Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunani har ka takani baka sani ba kuma dai gashi ras kake"
Aliyu ya juyo tare da cewa.
"Lafiya lau Alhamdulillahi Amman kai haƙuri"
"Dan girman Allah ka gaya min Ni naji ajikina kana da damuwa Kuma musulmi ɗan uwan Musulmi ne duk da akwai nagari akwai mugu"
Cewar Mutumin.

"To ni baƙo ne ina zaune a sabon garin rigasa na fito neman abin yi"
Dariya Mutumin yayi.
"Ban yarda ba ranka ya daɗe sabida bakai kama da kalar wahala ba"
Aliyu yaɗan ware ido

"Dama wahala akwai kalar ta Tab"
Mutumin yace.
"To koma dai da wasa kake Ni sunana Dini ina zaune a hayin rigasa Kaga waccan titin Ƙaton ginin da kake gani To tsohuwar tasha ce da aka dena Lodi da ita To se Muka mayar da wajan Gareji ana gyaran motoci sannan ana sauke ƙarfen gyaran Mota wanda Kullum Mota sama da ashirin na kawo ƙarfen daga lagos Indai zakai aikin sauke ƙarfan zan maka hanya duk da basa buƙatar ma'aikata Ni bakani ke ne gyaran Mota nake aciki Muna mutunci da masu kawo ƙarafan"
Aliyu yace.
"Da gaske malam Dini?"
Dini yayi dariya.
"In sha Allah ta yuwu inna taimake ka nima Allah yayi min abin da zato bai taɓa zato ba"
Aliyu ya cika da mamaki.
Jerawa sukai da Dini bayan Dini ya karɓo abincin daya siyo ƙaton gareji ne sosai Mutane nata kaiwa da kawowa Suka shiga wajan Ogan wanda Dini ya gabatar da Aliyu abin mamaki Ogan da Mutunci ya karɓi Aliyu dan har suna wasa da Juna yace masa aikin daga ƙarfe Bakwai na safe ne zuwa shiddan yamma kullum za'a baka Dubu Goma sannan Kuma kawai dan yaga Aliyu ne yaji yana ƙaunar shi amman ba da ban haka bama sun rufe ɗaukar ma'aikata akwai riga da wando masu tambari da sunan wajan ya ɗauko ya bawa Ali yace dasu ze ke zuwa.
Aliyu yaji komai kamar a mafarki yayita Godiya lallai Duniya babu tabbas yau Shine da aka ce za'a ke bawa dubu Goma yaji kamar an saka shi acikin aljanna wanda shi kafin faruwar hakan yana iya bawa Mutum kyautar Da se Mutum ya gigice da ita ma'aikatan sa nawa ne suke cin abinci a ƙasan sa

Bayan sun Rabu da ogan Godiya yayi tayiwa Dini har Dini yace godiyar ta isa haka Kayan a hannun shi ya tawo Gida gaba ɗaya mamaki da al'ajabin wannan alkairi daya haɗu dashi ya sanyaya masa Jikin sa

Kayan kawai ya aje ya fita masallacin sallar la'asar sabida Lokacin daya zo farha bata ɗakin Bayan  ya dawo ya tarar da ita ta shigo.
Se ɗaga kayan daya zube a saman katifa take tana kallo.
Bayan yayi mata sallama yace.
"Ina kika shiga nazo bakya ɗaki Nifa bani son yawo"
Tayi Murmushi.
"Naje kaiwa Inno Shinkafar dana dafa mata ne tana ta Godiya"
Ya nemi guri ya zauna.
"Wannan kayan fa na Menene?"
Cewar farha cikin sigar tambayar shi........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE 101*
kwanciya yayi a saman katifa ya tallafe kanshi da hannunshi yana kallon rufin ɗakin.
"Kana jina ina maka magana kai Min shuru shikenan"
Ta faɗa cikin rashin Jin daɗin yadda yake yi mata shuru wani bin idan tana yi masa magana.

"Fatimah nifa wani lokacin bana son yawan magana kaina har ciwo yake min in ana magana sosai Ki haƙuri Har na huta" ya faɗa a hankali Tashi tayi zata fita daga ɗakin ya Damƙo mata hannunta, "Ni ka cikani mai zan yi maka bayan na dameka da surutu"
Ta faɗa hawaye na zubo mata daga cikin idanunta.

"Subuhannallahi Why are you crying? Fatima, after I was with you, stop crying. I don't want you to be quiet" ya faɗa yana sa tafin hannunshi yana cire mata hawayen nata Kukan take sosai "Tausayin kaina nake" ta faɗa cikin kuka da sauri kuma a ruɗe yace "Kamar yaya tausayin kanki wani abun ke damun ki?" ta girgiza kanta "Idan banyi hira dakai ba da wa zanyi daga maka magana kace kanka na ciwo in ana magana" ta faɗa muryarta na shaƙewa ya marairaice tare da cewa "Bazan kuma faɗin haka ba Me kike so nace yanzu?" ta kalle shi da gaske yake gaya mata maganar Shi haka halittar shi take Mutum ne marar yawan son magana.

Ta ɗan matsa daga kusa dashi.
"A,a shikenan kawai a bar maganar" Yace "Fushi kikai dani ba kyau Saurin fushi" "Niba fushi nake dakai ba to mai kayi min"
Ya gyara zaman shi "Fita nayi Neman abun yi kinga kina da Juna biyu Dole akwai abubuwan Buƙata ga asibiti da zaki fara zuwa ina son In kaiki ganin Likita dan a duba Lafiyar Babynmu Kinsan abin da ya bani mamaki?" ta girgiza kai tana tsira masa idanunta.
Labarin dukkan yadda sukai da Dini da kuma Ogan tashar Ya bata ya ƙare da cewa "Gaskiya abin ya bani mamaki yadda Komai yake zuwa mana cikin sauƙi haka ɗan sauyin rayuwar Da muka samu kaɗan Ne"
Farha tayi Murmushi tace.
"Ai tunda ka ji ƙan Al'umma kai ma Allah zeji ƙanka sannan kuma Ka saka ɗumbin Mutane a farin ciki Ko kasan Allah yana son bawa ya saka bayin sa a farin ciki Ni dama naji ajikina Allah baze tozarta kaba"
Ya zuba mata ido.
"Allah yasa mudace"
Ya faɗa yana tashi lokacin ana kiran sallar magariba.
Ya shiga tattare hannun rigar shi.
"Bari nayi alwala"
Ta tashi da sauri ta ɗauki Buta ta cika masa da ruwa sannan ta komo ɗaki ta Ɗebi gishiri ta shiga bayin ta barbaɗa ta kora ruwa sannan takai masa Butar bayin

Ta dawo lokacin ze fito daga ɗakin.
"Na kai maka Butar Bayin"
"Nagode" ya faɗa yana fita daga ɗakin Ya Shiga bayin yayi abin da zeyi ya Nufi masallaci Da gaske bamai son maganar bane ta Lura haka yanayin sa yake se Dole yake mata magana doguwa.
Bayan tayo alwala tai sallah tayi azkar sabuwar Fitilar Batir daya zo da ita ɗazu Cikin kaya ta Buɗe ta kunna Ta fita waje da gas Ruwan Shayi ta ɗora masa tasan baya cin abincin mai nauyi da daddare kamar yadda yace mata Sauran indomie ɗin ɗazu Kuma ta ɗumama farar sauran Shinkafar data dafawa Inno ta ɗumama taci da ƙyar ta Kammala Komai ta shiga ɗaki Tayi sallar Isha'i bayan sallar Isha ya dawo tai masa sannu ta gabatar masa da tea ɗin da sauran Indomie Ɗin Tea ɗin ma kawai yasha yace ya Ƙoshi Fita tayi ɗakin shafa ta Miƙa mata Indomie tace ta bawa yara shafa taita Godiya har Mijin shafar ma seda ya Leƙo yace angode farha ta juya ɗaki Lokacin harya Cire kayan shi ma daga shi se Singlet da Gajeran wando yana kwance Ya lumshe idanun shi amman ba bacci yake ba Rage kayanta tayi itama ta raɓa Gefen shi Nan da nan bacci ya ɗebe su naji ya wanda basu sami damar yin shiba.

*KANO*

"Nidai ranka ya daɗe so nake ka bani ɗaurin bakin Mijina sabida dukkan abin da nake dan shi nake dan ya sami ƴan cin kanshi amman sam bai gano ba sannan Shi ma ƙanin Mijin nawa Ina son ai Masa Haɗaɗɗiyar Mallaka wadda zeji kaf Duniya ba wadda yake so sama da Jamila ta, Kaga in ya aure ta Dukkan Komai nashi ya dawo ƙasan Mu Inda hali shima a ɗaure masa bakin sa"
Sakina Kenan Gurfane a gaban tsohon Bokan ta wanda ta yarda shi bayan ta sami sabo wanda take waya dashi rannan da daddare ganin aikin sa bai mata yadda take soba yasa yau ta dawo wajan tsohonta nada wanda ta taɓa zuwa wajan sa amman bai taɓa mata aiki ba ta sauya waje se yau suka dawo ita da jamilar ta.

Ya janyo madubi ya zuba ƙasa akai ya fara zanawa yana bajewa.
"Mijin ki ze mallaku Zan baki baƙar laya wadda zaki sami sabuwar gawa wadda ba'ajima da Binnewa ba ki cusa a bakin ta yadda wannan gawa ta Mutu haka bakin sa ze Mutu Se yadda kikai dashi"
Ya ƙara baje wata ƙasar kana yace.
"Bana ganin Komai a tare da ƙanin Mijinki se haske Kwata kwata taurarin sa basa kawo bayani se haske kawai Gaskiya aikin sa yafi ƙarfina Ke Bama zan Ɓoye Miki ba Duk wanda yace Miki ze iya yi Miki aiki akan shi ƙarya yake Kuɗin ki kawai zeci bawai asiri bane baya kama shi a,a Wani irin Murɗaɗɗan Mutum ne mai taurin kai da kafiya uwa uba addini ya ratsa shi Da wuya aiki ya Huda shi nan Kusa A lissafin masana taurari ma za'a iya kai wa shekara hamsin ana masa asiri amman bai huda Jikin sa ba wannan shine gaskiyar Bincike na amman In kina Musu Kije wajan wani ki tambaya"
Sakina ta share zufa tare da cewa

"Ranka ya daɗe Nafi shekara biyar ina aiki akan sa da matar shi"
Da sauri ya ɗaga mata hannu yana zana ƙasar sa.
"Kin san kaf Bincike babu wanda yakai na ƙasa gani! To wallahi waɗanda kika kaiwa Kuɗin ki akan shi sun cuce ki dan babu wani abu naki a tare da wannan Mutumin matar shi Kuma ɓarewar Cikin Jikinta ya samo nasaba ne da yawan Bin malamai ita ma da suke Yi bata sani ba sheɗanun da suke turawa surukarta akan suyi aiki akanta sune suke Shiga Jikinta suna lalata mata Cikin da take samu yanzu haka mahaifarta ta fara saki In batai wasa ba ma Zata iya samun matsala"
Sakina tai wata zabura tare da gyara zama sosai
"Ban gane ba kai min yadda zan fahimta?"
Yace mata "Bani sunan matar Ƙanin Mijin naki" sakina ta gaya masa ya Cigaba da zana ƙasa yana gogewa har yakai Minti ashirin a haka.
Sannan yace.
"Na bincike ta tas Itama ai ba don Allah ta auri ƙanin mijin naki ba, mahaifiyarta bata ƙaunar surukarku sabida manufar ma ta tarwatsa farin cikin surukarku ta shiga ta fita ta haɗa auren ƴarta da ƙanin Mijinki Kullum faɗi tashin su akan Su kawar da surukarku suke sabida ana musu bincike ana gaya musu surukarku Ke Ɓarar da cikin ƴarta to basu sani ba sheɗanun da suke aiki dasu sune In suka raɓi Surukarku da ƙanin Mijinki In basu sami nasara ba sabida tsarkin dake tare da surukarku da ƙanin Mijinki to sesu Huce takaicin su ajikin ita matar ƙanin Mijin naki wadda a ƙasan mararta suke dira su lalata ɗan tayin Cikin Jikinta su sakar mata Jini ana ta aikin banza a asibiti ne amman ga ainihin inda matsalar take tattare yanzu haka mahaifarta ta fara gajiya ko wani lokaci zata iya fuskantar matsala"
Sakina tai Huci tare da cewa.
"Lallai dara taci Gida wato aljanun da suke aiki dasu don su Shiga Jikin Aliyu Ko Ammi in an turo su Jikin su Ammin basu sami Ƙofar shiga ba sabida tsarkin dasu ammin ke tare dashi wato se su Huce ajikin Mami su ɓarar da Cikinta su lalata shi kenan?"
Ya jinjina kai.
"Kinsan aisu sheɗanu haka suke sam basu da gwani zafin takaicin Raɓar da sukai Jiki mai tsarki Ƙonewar da sukai Shine suke Huce haushin ajikin Ita yarinyar"

"To sun jima suna Aiki da Sheɗanun Kenan?" cewar sakina.
"Ita dai surukarki tun farkon auren ne da suka Neme ta asirin ya Huda ta amman yanzu kam jikinta akwai tsarin addu'a duk abin da suke baya tasiri gaskiya Kuma ita a yanzu ma abin da yasa bata son ɗan nata yayi aure sabida sharrin matan zamanin nan ba don wata manufa ba sedai ana zaton wuta a maƙera seta Koma masaƙa labarin tane ya faɗo nan"
Ya faɗa yana dariya.

Sakina ta tsorata dasu mami ashe suma a tafe suke.
"To ni yanzu kace Ba abin da ze tasiri a jikin ƙanin Mijina to meye amfanin na ɗaure bakin Mijina kuma yaya batun auren shi da jamila?"
Ya cigaba da binciken sa.
ya ɗago tare da cewa.
"Idan kika ɗaure bakin Mijinki zaki sami Haɗin kanshi ta yadda zaki tarwatsa Komai na ƙanin Mijin naki sabida Ƙanin nashi ya bashi yarda sosai Mijin ne ze zama garkuwarki Duk dukiyar ƙanin Mijin taki dake wajan Mijin ki seku tattare ku hana shi In ma kika ɗaure bakin Mijin baki da buƙatar auren ƙanin Mijin naki da ƙanwarki Sakina nasan ki Muguwa ce Ke ita ƙanwar taki ai ba don Allah kike son ta auri ƙanin Mijin naki ba dan dai kawai Ta samo Muku dukiya ne" da sauri sakina tai masa Inkiya da hannunta murya can ƙasa tace "Rufa Min asiri ta tashi ta fita tana waya kar taji abin da kake faɗa ka ɓatan aiki"

Yayi Murmushi.
"To mubar batun auren su mu gama da wannan ɗaurin bakin"
Ta langwaɓar dakai..
"To yanzu ina zan sami gawa?"
Yayi dariya.
"Gaskiya da wannan don yanzu yawanci maƙabartu an saka Masu gadi sabida Irinku masu sakawa gawa laya da Kuma masu yankar sassan Jikin gawa shiyasa aka saka tsaro sosai"
Sakina tai jimmm.
"To ko biya zanyi a saka"
Ya girgiza kai "Gaskiya wannan aikin naki ne ba'a buƙatar hannun kowa"
Sakina tai Murmushi.
"Akan biyan buƙatata ba abin da ba zan iya yiba Sabida haka Nina san yadda zanyi Duk yadda zanyi danna sami gawa zanyi" adaidai nan kuma jamila ta gama wayar ta shigo ɗakin Lokacin sakina ta ɗauki jakarta ta Buɗe ta zuba masa Kuɗi a gaban shi sukai sallama suka yo Gida A gidan su suka kwana sabida dare yayi washe gari sakina ta sako yaranta gaba suka dawo gidan Ammi tun daga falon farko ta gano gidan babu lafiya jakarta ta aje tare da nufar ɗakin Ammi sabida Ko ina na gidan tsit hatta Kayan kallo suna kashe sallama tayi ta shiga ɗakin a hankali Ammi ta miƙe daga kwanciyar da tayi tana amsawa sakina sallamar tata.
Cikin ladabi sakina take gaishe da Ammi ta karyar da kanta tana cewa.
"Ammi waya ce ta gigita aka Min Jiya maman mu bata da lafiya, Shine Muka tafi ko sallama bamu yi Muku ba"
Ammi tace.
"Allah ya bata lafiya jikin girma ne se a hankali ai"
Shuru ɗakin yayi Lokacin sadiƙ ya shigo Cikin shirin fita kamfanin Aliyu dan ya gudanar da abin da ze dan cikin satinan yake son su wuce lagos sabida ya mayar da hankalin sa kan Kula da kamfanin Aliyu nacan.
Sadiƙ ya kalli Ammi cikin kulawa.
"Ammi har yanzu baki break fast ba dan Allah Ki barwa Allah Komai In sha Allahu Yana cikin Ƙoshin lafiya"
Kamar jira Ammi take seta fashe da kuka.
"Sadiƙ ta yaya hankalina ze kwanta tun Jiya nake Kiran Numbobin baba duka a kashe"
Sadiƙ yace.
"Kema ammi kina da maido da magana baya kin manta ya bawa Musa wayar tashi"
Ta share hawayenta "Ba Numbobin nasa da yawa ba ai wayar shi ba ɗaya bace ya Allah kasa Babana yana cikin Ƙoshin lafiya"
Sadiƙ ya kwantar da Murya yana bawa Ammi haƙuri har dai ta dena Kukan.
"Abban su baka ganni bane?"
Cewar sakina sadiƙ bai Ko dubi Inda take ba yasa kai zebar ɗakin

"Sadiƙ dawo Mahaifiyarta ce babu lafiya shine ta fita bata gaya maka ba kai mata alfarma mahaifi ya wuce wasa"
Cewar Ammi dan ita yanzu bata son ɓacin ran kowa tsoron Tafiyar Aliyu ma kaɗai bala'i ne a gareta.
Sadiƙ ya dawo jikinsa a sanyaye Jin Abin da Ammin sa tace masa Ya kalli sakina tare da ce mata..........
Autar manya ce marubuciyar......
*ƁOYAYYAR ƘAUNA*
*BA SON TA NAKE BA*
*ƊAN MAJALISSA*
*MURADIN ZUCIYA*
*ASHE ZUMA*
*TAURARO*
*KOBA SO*
*RABON WANI*
*FITAR RABO*
*DA IZZATA*
*BAƘON LAMARI*
*AUREN BARE*
*H A S K E*
*ZUMA A BAKI*
*BAƘAR FATA*
*RABO YA RANTSE*

*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 102*
"Kodan gaba bana son ki ƙara fita baki gaya min ba wannan ai Ba daidai bane"
Ya faɗa cikin nutsuwa sakina tayi ƙasa da kanta tare da ce masa.
"In sha Allahu......"
Ɗakin Ammi yayi shuru na wani Lokaci kafin sadiƙ ya yiwa Ammi sallama ya tashi ya fita sakina ta miƙe tabi bayan shi ya juyo ya kalleta.
"Yaya jikin Maman Inna tashi da wuri zan biya Mu gaisa na duba ta"
Sakina tayi saurin cewa
"A,a bama se kaje ba sabida Sun koma asibiti tun ɗazu ita da jamila"
Sadiƙ yace.
"Okay to Allah ya bata lafiya Inna dawo Ko zuwa dare se Muje dake Ina su Minal?"
Tace.
"Suna ɗaki suna Break fast ko a kira su?" ya girgiza kai har bakin Ƙofa ta raka shi Ya kama hanyar Office.......

*Mami*
Tunda tabar falon Ammi ta koma part Ɗinsu take faman safa da marwa kamar wata zararriya seta zube a ƙasan carpet tana rusa Kuka!
"Wannan wace irin baƙar rana ce tazo Mini na shiga Uku yanzu ashe duk yadda naso wannan yarinyar Kishiya tace Duk yadda na jata ajikina Kishiyata Ce Aliyu me yasa kayi Mini haka me yasa kayi Min bazata Ko a fuska baka taɓa nuna Min kana da alaƙa da wannan yarinyar ba?"...........
A haukace ta miƙe ta ɗauko wayarta ta shiga Neman layin Hajiya tajira mahaifiyarta idanunta a rufe suke Bata Ji bata gani haka taita Kiran Number Mahaifiyar tata.
"Mami wannan Kira haka na lafiya ne yaya akai?"
Cewar Hajiya tajira wadda daga ɓarin ta tana zaune ne tana Cin Abinci.
"Mama babu lafiya mama bokayen Mu maƙaryata ne mama duba ƙarya ne ba gaskiya ba Mama babu Mai sanin abun da ze faru yau ko gobe se Ubangiji mama wannan abun yasa naji na tsani Bokaye da duk ma mai binsu.......
"Dakata mami Ki fara sanin da wa kike yin magana Ki Nutsu kafin ranki ya ɓaci Farko tunda Kin tsani mai bin bokaye har dani Kenan da kanki dan ba da ban aikin bokayen ba da baki kai matakin zama matar Ali ba"
Mami ta share majina tare da cewa.
"Dama can Allah ya ƙaddara ni matar shice ba mahalukin daya isa ya hana Ko ya saka Mune dai idanunmu suka rufe Muke zaton aikin Bokaye ne yasa Aurena da Ali ya tabbata"
"Dakata mami Ni zaki wa butulci Nida naci kashi da Fitsarin Ki......
"Mama ba zan taɓa yi Miki Butulci ba ke mahaifiyata ce amman mama ina Roƙonki da cewa dan girman Allah daga yau Mu rabu da biye biye don ƙarshen alewa ƙasa! bakin alƙalami kuma ya riga ya Bushe Bokayen mu basu gano mana faruwar Auren Aliyu ba domin zancen da nake Miki tsayin watanni Uku Aliyu yayi auren shi da matar shi Muke zaune har tana da Cikin watanni Uku daga ni har Ammi da mutan Gida bamu san da wannan aure ba ashe Ammin da Muke zargin da hannunta a matsalar da cikina yake samu har Bokan da Muka je yana tabbatar mana yana bamu maganin kawar da ita ashe Ita ke faman yin faɗi tashi akan Aliyu kada ya ƙaran Kishiya wannan dalilin Ne ma yasa ya Ɓoye mata auren Shi sabida haka iya wannan kaɗai Mama ya dace Mu kama kammu Mu gane In Allah ya baka babu mai hanaka in Allah ya hanaka babu mai baka Kinga Munje wajan maƙaryata suna Cutar damu suna karɓar Kuɗin Mu abanza suna haɗa mu da makusantan mu.......
"Ke dallah gafara can Marar hankali se soki Burutsu Kike Min kin kasa fahimtar dani takai maimai ɗin abin da yake faruwa?"
Mami a nutse take gayawa mamanta dukkan abun da ya faru.
Tajira cilli tai da plate Ɗin abincin wanda har ya fashe a ƙafarta Jini ya ɓalle amman bata damu ba seta hau ashar! tana cewa.
"Na rantse da Allah da wanda ya haɗa auren da shi mai auren da ita yarinyar da ita Aminar gaba ɗaya Sena ɓatar dasu aduniya harni za'a kawowa maganar banza harni Amina zata rainawa hankali Kece yarinya ƙarama To bari Kiji Kitimurmura ce Ba wani tasan da batun auren nashi dani suke magana ki haɗa kayan ki da safe zanzo Mu tafi gida daga nan Kuma dole Na koma wajan Bokan daya haɗa auren Ki dana Ali shine kaɗai ze Min yadda nake so dan na nijar Ɗinnan na Kasa gane kan aikin shi sabida yadda gaba ɗaya naga Komai bai tafi yadda nake soba"
Bata jira cewar mami ba ta katse wayar.
Daran ranar mami batai bacci ba Komai ya tsaya mata cak ta kasa tunanin Komai akan wannan lamari sedai kaso goma na cikin Zuciyarta yafi gasgata cewar Duk abin da Bokaye da ƴan Tsubbu suke faɗi ƙarya ne ba mai yi se Allah ba mai hanawa se Allah da asubahi ta samu bacci ya kwashe ta wajan tara da wani abu Bugun Ƙofar mahaifiyarta ne ya tashe ta
Ta miƙe taje ta Buɗe mata Ƙofar falon ba ta tsaya jiran Gaisuwar mami ba ta tattare mata kayanta iya waɗanda zasu ci manyan akwatunan da suka Fito dasu Suka kama hanyar waje suna tafe Tajira tana tijara har zuwa sashin Ammi wadda suka tarar a ɗaki dan sadiƙ bai Jima da fita ba suka shigo a tsaye tajira ta tsaya ta kama Ƙugu tana cewa.
"To tsuhuwar Munafuka Ni zaki yaudara Kici amanar zumunta ashe aure kika wa Aliyu amman zaki wayance da Borin Kunyar banza wai bakya son ya ƙaro aure Gudun shu'uman cin matan zamani munafuka to ƙarya Kike da hannun ki a auren Aliyu har barin gidan da yayi da saka hannun ki"
Ammi ta ɗago a ɗimauce tare da cewa.
"Ki fahimce ni Yaya tajira wallahi bana da sa hannu akan Komai Yadda kowa yaji maganar auren shi Nima haka naji ki barni da tashin hankalin ɓatan yarona kaɗai ya isheni"
Tajira tai wata girgiza tare da cewa.
"Ai sha Allahu ya tafi kenan Kuma yadda kika tarwatsa min shirina kema ki kwana da shirin kinyi bankwana da farin cikin ki matsiyaciya Munafuka"
Mami ta saka kuka tana cewa

"Haba mama haba mama ammi bata da laifi akan hakan Please karki abin da zakiji Kunyar shi gaba"
Seta juyo wajan mami.
"Dama batun yau nasan tasono na haifo ba kekam Baki gadoni ba To shikenan duk abin da nake dan wa nakeyi Tunda kin zaɓi amina dani gata ga kinan Ku zauna"
Mami cikin kuka tace.
"Ba haka bane mama Yanzu Lokacin gyara kura kurai ne ba Lokacin wani abu ba rayuwar bata da faɗin da zamu ce se Munga komai daidai in ada munyi ba daidai ba yanzu akwai damar gyara"
Tajira ta juyo.
"In kika ƙara cewa tak Allah ya isa.......
Mami taja bakin ta tai shuru Ammi tace.
"Mami Allah yayi Miki albarka kuma Allah yana son bawan daze laifi yazo yayi nadama ya tuba duk da ban san mai Kukai ba amman Kije Ki tuba akwai ragowar damarki sannan Kibi mahaifiyarki Ku rabu lafiya daman Allah yana sako rayayye acikin matacce ya sako matacce acikin rayayye ba tun yau nasan Wasu abubuwan tirsasaki mahaifiyarki take akan yin su ba, kamar nice da Aliyu da dama wasu abubuwan danni yake Yinsu dan ya gama dani lafiya daga ciki harda auren ki Aliyu bai taɓa son ki ba sanadin biyayyar uwa yasa yake zaune dake amman mahaifiyarki bata ga haka ba nina sadaukar da farin cikin ɗana danna Ƙara ɗanƙon zumuncin mu Allah yana kallo wallahi banda gudun sharrin matan zamani babu wata manufar Ɓoye data sa na hana Aliyu ƙarin aure sedai kash yaya tajira Kin bani mamaki yau se gashi akan abun da duk ya shafe mu Kinzo kina Kumfar baki kina aibatani Kina jawa yarona jafa'i lallai Ɓoyayyan Nufin ki akaina da zuri'ata ya bayyana Kuma kin saka min shakkar auren da kika nace akan se ɗana ya auri ƴarki tabbas akwai manufar hakan dan Inda Kina ƙaunata baza kice Aliyu yayi tafiyar da baze dawo ba, sannan Sekin tarwatsan farin cikina mai nayi Miki tajira in ba alkairi ba dama alkairi yana zama sharri? Allah ya sani bani da Mugun Nufi akan ƙara auren Aliyu se Gudun kada ya auro mana ɓata gari wanda nasan Inzan haɗiyi kur'ani sabida rantsuwa ba ko wa ze yarda ba wani ma cewa zeyi sabida naga matarshi bata haihuwa ne yasa na hana shi ƙarin aure gudun kada ya auro wadda zata haihu Ya sami ɗan kanshi yanzu ma haka daya bar Gida nasan Ko ita matar tashi Kusan tunanin hakan zatai aranta Ni kuma nasan Ko kaɗan bani da wannan manufar manufata ɗaya ce Kuma na faɗa Nasan mami ba juya bace Ko min daɗewa zata haihu tunda Allah yana bata cikin zama ne kawai bayayi Shiyasa duk sanda yazo Min da batun Ammi zan ƙara aure nakan ce masa Baba Ina gudun sharrin matan zamani kai haƙuri ka zauna da mami sabida kada ka auro ɓata gari wadda zata tarwatsa mana zumuncin Mu da zaman lafiyar mu mami kuwa Jinin kace In ma haihuwa kake so mami zata cika maka gida da yara To ashe gwara ma da Allah yake ƙaddara Dukkan Cikin

Please Login or Register in order to submit comment