Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zasu je Abuja shida Aliyu dan duba wasu motoci da aka kawo sabbi kamfanin Aliyun na can.



Su safna kuwa anga yaya sadiƙ ai sai ma miƙe ƙafa da sukai suna ta zuba masa zance kala kala suna bashi labarin makaranta shi kuma sai jansu yake yana ta sakin far'a Ammi wani irin daɗi take ji aranta gaba ɗaya ƴaƴan nata kansu a haɗe yake haka suke in sunga junan su kamar su haɗiye kansu Aliyu ne kaɗai bai da sakin fuska sai dai shi ɗin yafi dukkan Ƴaƴanta son ƴan uwanshi Kawai miskilancin sa ne da zafin zuciyarshi yasa ba'a fahimta.

Sai da sadiƙ ya sanya su Safna suka kai Kayan abincin kitchen yasha ruwa sannan yace musu su tafi su kwanta dare yayi.

Sallama sukai masa suka nufi ɗakunan kwanan su.

Falon yayi shuru daga sadiƙ sai Ammi ya gyara nutsuwar shi ya kalli Ammi sosai cikin sakewa dan Ammi bata alkunyar ɗan fari da Sadiƙ gaba ɗaya ta sake da ƴaƴanta yadda ba'a zato sabida sune sanyin idaniyarta Sune garkuwa a rayuwarta tun suna ƙananu take gwagwarmaya dasu Sabida suna ƙananu mahaifinsu ya rasu yabar mata su duka duka lokacin Sadiƙ baifi shekara goma sha biyar ba Aliyu sha Huɗu dan tsiransu da sadik shekara ɗaya ne Salma ce suke da ɗan tazara da Aliyu na kusan shekara Biyar ita lokacin tana shekara tara Bashir shekara bakwai Safna shekara huɗu sajeeda shekara Ɗaya haka Allah ya ɗauki ran mijin nata yabar mata waɗannan ƙananun ƴaƴa wannan tasa ta shaƙu da ƴaƴan nata taja su ajikinta fiye da ƙima.

"Ammi tun safe Aliyu ya kirani a waya wai Mami ta tashi tana ta zubar da Jini haka yace sunje asibiti a gigice hankalina ne yaƙi kwanciya shine na biyo jirgin dare nazo akan wannan batu"
Sadiƙ ya faɗa cike da nutsuwa yana fuskantar Ammi wadda ta bada dukkan nutsuwarta a tare dashi.

"Nima bai gaya min ba sai a wajan masu aiki naji, Amman dan shishshigi har ƴan cikin gidanku sun cika asibitin"
Sadiƙ ya kawar da abin da Ammi tace dan har ga Allah baya jin daɗin yadda Ammi take wa ƴan uwan mahaifin nasu.
"Ammi ni ina ganin kamata yayi kawai Aliyu ya ƙara aure, Dan wannn matsalar tayi yawa"
Ammi ta watsawa Sadiƙ wani kallo.
"Haka ya aiko ka waje na kenan? saƙo ya baka?"
Sadiƙ ya gigice dan yasan Halin Ammi inta botsare musu.
"Wallahi Ammi ko ɗaya kawai dai ni tausayi yake bani ne kinga fa tare akai mana aure dashi yanzu haka Minal shekarun ta goma a duniya kinga shima in da Allah ya bashi da tuni yana da sama da ƴaƴana"

Ammi ta dube shi.
"Sadiƙ zaku ga kamar ina takurawa Babana ne akan Lamarin auren shi, Ko ɗaya ni tsorona kada ya auro matar da zata rabamu dashi Na san Baya son Mami ko kaɗan tsananin biyayya ce ta sa ya aureta Ni kuma na haɗa shi da Mami ne sabida Duk tsiya mahaifinmu ɗaya da Mahaifiyarta Kaga Mami tamu ce bamu da matsala da ita Kuma auren su zai ƙara ƙarfin zumuncin mu da mahaifiyarta"

Sadiƙ ya sunkuyar da kanshi a ƙasa Duk wannan fa ba Masalaha bace A zuciyar shi yake faɗin haka duba da yadda Ammi take Takura Aliyu akan abubuwa da dama ko lokacin auren su ma shi direct daya kawo sakina Ammi bata musa ba Amman shi Aliyu daya kawo wata Najuwa wadda sukai B.U.K tare da ita yace ita zai aura Fafur Ammi ta rufe ido tace bata yarda ya auri Najuwa ba, Haka yace yana son wata ƴar nan galadanci itama Ammi taƙi daga haka yay fushi yace shi yama fasa auren kwata kwata katsam Ammi taje gidan Yayarta dake fagge ta kawo masa babbar ƴarta Mami tace ala dole sai ya aureta Duk da ba wani sonta yake ba amman haka ya auri yarinyar.

"Ammi Wannan fa duk ba Mafita bace, Kowa yana son yayi aure dan ya haihu shima ya sami ɗansa na kanshi tunda Mami tana da matsala wajan ɗaukar ciki yakamata abar shi ya ƙara aure wataƙil Allah ya bashi rabon a jikin wata"
Ammi ta sunkuyar da kanta ƙasa kafin tace.
"Mami yarinya ce mai ladabi ka duba dukkan Mu babu wanda bata ganin darajar shi, uwa uba mahaifiyarta ma mace ce mai son zumunci, bana son ya auro wadda zata tarwatsa mana gidannan sannan yadda matan nan suke da wankakken ido ba kowacce bace zata aure shi dan Allah wata ma dan dukiyar shi zata aure shi, Muyi addu'a Allah ya bawa mami dan ita ce tamu Kome zata zama agidannan tamu ce ba bare ba"

Sadiƙ yabi Ammi da kallo ya kasa fahimtar maganar Ammi kawai yadai fahimci Ammi tana tsoron kada Aliyu ya auro matar da yake sone tazo ta rabasu shiyasa ta aura masa mami sabida tasan baya son mami biyayyace yake mata sannan kuma bayan haka tasan kome mami zata zama ta tace tunda ƴar yayarta ce.

Sallama yayi mata ya nufi masaukin shi ya kwanta Cike da tunani kala kala sai da Asubahi suka haɗu da Aliyu a masallaci.

Cikin barkwancin da yake jan Ya sadiƙ dashi dan in kana son kaga Aliyu ya sake sosai to Sadiƙ na wajen sabida shaƙuwar da sukai da Sadiƙ Aliyu baya Ɓoye wa Sadiƙ komai nashi kamar yadda Shima sadiƙ ɗin baya ɓoye masa tun asali basu da abokai awaje su biyu ne aminan juna wanda ko Ammi bata san wani sirrin nasu ba.

"Ah Babban yaya kaine agidan namu?"
Aliyu ya faɗa yana murmushi.
Sadiƙ yace.
"Ba dole ka ganni ba tunda kai min waya hankalina bai kwanta ba wallahi yaya mamin?"
Aliyu yayi murmushin gefen baki haka suka jera zuwa sashin Ammi a falo sukai zaman shan baƙin shayi har wajan takwas suna tare da sadiƙ Aliyu ya miƙe yaje yay wanka ya dawo cikin shirin tafiya Bashir ya fito Musa ne ya kaisu airport Bayan sunyi sallama da Sadiƙ wanda zai je ya dubo mami sai ya wuce lagos shima..........
AUTA 09022260850

*RABO YA RANTSE...!!*🌹
          
           *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *004*

Baƙa ce sosai irin baƙin nan mai ɗaukar ido dan fuskarta har maiƙo take yi ga wasu ƙuraje da suka cika fuskar tata ƙananu Tana da Ƙananun ido marasa girma da gajeran hanci ba zaka sanya ta cikin Mata masu tsananin kyawu ba Bata da tsayi sosai ƴar ƙarama ce kamar zaka hureta ta faɗi sabida ƙanƙantarta sai dai daga samanta acike take dam haka zalika ƙasanta ma ta wajan hips ɗinta a cike yake dam amman tafarar ɗaya ba zaka hango hakan ba har sai ka ƙura mata ido Tana da wani irin jiki Wanda ake ce masa karuwan Jiki mai ɓoye halittar jikin mutum, Yanayin jikinta shiya ɓoye mata shekarunta wanda tana cikin shekaru Ashirin da huɗu da haihuwa amman in ka dube ta sai kace ƴar shekaru goma sha shidda zuwa sha bakwai ce, sabida ƙanƙantarta yawanci Ƙawayenta basa kiran sunanta sai dai suce mata bakwaini wannan suna In taji sun gaya mata shi faɗa ake da ita sosai sabida kowa yasanta bata barin kota kwana ƴar hayaniya ce FARHA kenan wadda sunan ta na Asali shine Fatimah Ƴar gidan Malam Abubakar Mai Bulo dake Ɗandago wanda jama'a kewa gidan laƙani da gidan Cida kai ko gidan yawa sabida tsabar yawan ƴaƴan babansu Malam Abubakar mai Bulo shine tasa kowa a gidan yake fafutukar abin da zai ci dan tuni Mahaifin nasu ya sallamawa kowa ce mace nauyin kanta ita da ƴaƴanta sabida tsabar yadda nauyi da rashi yayi masa yawa Mata uku ne agidan su Farha Babar su Hadiza Nada Ƴaƴa Goma Babar su Ruƙayyah nada ƴaƴa Goma babarsu farha nada Ƴaƴa Biyar Gaba ɗaya ƴaƴan gidan su ashirin da biyar ne cif.
Malam Abubakar mai bulo mutum ne mai son ya kyautatawa iyalinshi ada sanda yana dashi anji daɗi agidanshi dan wadatar sa ma ita ce ta saka ya tara mata har uku da ƴaƴa batare daya ji wata shakka ba, sai dai yau da gobe ga girma ga nauyi yasa abubuwan suka caɓe masa hakan tasa yaja tagumi ya zubawa matan sa ido yanzu haka suke buga buga dan asirinsu ya rufu wani bin inya sa mu yakan ƙoƙarin wajan yaga ya kawo gida mai girki ta sarrafa sai dai akan Shinkafa Rabin kwano ana iya bawa hammata iska acikin gidan Musamman da Farha wadda ita bataƙi tai dambe da ɗan ƙaramin yaro akan shinkafa loma ɗaya ba, in suna faɗa akan abinci agidan tamkar basu taɓa cin abincin ba haka suke cika gidan da hayaniyar su har maƙota sai sun shigo rabo ga matan ko wacce ba haƙuri daga ana faɗan kowacce ɗanta take tare wa Malam Abubakar mai bulo ( kawu ) mutum ne mai zafi manyan ƴaƴan sa  da ike mata ne suna gama primary ya aurar dasu suma sauran ƴammatan sabida yadda zamani yazo ne da ƙyar aka shawo kanshi ya barsu suke karatun bokon waɗanda suke duk ƙannen farha ne Don ita farha ma ta kammala karatun ta a F.c.e kano inda ta sami diploma a ɓangaran mass communication kuma Cikin ikon Allah ta sami nasarar amsar result ɗinta wanda bata da wata matsala sabida tana da hazaƙa sosai, amman in kaga ƙannen farha sai ka rantse Yayinta ne.

Ƴaƴan ɗakin su farha Yaya sadiya tai aure Yaya Nafisa tai aure Fa'iza tai aure wadda farha take bi yanzu haka daga farha sai ƴar ƙaramar ƙanwarta mai suna ikram wadda ita ce autar umman su farha.
Suma ƴaƴan ɗakin Babarsu Hadiza wadda take itace uwar gida matanta takwas ta aurar da uku saura biyar hadiza ce Babba yanzu a ƴammatan tana shekarar ƙarshe a secondry sai ƙannanenta mata da suke tawosa sai maza samari guda biyu waɗanda suka girmewa Farha sai ƴaƴan babarsu Ruƙayya itama ta aurar da biyu yanzu haka akwai shida agabanta Ruƙayya ce Babba a ƴammatan gabanta sai sauran sai maza biyu suma samari Ɗaya ƙanin farha ɗaya yayanta Umma mahaifiyar farha bata kai sauran matan gidan jin jiki ba sabida bata da nauyi da yawa sosai tana kuma sana'arta ta wankau sai dai yawanci kuɗin basa zama daga an samu ake kashewa Musamman Lokacin da Farha na makaranta sabida umma ce ke hidimar taimakon farha akan karatun nata wanda ta ƙwallafa rai akan sai ta karanci aikin jarida, Haka Umma ta tsaya akan karatun farha da taimakon Salim saurayin farha ɗan Abokin kawu wanda tun kafin farha ta taso Salim ke hidima da ita suna son junan su sosai Salim yana kashewa farha kuɗi sabida ɗan kwari ne anan yake sayar da atamfofi Yayi nacin ya kawo kuɗi Gidansu farha Lokacin da tagama karatu tace ya bari ta sami aiki sabida taga yadda Iyayenta mata ke shan wahala agidan su akan neman abinda zasu ci ba ason ran kawu farha ke zaune ba aure ba ga zabga zabgan ƙannenta nan duk sun taso sun cika gida yafi son ya soma aurar da ita kafin ya aurar dasu Ruƴayya waɗanda zasu kammala karatun su na secondry a wannan shekarar Kawu mutum ne mai zafi abu ƙanƙani in yaji ɗansa yayi yakan iya kullo ƙofar gida ya zane shi tas ya huce dukkan baƙin cikin talaucin sa akan ɗa bai ƙi ya karya ɗa ya aje uwar sa tai jinya ba shiyasa duk hayaniyar ƴaƴan gidan daga kawu ya shigo zakaji sunyi tsit kamar Ba Wani ɗan adam dake rayuwa acikin gidan.

Ta shirya cikin baƙar doguwar riga wadda ta yane kanta da baƙin mayafin doguwar rigar ta ɗauki jakarta bayan ta dubi ƙanwarta Ikram wadda bata fi shekaru goma ba tana zaune a saman tabarma tana shan koko.
"Ikram jeki ɗakin kawu kiwa ummammu magana ni zan fita"
Ikram ta tura baki gaba tana hararar Farha.
"Kutss ni kike harara Auta? dan ubanki ni sa'arki ce dan wa nake fafutukar fita neman aikin, idan danni da Umma ne sai mu sha ruwa mu kwanta jiya ina ba haka kikai ta mana kukan yunwa ba"

Ikram ta miƙe aguje ta fita daga ɗakin sanin halin farha na rashin haƙuri yanzu sai ta hau jibgarta.
Ummah dake ɗakin kawu taje kai masa kokon karin kumallo ita ta dubi Ikram wadda ta faɗo ɗakin tana nishi.
"Auta meye haka zaki shigo ɗakin Kawunku da gudu?"
Ikram data san halin kawu wanda ta haɗa ido dashi yana zaune saman darduma da sauri ta koma da baya tana cewa.
"Ummah wai yaya ce zata fita shine tace in gaya miki"
Ummah ta dube ta.
"To kuma sai kin yi gudu daga ɗakin zuwa nan"
Ikram ta koma bata bawa umma amsa ba sabida yadda taga kawu na zabga mata harara.
"Nifa Hasiya na gaji har ga Allah, lamarin ku keda ƴarki ya isheni haka tace candy na barta tace cigaba da karatu na barta wai mai kuke nufi da Salim ne?"
Bai jira amsar ummah ba ya cigaba da cewa.
"Maganganu ko ina nata tashi a cikin unguwa ance cin kuɗin sa muke alhalin ba bashi ƴarmu zamuyi ba, To ni Allah ya gani kuma shaida ne ban taɓa amsar ƙwandalar yaron nan akan Fatimah ba, Hasalima sanin danai wa mahaifinsa a matsayin sa na aminina yasa naji yaron ya ƙara shiga raina amman kun kafe sai tai karatu ta gama kunce sai ta kama aiki to nikam na gaji wallahi kuna kaini bango sai dai ta nemi wani uban bani ba dan nagaji inji dana gabana ma mana haba jama'a"
Umma tai ƙasa da murya sabida ƴan laɓe dan sana'ar matan gidan ne.
"Kayi haƙuri ka ƙara mana lokaci in sha Allah daga lokacin da zaka ƙara ba zamu haura ba"
Kawu yace.
"To kice mata na bata wata guda salim ya aiko na aurar da ita inta ƙara haura hakan to ta nemi wani uban ba Habubakar ba"
Daga haka yaja rediyon shi ya kunna yabar umma riƙe da haɓa.
Tashi tai ta fita tsakar gida cin karo tai da Babarsu Hadiza wadda tai saurin Komawa da baya tana sosa kai Umma tasan labe tai musu anjima kaɗan kawu na fita zata kwaza maganar a tsakar gida yanzu shakkar kawun ce ta hana tai mata habaici.

Umma ta ƙarasa ɗakin.
"Umma ni fita zanyi sabida na gaya miki wannan ƙawar tawa tace yau yayansu yace zamu ga mutumin nan mai gidan rediyon kin san sabuwa ce tashar ana buƙatar sabbin ma'aikata"
Ummah ta bita da kallo.
"Ke ko ɗan man leɓe da hoda ba zaki saka ba? gaki baƙa kin ɗauki baƙaƙen kaya kin lafta babu wani armashi a shigar taki..................
09022260850
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
          
           *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *005*

Farha ta tura baki gaba ta cinno shi sosai nan da nan ta fara sosa ido kamar zatai kuka.
Muryarta a shaƙe ta soma magana.
"Haba umma wani irin ba armashi a shigata  nida zan je wajan neman aiki kwalliyar me zanyi, nifa umma ba kyakykyawa bace koda nai kwalliyar ma ba kyau zata min ba nafi son fuskata a haka nidai fatana Allah yasa yau na dace dan wallahi har na gaji da zirga zirga"
Ta ƙare maganar tana langwaɓar da kanta kamar wata ƙaramar yarinya koda yake in ba Sanin shekarunta kai ba tabbas zaka ɗauka irin ƴar ƙaramar yarinyar nan ce.

Umma takai duba wajan kofin kokon data ajewa farha wanda bata shaba tace mata.
"Ga kuma kokon naki baki sha ba, kin san dai ba wani kuɗin abinci zan baki ba iyakaci na baki Kuɗin mota daga nan zuwa ƙofar nasarawa nawa zasu kaikin?"
Farha tace.
"Ki bani ɗari biyar inda canji sai na dawo miki dasu, sannan kokon nawa ki rufen inna dawo zan siyo awara wajan Babar su Ruƙayya na haɗa naci yanzu sauri nake kada na makara"
Ta kai maganar tana buɗe handbag ɗinta.
"Kinga umma bani da canji a jakar tawa ma, bari nai sauri zan duba agogo a ɗakin su Ruƙayya tunda ba waya a hannuna yanzu tunda tawa ta faɗa rijiya shikenan"

Umma ta kunce Haɓar zaninta ta ciro Tsohuwar Ɗari biyar ta miƙowa Farha tana ce mata.
"Ni gwarama da wayar taki ta faɗa rijiyar sarai kin san abin magana bayawa kawun ku kaɗan, tunda ya saka dokar hana riƙe waya gwara kin haƙura in kinyi auren kya riƙe ta sannan kuma ki sauri yau karki kai yamma dan jiya baki je Islamiyar dare ba nan yazo kamar zai kawon duka sabida faɗa kin san dai halin sa"

Farha ta rufe handbag ɗinta, Bayan ta saka Kuɗin aciki.
"Umma duk su Ruƙayya da wayoyin su nima Salim yace zai kawon in ya dawo daga lagos nina san zagon ƙasa ake min a wajan kawu ba da ban an kai mai rahoto ba ina yasan ina da wata waya Munafukan banza"
Tana faɗin haka ta sanya kanta tabar ɗakin Ummah ta bita da addu'ar nasara.
Ta ɗaga labulan Ƙofar ɗakin su Ruƙayya Tana cewa.
"Mutanan ɗakin nan suna kusa a duba min agogo?"

Babar su Ruƙayya ta Ɗago kai tana wa Farha wani kallo.
"A,a manyan ma'aikata yau kuma ina aka cillah?"
Sarai farha tasan magana ta gaya mata sabida haka sai tace.
"Alkairi muka nufa kuma dashi zamu dawo ƙarfe nawa?"
Babarsu Ruƙayya ta Cije baki tana cewa.
"Ki shigo ki duba mana sai kace ɗakin baƙon kine"
Farha ta Ƙaraso cikin ɗakin ta kalli agogon dake bangon ɗakin sannan ta ƙarasa gaban madubin Su Ruƙayya ta ɗauki Hoda ta shafa ta fesa turare, dan su Ruƙayya ƴan kwalliya ne saɓanin ita da ko hodar ma sai dai ta bi ɗakunan su ta shafa tasu dan bata da ita sabida kwalliya sam bata dame taba.

"Keko farha ko ɗan caro white ɗinnan na zamani ba zaki siya ki goga ba wannan baƙi naki har yayi yawa ki duba kaf ƴaƴan gidannan Kamannin kawun ku suka ɗauko farare tas kyawawa amman ke wallahi kamar ƴar gudun hijira nina rasa mai salim ya gani a tare dake keba Tsaho ba keba wata cikar ƴa mace ba"
Babar su Ruƙayya kenan mai gaɓa gaɓa ita kai tsaye take Nuna ƙyashinta akan farha kuma duk maganar data fito daga bakinta haka zata faɗe ta babu batun ta tauna ta saɓanin Babar su Hadiza mace ƴar bariki sam ƙaryane ka gane inda ta dosa sai dai farha tana lura da kowacce kawai sai dai ka zauna da mutum ne da halin shi kuma ba komai bane ya tsone musu ido ba illah son da Salim yake mata suna ganin duk yafi mazan ƴaƴan su rufin asiri sai kuma karatun datai musamman wannan aiki da take nema ya tsone musu ido shiyasa ko wacce ta dage sai ƴarta tai karatu sabida suma su sami aiki in sun gama baƙin cikin su ƙiri ƙiri baya ɓuya Wanda suka haɗewa Umma kai su biyun ba'ajin kansu Gwarama ƴaƴan babu ruwansu ta wani bin amman wataran in iyayen suka zugo su haka za'aita bala'i agidan har sai kawu ya tsawatar in kuma aka shirya shikenan.

"To babar su Ruƙayya in dai kawu ne ya haife ni ai shikenan kyau kuma tunda su rukayya nada shi na bar musu suje suyi gasar shi"
Daga haka ta ɗaga labulan tabar ɗakin tana gab da kaiwa soro taci karo dasu humaira Ƙannenta ƴaƴan su babarsu rukayya suna dambe akan kwaɗan kwaki tsaki farha taja aranta tana takaicin wannan ɗabi'a ta yaran gidansu a kullum tana addu'ar Allah ya bata abin da zata wadata gidansu da Abinci.

Har takai bakin titi wannan takaici bai bar ranta ba Suke nan kullum cikin dambe akan abinci kamar wasu mayunwata har ƴan layi sun shaida su tana nan tsaye a bakin titi Allah ya bata adaidaita sukai ciniki dashi akan zai kai ta  ƙofar nasarawa akan naira ɗari biyu tafiyar ba wahala sabida babu cunkoso a titi bayan ta sauka ta bashi kuɗin sa ya ciro canji ya bata layin gidan su ƙawarta shema'u ta shiga tana tafe tana sauri haka ta shiga gidansu shema'u ta tarar da ita Itama tana shiri tana ganinta ta washe baki.
"Ƴar halak yanzun nan ya gali yake maganarki dafatan dai kinzo da komai naki?"
Farha tai dariya.
"Da takarduna nake kwana fa a jaka sabida kiran kota kwana, ina mamanku?"
Shema'u tace
"Tana wajan aiki bara na masa magana sai mu tafi"
Shema'u ta faɗi tana ɗaukar mayafinta Jim kaɗan suka fito tare da Ya gali Farha ta rissuna ta gaishe dashi ya amsa yana sakin murmushi suka jera zuwa bakin titi ya samar musu adaidai ta zuwa Inda Gidan rediyon yake a titin audu baƙo way ne A bakin gate mai ɗan sahun ya sauke su suka bashi kuɗin shi, Farha ta kalli saman gate ɗin inda aka rubuta GARKUWA RADIO da manyan harufa  ya gali ne agaba su kuma a bayan shi.

Haka suka shiga cikin gidan radion sun jima a zaune kafin suga Md ɗin wanda yace su shigo office ɗin shi bayan sun gaisa ya fara duban shema'u yana cewa yaga takardun nata ta miƙa mai sannan ya karɓi na Farha.
Ya jima yana duba takardun  nasu kafin ya dubi Ya Gali.
"Gali kasan fa wannan tashar tamu sabuwa ce gaskiya muna buƙatar gogaggun ma'aikata waɗanda suka san kan aiki su waɗan nan yaran da alamu ma basu taɓa yin harkar ba"
Caraf farha tace.
"A,a wallahi lokacin da muke school an taɓa tura mu gidan radio kuma ba laifi mun sami gogewa a wani ɓangaran"
Md yayi murmushi kafin yace.
"To shikenan babu matsala In sha Allah gobe da safe ku dawo domin muyi muku screening, In mun sami abin da muke nema a tare daku shikenan"
Farha harda zamowa daga saman Kujerar da take zaune.
"Dan Allah ka taimaka mu sami aikin nan musammam ma ni dana ke ta zarya kaga yau zuwa na kusan uku kenan Ban sami ganin kaba, sai yau da Ya Gali yace mu tawo tare dashi"
Daga Md Har Ya Gali da shema'u dariya suka sanya mata sabida yadda tai kamar zatai kuka.
"Karki damu Fatimah Ko?"
Da sauri ta ɗaga kanta.
Sannan Managern director ɗin ya cigaba da cewa.
"Mudai fatan mu wannan tasha tamu ta sami karɓuwa ta ɗaukaka tai suna wannan shine burina"
Da sauri farha tace.
"Wallahi zamu yi iya yinmu ko kasuwa ka turani nikam zuwa zanyi"
Sosai aka ci dariyarta a wajan haka sukai sallama suka baro Office ɗinsa A bakin gate suka rabu Ya Gali ya basu kuɗin adaidaita shikuma ya tafi Inda zashi har suka rabu da shema'u dariya shema'u kewa farha sabida yadda tai ɗin kowa ya gani sai yaci dariya.
Bata damu ba ita dai burin ta Allah yasa ta sami wannan aiki haka ta wuce gida a bakin titi ta sauka ta ƙarasa Cikin layin su da ƙafa ga uwar ranar data ƙwalle sosai. *09022260850*

*RABO YA RANTSE...!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*006*

Idanunta Jajir ta shiga cikin gidansu da gudu ta suri buta tayi cikin banɗaki sai dai taja ta tsaya a ƙofar banɗakin sabida yadda ta tarar da Salima Ƴar ɗakin su Ruƙayya a saman masai tana kashi.
"Dallah ke salima ki maza ki fito kinje kin sami banɗaki kin zauna kamar ɗaki"
Cewar farha tana rawar diskon Fitsarin daya kama mata marar ta.
"Ba zata fito ɗin ba ai ba gidan Babanki bane ke ɗaya aikin banza aikin wofi Baki iska kin takura taba"
Cewar Habiba wadda take bin Ruƙayya tana bakin rariya tana wanki.
Farha dama mai jiran ƙiris juyowar da zatai ta ɗaga bokitin wankin Habiba ta zubar tare da wanka mata mari.
Wata ƙara Habiba ta saka wadda ta sanya sauran matan gidan Yowa kansu nan da nan dambe ya kaure da ƙyar aka shiga tsakaninsu.

Babarsu Ruƙayya data kama habiba masifa ta soma yi tana cewa.
"Ai ba habiba bace takar zomon haka kawai kinje yawon gantalinki kin fake da neman aiki ba nasara shine zaki huce masifar ki akan ƴata to kije Allah ya isa"

Halifa daya shigo gidan ɗan ɗakin su Ruƙayya ne shima kuma yayan farha ne a wajan uba Muzurai yahau yi yana tambayar ƙanwarsa mai akai mata take kuka! ƙarya da gaskiya Habiba take gaya masa nan da nan yayo kan farha wadda tai ɗammara da mayafinta tana girgiza jikinta Duka ya kawo mata.
Tai tsalle tayi baya tana cewa.
"Wallahi Halifa in ka taɓani sai na maka illah danni ba ƴar ɗakin ku bace shine zakuyo min taron dangi toni ɗaya ce amman

Please Login or Register in order to submit comment