Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba Bashir bane ya sauke gajiyar shi ajikin su?"
Ammi da ta kuma haɗe rai tamau ita ta dubi salma tare da cewa........
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 34*

"Ai inda Bashir ne ya dake su da ba zakiji wayata ba, sabida ina bashir ze iya musu wannan azababban dukan"
Salma tasha jinin jikinta can kuma tace.
"Ammi Allah yasa ba rashin kunyar tasu suka ma wani a waje ba dan wallahi ba kowa ne ze iya jure halin ƴaƴan kiba Shiyasa kullum faɗan da nake musu kenan wannan tasa yanzu suka min ƙaura suka dena zuwa in da nake don basa son gaskiya"
Ammi tayo kan salma tana cewa.
"Kin fara wa'azin naki ko me shegen iyayi da manyan ce kamar wata uwata to ɗan uwanki ne ya saka waya ya zane su kamar jakai haka ya Mayar min da ƴaƴana wallahi ba dan cikin su ɗaya ba sena maka shi a kotu"
Salma ta kama haɓa kullum Abin Ammi ƙara gaba yake akan su safna su kaɗai ne matsalar Ammin su.
"Ammi akan Su safna zaki maka Yaya Ali a kotu? dan nasan Ya Sadiƙ baya kano tunda kika ce ɗan uwana nina san da Ya Ali kike Ammi meye yayi zafi Ammi Kin san baze dake su There is no reason ba"
Salma takai maganar cikin sanyin halin ta wanda kowa yasan ta da hakan sam bata ɗauki duniya da zafi ba.
"To bari kiji wata matsiyaciyar ƴa musa ya kawon yau kwana biyu wai marainiyace ƴar ƙanin mahaifin sa tunda yarinyar nan tazo gidannan shikenan Ya shiga takura wa ƙannen shi akan ta dan kawai safna zata shiga toilet taje tana buga mata ƙofa akan ta Miƙe ta wanke mata Shine tahau zagin mahaifin safna kin san safna da zuciya koni yaya nake da ita shine fa suka hau kokawa Sajeeda ta fita tana taya safna Wallahi Salama baki yadda ya Dinga dukan ƴaƴan nan ba kalli fa jikin su duk shatin tabon Duka"
Ta faɗa a ƙufule.
Salma taja ajiyar zuciya.
"Ammi Idan na fahimceki Musa P.a ɗin yaya shine ya kawo Maki Ƴar uwarshi amman kamar aiki zata ke Miki Ammi akwai gyara anan shin Kin bibiyi kowa acikin su kin gano me laifin ammi ɗa fa na kowa ne su yanzu su safna ba zasu iya wanke Toilet ba har se me aiki tazo ta wanke Musu kafin su shiga fisabilillahi Ammi wani ɗa namijin ne ze yarda da haka wallahi ni yanzu baban su Dady kafin ya tashi na kammala komai idan ze tafi Office da abincin sa yake tafiya kuma kinga dai ina aiki wani bin har Night duty nake amman Ban taɓa sakaci da hidimar shiba to su waɗannan idan basu saba tun yanzu ba ai ba'a san mijin da zasu aura ba Dan kawai yayan su yana da kuɗi se ya zamana komai se an musu"
Salma ta faɗa tana Hararar gefen su safna.
Ammi cikin ƙosawa da maganar salma tace.
"To idan basu ji daɗi yanzu ba se yaushe zasu ji Da wace irin wiya ce bamu sha ba ke kinga rufa min baki lokacin abu kawai ayi sa idan ya wuce ba za'a yi ba"
Salma tai dariya me ciwo.
"Ammi kenan idan watarana mune watarana ba mu bane mu dinga tina Mutuwa kada ki tafi ba fata nake ba kibar ƴaƴan nan cikin wahala yes wahala mana wallahi Koni ba zan iya Riƙon su da wannan halin nasu ba bare kuma matan Yayye waɗanda basu da tabbas Shi kan shi ya Ali ɗin wani abun ai yana sakar muku ne dan bashi da ɗan kanshi amman bara kiga ya sami matar da yake so da ɗan kanshi idan ance wani ma yayi wani iskancin baze yiba haka kwana ki shima bashir ya kirani yana masifa wai london yake son zuwa ya ƙaro karatu ya Ali yace yayi haƙuri yaje Jami'atul madina sabida Yafi son bashir ya ƙaro Ilimi akan harkar addini sosai ke baki ga yadda ya dinga cin mutunci ba ni ai naso a gaban yayan yayi da ya ci uban shi Shiyasa naji daɗi daya hana shi fita wajan ma kwata kwata ya zauna anan ɗin yara su dinga rashin Mutunci ana ɗaure musu gindi"
Salma takai aya.
Ammi ta ɗaga mata hannu alamar tai mata shuru.
"Da kike min fatan mutuwa ko yanzu tazo ni nagode Allah Kuma da kike Maganar matan yayye ko ba wanda ze riƙen su mami Allah mata albarka zata riƙe min ƴaƴana har ma tafini basu gata zancen ƴaƴa kuma aini nafi son baba ya haihu fiye da kowa sai dai ki gyara batun wata mace ai daga kan mami babu wata mace da zata shigo gidannan Kina kallon akan waccan Filfiwar yana dukan ƙannen shi ina ga kuma ya samo wadda ya aura yake so take son shi Ina da sake ai kodan haka bama zan bari baba yayo wani aure ba haka nan ze hakuri mami ta zame masa matar ƙaddara mutu ka raba takalmin kaza"
Salma tabi Ammi da kallo.
"Ammi duka maganganun ki se naga kamar kina son kanki ta yaya zaki ce baze yi aure ba bayan da Kuɗin sa da ƙuruciyar shi Allah ya huci zuciyarki Ammi su kuma su cigaba da rashin Kunya da ɗaukar baki sun manta dukan daya taɓa min seda yaji Min targaɗe akan abin da bai ka ya kawo ba Nikam Ammi na wuce su Dady zan ɗauko a school Allah ya basu lafiya"
Salma ta faɗa tana ɗaukar handbag ɗinta tabar ɗakin.

Ammi bata iya cewa salma komai ba sabida ita indai akan su safna ne to faɗa take da kowa Bare kuma ka taɓa Mami.

Salma na fita falon suka ci karo da Hajjo dake Ɗebe kayan abincin safe wanda basu taɓa shiba tana jera na rana.
Har ƙasa salma ta zube tana gaishe da hajjo.
"A,a uwar masu gida kece a gidan namu bara na haɗa abinci"
Hajjo ta faɗa tana dariya.
Salma ma dariyar tayi.
"Wallahi Hajjo tafiya zanyi sabida su Dady suna school zan ɗauko su nima kiran ammi ne ya fito dani daga Hospital da ba abin da ze kawo ni nan sabida yara suna makaranta"
Hajjo tayi dariya.
"Allah sarki su Almustapha sarakan ƙiriniya mutanan su safana amman zasu ƙara zuwa mana hutu ko? dan naga Alhaji Ali yana son yaran nan suzo hutu yayta ɗaukar su suna fita siyayya shima dai Allah ya bashi nasa"
Salma tayi dariya.
"In sha Allah hajjo zasu zo ammi ce bata auren dasu faɗa suke amman zasu zo se anyi Hutun School, ai yaya Ali akwai son yara yakan je min jifa jifa amman ba danni ba se don su Dady Dan har yazo ya tafi ma baifi yamin magana ɗaya zuwa uku ba yana can tare dasu suna wasa kin san in yaga yara"
Hajjo tace.
"Haka ne akwai son yara kam Alhaji Ali shima Allah ya bashi"
Salma ta amsa da "Amin" kafin ta buɗe jakarta ta ɗauko dubu biyar ƴan ɗari biyar ta miƙawa hajjo.
"Gashi hajjo kisai Goro"
Hajjo tai dariya tana cewa.
"Ke wai bakya gajiya salamatu Da sallah kimin ɗinki duk da wanda hajiya ammi da Alhaji Ali da sadik ke min kema se kinyi ki sai min ragon layya gashi har wannan shekarar zanje aikin hajji"
Sai ta soma ƙoƙarin yin kuka.
Salma tace.
"Haba Hajjo ai kome mukai miki bamu faɗi ba ai shege shike manta alkairi abin da kikai mana dan kawai kin ƙi yarda da zaman sashin nan ne kika ce Kinfi son na ƴan aiki ai ba da ban haka ba hajjo da ba zaki dinga komai agidannan ba makka ba dan kirata bace ai da ba zakije yanzu ba da tuni kin manta da zuwa"
Salma ta faɗa.
Hajjo tace.
"Allah ya saka muku da alkairi yadda kuka riƙeni Allah ya duba ku ya ƙara muku wadata"
Salma tace "Amin hajjo ina ɗakin ƙanwar Musa?"
Hajjo tace "Muje ciki gashi can"
Suka jera zuwa ɗakin da Farha take ciki tare da Hajjo........
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 35*

Salma ce a gaba sabida haka ita ta soma buɗe ƙofar ta shiga kwance ta hango yarinyar sai shashsheƙar! kuka! take ta dunƙule jikin ta waje ɗaya acan ƙarshen gado.
Gyara Murya salma tayi tare da cewa.
"Assalamu Alaiki"
Farha ta ɗago da ƙyar tana kallon meyin sallamar wadda sam bata ji shigowarta ba sai sallamarta kallo ɗaya tayi mata ta kauda kai kamar su har tayi yawa dashi daga gani babu tambaya itama ƙanwar shice.
Da murmushi a saman fuskar salma ta ƙarasa bakin gadon ta zauna.
Hajjo kuma ta tsaya a gaban madubi Fuskarta cike da tausayin farha take ta faman jera mata sannu.
"Zaki iya tashi? naga fuskarki duk ta haye ta suntume"
Cewar salma cikin kulawa.
A hankali Farha ta saka hannunta a saman gadon ta dafa shi tana Ƙoƙarin tashi sabida gaba ɗaya jikinta ciwo yake mata.
Hajjo tazo da sauri ta taimaka mata suka miƙe.
"Hajjo muje Ki samin ita a mota sauri nake so dole zan ɗan dubata idan yaso zan sanya driver ya maido da ita Ki shaidawa Ammi"
Hajjo tasan salma dama akwai ta da tausayi.
"Allah yayi miki albarka yadda kika taimaki marainiyar Allah kema Allah ya taimake ki"
Da taimakon Hajjo ta saka hajib ta riƙo ta ajikinta har parking space salma ta sanya ta a mota tana ƙara jadda dama Hajjo akan ta sanar da Ammi A back seat farha ta kwanta salma ta shiga driver seat ta zauna ta tayar da Motar suka bar Gidan.

Hajjo cike da bin umarni ta isa ɗakin Ammi bata ciki sai ta shiga ɗakin Ƴammatan wanda ta tarar da Ammi zaune tayi tagumi ta zuba musu ido duk suna kwance kamar zata Shiga Jikinsu sabida kusanci.
"Sannu da hutawa Hajiya Ammi"
Hajjo ta faɗa tana Zama a saman carpet Ɗin Ɗakin

"Yawwa Hajjo salma ta tafi? ga ruwan data sama safna ya ƙare amman tunda ta nuna Min bara na cire"
Hajjo ta kama haɓa cike da al'ajabin langwan ƴaƴan na Ammi kafin tace.
"Wato abin har yakai ga ƙarin ruwa ikon Allah shiyasa yadda na jera abinci haka nazo na kwashe se masu gadi na bawa"
Ammi da take Cirewa Safna allurar Ruwan da aka saka mata tace.
"Hajjo waya ke ta wani abinci ni ai banda kwanciyar hankali har se naga yarana sun dawo yadda suke Kinsan Allah jiri nake ji da ƙyar idan Jinina bai hau ba Yau Baba ya ɓata min rai na ba ɗan kaɗan ba"
Hajjo tayi saurin tare ta tare da cewa.
"Kuma karki sake ki masa baki akan Abin da bai kai ya komo ba dan ke uwa ce"
Ammi dai bata ce komai ba Hajjo ta kuma cewa.
"Dama Uwar masu gida ce tace na shaida Miki ta wuce da ƙanwar Musa zata duba ta dan sunji mata rauni itama amman zata sa driver ya maido miki da ita"
A hasale Ammi ta juyo tana cewa.
"To ina ruwana da ita ni dama daga wannan fitar kada ta dawo Min gidana tsinanniya mai baƙar fuska Tauraruwa mai witsiya ganinta ai baya da alkairi a tare dani"
Aran hajjo tace da yake an taɓa ƴaƴan gwal amman a fili se tace
"Hajiya Ammi shifa ɗa na kowa ne da ɗa da dukiya baka musu Mugunta ki sassautawa marainiyar Allah a ƙa'ida daga ita har Safana basu kyau ta ba duk sun zagi iyayen su"
Ammi ta ɗaga wa Hajjo Hannu tare da cewa.
"Ke kinga sanda akai hakan har da zaki zo kina Faɗin yadda akai da Allah tashi Kije kawai maganar nan ɓata mini raina take"
Hajjo ta kama Haɓa cikin mamakin halin Ammi akan ƴaƴanta.
"To Hajiya Ammi ki haƙuri nayi ba daidai ba meza a dafawa Hajiya ƙaramar Naji kince yau zata dawo"
Bata ko kalli saitin Hajjo ba tace.
"Koma meye ni bata tata nake ba yanzu ta yarana nake"
Adaidai nan sajeeda ta farka tana Jan Numfashi da sauri Ammi tace.
"Hajjo bani ruwan sanyi da ɗan tsumma har yanzu da zafin zazzaɓin a tare da ita"
Hajjo da sauri ta shiga toilet Ɗin su Kaca kaca toilet ɗin ba alamar an wanke ita dai taro ruwan tayi ta kawowa Ammi tare da tsumma fari mai kyau.
Hajjo ce ta taimaka mata ta tubewa Sajeeda riga ta dinga goga mata ruwan sanyin ita kuma sajeedar ta kwantar da kanta a kafaɗar Hajjo tana hawaye.
"Jiba fa hajjo kalla shatin waya har wuyanta kai gaskiya Baba ya cuceni"
Ammi ta faɗa kamar zatayi kuka.
Tana gama gogewa sajeeda Jikinta a hankali ta mayar mata da rigar Jikinta Muryar sajeeda a hankali tace

"Hajjo zan sha tea"

A hankali ta faɗa tana komar da kanta saman pillow ta kwantar Hajjo ta miƙe ta fita dan ta haɗo mata shayin a ranta tana cewa yau fa ba sauƙi an taɓo Kitse a saka ka a rana ka narke a barka a inuwa ka daskare.

Hajjo ta haɗo shayin mai kauri ta kawo mata kurɓa ɗaya tayi tace bata sha agigice Ammi tace "Me kike so a dafa Miki ko asaka driver ya siyo Miki?"
Sajeeda ta girgiza kai alamar bata Buƙatar Komai daga Hajjo har Ammi sannu sukai mata ta koma ta kwanta Safna ma Buɗe ido tayi wanda Ammi ta mayar da kallo kanta tana cewa "Sannu meke miki ciwo yanzu"
Ɓare baki tayi kamar wata yarinyar Goye.
"Ammi ina ga ya karya min hannuna nauyi yake min wayyo Ammina"
Ammi tayi kan safna tana duba hannun ita dai hajjo kama haɓa tai yau tana kallon Ikon Allah safna fatan dankali ta buƙata hajjo ta kawo mata a wulaƙance tasha kaɗan ta ture.

Ammi ta dubi hajjo ido jajir.
"Hajjo jeki ɗakina saman madubi na akwai maganin hawan Jinina ki ɗauko Mini jiri nake ji"
Hajjo ta dubi ammi.
"Haba Hajiya Ammi akan wannan ɗan abu zaki ɗagawa kanki hankali har Jinin ki ya hau Idan Alhaji Ali be dake suba waye ze dake su kada fa ki bada gudunmawa wajan sangarta ƴaƴan ki"
Ammi ta ɗago ido tace wa hajjo

"Ai idan ƴaƴana basu kasheni ba ke kya kasheni da waɗannan maganganun naki zaki ɗebo min kona tashi da kaina"
Hajjo ta Miƙe ta nufi ɗakin Ammi ta kwaso mata magungunan wanda dama tana da hawan Jinin tun bayan rasuwar Baban su Aliyu ta kamu dashi sedai bai fiye tasiri ba sabida tana shan magani Kuma duk ƙarshen wata Aliyu na fita da ita waje ganin Likita waɗannan ƴan watanni nema basu fitan ba sabida tace ita taji daɗin Jikinta ya rabu da ita.

Hajjo ta kawo mata haɗe da ruwan roba ta karɓa ta sha ta kwanta a kusa da ƴaƴanta waɗanda suka sanyata a tsakiyar su.

Hajjo fita tayi ta rufo Musu Ƙofa wato ɗan adam tara yake be cika Goma ba duk yadda Ammi take da Kirki akan ƴaƴanta idanunta rufe wa yake Musamman waɗannan sarakan Guda Biyu basu da mutunci ko kaɗan Kuma baka isa kayi magana akan su ba.
Hajjo ta watsar da tunanin ta Koma kitchen tana cigaba da gyara kajin da zata ma Mami farfesu dan taji ance yau zata dawo.

Bayan fitar Hajjo sajeeda ta Miƙe ta shiga wanka Ammi ta juya tana kallonta "Zaki iya kona zo na taimaka miki?" ta girgiza kai ta shige toilet ɗin ta fito tana Yamutsa fuska "Ammi ba a wanke yake ba toilet Ɗin" Ammi taja tsaki "Ai salma ce da neman suna ta ɗauketa suka tafi Gidanta bada ban haka ba da ba seta zo ta wanke Muku ba" Abin mamaki ammi da kanta ta shiga Toilet ɗin ta hau wanke wa Sajeeda tana tsaye akanta harta gama juyowar da zatai santsi ya kama ƙafarta takwa faɗi tum sajeeda ta ƙwala ƙara tayi kanta tana Ƙoƙarin ɗagata.
Hajjo da gudu data juyo Ihun tayo ɗakin ganin Halin da Ammi ke ciki ya ɗaga mata hankali tana kwance Cikin Kumfar banɗaki da taimakon Hajjo Suka fito da Ammi wadda har ƙafarta ta haye tai sumtum abun ka da farar fata.
"Garin yaya Hajiya ammi Allah ya sawaƙe"
Cewar Hajjo sajeeda tace "Wai Toilet ta shiga ta wanke min zanyi wanka shine fa ta Faɗi"
Ammi ta matse fuska saboda yadda ƙafar ke mata zafi.
"Hajjo ɗauko Min man zafi a ɗakina"
Hajjo ta fita ta ɗauko mata man zafin ta kawo mata.........
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 36*

Hajjo ta rissuna har ƙasa ta miƙawa Ammi man zafin.
Ammi ta rintse ido sabida yadda ƙafar ke mata azababban zafi.
Muryar ta abin tausayi tace wa Hajjo.
"Shafa min daga saman Yatsuna"
Hajjo ta lakato man zafin ta soma goga mata a yatsun ƙafafun nata waɗanda duk sun haye sunyi suntum Hajjo se faman sannu take jerawa Ammi Ita ko Sajeeda wankan ta tashiga ta fito ta zauna gaban madubi ta shafa mai ta zira riga ta kwanta hajjo ta bita da kallo Ammi kwanciya ta kuma yi nan da nan zazzaɓi ya rufeta ruf Hajjo ta baro ɗakin ta wuce kitchen ta cigaba da aikin dake gabanta.

Tunda suka hau kwalta salma ke sharara gudu har ta ƙarasa unguwar sharaɗa Sai da ta biya ta ɗauko Ƴaƴanta a school sannan suka wuce gidanta Haɗaɗɗan ƙaton gida mai Jan gate tai horn mai gadi yazo ya buɗe mata gate ɗin ta tura hancin Motar ta ciki ta shiga tai parking.

Yaranta farare masu kama da ita suka fito daga gefenta suka tsaya salma ta zaga can back seat inda Farha ke kwance ta buɗe tace mata.
"Ki sauko a hankali mun iso"
Farha ta yunƙura a hankali ta sauko daga cikin motar yaran suka bita da kallo salma ta kama hannunta suka miƙi wata hanya wadda ta kaisu Ƙofar Ƙaton Falon sanyi da ƙamshi ne sukai wa farha sallama a cikin hancinta ta lumshe ido ta nemi guri ta zauna Mai aikin Salma nata zirga zirga daga kitchen zuwa dining wadda ke girki iya na rana sabida yaran salma dake makaranta da sun dawo suci sai wanke wanke da shara amman sauran Hidimar girkin mai gida da gyaran ɗakuna duka salma ke yin kayanta bata yarda mai aikin tata tayi mata ba.

"Maman Dady sannu da zuwa yaya aiki?"
Mai aikin salma ta faɗa mata hakan bayan ta ƙaraso wajan
Salma ta dube ta da kulawa.
"Lafiya lau zuwaira yaya hidimar Gida?"
Zuwaira mai aikin Salma tace.
"Lafiya lau"
Tana kama hannun yaran suka nufi hanyar ɗakin su.
Salma ta dubi farha data zauna a ƙasan carpet tace mata.
"Taso muje ciki bakya zauna anan ke kaɗai ba"
Ta miƙe suka jera zuwa cikin wani ɗaki wanda ƙaramin gado ne acikin sa sai Toilet da carpet shinfiɗe a ƙasan sa.
"Ki zauna anan bari nayi wanka na fito"
Farha ta jinjina kanta Bayan ta zauna a ƙasan carpet ɗin kanta ne ke mata wani irin ciwo har ganin ta na neman juyewa.
Sama sama taji muryar salma akan tana ce mata.
"Me zakici na kawo miki seki sha magani ki kwanta ki huta"
Ta ɗago tana share hawayen ta.
"Dan Allah maman dady ki bani kuɗin mota na tafi gida"
Ta faɗa kamar yadda taji mai aikin nata ta faɗi sunan nata.
Neman gefen gado salma tayi ta zauna ta dubi farha wadda take kuka.
"To yanzu idan na baki kuɗin mota kin san hanyar garin ku?"
Da sauri ta ɗaga kanta tana cewa.
"Na sani maman dady dan Allah ki taimaka mini"
Salma tayi jim kafin tace

"To Amman shi musa daya kawo ki idan har yaji bakya wajan Ammi ai ranshi ze ɓaci"
Kukan farha ta cigaba dayi tana cewa.
"Baze ce komai ba daman nina jawa kaina Nace masa ina son aikatau to tunda abin ya zama haka gwara na koma gida"
Farha ta faɗa har lokacin kuka take

"Ina ne garin naku ni sai na saka driver na ya kaiki amman baze yuwu a sakeki ke kaɗai ki tafi ba sabida hakan ze zama matsala babba"
Gaban farha ya faɗi ita anya ma suna da ƙauye kuwa ita dai a tarihin ta bata taɓa jin kawu ko umma sunce zasu ƙauye ba duk ƴan uwansu suna cikin gari.
Ƙifta ido tai tana inda inda.
Fahimtar Hakan yasa salma cewa.
"Kinga hakan bamai yuwu wa bane tunda naga kamar kanki be waye da hanya ba, Zan kira yaya se ya turo min da number musa sena kira shi yazo nan ya tafi dake"
Gaban farha ya kuma faɗuwa tasan idan har ta gaya masa baze bari ta barta ta tafi ba.
"Maman dady zan fa gane kedai ki taimaka min na tafi ko ma baki bani kuɗi ba ki barni na fita zan san yadda zanyi har naje gida"
Salma ta miƙe ta fita daga ɗakin batare data yi magana ba.

Bedroom ɗinta taje ta ɗauko wayarta Numbern Aliyu ta shiga kira sedai taƙi shiga sai da ta fito daga ɗakin sannan Number ɗin ta shiga taita ringing bai ɗauka ba.

Haka ta dawo ɗakin da farha take zaune.
Ta ɗaga murya ta kira zuwaira.
Da sauri zuwaira ta ƙaraso.
"Maman Dady kira kike gani"
Salma ta dubi zuwaira

"Dan Allah zuwaira ki haɗo wa wannan baƙuwar tea mai kauri da ɗan Abu marar nauyi, sannan ki bawa su dady abinci su tafi islamiyya"
Zuwaira da ladabi ta amsa kana ta fita daga ɗakin

Minti kaɗan ta dawo ɗakin da ƙaton tray a hannun ta ajewa tayi a gaban farha salma ta dubi farha

"Ci abincin amman ki fara shan tea ɗin kafin kici abincin sabida ya warware miki hanjin cikin ki"
Farha ta ɗaga Cup ɗin tea ɗin ta sanya spoon tana juyawa ta ɗaga shi tana kurɓa kamar maɗaci take jin bakin ta dan kwata kwata babu ɗanɗano ta kurɓi ɗaya biyu uku sai amai ya biyo baya awajan ta dinga kwara amai tana riƙe ciki salma nata jera mata sannu anan wajan ta kwanta tana numfashi salma ta gyara wajan ta taimaka mata suka je toilet ta wanke mata Jikinta saman gadon salma tace tahau jikinta se rawa yake zazzaɓi ne ya rufe ta ganin ta galabaita da yawa yasa salma ta shiga ɗaki ta ɗauko allura da drip ta tsira acikin drip ɗin ta haɗa ta saka mata Allurar harda ta bacci aciki salma ta rufe mata jikinta da bargo bayan bacci ya ɗauke ta taja mata ƙofar tabar ɗakin.

Se wajan la'asar ruwan ya ƙare salma ta cire mata har lokacin Bacci take Bini bini salma zata leƙa amman har aka kira Magariba bata tashi ba salma na idar da sallar magariba taga kiran Aliyu.
Ta ɗaga cikin ladabi tayi sallama tana gaishe dashi.
Cikin taushin muryashi yace wa salma.
"I'm sorry salma naga kiran ki, But kin san kan ƴan mazan a wajan nema ɗaukar zafi yake hope kuna lafiya yaya su Babana?"
Salma tayi murmushi.
"Lah dama nayi zaton haka Yaya Suna lafiya Allah ya taimaka, dan Allah yaya numbern musa zaka tura mini in ba damuwa"
Batare da tunanin komai ba dama shi bai da yawan bincike akan lamarin wani ko ya saka idanu akan Harkar da ba'a saka shi acikin taba.
Yace mata.
"Okey ba matsala amman yanzu haka na fito daga masallaci zan je gida zuwa anjima zan tura maki"
Salma tai saurin cewa.
"Yaya ko kawai bara kaji maganar wannan ƙanwar tashi ce"
Da rashin gane inda ta dosa yace mata.
"Wa kike nufi kenan?"..............
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*








Ya matsa kusa da farha kaɗan yaɗan ja bargon ya ɗora hannun shi a saman goshinta babu zafi a goshin nata.
Buɗe Idanunta tayi wanda har Lokacin bai ɗauke hannun shi a goshin nata ba.
Gabanta ya faɗi ta mayar da idanun ta Lumshe.
"Sannu"
Ya faɗa a hankali.
Ta yunƙura zata tashi jiri ya ɗebe ta, ta koma ta kwanta tana jan numfashi hannu ya sanya ya ɗagota ya jinginar da ita ajikin Bango idanunta har Lokacin a rufe yake.
"Kin yi sallah me zaki ci?"
Duka ya jefa mata tambayoyin.
Banza tayi masa dan yanzu bata son magana mai tsaho ta dinga haɗasu sabida ta fahimci ya iya danƙara baƙar magana.
"Wai ke kurma ce ina miki magana kin min banza"
Ya faɗa a hasale.
Adaidai nan salma ta shigo.
"Afuwan yaya ina hidimar babansu ne, yawwa Kin tashi ki ƙoƙari kiyo alwala ki sallah se kici abinci Yaya ina zuwa dan Allah ina haɗawa Baban su abinci ne"
Bai mata magana ba ta fita farha ta miƙe ƙafafunta ta dafa bango ta yunƙura ta shiga toilet ya bita da kallo wato yau ba bakin tsiwa tana rashin lafiya.
Tayo alwalar ta fito juya ta

Please Login or Register in order to submit comment