan wani irin BAƘON LAMARI Ya ziyarci zuciyarta.
"Nasan zaki mamakin yaya akai nazo har gidanku? Ba mamaki abin da kake so shi kake bibiya Naje har gidan Radio ɗin da kike aiki wanda anan hanyar na ganki amman Naga gidan Radio ɗin a Ƙone mai ya faru da shi?"
Gaban Farha ya faɗi waige take Ko wani zai zo wuce wa daga cikin ƴan gidansu ganin babu kowa yasa taja ajiyar zuciya.
"Bawan Allah kayi haƙuri dan Allah, Nima ban san mai ya faru da gidan Radio ɗin ba, Kuma kabar Ƙofar Gidannan sabida Kawun mu in yazo ya tarar dani da wani raina zai ɓaci"
Aliyu ya zubawa ɗan ƙaramin bakinta ido wanda take sarrafa shi wajan yi masa magana dashi ya wani Lumshe ido tare da warasu akanta Kana yace.
"Ina son ki kuma ni da maganar auren ki nazo in baba ma ya ganni zan sanar masa Naga matar aure agidan shi"
Farha ta firfito da idanunta waje cike da tsaro.
"Dama ana aure batare daka san Mutum ba Bawan Allah?"
Aliyu yayi Murmushi yana danne Abin da ke taso masa a ƙasan ranshi.
"Sunana Bawan Allah anan cikin gari nake nagaya miki in zaki fita aiki nake ganin wucewar ki gashi ma baki gayan dalilin Ƙona gidan Radion naku ba"
Farha ta dafe ƙirjinta dake barazanar faɗowa ƙasa dan tsabar yadda yake Luguden duka.
"Kayi haƙuri Dan Allah, Ina da wanda zan aura in Babana yazo ya ganka sai ya halaka ni"
Aliyu ya wani zaro ido wanda ya ƙara haska zatin kyansa wanda ya kuma ruɗa farha.
Yace.
"Nima ai mijin aure ne serious ina sonki kuma da gaske in da hali zan maye gurbin wancan"
A wannan karon muryar farha da ɗan tsiwa tace.
"Zaka biya dukkan hidimar daya ɗauka shekara da shekaru yana mini Idan har na Rabu dashi ai naci amanarshi na yaudare shi Kuma zan sanya Ƴan uwana da iyayena cikin damuwa"
Aliyu ya cije leɓe.
A zuciyar shi yana Cewa Ni kuma silar labarin ki ɗaya a jiya ya cillah dukkan ahalina cikin matsala ya sanya Mahaifiyata zubar hawaye Wallahi bama zan barki ba sai nai amfani da ƙarfin soyayyata na ruguza dukkan farin cikin ki yadda kika min.

Gani yaƙi cewa komai yasa ta juya zata shiga gida, Hannun shi ya ɗora a saman ƙafaɗunta ya juyo da ita tana kallon Fuskar shi.
Ya matso gabanta har yana fesa mata Hucin Numfashin sa

"Ni ina son ki, Kuma auren ki zanyi ina son ki min list na duk abin da yayi Miki ni zan ninka masa"
Daga haka ya turata soron gidan da ƙarfi ya juya yana tafiyarsa mai cike da burgewa.
Zubewa tai a wajan tana Mayar da Numfashi wata sabuwa!
Da ƙyar ta shiga cikin Gida duk maganar da Umma kewa Farha sam taƙi bata amsa gado ta haye tana tunanin anya ba aljani bane ba Ita dai bata san shiba sannan kuma bata taɓa ganin Mutum mai kyanshi ba ɗan gayu ga ƙamshinsa ya cika mata hancinta Tsintar kanta tayi da Lulluɓe Jikinta duk rufe idanun da zatai hoton shine ke yawo acikin idanunta tashi tai ta Zabga tagumi Ganin hakan baze fishsheta ba ta miƙe ta fita tsakar Gida ta ɗauro alwala ta soma nafila.

********
Yana murmushin samun nasara ya shiga Motar Ko kaɗan batai masa ba hasalima bata burge shiba kawai zai aure tane dan ya ƙuntata mata ya kuma sanya takaicin ta acikin zuciyar mahaifanta ya fahimci daga ita har mahaifanta suna bala'in son wannan saurayin nata sabida haka zai amfani da ƙarfin Soyayyar shi wadda zai cusa mata ta ƙarfin tsiya dan ya wargaza dukkan farin cikinta ita da mahaifanta kamar yadda tai jagaba wajan Yaɗa sharrin sa.
Sam baze miƙata ga Hukuma ba aurenta kaɗai da zeyi shine dorinar dukan dukkan laifi kan data masa Sabida ta yaya ma zai tsaya yana shari'a da mace.
Gumi ya share sanda ya tuno da Ammi yasan ko yasha giyar wake baze tari Ammi da batun zai auri yarinyar nan sabida Hukunci ga laifin data masa ba to meye mafita zai boyewa Ammi auren sane Girgiza kai ya shigayi ammi bata cancan ci haka daga gareshi ba Sannan kuma yasan inta sani bazata yarda ya auri yarinyar ba Shi kuma ta hanyar aure kaɗai ya zaɓi Ƙuntata mata dan shi ba mazinaci bane bare yay amfani da wata dama dan ya tarwatsa mata Farin cikinta Kuma shi ya tabbatar wa zuciyar shi cewa baze taɓa barin Wannan yarinya ba wallahi sai ya ɗauki fansar Abin da ta masa.
Har suka ƙarasa gidan shi bai sami mafita ba sallama sukai da Musa wanda bai san yadda Aliyu Yayi da yarinyar ba kuma bai sami fuskar tambaya ba bare ya tambaye shi.
Part ɗin Ammi ya nufa ta tirsasa shi akan dole sai yaci abinci yana ci tana masa Bayanin Maman Mami tazo da Ƴaƴanta Dan su masa jaje, Sannan ta buƙaci Daya Musu alfarma Mami zata ɗan kwana biyu agida ta huta.
Taɓe baki yayi tare da cewa.
"Nifa Ammi cikin satin nan ma zanje chaina dan zan shigo da sabbin Motoci kamfanina dake lagos sabida haka bani da matsala da zamanta agidan nasu"
Daga haka ya tashi yayi mata sallama yabar part ɗin.
Kwanciya yayi akan gadon shi yana hasko fuskar yarinyar Ƙaramar yarinya ce sosai Shi dariya ma ta bashi yadda yaga duk ta tsorata in banda Abin shiri na zuciyar mace ina ita ina shi Ya kuma gyara kwanciya yana hasko ƙanƙantar ta Lallai wannan ma in yace zai haɗa ƙirji da ita tabbas Mutuwa zatai dan yayi mata girma shi bai ma taɓa ganin Halitta ƙarama kamar ta wannan yarinya ba komai nata ƙarami hatta yatsun hannunta daya kalla ƙananu ne.
ALIYU KENAN.
Yaja Bargon shi ba jimawa bacci yay awon gaba dashi.
Da safe ya fita kamfanin shi tuni ya watsar ma da batun wannan yarinyar ya shiga sabga da ma'aikatan shi wanda yawanci Jaje ne suke masa akan abin da ya faru Dan nacin Ƴan jarida har can suka bishi akan suna son jin ta bakin shi fafur ya hana ma'aikatan shi barin ƴan jaridar su shigo masa haka ya wuni a office yana saka hannun a takardun Motocin da aka tura wasu jahohin bai tashi ba sai wajan Magariba ƙofar Gidan shi ma ba masaka tsinke tun yana magana muryarshi tana fita har muryar tashi sai da ta dashe sabida amsa gaisuwar jama'a bai shiga gida ba sai wajan 12 na dare Yana mai jin farin cikin yadda al'umma suka nuna rashin jin daɗin su na abin da ya same shi lallai ya yarda jama'a rahma ce Kuma alkairi Daɗi gare shi wanka yayi ya kwanta jikinsa fal gajiya Hutu kaɗai yake buƙata..........
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
          
           *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                        *14*

Juyi kawai take yi a gado jikinta sanye da ƙaramar riga mai hannun shimi hannunta dafe da daidai ƙasan mararta wanda take dannawa sai Nishin azaba take Kukan ma yaƙi zuwa

Please Login or Register in order to submit comment