Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rayu tare saɓanin mahaifiyarta da kawai daula da dukiyar take hange ba komai ba sallama sukai mami ta kashe wayar anan tai kwanciyarta tana saƙa wasiƙar jaki har dare ya raba ta kasa bacci Kuma ta kasa tinkarar ɗakin Aliyu sabida shakkar sa take tunda yace mata idan yaci ze Mutu shikenan taji tana shakkar Tunkararsa a taƙaice anan ta kwana wanda se asubah bacci ya ɗauketa ba ita ce ta farkaba se bakwai na safe tai sallah ta Kuma komawa Baccin nata.

Da ƙyar Farha ta tashi taje toilet alwala ta ɗauro a zaune ma tayi sallah sabida yanzu kuma ƙafafunta ke mata wani irin ciwo jita ke kamar ana sara mata su wainar jiya daya aje a saman madubi ta ɗauka a haka ta dinga cusawa tana ci duk da tayi yami amman ita tai mata daɗi tana gama ci ta koma gado se Bacci Hajja data zo aikin safe ta leƙo ɗakin ganin Farha na bacci ne yasa bata tashe taba ta shiga kitchen ta soma haɗa musu abin karyawa wajan ƙarfe goma sakina ta fito falon lokacin hajja tana tsaka da jera kayan kari a dining suka gaisa da sakina wadda ta zauna a saman Kujera sakina ta ɗan dubi hajja tana cewa.
"Dan Allah Hajja ina wannan yarinyar ta jiya?" Hajja tai Jimm kafin tace "Oh fati tana ɗaki bacci take dan Jiya tasha aiki"
Sakina ta ɗan kalli Hajja se kuma tayi shuru can kuma tace "Taso min ita tayiwa yarana wanka zamu fita ne Nida Jamila zamu je gidanmu" Da Hajja har zata yi magana se kuma ta fasa ta kama hanyar Ƙofar ɗakin Farha da ƙyar Hajja ta farkar da ita daga baccin sabida baccine mai nauyi "Tashi fati zaki wa ƴaƴan sadiƙ wanka inji Hajiya sakina tana jiranki a falo" Idanu jajir Farha ta miƙe Jiri ke ɗibarta Wanka tayi sama sama ta fito Doguwar rigar material ta saka tare da yafa ɗan ƙaramin Mayafi a saman kanta wanda ya tsaya iya wuyanta Doguwar rigar ta karɓi surar Jikinta domin daga ƙirjinta ta kamata daga ƙasa ne ta buɗe ta ɗan fesa turare kaɗan ta fita falon tunda ta fito sakina ta zuba mata ido haka kawai aranta take jin yarinyar batai mata ba ita dai Farha a gaban sakina ta tsugunna tana gaishe ta a yatsine tace.
"ki shiga bedroom ɗin da muka kwana ki gyara mana shi ki wanke mana toilet sannan kiwa yarana wanka"
Daga haka sakina ta tashi tabar Farha a wajan
Cije baki farha tayi domin yadda ƙafafunta ke ciwo ba zata iya sunkuyon wankin banɗaki ba sedai babu damar ta musa cibi ya zama ƙari haka ta miƙe tayi hanyar ɗakin da sakinar ta umarce ta a bakin ƙofar ma seda ta ɗan tsaya tana cije baki kafin ta tura ta shiga ciki bakin ta da sallama Wannan budurwar da suka zo tare da sakina ce zaune a saman sopa ta bawa ƙofar baya tana waya tana dariya kalma ɗaya Farha taji Budurwar ta faɗa wadda ta sanyata taji ƙafarta ta sage.
"Aunty da alamun nasara fa Aliyu yaje lagos tare ma muke dashi yanzu haka ina gidansu Ku dage Aunty ba mamaki na zama Amarya" Sum sum farha ta wuce Toilet tana wasi wasin maganar Budurwar Giftawar Farha yasa jamila ta aje wayar tabi Farha da kallo kafin ta kirata tana cewa.
"Ke zonan agidan ku ba'a koya Miki sallama bane?"
Farha ko kallon jamila bata yi ba dan ƴaƴan gida ba zasu raina mata hankali ba sannan wata can daga wata uwa duniya itama tazo ta raina mata hankalin ta ɗauka ba Wankin banɗakin ta fara tana gamawa ko kallon Ƴaƴan da sakina tace tayi wa wanka batayi ba tayi ficewar ta dan yadda take jin jikinta idan har tai musu wankan zata iya cutar kanta Tazo ta wuce ta gaban jamila wadda take ta faman Cewa ke! ke! farha tai mata banza tana fita falon sakina ce kaɗai har Lokacin kitchen ta wuce wajan Hajja tai zamanta aciki amman ƙasan zuciyarta tana Allah wadai da munafurcin wasu mazan ashe Lagos ɗin daya biya wajan waccan Guzumar yaje ita kam wallahi ta dena bashi Jikinta sedai ya saketa dan ba zatai Kishi da waccan Guzumar ba ita kaɗai se cika take tana batsewa Ƙiris take Jira ta fashe dan tsananin yadda take jin zuciyarta................*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 67*

Idanunta har wani ruwa ya tara na ɓacin rai bakin ta na mata wani irin ɗaci ita sam bata son Munafurci me yasa baze gaya mata Ƙanwar matar yayan sa Budurwar sa bace amman ko a fuska bai nuna mata ba ita bata Kishin Mami dan matar sace kuma zuwa tayi ta tarar da ita sannan kuma Alkairi yana kore sharri mami ta sota ta jata ajiki dan haka ko a zuciyarta bata jin zafin mami dan ita ya dace ma mamin taji zafi tunda ita ta aure mata Miji amman da Hanan ɗin data ji yana waya da ita rannan da waccan Guzumar wallahi sedai a ƙone muddin yace ze auri ɗaya daga cikin su ba zata zauna dashi ba dama yace Ita yake tausayawa shi yana da mata to taji gwara son shi ya kasheta data yarda ya auro mata su.

"Fati lafiya se faman jijjiga ƙafafu kike yi taso Muci abinci"
Ta girgiza kai tare da cewa.
"Hajja na ƙoshi bar abincinnan" Sabida ko sha'awa ma bai bata ba Hajja ta bita da kallon tausayawa se kuma ta soma rarrashinta
"Fati ban taɓa ganin ki a irin wannan yanayi ba idan ɓata miki rai akai aciki kiyi haƙuri watarana se labari maraici ne duk yaja miki hakan"
Hannu ta sa ta rufe fuskarta nan da nan hawaye ya soma wanke mata Fuskar tata wani irin kuka take mai cin zuciya dan har zafi ƙirjinta ya soma yi mata tunda take kuka bata taɓa mai zafi irin wannan ba Hajja tasowa tayi wajanta tana rarrashinta itama hawayen take yi sabida yadda take ƙaunar Farha jinta take har ranta seda tayi Kukan mai isarta sannan ta miƙe ta wanke Fuskarta ta nufi hanyar fita don ta koma ɗakinta.

"Fati ga ruwan shayin naki ki tafi dashi kya zauna haka baki ci Komai ba" cewar hajja farha ta juyo tace "Hajja bana jin daɗi anjima amman zan sha" daga haka ta juya ta fita falon wanda Yayi daidai da sanda Bashir Shima ya shigo shida Sadiƙ Daga cikin falon Kuma Sakina da jamila ne wadda take faɗawa Sakina rashin Mutuncin da Farha tayi mata.
"Yanzu bata wa su Hidaya wankan ba kome?" cewar sakina
"Bata musu ba yaya ai wannan yarinyar inaga se mun gyarata kafin Mubar gidannan wallahi"
Adaidai nan farha ta Zo zata wuce ta shiga ɗakinta Da wani irin sauri Jamila tayo kanta wani tsalle farha tayi tare daja baya ganin Jamila na ƙoƙarin kawo mata mari.

Cikin sauri Bashir yace
"A,a jamila mai tayi Miki kuma fisabilillahi zaki dakar Musu Ƴa"
Da jin haushi a saman fuskar jamila tace
"Wai wannan kucakar yarinyar harni zan mata magana tai Mini banza dan ubanta" da sauri sadiƙ dake haɗa tea a dining yace "A,a jamila ban da zagin mahaifi Ke kuma shige ki tafi ɗakin ki"
Ya dubi farha Jamila ba yadda ta iya haka ta tsaya tana jan ƙwafa sakina data ji zafin abin da sadiƙ ya faɗa akan farha da sauri ta Taso tayo kan farha tana cewa.
"Tunda An hana jamila taɓa ki Ni bari naji uban daya hana kiwa ƴaƴana wanka komu sa'annin kine?"
Bashir yayi saurin katseta cikin Jin zafin abin da suke wa yarinyar "Haba Aunty sakina wannan ba girman ku bane ina yarinyar nan zata saka kanta ke Kina mata ƙanwarki ta gama mata kuma kowanne acikin ku mahaifanta yake zagar mata talauci hauka ne Ina ne ba'acin arziƙi dan tazo gidannan aiki ba yana nufin ta zama jaka ba"
Bashir ya faɗa cikin Fushi dan dai bai da hurumin hana sakina ne daya nuna mata ƙarfin namiji da mace ba ɗaya bane.
"Bashir ba zaka gane ba wannan matsiyaciyar yarinyar tun jiya take mana kallon banza bara na nuna mata akwai tazara a tsakanin mu na zaneta na ɓallata na watsar da ƴar iska karnuka su cinye ƙashin Ƴar banza"
Cikin Fushi farha tace.
"Sedai karnuka su cinye ƙashin uwarki da uban ki kuma kece ƴar banza bani ba shasha sha" daga sadik bashir sakina jamila kowa kallonta ya tsaya yana yi se Huci take ta kama Ƙugunta to dama farha ta lafiya ce.
Wani Irin kukan kura sakina tayi tare da shaƙo wuyan farha tana ihu ta cika falon da ihu da ashar.
"Ni zaki zaga dan ubanki baki da tarbiya to bari na gwada Miki bambancin mai kudi da talaka zan karyaki zan La'anta ki dan ubanki"
Sakina tana faɗa ta shaƙe wuyan farha sadik da hankalin sa yayi Mugun tashi ya taso yana jan sakina amman taƙi Sakin farha Bashir kam ya ƙame Sabida takaicin sakina adaidai nan Ammi dasu Safna suka fito falon Da sauri Ammi tayo kan sakina sedai duk Ƙoƙarin ta itama ta kasa cire sakina daga jikin Farha Hankalin Ammi yayi Mugun tashi ganin za'a mata kisan kai agida sam bata san abin da ke faruwa ba cikin ɗaga Murya Ammi take magana.

"Sakina kada ki kashe Musu yarinya In ma wani abun tayi miki sakin ta zaki Muyi magana"
Muryar sakina a dashe take cewa.
"Ammi gwara na kasheta nima a ɗaure ni ubana fa take zagi"
Adaidai nan Aliyu da Mami suka shigo falon wanda gaba ɗaya ƙamshin turaren shi na labbra ya cika falon sanye yake cikin Baƙin Boyel mai gidan sukari kanshi ba Hula se haɗaɗɗan Agogo baƙi oyster daya sanya a tsintsiyar hannun shi Ganin Kowa a falon yayi cirko cirko yasa ya ƙarasa ciki da sassarfa jin muryar Ammi yayi tana cewa "Sakina ki cika musu ƴarsu ki rufa mana asiri kada ki mana kisan kai" sakina cikin zafin zuciya ta kuma cewa "Ammi gwara na kasheta nima a kashe ni" se Lokacin ya lura da abin da ya faru da sauri yayi kan sakina ya Finciketa daga jikin farha wadda harta yaga mata Riga zamewa farha tayi ƙasa ta ɗora hannunta a wuyanta tana Wani irin tari kukan kura sakina ta kuma yowa zata kuma shaƙota Aliyu ya taɗeta ta faɗi cikin kakkausar Murya yace.

"Ashe sakina baki da hankali, Ashe baki da tunani kisan kai zaki agidannan kowa yana miki magana kina hauka Okey zoki ƙara shaƙeta ki gani wallahi da sena ɗaure kaf danginku wallahi se kun ƙare rayuwarku a prison marar hankali Kinci darajar auren Sadiƙ wallahi dase na ƙarya ki a wurin nan"
Daga haka ya Sunkuya ze ɗaga farha dan shi idanun shi ma ya rufe dasu ammi na wajan wata irin zabura farha tayi da sauri ta ture masa hannun shi daya kawo Jikinta aguje tayi ɗakinta ta murza key ta faɗa saman gado tari take tayi tana kuka.

Cikin Fushi Aliyu yabar falon Ammi sabida shima idan yace ze tsaya komai na iya faruwa wannan tasa ya fice daga falon gaba ɗaya yana buƙatar nazari kanshi gaba ɗaya ya Kulle............
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 68*

Cikin Ɓacin rai Ammi tace
"Wato sakina ni ban isa dake ba har na fito ina miki magana ki min banza har kina furta zaki kashe musu yarinya ko, wannan wani irin sakarci ne?"
Cikin kuka sakina data ke zube a ƙasa tun bayan da Aliyu ya taɗe mata ƙafa tace.
"Ammi kamar ni yarinyar can ta kama zagin ubana dan kawai nace tayi wa su hidaya wanka batai Musu ba nazo zan Mata faɗa Abban su ya hana ni har yana cewa ta tafi ɗakin ta to meye tsakanin shi da ita" ta faɗa tana kuka wanda ya nuna cewa Tsananin Kishin maganar da Sadik yayi ce tasa idanun sakina suka rufe take neman halaka farha.
"Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un wannan wace Irin annoba Musa ya kawo min gidana tun da nake da sakina bata taɓa min Musun magana ba se yau Tunda Baba yake da sakina bai taɓa Gaya mata magana mai zafi ba seyau har yana cewa ze ɗaure ta wannan wace Irin annoba ce tazo Min gidana ni Amina"

Bashir daya ji daɗin abin da Aliyu yayi shine cikin zafin zuciya yayi magana.
"Ammi ga babbar Annoba nan jamila ai itace Munafukar komai ita ta haɗa har Aunty sakina taso ta kashe yarinyar can wallahi ko yaya Ali bai ɗaure suba ni sena ɗaure su inda sun mata illah"
Bashir ya faɗa a fusace yabar falon Ammi wata irin tsuma ta soma yi tabbas hasashen ta ze zama gaskiya tsakanin Bashir da Aliyu akwai ayar tambaya a tsakanin su da wannan yarinya.
Sadik kam dan takaicin abin da sakina tayi tashi yayi yabar falon Ammi ta kalli sakina cikin sanyin Jiki.
"Ki haƙuri kada ki ƙara Ƙoƙarin Yiwa wani haka nan gaba ita kuma yau zata bar mini gidana base Gobe ba"
Mami takaicin sakina ma ya hanata magana se kawai ta juya tabar falon In ba tsabar hauka ba dan kawai Mijinki yace yarinya taje ɗaki shikenan seki hau Jibgar ƴar Mutane lallai in bata gyara wannan halin zafin Kishin nata ba watarana zata aikata dana sani.

Sum sum jamila ta koma ɗaki Sakina tabi bayanta Shirin fita suka yi ba jimawa suka fito tare da ƴaƴan sakinar sukai wa Ammi sallama suka wuce dama gidansu zasu je dan acan zasu wuni yau suna fita sajeeda taja tsaki.
"Wallahi Ammi Aunty sakina ce bata da gaskiya kuma abin da Yaya Ali yayi shine daidai domin in aka kashe waccan yarinyar harmu abin ze shafa Kishi hauka ne Fisabilillahi daga tashin ta tai mana girkin safe raba kanta uku zata yi ita jamilar uban me take da bazata yi wa su Hidayar wankan ba" Ammi ɗagawa sajeeda hannu tayi alamun bata son maganar kafin ta miƙe tabar falon ɗaki ta shiga ta ɗaga waya ta shiga Kiran Numbern Aliyu.

Kiran duniya Ammi tayi masa yaƙi ɗauka seta shiga kiran Number ɗin Bashir wanda ya fito cikin shirin fita Office.
"Kazo ina son ganin ka"
Daga haka ta katse wayar Bashir ya ƙaraso ɗakin Ammi tana zaune a bakin gado har Lokacin Numbern Aliyu take Kira Amman bai ɗauka ba.

Bashir ya zauna a gabanta yana kallonta.
"Dan uban ka meye nufin ka akan yarinyar can? har da zaka wa sakina rashin Kunya akan ta?" Bashir ya ɗaure Fuska "Ammi ni fita zanyi idan na dawo mayi maganar Nidai nasan a bayan gaskiya nake ita jamilar bata da gidan uba da zata biyo yayarta nan zata haɗa mana rigima agida" Ammi tayo kan Bashir cikin hargowa "Dan ubanka kai ma nan ɗin gidan uban ka ne ba gidan baba bane Kai idan kana da kunya zaka kalli ƙanwar matar ɗan uwanka ka zageta akan bare To bari kaji idan ma akwai wata manufa a zuciyarka ka cire ina nan yadda nake ban sauya ba" Gaban bashir ya faɗi Dan jin soyayyar yarinyar yake kamar ranshi haka ya miƙe yabar ɗakin Ammi cikin sanyin Jiki.


Aliyu yana fita daga falon ammi waya ya samu daga mai girma gwamna da gaggawa akan zasu shiga meeting duk da ɓacin ran dake cikin zuciyar shi hakan bai hana shi amsa kiran mai girma gwamna ɗin ba cikin wata Red colour mota ƙirar samfirin Mcleran 75os ya shiga yayi revers ya nufi bakin gate da sauri masu gati suka Buɗe masa gate ya fice aguje kamar ze tashi sama Yana driving kiran sadiƙ na shigo masa da ɗayan hannun ya ɗaga wayar ya kara a kunnen shi cikin damuwa sadik yace masa.
"Aliyu dan Allah kayi haƙuri da abin da sakina tayi naga kamar ranka ya ɓaci wallahi tun kafin kazo nake magana amman da yake ta rainani bata jiba"
Aliyu yaja ƙaramin tsaki tare da cewa
"Kada ka damu, Ni dai ka jamata kunne koda wasa kada ta kuma gigin taɓa ƴar mutane dan tana taimakon Ammi baze zama ticket na kowa ya dake ta ko ya zageta ba, Ya sadik wallahi dan dai matarka ce sakina amman da yau seta yi kwanan cikin cell dan ban ga abin da ƴar mutane tayi mata ba da zata shaƙe ta"
Sadik daya cika da mamakin furucin Aliyu wanda yake nuni da kamar yana da wata alaƙa da yarinyar yace.
"Kayi haƙuri zan ja mata kunne, sannan kai ma kayi wa yarinyar faɗa a matsayin ka na uban ɗakin ta ta dena wa manya rashin Kunya dan sakina ba sa'arta bace"
Aliyu yayo wa sadik ka tare da ce masa.
"Dan Allah malam kai min shuru sakina sarki ce da dole seta bita zagi inta zagi sakina So what wadda tafi sakina ma ana zagi bare ita Nidai na gaya maka wallahi ka jawa matarka Kunne kada ta sake Gigin dukan ta in banda ma ɗaukar hakki yarinyar nan guda nawa take dubi sakina ƙatuwa ta shaƙe ƴar cikinta dan Mugunta"
Sadik sakin baki yayi amman sabida tsabar haƙuri irin na sadik bai ce komai ba se can yace.
"Kayi hakuri Ba zata kuma ba, Amman wannan zaƙewa taka tai yawa akan yarinyar anya kuwa?"
Aliyu yayi saurin katse sadik dace wa
"Lafiya lau kasan ni bana Ɓoye al'amurana ni zalinci kaɗai shine bani so dan Allah kada hakan ta kuma faruwa" Daga haka ya katse wayar yabar sadik cike da al'ajabi Sadik yayi tagumi yana nazarin maganganun Aliyu wanda ko matarsa iya abin da zeyi idan an taɓa ta kenan Yasan Aliyu baya shiga abin da ba ruwan shi but amman yadda yaga yayi ruwa da tsaki akan case ɗin wannan yarinyar abin yaɗan Bawa sadik mamaki duk da shima ko kaɗan bai goyi bayan sakina ba amman yana son itama yarinyar ta dinga saita bakin ta dan gashi nan garin rashin kunya tasha matsa a banza.

Tashi sadik yayi da zummar zuwa ya shatawa sakina Layi akan Yarinyar Tare da gargaɗin ta akan kada ta kuma taɓa musu yarinya sedai yana zuwa Ammi tace masa sakina sun je Gidansu da Jamila A wajan Ammi sadik ya zauna suna maimaita abin da ya faru shidai duk bai ji dadin hakan ba musamman da yadda yaji Muryar ɗan uwan shi cikin ɓacin rai.


Aliyu bayan sun gama Meeting sallah yayi ya wuce kamfanin shi manyan Buhunnan shinkafa tare da katan katan na taliya macaroni maggi manja man gyaɗa shine Aliyu yasa musa ya firfito dasu domin rabawa ma'aikatan kamfanin shi sabida gabatowar watan azumin ramadan wanda za'a shiga Gobe idan Allah ya kaimu za'a tashi dashi har la'asar suna aikin fitar da kayan abincin wasu ankai gidan marayu wasu an kai gidan yari wasu ankai makarantun allo sannan yazo ya ware na gidajen ƴan uwa da maƙota duk aka zuba a mota se bayan magariba ya sami Nutsuwa Lokacin ko driving bayajin ze iya da kanshi, Musa daya dawo daga kai saƙon Gidansu farha wanda suka je da abokin shi kamar yadda yake yi idan Aliyu yace yakai saƙo shiya Ke Driving ɗin Aliyu dan yay droping ɗinsa a gida.

Aliyu dake zaune a back seat ya dubi Musa yana ce masa.............

*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 69*

"Musa kun je gidan su Fatiman kuwa Hope everything is going well?" Ya faɗa yana fito da wayar shi tarin Misscall ɗin Ammi reras ya gani yasan kira ne shikuma tunda yabar wayar bai ɗauka ba se yanzu Musa yace "Mun je yallaɓai komai yana tafiya daidai sedai har yanzu mahaifanta sun kasa sakin Jiki da tarin alkairan da kake Musu duk sun tsure kamar yadda Abokina ke Gaya min More especially ma mahaifiyar Fatima gaskiya Abokina yace ta shiga damuwa sosai Duk a tsorace take ga kuma Ƙarin damuwar rashin Yarinyarta"
Aliyu yayi wani murmushi mai sauti tare da cewa "I kon Allah! ka bawa Baba ɗin wayar da sim card?" Musa yace "Eh abokina ya bashi bayan mun sauke musu kayan abincin nasu da na wanda zasu rabawa maƙotan su" Aliyu bai ce komai ba na tsayin Mintuna can kuma yace "Oh bani number ɗin" Musa ya ɗauko wayar shi ya miƙawa Aliyu ya amsa yana copy number ɗin to wayar shi har ya gama ya miƙawa Musa wayar Number ɗin yayi dialing wadda shine yayi ma Musa umarnin daya saya ya bawa Kawu.
Ringing ɗaya tayi kawu ya ɗaga Aliyu ya jingina kanshi da seat muryar shi a hankali yayi sallama Kawu ya amsa.
"Baba nasan baka gane mai maka magana ba, Aliyu ne Mijin Fatima da fatan kuna nan lafiya?"
Cikin farin ciki da kwanciyar hankalin da kawu ya shiga Lokacin daya ji Aliyu yace Mijin fatima ne kawu ya washe baki yana cewa
"Alhamdulillahi Naji dadin jin Muryarka yanzu ina fatiman take?" Aliyu ya jinjina soyayyar da Mahaifin nata yake mata kafin yace "Bana gida, kuna lafiya ko? dama na kiraka ne danna gaya maka ka kwantar da hankalin ka Baba akan kome zaka gani daga wajena Ina ɗaukarku a matsayin mahaifa dan Allah ku saki ranku fatima tana cikin Ƙoshin lafiya kuma zata zo gare ku Very soon cikin farin ciki" Kawu yahau share ƙwalla har Muryar shi tana rawa lokacin da yake cewa "Nagode Nagode Ali Allah yayi maka albarka ada ina ta ɗar ɗar amman jin kamilalliyar Muryarka yasa naji nutsuwa Kuma muna ta ganin saƙo yau ma kayan abinci sun Kuma sauka wasu kan wasu harda na maƙota mun gode ƙwarai" Aliyu yaji Nauyin godiyar kawu seya basar da amsa godiyar yace "Ina mama kuma mu gaisa?"kawu yace bari ya miƙa mata Umma tana ɗaki ta zabga tagumi duk abin duniya ya dameta ita fa kada suje ko kuɗin kan yarsu ake kawo Musu da sunan Kayan abincin kawu yayi sallama ɗakin yana cewa "Ungo Hasiya kuyi magana da Mijin Fatima" umma ta saki ajiyar zuciya ta amshi wayar tun kafin tai sallama Aliyu ya rigata yana kuma haɗawa da gaisuwa cikin ladabi.
Cikin jin nauyi umma take amsa gaisuwar kuma daga jin muryarshi tasan Ba ƙaramin yaro bane dan babu baragada ko shirme a nutse yake gaishe da ita.
"Umma Aliyu ne Mijin fatima na kira ne Mu gaisa kafin nazo Muku da ita dan Allah ki kwantar da hankalin ki wallahi Fatima tana cikin Ƙoshin lafiya kuma komai kika ga na aiko da zummar na kyautatawa mahaifana Nayi muku bada wata manufa ba dan ku kamar iyayena kuke"
Umma ta saki fuska tace.
"Babu komai na Gamsu Kuma in sha Allah zan dena wasi wasi a game dakai nidai ina roƙon ka daka dinga haƙuri da halin Farha yarinya ce mai tsiwa Se an haɗa da haƙuri watarana se labari sannan Muna son zamu turo ƴan uwanta don suga inda take kaga ba abin da akai mata na aure daga cikin abin da ya shafi ɓangaran mahaifa dan haka ina son ƴan uwanta suzo nan su ganta"
Aliyu ya Lumshe ido ya buɗe tare da cewa.
"In Sha Allah Mama Fatima ce zata fara zuwa ta gaishe daku,sannan maganar wani abun ɓangaran iyaye kada ki damu komai zan mata ai haƙƙina ne ina son zanje umara nan da ƴan kwanaki Se bayan sallah inna dawo zamu zo daga nan ma suma zan ɗauke su sesu gano inda take"
Umma cikin Nutsuwa tace

"To angode Allah yayi maka albarka Munga abin arziƙi Allah yasa kafi haka Allah ya raya maka zuri'a"
Cikin alkunya yake amsa addu'ar da umma keyi Masa, Bayan kawu ya amshi wayar Aliyu ya ƙara Kwantar masa da hankali kuma sosai kawu ya sami Nutsuwa da hakan sukai sallama.
Aliyu ya aje wayar ba tare daya kira Ammi ba dan har gabanshi faɗuwa yake inya tuno gida dan yasan Ammi nacan na jiran shi seda ya cewa musa ya tsaya yayi masa siyayyar kayan lashe lashe dana marmari Musa ya fita yaje ya siyo ya dawo mota suka ƙaraso gida A harabar Gidan Musa ya bawa Aliyu keyn motar suka yi sallama da juna seda Aliyu ya tsaya a masallacin Gidanshi yayi sallar Isha'i wadda ake ta kira kafin ya ƙarasa Part Ɗinsa siyayyar ya raba Biyu ɗaya ya bari a mota ɗayar ya shiga da ita ciki.

Da sallama acikin

Please Login or Register in order to submit comment