Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ajikinsa.
"Mami tace Min baki da lafiya oya tell me meke damun ki Muji Jikin naki?"
Ya faɗa yana Buga mata Numfashinsa a saman Fuskarta Lumshe idanunta tayi lokacin dataji ɗumin tafin hannunshi a saman Cikinta yana wasa da tsakiyar Cibiyarta.................
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 93*

Jikinta ne ya hau rawa tana wani irin shige masa kamar mai jin sanyi zullewa take tana cusa kanta a cikin Ƙirjinsa a hankali ta riƙo hannun shi dake Cikin rigar tata.
Fuskarta ta ɗago wadda tai kalar tausayi kamar zata yi kuka! ta ce masa "Dan Allah ka dena" Cikin raɗa kuma a hankali yace "Sabida me bayan ni daɗin hakan nake ji" ya faɗa yana Ƙara shigar da hannunshi sosai Ya shiga Murza Ɗan tudun daya ji a ƙasan marartata Huci ta sauke tana kwanciya sosai a jikinsa wani irin wahalallan Numfashi take ja gaba ɗaya ya saukar mata da kasala ajikinta hannu tasa ta kamo fuskar shi ba zato yaji saukar danshin Bakinta a saman lips ɗinsa tana tsotsa a hankali ya Jinginar da kanshi a saman Pillow ya Lumshe idanunshi Ji yake dama zasu dawwa ma acikin wannan yanayi mai wuyar Misaltawa......

"Ammi ya kamata ki kwantar da hankalin ki Jikin Yaya Aliyu da sauƙi sosai dan yanzu haka ma Aunty mami tana tare dashi" cewar Bashir wanda yake tsugunne a gaban Ammi sadiƙ daya Fito cikin shirin tafiya asibitin sabida ya makara sakamakon Rashin baccin da bai samu a daran Jiya ba shine ya dubi Bashir wanda ke gaishe dashi Bayan ya amsawa Bashir ya kuma ce masa "A,a yaya na ganka agida Kuma shi Aliyun da wa ka bar shi ai da kayi min waya dana je in yaso kai seka tawo" Bashir yaɗan sosa kai tare da cewa "A,a Aunty mami taje har da kayan break fast ma shine nace ni bari nazo nai wanka sena koma" Sadiƙ ya zauna a kusa da Ammi yana gaishe ta kafin yace "Okay to yaya ƙarfin Jikin nashi?" bashir yace "Da sauƙi amman har na tawo be farka ba" Cikin wani irin yanayi ammi tace "To kuma shine zaka ce bazan je na ganshi ba wannan wani irin Bacci ne tun jiya har yau Mutum bai farka ba kaga in da wani abun da kake ɓoye Min gwara ka gaya min nasani ni Musulma ce kuma ba mutuwar da ban gani ba tunda naga ta uwata da ubana naga Ta mijina" Ammi ta faɗa tana share hawayen ta! Bashir ya soma rarrashinta "Wallahi Ammi ya sami sauƙi bacci ne kawai yake sabida allurar da akai masa mai ƙarfi ce haba Ammi in akwai wata matsala ai dana gaya Miki Kuma abin da yasa nace Miki ma ba zaki je ba sabida shima nan da Anjima za'a bashi sallama naga kuma kema ba lafiya ce dake ba Ki sha maganin ki kikwanta ki huta" Bashir ya faɗa cikin sigar rarrashin Ammi Sadiƙ ne ya saka baki Haka suka haɗu da ƙyar dai suka samu Ammi ta dena Kukan Amman ta kafe tace wallahi seta je asibitin Badan ran Sadiƙ Yaso ba yace ta shirya su tafi Su safna ma sun fito cikin shiri sadiƙ ya dubi Sajeeda tare da cewa.
"Ki leƙa kice wa maman Minal ta fito muje asibitin" Sajeeda ta amsa tare da Nufar ɗakin da sakina take Ciki sedai koda ta shiga babu kowa acikin ɗakin dawowa tayi tare da shaida masa cewar basa nan.
Sadiƙ cikin mamaki yace

"Fita sukai amman basu gayawa kowa ba Ko Ammi sun leƙo sun ce Miki zasu fita?" Ammi ta girgiza kai tana tashi ta shiga bedroom ɗinta dan ta kintsa sadiƙ wayar shi ya ɗauko ya shiga kiran Number ɗin sakina sedai koda ya Kira Number Ɗin Bata shiga yaja tsaki aranshi yana ayyana Rashin Mutuncin daze wa Sakina wannan wani irin iskanci ne ta fita ba tare da izinin shiba da ƙyar ya saita kanshi dan kada ƙannen shi su gano akwai wata matsala haka Ammi ta fito suka rufo part ɗin suka nufi compound a nan suka haɗu da Mami wadda ta fito da kayan Aliyu data zo ɗauka masa A babbar Mota suka tafi asibitin sabida ƙananun Motocin gidan ba zasu ɗauki yawan suba.


Gaba ɗaya hannayen shi suna zube a gadon bayanta ya riƙe ta gam ya sakar mata Jikinsa sabida yadda take Kissing ɗin nashi ji yake kamar Numfashin sa ze bar gangar Jikinsa A hankali ta zare harshen ta daga cikin bakin nashi tana sakin wani irin wahalallan Numfashi, Ƙoƙarin sauka take daga jikinsa wanda shi kuma yaƙi bata damar hakan idanunshi jajir Muryarshi ta dashe yace mata.
"Dan Allah kar kimin haka"
Ta ɗan tura bakin ta gaba kamar wata ƙaramar yarinya

"In wani yazo ya gammu fa kuma ma ai baka da lafiya" ya sa hannun shi ɗaya ya shafi gemun shi yama kasa magana gaba ɗaya Jikinsa ya saki Murya can ciki ya furta mata "Kullum ƙara sauyawa kike Ji nake in bamu kasance tare ba kamar zan rasa raina dan Allah fatima" ya faɗa yana wani taɓe baki kamar ƙaramin yaro.
Ita abin ma dariya yake bata se kace wani ƙaramin yaro.

"To ni me zanyi maka kalli fa ƙafarka Tana ciwo da kanka"
Janyo hannunta yayi tare da saka yatsanta guda ɗaya a cikin bakin shi yana tsotsa a hankali kwantar da kanta tayi a saman Ƙirjinshi ta Lumshe idanunta wani irin bacci ne yake kawo mata hari amman tasan nan ɗin ba wajan bacci bane A hankali taji takun takalman Mutane wani irin zullo tayi zata sauka daga saman gadon Ya wani janyota ya matseta kamar zatai masa kuka tace.
"Tawowa fa ake wallahi ga ƙarar takalman Mutane nan dan Allah ka sakeni kada ka min haka" Duk ta faɗa cikin tsoro.
"To ki sauka a hankali wannan dirar da zaki ai da matsala" bata saurare shiba tai saurin sauka ta Tafi can nesa da gadon nashi ta zauna sedai gamai hankali kallo ɗaya zakai mata kasan Bata da Nutsuwa Tana zama Kuma taji ana murɗa handle ɗin Ƙofar kafin hayaniyar su Ammi ta cika ɗakin dukkan su suka shigo kuma babu wanda ya kula da ita gaba ɗaya gadon suka nufa suna yi masa sannu Idanunshi a lumshe yake yana sakin Numfashi sabida idan ya buɗe idanun nashi tabbas za'a fuskanci yana cikin wani hali Cikin Jimami ammi take kallon shi.
"Baba kai mana magana mana kowa ya kasa bacci jiya sabida kai dan Allah kai min magana" ta faɗa muryarta tana rawa a hankali ya tashi ya jingina da pillow yaɗan kalli ammi Yana kama hannunta ya ƙaƙalo Murmushin dole "Ammi dafa sauƙi naji sauƙi" ya faɗa a hankali su safna suka shiga gaishe dashi sannan suka gaisa da sadiƙ Mami tace masa "Ga kayan na ɗauko maka kayi break ɗin Kuwa?" ya jinjin mata kai dukkan su zama sukai sedai sun rage hayaniya sabida shi A hankali Ammi ta jefa idanunta kan farha wadda taji kamar ta saki fitsari dan tsoro "Ke kuma waya kawo ki nan kinyi tsuru kamar shege a rabon gado?" da sauri mami tace "Nice nazo da ita Ammi kin san jiya da ita muka kwana" daga haka ammi bata ce komai ba Farha taja ajiyar zuciya sabida mami ta kareta ɗakin shuru yayi sedai Aliyu da sadiƙ suna ɗan yin magana jifa jifa akai sallar azahar duk suka tashi dan zuwa suyi sallah sadiƙ da Aliyu masallaci suka tafi farha kam bata motsa ba ta matsu subar asibitin bayan sun dawo daga masallaci Doctor ya shigo ya miƙawa Aliyu hannu.
"Ma sha Allah! jiki yayi kyau ko yanzu ma za'a iya sallamarka amman kafin nan zo muje Office na ɗan Gwada jinin ka" Aliyu da sadiƙ suka bi bayan doctor suka fita Wanda adaidai Lokacin da sadiƙ ya gifta ta wajan farha ƙamshin turaren shi mai ƙarfi ya doki hancinta jitai kanta yana juyawa seta fara rufe idanu tana dafe bakinta wani irin amai ne mai ƙarfi ya tawo mata Da gudu ta miƙe ta shiga Cikin Toilet ta tsugunna ta dinga sheƙa amai kamar zata amayar da hanjin cikinta mami tana tsaye akanta tana jera mata sannu ta gama Mami ta wanke mata bakinta suka fito sedai yadda ta wahala a wajan aman ga yunwa dan rabon ta da abinci Tun jiya se jiri ya ɗebe ta a wajan ta zube tana sakin Numfashi Cikin tausayi Ammi ta dubi Mami dake ƙoƙarin ɗago farha.
"Mami aje akira Nurse su duba ta ko ɗan ƙarin ruwa ne ai mata dama bata da lafiya ne?" mami tace "Tun jiya dama na fahimci bata jin daɗi" Sajeeda ce ta kira Nurse wadda tazo tace Su ƙaraso da farha wani ɗaki dake Kusa dana Aliyu Da sajeeda da mami ne suka kamata suka kaita ɗakin Nurse ɗin ta dubi Farha bayan su Mami sun fita.
"Me dame yake damun ki?"
Farha tace.
"Yawu ke taruwa a bakina se kasala da amai da yawan bacci"
Nurse ɗin tace.
"Yaushe rabon ki da ganin Period ɗinki Ai kina da aure ko?"
Gaban farha yayi mumnan faɗuwa a hankali tace.
"Eh ina da aure sedai rabona da ganin Period ɗina zan kai wajan wata Uku Babu kwanaki Kuma ni hankalina bai kai Lissafinsa ba sabida ban da nutsuwa"
Nurse ɗin tace mata.
"Shiga wancan toilet Ɗin ki fitsari a wata kwalba ki miƙo min"
Jikin farha da matiƙar sanyi ta shiga bayin tayi fitsarin ta miƙowa Nurse ɗin wadda ita kuma ta fita tana fita su mami dake tsaye a bakin Ƙofar suka tare ta da cewa "Yaya jikin nata?" Nurse ɗin tai Murmushi tare da cewa "Ku kwantar da hankalin ku bari naje yanzu zan dawo" Mami ta saki ajiyar zuciya dama ita kaɗai ce ta damu da lamarin Farha ɗin se sajeeda wadda Take tayata tsaiwar ammi kuma da Safna suna cikin ɗaki.

Gaba ɗaya Jikin farha rawa yake hankalinta a Mugun tashe yake Ji take dama bata cewa Nurse ɗin tana da aure ba da seta roƙeta akan ta rufa mata asiri koda gwajin da zatai mata ya bada wani sakamako kada ta gayawa kowa dan gaba ɗaya tunanin farha ya tafi akan tana da ciki dan ta taɓa jin wata rana Yaya sadiya ke gayawa yaya nafisa ita fa wata biyu bata ga al'adarta ba tana zargin Ko ciki ne da ita tundaga nan ta fahimci hakan Sam tunaninta ya gushe ga fahimtar yanayin ta se yanzu da Nurse Ɗin ta tunatar da ita koda yake rashin kwanciyar hankali ma kaɗai wanda take ciki ze hanata fahimtar tana da shigar Cikin wato shiyasa Komai nata ya sauya.

Cikin farin ciki Nurse Ɗin ta fito wanda ta nufo ɗakin da Farha take kwance domin tayi mata albishir da tana da shigar ciki na watanni Uku cif sedai Mami ta kuma shan gaban nurse ɗin tana ce mata.
"Yaya mai jikin tamu amman ba wata matsala bace?"
Nurse ɗin tai Murmushi tare da cewa.
"Ki kwantar da hankalin ki madam Da farko dai ina tayaku Murna dan tana ɗauke da ciki na wata uku cif ajikinta"
Ƙafafun mami ne suka soma rawa sajeeda da rawar Jiki kuma muryarta da ƙarfi tace.
"What Ciki fa har na wata uku ƙanwar musan ?"
Da sauri Ta buɗe ƙofar ɗakin dasu Ammi ke ciki tana cewa.
"Ammi baki ga ta zama ba wallahi yadda tazo sedai ta Koma Kinji ciki ne da ƙanwar musa har na wata Uku"
Ammi da safna agigice suka fito gurin nurse ɗin wadda take tsaye mami kuwa tama kasa magana.
"Ke ƴarnan wake da ciki?"
Cewar ammi Nurse Ɗin tace.
"Mama ku kwantar da hankalinku tana cikin ƙoshin lafiya sannan tunda tace min matar aure ce ita ai No need ku ɗaga hankalin ku haka"
Ammi cikin masifa tace.
"Ƙarya take Munafuka Budurwa ce mai aikina ce Wallahi bazata ƙara kwanar Min agidana ba Safna ku kamo min ita Muje gida ta haɗa kayanta tabar Min gidana bazan ɗauki jaraba ba ƴaƴana basu kwason abin Kunya ba ɗan wani baze kwaso Min ba shegiya munafuka Mami muje Mota kidena mamaki dama ƴaƴan ƙauye wasu ai sunfi na birni jaraba Su Baba sa same mu agida dan bazan kuma zama anan ba Muje Gida tabar Min gidana"

Duk yadda Nurse Ɗin taso ta fahimtar da Ammi taƙi sauraronta Su safna a wulaƙance suka janyo hannun farha suna aibata ta harda ce mata ƴar iska mazinaciya Suka wurgata Mota da ammi da mami suma suka shiga mami Jin komai take kamar mafarki to tayaya farha tai ciki lallai Mutum mugun Icce driver ne yaja Motar suka bar asibitin suka tafi gida..............
Autar manya ce marubuciyar......
*ƁOYAYYAR ƘAUNA*
*BA SON TA NAKE BA*
*ƊAN MAJALISSA*
*MURADIN ZUCIYA*
*ASHE ZUMA*
*TAURARO*
*KOBA SO*
*RABON WANI*
*FITAR RABO*
*DA IZZATA*
*BAƘON LAMARI*
*AUREN BARE*
*H A S K E*
*RABO YA RANTSE*
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*


*A LOVE STORY 94*

Doctor ya zare farin glass ɗin dake idanun shi yana miƙawa Aliyu Doguwar farar takardar dake hannun shi tare da cewa.
"Alhamdulillahi Mr Madaki I hope your blood is back to normal, but you should be very careful if something like this happens in the future domin jiya a yanayin da aka kawo ka abin it was very sad Allah ya kiyaye gaba"
Aliyu ya naɗe takardar ya cusa a aljihun jallabiyar Jikinsa dan be samu yayi wankan bama kayan shi da Mami tazo mai dasu suna ɗakin da aka kwantar dashi.
"Nagode doctor And I will keep all the commandments that you told me in sha Allah, Se maganar Bill"
Doctor yayi murmushi.
"Ɗan uwanka tun jiya yayi dukkan abin da ya kamata"
Sadiƙ yace.
"Rabu dashi Likita so yake ya nuna mana shi me Kuɗi ne"
Aliyu Murmushi yayi yana shafa Gemu bai kuma cewa Komai ba dan har Lokacin bai Koma normal ba

Tashi suka yi suka miƙawa doctor hannu sukai sallama Suka fita daga Office adaidai bakin Ƙofar fita Aliyu ya dafa ƙafar shi tare da cewa.
"Washh Allah na!"
Sadiƙ da kulawa yace.
"Subuhanallahi ƙafar ce dai Ko gidan masu ɗorin gargajiya zamu je in mun fita sannu"
Aliyu ya dafe Ƙirjinsa sakamakon wata Mummunar faɗuwar gaba data ziyarce shi.
A fili ya furta.
"Subuhanallahi Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un"
Ya faɗa da ƙarfi Kuma da sauri yana dafe ƙirjinsa yana Riƙo kanshi sadiƙ ya zuba masa ido.
"In kana ganin baka jin daɗi har yanzu Mu ƙara kwana ka huta Sosai"
Girgiza kai yayi.
"In ban yi ƙarfin hali ba Ammi ba zata kwantar da hankalinta ba banson ciwon ta ya tashi"
Sadiƙ yaɗan kalle sa tare da cewa.
"Kai kuma seka kashe kanka Ko me? baka warware ba ma karɓi sallama ba gwara ka ƙara zama Normal ba"
Dafa ƙafaɗar sadiƙ yayi suka jera A tare suka Miƙe hanyar da zata sadasu zuwa wajan su Ammi.
Abin mamaki koda suka je Cikin Room ɗin babu kowa acikin sa Aliyu ya saki kafaɗar sadiƙ yana ƙarewa ɗakin kallo.
"Ina su Ammi?" ya faɗa a fili Sadiƙ yace.
"Ko gajiya sukai da jiran mu suka tafi Gida"
Aliyu ya girgiza kan shi.
"Gaskiya su Ammi ba zasu tafi gida haka ba there is something that happened"
Ya faɗa yana fita daga ɗakin Sadiƙ yayi saurin Bin bayan shi a Farfajiyar asibitin yaja ya tsaya ya kama Ƙugu Kamar daga sama kuma ya hango Nurse na tawowa zata shiga Office yasha gabanta.
Ko sallama bai mata ba.
"Da Allah ko kinga wasu mata haka anan ɗakin?"
Wannan nurse Ɗin ce wadda ta gwada farha Cikin sakin fuska tace masa.
"Ƙwarai akwai wadda na duba acikin matan da suka zo Dubaka To abin da yasa ma na duba ta sabida nayi amfani da file ɗinka ne na nan asibitin tunda aikin gaggawa ne tana buƙatar taimako"
Da sauri yace "wacece babbar macece?"
Duk zaton sa ko Jikin Ammi ne ya tashi a lokacin sadiƙ ya ƙaraso wajan Nurse Ɗin tace "A,a wannan Matashiya ce mai ɗauke da Cikin wata Uku amman dai naga dana faɗa musu duk sun Shiga tashin hankali Kuma ita tace Min matar aure ce Nadai barsu sun tafi gida......

Ai ina bai ma ƙarasa Jin sauran ba ya saka kai yabar wajan duk uban Kiran da sadiƙ ke masa bai Jisa ba Har yakai bakin gate ya tari napep Da ƙyar sadiƙ ya cimmasa Suka shiga Ciki Duk uban maganar da sadiƙ ke masa sam bai magana ba Addu'a yake Akan Allah yasa kada Cikin Jikin farha ya sami matsala idanunshi sunyi jajir har wani Jiri yake Ji dan tashin hankali.


Tunda suka hau motar Ammi take cin Mutuncin farha babu kalar aibatatan da batai ba kamar Ammi bata taɓa haihuwa ba Farha ta kasa kuka se ajiyar zuciya take Numfashinta yana kaiwa da Komowa ashe Kuka ma se ana cikin kwanciyar hankali ake Yinsa tabbas Tunda take ganin Ƙaddarar Gidan Miji bata taɓa ganin mai kama da tata ba Mami ke bawa Ammi baki tana ce mata.
"Ammi dan Allah ki mata a hankali Muje Gida a kira Musa duk ai komai Cikin Nutsuwa nina fi zargin fyaɗe akai mata dan Farha tana da kamun kai"
Ammi tace.
"Dallah gafara can rufe min baki wannan mai kama da ɗanwaken ce za'awa fyaɗe babu wani ita takai kanta dama Jiya tunda na ganta Naji gabana ya faɗi to bazan Goya ɗan shege agidana ba Zuwa zamuyi ta tattare kayanta tabar min Gidana tun ma kafin na waje suji a ɓatawa Gidana suna"
Safna da sajeeda se dariya suke Farha ƙasa tai da kanta Tana Jin Zuciyarta na wani Irin Buguwa tunda take bata taɓa ganin ƙasƙanci kamar wanda Ammi tai mata ba har suka ƙarasa Gidan Ammi tana cin zarafin farha A wannan karon ma Su safna Ne suka janyota har zuwa sashin ammi a falo suka zubar da ita ta dafe Gefen mararta tana rintse Ido ɗakinta Ammi ta shiga ta dinga jido kayanta tana watsa mata a jikinta.
"Ki tashi ki tafi matsiyaciya mazinaciya Kije Ki nemi uban Cikinki"
A wannan karon Mami ta kasa daurewa Kuka ta saka wiwi sabida yadda farha ta bata tausayi Ammi Masifa ta cigaba dayi wadda farha tai Shuru sabida kokawa take da Numfashinta.

"Nace ki tashi ki tafi Ba zaki ƙara zamar Min agida ba makira Mazinaciya Kije ki Nemi uban Cikin Jikinki.......
Cewar Ammi tana tsaye akan farha su safna na zaune suna dariya Mami tana Tsugunne a gaban farha tana kuka tana tattare mata kayanta.

Adaidai nan Ya shigo kamar an cillo shi Kuma lokacinne ammi takai maganarta ta ƙarshe wadda tace mata Kije ki nemi Uban cikin Jikinki.....

"Ammi Nine uban Cikin Kuma Fatima ba mazinaciya bace Nine Mijinta auren sunna mukai"
Daga Ammi har su safna Ƙamewa sukai Mami kuma ta Miƙe tsaye sadiƙ ya ƙame a jikin Ƙofar shigowa Aliyu gaban farha ya ƙarasa da sauri yana Kama hannunta bayan maganar ta gama fitowa daga bakinsa.
"Tashi fatima mu gani babu abin da sukai Miki ko?" Ƙura mai ido tayi lallai ɗan halak ne kuma yayi mata halacci se lokacin Kuka ya ƙwace mata Ta faɗa Jikinsa tana wani Irin Kuka kamar ranta ze Fita.

"Baba Kazo ka tasheni daga mafarkin da nake Cikin ka matarka duk ina me akai hakan Zaman dadiro Kuke da ita dama shine dalilin daya sa ka hana na sallameta baba sakamakon da zaka Min Kenan zina.........!"
Seta rushe da Kuka.
Da sauri ya saki farha Hankalin shi a Mugun tashe ya Nufi gaban Ammi wadda ta ɗaga mai hannu alamun bata buƙatar Ganin shi a gabanta.
Ya zube Dukkan gwiwowin sa a ƙasa ya kama hannunta ya rintse idanunsa.
"Ammi kada ki jefeni da kalma mafi Muni ga Mumuni ammi ban taɓa zina ba Kuma ba zanyi ta ba In sha Allah"
Tureshi tayi tare da bashi haɗaɗɗan Mari har Guda Biyu ta Miƙe a haukace.
"Ubanka kayi in ba zina ba dan ubanka a ina ka aure ta ban sani ba?"
Aliyu ya dafe Fuskarshi tare da cewa.
"Ƙaddara Ammi ƙaddara ce ta haɗani da ita wadda bana fatan na bayyana ta a gaban kowa Nabar ta tsakanina da ita sedai ƙaddarar mai Kyau ce Tunda ta kaimu ga yin auren Sunna Ammi in kina kokwanto ki Kira su Baba Usman sune suka karɓa Min auren fatima a wajan mahaifinta Tare da cikakkun shedu da sadaki fatima matatace Cikin jikinta na wane Nina mata kuma nasan dashi Ammi Ki haƙuri na Ɓoye miki ne sabida bakya so na Yiwa mami kishiya Ni kuma ina Gudun ɓacin ranki Ammi"

Ya faɗa a wahale sabida yadda kanshi Ke sara mai.
Da baya ta dinga ja tana dafe kanta.
"Su Usman sun cuce ni Dasu ka haɗa baki Kuka cuce ni kaje kai aure ban sani ba Ka ɓoyewa kowa Na cancanta Da haka a gareka Baba ni zaka yaudara Baba ashe matarka ce To bari kaji wallahi se an zubar da Cikin nan kuma seka saketa"
Da sauri sadiƙ ya ƙaraso Duk hawaye ya Jiƙa masa Fuska kuma bana komai bane ba sena tausayin Aliyu.
"Ammi kada ki yanke Hukunci Cikin Fushi nina gamsu da Aliyu baze Mana ƙarya ba Allah yasa hakan alkairi ne a gare shi"
Ta bugawa sadiƙ tsawa.
"Matsa ka bani waje shasha sha Ni zai ranawa hankali to ya saketa kuma na Kira salma tazo yanzunnan ta zubar da Cikinnan Tunda nasan ba asibitin da suke zubda Ciki sabida Doka ce"!!


Jada baya Aliyu ya dinga yi yana girgiza kansa.
"Ammi ina son matata babu dalilin da zesa na saketa Kuma Allah ma baya son saki duk da ba haram bane! Sannan Ammi in kika zubar mata da Ciki Wallahi Nima rasa ni zaki dan In kina ƙaunata To Kiso Cikin Jikin fatima nina ɗauka Murnar Cikin Jikinta zata Goge Dukkan wani ɓacin ranki au ashe ba haka bane........

"Dakata baba ni bana son wannan yarinyar ba kuma nason na haɗa zuri'a daga tsatsonta sabida haka koka bi zaɓi na Ko ɓacin rai ya Biyo baya wallahi"

Ammi ta faɗa cikin hargowa.

Farha ta dinga shafa Cikinta tana Kuka Jitai Tana masifar son abin da ke Cikin nata.

Aliyu a hankali ya Miƙe yabar falon yana tafe yana haɗa hanya Ammi ta janyo wayarta ta shiga Kiran salma ta bata Umarni akan tazo Cikin gaggawa Falon Shuru yayi ammi ta bar wajan Su safna Suka Nufi ɗakin su sadiƙ ya Juya ya fita mami da dafe bango Ta bar falon sabida har Lokacin mafarki take.

Falon yayi tsit se Sautin Kukan farha a hankali ya tako ya ƙaraso gabanta.
"Taso"
Ya faɗa babu walwala tashi tayi shikuma ya ɗauki Kayanta Suka fita daga falon Harabar Gidan tsit sabida Lokacin ana sallar la'asar Cikin wata Mota suka shiga da kanshi yaja Motar Har zuwa Bakin titi kafin ya ɗauko wayar shi ya kira Musa zaman Jiran Musa sukai wanda kusan Minti talatin yazo.

Aliyu ya Koma baya kusa da farha Musa yaja Motar tafiya sukai harta kusan awa se gasu a wata babbar tashar Motoci Kaduna Shine abin da kwandastan motar yake faɗa

Aliyu yace Musa ya Tsaya suka fita ya fito da kayan shi da nata Babbar Wayar shi Ya miƙawa Musa tare da cewa.
"Ka aje Min a wajan ka Wannan Kuma takardar ka kaiwa Ammi"
Daga haka ya kama farha Suka Shiga Cikin Motar dama Mutum Biyu ne suka rage yabar Musa a tsaye kamar an dasa shi yama rasa me zeyi sabida bai san Komai akai ba.
Da sanyin Jiki Musa yaja Motar zuwa gidan Aliyu kuma kamar yadda ya faɗa kai tsaye Musa sashin Ammi ya Nufa Lokacin salma ta ƙaraso duk hankalinta a tashe Kusan a tare ma suka shiga sashin ita da Musa Lokacin da suka shiga falon sadiƙ da Bashir suna tsaye se Ammi Dasu safna daga gani kamar magana suke sallama sukai suka shiga falon Musa ya rissuna ya miƙawa Ammi doguwar takardar da Aliyu ya bashi tare da cewa.
"Ammi gashi Inji yallaɓai yanzunan na kaishi tasha"
Har rige rigen Miƙa hannu sadiƙ da Bashir sukai wajan amsar takardar Jikin sadiƙ rawa yake a fili yake karanta saƙon da takardar ta Ƙunsa mai ɗauke da Rubutun Aliyu ajiki.

_Ammi ki yafe Min ko zamu gana ko ba zamu gana ba Ammi na zaɓi na nesanta kaina dake sabida matakin da Kika ɗauka akaina duk ba zan Iya ba Domin Ko a addini haka haramun ne saki halak ne amman Allah baya so Bare Ni fatima batai Min laifin da zan sake taba sannan Kuma in na yarda Kika zubar mata da ciki kamar nai Kisan kai ne bare ma Ni ina son cikina Tunda matata ce ta sunna amman In kina Musu

Please Login or Register in order to submit comment