Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali acikin wannan satin?"
Farha tai jimm can sai batun Data ji umma nayi jiya ya faɗo mata.
"Yallaɓai Naji Dai Maganar SA na gwamna a ɓangaran matasa wanda zai basu tallafi na Musamman wai ko a kamfanin shi Oho dai"
Md ya ɗaga waya ya kira ɗaya daga cikin Abokan aikin su farha.
Da sauri Taj ya ƙaraso suka gaisa da Md.
"Kaji abin da yake ta Yaɗuwa a gari shine batun bada aiki na kamfanin SA na gwamna a ɓangaran matasa nima naji wannan labari kuma naso daga tashar mu ya soma fita dan hakan zai calling attention ɗin jama'a zuwa tashar mu tunda hakan bai samu ba Taj ina son Mu nemo Wani labarin akan shi wanda zai Jawo hankalin Mutane zuwa tashar mu nidai suna nake so kamar yadda kuka sani"

Office ɗin yayi shuru Farha da shema'u na raba ido Taj yace.
"Gaskiya yallaɓai nidai a sanina Yadda naji ana Faɗin alkairin Madaki zai wuya ka sami wata matsala daga ɓangaranshi kuma idan har ka lalubota ƙarshe abin akanka zai ƙare dan Babban mutum ne a garin nan Kaje Ƙofar na'isa zuwa galadanci zuwa gwangwazo zuwa gudundi Mandawari gidan sarki kaga yadda matasa suke Yinsa kaga taɓa irin waɗannan akwai Bala'i"

Md yayi dariya.

"Nifa taj baka fahimta ni babu wata matsala data taɓa haɗani dashi, Hasalima a pasta kaɗai nake ganin shi kawai yadda yanzu zancen shi ya cika gari nake son na samo Koma meye da sunan shi dan nasan tashata zatai farin jini kaga daga nan zan soma amsar manyan advert a wajan mutane"

Tajjuddeen yayi shuru.
"Eh to yallaɓai yana da Special Issue amman wannan na familyn sane Naji ance bai taɓa haihuwa ba duk cikin da matarshi ta samu zubewa yake"
Jikin Md har rawa yake wajan cewa.
"Serious taj? wajan wa kaji?"
Taj yay murmushi.
"Ah Kasan Babban mutum ne shi to dole wani bin koda yana son Sirri hakan baze yuwu ba dole maganar shi ta dinga fita more especially daya soma siyasa"
Md yace
"Haka jeka taj zan nemaka"
Md ya dubi su farha bayan fitar Taj.
"Yawwa ina son ku juya wannan labarin nashi ya koma cewar Tsafi yake da duk Cikin da matar shi take samu domin yayi kuɗi"

Zufa ce ta soma karyowa daga Jikin farha da Shema'u.............
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
          
           *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *009*

Duk da uban raɓar na'urar A'c data ke kaɗawa a office ɗin, Hakan bai hana Gumi wanke musu Jikin suba.
Shema'u ta kalli Farha wadda take ta faman ƙifta ido kamar zata fasa ihu.
Maganar Md ce ta karaɗe Office ɗin.
"Wannan labari zai jawo hankalin Mutane zuwa wannan tashar tamu uwa uba manyan ƴan kasuwa zasu san da zamanta har ma su fara bamu manyan tallika sannan Ƴan hamayyar jam'iyarsu Suma zasu neme mu ƙila ma su ɗauki Nauyin fili na Musamman dan tattaunawa akan Harkar siyasa"

Md ya faɗa hankalinshi kwance.
"Gaskiya nidai bazan iya ba sabida taɓa Babban Mutum irinshi akwai matsala kamar yadda Taj ya faɗa Kuma ma hakan ya zama kamar Ɓata masa suna zamuyi hakan zai janyo mana babbar matsala"
Cewar shema'u wadda ta faɗa kanta tsaye Md ya ɗaga mata hannu.

"Ƙin Amincewar kowacce acikinku shine Tikitin Barinta aiki a wannan tasha kuna nufin zan ɗaukeku na baku Dubu ashirin duk wata a banza ne Jiya ma kaɗai dana tura ku ɗauko rahoto Guduwa kukai sabida haka wannan Labari dana buƙata shi nake so ku watsa Ƙin amincewa kuma kora ce Amincewa kuma Ƙarin albashine tare da Karramawa ta musamman danna san ba ƙaramin alkairi zamu samu ba"
Ya faɗa yana girgiza ƙafafun shi Farha ta bishi da ido Duk yadda Allah ya rufa mai asiri Amman bai godewa ba yake hango abin da zai saka shi acikin matsala, Har ta ɗaga kai zata ce ita ma bazata iyaba sai ta tuna da yadda aurenta zai zo ga hidimar Kayan ɗaki wanda da wannan aikin Ita da umma suka laru domin su rufawa kansu asiri dan tasan kawu ba abin da zai Sannan matan gidansu kowa ya sawa aikinta ido idan har ta daina wannan zai basu ƙofar Yi mata habaici da dariya sannan zata jefa zargi a zuciyar umma na dalilin daya sa aka koreta tasan kota faɗi dalili ba lallai a yadda.

"Yallaɓai zanyi ni zan iya"
Ta faɗa Muryarta na rawa.
Md ya washe baki yana cewa

"Yawwa ƴar gari To shikenan Gobe zamu fitar da tsarin Komai Yau na sallameki da wuri tafi gida ke kuma ga takardun kinan kada ki kuma dawo min Tasha"
Yana faɗin haka ya miƙe ya watsowa shema'u takardunta yabar Office Ɗin Shema'u ta ɗebe su ta zuba a jaka ta Miƙe tana bala'i
"Dama irin kune kuke ɓatawa ƴan jarida suna kuma in sha Allah wannan labari sai ya wargaza maka farin cikin ka, kawai dan biyan buƙatar kanka zaka ɓatawa Bawan Allah suna mutum mai taimako mai tausayi Allah baze baka nasara ba"

Tana gama faɗin haka ta fice Sauran ma'aikata na mata magana suna tambayarta ƙanwar Gali mai ya faru tai musu banza Ta tari Abin hawa da ƙyar Farha ta cimmata suka shiga adaidaita zuwa gida.

"Ke yanzu Farha akan abin da bai taka kara ya karya ba zaki zaɓi abin da zai ja miki matsala dan wallahi ƙarshenta ta rufta dake, Ki zauna ki karatun ta nutsu shi Md mai kuɗi ne ƙila ma ya ɗauke iyalinshi subar ƙasar ke kuwa fa? baki da tsuntsu baki da tarko wagairahun Ai a kano"

Farha tai murmushi.
"Shema'u baza ki gane ba nidai Allah yasa hakan ya zama alkairi Md ya ƙara min kuɗin nan dan na kashe matsalolin gabana"

Shema'u ta mata wani sakaran kallo kafin tace.
"Farha kenan mai yasa mu mutane muke da son kammu ne? kin zaɓi ki ɓatawa wanda nauyin sama da al'umma dubu suke ci a ƙasan shi dan ki kauda matsalar gabanki? kin zaɓi ƙuntata zuciyar wanda yake taimako domin Allah dan ki kauda taki matsalar lallai kin taro faɗan da baki da ƴan wasa Allah ya baki sa'a"
Duk wannan Maganganu na Shema'u basu saka farha taji wata karaya akan Ƙudirinta ba haka ta rufe ido tana Tunanin yadda zata kaya gobe.

Ba yadda shema'u batayi da farha ba akan ta janye amman taƙi daga ƙarshe haka suka rabu baram baram Farha a zuciye ta shiga gida Sabida yadda shema'u ta gaggaya mata magana har tana ce mata Shi mai kuɗi ne zai iya sawa a ɗaure kaf Familyn su Farhan.

Tana shiga cikin gidan ta tarar da su Umma a tsakar gida kowa farin ciki yake ta aje Handbag ɗinta ta nufi randa ta ɗibi ruwa ta kafa kai tana sha.
"Farha kinga Allah ya karɓi addu'ata Yau dai su Halifa sun sami aiki a kamfanin SA ɗin jiya"
Gaban farha ya faɗi tai murmushin dole tai Musu fatan alkairi ta wuce ɗaki.

Yau gidansu Farha gwanin sha'awa su Halifa anƙi fita konan da can suna gida ana taya su Murna Shi Halifa yana ɓangaran gyaran motoci Nura kuma sune masu Duba motocin da suka shigo da waɗanda suka fita dama an gama karatu ba aikin yi Ga zafin talauci ga Samartaka Wannan samun aikin Nasu Yayi wa kowa na gidan Daɗi hatta kawu sai da ya shiwa SA ɗin gwamna Albarka Abin daɗin Kuma shine Kowani ɗan ɗaki ya samu aikin Halifa ɗan ɗakin su Ruƙayya Nura kuma ɗan Ɗakin su Hadiza ita dama Umman Farha bata da ɗa namiji amman harta fi Iyayen yaran murnar samun aikin nasu.

Gaba ɗaya Farha jitai bata da sukuni Taƙi sakin Jikinta a gida sai faman Juyi take a saman gado Ko tsakar gida taƙi fitowa duk Murnar da ake agidan tana ɗaki a ƙunshe har magariba.

"Wai Farha meke damunki kada kija ace kina baƙin cikin samun aikin su Halifa kinsan halin Gidannan ba'a raina magana"
Farha taja Abin da ta rufe Jikinta dashi.
"Umma bana jin daɗin Jikina ne"
Umma ta dube ta da kulawa sosai.
"Allah yasa ba ciwon marar ki bane zai tashi ba, ga ba kuɗi a hannuna"
Farha ta dubi umma
"A,a lokaci bai yiba kuma ina neman sauƙi wajan Allah"
Ranar Ko makarantar dare ma bata jeba Umma kuwa yau hirar tsakar gida ce ta Ruɗe a gidan wanda Halifa ya baje yana ta basu labarin Yadda Mai Kamfanin Madaki Motors ɗin ya karramasu Kuma da kanshi ya Duba takardun kowanne acikinsu ya kuma raba musu aiki da albashi mai tsoka Halifa ya ƙara da cewa.

"Ai wallahi sanda naji labaran jiya ko bacci banyi ba Muna tashi Da asubah muka tafi Sai wajan azahar layi yazo kammu Mutum Ɗari da hamsin ya nema amman Mutum yakai Dubu da sukaje lallai ana zaman banza a garin nan"
Babarsu Ruƙayya tace.
"Allah dai yayi masa albarka yadda ya fitar damu daga takaicin rayuwa shima Allah ya yaye masa dukkan matsalolin shi"

Babarsu Hadiza tai caraf tace.
"Tab su masu kuɗi ina suka ga matsala zasu sha madara suci kaji Kai dai talaka mai neman na masara kaike da matsala"

Halifa yayi dariya sannan yace.
"Tab yadda naji fa ance bai taɓa haihuwa ba Mama ke kin ganshi kamar shi yayi kanshi dan kyau yadda kika ga Tumatur sabida ja wallahi ban taɓa ganin Mutum mai kyau irin nashi ba Kamar ka taɓa jini ya fito"
Ya ƙare yana kallon Babarsu.
Babarsu Ruƙayya tace.
"Lallai duk wadda Allah yasa ta haihu dashi ta girmi talauci Allah ya bashi ɗan kanshi"
Ire iren waɗannan hirar sukai tayi har kawu ya shigo shima ya saka baki ranar gidan dai ya wanzu cikin farin ciki ita kam Farha bata san wainar da suke toyawa ba haka tai kwanciyar bacci mai nauyi yayi gaba da ita.

***********

Ammi ta dubi Aliyu wanda shigowar shi kenan Falon nata dan tunda yazo bai sami damar zuwa wajanta ba, Yaje gidan gwamna yau kuma ya ɗebi ƙananun ma'aikata a kamfanin shi dan ko wajan wasan ƙwallon ƙafar matasan gwale bai jeba sai saƙo ya bawa musa yakai musu.

"Sannu babana mai za'a kawo maka?"
Ammi ta faɗa da kulawa.
"Ammi ni yanzu bazan iya cin komai ba dare yayi adai haɗo min Baƙin shayi kaɗai ma is ok"

Ammi ta kalli Sajeeda da duk ta shiga taitayin ta ganin dodonsu ya shigo falon.
"Auta  maza haɗowa Hammanki shayi a ƙananun Kofuna"
Ya turɓune fuska.

"Ammi kinsan bani son yarannan na taɓa abu kina bani"

Ammi ta kama haɓa tana dariya.
"To sarkin tsafta na manta ne ai, Bara na haɗo ma da kaina, Niko nace yaya Kaje ka dubo Mami kuwa? ɗazu na kira yaya tajirar ma bata ɗauka ba ina ga bata kusa da wayar tata ne"

Wanni kallo ya watsawa Sajeeda ba shiri ta Miƙe har tana haɗawa da Gudu tabar falon.

Kafin yaɗan kalli Ammi............

*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*10*

Ya fesar da zazzafan huci murya can cikin ƙasan maƙoshi ya furta.
"Ammi tun ina Abuja nai mata waya bata dawo ba kenan?"
Ammi ta bishi da kallon mamaki.
"Ban gane bata dawo ba kenan? kai da kuke haɗe waje ɗaya tayaya zaka zo kana tambayata"
Ya saki wani Miskilin Murmushi sannan yace.
"Ammi ai ban sani ba ko anan ta kwana tunda ni banbi takanta ba bacci yasha kaina jiya yau kuma tun sassafe nabar gidan"
Ammi bata Masa magana ba sai da taje Kitchen ta haɗo masa haɗaɗɗan Baƙin shayi wanda yaji citta da na'a na'a sai ƙamshi yake ta ɗora ƴar Butar shayin a saman tray sannan ta jero ƙananun Kofuna a gefe ta nufo Parloun dasu a hannunta.

Da sauri ya miƙe ya karɓi tray ɗin yana cewa.
"Sannu Ammi"
Ya janyo center table ya ɗora tray ɗin akanshi.

Ya koma ya zauna a saman kujerar da take facing ɗin wadda Ammi take zaune akanta.

"Wannan wace irin magana kake Babana? yanzu ace kai kana a matsayin Mijinta ka kasa leƙawa ɗakinta har ka kwana ka wuni agidan amman baka san ko ta dawo ba ko bata dawo ba?"
Ya ɗaga butar shayin ya tsiyaya a kofi sai faman turiri yake yi da zafin da komai yake kurɓa yana lumshe ido zafin na ratsa mai ɓargon Jikinshi.

"Ammi kimin uziri jiya ban shigo ba sai 12 na dare bayan na gama meeting da mai girma gwamna na shiga gidan Radio mun gana da Ƴan jarida, yau kuma kinga shigowata kenan yanzun nan nai sallar isha'i sai yanzu na sami kaina duba ƙarfe kusan goma da wani abu"

Ya faɗa yana ƙara tsiyayar shayin.
"Kaga irin abin da nake nuna maka wannan shine yake ƙara sanyawa nake ƙaunar mami har raina, Sabida ba kowace mace bace zata jure auren irinku sam baka da lokacin kanka, Yarinyar nan bata taɓa ƙorafi ba wallahi bata taɓa kawomin, Ƙarar kaba Kaga Tana gadon asibiti haka fa ka tsallake ka tafi Abuja Bana jin ka dubo ta yanzu kamata yayi kaje ka duba lafiyarta sai ku tawo tare"

Ya lumshe idanu yana sauraran Ammi harta gama maganar tata.
"Ammi tun ina can na mata waya ta dawo tunda bata dawo ba a rabu da ita May be hutawa take, Nidai nasan duk wani haƙƙi ina ƙoƙarin saukewa"
Ammi tabi sa da kallo yana da kafiya duk abin da yace zeyi to baya fasawa.

"Dalilin haka Ammi nake son na ƙara aure Kin san Bahaushe yace mai Mata ɗaya Aminin gwauro, bada ban kin gayan bata nan ba ni kam bamma san bata dawo ba"
Ya faɗa yana murmushi dan tsokanar Ammi yayi da batun zai ƙara aure Aiko nan da nan ta haɗe girar sama data ƙasa.
"Idan ma sabida haihuwa kake son ƙara aure in ka kwantar da hankalin ka kwana nawa ne matarka ta sake samun wani, Tunda Zaku fita India a duba matsalar yawan ɓarewar Cikin nata, kuma nan ma na saka ana ta addu'a kayi haƙuri kada ka ƙara aure sabida ina tsoron matan wannan zamani ba kowace mace bace zata aure ka dan Allah wata ma Da burin ta wargaza gidannan zata shigo ita kuwa mami duk tsiya tamu ce matar Rufin asiri ce duk abin da kake mana bata taɓa ɗaga ido ta duba hakan da suffar baƙin Ciki ba ina burin Allah ya albarkace ka da samun zuri'a daga Mami sabida nagartarta"

Ya jinjina kai duk maganganun Ammi haka suke shima kanshi yana mamakin Mami sam bata da matsala Haƙurinta har yayi yawa tundaga kan Ƴan uwanshi Har zuwa kan Ma'aikatan gidan suna yabonta Duk yadda zai Buzance mata yayi mata masifa inta masa laifi bata ko duban sa haka Duk nacin sa wajan Buƙatar aure bata raki Bare Ta ƙosa.

"Ammi mai ƴa nima dama wasa nake ni yanzu Ɗayar ma Bani da lokacinta bare har Biyu, Ina naga Lokacin ma duba matar Ina nan dai ina addu'a Allah ya bamu ingantacce ƙarshan watan nan ma doctor yace za'a mata ɗaurin mahaifa wanda yace In sha Allah Da zarar an kwance Kuma mahaifarta zata iya ɗaukar Ciki"

Ammi ta washe baki cike da farin ciki tace.
"Allahu yasa Ya Rabbi ya nunan wannan rana, Babana a yanzu ba abin da zance wa Allah sai godiya duk wata ni'ima yayi Min ita Burina naga Ɗanka Ko ƴarka A duniya yadda na matsu da wannan burin ban matsu naga auren su Bashir ba, Wallahi bada ban sharrin matan wannan zamani ba dani dakai na zan Ƙara nema maka wani auren a karo na biyu ko Allah yasa a dace, To Ina tsoron Sharrin matan wannan zamani Kuma sannan Mami ba juya bace Ɓari ne kaɗai matsalar ta shima Allah zai daidaita Gata ƴar uwarka ta jini gata da kyawu da biyayya Ni banga aibun taba Sabida haka ka ƙara damƙe matarka Koda wasa bana son ka kuma min maganar ƙarin wani aure"


Aliyu yayi Murmushi ya rasa mai Yasa Amminsa ke masifar son Mami wata irin soyayya Ammi kewa Mami sosai, Sannan yana ganin tsoro a fuskar Ammi ƙarara duk sanda yace zai ƙara aure Kullum batun ta akan hakan shine tana tsoron sharrin matan wannan zamani amman mami ita tata ce tasan ba tada Matsala.

Ya miƙe yana zube dukkan hannayen shi cikin aljihun Farar shaddar Jikin shi "Ammi ni zan kwanta mu kwan lafiya"
Daga haka ya juya yabar Ɗakin Ammi ta bishi da kallon tausayi Duk kawaicin sa wannan karon ya shiga damuwar Ɓarin Mami.

Koda ya koma ɗaki Shafa'i yayi ya kwanta ko kallon wayar shi da Mami ke faman Kira baiyi ba Daga ƙarshe ma kasheta yayi inta matsu dan kanta ta dawo shikam baze Je ba.
***********

Sukuku Farha ta miƙe yau har umma na ce mata ko ba zata aikin bane jiki ba ƙwari ta Shirya tai sallama da Umma ta fita Gabanta tun Jiya yake faɗuwa Haka ta ƙarasa Tashar tasu Md ya tareta da Murna yau har ɗakin yaɗa labarai ya rakata yana ƙara bata Hope akan Labarin da zata watsa a safiyar yau Ɗin.

Bayan sunyi sallama da Md ta duba doguwar takardar daya Miƙo mata sunan SA na gwamman a ɓangaran Matasa ne ya fita ɓaro ɓaro Jikin takardar.
Murya ta gyara bayan ta maƙala headphone tare da sanya ƴar ƙaramar loudspeaker a bakin ta

Cikin zaƙin Muryarta sautin maganarta ke Fita.
_Barkam mu da safiyar laraba ga labaran namu daki daki karku manta kuna tare da tauraruwar tasharku mai farin Jini GARKUWA RADIO mita goma da ɗigo tara, Da farko zamu fara leƙawa sashin siyasar Kano, zakuji cewa mai bawa gwamnatin jaha shawara ta musamman a ɓangaran matasa Alhaji Aliyu Audu Madaki, Wanda ya Ƙware a fanni bada tallafi taimakon yara mata marayu matasa wanda sunan shi yayi fice tun ma kafin gwamnatin ta bashi Muƙami, Ya ƙara rasa cikin da matarshi ke samu a karo na Huɗu nasan dai mai sauraro zai mamaki tare da aljabin yadda duk cikin da mai ɗakin mai bawa gwamnan shawara take samu yake ɓare wa, To ba abin mamaki bane in ka duba yadda yake shiga da fice da facaka da dukiya wadda wata majiya mai tushe ta tabbatar da Yadda yake salwantar da cikin matar tashi ne ta hanyar bawa matsafa Ƴaƴan cikin domin ai masa tsafi Kuɗinsa ya ƙara hauhawa wanda hakan shine maƙasudin arziƙinsa,wannan kenan sai kuma ɓangaran wutar lantarki wadda ta wadata acikin wannan jaha kada ku manta kuna sauraran wannan labarine daga wannan tasha tamu mai farin Jini dan kawo tallanku ko Gayyatar taron suna biki kuna iya ziyartarmu a shafikanmu na Facebook Ko adireshin mu dake Kan titin audu baƙo way_
Farha ta ƙarasa bayan ta yarfe zufar data wanke mata Jikinta kowa na ɗakin watsa labaran kallonta yake Jiki ba ƙarfi ta ɗauki jakarta kanta ciwo yake mata sai da ta gama labaran ma ta mance Ko sunanta bata faɗa ba Ga wata nadama na Cin zuciyarta.

Ko Bitakan Office Ɗin Md batai ba tayi hanyar titi sabida yadda idanunta ke Lumshewa.

Haka ta koma gida zuwa rana zazzaɓi mai zafi ya rufeta har haɗe haƙora takeyi.

Daga cikin garin kano duk wanda ya saurari labaran safiya na tashar Garkuwa yaji wannan ƙazafi da akaiwa Hasken matasa wasu sun yarda wasu sun ƙaryata kafin kace me labari ya cika gari Ƙofar Gidan Aliyu ya cika dam da matasa waɗanda suka zagaye Gidan domin bashi kariya koda wasu zasu yo zanga zanga dan barazana gare shi, Matasan Ƙofar na'isa kuwa Tuni sunyi zuga zuwa Gidan Radion garkuwa wasu da kalanzir wasu da ashana da taya Ba wata Sanya suka cinnawa Gidan Radion wuta wanda da ƙyar ma'aikatan suka sha Zuwa wani Lokaci gari ya ruɗe ƴan sanda sun cika titina sabida zanga zangar matasa waɗanda suka Fito suka nuna ƙin Goyon bayansu akan wannan ƙazafi da akaiwa Aliyu.
MD da gudawa ya ƙarasa gidanshi ya kasa zaune ya kasa tsaye tsoro nadama suke cin zuciyar shi yasan Ba Aliyu ba hatta ƙungiyar ƴan jaridu ta ƙasa sai ta tuhume shi akan wannan labari da tashar shi ta fitar sabida doka ce ga duk gidan Rediyon da bai tace labari ya tabbatar da ingancin shiba kafin ya fitar dashi, ga shinan son zuciya da bala'in Neman suna yaja masa bala'in da bai san Lokacin fitar shiba.

A guje Ammi ta nufi sashin Aliyu wanda duk ma'aikatan Sashin nasa sunyi cirko cirko wasu ma kuka suke sabida zuwa wannan Lokacin kowa yaji abin da ke faruwa.

Ta ƙarasa falon Musa na durƙushe agaban shi ga sautin maganar mai labaran nan raurau ya karaɗe Falon wanda Musa ya ɗauki Recording ya kunnawa Aliyu.............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*RABO YA RANTSE...!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*11*

Zagaye Ƙaton Parloun shi yake hannun shi Goye a bayan shi Sam ba zaka fahimci inda Halin da yake ciki ya dosa ba Idanun shi ya rintse Har yanzu sautin Muryar yarinyar da take Labaran bai bar amsa kuwa acikin Dodon Kunnen shiba.

"Iya sanina bani da abokin faɗa a Wajan sana'ata Bani da Abokin Gaba bani da wanda na taɓa Musayar Harshe dashi a ko ina Why zaku Min haka mai nayi Muku zaku ɓata min suna a idanun al'ummah idan wasu sun yarda wasu ba zasu yarda Ba"

Da sauri ya Zube a gaban Ammi wadda ta tallafe haɓa da hannunta hawaye nabin Idanunta.
Ya kamo ƙafafunta ya ɗora kanshi akansu.
"Ammi ki yarda dani wallahi bani da Hannu a zubewar Cikin Mami, Arziƙi Allah ne yayi Minshi nima ina mamakin Yadda duk abin da na taɓa sai Allah ya saka mai nasibi Ke shaida ce ammi kinsan yadda Muka taso"
Yana fara maganar Muryarshi ta shaƙe ya soma tari da gudu Ammi Ta buɗe Frij ta ɗauko ruwa ta ɓalle Gorar ta fara bashi Musa na masa sannu.

"Nina haife ka Nina san waye kai Allah ya tsareka daga dukkan wanda ya nufoka da sharri Allah ya kare ka daga dukkan sharri"
Ammi ta faɗa cikin kuka.

Da gudu ɗaya daga cikin masu gadin Gidan ya shigo falon Ammi ta zaro ido tana cewa.
"Sun shigo su kashe min shi ko? ku taimaka Ku Ɓoye min shi kada a far masa"
Mai gadin yayi Murmushi.
"Hajiya ku godewa Allah, Haƙiƙa baka Alkairi ka taɓe kamar yadda baka sharri ka gama lafiya, Dama zaki fito waje da sai Kin mayar da kukan ki Dariya sabida Ilahirin matasan Dake garinnan sunyi dafifi a ƙofar Gidannan domin bawa mai gida kariya, Yanzu haka mai girma gwamna ya turo da Motocin Ƴan sanda kusan Goma suna nan tsaye da Bindigu domin su bawa wannan Bawan Allah kariya Sannan matasan gari sun Je sun ƙona gidan Radion yanzu haka neman Mai gidan Radion suke ruwa a jallo dan dai basu sami Mutum Ko ɗaya bane daga cikin ma'aikatan sabida kowa ya gudu"


Ammi ta sauke ajiyar zuciya tana shafa kan Aliyu wanda ya kwantar dashi akan cinyarta.
Ya kasa magana Har Ammi ta sallami su Musa Falon yayi saura daga shi sai ita.
"Ka ɗauka hakan wata nasara ce daga Allah in sha Allah hakan ba ze zama sharri gareka ba sai Alkairi kuma bana son kai fushi ka daina taimako wannan ma ya zama ƙara ƙarfin ka wajan taimakon al'umma domin kaga ranar hakan da idanunka inda baka taimako da bamu san yadda abin zai zama ba, amman albarkacin al'ummar Annabi gashi kana ta samu kariya"
Aliyu yaƙi magana sabida zuciyarshi yadda take a karye ta yaya za'a ce shike salwantar da Cikin Mami dan ya ƙara arziƙi ta yaya za'a dangana dukiyar shi data tsafi shida ya sha wahala kafin ya tarata.

Duk yadda ake kiranshi a waya ya kasa ɗagawa Ta ya sadik kaɗai ya ɗaga data bashir waɗanda suka ɗaga hankalinsu akan Labarin da suka ji ya tabbatar Musu da cewa yana lafiya ya kashe wayar sai ta mai girma gwamna wanda ya bashi haƙuri yace kada ya saka abin aranshi hakan ma matakin

Please Login or Register in order to submit comment