Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa.
"Yaya kome ye ka gaya min in sha Allahu baka da matsala dani"
Ya gyara zaman shi sosai ya soma yi mata magana.
"Salma ga amanar fatima nan na kawo Miki ita ki kula da ita kamar yadda zaki Kula dasu Safna In sha Allahu da zarar mun dawo zanzo na ɗauketa, sabida tana da lalura dole se an kula da ita sosai tana ɗauke da juna biyu amman bana son ita kanta tasan tana da cikin kuma kema bana son ki sanar da kowa, Ina son dai ki dinga lura da ita idan da damar hakan"
Jikin salma ne ya ɗauki rawa hankalinta yayi masifar tashi"Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un" take faɗa a fili wato kowani ɗan adam akwai kalar tashi jarrabawar wato shi tashi kalar jarrabawar kenan to fyaɗe yayi wa ƴar mutane ta sami ciki Kome shi kuma sabida masifar son haihuwa ta Shiga ranshi yaƙi Zubar da cikin

"Amman yaya ban gane me kake nufi ba, Allah yasa ba zargin dana ɗarsa bane a zuciya ya tabbata yaya kada kayi mana haka Idan ma Ƙaddara ce ta faɗa muku Ni zanyi shahadar zubar da cikin kafin duniya ta sani dan na tabbata Ammi ma taji zata iya haɗiyar zuciya ta Mutu"
Salma ta faɗa muryarta tana wani irin rawa Tunda ta soma maganar ya kafeta da idanu Ranshi idan yayi dubu ya ɓaci sedai uzirin rashin sani da yayi wa salma shine yasa yaji zuciyarshi tana ƙasa tana sassautawa daga zafi da ƙunar da take masa.

"Wannan shine Kuskure na farko da zaki a rayuwarki, Koda wasa kada ki gangancin zubar Da cikin dake Jikin fatima dan fatima ba Lalata da ita nayi na mata ciki ba, Cikin jikinta na sunna ne Nine Mijinta wanda shedu da sadakina suka tabbatar da hakan"
Wata irin hantsila salma tayi ta Dafe ƙasan carpet ta zaro ido Jikinta yahau rawa lallai biri yayi kama da mutum, shiyasa lokacin data masa waya akan ya bata Number ɗin musa yaƙi yace kada ta bari ta tafi se gashi yazo.

"Yaya Ban gane ba wannan wani irin aure kayi wanda kaf ɗinmu bamu sani ba dan bani tunanin Ammi ma tasan wannan yarinyar matarka ce, Yaya mai yasa kayi hakan wanda ka san Wannan aure akwai matsala gagaruma acikin sa Wanda kuma gashi tun kafin aje ko ina rabo ya shiga tsakanin ku da ita"

salma duk ta faɗi maganar a hargitse.
Ya zuba mata ido yana jin dama bai gaya mata ba domin ya hango ruɗu kala kala a cikin idanunta koda yake dama haka ƴa mace take tana da ruɗewa ba kamar namiji ba wanda shine ze tsaya ya saurare ka har ma kuyi magana ta fahimta.
"To salama na ɗauki kayata na juya kenan dama wannan dalilin ne ai yasa nace Miki alfarma nake nema a wajan ki ba kuma komai ne yasa na gaya miki matata bace kuma tana da ciki sabida zan tafi ban san meze faru a Bayan tafiyata ba ƙila jikinta yaƙi daɗi daga ƙarshe ki dubata kiga tana da ciki wanda ƙila kafin na dawo Kin Koreta kokin sanar da wani shiyasa na gaya Miki gaskiyar lamari, But amman tunda naga kin shiga damuwa kin ruɗe ba wata matsala zan ɗauketa kawai Mu juya Nidai na tabbata Wannan ciki na wane kuma Na sunna bana shege ba"
Daga haka ya miƙe tare da zira hannayen shi cikin aljihun jallabiyar shi da sauri salma ta miƙe tana cewa "Dan girman Allah yaya kada kayi min haka kowa ma kajewa da wannan magana irin wannan yanayi ze shiga ta yaya zaka tsallake Duk gidajen dake garin nan kazo wajena sabida kana ganin ka isa dani sannan na kasa yi maka alfarma wadda bata fi ƙarfina ba in ban rufawa Iyalinka asiri ba wa zan rufawa yaya dan Allah ka zauna Muyi magana ta fahimta dan Allah ba domin niba"

Aliyu yaji jikinsa yayi sanyi sabida magiyar da salma keyi masa a hankali ya zauna salma ta zauna itama tana kallon shi jitai ta matsu taji meye silar wannan aure mai cike da ruɗu acikin sa.
"Fatima matata ce na aureta ne sanadin ƙaddara lokacin da akai Min sharrin nan agidan wata radio kin tuna? to na aureta ne da zummar ɗaukar fansa akan yadda ta jagoranci yaɗa labarin Bogi akaina sedai Kin san shi Allah babu yadda bayayi da bawan sa yarinyar ta soni tun kafin tasan waye ni lokacin dana je mata da maganar aure akwai maganar wani akanta amman haka ta bujure tace ni take so Duk da ni bada Soyayyar gaskiya naje mata ba Ni kawai naje ne akan ɗaukar fansar abin da tayi Min sedai tashin farko mahaifinta yace Kona zo na aure ta ko kuma ya bada ita sadaka tunda tafi sona akan wanda ya bata a daran ranar najewa ammi da bayanin Ina son nai aure amman ammi ta rufe idanu akan ga mami ba zan yi wani aure ba, Ni kuma kawai sena tura su Baba Usman da sadakina aka auro min ita na kawo ta gidan Ammi akan zata ke mata aiki bama nine na kawo taba Musa na saka yace ƙanwar shice Nufi na intai kamar shekara sena sallameta sedai kwatsam Kuma Allah ya ƙaddara Min tsananin son ta har takai ga wannan rabo ya shiga tsakanina da ita yanzu haka in ba keba babu wanda yasan wannan magana dake tsakanina da wannan yarinya hatta ammi bata san Komai game da ita ba"..............
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 78*

Ya ƙarasa maganar cikin Nutsuwar sa tare da zubawa salma ido wadda duk jikinta yayi sanyi ga mamakin sa se yaga salma ta fashe da kuka wanda bai hanata yin Kukan ba har ta ɗauki Lokuta masu tsayi tana faman yin kukan kafin ta ɗago ta share hawayenta tana kallon shi wani irin tausayi ɗan uwan nata ya bata ba ɗan kaɗan ba

"Nagode wa Allah da Allah ya ƙaddara wannan ciki ta silar sunna aka samar dashi wallahi da ko baka auri yarinyar nan ba dafa seka mata cikin nan sabida akwai rabo a tsakanin ka da ita rabon haihuwar dake tsakanin Kune yayi ta ɗawainiya da ita har taƙi shi wanda mahaifin nata ya bata ta aure ka, sannan kai ma rabo ne fa ya kaika gidan su domin ba da ban haka ba kamar yadda ka ɗauki mataki akan shugaban gidan radio ɗin ita ma haka zaka ɗauki mataki akanta, amman da yake Allah ya ƙaddara ta silar faruwar haka zaku haɗu shiyasa Allah ya tsara Muku hakan Kuma naji matiƙar daɗi nai Farin ciki kuma zan bata duk wata kulawa Kuma zan rufe maka sirrin ka in sha Allahu"

Salma ta faɗa cikin sakin fuska tagumi yayi yana kallon salma yaji ya sami Nutsuwa da maganganun data yi masa.
"Sedai salma ina tunanin ranar da Ammi zata san gaskiyar lamarin nan babban tashin hankalina shine na kasa yiwa ammi biyayya akan abin da bata so nayi wannan shine tashin hankalina dan nasan In ta sani ranta ze ɓaci"
Salma ta bishi da kallon tausayawa Duk ƴaƴan ammi babu mai biyayyar shi babu mai gudun ɓacin ranta kamar shi wannan tasa Ammi tafi riƙe mai wuta fiye da kowa.
"Kada ka saka wannan tunanin aranka dama shi ciki ɗan duma ne dole ammi tasan wannan magana komi daran daɗe wa kuma dama ammi bata da wani dalili na hanaka aure tunda hakan bai saɓawa addini ba dan kawai ta Burge ƴar yayarta ta faranta mata seta Ƙi barin ka kai aure fisabilillahi yanzu in a waje akai Cikin nan yaya zata yi sufa Mutane sun kasa gane cewa Rabo kamar ajali yake Allah ya ƙaddara matar kace Akwai rabo a tsakanin ku dan haka se kawai a barwa Allah ikon shi, yaya kaje kaita addu'a kada ma kasa ka damuwa aranka In sha Allah akwai nasara acikin lamuranku"
Da ire iren waɗannan maganganu salma tayi ta kwantar masa da hankali har zuwa sanda taga ya saki ranshi Kuma ya sami Nutsuwa tashi yayi yana ce mata shi ze juya amman Musa ze kawowa fatima kayan sawa Sallama sukai dan yace yana gudun Rigimar fatima ne shiyasa baze je suyi sallama ba


Bayan tafiyar shi salma ta rafka tagumi lallai Ammi in batayi wasa ba a kan wannan yarinya zata iya rasa farin cikin Ɗanta mai biyayya dan salma ta hango irin ɗumbin soyayyar da yakewa wannan yarinya.

Miƙewa salma tayi ta shiga ɗakinta Ko Mijinta bata gayawa gaskiyar abin da ke faruwa ba sabida sirrinta ne ita da ɗan uwanta tana Ƙoƙarin fita taji wayarta na ƙara tana duba taga Kuɗi ne masu yawa yayo mata transper ta account Ɗinta fita tayi da wayar zuwa ɗakin da Farha ke ciki tana zaune su Dady sunyi bacci ita kuma farha ta zuba uban tagumi wanda tausayin ta ya kama salma Sallama salma tayi tare da zama a kusa da ita ta riƙe wayar tana Kiran Number ɗinsa yayi rejecting kiran salma shiya kira.

"Assalamu alaikum,yaya ya zaka min haka naga ka turo mini kuɗi na menene?"
Yayi Murmushi lokacin yana driving ze koma gida.
"Ki dinga siya mata abin da take so, Saboda Koni ma tana ce min tana son abu kaza da abu kaza to kada na ɗora Miki nauyi idan kuɗin ma bai isa ba Ki min magana sena ƙaro sannan inda hali ina son ki duba min ita ki tabbatar da akwai cikin nan ma kuwa danni ban kaita asibiti ba kawai hasashe nake yi dan naga Shigen irin yadda take yi mami keyi in tana da juna biyu"
Tausayi da dariya ya bata tausayin na farko shine harda tura mata Kuɗi akan ta kula da yarinyar lallai yana son wannan yarinya da yawa dariyar kuma daya bata ashe shi kaɗai yake shagalinsa ko asibiti ma bai kaita ba lallai se abar yaya.
"Allah ya kiyaye wallahi Ficika ma bazan taɓa ba ta yaya zan ɗauki Kuɗinka kome take so baze fi ƙarfina ba In sha Allah zan mata duk yadda kace"
Ya ɗan sauya murya.
"A,a nidai ki riƙe ban ɗorawa kowa wahala ba Ko ki riƙe koki zubar dasu duka ɗaya nidai na tura yanzu tana ina bani ita"
Salma tayi dariya tare da bawa farha wayar ta fita dan tabar Musu ɗakin.

"Kina jina fatima?"
Ya faɗa cikin wata irin murya mai kama data wanda yake jin sanyi.
"Ummh ina ji"
Ta faɗa sabida yawun daya cika mata bakin ta.
"Menene naji Muryarki ta sauya ko kina cin wani abunne?"
Ta miƙe tsaye taje ta zubar da yawun ta dawo tare da cewa "A,a bakina ne miyau ya cika shi amman naje na zubar"
Ya sauke ajiyar zuciya

"To kinci farar taki ko kina son wani abunne?"
Ta girgiza kai kamar yana ganinta

"A,a wai ka tafi ne?"
Da sauri yace "Na tafi sabida in ma nazo nayi miki sallama Kuka zaki Ni kuma bana son yawan koke koken nan naki"
Ta langwaɓar da Murya tawani shagwaɓe kamar zata masa kuka.
"Shine ka tafi amman koka zo ka min sallama ai shikenan"
Yayi dariya kaɗan "I'm sorry rigimarki nake gudu amman Koda yaushe zannan kiran ki Muna gaisawa harta Vedio call ma, yanzu de ba inda ke maki ciwo ko?"
Ta shafa cikinta "Babu ko ina kawai saman Cibiyata ne inda ka taɓa naji yayi tudu da marata tayi tauri"
Yayi Murmushi mai sauti "Ki dinga cin ayaba sosai ko tsutsar ciki gareki" ya faɗa yana dariya daga haka ya kashe wayar Tabi wayar da kallo aikuwa indai tsutsar Ciki gareta zata dage dacin ayaba dan taita yin kashinta.
Ta jima a zaune kafin salma ta dawo Ta dube ta da kulawa

"Har kun gama wayar?"
Tayi ƙasa da kanta tana miƙawa salma wayar salma dariya tayi.
"Aunty fatima yau kuma kunya ta kike ji"
Yadda salma tace mata Aunty se abin ya bata mamaki.
"Yanzu me kike so Kici na dafa miki?"
Cewar salma Farha ta girgiza kanta.
"A,a wallahi Aunty salama na ƙoshi bacci dai kawai nake ji"
Salma tace mata.
"Taso Muje ɗakin dake kusa dana su Dady seki kwanta acan yafi wannan faɗi"
Salma ta ɗaukar mata kayan suka fita zuwa ɗakin babbane sosai da toilet da tv da komai na More rayuwa acikinsa ga ƙaton gado da Manyan barguna salma ce ta jere mata kayan sawarta acikin Wardrobe sannan ta dube ta.
"Duk abin da kike so ga kitchen nan ki shiga ciki sannan Kome kike buƙata ki gaya min Ni ƙanwarki ce"
Dariya farha tayi kafin tai magana salma ta fice daga ɗakin gadon tahau taja bargo nan da nan wani bacci mai daɗi yayi gaba da ita dama shi take Ji.....

Wani irin missing ɗin fatima yake Ji acikin zuciyar shi da dukkan sassan jikinsa.........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*


*A LOVE STORY 79*

Cikin sanyin jiki dana zuci ya shiga gida a harabar adana motocin gidan yayi parking tare da shiga sashin Ammi Lokacin daya shiga dukkan su suna saman dinning suna shan shayin dare wanda ƙa'idar ƴaƴan Ammi ce shan wannan baƙin shayi,Ammi ce da bashir da safna da sajeeda.
Sallama cikin bakin sa ammi ta amsa ya nemi guri ya zauna Ammi ta tsiyaya masa Kunu cikin cup ta tura masa ya ɗauka yaɗan kurɓa ya aje.
"Yaya maganar tafiyar tamu ne Banji kace wani abun ba?"
Cewar Ammi yace mata "Gobe in sha Allah zanbi Jirgin ƙarfe Ukun yamma Ku kuma se wajan Jibi da safe haka Zaku wuce" ya faɗa yana kallon Bashir wanda ya mayar da hankali kan wayar hannun shi yana dannawa sedai sam hankalin shi ba'a kan wayar yake ba yana kan Ƙofar ɗakin waccan yarinyar Burinsa ta fito ya ganta Dan ba lallai Gobe su haɗu ba tunda Abuja ze wuce.
"ka gama haɗa kayan naka kuwa? sabida in sha Allah gobe tare zamu je airport inna tashi kai kuma seka sami ticket ɗin abuja"
Bashir ya sosa kai tare da cewa "In sha Allah dama ban zo da wasu kayan kirki ba"
Daga haka su safna Tashi sukayi suka bar falon Bashir ma daya ƙwallafa rai akan son ganinta daya ga Boss a wajan miƙewa yayi ya tafi Ammi ta dube shi.
"Komai da komai ya kammala Ɗazu Matar kawu ta Kirani tana min godiya da irin Hidimar da ka aika Musu, Ni dan dai Lokaci ya ƙure ne amman da Mun koma da tajira umara, dan rabon ta da saudi tun hajjin Bara da mukai tare"
Bece mata komai ba can kuma yace mata"Ai lokaci ya kure dakin magana da wuri,Wanda ma nake son ya koma baba usman" Jin haka yasa ammi ta sauya yanayin ta yayi saurin kauda maganar "Na bawa musa yarinyar nan sun tafi tun ɗazu" da mamaki ammi ta dube shi"Kana nufin har ka kira musan kenan sun tafi amman baka gaya min ba ai da ko ɗan sabulu na bata" Murmushi yayi me ciwo "To Ammi gobe zan tafi ban san abin da ze faru bayan bana nan ba shiyasa na Damƙa mai ita shine kawai samun masalaha" Ammi ta haɗe rai tamau "Kai baba wani irin masalaha kuma ban gano nufin kaba wai da kake ma wannan Haƙilon uban wa musa ya bawa yarinyar idan bani ba kuma dan Munafurci ai baka gayan zata tafi yau ba ashe bayan kabar ɗakina zuwa kai ka ɗauketa ka bawa Musa to ko na dawo ma kada ta dawo min gida bana buƙatarta" yarasa mai yasa ammi take ɗaukar zafi a duk Lokacin daya sako mata maganar fatima"Ammi ai kece kika ce Kin mata alfarmar zama har zuwa bayan sallah" tayo masa kaaa da maganarta mai ƙarfi "To yanzu na fasa kai nifa bana son wannan zaƙewar da kake akan wannan yarinyar mai kama da igiyar shanya Ni bamma san jarabar data sa Musa ya kawo Min itaba waya sani ma koda wani surkullen nasu na mutan ƙauye tazo min gidana tunda nake dakai baka taɓa Min tirjiya ba se akanta duba dukan dakawa su sajeeda akanta kamar ba ƴan uwanka ba wallahi bana ƙaunar yarinyar nan" Ƙurawa Ammi ido yayi gabanshi yana tsananin faɗuwa Tun yanzu ma ammi tana irin waɗannan maganganun inaga tasan Matar shice Muryar shi sanyi ƙalau yace mata "Ammi Dan Allah ki dinga kwantar da hankalin ki ni babu wata manufa a tsakanina da yarinyar in kika cire ta dalilin Musa kuma abin da yasa yanzu ma na Bawa Musa ita dan Gobe zanbar ƙasar ne Ku kuma jibi Kinga ba Lokacin Tsayawa akan jiran har se anyi wata shawara akan tafiyar tata, amman inna ɓata miki rai akan hakan Allah ya baki haƙuri Allah ya huci zuciyarki" ya faɗi maganar cikin sanyin Murya se kuma tayi ƙasa da muryarta "Ni kawai shiga hurumin yarinyar ne bana son ka dinga yi Koda yake ma ai Allah ya raba zaman namu Tunda ta tafi shikenan" da sauri yace "A,a ammi in kuka dawo zata dawo In sha Allah haƙuri zaki ɗa na kowa ne kuma kece kika yi alƙwari" shuru tayi masa shikuma seya tashi yayi mata sallama ya wuce part ɗin shi, Ammi tashi tayi bayan ta kashe ƙwan falon ta nufi ɗakin ta.


Jamila ta dawo da baya lokacin data ga ammi ta nufo ɗakinta, Saboda da niya tayi tabi bayan Aliyu Sakina ta dubi Jamila "yana ga kin dawo kuma?" jamila ta zauna jagwab a saman sopa ta saka hannu ta kama Kumatunta"Yaya Ammi nagani zata shiga ɗakin ta shikuma ya fita kin san shi akwai saurin tsiya" sakina taja tsaki mai ƙarfi "Kina nufin haɗuwar ku ba zata yuwu ba kenan asarar kuɗina zanyi kome?" jamila ta share hawayenta daya ke faman zubo mata "Yaya wallahi kona Bisa nasan yanzu ya shiga sashin sa" sakina ta haɗe rai "Gashi Gobe ze wuce naji abban su yana faɗa ɗazu Mukuma jibi Amman banso Kuka ƙi haɗuwa ba sabida turaren nan malam ya tabbatar min da in ya shaƙi ƙamshin ajikin ki shikenan magana ta ƙare,amman ki san duk yadda zaki a goben ku haɗu ki ƙara goga shi a goshin ki da Jikin ki ya shaƙa Shikenan magana ta ƙare wallahi da tsada na amso shi"
Jamila tace "Naso jiya aka samo shi yaya dan na haɗu dashi a falo Allah ya sa Dai wannan karon aikin namu yayi tasiri akan Aliyu, Dan ina hango mana daular da zamu shiga mu warwasa Muji daɗi" ƙaramin tsaki sakina taja" duk wani lissafina akan ki yake burina naga kin auri Aliyu waccan matsiyaciyar matar tashi bana ƙaunarta sam Yaushe Ina ji ina kallon daular shi ga ƙanwata ai wallahi se inda maina ya ƙare" Jamila tana dariya tana kuka ta kuma damƙe kwalabar turaren Sakina ta kuma ce mata "Wannan shirin nefa yasa nace miki ki sauka anan gidan To kuma ashe tafiyar tamu ma a kusa take, amman Zamuyi amfani da damar Gobe tunda ta yau ta Kufce Ina son ki zama matar Aliyu uwar ƴaƴan shi wannan tasa duk wani ƙoƙarina akan hakan yake tafiya" jamila ta Lumshe ido batace komai ba ita kaɗai take hango wadaƙar da zasu yi in Burin su ya cika akan Aliyu.


Duk zuciyar Aliyu babu daɗi haka ya shiga falon shi mami ta jere masa kayan abinci taci kwalliya tana zaune a falon tana jiran shi yanayin data ganshi ne yasa taji hankalin ta ya tashi ta dube shi a raunane.
"Ga abincin ka na haɗa maka"
"Na ƙoshi" daga haka ya haye saman shi yana shiga ɗakin Rigar shi ya tube ya kwanta Maganganun Ammi suna masa amsa kuwa acikin Kunnen shi na Yadda ta nuna fatima ba zata Kuma zauna mata agida ba,rasa tunani da madafa yayi da haka bacci ya ɗauke shi Cikin dare ya farka sallah yaga mami kwance a gefen shi ya janyota ya gyara mata kwanciyarta Ya miƙe sallah ya jima yana yi har wajan ƙarfe Huɗu da tea yayi sahur ya koma bacci da asubah yayi wanka ya fita masallaci.


Umma ce ta dubi Yaya nafisa wadda zuwanta gidan kenan sabida Jikin umma daya ƙi daɗi a kwanakin nan...............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 80*

"Nafisa na rasa me yasa zuciyata take rawa tunani na yake tsayawa cak hankalina ya gaza kwanciya kullum na kwanta bacci mafarkin farha nake yi wallahi kome nake farha nake gani a idanuna baki ɗaya tsoro ne a tare dani ban san a wani hali take ba ban san a wani matsayi take ba"
Umma ta faɗa idanunta yana kawo Ruwa yaya nafisa cikin sanyinta ta matsa gaban umma tana share mata hawayen dake zubo mata sabida dama ita yaya nafisa sanyin hali ne da ita kamar halin umma yaya sadiya ce mai zafi kamar na kawu cikin sanyin murya yaya nafisa tace.
"Wallahi umma bake kaɗai ba muma kammu hankalin mu ba'a kwance yake ba ko jiya babansu seda yace Min anya muna bibiyar halin da farha take ciki nace masa kuna waya da Mijinta kamar yadda yaya sadiya take gayan shine yace ai waya ba tabbas bace mu ganta shine tabbas tunda duniya yanzu babu gaskiya acikin Mutanan ta"
Yaya nafisa takai maganar cikin sanyin Jiki umma ta kuma goge hawayenta tare da cewa "Hidimar da Mijinta yake mana tayi yawa, na fahimci shi kuma kawun ku wannan wayar da sukai da mijin nata ya sami nutsuwa Nikam har yanzu hankalina baya kwance ga kuma maganar yaron nan da Ya nemi auren farha Jiya Kawun ku yake cewa Baban sa yace dai basu haƙura ba suna neman iri dai acikin gidannan a ƙara bashi guda ɗaya daga cikin yarannan ni nace ga Ruƙayya ko Hadiza amman kawun ku yace Ikram za'a bashi wallahi Jiya baki ga bala'in da a kwasa ba Nan Babarsu Hadiza tazo tagama cimin mutunci har da cewa waya sani ma ko anyi tsafi da farha kuɗin kanta Muke ci wannan abu ya ƙara ɗaga min hankalina Kin san shi maƙiyi kome zaka masa bazaka Burge shiba nina rasa mai nayi wa matar nan ta tsane ni nida ƴaƴa na wallahi babarsu Ruƙayya ta sakko har nan take zuwa muyi hirar mu wani bin sirrinta ma zata kwaso ta gaya mini"

Yaya nafisa ta numfasa kafin tace.
"Au umma salim ɗin ne dai bai haƙura ba wato yanzu kuma da ikram za'ayi to umma Allah yasa haka ne mafi alkairi sedai Kuma Tana makaranta katse mata karatun zaku yi kenan?"
Umma tace.
"A,a nifa hankalina har yanzu bai gama kwanciya ba, Kin san dai yadda muka ƙare da mahaifiyar shi babu kalar maganar da bata jefe mu da ita ba akan farha bada ban Allah yasa ma Mahaifin nashi a tsaye yake ba ina ga da har gidannan zata zo taci mana mutuncin maƙiya suyi dariya to Se Allah yasa mahaifin sa a tsaye yake shine ya taka mata burki, to kawun kune yaje har gida yana ƙara bawa mahaifin salim ɗin haƙuri dan yadda kawun naku ke faɗa ko a hanya baya yadda su haɗu da mahifin salim sabida yadda yake jin kunyar shi, to shine fa mahaifin salim ɗin kecewa kawun ku Shifa yana ganin acikin ƙannen farha a sake bawa salim guda ɗaya tunda ya gama ginin shi yayi komai matar dama ake jira"
Yaya nafisa ta katse umma da cewa.
"To shine aka bashi Ikram?"
Umma ta girgiza kanta.
"A,a shi kin san kawun ku in ze magana tara mu yake gaba ɗaya har yanzu shibe san ya ware mace ɗaya yayi shawara da itaba, To shine jiya ya taramu yake gaya mana Shine na buɗi baki nace to tunda haka ne ga Ruƙayya ko Hadiza tunda Wannan shekarar zasu gama makaranta, Amman shi kawun naku se yace a,a ga Ikram nan ƴar ɗakin su Farha in aka bawa salim seya fi jin daɗi, Kuma ma ikram tafi farha sanyin hali da haƙuri to tundaga nan suke ta ƙananun maganganu musamman ita babarsu Hadiza dan ba'a ƙare taron da ita ba tashi tayi tabar mana wajan tana Mita, nifa Nafisa bana Murnar wannan abu saboda Ikram duka nawa take ma da za'a mata maganar aure"

Yaya nafisa ta saki fuska cikin farin ciki tace.
"Umma bafa aja da ikon ubangiji ke dai addu'a zaki muma kuma mu tayaki duk abin da

Please Login or Register in order to submit comment