Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*RABO YA RANTSE...!!*🌹
          
           *NA*
*AUTAR MANYA*


Bisimillahi Rahmanir Rahim

       
             *001*

Ya zuba wa likitan jar fuskar shi yana binsa da kallo da manyan idaunshi waɗanda suka rine daga farin su na asali zuwa jajir har wani ruwa ne ya kwanta acikin su gaba ɗaya jijiyar dake kanshi ta miƙe, shi kanshi likitan bai iya haɗa ido dashi ba sabida yadda halittar idanun nashi ta sauya ta jirkice kai kana kallon shi kasan yana cikin tashin hankali ba ɗan kaɗan ba.
A hankali likitan ya ɗauko gorar ruwa daga cikin frij ɗin dake office ɗin shi ya ɓalle murfin ya miƙa masa, bai musa ba ya amsa ya kafa kanshi a saman gorar wadda bai ajeta ba sai da ya shanye ruwan tas! wanda gumi ya sami damar yanko masa ta kowa ce kafa ta jikinsa tamkar babu na'urar Ac acikin office ɗin.
Sai dai har lokacin idanun nashi basu sauya launi ba wani ƙaton abu ne ya zo ya tokare masa maƙoshin sa zuciyar shi tai rauni a lokacin yasan kuka ma rahma ne in da zai iya da yayi sai dai taurin dake cikin zuciyar shi irin na jaruman maza sadaukai Masu tawakkali da yarda da ƙaddara shine ya bashi damar yin dakiya acikin wannan lamari da ya kuma afkuwa a gare shi.

"Doctor kana nufin wannan karon ma nayi asarar Beby na a karo na Huɗu?"
ALIYU ya faɗa cikin Sanyi murya kamar ba tashi ba.
Doctor ya dube shi.
"Kayi haƙuri yallaɓai haka Lamarin Allah yake, Ka ɗauka haka ya tsara maka ma a wannan karon"
A hankali ya shafo tulin sumar dake kanshi wadda take a nannaɗe irin ta fulanin asali ɗinnan baƙa irin wadda tai kamar an shafa mata relacxa bai ce komai ba har wajan mintuna goma.
Kafin yace.
"Muje doctor a ɗibi jinin nawa a ƙara mata ina fatan tana cikin ƙoshin lafiya?"
Likitan ya miƙe yayi gaba yana cewa.
"Har yanzu bacci take, bata riga ta tashi ba"
ALIYU bai ce komai ba yabi Likitan zuwa ɗakin ɗiban jinin sai da aka ɗibi leda uku a jikinshi sannan likitan yace masa ya kwanta a wani ɗan gado dake ɗakin dan ya sami Hutu.
A hankali ya miƙe yana rangaji yabar Ɗakin batare daya tankawa Likitan ba, a harabar rantsatstsan asibitin Kuwa Jama'a ne Burjik mafi aka sarin su ƴan uwan ALIYU ne na jini sai ƴan uwan Matar tashi.
Da sauri Musa Yaron shi ya taso ya kamo shi yana cewa.
"Sannu oga ai da ka kirani dana zo na taimaka maka"
Idanun ALIYU da suka fara rufewa ya ɗago ya dubi Musa murya a hankali yace masa.
"Musa kaini gida please"
Jikin musa na rawa ya ɗaga murya ya kwaɗawa drivern ALIYU kira wanda ya taso da sauri ya shiga cikin wata baƙar jeep wadda tsayawa faɗin tsadar tama Ɓata baki ne ya ƙaraso gaban su Musa ya taimakawa ALIYU ya shiga cikin motar ya kwantar da kanshi jikin Kujerar motar ya lumshe idanun shi driver yaja motar ƴan uwan ALIYU suna ta ɗaga mai hannu duk jikinsu a sanyaye.

Motar bata tsaya a ko ina ba sai a ƙofar gidan Shugaban kamfanin sayar da manyan motoci da ƙananu wanda ke garin kano da kuma lagos da abuja mai suna  *MADAKI MOTOR'S* kuma shine mai bawa  gwamnati mai ci a yanzu shawara a ɓangaran *MATASA* Ko ina ka duba pasta ce mai hoton ALIYU tun daga farkon Titin Gidan wanda ke unguwar ƙofar Na'isa,har zuwa jikin ginin gidan wanda aka rubuta *HASKEN MATASA TALLAFIN MATA DA ƘANANUN YARA*
Da gudu masu gadin gidan suka wangale ƙaton gate ɗin wanda motar da ALIYU ke ciki ta kutsa kai cikin ƙaton filin adana motocin dake gidan wanda yawan motocin wajan kaɗai in ka gani sai ka shiga ɗimuwa, Masu gadin da sauran ma'aikatan gidan tuni sun zagaye motar kowa Burin shi Yaga halin da ALIYU yake ciki sannan yayi masa jaje akan abin da ya same shi Musa ne ya taimaka mashi zuwa part ɗinshi wanda ko masu hidimar gidan basu sami Zarafin yin magana da ALIYU ɗin ba.
A hankali ya nufi haɗaɗɗan Parloun shi wanda ya gaji da haɗuwa Ko ina ƙamshi da sanyi ne ke tashi ga masu hidimar part ɗin suna ta kaiwa da komowa baya amsa gaisuwar da suke masa haka yaja ƙafafun shi da sukai masa sanyi ya haura saman shi kai tsaye bedroom ɗinshi ya nufa ya faɗa ƙaton katafaran gadon shi idanun shi ya rufe ruf yana sakin numfashi.

Gaba ɗaya masu hidimar gidan jikinsu yayi sanyi na yadda suka ga uban gidan nasu duk da bamai yawan magana bane amman sanyin shi na yau kaɗai yafi na koda yaushe.

A Ƙaton parloun ta tana ta sintiri hannunta goye a bayanta taka sa zaune ta kasa tsaye tana ta faman kiran Numbobin ALIYU bai ɗauka ba cikin sauri wata dattijuwa ta shigo parloun ta dubi Matar dake sintiri a parlon babbar macece sosai dan ta manyanta a shekaru sai dai a fuska da jiki zaka ga ba sosai shekarun nata suka fito ba sabida yadda take cikin hutu da jin daɗi Kallo ɗaya zakai mata kasan ita ce mahaifiyar ALIYU sabida yadda kamannin nasu ya fito sosai kamar tayi kaki ta tofar haka suke da ALIYU bata da jiki sosai fara ce tas kana kallonta kaga Bafulatanar asali.
"Ranki ya daɗe Alhaji ya dawo sai dai jikinsa duk a sanyaye yake wanda bamu san halin da hajiya ƙaramar take ciki ba"
A hankali Matar ta juyo ta kalli dattijuwar wadda tai saurin yin ƙasa da kanta fuska babu walwala tace.
"Nagode Hajja jeki kitchen ki ɗora mana abincin dare"
Daga haka ta Nufi ɗakinta wanda tsayawa faɗin tsaruwar sa ma ɓata baki ne Mayafi ta ɗauka ta fita daga Part ɗin nata ta nufi wanda ALIYU ya shiga Tun farkon shigowar sa Duk masu hidimar sashin ALIYU sun shiga nutsuwar su sabida ratsowar Ammi mahaifiyar ALIYU Ɓangaran sai zubewa suke suna miƙo mata gaisuwa  bata amsawa hasali ma ko kallo basu ishe taba haka ta wuce babban parlon shi ta haura saman kanta tsaye ta shiga ɗakin baccin sa.

Ta ja ta tsaya a kanshi tana Mai zuba masa idanunta tsananin tausayin yaron nata na ratsa dukkan Jikinta.
"Yanzu kai ba da ban ma'aikatan gidannan sun gayan Mami bata da lafiya ba, da ba zaka gayan ba haka kuka wuce asibiti tun safe ina matsayin mahaifiyarka amman baka gaya min ba?"
Firgit!
ALIYU ya miƙe zaune yana zuba mata ido wanda har lokacin basu dawo daidai ba.
"Allah ya baki haƙuri Ammi tsananin ruɗewa ce ta saka ban gaya miki ba, Suma Ƴaƴan gidan su Mamin, ita ce ta shaida musu, Sannan Mun haɗu da Khalil a asibitin shi ya faɗawa cikin gidan Baba Madaki, yanzu haka duk mun baro su a asibitin"
Har ALIYU, ya gama maganar Ammi bata ɗauke idanunta daga kallon shiba inda abin da Ammi tafi tsana a duniya bai wuce gidan Baba Madaki ba wanda Yake gida ne na kakannin su ALIYU waɗanda suka haifi Mahaifin su, dukkan ƙannen mahaifin ALIYU  anan cikin gidan Baba Madaki gidajen su yake wanda suke a bayan gidan su ALIYU ɗin wajan galadanci Mahaifin ALIYU kaɗai ya tsallako ya fito daga cikin gidan amman dukkan sauran Ƴan uwan shi suna cikin gidanne.
Wanda Ammi sam bata shiri da Ƴan uwan mahaifin su ALIYU.
"Ka kyauta min da abin da kayi"
Ammi ta faɗi tare da barin ɗakin nashi.
ALIYU a hankali ya koma saman gadon shi ya kwanta sai Lokacin ya tuna da wayoyinshi dake wajan Musa tuni ya kashe wayoyin sabida yasan yadda mutane zasu dame shi da waya shi kuma baya son Magana a halin da yake ciki a yanzu.

Bai tashi ba sai gab da magariba ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito ya sanya jallabiya fara ƙal yay ɓarin turare mai kamshi sosai ya fita masallacin dake harabar gidan nasu yaɗan sami nutsuwa anan ya dinga Gaisawa da ma'aikatan gidan daga nan ya wuce part ɗin Ammi sai dai bai same ta ba wai tana asibiti cewar ƙannen shi ƴammata sajidah da safnah  daya tarar suna kallo a parlo suma dawowar su daga makaranta kenan inda suke karatu a jami'ar bayero dake kano suna lavel 2

Cikin wata ƙaramar honda civic fara ya shiga
A hankali yajata yana driving kanshi bayan ya sanya p cap ya kare fuskarshi sabida gudun idanun jama'a Masu gadi suka hangame ƙaton gate ɗin gidan ya fita da motar dandazon matasan daya gani a ƙofar gidan ne ya bashi mamaki da gudu yaja motar yabar harabar gidan yana gudun kada su gane shine cikin motar.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙarasa asibitin yay horn aka buɗe masa gate ɗin ya shiga cikin harabar asibitin yay parking motar ya fito gudu gudu sauri sauri ya shiga ɓangaran da aka kwantar da Mami matar shi Ya tura ƙofar ɗakin ya shiga ciki tana kwance har Lokacin ga ledojin ƙarin jinin da akai mata sun ƙare an cire Ammi zaune ita da Maman Mami sai ƙannen Mami ɗin duk sun yi tagumi Kallo guda zaka ma Maman Mami kaga suna
yanayin kama da Ammi kasancewar yayarta ce Mahaifin su ɗaya.
ALIYU ya tsugunna ya gaida Maman Mami wadda ta amsa mai cikin kulawa tana mai tashi ta fita daga ɗakin Ammi data masa kallo ɗaya itama tabi bayan maman mami sauran  ƙannen Mami  miƙewa sukai suka fita ɗakin yayi saura daga ALIYU sai Mami dake kwance a saman gado.
*Idan kina buƙatar na tallata miki kayan siyarwar ki a ƙasan shafikan littafin nan kimin magana kai tsaye duk shafi 2 500 naira ne 09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
          
           *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *002*

Cikin sanyi jiki ALIYU ya ƙarasa Bakin gadon da Mami take kwance ya zauna a gefenta, Hannun shi mai taushi ya sanya ya tallafo kanta ya ɗora saman jikinshi ya zuba mata ido tsananin tausayinta ne yake ratsa masa cikin zuciyarshi wanda har yake huda dukkan sassan jikin shi.
Mami idanunta ta lumshe wanda ruwan hawaye ke ta firfitowa da gudu babu ƙaƙƙautawa a wannan karon raunin ta yafi na ko da yaushe bayyana wanda ganin hakan ya ƙara Razana Aliyu sosai ya firgita da yadda yaga ruwan hawayen dake fitowa daga idanun mami Sai dai tsabar kawai ci bai sanya ya bayyana wannan razana tasa a fili ba.

"Kiyi haƙuri Mami, wannan kukan bai da amfani"

Aliyu ya faɗa cikin tattausan lafazi.

Ta ɗago ƙwayar idanunta wadda tai jajir ta kalle shi tana mai ɗauko hannun nashi ta ɗora akan cikinta muryarta wadda ta dashe sabida tsabar kuka ita ke shiga cikin kunnen shi.

"Yayah Aliyu wannan karon ma cikina ya zube, cikin dana ƙwallafa raina akan shi cikin da nake mafarkin na haife shi....."

Sai ta kuma fashewa da kuka!
"Shitt!"
Ya ɗora yatsun sa a saman bakinta ya lumshe manyan idanun shi aran shi yana jin dama shima zai sami damar kukan daya koka dan yaji sanyi acikin zuciyar shi.

Muryar shi mai cike da taushi nagarta gami da haiba ita ke fita ƙasa ƙasa kamar yana yin raɗa, dama shi tun tuni bamai buɗe murya bane in zai yi magana.
"Mami ki shuru wannan kukan naki yana ƙara min zafi acikin zuciyata, Allah ne ya bamu ya kuma nufa bamai rayuwa bane shiyasa ya amsa mu duka haƙuri zamu yi"
Yafaɗa cikin dakiya da jarumta.

Ƙofar aka turo da sauri Mami ta sauke kanta dake jikinshi ta gyara ɗaurin ɗankwalinta Maman ta ce.

Cikin alkunya ta ƙaraso Wajan su taja kujera ta zauna wanda Aliyu yay tsam ya miƙe yana sosa kanshi.
"Aliyu sai fa haƙuri mami taƙi kwantar da hankalin ta, Ni ina ganin wannan kukan kamar harda wauta sabida ba wanda ya isa ya tsaida Allah acikin dukkan al'amuran daya riga ya saukar"

Aliyu ya saki murmushin daya fi kuka ciwo.
"Mama ki barta tai kukan May be, zata ji relief acikin zuciyarta"
Yana faɗin hakan yayi saurin barin ɗakin Ya fita waje ya sami Ammi zaune a saman kujera tana ganin shi ta miƙe.
"Bara nayi musu sallama sai mu wuce"
Daga haka ta kama handle ɗin ƙofar ta shiga Maman Mami tana ta aikin rarrashin Mami Ammi tai musu sallama ta baro ɗakin.

Ƙannen Mami cike da ladabi sukai wa Aliyu sallama, Maman Mami har wajan Mota ta biyo Ammi suna ƙara tattaunawa wanda Maman Mami sai mita take na yadda Mami duk tabi ɗaga hankalin ta.

Ammi ta shiga motar wadda Aliyu ya buɗe mata Ta zauna sosai sannan shima ya shiga Bisimillah ɗauke a bakin shi yaja motar yana ɗagawa masu gadi hannu suka buɗe masa gate ɗin ya cillah hancin motar shi titi.
Motar tayi shuru Ammi ce ta katse shurun nasu ta hanyar ce masa.

"Kadai ci abinci amman kafin ka tawo nan?"
Ya shafa kanshi kamar koda yaushe yace mata.
"A,a ina son sai nayi sallar isha'i sannan sai na ɗan haɗa coffee In sha dan ina son gobe da sassafe zan je Abuja"
Ammi tai jimm kafin tace.

"Ya Kamata ku ƙara komawa wajan wannan Likitan Na ƙasar india akan matsalar ɓarewar cikin nan na Mami ni abinnan har tsoro yake bani ace daga ta samu ciki ana murna kuma sai aga ya ɓare ba wani dalili"

Ta cikin Madubi ya dubi fuskar Ammi wadda ta bayyana da damuwa ƙarara.

Cikin nutsuwa ya furta.
"Ammi babu wata dubara da za'ai akan abin da Allah ya ƙaddara bamai rayuwa bane, wannan rubutu ne tun asali haka Allah ya ƙaddara in muna da rabo Allah zai bamu"

Ammi tana jinjina wa Aliyu ta ɓangaran tawakkali bai taɓa dangana matsalar matar shi da wani abu ba ko wancan karon ma ita ta tilasta musu fita ƙasar india akan matsalar ɓarin da matar sa ke ta samu amman shi koda yaushe faɗin sa ɗaya shine Komai muƙaddari ne daga Allah.

"Shikenan Allah ya baka wani mai albarka ya kuma inganta"
Ammi ta faɗa a hankali.

Shima a ƙasan laɓɓansa ya amsa da.
"Amin"
Motar ta ɗauki shuru titin nasarawa gidan gwamna dama ya gaji haka har suka ƙaraso cikin gari babu wanda ya kuma magana acikinsu dama shi bamai yawan magana bane yawanci shurun sa yafi maganar shi yawa shiyasa wasu ke masa kallon Miskili.

A daidai ƙofar gidan shi yayi parking wasu matane cunkus wasu da goyo wasu ma sunyi bacci akan dakalin Ƙofar gidan Ammi takai duban ta ga matan.
"Kasan dai wannan duk jama'ar kace nidai taimaka ka shigar dani sai ka fito"
Yayi lallausan murmushi ya danna Horn masu gadi suka wangale masa ƙaton gate ɗin ya tura hancin motar shi zuwa harabar adana motocin gidan yayi parking da sauri ya fito ya buɗe wa Ammi motar ta fito ya take mata baya har zuwa part ɗinta.

A parlon ya tsugunna har ƙasa ya dube ta.
"Ammi zan fita na sallami matan waje ko kina buƙatar wani abu ne?"
Ammi taji wani irin farin ciki ya nunku acikin zuciyarta ciki da kulawa tace.
"A,a kaje Allah yayi maka albarka"
Ya miƙe bai koma part ɗin shiba ƙofar Gidan ya koma Da sauri matan suka miƙe suna gaishe dashi babu ƙyama bare nuna cewar shi mai kuɗi ne ya janyo kujerar roba fara ya zauna yana facing ɗin matan.

Ta farko ce ta ƙaraso gaban shi.
"Yallaɓai tunda ga ɗorayi unguwar Bello na tako da ƙafata ina fatan Allah ya haɗani da kai mijina ne ya rasu ya barni da marayu bakwai ina sana'ar wankau yau da gobe sanyi yaci ƙarfin jikina ina ta wahalar magani ga yarana ƙananu ne, takai ta kawo bamu da abin da zamu ci"

Ya dube ta kullum a cikin irin waɗannan al'amura yake kashe lokacinsa.
"Tom shikenan zan baki jarin da zaki sami abin da zaki dogara da kanki sabida ki taimaki yaran ki, ba zan baki kuɗin da bazaki sana'a dasu ba dan zan kashe miki zuciya kuma kinga in yau mune gobe bamu bane ba ina ganin na baki abin da zaki tsaya da ƙafafun ki yafi na baki kuɗin da zakici abinci"
Ya faɗa cikin muryarshi ta dakakkun Maza.
Nan da nan matar ta soma goge hawaye.
"Allah yayi maka albarka, Allah yasa ka gama lafiya, naje gidajen masu kuɗi yakai talatin da wannan buƙatar babu wanda ya dube ni, tabbas in da za'a sami jajurtattu irinka da yawa acikin al'ummah da tabbas bara da sace sace da maula da sun ƙare Allah yasa kafi haka"
Murmushi yayi kawai ya ɗaga mata hannu batare daya ce komai ba.
Ta biyun itama ta matso gaban shi.

"Ni kuma mijina ne, yake aikin saka roɗi agarin ɗora dakin gaba ɗaya ginin ya faɗo masa sama da shekara biyar yana kwance yana jinya duk abin da muka tara ya ƙare"
Ta faɗa tana kuka.
"Share hawayen ki Allah ya bashi lafiya"
Ya faɗa da tausayawa A hankali sauran matan keta ƙaraso wa gaban shi ko wacce da kalar tata damuwar.
Sai da ya gama dasu sannan ya miƙe ya shiga cikin gida jim kaɗan ya fito Da leda a hannun shi ko wacce sai da ya sanya wani daga cikin masu hidimar gidan ya ɗauki sunanta da kwatancenta aka rubuta akan kuɗin da zai bata Kuɗi ne masu kauri ya babbasu yace ko wacce taje ta sami sana'ar da zata tsaya da kanta.

Aliyu yasha godiya wajan matan ya miƙe da kujerar da ya zauna ya shiga cikin gidan yana mai jin farin ciki a zuciyar shi burin sa kullum ya bayar shiyasa Allah bai taɓa hana shi ba.

Yana ƙoƙarin shiga sashin sa Musa dake zaman jiran shi yasha gaban Shi yana rage tsayin sa.

"Musa mai kake har yanzu baka tafi wajan iyalin kaba?"
Musa ya shafa kai yana zaro wayoyin Aliyu daga Aljihun sa.
"Yallaɓai dama wayoyin kane a waje na"
Ya miƙa masa, sallama sukai da Musa Ya kama hanyar part ɗin shi.
Yana shiga wanka yayi ya sauya kaya zuwa singlet da boxer ya sauka ƙasa sanin ba wani ma'aikacin dazai shigo masa Parlo a wannan lokacin tunda gejin su daga magariba ne zuwa Bayan magariba sun jere musu abinci sun bar part ɗin sun koma nasu sai kuma da safe.
Ya shiga kitchen ya haɗo coffee a cup sai turiri yake yana daga tsaye ya shanye shi tas ya aje cup ɗin ya koma saman shi alwala ya ɗauro yay sallah isha'i tare da shafa'i Wuturi sai ya tashi cikin dare ya idar ya jima yana addu'a sannan ya shafa ya cire kayan jikin shi yayi saura daga shi sai dogon farin wando wanda dama baya saka riga in zai kwanta bacci ko takan wayoyin shi baibi ba ya zube su a gefen gadon shi.......*Idan kina so na tallata miki kayan sana'arki a ƙasan shafukan littafina Duk shafi biyu 500 naira kimin magana kai tsaye domin a fara tallata miki hajarki*
09022260850
*RABO YA RANTSE...!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*003*

Pillow guda ɗaya ya matse a saman ƙirjinshi bai rufa da komai ajikin shi ba, dama haka tsarin shi yake duk sanyi baya rufa idan yana bacci kuma baya sanya riga iya kacin shi dogon wando kaɗai, baccin shi yake cikin nutsuwa sabida yadda gajiya ta zirga zirga ta kashe masa jikin sa damma namijin duniya ne wajan gwagwar mayar rayuwa.

Ammi ta ƙarasa bedroom ɗinta bata zauna ba alwala ta ɗauro ta fito daga Toilet Sadiƙ Yayan Aliyu, Aliyu shike bin sa yana zaune a Garin lagos yana kula da kamfanin ALIYU na lagos,Tare yake zaune da matar shi acan Aunty sakinah da yaran shi guda uku mata, yayi sallama cikin ɗakin nata.
Fuskarta a sake ta amsa tana cewa.
"Kaikuma zuwan dare kayi kano kamar korarre"
Sadiƙ ya shafa kai yana dariya.
"Hajiya Ammi tamu, to ki fara bani abinci naci sai muyi maganar data kawo ni"
Ammi tayi murmushi.
"Bari nai sallah tukunna sai na ji dakai"
Ta shinfiɗa darduma a nutse take sallar wadda taja lokaci mai tsayi dama Duk sun san yadda sallar Ammi take ɗaukar Lokaci Sadiƙ har sai da yakai ga yana gyangyaɗi a ƙasan carpet.
Muryar Ammi yaji.
"To sarkin bacci tashi mu fita daga falo sai kaci abincin"
Ta faɗa tana fita daga ɗakin Sadiƙ ya bita suka zube nan ƙasan carpet.
"Lah Yaya Sadiƙ yaushe ka shigo bamu sani ba?"
Cewar sajeeda wadda ta buɗe ƙofar ɗakinsu ta fito tana murnar ganin sadiƙ sabida shi mai barkwanci ne da sakewa ba irin Ya Aliyu ba mai tsare gida sam in ya shigo sashin su basa sake wa har sai ya fita.

Buɗe hannunshi yayi yana dariya yana cewa.
"Zo mana autar Ammi ina safnah?"
Da sauri sajeeda ta ƙarasa jikin Sadiƙ ya rungumeta suna dariya Muryar Bashir Ce ta karaɗe Falon shima Dariyar yake shigowarshi kenan gidan.
"Babban yaya kaine da tsohon daran nan?"
Bashir ya faɗa yana dariya.
Sadiƙ yace.
"Ina naga ta zama mai gida ya kirani ɗazu naji muryar shi babu daɗi dama kullum abu a cunkushe babu fuskar far'a"
Bashir dariya ya saki sabida yasan da wa yake yana nufin Ya Aliyu.
Ammi ma dariyar tayi tana cewa.
"Ina ruwan ubana nina rasa wannan rashin far'a na wa ya ɗebo"
Sadiƙ yayi dariya yace.
"Ammi ke ya gado danni Ammi wani bin in kika ɗaure fuska wallahi har tsoron yi miki magana nake"
Gaba ɗaya Falon dariya aka saki Ammi ta ɗauki Pillow ta jefawa Sadiƙ Ya cafe yana dariya Safna ta fito itama Tafiya tai wajan Ya Sadiƙ tana Murnar ganin shi dan shi yake iya ɗaukar duk sangartar su saɓanin Aliyu da yake cin Ubansu babu sauƙi.

Ammi ce ta miƙe ta nufi kitchen ta haɗowa sadiƙ abinci yana ci ana hira har wajan Sha ɗayan dare Bashir ne ya fara miƙewa yayi musu sallama sabida Gobe

Please Login or Register in order to submit comment