Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake jahar katsina wajan Bokanta taje wanda tai Imanin Aikin shine yaci sanda Aliyu ze auri Mami Ta sami damar ganin Bokan wanda ya haɗa mata Mugayen ayyuka wanda daga ciki harda haukata Farha matar Ali sabida tace base da lafiya zatai rayuwar auren ba sannan Ita kuma Ammi a sakar mata Cutar shanyewar Jiki Aliyu Kuma a birkita masa tunanin sa ya zama baya daji ko gani se Mami a duniya waɗannan zafafan ayyukan aka haɗowa tajira ta zube masa manyan Kuɗi Ta kamo hanyar gida tare da sharaɗin nan da kwana uku sheɗanun da Bokan ze tura Jikin su zasu fara aikin sedai ya bata wani baƙin magani yace ta saka A kusurwa uku ta Farha data Ammi data Aliyu wanda shine kan Aikin Kuma yace lallai ta saka wannan magani in ta kuskura to aikin ze juya kanta

Sedai a hanyar dawowar ta Allah yayi Ikon sa akan motar su wadda ta ɗebo mutane daga wannan ƙauye zuwa kano wata ƙatuwar Motar katako tabi takan Motar tasu wanda motar ta gangara Gefen hanya Mutanan ciki duk sun sami raunika Wanda Har da tajira acikin waɗanda suka sami Rauni wanda nata yafi Na kowa shahara dan ta karye a cinyarta Ƙashin kwankwasonta ya ɓalle Kanta ya fashe da ƙyar aka haɗa wayarta data yashe can Ƙasa aka kira Numbern da aka gani acikin wayar tata. ALLAH KENAN!


wajan ƙarfe Ukun Dare wayar Hassana ta fara Ringing wadda ta manta Bata kashe taba.
Cikin magagin bacci ta ɗaga wayar Muryar wani namiji ce yace.
"Da Allah da Hassana Muke magana?"
Hassana ta watsake tare da cewa.
"Nice"
Se yace mata.
"Mun sami Numberki a wayar wata mata naga kece ƙarshen Kiranta to bamu san dai halaƙar ku ba Sabida bata hayyacinta Motar su ta sami hatsari ne a tsakanin Hanyar dawowa katsina zuwa kano yanzu dai Mun samu an saka su a wata motar Muka tawo dasu babban asibitin murtala dake Cikin kano yanzu haka muna sashin ƴan gaggawa"
Wayar ce ta Mutu hassana ta ɗora hannu aka tana cewa.
"Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un mama kin jawa kanki Babu wa'azin da Aunty mami batai Miki ba Amman kika Murje dama in baka godewa Allah akan Ni'imar saba zaka godewa azabarsa"
Maganganun Hassana ne suka tada mami da sauran ƴan uwan haka suka fita da ƙyar suka ƙarasa Asibitin dan akwai tazara tsakanin fagge zuwa asibitin Murtala sabida dare ne babu abin hawa Koda suka je asibitin ma seda suka sami ɗan sanda sannan suka sami ganin tajira wadda sam bata gane Kowa Mami kuka tasa a haka suka zauna har asubahi taimakon gaggawa aka bawa tajira Wanda ta samu ta dawo hayyacinta sedai Likita ya tabbatar wa su mami sedai su ɗauketa su kaita asibitin ƙashi ai mata Hotuna a wajan data samu rauni kan Mota suka samu aka sakata zuwa babban asibitin ƙashi dake Dala Iya kuɗin Hoton Cinyar Tajira dana kwankwasonta seda ya saka mami ƙaramin hauka dan basu da wannan Kuɗi duk bokaye sun cinye Musu kuɗaɗan su hatta Motar da Aliyu ya sai Musu sun siyar basu da komai se Gidan da suke Ciki se ɗan Kuɗin Cin abinci Suna kuka suka mayar da ita Mota tana wata Irin ƙara sabida da an taɓa mata jikinta ji take kamar zata mutu dan azaba.

Zubawa sarautar Allah ido sukai akan lamarin tajira dan basu da hanyar Kuɗin hotunan ta bare aje ga batun aiki Kashi da fitsari a kwance take dan tun da suka dawo Gida ko zama bata iya yi.
Abin al'ajabi da mamaki bayan kwana uku Tajira ta soma wani Irin Gurnani tana Ihu tana zabure zabure Ga shi gaba ɗaya Ko wace Gaɓa ta Jikinta ta dena aiki Sedai taita ihun tana zabura amman babu damar tashi Kafin sati tajira har haushin kare yi take tana wata irin dariya tana xare ido maƙota na shigowa dubata Tuni magana ta cika unguwa kowa da fassarar da yake ganin haka yasa su mami suka dena Buɗe Gidan su Kuma suna Ƙoƙarin gyara mahaifiyarsu sedai fa a tsorace suke mata Komai dan Gudu suke kada ta musu Illah.
Yau da gobe se Allah gaba ɗaya rayuwa ta sauyawa su mami duk kayan mami dana tajira na alfarma masu kyau haka ta kwashe ta siyar saboda suci abinci damma su Hassana na Koyarwa da wannan suke Ganɗawa su sami na abinci rayuwa ta sauyawa tajira Da iyalanta Kullum gidan kamar na makoki duk ƙawayen tajira sun janye ƙafarsu sun dena zuwa Inda take Tana son magana amman babu dama sabida bakinta ya shanye ga wani yawu da yake zubo mata mai Mugun Ɗoyi bada ban ɗanka ɗanka bane babu yadda za'ai ka iya zama da tajira na minti Goma amman haka Ƴaƴanta ke hidima da ita a hankali Mami itama ciwo ya soma Cinta Koda taje asibiti aka duba ta aka tabbatar mata da mahaifarta ce ta soma Ruɓewa sedai a yanke mata gaba ɗaya Mami tayi Kuka ta gode Allah ranar da wani ƙanin mahaifinsu yazo duba tajira yaga mami tana cikin ciwo seya tausaya mata Shine ya tafi da ita wani asibitin Kuɗi mai kyau anan akai mata aikin aka cire mahaifar ya biya Kuɗin harda na magani mami tai kuka tai kuka shikenan ita ba zata Kuma haihuwa ba aduniya bayan ta dawo Gida still dai ciwon Bai daina ba ta kira ɗan uwan mahaifin nasu a waya shine yazo da wani malamin addini yace Kona Islamic za'a gwada Koda malamin yazo ya kalli mami kawai yayi murmushi yace mata ze mata tofi a zamzam Kafin taci Komai kullum ta fara sha yace sheɗanu ne Suka taɓa mata mahaifar tata inda ba'ai gaggawar Cire mata mahaifar bama da zata iya Gamuwa da babbar Illah.

Mami ta kalli malamin tace masa.
"Malam mun aikata laifuka a baya nida mahaifiyata kuma ni abin ya dameni...........
Tas ta kwashe komai ta gaya masa malamin ya jinjina Abin da su mami sukai amman bai Nuna mata ba.
"Kya iya zuwa ki nemi yafiyar waɗanda Kika zalinta tinda suna raye sannan Ki nemawa mahaifiyarki tunda ita bata da bakin magana Ita kinga taka maimai ma ba'a san abun da yake damunta ba amman kodan gaba kada Ki ƙara bawa maganar Boka gaskiya bare har ki aiki da abin da zece Miki sabida aljanun da suke turawa bama su amana bane In suka je gurin wanda aka tura su basu sami nasara ba to dawowa suke Jikin Wanda ya tura sun su masa Illah dan babu Ko tamtama ciwon mahaifiyarki nada nasaba dasu harma da ciwon dake marar ki amman sha Allah kina shan wannan Tofin zakiji daɗi"
Mami ta fashe da kuka.
"Malam ni nafi zaton Koma sune suka lalata min mahaifata ya Allah na tuba"
Malamin yace.
"Allah masanin gaibu koma dai meye Ki godewa Allah zaki ƙarasa rayuwarki cikin yarda da tabbatuwa da tuba ga Allah ki duba mahaifiyarki mana Ki gani ita ba'a ma san ta ina matsalarta take ba"
Shawarwari ya bata suka musu sallama suka tafi mami ta dage wajan shan zamzam ɗin Kuma Alhamdulillahi tana jin daɗi Kuma tana godiya ga Allah daya sa a haka sakamakonta ya tsaya wanda ya ƙara tsoratar da ita tare da gudun zalunci ko cutarwa ga wani dan ta tabbata hakki ne yake bibiyar su.
Haka rayuwar ta cigaba tsayin wata Huɗu tajira tana cikin Jinya dan mami kam ta warke ras Ciwon ta ɗaya in ta tuna da an yanke mata mahaifarta wannan kan sakata kuka dan ɗa rahma ne koga su yadda suke Hidima da mahaifiyar su, wadda ta rame tai baƙi Fuskarta kamar gawayi Ta koma fiyau kamar ba tajira ba lallai Duniya abar tsoro ce.



LAGOS.
Cikin damuwa sadiƙ daya haɗa kayan sa ze tawo kano sabida yanayin jikin ammi wanda har takai ga tana kwance a asibiti ne salma tayo masa waya safiyar yau ya dubi sakina wadda duk ta koma kamar tsakuwa se rama take tana baƙi sabida wannan tsoratar da take fama da ita Kimanin watanni Huɗu tun sanda taje maƙabarta kai laya da aka firgitata har yanzu bata daina tsoratar ba Kullum dare bata iya bacci ita kaɗai tasan a wani hali take Ciki.
"Zan tafi kano ban san Lokacin dawowa taba sabida Jikin Ammi daya takura ta"
Tai kamar zata ɗora hannu aka tai kuka.
"Abban su dan Allah ka tafi dani"
Ya kalleta sabida shima kanshi yanayin nata yana bashi mamaki gaba ɗaya ta koma wata iri duk ta susuce daidai da Girki bata yi sedai Kullum su fita cin abinci Ƴaƴanta bata gyarasu Shima kanshi rabon data bashi haƙƙin sa tun Suna kano abin dai se Godiyar Allah.
"Sakina wai me yake damunki dan Allah ki gaya min amman bazaki kano ba sabida makarantar yara"
Sakina ta daki kanta da ƙarfi sabida wani abu mai kama da Kiyashi dake Bin kanta yana yawo kamar tsutsa aciki ta fara sosa Jikinta.
"Babu komai Hmm babu komai"
Ta faɗa tana maimaita magana ɗaya sadiƙ yayi mata sallama sabida Jirgi zebi ya baro Gidan Koda ya fita daga Gidan se sakina ta ɗauki wayarta ta kira jamila tana roƙonta akan tazo kodan kula da yara Jamila tai dariya.
"Haba yaya sakina ai Kifi yana ganin ka mai jar Koma! tun ranar da Mukaje wajan wannan Mutumin naji dukkan abun da kuka ƙulla ashe Ba don Allah kike so na auri Aliyu ba dan ki samu ajikina ne Ki amfani dani dan ki cika Burin ki Nikam yaya tsoronki nake sabida wannan layar da Kika amsa ba mamaki In kika rasa gawar da zaki sakawa Ki Zuban guba nasha na Mutu ki sami Gawar da zaki cusa layar aciki dan yadda idanunki ya rufe ason duniya ba abin da ba zaki ba Ni yanzu yaya na nutsu yanzu haka maganar aurena ta taso Ni na yarda dake ashe Ke da wata manufar taki ta daban akaina wato Ke ƴaƴanki da Mijinki kaɗai Kika sani wallahi yaya kin bani mamaki"
Sakina tasa kuka.
"Wallahi Ni kaina ban san ina layar take ba jamila kema tsayin wata huɗu ta yaya zan ajeta har sekin zo na saka Miki Ni na san abin da yake damuna wato tunda naje maƙabarta kai layar nai gamo se firgita nake Kullum bana iya bacci ƴar uwata kizo Ki Tayani Kula da ƴaƴana"
Jamila tai dariya.
"Yaya sakina an fa kai Kuɗin aurena tun bayan tawowarki dama ina da wanda yake sona Yadda Kika dage sena auri Ali ne yasa nake ta zabga masa wulaƙanci to Allah ya nunan manufarki sena bawa mai sona dama yanzu haka shirin aure nake Nina hana kowa ya gaya Miki wato Ni na ƙare a bauta Miki keda ƴaƴanki kada nai aure ai Firgita da bala'i yanzu kika fara gani tunda kin kasa gane Cewar Allah ɗaya yake bai da abokin tarayya Nikam In sha Allah na dena zuwa wajan Kowa zanyi aurena na cigaba da istigifari babu ni'imar da Allah bai Miki ba amman ke kin raina wannan Ni'imar taki ta wanin ki kike hange wanda wani Irin takin yake nema bai samu ba lallai kin ɗaura ƙafa da masifa Tunda baki yarda da Allah ba"
Jamila tana gama faɗa mata hakan ta kashe wayarta tana tsaki domin tun sanda suka je wajan wannan Boka da jamila taji maganarsu lokacin da ta fita waya taji Komai ya sire mata lallai mutum bai da tabbas.
Sakina tai Kuka har ta gaji haka ta aje wayar sedai tun bayan tawowar sadiƙ take wasu irin Muggan mafarkai wanda abin har yakai ga tana ganin wata irin halitta mai kama da ƙadangaru manya baƙaƙe a zahiri sosai sakina take Firgita ita kaɗai taita sosa jikinta daga yaranta sun zo inda take ta rufe su da duka ga ƙananun zance ita kaɗai taita magana tana dariya kaɗan kaɗan abun na sakina fa se du'ai.
*KANO*

Autar manya ce marubuciyar......
*ƁOYAYYAR ƘAUNA*
*BA SON TA NAKE BA*
*ƊAN MAJALISSA*
*MURADIN ZUCIYA*
*ASHE ZUMA*
*TAURARO*
*KOBA SO*
*RABON WANI*
*FITAR RABO*
*DA IZZATA*
*BAƘON LAMARI*
*AUREN BARE*
*H A S K E*
*ZUMA A BAKI*
*BAƘAR FATA*
*RABO YA RANTSE*


*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*RABO YA RANTSE 105*
Duk yadda sadiƙ yake zaton yanayin Jikin Ammi abin ya wuce tunanin sa sabida gaba ɗaya Jikin nata ya rikice bata da magana se ta akira mata Baba kada ta mutu bata nemi yafiyar shiba wannan tasa Likita yace a dena zuwa wajan ta aka barta ita kaɗai a ɗakin se Likitan dake zuwa dubata dan koda yaushe Jininta baya sauka ga ciwon kai mai tsanani dan bata yin bacci ganin haka yasa Sadiƙ yaje ya shaidawa ƴan uwanta da kuma dangin mahaifinsu ƴan cikin Gida ranar asibitin ya cika da ƴan uwa Sosai su Baba Usman sukaiwa sadiƙ faɗan mai yasa bai gaya musu abin da yake faruwa ba nan da nan Baba Usman yasa aka fara roƙon Allah akan Allah ya juyo da hankalin Aliyu gida a duk inda yake sannan ya sa aka sallami Ammi daga asibitin Gida suka dawo aka fara rubuce mata alkur'ani ana wanke mata da ruwan sama tana sha waraka ne ga dukkan damuwa ko ciwo ko wata matsala Cikin Amincin Allah ta fara dawowa daidai Jikin nata ya soma sauƙi Ammi kuka ta sanya tana roƙon gafarar su Baba Usman suma Kuma haka suka nemi gafararta Suka shirya kamar ba su taɓa Yin gaba ba zaman su yay daɗi dan koda yaushe Ilahirin zuri'ar cikin gida suna wajan Ammi suna Kula da ita Dan tuni baba usman yace wa salma ta koma gidanta Umma suwaiba ce ta dawo Gidan sabida ta dinga ɗebe wa Ammi kewa ga kuma su Hajja dama ance Shi ɗan adam rana gare shi Kuma Alhamdulillahi a wannan karon dangin mahaifin su Aliyu sun nuna bajintar su domin sunyi zumunci akan matsalar Ammi da kuma tafiyar Aliyu dan har masallatai Baba Usman yakai Barar addu'a akan a taya su da addu'a Allah ya juyo da hankalin ɗansa Gida.

Acikin wannan ƙadamin Iyayen Kamal suka zo wajan Baba usman akan maganar auren safna wanda ada mahaifiyar kamal taso ta dakatar dashi ta hanashi auren safna sabida akwai wadda taso ta bashi Amman yadda yake son safna yasa mahaifiyar shi ta amince masa akan ya aure ta ɗin tare dayi Musu fatan alkairi haka aka kawo kuɗi da saka ranar safna da kamal watanni Biyar masu zuwa

Al'amarin soyayyar Sajeeda da Nura abin Kullum gaba yake daga wajan ta amman ta Rufe ba wanda ta sanarwa addu'a take wanda ita ce ta zama garkuwanta don sosai take Komai kan hankalinta tana jin Nutsuwa na saukar mata tare da neman zaɓin Allah akan lamarin Domin haka mahaifiyarsu ta koyar dasu akan Komai nasu su nemi zaɓin Ubangiji.

Kimanin sati Guda da faruwar Komai yau da safe Jikin Ammi ya motsa Wanda gaba ɗaya kowa ma ya karaya da ita dan se Neman gafarar kowa take sadiƙ daya haɗa kaya ze Koma lagos se Zama yayi ya sakata a gaba yana Kuka zuwa yanzu Ji yake inda yasan inda Aliyu yake daya Je yazo wa Ammi dashi dan ya shaida wata irin soyayya ce a tsakanin ta da Aliyu Zamzam Baba usman ya ɗauko yana tofa mata addu'a aciki ya bata tasha wanda anan ta samu bacci.

ALIYU
Gaba ɗaya Aliyu jinsa yake wani iri acikin waɗannan Lokuta sanyin Jiki da faɗuwar gaba sun sako shi a gaba Tun farha na tambayar shi har Tai masa shuru dan itama ta kanta take yi.
Yau tunda ya tashi yaƙi ma fita Aiki ba wadda yake son gani se Ammin sa kawai seya tashi yahau haɗa kayan su Seda ya haɗe kaf sannan yace wa farha.
Ta tashi su tafi kano ta kalle shi tare da cewa.
"Kamar yaya Kano kuma nidai gaskiya ba zan iya doguwar tafiya da wannan cikin ba"
A fusace ya kalleta.
"In ba zaki tafi ba seki zauna Ni mahaifiyata nasan tana buƙatata a wannan Lokacin Jin Garin nan nake kamar wuta"
Dama addu'a ai bata faɗuwa ƙasa yadda ƴan uwanshi da Mahaifiyar shi suke addu'a Allah ya juyo da hankalin shi gida ne yasa yaji kadunan tai masa zafi.
Farha taji takaicin wannan magana daya yaɓa mata wato ya mayar da ita sakarai.
"Nima ƴan uwana da mahaifana suna buƙatar ganina dan haka kona koma kano ba zan zauna Kamar da ba wallahi a wannan karon Sedai ai wadda za'ai Koka sake ni Koka Sama min Gidan da zanzauna cikin ƴan cina dan ba zan Kuma Irin zaman danai a baya ba na gaji ni ma ƴace kamar Kowa kuma mace kamar kowa"
Bai kula taba dan ya fuskanci a sama take ya saɓi kayan a kafaɗar shi Suka fita dan jaraba ko wanka babu wanda yayi acikin su daga Inno har su shafa basu Ji daɗin wannan tafiya ba dan Inno harda Kukan ta Aliyu yace su kwashe kayan abincin da komai da suka rage Kuma ze waiwaye su komin Bajima komin ba daɗe haka Suka rabu duk babu daɗi dama bahaushe yace sabo turken wawa suna zuwa tasha suka sami Motar kano Haka suka shiga ya biya Kuɗin Mota tafiya sukai har zuwa garin kano gaba ɗaya ƙafafun farha sun Kumbura Duk ciwo suke mata Har suka sauka Da ƙyar take taka ƙafafun Napep ya samu sukai tsada zuwa gida bayan ya zuba musu kayan su acikin napep ɗin farha ta Tsaya taƙi shiga napep Ɗin a wahalce ya juyo ya kalleta sabida Shima ba ƙaramar gajiya yayi ba.
"Fatima muje mana"
Ta juya fuskarta wadda ta haɗe ta tamau tace.
"Ni gidanmu zani danni ma mahaifana suna Buƙatar ganina Rabon umma dani Har wata nawa dan haka kowa yayi Gidan su kafin asan abin yi dan ba zan ƙara zaman rashin ƴan ciba wallahi in ada nayi haƙuri yanzu ba zan iya ba"
Ta faɗa da iyakacin gaskiyarta.
"To shikenan Indai ni nake riƙe da igiyoyin auren ki ban amince Kije gidan kuba In kuma kika je keda Allah ai seki bari muje Gidan Ammin tukunna kiga wace irin karɓa zasu yi Miki kafin ki Ɗauki mataki Kuma ke ai sheda ce tunda can ban yarda an taka mutuncin kiba"
Kuka tasa tana cewa.
"Dan kawai kana aure na seka haɗa ni da Allah bayan kasan tsoron sa ze hanani tafiya gidanmu nidai na cuci kaina dana zaɓi auren ka"
Murmushin takaici yayi bai iya magana ba Ya shiga napep Ɗin haka ta shigo itama tana ta Kuka ya sassauta Muryar shi.
"Dan Allah fatima ki shuru kinga a condition ɗin da kike ki rufa mana asiri ki haihu lafiya"
Da ire iren maganganun nan yayta kwantar mata da hankalinta har ya samu ta dena Kukan se ajiyar zuciya ya kama hannunta ya riƙe tare da cewa.
"Inna Cutar dake Allah baze barni ba haka zalika inna juya Miki baya Na zama butulu fatima ba irin wannan zuwan nake so kiyi wa mahaifan kiba Duba duk kin rame Kinyi duhu kowa ya ganki yasan bakya cikin kwanciyar hankali Na fison ki zuwan da kowa ze sha'awarki mahaifan ki suyi alfahari da aurena da kikai dan Allah ki Nutsu mubi komai a sannu"
Ko kula shi ma tayi banza tai masa dan zafin Ammi take Ji sosai dan se yanzu ma take ƙara tuno Cin mutuncin data sha wajan Ammi a zamanta.
Har Bakin gate mai napep ɗin ya dire su Ya sallame shi ya shiga sauko Musu da kayan su Hohoho Masu gadi Ma'aikatan gida Ihu suka sa suna Wa Aliyu barka da zuwa dan basu da labarin Dalilin tafiyar shi sudai sun san sunyi Missing Uban gida nagari mai tausayi da Jinƙai Kayan nasu Suka amsa suka Nufi Cikin Gida gaba ɗaya Falon Ammi cike yake sabida yadda Jikin nata yau se a hankali ganin ana shigo da kaya yasa Bashir daya zo Shima daga abuja yake tambayar su na menene kafin ya rufe bakin sa Aliyu ya turo Ƙofar falon hannunshi Riƙe dana farha wadda da ƙyar take taka ƙafafunta.

Ai Ammi dake kwance kanta yana saman Pillow tana hango Aliyu ta miƙe a guje ta Nufesu su dukan ta haɗe ta rungume seta fashe da kuka tana cewa.
"Baba ina ka shiga baba da tuni na Mutu baka tare dani nayi nadamar abin da nai Muku fatima ki yafe Mini na tuba"
Seta hau kuka wanda duk dauriyar Aliyu shima kukan ya saka farha ma Kukan take seda ƙyar aka rarrashe su Suka ƙaraso falon Hannun Ammi cikin na Aliyu yau ciwo ya ƙare Su sadiƙ se farin Ciki Shikam Aliyu Yana ta kallon ammi duk ta rame tai duhu Se sannu take wa farha kamar zata mayar da farha cikinta wanda nan da nan tausayin Ammin ya rufe farha nan fa aka shiga mayar da zancen abin da ya faru bayan basa nan Cutar Ammi ta ɗagawa Aliyu hankali se kallonta yake Yafiyar farha Ammi ta nema wadda tace ba Komai ai ita mahaifiyace a wajan ta sabida haka Komai ya wuce Har dare falon yana cike shidai Aliyu zamewa yayi ya tafi yayi wanka bai shigo ba se wajan taran dare Lokacin mutane sun ragu kowa ya kama gabansa farha tana can gadon Ammi tana baccin gajiya bayan tai wanka an bata sabbin kaya ta sanya.
Ammi da kanta ta haɗawa Aliyu abinci ranar ciwo ya ƙare seda ya gama cin abincin sannan take sheda masa mami bata nan mahaifiyarta tazo ta tafi da ita sedai in ya huta yaje ya dawo da ita.
Aliyu yayi Murmushin takaici.
"Ammi kawai mami tai zamanta Na sake ta saki Biyu dan na kama mami da tarin laifuka kafin nabar Gidannan kona zauna da ita ma akwai zargi Sabida dumu dumu na kama ta da laifin Yunƙurin kasheki ta hanyar zuba Miki magani agirki Kuma ban tabbatar ba seda na kamata da manyan Hujjoji wanda ni ban san dalilin ƙudirin hakan gare taba"
Ammi ta share hawaye nan take gaya masa Dukkan abun da ya faru wanda tajira tazo tai mata agida Tsaki yaja yana Allah wadai da wasu mutanan to mai wani ya isa yayi maka In ba Allah ba.
Ya jima suna hira da Ammi wanda washe gari yacewa Ammi ta shirya suje har gidansu mami ya miƙa mata takardar sakin nata tare da bayyana dalilin sa na sakin a gaban mahaifiyarta Sedai koda suka je Gidan su mami yadda suka ga tajira abin babu daɗi se ɗagawa Ammi hannu take amman ba damar Neman yafiyarta.
Mami ta bawa Ammi tausayi dama shi Aliyu tunda ya bata takardar ta ya bayyana mata laifukan ta wanda bata Musa ba ta saka Kuka tana neman yafiyar shi yace ya yafe mata Allah ya yafe masu gaba ɗaya ya fita Ko kallon ɗakin da tajira take beyi ba Ammi da tunanin tajira ta dawo Gida seta ƙara Jin tsoron Allah lallai Mutum ba abakin Komai yake ba.

Kuma a ranar Sadiƙ ya gabatarwa Aliyu riba da ci gaban da kamfanin nikan shi suka samu bayan baya nan Aliyu kuma bai ƙasa a gwiwa ba wajan tara ƴan uwan shi a wannan rana ya sheda cewa ya mallakawa Sadiƙ kamfanin shi na Lagos halak har abada ya mallakawa Bashir kamfanin shi na Abuja har abada shi Kuma ze mayar da hankali ana kano da wanda ze Buɗe a garin kaduna dan mutan kaduna sun zame masa dangi Ranar Ammi tai Kukan daɗi sadiƙ Kuwa yama kasa magana haka Bashir bayan gama Murna Aliyu ya kuma yiwa Bashir albishir da yaje ya Nemi auren Hanan ƴar Gidan Alhaji hamishi wadda yace se a haɗe dana Safna Bashir yayi Godiya sosai haka taron ƴan uwan ya tashi Cikin farin ciki.
Wata irin kulawa Ammi take bawa farha tun farha na jin kunyar Ammi har ta ware ta mayarta kamar umma dan shagwaɓa take zubawa Ammi wadda Komai tace Aliyu ya sauya na ɓangaran shi in farha ta haihu seta tare acan dan haka sabbin gyara aka soma yiwa part Ɗin Aliyu Daidai da sutturar farha ammi ta bawa masu aiki sabbin kaya aka ɗinka mata akwati akwati masu kyau da tsada Su safna Sun Haɗe kai da farha sun koma ƴan ukun Ammi.

Musa daya zo Aliyu ya karɓi wayar shi ya kunna tarin saƙonni Yayta bi Haka yaje Gidan gwamna ya sheda ya dawo dan sadiƙ ya gaya masa sunje Sun bada Uzirin yayi tafiya har gidan su farha seda yaje anan Su kawu sukai ta masa Godiya da mamaki ya kalli Musa bayan sun fito yake tambayar shi bayan baya nan ana aika masu da saƙo ne Musa yace Shiya

Please Login or Register in order to submit comment